Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya amsa yana hade rai tare da zaro d'ari biyu ya mi'ko mata kaita girgiza tana mikewa tace "a'a dama kawai nazo gaida ku ne sai anjima" mayar kudin sa yai da sauri yana cewa "to to sannun ki da kokari tun kina yarinya kinsan zumunci ki gaida yan gidan naku" to tace tana fita Bara'atu ta tsayar da ita da cewa "Amatu har kin fito ki tsaya na sauke miya kici abinci ga kaji nasan kila yau bakici komai ba tun dumamen safe" juyowa Amatu tai da sauri ta na kallon Bara'atu da mamaki saidai batace komai ba kuma bata nuna ta damu ba tace "a'a nagode sai anjima" ko magana bata bari Bara'atu ta sake yi ba tai waje tana mamaki wato haka baba Ilyah ya koma amma ya taimaki mahaifin ta koda jari ne ya'ki.

Jitai zuwa gidan baba Sabi'un ma ya gundureta ya fita a ranta amma haka ta daure tabi ta gidan su Fatima domin ta rakata duk da gaban ta na fad'uwa batasan me zata tarar ba acan tunda shikam ya riga ya rasu sai matar sa da 'ya'yansa a gidan biyu sunyi aure da daya mara aure da mata uku a d'aki Kowacce da yaranta da sallama suka shiga Innah Rakiya tana zaune gaban murhu tana aikin girki da mamaki tace "a'a mamar kowa da gaske kece kamar a mafarki kai maraba lale sannunku da zuwa keda Fatima ne yar gidan malam Mato can kusa da dandali" tabarma ta dauko ta shimfida musu tana cewa ku zauna zama sukai suna gaida ita cikin fara'a ta amsa musu tana tambayar su can wajen anguwar har ta 'kare tuwan shinkafar da take tai kunu suna zaune domin sunyi yunkurin tafiya itace ta hana su saida suka ci suka koshi ta zuba musu wani tace Amatu taje gida dashi godiya sosai Amatu tai mata cikin jin dad'i da karramawar datai mata domin ta matukar burgeta shimfidar fuska akace ta wuce ta tabarma.

Daidai zasuyi sallama manya manyan motoci guda biyu sukai parking a kofar gidan Ilyah yana tsaye ya fito taryar su sai kancara ha'kora yake dan tabe baki Amatu tai tana kallon Fatima tace "amma ba anan zamu rabu ba zaki karasa gidan mu ko"? Kai Fatima ta girgiza tana cewa "a'a anan zamu rabu zanje gidan baba dala ne" kai Amatu ta d'aga "to shikenan Fatima na gode" sallama sukai ta shiga gida Fatima kuma ta wuce.

Da mamakin ganinta da katon kwano yasa malam Habu cewa "mama na daga ina"? Ya mata tambayar ne duk da shima yasan daga inda take kuma yasan ba kwanon gidan Ilyah bane saukewa tai a gaban sa tana zama kusa dashi tace "baba Rakiya ce ta bani na kawo muku" ta karasa maganar tana bud'e murfin kwanon fuskar malam Habu da fara'a yace "Aiko Allah yaiwa Rakiya albarka ya bata abinda take nema duniya da lahira kamar tasan a yau banci komai ba tun safe haka na wuni"๐Ÿ˜” kallon sa Amatu tai jin abinda yace sunkuyar dakai tai saiga hawaye shar yana zuba a idonta da sauri ta mike tana shiga daki ta dauko kwano tazo deba masa tana ajewa gaban sa tace "baba kaci" kallon ta sosai malam Habu keyi cikin tausayawa tare da ri'ko hannunta yace "Mamana ki daina kuka kinji komai yai farko zaiyi karshe insha Allahu bazan tabbata a haka ba" kai ta d'aga tana daukar sauran ta kaiwa umma kafin tadau kofi ta debo ruwa mai sanyi a randa tana ajewa malam Habu daya nade hannun riga yana kai lomar tuwo sai kallon sa kawai take tana share hawaye tuna abubuwan data gani a gidan baba Ilyah ya tanadarwa ba'kin sa ga d'an uwansa jini daya uba daya amma ya'ki taimakon sa............

