Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazasu zo ku kwanta a inda kowa ya kwanta ba saidai su kwana a motar wai me kuke haka ga guri nan malala da yawa amma dan masifa danku d'aga min hankali kunzo kun dameni haba da Allah gafacan kuban guri" ta karasa maganar tana wucewa ta koma cikin baranta ta nemi guri kusa da yan uwanta dake ta aikin yanka alayyahu dasu albasa za'ai sabuwar miya gobe ma gagarumin biki za'ai sannan da kusan magriba amarya tad'au hanyar birni kamar yadda take fata.

"Kan bala'i Hassan kaga wata shariya a gurin Umma wai da gaske take a cikin wadannan mutanen zasu zo su kwanta haka kawai su zuba musu 'kwar'kwata a kyakkyawan gashinsu🤣.

Tsaki Hassan yai yana cewa "wallahi bazasu kwana a kasa ba muje d'aki shegiyar amaryar ba bikinta suka zoba ta d'aga tata katifar ta basu ko naci ubanta" yana rufe baki sukai d'akin Nafisa a kwance suka sameta har tayi barci wani duka Hassan ya sauke mata wanda a firgice ta tashi cikin gigin barci ganin basawa tsaye a kanta yasa tace.

"Meya faru"?.

Harararta Hussaini yai yana cewa "ubanki ne d'aga mana katifa yan matan mu zasu kwanta".

Jin abinda yace yasa Nafisa tace "kai dan Allah Hussaini daga yau nima fa shikenan nayi bankwana da katifar kuma a kasa zan kwana"?.

Dundu Hassan yai mata yana cewa "a bola zaki kwana dan uwarki ba kasa ba har ana magana kina mayarwa mutane wato ke ga amarya ko rainin amarci ya shigeki wallahi so kike yanzu nan na karya miki qafa sai naga gaggawar zuwa gidan mijin shegiya 'kwartuwa🙈 zakici ubanki da qafafunki zaki nemi hanyar qauyenku ki gudu idan kikaji maza🙉.

SUBAHANALLAHI WADANNE IRIN YAYU NE WANNAN😂.

Tsayawa Nafisa tai tana kallon sa cikin tsawa yace "zaki d'aga ko saina hautsinar dake".

Ba arziki da gudu Nafisa ta d'aga tana ficewa d'aga d'akin tsaki Hussaini yai yana cewa "idan ba jaraba bama wannan yarinyar ina ta isa aure kaga fa yan matan mu dame muka fisu amma a hakan iyayensu sunce mana yara ne mud'an kara jira hummm zata ci ubanta ne kama muje" d'aukar katifar sukai waje.

Da gudu Nafisa ta karasa gurin Bara'atu tana kuka tace "Umma Kinga su Hassan sunje ina barci na suka daddake ni sannan suka qwace min katifa ta wai yan matansu ne zasu kwanta".

Dafe kai Bara'atu tai tana kallon ta tace "Kinga Nafisa daina kuka iya yau ne zaluntar taki gobe iyanzu koda kud'i bazasu ganki ba balle su zalunce kin saidai su zalunci kansu tashi kije d'akina ki kwanta" mi'kewa Nafisa tai tana shiga d'aki.

Bara'atu kuma ta tashi tana zuwa kofar d'akin su Hassan harsun shimfid'a katifar sun sa bargo su d'ame sun d'auko fulo guda biyu sun jera suna kafa 'kusa zasu daura musu net tabi Bara'atu ta ri'ke tana cewa.

"Yanzu ku kun kyauta kenan yarinyar tana barci tsabar ba'kar mugunta kuje ku daketa hakan bai isheku kuka murgineta kuka kar'be katifar yayi muku kyau".

Daina kafa 'kusar Hassan yai yana cewa ''to Umma tsakani da Allah kuma fa ba haka akeyi ba taya zamuzo da ba'ki tun daga wata 'kasar ku kasa tarbarsu da abun arziki alhali hadisi ne guda cewa "wanda ya bada gaskiya da Allah da ranar alkiyama ya girmama ba'konsa" kodan kuba sani kukai ba gashi yanzu na sanar daku gobe saiku tashi da wuri ku nema musu kayan kari na Alfarma don baza suci abincin biki ba sannan a ragunan baba a yanka musu daya ko a bamu kaji biyar gobe mu kaisu masu suya su sayo musu kuma naga wannan shegiyar yarinyar anyi mata gara to wallahi kar mu tashi tafiya ace ba'a d'iba musu ba tunda muna da mota har Kanon zamu bita muje mu d'ebo musu".

