Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tanko yace "kuma fa kaima kayi gaskiya da zama irin na gidanka gara mutum ya zauna babu aure na yarda da wannan shiyasa na'ki yin auren tsabar asaranci na zauna tuzuru sai iya kwartanci da 'kananan yara a guna Ina basu kud'i saboda jahilci gaskiya ne Tanko kayi magana anan da irin wannan mutumin gara kai da baka wadata iyalan naka".

Dariya guri ya rud'e kowa yana kallon Mudi Dan kaf gurin sunsan dashi malam Habu yake waye wanda ya'ki aure inba shiba kuma kullum 'yan iskan 'yan Mata daga wasu 'kauyukan suna zuwa masa ansha ganinsu Dan haka bashi da bakin magana balle ya musa kowa cewa yake "Allah dai ya biya Malam Habu gaskiya kana sanya mu nishad'i" Mudi kam sak yayi jikinsa yai la'asar kamar an jefa akuya a ruwan sanyi ransa na turiri gashi yana tsoron yai magana kada Malam Habun ya sake gasa masa wata maganar da zaizo yai dana sani yana kallo malam Habu da Sadi suka bar gurin mutane sai cagwada suke masa amma Saboda yasan halinsa ne tari dabai kamashi ba baiyi ba.

🌃 MARSHALL ISLANDS🌃
Asad yana zaune tare da Isham yana fad'a masa cewa akwai wanda ya gano 'kungiyar kuma mace ce saidai bai santa ba baisan a inda take ba ko 'yar waye Isham ya matukar kad'uwa kuma ya karaya dajin batun yana ganin kamar tunda haka ta faru shikenan Asad yayi losing komai kamar yadda shima Asad d'in a nasa 'bangaren yake jin hakan kallonsa Isham yai yana cewa.

"What do you do now bayan daka gano an samu wacce ta sani a ina take"?.

Kai Asad ya girgiza yana kallon laptop yace "I don't know Isham".

A damuwance Isham yace "amma Buddy mai zai hana kad'au hutu koda na wata d'aya ne ka zauna guri d'aya ka samu nutsuwa kayi bincike a hankali saikafi fahimtar komai".

'Dagowa Asad yai yana kallon sa jin abinda yace cikin nazari kuma yaga kamar hakan shine daidai ya kar'bi hutun ya tsaya guri guda ya samu yayi bincike akan koma wacece kuma dama yana son zuwa gida gurin Abba (mai martaba) daga nan saiya tsaya ya bincika sosai acan d'in ma zaifi samun nutsuwa fiye danan babu takurar Kiran wayar Clarah da damunsa akai akai.....

Muryar Isham ce ta katse shi "Buddy tunanin me kake ko shawaran dana baka batai ba"?.

Kai Asad ya girgiza "no tayi zuwa gobe zanje nayi magana da sir murtih Jonah Ina so zamu had'u da sir Jalalunddeen kafin na tafi domin wannan al'amarin babba ne inaso na tambaye shi ko akwai wanda yazo cikin jami'an mu yace an samu wanda ya gano abinda ake nema Kuma wai mace? Mace dai"? Asad ya karasa maganar da surprise sosai a fuskarsa wanda yasa Isham ya saki dariya yana cewa..

"Oh Asad kaifa yanzu baka shiri da mace tun daga abinda sister d'inka tai maka mine a ciki idan macen ce ka nemeta ka bincike ta ka samu abinda kake so shine magana aiba duka suka taru suka zama d'aya ba akwai matan da zasu saka kayi sanyi Asad".

Isham ya karasa maganar yana kallon yanayin da Asad zai shiga akan abinda yace aiko da qarfi Asad ya d'ago har yana zaro ido waje yace "me kace Isham mace tasa nayi sanyi amma dai ba mace wacce na sani ba"😠?.

'Dan murmushi Isham yai dan tsaf ya gano Asad son bijirewa maganar daya fad'a yakeyi yace "eh Asad mace dai wacce ka sani ba abinda mamaki bane kasan miyasa nace haka? Saboda macen suna ne amma kada kayi musu kud'in goro kowacce halinta daban akwai na musamman a cikinsu".

"Amma irinsu Mami kake fad'a ko? Ina nufin uwaye"?😛.