Muryar A'i ce ta dawo da ita daga d'an gajeran tunanin da take kallonta tai tana zaune kan kujera a bakin kofar d'akin ta sai cewa take "haba da Allah malam kaji fa wani irin tuwo me mugun dadi amma ace kullum daga gero sai gero ni Allah Allah nake ma dawa tazo mu huta da wannan 'kuncin kullum girki iri daya babu canji kaga kaima malam yadda ka karkace hula kana aiki amma ka noma shinkafar a gonar ka ka'ki kodan ina kaga gonar wata miyar sai a ma'kota" ta tafar sauke ko ci kanki malam Habu bai ce ba sai Amatu dai da take ta jin d'acin maganganun A'i.

Fatima na shiga gidan su Dalah tai turus ta tsaya ganin yadda Balarabe ke surfa bala'i ga Indo
a gefe ta kifa kai tana kuka Asabe data fito a d'aki cikin tabe baki tace "yo ai malam wannan kaso kanka iya dan dukan da zakai mata kenan ni na dauka zaka karya mata 'kafar da take zuwa kwartancin da ita ai anzo har gida an fad'a ranar talatar data wuce karfe sha d'aya na dare wani me mota yazo ya sauketa malam idan bakai a hankali ba Indo zata fi karfin ka kawai ka aurar da ita kafin ta jawo maka abin kunya" cikin fad'a Balarabe yace "to wa ma zai sota a haka kalli fa duk kowa yasan tana bin maza nidai ba gado na kikayo ba saidai dangin Dalah kuma wallahi bari kiji duk ranar da tsautsayi yasa kikayo cikin shege saina kashe ki a gidan nan".

Dad'i ne sosai ya kama Asabe tana kallon Dalah datai tagumi tace "ai malam ga shawara kawai yau da asuba bayan anyi sallah a masallaci ka fad'awa liman ya sanar kana da 'ya zaka bada ita sadaka ka wanda keso sadaki kawai zai biya" shiru Balarabe yai a zabure Asabe tace "tunanin me ka tsaya yi ko shawarar tawa batai ba nasan tayi saidai kace baka so" da sauri Balarabe yace "a'a shawarar ki tayi zanyi hakan yanzu bari na fita majalisar mu shima malam Habu muyi wacce zamuyi ya karasa maganar yana yin kofar fita yana tafe yana magana shi kadai kamar ta'babbe la'bewa Fatima tai tana jiran Saida ya wuce sannan ta shigo gidan da sallama hankalin ta nakan indo wacce har lokacin kanta yake duke tana shar'bar kukan damuwa da takaicin 'kuncin rayuwa.

Kanta taje ta tsaya rai 'bace tace "Indo" da sauri Indo ta d'ago ganin Fatima yasa cikin kuka tace "Fatima me naiwa mutane ne meyasa bani da farin jini kamar wacce mujiya ta a ina fatan mutuwa a wannan lokacin da rayuwa ta" kai Fatima ta girgiza cikin tausayawa tace "a'a Indo kada kiyi sa'bo ki dauka hakan kaddararki ce kiyi kokarin cinyewa sai ki samu mafi alkairin sa".............

Asabe ce ta katse su da cewa "ke munafika uban me kika zoyi gidan mutane"? Ko inda take Fatima bata kalla ta d'ago Asma'u y suka shiga d'akin Dalah mikewa Dalah tai tana bin bayan su sakin gud'a da shewa Asabe tai tana rawa "ahayye nanaye ayuriiiiiiiii abun yazo kaga munafikai zaku fito ne kome kuke kitsawa to wallahi nidai nafi karfin ku idan ma ku mayu ne kurwata tai muku nisa nama na yai muku daci kuma Dalah kisa ido ki gani saina hana ki shan ruwa a gidan nan muje zuwa daya Kenan kuma idan akai munafirci na ban yafe ba" d'aki ta juya tana rera wakar munafirci kunun kanwa uwarku ta fara damawa.