Sauke numfashi Bara'atu tai jin zai mayar da ita sokuwa ya d'ora mata ciwon kai bata biyewa maganar saba ta juya tana cewa.

"Allah ya shirye ku".

Dariya Hassan yai yana cewa "Amin Umma addu'a ce mai kyau kikai mana kai Hussaini jeka shigo dasu Allah yasa basuyi barci a cikin motar ba aiduk laifin umma ne kaga fa mu yadda suke mana acan ga mahaifansu na sonmu in munje suyita hidima damu amma nan sunxo gurin kwanciya mai kyau ma ya gagara haba" fita Hussaini yai yana shigowa dasu suka zo suka kwanta su kuma sukai waje domin ba sosai dare yayi ba.

Washe gari ranar yinin biki amarya an'ki zama guri d'aya ayi yu ayi nan fuuu sai sallama takewa mutane kamar bazata sake dawowa garin ba har abada bakinta har kunne yau zatai kwanan birni la'asar nayi motocin d'aukar amarya suka fara jerowa harsu biyar ras amma sakamakon yanayin dawowa saboda idan sun kaita acan zasu kwana su d'anyi mata gyare gyare sai su taho shiyasa aka za'bi mutum shida kadai motar amarya ita kad'ai sai Maimuna sannan sauran motar mutum had'un suka shiga aka dau hanyar birni dan tsabar d'oki da'kyar Nafisa ta tsaya aka d'anyi mata nasiha sai mi'kewa tsaye take ana dur'kusarta🤔 a haka aka gama fad'an ba lallai nasihar ta shiga kunnen ta bama hankalin ta ya kad'a gaba haka ta tafi tabar su Bara'atu da Ilyah cikin farin ciki da murna 'ya ta koma rayuwar city🏙️.

🏙️KANO🏙️
________Uhm Allah yayi amarya Nafisa a gidan Nurain yaudai mafarki ya zama gaskiya buri ya cika anzo birni za'a bararraje a gwangwaje a d'ebi nishad'i balle wadanda suka rakota ba yawane dasu ba daga mutum biyu ta bangaren Ramatu sai dangin Bara'atu suma su biyu sai kuma Maimuna da Salma suna zaune a part d'in da aka baiwa Nafisa sai zizzilla ido suke suna santin gidan Nafisa tazo aljannar duniya haka Nurain ya kawo musu kayan abinci da abun sha iri iri na alfarma masu tsada wanda basu ta'ba ganin irinsa ba wani tsoro sukaji kar suci ya jawo musu matsala sannan yace su tsaya su kwana saboda dare yayi musu gobe da safe sai yasa a mayar dasu aiko dad'i ne ya rufesu jin zasuyi kwanan daula.

Har Nafisa na tambayar Salma "amma dai Salma badake zasu koma ba? ki tsaya kimin sati tunda bikinki sai watan gobe zansa Nurain ya miki sayayya sannan ya kaiki har gida da kansa".

Zaro ido waje Salma tai tana kallon Nafisa dake wani fari da gwalli irin na amare kafin tayi dariya tana cewa "ni yar ubana rufa min asiri ban shirya zaman birni ba wallahi tare dasu zamu koma ba zaman da zan kimaji na fad'a miki dan kada ma kisa rai ehe bazan zauna ba".

Marairaice Nafisa tayi "haba ke kuwa Salma yanxu in kuka tafi bansan ranar had'uwar muba idan ba garin nazo ba dan Allah ki tsaya kiyi min sati"?.

Kai Salma ta girgiza tana cewa "kefa wallahi bazan zauna ba ko kwana d'aya ne yadda muka zo tare dasu tare zamu koma garama kibar ro'ko na".

Kallon maimuna Nafisa tai tace "dan Allah umma Maimuh kisa mana baki a zancen nan ko Salma zata yarda ta zauna min zansa Nurain ya mayar da ita".