Dariya Isham yai "a'a ina nufin irin 'yan Mata nake fad'a maka kagane kamar.......

Katse shi Asad yai da cewa "eh na gane abar maganar haka muje inason zamuyi magana dasu a yau Isham gobe nake son tafiya gida".

Cike da tsokana Isham yace "kai Asad da wuri haka aina d'auka sai kamar zuwa qarshen watan nan ko"?.

Kai ya d'aga masa "no da ace tafiya na zai yuwu ayau zan tafi Isham Ina so nayi magana da Abba".

"Ok shikenan Buddy na fahimta muje" mi'kewa Asad yai yana rufe laptop d'in suka fita daga gidan domin suje gurin sir murtih akan maganarsa zuwa gida.


gidan amare
Uhmm Indo/Dauda munzo ganin cin amarci duk da ba'a gayyace mu sayan baki☺️ ba fans ga mota🚗 ga Wanda zaije?😶 kuzo muje nikam zanje zanga yadda ake soyayya🙈🤸.

Indo tana kwance🤭 akan katuwar katifa ta lullu'be jikinta duka amma banda fuskarta idonta biyu suna rufe tanajin qarar 'yar qaramar Tv su dake aje akan wani center table saidai ba barci take ba shigowar ango Dauda😂 yasa da sauri taja bargon tana rufe kanta tare da yin tsit kamar ta mutu zama yai a bakin katifar yana janye abun rufar yace.

"Indo".

Shiru tai ta kasa amsawa saida ya kirata a karo na biyu sannan da'kyar ta amsa amma har lokacin bata bud'e ido ba yana rufe kamar makauniya.

"Ki tashi daga kwanciyar haka ki shirya inafa da mutane zuwa nan da jimawa zakiga sun fara shigowa tayani murna kuma suzo su sameki a haka ai sai kisa naji kunya".

Ita dai shiru tai tana sauraron sa kamar ta fashe da kuka domin da yasan yadda take ji a jikinta da bazaice ta tashi ba kawai ya kakkarya mata 'kasusuwan jiki taya zata iya tashi balle har tayi tafiya............

Tana cikin tunani taji ya d'agota qara tayi tana samai kuka zaro ido yai yana kallon ta da mamaki kafin yace.

"Lafiya meya faru"?.

Cikin kuka Indo tace "nifa bazan iya tashi ba".

Kallon yadda take shashshe'ka Dauda yai yana jinjina kai bai sake magana ba ya mi'ke tsaye yana d'aukarta yai waje da ita domin yanzu kam ya yarda bada banza ba take kuka ba Indo tana da juriya duk abinda kaga tayi masa rauni to lallai ka bincike shi barota yayi a toilet din ya dawo d'akin ya gyara ko'ina ya share ya fesa air freshener😛 sauran kayan marmarin da basu shanye ba ya d'auke yakai kitchen kafin ya koma toilet d'in ya d'aukota yana dawowa da ita d'aki a daddafe tasha tea saboda jin wani mayan zazza'bi yana shirin kamata kawai ta koma kan katifar ta sake kwanciya baice mata komai ba ya tattare kayan suma ya kai kitchen ya dawo yana zama akan doguwar kujera ya maida hankalin sa kan TV Indo kam tana lullu'be batasan abinda yake ba shine madai lokaci zuwa lokaci yake d'agowa ya kalleta har tayi barci ganin haka yasa ya mi'ke yana d'aukar key d'in mashin ya fita zuwa kafin ta farka ya dawo.

INDIA CHENNAI🏥
Wani qwararran doctor ne zaune cikin office gabansa su Ajeeb ne yana musu bayanin halin da Khimiyyah take na cewa insha Allahu shi ya gano inda matsalar take bayan bincike daya zurfafa yayi game da ita wanda sauran likitocin suka gagara ya tabbatar musu da cewa tana gaf da farfadowa saidai bashi da tabbacin zata dawo cikin hayyacinta maybe kwakwalwar ta baza ta'bu sanyi farin cikin jin zata farfad'o amma kuma sunyi ba'kin cikin cewa zata samu ta'buwar kwakwalwa.

