Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bashir dan Allah ka taimaka masa da jari wallahi malam yana cikin damuwa da fuskantar 'kalubale a kauyen nan bai isa nuna wani abu da sunan nasa ba komai ya ta'ba a narke ya rasa inda zaisa kansa hatta yarinyar nan Amatullahi tana cikin damuwar mahaifin ta kullum tana cikin kuka da fad'a min cewa taya zata taimaki babanta wannan dalilin yasa nazo dan Allah Bashir ka taimakawa malam".

"Shikenan aunty kada ki damu insha Allahu za'a bashi jari malam Habu mutum ne na 'kwarai lokacin da kukazo banji dad'in yadda na ganku a rame ba saidai wannan bayanin da kikai min na gamsu dashi zan baki dubu d'ari ki tafi masa dashi a cikin kudin da zanyi zakka ba fitar ki bashi dubu hamsin ki dauki dubu talatin ki bawa kishiyoyin ki dubu goma goma zansa a mayar dake gida a mota zan fad'awa Safiyyah zata zuba kayan abinci a motar ki tafi muku dashi nasan zai ishe shi kice zansa a kawo masa kayan da zai ri'ka saidawa daga baya hakan yayi" sosai Binta tai masa godiya cikin tsananin farin ciki harda hawaye Bashir ya nuna mata babu komai.

Harta mike zata tafi sai kuma ta sake zama tana cewa "karka gaji dani dai Bashir ka taimaka kasa Amatu makaranta tayi karatu yarinyar nan nason tayi karatu babanta ma naso amma rashin kud'i ya hana tun daga secondary batai gaba ba ko zata samu"?.

"Ba matsala aunty kada ki damu ina takardun ta"?.

"Suna nan na taho dasu a jakata" "ki kawo min yanzu na duba idan zan fita zanje dasu a yanko mata fom ta fara zuwa wanne bangare take son karanta"? "Ban sani ba saidai na tambaye ta" "ok shikenan babu damuwa ki kawo min takardun yanzu zan fita" to tace tana mikewa ta fita cikin jin dad'i taiwa Amatu albishir din abinda Bashir yai musu da jarin dazai baiwa malam Habu tsaba farin ciki Amatu fashewa tai da kuka tare da kifa kanta akan cinyar Binta.

Shafa bayanta Binta keyi cikin lallashi tace "kiyi shiru kinji ai a tunani na farin ciki zaki ba kuka ba"? 'Dagowa Amatu tai tana cewa "umma kukan farin cikin nake nasan cewa yanzu shima baba zai samu abin kansa ya rike mu abar yi masa gori da nunensa" kai Binta ta d'aga "eh haka ne Amatu kuma nayi magana da Bashir akan ci gaba da karatun ki yace na kai masa takardun ki zai fita dasu ya miki rijista ki fara zuwa da haka anan zan barki" da mamaki Amatu tace "yanzu zanyi karatu kenan nima zan samu ilimi gaskiya naji dad'i saidai bazan juri sai anyi hutu na ri'ka zuwa ganin ku ba" "a'a Amatu zaki jura dan Allah ki tsaya ki nutsu kiyi karatun ki" "to shikenan nan umma zanyi" "yauwa Amatu Allah yai miki albarka tashi muje ki masa godiya nima inaso zanje miyatti zuwa la'asar na tafi" mi'kewa tai suna fita a d'akin domin suje tayi masa godiyar.