Itama Maimunan da yake bata goyon bayan zaman Salman bataga me zata zauna tayi ba a yanxu dan haka cikin zillewa da wayancewa tace "a'a ni ba ruwana da safgarku ta shirme ku daina sani a ciki kuyi iyaku" ta fad'a tana kau dakai Salman ma ta kafe bazata zauna ba dole haka Nafisa ta ha'kura da niyyar idan Nurain ya shigo zata fad'a masa ya lallmi Salman ta zauna tayi satin.

washe gari ma saida suka wuni suna shishshirya mata abubuwa da suka gama sukai wanka bayan la'asar Nurain yasa drivern Daddy yazo ya daukesu domin ya mayar dasu gida haka suka bar Nafisa ko d'an irin jin kewar nan babu itadai kawai tazo birni shine abinda ranta ya d'auka kuma idan ta tuna take jin girman Kai ya hauta.🤔

Misalin karfe takwas na dare Nafisa anci wankar taryar ango an bad'a kwalliya a fuska pawder tayi fau kamar biri🐵 an fesa turare anhau gado an lullu'be jiki da mayafi ana jiransa ya shigo tana zaune shiru shiru taji an bud'e kofa an shigo ta d'auka shine harda sake gyara rufe mayafin zuwa fuskarta tana murmushi yau gata ga Nurain sunyi aure a birni wani irin dad'i ne taji yana ratsa ta har tana lumshe ido a ranta tace yanzu lokacina zai fara daga yau zan bud'e sabuwar rayuwa..........................

Katse mata maganar zucin da take akai da cewa "hum'um kan bala'i lallai ya Nurain ya fad'o yanxu mine abun so a village girl harzai aurota yasa a gidansa heyeee ke madam 'kwas-'kwas bud'e wannan banzan mayafin naki ki kallemu sannan ki bud'e kunne ki saurare mu munzo miki da wasu maganganu ne".

Bud'e mayafin Nafisa tayi tana kallon su cike da mamaki tace "su waye ku"?.

Wata iriyar ba'kar harara tai karo da ita daga dukka su hud'un kafin Mimah tace "oh wai kina nufin baki gane muba humm to bari na miki bayani wannan uwarki ce wannan ubankice wannan kanwar ubanki ce ni kuma kanwar uwarki ce yanzu kin gane mu? kiji min shegiyar yarinya fa Meelat wai har tambayar mu take suwaye mu"?.

Tsaki meelat tai tana cewa "ke kika tsaya yi bayanin mu suwaye maiyasa data tambaya baki kifeta da mari ba wanda azaba zata sa ta gane yaren da kike nufi domin wannan akuyar tana bu'katar dusa but not now mubari zuwa gobe zaki bayani barka da shigowa kabarin ki kuma lahirarki ke da'ki'kiya fatan kinzo da likafani? Idan baki zo dashi ba kisa ya Nurain ya sayo miki gobe kuzo mutafi kada yazo ya same mu muna nan kuma tsautsayi yasa ki fad'a masa cewa wasu 'yan mata sun shigo gunki humyim wallahi gobe saimun canza miki halitta".

Kallon Mimih dake tsaye Mimah tai tana cewa "ke baki magana ba ko sai goben"?.

Kai Mimih ta girgiza tana kara dukawa akan Nafisa tare da sake bud'e mata dukkan girman idonta kafin tace.

"Unbelievable sannu amarya ya kike ya gida"?.

Da mamaki sauran suka kalleta Meelat da hartaje bakin kofar fita da sauri ta dawo tana cewa "Mimih me naji kince mata sannu amarya humm tofa ashe zata samu shiga ta bangaren ki ko"¿.

