Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kure musu suba masana daji ba basu San karshensa ba yasa malam Habu yaiwa fulanin sallama yace zasu d'ora tafiya tambayarsa sukai inda zaije daga yace shima bai sani ba yana son fita dai daga dajin ya samu hanya ne dan haka sukace masa ya tsaya ya kwana gaskiya yanzu idan yace zai fita a dajin dare zaiyi masa saidai gobe da safe su sashi a hanyar inda ya kamata yabi godiya ya musu sosai kuma yayi farin ciki da karamcin da suka nuna masa dashi da Iyalansa.

Washe gari da safe bayan sun karya sukai wanka a gidan domin tunda suka baro gida yau kwana uku babu wanda jikinsa yaga ruwa inba na alwala ba bayan sun gama shiri haka d'an fulanin ya wuce gaba domin ya fitar dasu a dajin harda matarsa suka tafi saida suka kaisu ga'bar dajin suka sasu a hanya sukayi musu kyakkyawan kwantance inda ya kamata subi sannan sukai bankwana harda basu dubu goma d'an fulanin yayi yace malam Habu yai 'karin guzurin tafiya Allah ya tsare ya kaisu lafiya duk inda suka nufa ya saukesu cikin sa'a godiya sosai Malam Habu yayi musu har saida sukace masa ya isa babu komai kafin suka sake gaisawa da sallama suka wuce su kuma fulanin suka juya zuwa gida.

Kamar yadda sukai musu kwatance haka suka ri'ka bi sannu a hankali duk wata alama da fulanin suka fad'a musu zasu gani sun gani har suka samu suka fito daga dajin sai gasu a wani karamin gari wanda ba mutane da yawa wani mutum da suka fara had'uwa dashi Malam Habu ya tambayeshi dan Allah nan wanne gari ne ya fad'a masa sunan garin yayi masa godiya sukai gaba a wannan garin ko zama basuyi ba suka tari 'yan mashina malam Habu yace su kaisu bakin titi inda zasu samu mota.

'Daukarsu sukai a jere bayan an gama ciniki suka fita dasu daga garin suka kaisu bakin titi wajen 'yan yuniyan masu tsare mota biyansu hakkinsu malam Habu yai sannan yaje gurin yan yuniyal d'in yace musu Kano zaije to sukace masa amma ya jira kafin a samu mota komawa yai ya zauna zuwa wani lokaci da aka samu mota kamara ce ma taxi🚗 babu kowa a ciki suka tare masa ita aka saka musu kayan a but sannan suka shiga bayan direban ya sallami 'yan yuniyal d'in ya shiga suka tafi.

A hanya yake tambayar su wacce anguwar za'a kaisu malam Habu yace shi baisan sunan anguwanin Kano sosai ba idan badan yanajin radio ana fad'ar wasu ba murmushi driver yai yana cewa "nima kuwa kaga ba d'an Kano bane daga yola na taso na dawo nan farko bakaga irin wahalar danasha ba kafin na zama d'an gari a farawa nafara zama ina haya mai gidan ya tashe ni ya zuba wasu tsabar wulakanci ba laifin tsaye bana zaune ba hanashi kud'in hayarsa nake ba amma ya tozarta ni daga nan na tashi na dawo d'orayi a nan ma mukai fad'a da Alhajin da nake hayar a gurin sa nan shima dai ya koreni yanzu maganar da nake maka Ina anguwar kabuga jan bulo na samu wani d'an arziki tunda na kama hayar gidansa ko banida kud'i yana d'aga min kafa kusan shekara goma maganar da nake maka a yanzu idan za'a kar'bi kud'ad'en hayar gidajensa ni yake wakiltawa ya yarda dani fiye da yadda kake tunani ko wannan motar da kake gani shine ya saya min nake haya kuma kwata-kwata a wata cewa yayi na ri'ka bashi dubu goma ai kafin a samu irinsu Alhaji Abubakar masu kyawawan zuciya za'a tona suna wuya a yanxu Malam humm".