Yana shirin fitowa daga part din nasa suna shiga dan haka yace su karaso main parlon sunyi maganar zama sukai Amatu na kasan carpet da fara'a Bashir yace "Amatullahi kina son karatu ko"? Kai ta d'aga "eh ina so Abba" "ok kada ki damu insha Allahu yau zan fita da takardar ki basai gobe ba zan yanka miki fom ki fara karatu kinji" "to Abba nagode Allah ya saka da alkairi" Amin yace yana shirin mi'kewa ya kuma jefa mata tambaya "wanne 'bangare kike son karanta likita 'yar jarida lauya teacher ko business zaki karanta sauke ajiyar zuciya Amatu tai tana kara yin kasa da kanta ganin batai magana ba yasa Binta cewa "Amatu dake fa ake me zaki karanta ki za'ba yana sauri zai tafi wajen aiki" d'agowa tayi tana kallon mahaifiyar ta sannan muryarta cikin sanyi dan batasan a yadda zasu dau maganar ba tace "SOJAπŸ™Š" "a'a kamar ya soja kuma shine amsar"? Binta ta tambaya tana kallon Amatu kai Amatu ta girgiza tana cewa "karatun bangaren aikin soja zanyi shine buri na" ba Bashir da Binta ba hatta Safiyyah dake gefe kan dinning ita da yaranta sun sha mamaki basuyi tunanin haka ba a d'ari kowa ya zaro ido waje yana kallon ta Nabilah har 'kwaruwa tayi wajen cewa "soja kuma Amatu"? Maryam tace "tabdijan a banza zakije a kashe ki nikwa ko hauka nake ai bazanyi aikin soja ba koni namiji ce balle ina mace" dariya Safiyyah tayi tana kallonsu tace "ra'ayi kenan cin d'an wake da diga kunga laifinta ne abinda ke ranta ta fada" raf raf sukaji ana tafi duk kallon gurin sukai Ahmad ne tsaye da murmushi a fuskarsa yace.

"Haka nake son ji jaruma ta gaskiyar aikin soja babban aiki ne kuma babu wanda zai hana ki cika burinki ni nan da kike gani zan tsaya tsayin daka naga fatan ki ya samu nayi matukar jin dad'in haka Amatullahi kuma na jinjina miki da hannu dubuπŸ˜…" "uhm haka dai ka iya matsoraci ka refaye baki sai zuba zance kake kamar gaske bayan kai aka fara yiwa tayin aikin sojan ka 'ki wai tsoron mutuwa to yanzu fad'a min bakaji kunya ba ga mace a gaban ka tana cewa ita kuma aikin take so"?.

Cikin fuskewa Ahmad ya maze tare da cewa "mom ai ba tsoro ya hana nayi ba kawai aikin ne bana so kullum mutum yana ciki tashin hankali da aiki kamar wani agogo sannan bana son nayi nisa daku" "humm ba wani ka iya yawan gulma ai ya kunun ni'ka yanzu ba hospital zakaje meyasa ka dau wannan"? Ta fad'a tana nuna jakar matan dake hannunsa d'an hade fuska yayi yana cewa "ai kuma mom baza a duba wannan ba nayi mata alkawari ne kuma idan na karya babu kyau ko a addinance bayan haka zataga kamar ba sonta nake ba kawai ina mata yawo da hankali ne" "ok yayi na gaji da surutun zaka iya fecewa kullum kana sanye da farar riga kamar wani fatalwa" dariya yayi yana kallon farar rigar uniform din doctor din dake jikin shi yace "martaba ta kenan ni shine buri na shiyasa itama nake so ta cika nata burin domin nasan da d'aci ka nemi abu baka samu ba" yana kai nan yai waje yana sake cewa "Amatu karki damu in Allah ya yarda zaki cika burinki zaki zama soja wata rana" ita dai Amatu shiru tayi tana jiran hukuncin da Bashir zai yanke mata saidai tana fatan ya amince idan kuma yace a'a dole zatai hakuri tabi son ransa.