Ajeeb dake kallonsa cike da damuwa yace "Amma doctor babu wata hanyar da za'a bi ta dawo cikin hankalin ta bayan ta farfad'o dan saboda akwai matsala ace bata dawo daidai yadda take da ba gashi an d'auki shekaru a haka".

Kai doctor "eh gaskiya babu tabbacin dawowarta yadda take da ba nace zata dauwama a ta'bin 'kwa'kwalwar bane a'a zata iya dawowa daidai cikin hankalinta sosai saidai yin hakan ne zai zamo wahala".

"Ok shikenan doctor yanzu me kake gani za'ayi"?.

'Dan shiru doctor yai zuwa wani lokaci ya d'ago yana kallon su yace "yanzu bansan yadda zance muku ba amma ku bani lokaci akan matsalarku insha Allahu I will try to do my best na ganin ta dawo yadda take maybe idan ta dawo normal zakusa hannu ayi mata wankin 'kwa'kwalwa idan akai sa'a sai a dace".

Kai Ajeeb ya d'aga "ok doctor mun gode sosai muna jira" ya karasa maganar yana mi'ko masa hannu🤝 gaisawa sukai doctor nacewa.

"Ok sai kun jini".

Sannan ya mi'kawa Ameer ma sukai musabaha kafin ya mi'ke suka fito tare zaiyi musu rakiya yana sake basu haske da 'karin bayani har sukazo reception indai Mami da Annur suke jiransu anan Ajeeb yake sanar dasu yadda sukai da doctor yanzu ga abinda yace bayan ta farfad'o za'ai mata wankin 'kwa'kwalwa ita dai Mami shiru tai kawai tana sauraren su suna zancen tsakanin su uku batace komai ba saidai ta damu yarinyar nan ta farfad'o Allah ya bata lafiya subar India su koma gida gashi abin takaicin d'azu ta gama waya da Asad yace mata gobe zaije Nigeria ji take kamar ta barsu Ajeeb taje ta ganshi ya ganta yadda suka dad'e basu had'u ba shekara ba d'aya ba kuma ba biyu ba saidai ba yadda ta iya dole ta danne duk yadda takejin kewarsa a ranta domin yanzu idan taje zatasha magana agun Sultana Hadizah zataga kamar tayi haka ne dan ta nuna ta damu da d'anta shiyasa ta taho tabaro mata tata 'yar cikin halin rai ko mutuwa balle gashi ana zancen wankin 'kwa'kwalwa idan Sultana Hadizah taji hauka ne kawai bazatai ba.

👑EMIRATE👑
Asad kam ya diro cikin masarauta lafiya saidai rashin Mami ba karamin ciwo ya haifar masa ba ji yake kamar yaje Chennai ya ganta saidai yasan idan yaje za'ai ba dad'i shiyasa kawai ya 'kyale bai cewa kowa komai ba abun dai daya bashi mamaki kuma ya faranta masa ransa shine ganin yadda Amjadd ya tsaya tsayin daka ya kula masa da stockyards d'insa tamkar yana nan dan idan ba bud'e masa ido sukai ba gani yai sunyi wani irin girma 'yar giwar nan daya barta a jaririya yanzu itama ta zama uwa balle azo 'bangaren zakinsa humm wannan in ana sallah ba'a magana gashinsa har wani she'ki yake da'kyar yake tafiya tsabar koshi.

Bayan kwana sha biyar mighty Alhussain ne yana zaune cikin parlon sa yana waya da Ajeeb Sultana Hadizah ta shigo ta riski zancen da suke hankalinta ya tashi murna ta rufeta jin wai Khimiyyanta ta farfad'o amma a halin hauka ko bari ya gama wayar batai ba ta fashe da kuka wanda da sauri Alhussain ya kashe wayar yana mata kallon mamaki yace

"Ke kuma wannan sakarcin fa fita anan bana son hauka"?.

Jin abinda yace yasa Sultana Hadizah d'ora hannu aka tana cewa "na shiga uku na lalace shikenan na fito rana yanzun wankin 'kwa'kwalwa za'ai wa Khimiyyah? Asad ya cuceni bazan ta'ba yafe masa ba".

Kai Mai girma Alhussain ya jinjina yana kallon ta yace "Hadizah fita anan kafin kisa na aikata abinda baza aji dad'in saba".