Shiru Malam Habu yai cikin tunani ko yai nasa magana idan zai hadashi da Alhajin? Eh kawai ka tambayeshi tunda bakasan inda zaka samu sa'a ba jin zuciyarsa ta bashi shawara yasa ya d'ago yana cewa "a wata nawa kuke biya kud'in hayar"?.

Kai driver ya jinjina har malam Habu ya tsorata ya d'auka kud'ad'e za'a fad'o masa sai yaji yace "ba wata wata ake biya ba yanayin yadda ka kama gidan dakuna biyu da toilet da kitchen dubu d'ari ne a shekara".

Sauke ajiyar zuciya malam Habu jin sai shekara ma ba duk wata ake biya ba yace "ko zaka had'ani dashi idan munje kano d'in Nima dama bansan inda zanje ba banida kowa bansan kowa ba kawai daka na taho neman kud'i".

Kai driver ya d'aga masa yana cewa ''ok ba matsala amma gaskiya yanzu baya gari yayi tafiya zuwa wata 'kasar sannan indai ba yana da wasu gidajen a wasu anguwanin ba bana tunanin akwai sauran wanda suke empty ba mutane a ciki gaskiya ba lallai ku samu ba yanzu wacce anguwa zan kaiku"?.

Shiru Malam Habu yai jikinsa yayi sanyi har saida ya sake tambayar sa sannan yace "kaimu can anguwar da kake meye ma sunanta"?.

"Jan bulu" driver ya fad'a yana kallon sa.

"To ka kaimu can Allah ya dafa mana🤲" Amin driver yace🙏 daidai sun shiga Kano ya tsaya yasha mai kafin ya tashi mota ya d'ora tafiya zuwa wani lokaci ya shiga anguwar saida ya samu inda ya kamata ace ya saukesu gurin da ba fuskar mutane ba inda yake da wani kango sannan ya tsaida mota suka fiffito ya bud'e but ya sau'ke musu kayansu Malam Habu ya biyashi yayi masa godiya sannan drivan yace masa karya damu zaiyi waya da Alhajin zai tambaya masa idan akwai zuwa Nan da karfe goma na dare zai ganshi ya dawo gurinsu to malam Habu yace masa ya sake masa godiya.

Bayan driver ya tafi suna nan zaune kamar marayu umartarsu Malam Habu yai cewa su tashi su shiga cikin wannan kangon suyi sallah amma karsu shiga da kayansu tunda ba tambayar meshi sukai ba ya sayo musu ledar pure water guda biyu ya kawo musu kowa ta d'auka tai alwala sukai sallah yana tsaye yana jire musu kayansu saida suka fito shima yayi tasa alwalar a matsayinsa na ba'ko baisan ko'ina ya tafi neman masallaci daka ya samu akusa yayo sallah ya dawo sai kuma yunwa da take damun kowanne nan kuma birni ba qauye bane balle ace za'aga masu abincin saidawa a layi suna yawo dashi nan saidai restaurants ko masu saidawa a shaguna.

Sunata zaune zaman jiran tsammani har wani yaro yazo wucewa da bokiti a hannunsa tambayar sa malam Habu yai.

"Kai anan garin a ina ake sayar da abinci"?.

Kallonsa yaron yai yana cewa "babu inda ake sayarwa saidai kaje gidan cin abinci".

Kallon bokitin hannun nasa malam Habu yai ga kuma fork da plate🍽️ dan haka yace "kai me kake sayarwa"?.

Amsa yaron ya bashi "gurasa ce mai 'kuli amma ta kare saina d'ebo wata zaku saya"?.

Kai malam Habu ya d'aga "eh zamu saya idan ka d'ebo ka kawo mana kayi sauri yanzu" to yace yana yin gaba ba'a dad'e ba ya dawo ya ciko bokitin yace guda d'aya d'ari haka suka saye masa ita du saida bokitin ya koma gida.

Har bayan sallar isha suna nan zaune shiru shiru sunata jiran drivan nan daya kawosu ya dawo ya fad'a musu ko an samu amma har dare yayi nisa kusan karfe sha biyu ba labari harsun cire rai saigashi yazo da mota yayi parking bayan ya fito yace.