"AMATULLAHI" taji Bashir ya fad'a wanda ya katse mata tunani muryarta na d'an rawa tace "na'am Abba" cigaba Bashir yayi "naji abinda kike so ki zama soja indai shine burinki zanyi kokarin cika miki sannan na biki da fatan alkairi da sa albarka a duk inda kika tsinci kanki ki zama mai juriya da tawakkali ki yarda da kaddara mai kyau ko akasin ta kinji" kai ta d'aga "eh Abba nagode Allah ya saka maka da alkairi ya kara arziki" "Amin yace yana mikewa shima ya fita Binta da bakinta ya'ki rufuwa tace "tofa maman masu gida ke kuma abinda kike sha'awar yi kenan soja ikon Allah babu abinda nake tsoro a rayuwa ta kamar naga sojaπŸ˜‚ ashe wata rana zan bud'e ido naga 'yata jini na da kayan sojoji" murmushi Safiyyah tayi tana cewa "ai aunty haka al'amarin yake sai godiya kin gani dai ga Amatullahin ki tace soja take so masha Allah" huuuuuuh sauke ajiyar zuciya Binta tai tana mi'kewa tace "kinga kar zuwa miyattin nan ya shiririce min bari na tashi" katse ta Safiyyah tayi "ai aunty na ta kaina dakin barshi idan naje zance kinzo kina ma gaishe dasu" kaita girgiza "a'a barni Safiyyah dole naje mu gaisa da mahaifanki sun iya bada tarbiyyah tsakanin mu dasu sai son barka irin ahlinku ake nema a had'a jini dasu" murmushin jin dad'i Safiyyah tayi na yabon da Binta kewa mahaifanta tace "shikenan aunty mu gode sai kin dawo ni kuma Amatu tashi ki raka ni yadi gidan 'kawata" to tace tana mi'kewa Nabilah data dauko jaka tace "nima dai momy binku zanyi" hararar ta Maryam tai "baki isa ki rusa min tafiya ba tun shekaran jiya nake bin yarinyar nan ta raka ni na kar'bo dinkuna na tace sai yau kuma dan rainin hankali kice wani bazaki jeba aiko baki isa ba" had'e rai Nabilah "ina ce 'kafa tace bata mutum ba kuma nace na fasa rakiyar ko dole ne"? Kai Maryam ta jinjina tana cewa "mom kina jinta tanai min raahin kunya ko"? Cikin son raba fad'an tace "kinga Nabilah ba'a haka kin manta kome kikacewa Maryam kina so tanai miki idan har baki raka ta ba nan gaba kikaga wani abu a gurinta kina so ko kice ta baki kaza ko tayi miki kaza ni da kaina zan hana ta domin ba kece kika gina ta ba" kwa'be fuskarta Nabilah tayi "ni mom ke nake son bi" "na sani Nabilah kiyi hakuri ki raka ta meye zan taho miki dashi nasan yanzu tayo sarin kaya" Nabilah na kumbura fuska tace "takalmi da jaka sai mayafi shi nake so" "ok karki damu zan sayo miki tashi kuje ki rakata" badan ranta yaso ba tana jujjuya kai suka fita Maryam na balbale ta da masifa "wallahi Nabilah kina bani mamaki wai tsabar wulakanci in kina son abu a gurina kiyi ta min ladabin kura ga mai akuya amma babu komai bari Abbanmu ya dawo zan hada ki dashi" ita dai Nabilah shiru tai tana bin bayanta har suka fita harabar gida ta jirata taje ta dauko motar tana shawo kwana da ita sannan ta tsaya bud'e kofa Nabilah tayi ta shiga suka wuce.

A zaune Malam Habu yake a cikin d'akinsa ya zuba wani uban tagumi mai ban tausayi yayi zurfi cikin tunanin rayuwarsu ta baya tun daga tasawarsu har zuwa yanxu da yake shan wannan ba'kar wahala da quncin rayuwa baisan hawaye yana ta zuba a idonsa ba ko motsi baiyi tsabar nisan dayai da duniyar mutane ya fad'a duniyar tunani da tuna baya yadda rayuwarsu ta kasance kifa kai yai yana rufe ido kawai ya soma kuka sosai kamar qaramin yaro saboda tuno mahaifansu kawai ya zurfafa da tunanin da.

TUNA BAYAπŸ€”.
AYYA ALLAH SARKI MALAM HABUπŸ˜£πŸ˜žπŸ˜”πŸ˜’.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘😘😘

Sai mun sake haduwa idan Allah ya kaimu gobe darai da lafiya zakuji asalin tushen tarihin labarin suπŸ€”.
Reader's baku tambaye niba shin ya akai malam Habu ya talauce πŸ˜”?
Meye asalinsuπŸ™ƒ?
Wanne kalar 'kalubale ya fuskanta a baya😭?
Me ya jawo silar tauyar arzikin sa?