Ba'kin Ilyah sun sauka lafiya kuma yai musu kyakkyawar tarba jiki na rawa daga shi harsu Bara'atu sai son yin gwaninta suke wannan karon Kam Nafisa kwalliya aka yi aka sa kayan 'kure ajiya itace mai kai musu komai idan ta ajiye saita kalli fuskar saurayin dake gefe amma shi ya'ki d'agowa ya kalleta sai zuwan karshe ta mike zata tafi gyalen ta ya zame ya hango breast dinta Dan lumshe ido yai ya sake budewa akan fuskarta daidai ta d'ago suka hada ido ya sakar mata murmushi mamaki ne ya kamata da sauri ta fita yayin daya cire lips dinsa yana sake bin kofar da kallo.
Nafisa kam na fita da gudu ta karasa d'akin su tare dayin tsalle ta haye katifa tana fasa ihu a firgice Salma dake bacci ta farka tana kallon ta tace "lafiya meya faru kike ihu"? Dariya Nafisa tai tana cewa "ke Salma albishir dinki wannan zuwan anzo da wani saurayi naga sai kallo na yake yana murmushi watakila Sona yake kai wayyo Allah, Allah yasa da gaske ne dan ina matukar son zaman binni kinsan da dad'i kalli fa su yaya Hassan tunda suka tafi kin jisu shiru suna can suna jin dad'in su" tabe baki Salma tai tana cewa "umh umh fa kinga Nafisa ki kiyayi kanki yan binni wayo garesu wallahi kada ki saki jiki dashi ya saki kuka wata rana nidai na fad'a miki" had'e rai Nafisa tai tana hararar Salma tace "kinga goggo Salma idan bazaki bani karfin gwiwa ba kada ki karya min zuciya mu tsaya iya haka nikan yayi min ina son shi" cikin haushi Salma tace ai saiki je ki fad'awa baba ya aura miki shi inga karshe rashin kunya" gyara zama Nafisa tai tana cewa "meye abun rashin kunya bayan na gani ina so kinga kema ta dalili na zaki shiga binni kiga yadda yake" mikewa Salma tai zata fita a d'akin tace "Allah ya kiyaye kema dan bakisan ciwon kanki bane ina fata ki gane da wuri" shiru Nafisa tai tare da bin kofar da Salma ta fita da kallo saidai tafi tunanin ko Salma kishi da hassada take mata.

Tana nan zaune har Salma tayo alwala tazo zatai sallah ita kuma sai powder data kara daukowa tana sake fante fuskarta Salma na shigowa Bara'atu tai sallama tana cewa "ke Nafisa kizo baban ki na Kira baki zasu tafi an gama loda kaya daya daga cikin yace yana son zakuyi magana Allah yasa yace yana sonki ki fita zakka a kauyen nan ki auri dan binni mai kud'i" jiki na rawa Nafisa ta mike tana fita cikin zumudi bayan Salma ta shafa addu'a ta juyo tana kallon Bara'atu tace "amma umma wannan fa kuskure ne take aikatawa ya daga ganin mutun ba sanin sa akai ba kawai tace zata aure shi tasan halinsa ko baba nasan baisan komai game dasu ba iya kaci suzo da kud'i ya siyar musu Kaya su tafi dan Allah umma ku tsaya ku duba" wani kallo Bara'atu tai mata tanacewa "ke jimin yarinya da shishshigi me kike nufi dan kawai yazo daga binni kuma yace yana son ta saimu 'ki amincewa dashi"? "Eh ina tunanin abinda zaije ya dawo ne kuma ku idan yace zai aureta zaku bashi ne"? "maizai hana zai kashe tane"? Kai Salma ta girgiza "Amma umma a tsaya ai bincike kafin a amince masa" kallon ta Bara'atu tai "kinga Salma saurara meye damuwar ki ke ba kince kinfi son zaman kauye ba to saiki kyaleta itakam sai rayuwa a maraya" shiru Salma tai bata sake cewa komai ba itama Bara'atun haka.