Bud'e baki Tai zatai magana cikin tsawa yace "get of my sight" jin tsawar dayai mata yasa da sauri tai waje tana sake fashewa da kuka.

Takaici ne ya cikashi har a ransa yana kokwanton anya itama Sultana Hadizah bata samu ta'bin 'kwa'kwalwar ba dan yawancin lokuta bata abu na masu cikekken hankali tsuka yaja yana tashi ganin kiran mai martaba Alhassan yasa ya d'aga cikin girmamawa yana gaidashi wanda in kaga yadda yake bashi girma saika rantse da Allah ba rana d'aya aka haifesu ba magana ya masa akan yazo part dinsa yanzu ya sameshi amsa masa yai yana sauke wayar kafin ya mi'ke yana fita zuwa 'bangaren mai martaba a zaune ya sameshi ga Asad a gabansa da alama magana suke zama yai da murmushi a fuskarsa yace.

"D'an gidana yau duk ban ganka ba sai yanzu Ina kaje ne"?.

Gaida shi Asad yai murya a nutse yace "Ina part d'ina aiki nake yi".

"Ok Allah ya taimaka d'an gidana".

Maida hankalin sa kan me martaba yai yana cewa "yaya ka Kira nine"?.

Kai Mai martaba ya d'aga yana cewa "eh Alhussain magana ce akan Khimiyyah dama nace a bari sai Asad ya dawo gida za'ayi ta".

'Dan shiru mai girma Alhussain yai cikin damuwa shifa harga Allah bayaso a ri'ka tada maganar ma sam d'agowa yai yana kallon d'an uwan nasa yace .

"Amma yaya nikam nace abar maganar dan Allah kada a tada zaune tsaye yanzu nayi waya da Ajeeb ya fad'a min cewa ta farfad'o saidai bata hankalinta ba sai anyi mata wankin 'kwa'kwalwa idan akai sa'a zata dawo daidai shiyasa nace a 'kyale maganar komai ya wuce"…

Kai Mai martaba ya girgiza yana cewa "amma meyasa zamu bar maganar bayan kasan me matarka tace tad'au abun da zafi dole mu zauna akan haka amma sai bayan sun dawo daga India ayi komai a gaban kowa karka damu d'an uwana babu sa'banin dazai shiga tsakanin mu insha Allahu mace baza ta ta'ba raba muba".

Sauke ajiyar zuciya Mai girma Alhussain yai yana cewa "shikenan to yaya Allah ya rufa asiri" kallon Asad wanda ke saurarensu yai yana cewa "d'an gidana muje kai min rakiya zuwa wani guri dama nayi kewar fita tare dakai tsawon shekaru".

Murmushi mai martaba yai yana duban Asad batare da yace komai ba Asad ya mi'ke suna fita daga parlon daidai kiran Mami ya shigo wayar Mai martaba ya katse yana danna kiranta ta d'aga suna magana duka dai labarin d'aya ne akan Khimiyyah ne.


🌆KANO🌆
Nurain ne zaune gaban mahaifansa suna masa fad'an ya akai Zainab tai yaji watanni kusa hud'u duk dan ya mayar dasu kakanun mutane shine bai iya zuwa ya sanar dasu ba har saida iyayen Zainab d'in sukaga shirun yayi yawa sukai magana shi kuma Nurain ya nuna musu ga abinda ya hadasu har tayi yajin.

Wani kallo Mum tai masa tana cewa "au kuma dan zaka qara aure tsabar shashanci baka zo kayi magana damu ba kawai saika kama fad'a da matarka wacce yarinya kake so"?.

Shiru Nurain yai cikin fargaba yana kuma addu'a da fatan Allah yasa kada su hana shi idan ya bayyana musu ita...........

Saukar muryar Daddy yaji yace "Nuraddeen ba magana Mumynka take maka ba kayi shiru wacce yarinya kake so a ina take waye ubanta"?.

Cikin d'an samun 'kwarin gwiwa Nurain ya kalli Daddy yana cewa "Daddy Nafisa ce 'yar gidan Alhaji Ilyasu🙊".

Da alamar tambaya Daddy yace "waye Alhaji Ilyasu kuma a ina yake"?.