Domin samun amsoshin wadannan tambayoyin ku kasance tare daniπŸ‘‡.

+2348160983083
YUSRAH MUSA ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTYπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ.

We will meet again.
πŸŽΉπŸŽΊπŸŽ·πŸ’ƒπŸ’ƒπŸŽΆπŸŽ΅πŸŽ» Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke shagali 😘 ranar mu tayi haske πŸŒƒ.

TYPING πŸ“² TUE, MAR 5 /24 8:10AM🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈.

πŸ’ŽME KAMAR SARKI πŸ’Ž


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION πŸ’« HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY.


Story and written by
πŸ“šβœοΈMrs al'ameen Ahmad ce 😘.

Tnk u masoya godiya sosai sosai godiyaπŸ’–πŸ’•.

Always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life 🌌 always 🌹.

Be good be helpful everybody will like u to be a happy child like my daughter Fatima Ilham πŸ‘Œ then people will like u.

Ayi hakuri idan an samu typing error matsalar keyboard ne.

πŸ€”Think before you do 🚨


15~AL-KAHHARU
The subduer
16~AL-WAHHAB
The bestover.

8~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Hamidina.

πŸ“šβœοΈYUSRAHMSπŸ’žπŸŒΉπŸ’ƒπŸ‘Œ.

πŸŒ„ REMEMBER ND STRUGGLE πŸŒ„
Episode 15&16
Asalin su duka 'yan wani 'karamin 'kauye ne wanda ya shahara da mutane ba'ki 'yan garin d'ai d'ai ne mahaifin malam Habu ya kasance a wannan garin matan sa uku Salamatu itace uwar gida danta daya Sabi'u sai 'yar tsakiya Ramatu ita ce mai yara biyu Ilyah da 'kanwarsa Lami sai kuma amarya Kulu wato Hauwa amma ta rasu d'anta daya Habubakar suna wata kalar rayuwa a hagunce wacce babu girmamawa ga wanda ka fi hakan kuma ya samo asali ne a wurin 'yar tsakiya Ramatu sam bata da kirki kuma bata da kara batasan meye mutunci ba Baffa mijin su kullum yana nusar da ita yayi yayi ta gane amma ta'ki ta kauda kai.

Zaune suke a tsakar gida kowa na harkar gaban shi wata yarinya ta shigo dauke da farantin talla a kanta tana kuka wiwi kamar ranta zai fita da gudu Ramatu ta fito daga d'aki tana cewa "ke Lami me akai miki kike kuka keda waye wanne d'an iskan ne la'ananne fad'a min yanzu nan naje gidan uwarsa na tsige mata gashin albarka tassss".

Har lokacin kuka Lami keyi ta kasa magana "ki fad'a min uban me akai miki ko shashancin naki ne ya mitsa dama yau naga ba'a son ranki kika fita tallar nan ba".

Kai Lami ta girgiza tana cewa "a'a Innah ba haka bane yaran gidan su Abu ne suke ce wai banyi karatu ba ni jahila ce jaka dakikiya bansan komai ba sai daukar kaya kamar 'yar dako".

Cikin masifa Ramatu tace "kuturun uban can lallai yaran nan akwai matsiyata ba kece jahila ubanninsu ne kwashashshu masu kai duk 'kwar'kwata".

Share hawaye Lami tayi tana cewa "dan Allah Innah na gaji da wannan gorin da ake min ki taimaka ki barni na ri'ka zuwa makaranta ko sau biyu ne a sati".

Zaro ido waje Ramatu tai kamar an fad'a mata abu mai muni har tana make Lamin cikin fad'a tace "uban karatu zaki kinsan Allah Lami indai ina raye bakiyi makarantar boko ba zaki 'kari maitarki ki barni domin tallar da kike yafi min da ubanki zan saya miki kayan d'akin? Dama hakan ne yasa ki dawowa gida da kuka tashi ki koma ko kija abinda zanyi miki tsinannan dukan da sai kin kasa tashi".