Da sallama Nafisa ta shiga d'akin ba kowa shiru saishi zama tai dan nesa dashi yana kallon ta yace "barka da wannan lokaci kyakkyawa a gaskiya kin iya kwalliya kallon ki yasa na kasa furta kalma daya amma dai zanyi miki tambayoyi uku ki bani amsa, na farko mene sunan ki"? Ya fad'a yana kafeta da ido duk jitai ta takura da'kyar tace "Nafisa" a bakin shi kamar shine ya rad'a sunan ya maimaita "oh Nafisat nice ne, tambaya ta biyu kinji nai miki kina sona? tambaya ta uku zaki aure ni"? Ina jiran ki amsa hajiya Nafisa kece mace ta farko da naiwa kallo d'aya naji na kamu da cutar sonta kuma ina fatan kema zaki amince min"?.

Zaro ido tai tana kallon sa tace "da gaske sona kake"? Kai ya d'aga mata "eh sonki nake irin ainun dinan fatan kema haka kina yina"? Cikin wawanci ta fara dariya wanda shi mamaki ma yasa ya tsaya kawai yana kallonta saida ta gama yace "yadai kiban amsa zamu tafi jira na suke" ko kunya balle kara haka Nafisa tana kallon idanuwan shi tace "eh ina sonka kuma zan aureka domin ba abinda nake so kamar zaman binni" wani kallo ya mata to maye abin son zama a birnin ko'ina ba gurin rayuwa bane gira ya dage tare da mikewa yace "shikenan to nagode da so zamu tafi" itanma mikewa tai suna fita tare saida tai masa rakiya har waje ya shiga mota suka wuce Ilyah sai yan'kare baki yake yana annaahuwa ganin dayai Nurain ya nuna yana son Nafisa yasan yanzu zai sake zama me dukiya fiye da da idan ya samu ta aure shi.

Gida suka shiga yana kiran Bara'atu d'aki gata ga Nafisa yace "to batu ne game da zancen Nafisa ga dai yaro Nura dan gidan alhaji Tajuddeen ya ganta ya yi maganar yana sonta to ni abinda nake so anan shine ku bani goyon baya d'ari bisa d'ari mu jajirce mu tabbata Nafisa ta aure shi ta fita daga kauyen nan ina da tabbacin wata rana sai munyi zaman binni mun bar wannan karkarar tun ta iyaye da kakanu domin ban aje kowa ciki ba daga ni sai ku iyalai na bani da wani 'kani ko d'an uwa Habubakar ne kuma shi gara kare ma dashi a gurina".

Dariya Bara'atu tai tana cewa "gaskiya ne malam ka fad'i gaskiya idan muka samu Nafisa ta aure shi mun samu kofar arziki ba karama ba mutanen dake da miliyoyin kud'i a banki a boye" cikin nuna son zuciya Ilyah yace "to kin gani dai nasan 'ya'yana suna da 'kashin arziki yanzu abinda za'ai shine ke Nafisa idan sun sake dawowa kice ya sai miki waya wacce zaku ri'ka magana kinji kuma ki tabbata kina tatsar sa kudade domin baisan ciwon su ba" "to baba" Nafisa ta fad'a tana mikewa ta fita sai murmushi take ita kadai farin ciki ya ishe ta har ji take wata sabuwar iska mai launin sanyi tana shigarta.