Cizon yatsa Mimih tai tana jin kamar ta d'aga hannu ta kwad'awa Nafisan mari kafin tace "heeeyy tabd'ijan dan'kari anan ake bele'u kuturun ubancan yanzu ya Nurain duk kyansa da jin kansa amma ya haure city ya tafi can wani dabban stupid d'in qauye yaje ya auro wannan ba'kar jahilar yasata a cikin familyn mu ta haifa mana da'ki'kan yara munana irinta hum'um kalleta da Allah wai amarya guda amma babu suturar arziki kalli wani banzan jakin lalle a kafarta wannan tsaya da saltif sukai ne ko kuma tsabar kauyanci haka aka dam'bara lallen? kutumelesi kiji wani wani kafurin d'oyi🙊 babu d'an kamshi da yake tashi na amaren nan sai tsamin kanta ke buguna tayi kitsone ma wannan jakar kauyen"? Ta karasa maganar tana fisge kwalin dake kanta a d'aure kallon 'kyama taiwa kan tana shirin 'ka'karin amai tace.

"Subahanallahi kai ku muje wayyo zan mutu da wari" ta karasa maganar tana fifita hancinta da hannu.

Ri'ke kunnenta Meenah tai cike da kishi da tsana tace "oh wai dama akan wannan ya Nurain ya rud'e ya mayar da hankalinsa qauye har saida ya aureta ya samu nutsuwa tabbb na rantse da Allah wannan kazamar yarinyar ko 'yar aikin gida bazan yarda a gidanmu a d'auke taba balle wai mata matar ma ta ya Nurain anya ya Nurain kansa d'aya kwakwalwar sa bata fara ta'buwa ba gaskiya ya kamata ya je hospital a duba shi domin wannan tsinanniyar ko 'yar goge takalminsa bata kai ba" ta karasa maganar tana hankad'a Nafisa baya ta fad'a saman gado.

Tsaki Meelat tana cewa "Humm kema dai kya fad'a Meenah gadaita nan a gashe ba mai'ko a dafe ba moro zataci ubanta ne damu take wasan badai kin aureshi ba? zaki bayani" Mimah kuzo mu tafi dan idan naci gaba da tsaiwa wannan tinkiyar ba'kauyiyar zatasa nayi aman fruit salad🥗 dinan da muka ci yanzu" tana rufe baki ta dunguwa Nafisa goshi kafin suka fice daga bedroom d'in.

Tsumu-tsumu Nafisa tai tana zaro ido waje kamar zata fashe da kuka ta shiga uku🙆 daga dirowarta garin tazo da farin ciki wadannan kuma su waye zasuzo su d'aga mata hankali daga ina suke waye ya turosu? Wannan tambayoyin sune fal ranta ta rasa yadda zatai gashi harsun hautsina mata ciki rasa inda zata sa kanta taji dad'i tayi saidai ta juya can ta kalli nan har Nurain ya shigo sai sannan ta d'an samu nutsuwa shikam baisan meke faruwa ba sai baje mata baki yake yana kallonta itakam saidai tayi masa murmushin ya'ke gashi sun gargad'eta akan kada ta kuskura ya sani duk wani farin ciki da take ji ya koma ciki haka dai kamar mara lafiya sukai abubuwa.

Washe gari sai wajen karfe d'aya Nurain ya fita shima a bisa dole Yazid ne ya kirashi yace masa yana so dan su had'u yanzu a ina zai sameshi ganin Nafisan barcin safe take yasa bai tasheta ba kawai yayi wanka ya shirya ya fice duk abinda yake su Mimah suna ankare dashi suna jin tashin mota da qarar bud'e gate da rufewa sunsan ya fita kuma Zainab ma tuni ta wuce hospital iya sune a gidan har karo suke da juna sukai part d'inta tana kwance tayi d'ai d'ai akan gado ta bararraje tana she'ka barci harda munshari saboda bata samu tayi da daren ba😉.

Fridge Meenah ta bud'e tana d'auko robar ruwa mai sanyi har ra'ba take ta juyeshi a cup ta d'aga ta watsa mata jiki tana cewa.

"Ke jaka tashi a kwanciyar nan dama barci kika zo dan uwarki harda bajewa kinai mutane gwarci kamar rago" ta karasa maganar tana kware mata sauran ruwan.

A firgice Nafisa ta farka jikinta na kakkarwa tsabar sanyin ruwar kamar mai zazza'bi sai makyarkyata take bakinta na rawa ta kasa magana tana kallon su cikin tsoro.