Mi'kewa Lami tai cikin ladabi ta sake daukar farantin ta fita Allah ya d'igawa yarinyar hakuri na kwatance kome za'ai mata bata fushi bata nuna gajiyawa.

Daidai zata fita Baffa ya shawo kwanar gida gida suka had'u a zaure ganinsa yasa da sauri ta goge sauran hawayen fuskarta tana cewa "sannu Baffa kawo tabarmar na kai maka" murmushi ya mata yana matukar kaunar yarinyar domin tana da cikakken hankali tun kafin ta mallaki hankalin kanta sake kallon ta yai karo na biyu kafin yace.

"A'a jeki tallar ki kinji zan 'karasa Allah ya miki albarka" "Amin Baffa ta fad'a tana juyawa ta fita shi kuma ya shiga cikin gidan ko bari ya karasa sallama Ramatu batai ba ta soma babbaka fad'a "malam yanzu haka rayuwa take wai 'yan iskan yaran nan gidan can harda tare Lami a waje suna ce mata jahila uban wa aka haifa da sani dama jiran ka nake ka shigo na dauki mayafina naje gidan saina yiwa Jummai tass zagi na tsamar nama domin banga dalilin da 'ya'yan ta zasu hana tawa zaman lafiya".

Ganin ta yayimo gyale daga jikin igiya tana shirin fita Baffa ya katseta Ramatu ina zaki je babu neman izini na" bata saurara ba tace "yo malam ai kaji inda nace zanje indai ba son maimaita magana ba dole na 'kwatawa 'yata yanci cikin 'kawayen ta domin ni ban haifi jahila ba".

"Ban baki izinin fita ba Ramatu ki dawo ai basuyi karya abinda suka fad'a ina jin lokacin da suke fad'an har mutane na cewa kaji gorin da akewa 'yarka tsabar kunya na kasa magana ji nayi kamar nayi nutso cikin 'kasa".

Tabe baki Ramatu tai "yo malam ai ka nutse a cikin 'kasar hakan ma da kyau nikam zuwa zanyi naja musu kunne akan 'yata bazan dauka ba" zata fita ya kuma dakatar da ita da cewa "Ramatu kada kije gidan mutanen nan kiyi musu wani abu Allah ya la'anci mai tashin fitana kibi a sannu idan kinsan farkon sa baki san karshen saba" bata fasa ba tace "wallahi malam saina je saina tabbatar musu na amayar abinda ke cin raina tunda kai bazaka iya ba" tana fadin haka fuuuuu tai waje kai malam ya girgiza batare daya kalli sauran matan nasa ya shiga d'aki cikin tausayawa suka bishi da kallo domin a zahirance Ramatu tana matukar wahalar dashi da halinta.


Mayafi a kafad'a Ramatu ta shiga gidan ganin yaran ta 'yan mata su biyu kawai ta fad'a musu da duka babu neman dalili ko tsayawa tambaya tana masifa "ina tsinannun gidan nan ku fito naci uwar ku dan dambun ubanku jahilci akai ya Jummai da Mamman matsiyata 'ya'yan Allah bani mu huta gori kina ina ba'kar munafika fito nace".

Fitowa Jummai tai cikin mamaki take kallon Ramatu dake ta jibgar 'ya'yan ta kamar ta samu kayan wanki sai ihu suke rai bace tazo tana rufe Ramatu da duka ita nan fad'a ya kaure hayaniya ta cika gida mutanen ma'kota sai shigowa suke tuni akai caaa aka rabasu kowa na tambayar mai ya faru.