"Kayi hakuri malam wallahi ba mantawa nai daku ba nayi kiransa tun d'azu uzirin gida ya hanani dawowa kaga munyi waya dashi yace min babu sauran gidaje a hannunsa kayi hakuri saidai zanyi kokari na lalubo muku wani amma kafin nan ku shiga kangon nan ku aje kayanku nasan mai gidan sunansa Alhaji Musa mutumin kirki kafin dai na samo muku gidan hayar da zaku zauna nasan zai barku".

Kai malam Habu ya d'aga yana cewa "to shikenan na gode Allah ya saka da alkhairi" mi'kewa yai yana d'iban kayan suna shiga dashi sannan ya shikuma ya tafi haka suka kwana a kangon amma saboda tsoron nan ba garinsu bane basusan ya tsarinsa yake ba kada su ta'ba kayan wanda zai wulakanta su yasa tun kiran sallar farko na asuba malam Habu ya tashesu bayan yayi alwala ya fita xuwa masallaci tare da basu umarnin idan sunyi sallah kada su zauna su d'ebo kayan su dawo waje kada mai gidan yazo musu zuwan bazata kamasun dayai a ciki ya jawo musu matsala shiba wani kud'i ke gareshi ba.

Aiko suna ana shiga sallah bayan anyi sallama wuta-wuta sukai suka fita da komai waje kamar yadda ya umarcesu sai a wajen suka yi 'yan addu'o'i gari yayi haske malam Habu ya dawo dukka suka gaidashi bakin A'i da baya shiru ta kalleshi tana cewa.

"Oh ni A'i na fad'o daga sama na zarce rijiya gaba dubu Malam muna d'an zaman mu a gida cikin rufin asiri Rakiya tayi mana sutura ta bamu gurin zama haka kawai ka tashi tafiya batare da kasan inda zakaje ba kuma kaiba gurin kowa kazo ba ka kawomu tsakiyar birni ka ajemu ko tsoron azo a sace mu bakayi yanzu kila wani ya ganmu rakwacam har mu takwas kila yana nan yana fakon mu sai dare yayi yazo ya yashemu da d'ai d'ai wallahi nidai da ido d'aya da rabi nayi barcin jiya saboda naji ance birni ana yankewa mutane kai wai dama haka Kanon take da kyau tabdijan gaskiya dole su yaya Ilyah da Bara'atu su dage akan Nafisa ta auri d'an birni wa ya'ki dad'i umm kalli dan Allah Malam gidaje masu kyau ai ban ta'ba fitowa daga 'kauyen mu naje wani wuri ba kice muba rayuwa muke ba muna binne a kasa nifa idan ba yanzu ba ko a mafarki ban ta'ba zuwa Kano ba gashi dai a jihar nake kodan muna nisa dasu kuma cikin lungu sosai kai gaskiya garin yayi Masha Allah" ita kad'ai A'i sai sambatu take babu wanda yace mata ta tafar sau'ke suna zaune zaman jiran wannan yaron na jiya daya kawo musu gurasa suka saya ga drivan daya kawosu jiya shima yace zai dawo da safe amma shiru har Allah ya kawo wannan yaron mai gurasa kamar yadda yace musu da safema in suna so zai kawo su saya kud'insa malam Habu ya bashi suka juye fal babban bokiti sannan ya basu plate suka rarraba kowa ya karya yasha ruwa kafin yaron ya tattare kayansa yayi hanyar gida yana murnan zuwan wadannan ba'ki🙃.

Suna ta zaune dai suga ta inda driver zai 'bullo yazo ya fad'a musu idan ya samo musu gidan hayar amma shiru babu shi babu alamarsa sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana girgiza kai tare da d'an rufe ido a ransa yana tunanin indai yau drivan nan bai zo ya fad'a musu an samu gidan ko ba'a samu ba tofa baza suci gaba da zama anan ba duk dare yau sai sun sauya anguwa ko Allah zai basu rabons............................