"Keee uwarki kike kallo a jikin mu"? Meelat ta fad'a tana fisgota daga kan gado ta fad'o kasa Mimah tasa kafa ta take ta tana cewa.

"Ke jiya me muka ce miki dama kinzo hutu ne tabd'i humm aiko yau saikin gwammace baki ta'ba sanin waye ya Nurain ba a rayuwarki".

Dam'ko ta Mimih tai tana mi'kar da ita tsaye tana kare mata kallo kafin tace "kai ku duba min na shiga uku me nake gani yarinyar nan kamar kuka tayi kodai ya Nurain yayi first night da ita😳 "?.

Mimih na rufe baki duk suka zuba mata ido suna qare mata kallo zaro ido Meenah tai tana cewa "kuturun ubancan lallai kam wallahi maganar ki nakan hanya Mimih wannan tsinanniyar ta shigo familyn gaskiya ya Nurain ya qasqantar da ahlinmu yanzu tsakani da Allah matsayin mata yad'au wannan kucakar yarinyar"? Mtswww.

Ta'be baki Meenah tai tana hararar Nafisa tace "hum kema dai kya fad'a Mimih wannan bala'in har ina na rasa me ya gani a jikinta abinso ita ba kyau ba itaba dirarran jiki ba kalleta fa kamar ta'barya ko'ina kai d'aya babu shape saikace gongonin peak milk haba wallahi ya Nurain yana da abun mamaki".

Qwafa Meelat tai tana cewa "kunga karmu tsaya surutai harya dawo bamuyi abinda ya kawo muba ta wuce muje ta fara bautar daya kawota gidan ta wanke mana toilet ta gyara mata bedroom da part d'in Aunty Zainab sannan tayi mana abun breakfast muna tsaye a kanta kuma bata isa ta shiga kitchen ba a garden zatai da gawayi zaki bayani wallahi sai munci uban daya kawoki duniya da kafafunki zaki gudu karkara kuma zaki gani muje dalla gafara akuya kawai" ta karasa maganar tana hankad'a ta da gudu Nafisa tai waje su kuma suka bi bayanta.


MALAM HABU.
________Kamar yadda Hajiya Aisha ta shawarci Alhaji Musa ya samu malam Habu ya fad'a masa bu'katar sa kasawa yai idan sun had'un ma baya iya fad'a masa harsu rabu sai daga baya abin yake damunsa musamman yanzu da suke zuwa kallon Asma'un ta kile sosai ta kara wayewa an zama 'yan birni tuni yaji hankalin sa ya tashi dan haka daya kasa tunkarar Malam Habun sai kawai ya tura abokinsa Alhaji Aminu yayi masa bayanin komai yadda zai fad'awa Malam Habu din sannan duk yadda sukai yana jiransa ya dawo ya sanar masa.

Alhaji Aminu baiyi kasa a gwiwa ba yaje har kofar gidan malam Habu da dare ya zayyane masa komai abinda yake faruwa ya kara masa da cewa Alhaji Musan yace ya tsaya yayi tunani tukuna idan yaga takura dan Allah kada ya 6oye masa ya fad'a zai fahimce shi babu wanda ya'ki shawara dan haka malam Habu yace zaiyi magana da iyayansu mata kome suka yanke zai sanar masa duk da yaji matukar mamaki kuma zuciyarsa ta girgiza dajin batun baya jin zai iya hanawa Alhaji Musa yayi masa komai a rayuwa domin shine ya bashi magani a lokacin da yake tsananin bu'kata ana barin halak dan kunya.

Saboda haka yana shiga gida yayi kiran duk su ukun d'akinsa dansu samu damar tattaunawa yadda ya kamata kuma ya fad'a musu ga abinda yake faruwa sa'kon Alhaji Musa zuwa garesu duk basu goyi baya ba domin maganar gaskiya gani suke idan sunyi haka sunci dinduniyar Hajiya Aisha wacce ta mayar da Asma'un kamar 'yar data haifa babu wanda ya gamsu a cikinsu Shima kuma Malam Habun dama yacewa Alhaji Aminun hakane saboda kada ya yanke hukunci ba neman shawara komai yana bu'katar nutsuwa.