"Jummai na huci tace "ina nasan abinda ke faruwa kawai ji nai yara suna ihu ina lekowa naga ta danne su sai dukan su take komai sukai mata oho matsiyaciyar mata kawai" han'kurowa Ramatu tai zata kawowa Jummai cafka mutane suka tare tana cewa "dama taya zaki san abinda sukai min tsinanniyar kanta munafika mai ba'kin hali wallahi bazan yarda ko kijawa yaranki kunne ko jiki yai tsami ina d'an dalili zasu tisa min 'ya a gaba sai ramar ta suke bata da sukuni kamar wata mujiya kullum tana ra'be a gefen dandali bata da wargi hakan bai ishe suba sai sunce mata jahila to ku sani ba itace jahila ba Jummai ce" ta karasa maganar tana sake kai hannu zata cafko yarinyar dake gefe tana kuka tace "zo nan dan uwar ki mai siffar aljanu har nice zanyi magana ki zuro min ido kina kallona.

Mamakin 'karfin halin Ramatu kowa keyi Jummai takai matukar jin d'acin maganganun da Ramatun keyi amma ta dake tana kallon yaran nata tace "meyasa zaku ce wa 'yarta jahila ina ruwanku da ita" cikin kuka Hanne tace "wallahi babah bansan da wannan zancen ba ni a yau ma ban had'u da Lami ba" kallon dayar 'yar Jummai tai cikin fad'a tace "dan ubanki kece ko? ina ruwan ki da ita"? Itama cikin kuka tace "ni fa bani bace wallahi bance mata komai ba" a hangule t Ramatu tace "kuna nufin sharri zatai muku dan darar ubanku"? Haushi ya kama Jummai tace "Ramatu wulakancin ya isa haka sunce basu bane dole saikin tilasta musu sun karbi laifin da ba nasu ba na rantse da Allah bazan yarda ba sai munje gaban me gari yai mana iyaka bani bake ba 'yarki ba 'ya'yana karar ki zankai".


Shewa Ramatu tai tana cewa "kin dad'e baki kaini ba mai garin banza da wofi ai ni kare ya fishi a wajena in kinga dama ki kaini ramin gyare karewar kara aikin banza kawai ina jiranki idan kin fasa kaini uwarki cikin shegen ki tayi ta haife idan kin fasa kaina ba'a haifeki da jini ba idan kin fasa kaini ke ba yar halak bace goyon bola da juji ce ke" tana gama fadin ta sa'bi gyalen ta dake 'kar tai waje kamar wacce ta samu ta'bi sai hararrami take.

Kowa mamaki yake duk da dama sun san Ramatu sani na ha'ki'ka ba mace mai kirki bace wata mata dake kusa da Jummai ce ta kalle ta tana cewa "ke kwa Jummai wanne tsautsayin ne ya had'o ki fad'a da rahma"? 'kwafa Jummai tai cikin takaici tace "taya zan sani Ladi ina d'aki fa naji kukan yaran nan kawai tazo ta rufe su da duka wai sunce wa Lami jahila kiji fa dan Allah gashi yaran da bakin sun ce basu bane".

"Aiko wallahi Jummai karki yarda ki kai kararta gurin mai gari ko ki biya kud'i ki hau mashin kije ki d'ebo mata 'yan sanda domin wannan cin fuskar yayi yawa azo har gidan a zageka a d'aki yayanka" Ladi ta fad'a ranta a'bace "ai basai kince komai ba Ladi dole na kaita kara idan na bari ni banza tasha gaba ma wata tsiyar zata sake tsirowa tazo ta sauke min idan taga ban dau mataki a wannan ba" "a tabbas karki ta'ba yarda Jummai ki kaita kara a yau din nan kice baki yarda ba a bi miki kadin zuwa miki gar gida datai ta dakar miki 'ya'ya" hijab Jummai ta dauka tana cewa "yanzu ma kuwa zanje" fita sukai tare da sauran mutanen da suka zo ceto Jummai ta nufi gidan mai gari.