A firgice Malam Habu ya bud'e ido sakamakon jin 'kara har baisan lokacin daya mi'ke tsaye daga zaune ba kallon motar da tazo tai parking gaf dasu yai amma baiga mutumin ciki ba saboda duhun glass d'in salati ya fara a cikin ransa tuni yaji hankalin sa ya tashi karfa ace mai wannan gidan ne yazo to yanzu me zasuce masa¿.....................

Jin an sake horn yasa Malam Habu d'agowa daga tunanin da yake ya kallo motar zuciyarsa na harbawa da karfi sosai daidai an bud'e kofar yaga wani lafiyayyan Alhaji ya fito yasha wanka cikin shadda mai tsada ga d'oneniyar hula wacce taji sitati tasha kari sannan takalmi👞 da agogo⌚ na ma'kudan kud'ad'e kai harda zobe💍 humm kawai siffarsa a kirashi sugar Dad☺️ sannan beauty no filter😃 haka yake ta ko'ina cass kuma kyakkyawa ne mai hanci ga fari ba irin alhazawan nan ne da suka aje tumbi kamar kayan wanki ba😳🤐.

Ganin ya kallesu yana dafe da murfin motar yasa jikin malam Habu ya d'an fara rawa neman jarumtarsa yake amma ya kasa saboda ganin irin kallon da mutumin ke musu da yake su matane har sufi malam Habun rud'ewa da hannu mutumin ya yafito malam Habu yana masa nuni da yaje gurin sa,.

Da'kyar Malam Habu dake tsaye daskare guri d'aya ya d'aga takalminsa ya fara tafiya zuwa inda Alhajin yake kamar mai ciwon 'kafa haka yake janta yana d'ari-d'ari da d'ar-d'ar d'in tsoro😞😥 saida ya kusa dashi sannan yaja ya tsaya murmushi mutumin yai yana cewa.

"Haba kai kuwa aboki karaso man ba wani abu bane magana zamuyi matso kusa kada ka damu".
Sauke numfashi Malam Habu yai jin abinda yace masa sai sannan ya d'anji hankalin sa ya lafa amma dai bai kwanta ba karasawa yai zai dur'kusa ya gaida dashi mutumin ya d'ago kafad'arsa da sauri yana cewa.

"A'a basai ka gaida dani a kasa ba aboki bani hannunka mu gaisa🤝" ya fad'a yana ri'ke hannu malam Habu sukai musabaha yace.

"Barka da asuba yakake"?.

Cikin jin sassauci malam Habu yace "lafiya alhamdulillah".

Kai ya d'aga masa yana cewa "hakan nada kyau dama tambaya ce zanyi maka idan bazaka damu ba sakamakon nayi mamakin ganinku har yau anan a layi kamar marasa gata ga mata da yara kuma 'yan mata babu dad'i jiya nazo na wuce tanan bayan na dawo daga office zan tafi gida na ganku a zaune kuma yauma na sake ganinku a nan d'in dai baku tafi ba shine nace ko bakusan kowa bane ku ba'ki ne ko"?.

Kai Malam Habu ya d'aga yana cewa "eh gaskiya mu ba'ki ne daga wani qauye muka taso nazo nan ne domin na kama hayar gida kuma nayi sana'a to munyi magana da direban motar daya kawo mu cewa zai laluba mana gidan haya amma shiru babu alamarsa tun jiya daya tafi yace mu shiga wannan kangon mu kwana kafin yau duk da shi yasan mai kangon amma mufa muna ciki a zaune bamu sanshi ba yazo duba gidansa ya ganmu a ciki kuma ba tambayar sa mukai ba shiyasa gari yana wajewa tun asuba nace mu fito waje kada Mai gidan yazo ya samemu a ciki nan ba garinmu bane bamusan ya tsarikansu suke ba ko abun laifi baya yawa muyi abinda zaija mana d'auri"?.