Karo sukai da Salma zata fita tare ta Nafisa tai "ke ina zaki je haka ko gurin wancan saurayin naki me kama da tuntu'be shine kike wannan saurin kamar zaki tashi sama anji kunya" wata uwar harara Salma ta sakar mata tana cewa "akwai wanda yaji kunya irin ki kawai tsabar gidahumanci daga ganin mutun ba sanin sa kikai ba babu binkice kawai kice wai kina sonshi" rama hararar Nafisa tai tana cewa "eh haka nake kuma son kayana kuma banga abinda zai hana na aure shi ba sai mutuwa" wucewa Salma tai cikin jin haushin ta tace "au aina dauka mutuwar ma bazata hana kiba nidai yar uwarki ce ta jini a matsayi na namai sonki nake fad'a miki kibi a sannu" da kallo Nafisa ta bita tana tabe baki tace "ji shegiyar yarinya waini zatai wa wa'azi bazan bi a sannun ba da karfi zanbi sainaga wanda zai hana haba Salma na fahimci ba'kin ciki kike dani kuma saidai ki mutu domin mijin dazan aura ya kere naki kyau dan dadai ne babu inda ya zarta ba irin naki ba tudu da gangare yana tafi kamar agwagwa zaki dawo ki same ni" ta karasa maganar tana shiga d'akin su ta kwanta tare da rufe ido kawai tana tunanin Nurain a ranta.

Fatima kam daga gidan Dalah kai tsaye gidansu ta wuce Aliyah babarta na zaune ganin yadda ta shigo yasa tace "Fatima lafiya naga kamar kinyi kuka"? Zama Fatima tai sai ajiyar zuciya take saukewa cikin takaici ta soma magana hawaye na zuba "yanzu tsakani da Allah umma babu wanda zaiyi magana sai baba Balarabe ya kashe Indo da duka yau ma baki gani ba yadda ya sata a gaba yana tsine mata da debe mata albarka wai Asabe harda zuga shi idan yaje masallaci ya cewa liman yai shela duk wanda yake neman mace sadaka yazo ya aure masa ita" dafe kirji Aliyah tai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un yaushe hakan ta faru wai Balarabe meke damunsa ne da dai ba haka yake ba amma yanzu gabadaya ya gama canzawa kamar mai aljanu lallai da alamar tambaya kinga ki daina kuka Fatima tashi kije ki sallah maza kizo na aike ki gurin Kande ki ce ta bada kudin adashen nan ita kadai ake jira" to Fatima tace tana mikewa yayin da Aliyah tai tagumi cikin tausayawa yar uwarta Dalah da kuma halin da Indo ke ciki saidai tana fatan Allah yasa Dauda ya dawo da wuri insha Allahu tana sa ran zai auri Indo yarinyar nan ta huta da kuncin rayuwa.

Suna tafe a mota Nurain dake kallon photon Nafisa daya dauka bata sani abokinsa Yazid ne yadan daki kafadarsa yana cewa "kai mutumi na kaji tsoron Allah idan har kasan ba son yarinyar nan kake ba karka yaudare ta kaga kuna yi da mahaifinta" dariya Nurain yai yana kallon sa yace "amma ai kasan nima da yaudarar ce bazan ta'ba furtawa ba tunda tasan yadda Daddy suke da babanta kawai haka nan naji ina sha'awar ta domin tana da kayan aiki kuma zan aureta" kai Yazid ya jinjina yana yana mayar da hankalin sa kan tuki yace "amma fa baka da kirki ko kadan kasan madam din ka akwai bala'in kishi tasan da wannan maganar saita kusan kone maka gida" tabe baki Nurain yai yana cewa "dama ai ba da ita kadai zan zauna ba ni mijin mace hudu ne innaga dama a yau naso auren Nafisa zanyi" "umh umh fa Nurain banda cika baki" "to zuba ido kasha kallo muna dawowa daga tafiyar da zamuyi da ita zan auri Nafisa" Yazid dai jinsa yake amma yasan karya ne saidai kawai zai kyale shi kada yai masa magana yaga kamar ya takura shi.