Ramatu na shiga gida ta aje gyale tare da bud'e randa ta kamfato ruwa tasha ta sake debowa tana jan kujera tace "haba kai sai yanzu naji sanyi a raina da naje na idar musu hankali na ya kwanta mu zuba idan basu gaji da ce wa Lami jahila ba nima bazan gaji da jibgar su ba haba mutum matsoraci ma bai had'u malam kowa ya d'ebo bolarsa kai zai zubawa tunda yaga baka da kata'bus amma idan ka iya masifa zakaga kowa yana tsoron ka" tana rufe baki yaro yai sallama yana cewa "wai malam yana nan"? Lekowa daga d'aki Baffah yai yana cewa "eh ina nan meya faru"? Yaro na kallon yadda Ramatu ke hararar sa yace "malam isubu ne yace wai kaje inji me gari" wani kallo Baffah yaiwa Ramatu kafin yace "jeka ina zuwa" yaro na fita Baffah ya kalli Ramatu yana cewa "sai ki tashi kije aina fad'a miki idan kinsan farkon fitina bakisan karshen taba babu ruwa na a cikin wannan al'amarin duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ke duka indai bazan fad'a miki magana kiji ba nima na zare hannu na daga safgarki" yana fadin haka ya koma daki.

Mi'kewa Ramatu tai tana cewa "bari nidin naje rigima ba uban wanda ta kashe kowa yaci tuwo dani miya yasha ba'ai d'an dazai taka ni na barshi ya huta ba saina 'kaddamar masa da daukar fansa" sa'ba gyale ta kuma yi tai waje matar Baffah Salamatu ta bita da kallo ta gaza gane wacce Ramatu takamaimai mutum ce ko aljan.


Fal ta samu gaban mai gari ya cika da mutane ana jiran zuwan ta ga Jummai a gefe tana zaune da yaranta itama zama tai tana harararsu can ta hango Lami tafi bayanta Iluh ne yaron mai gari da alama a dandali yaje ya kirata bayan sun 'karaso mai gari yace "Ramatu kinsan dalilin kiran ki nan"? Kamar bazatai magana ba sai kuma tace "eh na sani tunda naga wannan ba'kar munafikar tare da yaran ta nasan karata ta kawo" a fusace Jummai tace "kece babbar ba'kar munafika annamimiya mai hana zaman lafiy............................


Katse su mai gari yayi da cewa "ba hayaniya na ce kumin ba sannan bance kuyi zagi na zaga a gaba ba ke Jummai ba ke na tambaya ba ki bari nazo kanki" "kayi hakuri mai gari amma ka hana ta zagina" Jummai na rufe baki Ramatu tace "an zageki tsinanniyar tasha😲" tsawa Bukar ya daka musu cikin fad'a yace "gaban mai gari kuke hatta ko yanzu nan a kira muku hukuma" ta'be baki Ramatu "kai kuma asuwa baka da wannan matsayin ka bari wanda ya isa yai magana zaka kancaro mana jajayen ha'kora wani kai kai gaban mai gari kukeπŸ˜‚ ai mun sani tunda ba makafi bane mu" "ya ishe ki haka Ramatu" Bukar ya fad'a yana nuna ta da yatsa zatai magana taji mai gari yace "wai wannan wanne irin iskanci ne zaku saurare ni ko harkar gaban naku zakuyi shin kun dauke ni mutumin banza ne"? Shiru sukai sai isubu da yace "Allah ya huci zuciyar ka kayi hakuri ayi musu afuwa sunyi kuskure" caraf Ramatu tace "amma dai Isubu na kayan miya kake nema wanda yai lefi baibada hakuri ba sai d'an kallo" "karki 'kara domin ni ba sa'an yinki bane" dariya Ramatu tai kamar zararriya tace "a lallai Isubu wannan ai borin kunya ne idan na kara me zaka iya yi"? Kai tsaye isubu da ransa ya gama 'baci yace "zan kai ki gaban hukuma ne" nan ma dariya ta kuma yi tana cewa "anzo inda nake son ji kaga idan ka turo yan sanda suka kamani 'kalau dani gaba ta kaini dama ina son zuwa garin sarin kayan miya saina saro abina ko ya kace tunani me kyau" kowa kallon mamaki yai mata wato wannan matar ta zama annuba ba mai iyawa da ita.

Zuba musu ido kawai mai gari yai saida gama da akai sa'a Isubu bai sake kulata ba ya kalli me gari yana cewa "kayi hakuri ranka ya dad'e" d'an

Please Login or Register in order to submit comment