Murmushi mutumin yai yana cewa "kai daga kwana sai a d'aureku kamar wanda sukai sata? To kaga kwantar da hankalinka wannan kangon bana kowa bane nawa ne mallaki nane saiku saki jiki amma tunda gidan haya kake nema inada gidaje masu tarin yawa wanda ba mutane a ciki wasu kuma da mutane sannan hawa hawan kud'i ne sai wanda kake so na daidai qarfin ka idan kuma nasa muku murfin kofa a wannan d'in tunda na ganka da iyalai sosai kuma dama shima wannan d'in haya zansa amma me kace a shekara zaka iya biyan dubu d'ari biyu da hamsin"?.

Da sauri malam Habu ya d'aga kai yana cewa "eh na amince Alhaji kwarai zan biya insha Allahu za'a samu Allah ya dafa min Wallahi nayi maka alkawari zanyi kokari na biyaka lokacin da kake bukata dan Allah Alhaji ka amince"?.

"Ok shikenan karka damu za'a sa muku murfi yau tunda dama shi ya rage anyi filasta an d'anyi fenti sai kuyi maleji ko"?.

Kai Malam Habu ya d'aga "eh Alhaji na gode sosai Allah ya biyaka da mafificin alkairi".

Murmushi yai yana cewa "Amin amma mene sunan malamin"?.

"Sunana Malam Habubakar".

Hannu Alhajin ya mi'ko masa suka sake gaisawa yana cewa "alright u're welcome Malam Abubakar ni kuma sunana Alhaji Musa sannan nima anan anguwar nake ta by pass d'inku shikenan yanzu zan tafi office I don't want to be late but idan na dawo zamu qarasa maganar".

"To Alhaji nagode a dawo lafiya Allah ya kareka".

"Amin malam Abubakar nima na gode" ya fad'a yana juyawa ya shiga mota ya tadata yabar gurin da sauri malam Habu ya juya gurin iyalansa yana musu albishir ga yadda sukai da Alhajin kowa murna yake a take suka fara d'iban kayan suna shigarwa gidan sukai sa'a dakuna biyar ne malam Habu ya d'auki d'aya su Asma'u suka shiga d'aya sannan matansa kowa ta kama d'aya duk da babu koda ledar da zasu shimfid'a dole malam Habu ya fita da tambaya har yaje ya sayo musu taburmi da 'yan sauran canjin da suka rage masa domin Rakiya ma ta d'an bashi guzuri harda butoci da kofina da turmi karami na ice ya sayo tukunya guda d'aya kafin a samu yadda za'ai a qaro da sauran abubuwan aiyukan gidan wadanda ba'a rasa ba ya sayo musu kayan abinci kad'an da sauran kud'in sannan ya hawo adaidaita ya dawo gida.

Suka raba komai d'ai d'ai buta cokali plate sai tukunya ita kuma duk wanda shine da girki ya dora aiko a take faka-faka suka d'ebi 'bantaran bulo suka kafa murfi A'i sai murna ake anzo birni za'a fara shan shurba bakinta kamar zai yage😂 sai kallon shinkafar da ake gyarawa take tana hasko yadda za'ai mata cin wulakanci na an dad'e ba'a had'u ba😃 ga kayan miya🍅🌶️ a gefe abinka da maison bajinta harda d'an nama🥩 kad'an ya sayo asa cikin miyar samayar da mugun yawu na shekara da shekaru.