Har suka isa cikin gari kai tsaye gidansa ya wuce a parlor ya samu yaransa guda biyu suna zaune da littafi a gaban su babbar tana koyawa karamar zama yai yana cewa "Amnah ina momyn ku"? D'agowa Amnah tai tana kallon sa tace "u're welcome Dad Mom na gurin aiki bata dawo ba" sauke ajiyar zuciya yai yana mikewa ya shiga part dinsa baifi minti biyar ba ta shigo cikin parlon ganin yaran basu lura da ita ba yasa tace "auta na karatu kuke ya school" duk d'agowa sukai suna kallon ta da gudu suka je suna rungumeta cikin shagwaba karamar tace "ni momy yunwa nake ji" kallon fuskarta tai "oh sorry dear ina Falmata batai lunch bane"? Ta karasa maganar tana kallon dining ga kuloli nan alamar an gama rike hannun ta tai tana cewa "muje nayi serving dinki" kafada ta ma'ke tana cewa "ni mom biscuits da ice cream nake so" daukar ta tai suna zuwa gaban fridge ta bud'e ta dauko mata kafin tace "Daddy ya dawo daga kauye ne" kai Amnah ta d'aga "eh mom ya tambaye ni ma kin dawo office nace a'a" jin haka yasa ta wuce gurin sa tabar yaran anan baya bedroom ya shiga wanka dan haka fita tai zuwa nata part din itama ta shirya kafin ya fito.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE ๐Ÿ˜˜

Yau kam nayi muku typing da yawa dan haka bazan sake yin posting ba sai ranar monday idan Allah ya kaimu da rai ya bamu aron numfashi da kwana.

YUSRAHMS.

Be good be helpful than everybody will like u to be a happy child like my daughter Fatima Ilham.

Mrs al'ameen Ahmad ce
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

Ai littafin me kamar sarki bangarori ne daban daban zaku Sha labari kudai kawai ku taya ni da addu'a Allah ya bani dama da lafiyar yi muku typing da posting.

Mu kwana lafiya gaskiya zanyi kewar ku masoya ina mi'ko sakon godiya da gaisuwa ta gareku.
Batilah Abdullahi
Rakiya Abdullahi
Ruwaina Abdullahi
Surayyah magaji
Sadiya Khabeer
Ummi Ibrahim
Asma'u Abdullahi
Bintu 'Dalha.


Sai iyaye masu daraja girma hakuri kwazo Allah ya kara ri'ka muku ya tsare ku daga sharrin dukkan abun 'ki ya bamu rahmar sa duniya da lahira amin.
Mama Hauwa
Umman fati
Umman Basiru
Umman Suraj
Umman Huzaif
Umman usman
Maman baby
Maman Fadilah
Maman Maryam
Umma Habiba
Umma Addah
Sai kuma kaka mai kamar uwa kimin komai a rayuwa ta fatan Allah swt ya tsare ki ya kiyaye ki ya barmana ke ki kara tsahon kwana.
AISHATU SHU'AIBU๐Ÿคฃ
SHU'AIBU MAI ALEWA๐ŸŒน๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒนโœจ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน.


โœ๏ธJinjina nake gareku yan group din mu na ANNURI marubuta Allah ya taimaka ya rikar ido yai karko basira ta karu hannu kada ya kosa alkalami yaita zayyanowa.
Safiyyah Aliyu wakili
Hajjara Abla's Glam
Rahmat A Abba Jada
Rabi'at bichi
Mrs Abubakar
Chp~ melody
Indo ce kano.

Mrs AL'AMEEN AHMAD CE mai tambarin yma dutse Jigawa new world new life and new style ๐Ÿ‘Œ.

5~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil 'Da'ina.

################
##############
###########
#######
####
###
##
#

TYPING ๐Ÿ“ฒ {9:44AM 18/24}โœจโœจโœจโœจโœจโœจโœจโœจโœจโœจ

๐Ÿ’ŽME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž

๐Ÿ’ซ ANNURI WRITER'S ASSOCIATION ๐Ÿ’ซ.


09~ AL-JABBAR
The irresistible
10~ AL-MUTAKABBIR
The majestic ๐ŸŒน.