Da d'an mamaki Nurain yace "amma Daddy mutumin 'kauyen nan da kake turani kar'bo kaya a gunsa muke zuwa da Yazid wani lokacin muje dakai"?.

Kallon sa Daddy yai yana cewa "shi d'in har wata yarinya yake da ita wacce ta isa aure"?.

Kai Nurain ya d'aga "eh Daddy ba ita kad'ai bace akwai wata ma".

"Shi Ilyan yasan kana neman 'yarsa zai baka ita ko kawai kaine kake shirmen ka kai kad'ai su akwai wanda zasu bata"?.

Da sauri Nurain ya girgiza yana cewa "eh Daddy sun sani bata da wani saurayin acan sannan lokaci zuwa lokaci Yazid yana rakani gurinta kuma Daddy Ina sonta da gaske aurenta zanyi dan Allah karka hana sannan Zainab nayi magana akan dawowarta itace ta'ki".

Kai Daddy ya d'aga "ok shikenan ka fara dawo da Zainab d'in zan samu lokaci zuwa nan da karshen watan nan sai muje 'kauyen a kai kud'in gaisuwa karka damu tashi kaje amma kafin nan ku daidaita da matarka ka dawo da ita".

Mi'kewa Nurain yai cikin farin ciki yaiwa Daddy godiya yana fita ya Kira number Zainab amma bata d'aga ba ya sake kira ta katse dayai kira na uku yaji ta rufe wayar d'an tsaki taja yana shiga motarsa kawai ya nufi gidan Yazid domin da har yayi tunanin zuwa gurinta kuma gashi bata d'aga masa kiran ba balle ya sanar mata.

Zainab na zaune tare da 'kanwarta Nanah saidai itama tayi aure ganin gida tazo kuma ta tarar da Zainab d'in a gidan wanda bataji dad'i ba har tana tambayarta cikin fargaba ko sakinta Nurain yai anan take fad'a Mata dalilin dayasa tayi yaji saboda zai karo aure ne kuma ya rasa a inda zaiyo auren sai a kauye 'bacin rai ne yasa ta'ki komawa gidan Nurain din duk da tana son komawa kodan yaranta.

Ta'be baki Nanah tai tana cewa "tabdijan a gaisheki kema dai Aunty Zainab kamar ba wayayyiya ba ni wallahi harkin ban haushi meye abun yaji akan wata banza jaka yar kauye harki zauna anajin kanki da mijinki wace ita? ta shigo miki gida idan bamuci ubanta ba har ki tsaya 'batawa kanki lokaci bayan kina damu dukda ni nayi aure kamar kin manta kinada mimah ga Amira (milat suke ce mata) tab humm harki zauna kina 'batawa kanki lokaci kinsan tunda yasa qulafacin aurenta ba ha'kura zaiba balle kince akwai sanaiya tsakanin mahaifin ta da Daddyn Nurain d'in kinga yajinki banza hakan ba mafita bace gareki to nidai shawarar dazan baki ki koma gidanki kuma ki sake masa kamar komai bai faruba ki d'auke hankalinki daga kan aurensa ki barshi yayi kici uwarta koma wacce tsinanniyar yar kauyen ce daya kawo miki da kafafunta zata bar miki gida".

Kallonta Zainab tai cikin gamsuwa da abinda tace mata ta jinjina kai da wani shu'umin murmushi a fuskarta tace "shikenan Nanah zanyi abinda kikace insha Allahu yau zan koma gidana basai gobe ba bari na Kira shi" ta karasa maganar tana d'aga waya tasa kiransa dariya Nanah tana kallon ta tace.

"Yauwa Aunty Zee Zee na kokefa dakin tsaya 'bata ranki akan wata jahila akuya🙊.

TAB KACE SU ILYAH ABAR HAN'KARA BAKI NAFISA ZATAI KALLO😥😮.

Nurain yana zaune tare da Yazid da matarshi Kiran Zainab ya shigo yaji mamaki matar daya kirata ta'ki d'agawa karshe ta kashe masa waya yanzu kuma itane me kiransa humm kamar bazai d'aga ba saida ya bari ta kusa katsewa ya karasa katseta yana danna Mata kira.