Satin su Malam Habu d'aya da zuwa Kano Alhaji Musa ya sameshi akan yayi karatun boko ya kawo masa takardarsa ya bashi aiki a companyn sa yace a'a baiyi boko ba sai iya ta arabic yayi amma 'yarsa guda d'aya tayi makaranta sosai kwanan nan ta karasa karatunta saidai bangaren aikin soja ne ko zai taimaka mata ta cika burinta Alhaji Musa yayi mamakin jin wannan furuci wato a cikin yaransa yan mata akwai wacce take son yin aikin soja ya jinjinawa jarumtarta saidai gaskiya bashi da hanya dan haka yacewa malam Habu bashi da wata kofa dazai taimaka mata amma zai jarraba kokarin sa a kanta wacce irin sana'a Malam Habun yake sonyi yace masa kowacce amma banda mai kud'ad'e da yawa saboda yana tsoron ta'ba kayan mutane sakamakon anyi masa baiji dad'i ba jin haka yasa Alhaji Musa ya d'auki adaidaita cikin wacce yake bada haya ya bashi tare da sharad'in duk wata zai ri'ka bashi dubu ashirin Malam Habu yayi murna sosai ya kuma yi masa godiya haka ya dawo gida fara'a fal fuskarsa haka iyalansa nasa ma sukaita binsa da addu'a ta gari da fatan arziki Allah ya d'agashi a ranar daya fara fita yawon haya a ranar ya sayo asusu wanda za'a rika sa kud'in idan ya dawo daga hayar an cire na abinci sauran saiya saka a ciki.

Kullum haka yakeyi kuma alhamdulillah yana samu sosai tuni suka fara murmurewa kuwa domin suna samun komai akai akai yanzu babu abinda suka rasa wanda rabon da suga haka tun kusan shekara ashirin baya😥 sai yanzu aiko haka suka tashi a tsaye suka dage masa da addu'a abu d'aya suka tambaye shi yace a'a wato suna son suyi sana'a wai ta wanke wanke a gidajen masu kud'i shikuma ya nuna bai amince ba tunda yanzu yana da yadda zaiyi ya ciyar dasu ya tufatar dasu babu wacce zatai dole suka ha'kura amma sun so ya barsu domin zasuyi samuwa.

Saidai kuma ana cikin haka ne Alhaji Musa yazo masa da bukatar dan Allah a cikin yaranshi ya bashi d'aya kullum zata ri'ka zuwa tana taya matarsa girki da 'yan abubuwa domin 'yar aikinta tayi aure ya d'auko mata wata ita kuma bata da hali sata take musu suka koreta gashi aikin gidan Hajia ita kad'ai zai mata yawa kuma tana zuwa office.

Jin uzirin da Alhaji Musa ya kawo masa yasa malam Habu ya amince tilas badan yaso ba saidan halaccin dayai masa amma baya kaunar yaga yaransa a waje musamman da suka kasance mata ga gari ba nasu ba 'katon birni mai girma sosai da fad'i.

A ranar daya amince tun daga ranar yace Asma'u ta fara zuwa amma bai yarda tana zuwa ita kad'ai ba ta dauki Jamila ko Aisha ko Amatu wani ya rakata duk da suma yanzu sunada abunyi domin basu daina d'inkin hula ba kowa tana tsantsara d'inki kamar inji ne yake bugata ba hannu ba.

Amatu da Aisha basu jure raka Asma'u wajen aikinta ba Jamila tafi rakata har itama ta samu Hajiya tace tana wanke wanke da moping Asma'u aikin abinci a wata tana biyansu kud'i mai d'an kauri babu laifi tunda itama tana dashi mijinta nadashi gashi basu ta'ba haihuwa ba tunda suke basu da d'a sai d'an ri'ko saurayi gud'a daya yana can a Canada yana karatun likitanci sunansa Saleem (d'an lelensu🤭) d'an gidan 'kanin Alhaji Musan ne domin Alhaji Musa ba yaro bane zaikai sa'an Malam Habu saidai sakamakon shi jikinsa ba wahala babu damuwa da tashin hankali ya tashi cikin kud'i yayi girman kud'i idan ka kalleshi ka kalli malam Habu xaka rantse da Allah Malam Habu ya bashi shekara goma.