Dedicated to
Mr HAUSA EBOOKS ๐Ÿ“š
SHURAIHU CEO๐Ÿ“๐Ÿ“’๐Ÿ“”๐Ÿ“•


โœ๏ธYUSRAHMS ABUBAKAR
Mrs Al'ameen Ahmad ce๐Ÿ˜˜


๐ŸŒ„SESSION ND REASSURE๐ŸŒ„
Episode 09 & 10
Marshall islands misalin'karfe daya da rabi na dare ko'ina da haske ๐ŸŒƒ gari yayi tsit ba motsin koda tsuntsu zaune Asad yake da phone a hannun shi tun karfe bakwai yake kiran wayar Mami amma bata daga ba karshe yanzu daya kira sai yaji switch up gabadaya ya damu ya sani dama za'ai haka Mami tayi fushi dashi wurgi yai da wayar daidai Isham ya fito daga bedroom cikin zafin nama yai tsalle yana cafe ta tsuka Asad yai yana zamewa ya kwanta kan lallausar cushion din tare da rufe ido.

Mamaki ne ya kama Isham me Asad keyi har yanzu bai kwanta ba zuwa yai kansa ya tsaya cikin alamun tambaya yace "buddy what is it? Said you wanted to talk, but haven't said a word, what happened"? Shiru yai bai bashi amsa ba duk da dama haka yake tunani "Asad ka fad'a min meke damunka ko akwai wani taimako dazan iya yi maka"? Batare daya d'ago ko ya bud'e ido ba yace "don't know how this happened" da mamaki Isham yace "haba buddy kamar ya bakasan me ke faruwa ba? me ne ya hana ka bacci? shine abinda nake son sani".

Tashi zaune Asad yai yana barin wurin ya koma jikin window ya tsaya yana kallon waje da ko'ina ya mamaye da haske kafin ya fara magana "nayi kiran Mami a waya amma ta'ki d'aga min" "ta'ki d'aga maka kira maybe bata kusa ne" kai ya girgiza "no tana wurin" "to kenan laifi kai mata"? Isham yai maganar yana karasawa inda yake ya dafa shi yana cewa "meyasa baka tsaya saida ka bata hakuri ba ka taho"? "Wai Isham wa ya fad'a maka laifi na mata kawai an samu sa'banin fahimta ne tsakani na da cousin dina" cikin tsokana Isham yace "tofa ashe harka fara soyayya bamu sani ba ko aure zakai n...................

Bai karasa abinda yake son cewa ba sakamakon naushin da Asad din ya kawo masa da sauri ya goce yana cewa "which rubbish is this"? Har lokacin hannun na nan a dun'kule yana kallon Isham din amma baice 'kala ba ya baro window yana dawowa tsakiya parlon yace "dan nace maka cousin dina ce kawai zakai min hauka a duniya akwai wanda naji na tsana irinta" hararar sa Isham yai yana cewa "ba wani ni fa bana son cika baki shi so ba anan yake ba Asad ka daina fariya" "Isham indai akan Kimiyyah ne zan bugi kirji nace Allah ya sauwake domin wallahi badan Mami ba jiya da yanzu tana kabari" zaro ido Isham yai "kaii Asad cousin din taka guda zaka kashe lallai na jima banga mai zafin Zuciya irin ka ba dole Mami tai fushi dakai" tsaki Asad yai yana cewa "wa ya fad'a maka fushi tai dani ban ta'ba aikata laifi Mami tayi min fushi ba saidai tai min nasiha" "to ai baka ta'ba irin wannan a gaban su ba kisa fa kaso yi Asad a gabansu dole kasan Mami tayi fushi dakai" kai Asad ya girgiza yana cewa "Mami bafa irin wacce ka dauka bace baza tai fushi dani ba akwai dalilin dayasa bata d'aga min kira ba na sani na bari zuwa gobe zan sake kiran ta".

"Shikenan buddy, amma baka fad'a min ba taya ka samu sunan wannan 'kungiyar da location dinta sannan mene shirin su me suke aikawa a sirrince dahar kowa da kowa yake kokarin ganowa asirin su shin da akwai wata alama da zamuyi amfani da ita"? Kallon sa asad yai batare daya bashi amsa ba sai rufe ido dayai a iya sanin Isham yasan yadda Asad ya kwallafa ransa da sai ya gano asirin 'kungiyar nan ya hana kansa bacci ya

Please Login or Register in order to submit comment