Kallon wayar Zainab tai bayan ya katse murya a sanyaye tace "innalillahi Nanah ya kirani d'azu ban d'aga ba nina jawa kaina my choice bai iya fushi ba gashi ya reject din kirana yanzu ya zanyi"?.

Nanah na shirin magana kiran Nurain ya shigo aiko Zainab da sauri ta d'aga har tana 'kwaruwa tace "hello my choice kana jina"?.

Cikin basarwa dacin magani Nurain yace "Ina jinki ya akai meya faru kike kirana"?.

Zaro ido Zainab tai duk da tasan laifin tane amma saitai 'kas da murya tana cewa "dan Allah my choice kayi hakuri abinda ya faru".

Kamar baisan meya faru ba yace "wani abu ne ya faru kuma a ina miye kike bani hakuri kin min laifi ne"?.

Kai Zainab ta d'aga kamar tana gabanshi tace "eh my choice nayi maka laifi dana kasa tsayawa na fahimce ka amma dan Allah Ina neman afuwarka nayi kuskure inason gyarawa ka yafeni dan Allah" ta karasa maganar da shashshe'kar kukan qarya.

Kai Nurain ya jinjina yana murmushi yace "ok ok shikenan kinga daina kukan komai ya wuce karki damu dama kece baki tsaya kin fahimce niba ai amma yanzun tunda kin gane hakan yayi kyau yanzu Ina uziri zamu qarasa maganar in anjima".

Jin abinda yace yana shirin kashe waya batai abinda yasa ta kirashi ba tace "am my choice in anjima kazo ka d'auke ni"?.

Kai Nurain ya d'aga mamakinta na saukowar datai lokaci guda ya gama cikashi yace.

"Ok no vex ki kula zanzo" yana fad'in haka ya kashe kiran aje waya Zainab tai tana sauke numfashi ta kalli Nanah wacce itama take kallonta tace.

"Kai gaskiya Nanah naji dad'in zuwanki gida yau badan haka ba bansan ya zanyiba tunda Umma tace ba ruwanta Dad ma haka nikuma nace ni na d'auri niyyar qin komawa gidansa sai yazo biko na d'auke masa wuta ashe shirme nake aikatawa da saidai naji yayo aurensa hummm ranar da bansan yadda zanyi ba".

Kai Nanah ta jinjina tana cewa "Aunty Zee nace miki kibar 'bata lokacin ki akan wannan ba'kauyiyar yarinyar wallahi kibar komai a hannu mimah da Meelat sun isheta kawai kisa tunanin ki guri d'aya ki mayar da hankalinki kan mijinki idan kin koma ki nuna masa kamar komai bai faru ba" ta karasa maganar tana mi'kewa ta soma had'a mata kayan ta cikin akwati Zainab na zaune tana kallonta zuciyarta fal da tunanuka iri iri gani take kamar bazata iya abinda Nanan tace Mata ba ta danne ta yarda mijinta ya auro mata wata bagidajiya ba amma zataga abinda zata iya yi akai zuwa nan da fara zancen bikin.

MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CË😘
Nifa I have no girman kai🙆 if you are fushi😡 dani to wallhi you are 'batawa kan k lokaci🤷🙅.

See you next morning nagode🌹 we will meet again💃🤸.

🤝NAJA'AT MUSA ABUBAKAR🤝
'Yar uwata ta kaina jini d'aya Ina yabawa gareki Allah ya kiyayeki Allah ya raya mana babyn mu RAMLAT )(IKRAM)( fatana ki kasance cikin farin ciki a koda yaushe ke&da mijinki IBRAHIM )(LELE)( Allah ya barku tare🤲🙏.


YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

TYPING 📲 Sun, Aug 18/24 7:24AM Little Zarahn Aunty💃🤸🤸.


🌹ME KAMAR SARKI🌹

_______________
_______________________
________________________________
ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ÃSSÕÇÌÅTÍÔÑ 💫 HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY🕊️ gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya 🙅 ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda MA'KIYA NA KALLON KA ramin kura sai 'ya'yan ta🤷 haka taken mu yake🙅.

'YAN UWA MU DAGE NEVER STOP LEARNING BECAUSE LIFE NEVER TEACHING.

57~AL-MUHSI
The numberer of All
58~AL-MUBDI'U
The originator

28~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin nabiyyaz-zakiyat takiyyi.