Matarsa ma haka Hajiya Aisha zatai sa'ar Binta ko A'i amma batafi Saude ba kuma mace ce mai sakin fuska wayayyiya tana da kirki kuma tana sakewa su Asma'u idan sunzo haka zasuyi ta hira harda dariya kamar 'ya'yanta tana sha'awar taga ta samu d'an kanta amma shiru harta ha'kura ma sunyi yawo kasashe iri dabam dabam domin a bincika musu lafiyarsu ita da Alhaji Musa kuma abinda ya basu mamaki ko'ina sukaje abinda likitan waccan kasar ya fad'a musu to wannan likitan ma shi zaice sunyi tunanin basa haihuwa ne amma bincike ya nuna a'a suna haihuwa basuda wata matsala kawai Allah ne bai basu ba su kara ha'kuri yana sane dasu shiyasa suka kwantar da hankalin su tun daga yaye da suka amshi Saleem shikenan suka rikeshi basu mayar dashi ba suma iyayensa basu damu ba tunda suna da wasu yayan sai suka bar musu shi ya taso cikin daula da gata sosai ga shagwa'ba kamar mace.

Su Asma'u suna morewa a gurin Hajiya Aisha kuma suna jin dad'in zama da ita koda ace bata nan yanzu ta amince musu suje gidan su Mata aiki hatta mai gadin gidan yasan da zamansu sannan koda ma ace bata nan yadda ta saba idan sun gama aiki zasu taho 'ka'ida ne saita ciko musu kuula kullum da abinci sun taho dashi to koda bata nan zasu d'iba su kimtsa mata komai sannan su dawo gida.

Umm😊 sosai ahlin gidan malam Habu sukai 'bul-'bul har wani d'an glowing sukeyi balle dama gasu sun biyoshi sunfi kama dashi haka suke farare tarrr kamarshi babu wacce tai kama da uwarta a cikinsu duk siffarsa ce dasu gashi sunzo birni yanzu sun fara wayewa su fara sanin abubuwa wanda ada ko zaman shi a duniya basu sani ba ga kuma d'an shafe shafen mayuka irin masu sa kyan jiki wanda zai gyara musu fata sunayi harda su Binta🙃 tun tuni dama sunyi tashin komad'a kowa ya ciko ba wata rama ba damuwa ba kwanan fargaba.

Sunfa zo Kano a sa'a domin bayan duk wannan alkhairin yanzu Alhaji Musa ya sai musu makaranta da yake ya tambayi malam Habu ko sunyi karatu yace eh iya Junior suka tsaya d'aya ce tayi karatu sosai bayan Senior ma ta d'ora wata shiyasa yace su barshi haka tunda a qauye suke ba damuwa akai da karatu ba a haka ma yasha maganganu.

Shikam Alhaji Musa bai tsaya 'bata lokaci ba yacewa Malam Habu ainan birni ne babu wanda ya damu da wani kowa rayuwarsa yake cikin 'yanci zaman yaran haka bai kamata ba gara kowa ta kara karatu koda kad'an ne kafin Allah ya kawo musu mazajen aure Malam Habu har rasa bakin dazai godewa Alhaji Musa yai su Binta ma har gidansa sukaje sukai masa godiya haka ya yanka musu forms suka fara karatu a Legal su uku Amatu da yake ta zarcesu kuma karatun ta ba irin nasu bane yasa tata makarantar dabam take ta kud'i da yawa ce amma haka Alhaji Musa ya biya musu kamar 'ya'yan daya haifa haka yake jinsu.

TOOFAA😲 ANA WATA GA WATA🤨 WANI ABU YA DANNO KAI😮 FANS MU LE'KA MU GANI👀 MENENE🤔¿¿¿??? ME YAKE SHIRIN FARUWA NE¿‽😟😑.

Ranar wata litinin da dare wajen sha biyu malam Habu yayi dare da haya wasu samari suka tareshi suka hau adaidaitar cewa ya kaisu gaida ashe sunsha sun 'kwale shi kuma baisan 'yan 'kwaya bane ya d'auke su harya kusa kaisu suka dakatar dashi ya d'auka fita zasuyi sai ji yayi sunce ya fice ya basu adaidaitar su tafi da ita ko su kashe shi da mamaki ya juya zaiyi musu magana amma sai yaga d'aya ri'ke da wu'ka d'ayan kuma bindiga ga sauran biyun sun zare masa ido tare da d'ora yatsunsu a baki alamar shiru🤫 kada yayi ko tari idan ba haka

Please Login or Register in order to submit comment