Washe gari ya samu Alhaji Aminu ya fad'a masa yadda yayi da matansa duk basu goyi bsya ba saboda kirkin Hajiya Aisha bai kamata a saka mata da aure mata miji ba Alhaji Amanu yana barin gurin Malam Habu ya zarce ya sanar da su komai bsyanin da akai masa a take Hajiya Aisha tace su tashi haka suka sake zuwa duk su ukun gurin malam Habu yayi musu izinin shiga gidansa akai ta musayar magana dan suna nan akan bakarsu Asma'u bazata auri Alhaji Musa ba wannan butulci ne Hajiya Aisha ta nuna musu itace ma ta bashi shawarar da shine yayi tunanin hakan ba amma inaa babu wanda ya yarda da bukatar su karshen batu saida tasa musu kuka ta fad'a musu cewa tana so ya auri Asma'u ne dan ya samu Mai gadonsa ga matsalar dake faruwa dasu duk uwar dukiyar da suka tara babu Mai gadonta dan Allah kada su hana basu san me Allah ya 6oyeba watakila da rabo a tsakani dan Allah su duba al'amarin sai a sannan nefa jikinsu yayi sanyi da'kyar suka amince cewa sun bashi auren Asma'un sannan Jamila ita kuma Saleem yana ciki duk lokaci d'aya za'ai bikin Shima yana so xai koma Canada yaci gaba da school dinsa dama hutu yazo maimakon ace wanda aka baiwa auren 'ya ne zaiyi godiya saboda girmamawa da karamci malam Habu ne ke godiya kamar sunyi masa wata kyauta.

Da yake ba wani abun zafi bane sannan Alhaji Musa bayason maganganun mutane juma'a tana xuwa ya bada sadaki aka d'aura masa aure da Asma'u Jamila da Saleem shalele wai Allah sarki Malam Habu ranar harda kukan farin ciki yayi musamman tuna maganar Ilyah na cewa 'ya'yansa sun jibge sun tsufa a gidansa bazasu auru ba 'ya'ya mata ba'kin ciki ne da damuwa da maza ake tunkaho namiji ne komai in yayi ado ne hummm yau gashi Allah ya basu mazan auren masu daraja da kima wanda ba'ai tunani ba yana fata yadda Allah ya rufa masa asiri yayi auren su Allah ya kawowa sauran suma mazan aure na gari wanda zasu rikesu da mutunci.

A ranar juma'ar aka rakasu saidai Saude bataje ba A'i bataje ba iya Binta ce da Aisha da kuma Amatu zasuyi masu rakiya a junansu Hajiya Aisha da kanta tazo da mota har kofar gida aka fito da Asma'u dasu Binta suka shiga tace tana kunya Jamila surukarta ce zata turo mota a d'auketa bayan sun tafi ankai Asma'u Binta ta shigo motar driver da wasu dangin cikin yan uwan hajiya Aisha da Alhaji Musa suka zo taryan Jamilan itama aka rakata gidan part d'in Saleem shikenan bayan su Binta sun gama komai ta d'an yiwa kowaccensu nasiha ta fito parlor inda su Amatu ke jiranta zasu tafi Hajiya Aisha sai godiya take Mata kamar wanda ta bata kyautar wani gagarumin abu.

Tab su Saleem kam dama tuni anyi ciki ana can anaiwa Jamila shagwa'ba yau😀 Hajiya Aisha tana nan zaune a main parlor har Alhaji Musa ya shigo da mamaki ya kalleta yana cewa.

"Aisha ya naganki ke d'aya ina su Hajiya Hajaran suke ko harsun tafi bamuyi sallama ba"?.

Kaita d'aga tana murmushi tace "eh basu dad'e da tafiya ba nace su tsaya su kwana suka ce min a'a daga baya sa dawo su sake ganin amarya".

"Ok yayi kyau harda Hajiya Rabi'atun"?.

"Ai Alhaji duk sun tafi iya mune a gidan muje na raka ka d'akin amaryarka yau nice abokiyar ango" ta fad'a tana dariya tare da kar'ba kayan hannunsa ta wuce gaba murmushi yai yana bin bayanta uhm Asma'u tana zaune a tsakiya 'katon gado na alfarma ta lullu'ba da mayafi suna shiga kuwa ta nemi nutsuwarta ta rasa inda zatasa kanta domin kunyar Hajiya Aisha dama daya akai auren 'ki tayi itama tace bazata iyaba ta d'auka anbar maganar sai ji tayi wai an d'aura yau wuni ma tayi tana kukan kunya.