🌄DISCONTENT-REMEMBER🌄
Episode 57&58
🏙️️DUTSE MOPAL-BASE🏙️
Masha Allah alhamdulillah duk abinda aka sanyawa rana mai karewa ne kamar yau Amatu ta fara karatu gashi yau an gayyace mu graduate tayi murna tayi farin ciki har ba iyaka kuka tayishi ta kara najin dad'in karamcin da Alhaji Bashir ya mata shekara hud'u tana karatu yana kashe mata kud'ad'e daidai da rana d'aya bai ta'ba gajiyawa ba haka Malam Habu tare da Binta suka xo suma sukai masa godiya kai harda mokofcin Alhaji Bashir wanda ya biyawa Amatu wasu kud'ad'e ta zana jarrabawa tare da 'yarshi saida sukai masa godiya da addu'a a ranar malam Habu ya tafi wanda da'kyar ya rabu da Amatu ji yake kamar yace ta d'auko kayanta su tafi saidai saboda karamci ya kyale ya danne duk abinda yake ji ya koma cike da kewarta balle ya dad'e bai ganta ba kusan shekara biyu kenan rabon da suga juna.

🏕️'KAUYE🏕️
________Asabe na zaune ta zuba tagumin tashin hankali gefenta Markah ce sai bata baki take amma kamar gunki ko motsi batai balle fa tayi magana jin muryar Bahijjah tana she'ka dariya ta shigo gidan alamar yanzu iluh ya dawo da ita yasa Asabe zabura tana mi'kewa tsaye daidai Bahijjah ta shigo tana cin cingum da wa'ke-wa'ke ga buhun leda a hannunta fal da kayan irinsu gyad'a ba sallama tazo zata shiga d'aki ciki tsawa Asabe tace.

"Ke daga gidan ubanwa kike bance miki idan kikabi wancan tsinannan yaron iluh karki dawo min cikin gida ba shine wato saboda kin mayar dani ba komai ba kika bishi yau kuwa sainaci ubanki a gidan nan sai kinsan Nima Asabe ba kanwar lasa bace"?.

Ta'be baki Bahijjah tai tana ri'ke kugu tace "to yanzu me kike nufi nakoma gurin sa kenan kome bakya bukatar gani ba? Ai shikenan fad'uwa tazo daidai da zama dama kamar kinsan d'an rabuwar nan da mukai har kewarsa ta kamani bari na koma gurin nasa tunda dama bakya bukata ta me zan miki shi kuma mijina ne aurena zaiyi dashi zan zauna har abada zamana dake na wucin gadi ne haba da Allah malama mace sai takurar tsiya🤥"

Bahijjah na rufe baki ta juya zata fice a gidan Mi'kewa Asabe tai tana kukan kura ta dam'ki wuyan ta tana yar'barta a kasa cike da tsantsan takaici tabi ta take mata wuya hawaye na fita a idonta tace "Allah wadaran halinki da haihuwarki wallahi gara ace 'barinki nayi tun farko zanfi zama lafiya da bamuzo wannan matakin da muke kai yanzu ba amma hakan ma bata 6aci ba gara na kasheki na huta da wannan ba'kin cikin da kike d'ora min Wallahi Bahijjah gara mutuwarki da wannan masifar da kike son jefani a ciki kuma indai ina raye bazaki aureshi ba" ta karasa maganar tana rufeta da duka ta ko'ina.

Ganin da Markah Tai zata kashe Bahijjan da gaske take kamar yadda ta fad'a yasa ta taso da gudu tana janye Asabe dake ta naushin Bahijjah a ciki da'kyar ta 'bam6are ta tayi baya da ita yayin da Bahijjah ta mi'ke da gudu tana kuka tayi waje ko d'an kwali babu akanta balle mayafi ko takalmi.

Zaman dirshen Asabe tayi a kasa tana fashewa da wani kukan ba'kin ciki tare da d'ora hannu aka tana kiran "shikenan nikam na shiga uku na lalace haihuwa batai min rana ba Markah wanne wacce irin yarinya tana neman kasheni lokaci na baiyi ba Wallahi tallahi bazan yarda ba yanzun nan zan tafi gurin boka shashirgi ya

Please Login or Register in order to submit comment