Zama Hajiya Aisha tayi a gefen gadon tana d'aga mayafin ta yayeshi zuwa saman kanta tace "uhm Masha Allah Asma'u gaskiya kinyi kyau dole a biya kud'in sayan baki Alhaji saika biya".

Shikam Alhaji Musa tsaye yayi kawai da murmushi a fuskarsa yace "ok nawa zan biya kenan"?.

Gyara zama Hajiya Aisha tai tana cewa "amarya dubu d'ari ni kuma qawarta dubu hamsin😃".

'Dan zaro ido yai cikin wasa yace "kai dama ke qawar amarya ce bayan yanzun nan a parlor kikace kece abokiyar ango kodai Kinga amaryar tafi angon kyau shine zaki koma 6angarenta"?.

Itama d'an zaro idon tai kamar ta manta d'in nan tace "kuma fa anyi haka ashe ni qawar ango ce ai shikenan a biya amaryar nata nice ma zan biya transfer ko cash wanne take so"?.

"Cash take so aje a kawo mata ko zamu samu bakin ya bud'u".

Mi'kewa Hajiya Aisha tai tana fita zuwa minta biyu ta dawo da kud'i d'aure a kyauro tana ajewa a gaban Asma'u da kanta ke sunkuye tace.

"To amarya na wakilci ango na saye bakin duka sai ayi masa magana nizan tafi Allah ya bada zaman lafiya Allah ya sanya alkairi Allah ya kawo mana arziki mai d'orewa wanda zamuyi farin ciki dashi".

Iya Alhaji Musa ne yace Amin a fili Asma'u ta fad'a a zuciyarta kafin Hajiya Aisha ta juya tana fita tsaye Alhaji Musa yai yana kallon Asma'u datai shiru zuwa wani lokaci yace.

"Husnah😁".

Ji Asma'u tai gabanta ya fad'i ta ma kasa amsawa sai numfashin ta dake fita da sauri kawai ta sake qasa da kanta.

"Husnah".

Ya fad'a a karo na biyu da'kyar ta amsa muryarta na rawa can kasa sosai yaji na'am d'in da tace yayi mamaki domin yasan ba haka take ba sau tari yana jin surunta ita da Hajiya idan sunzo aiki to yau d'in meyasa? Kodan yau rana ce musamman a gareta batai kama da sauran ranaku ba tayi dabam kaiya jinjina yana sake qare mata kallo gaskiya 'ya'yan malam Abubakar kyawawa ne kuma duk kama suke dashi gabadaya fuskarsa suka d'auko kyau iya kyau ya fad'a a ransa kafin yace.

"Kinga ki tashi kiyi alwala bari na dawo" yana fad'in haka ya fita dan ya bata sarari ta samu tayi tana ganin ya fita ta mi'ke tana sauka a gadon jiki a sanyaye ta nufi kofar toilet bud'e ta shiga tayo alwalar tana fitowa yana shigowa ya sako jallabiya coffee ya cire wancan shaddar gaba ya wuce ya musu sallar nafila ta godiya da addu'o'i masu tarin yawa na fatan zaman lafiya da alkairi a tsakaninsu sannan ya mi'ke zai sake fita har yaje ba'kin kofa ya juyo yana cewa.

"Ki tashi kici wannan abun sai kiyi wanka ki kwanta kinji"?.

Kai ta d'aga masa a hankali tace "to" yana juyawa ya fita ta mi'ke tana tana zama a gaban gadon gaban glass table din ta bud'e ledar humm d'irka d'irkan kaji ne guda biyu wanda sukaji kyakkyawan gashi da lafiyayyan kayan had'i da'kyar ta samu ta iya cinye cinya daya🍗 tasha fresh milk mai sanyi sosai sannan ta tashi tana cire doguwar rigar jikinta ta duba sabon towel ta d'auka tana cireshi a

Please Login or Register in order to submit comment