Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gaskiya ka fad'a min wacece wannan yarinyar sannan meye ala'kar ka da ita"?.

'Dan shiru yai yana kallon ta kamar bazai magana ba sai kuma ya sauke numfashi yana cewa "kinsan 'kauyen da Dad yake tura ni 'karbo kayayyakin da ake kaiwa gidan marayu a gurin wani mai kud'i a 'kauyen"?.

Tsayawa Zainab tai da kukan tana kallon sa tace "shine ya baka 'yarsa"?.

Kai ya girgiza mata "no ba shine ya bani ba nine naganta naji ina son ta".

Zaro ido waje tai tana dafe kirji zatai magana ta 'kwaru ta soma tari da ruwa a kusa dashi ya zuba a cup yana bata maimakon data kar'ba tasha saikawai ta watsa masa shi a jiki tana sake fashewa da kuka mai ta'ba 'kwa'kwalwa muryarta na rawa tace.

"Kai kace kana son ta aurenta zakai my choice"?.

"Eh aurenta zanyi saboda inada dalili idan ban auri yarinyar nan ba akwai matsala ba 'yar kamara ba shiyasa nake so ki tsaya ki saurare ni zan miki bayani yadda zaki fahimta".

Yana rufe baki ta tashi da gudu ta shige bedroom da kallo ya bita cikin mamaki saidai yasan wace Zainab yadda take masa mahaucin so dama abune mai wuya ta iya kwantar da hankalinta ya auro wata mace amma hakan shine mafita gareshi dole ya auri Nafisa kodan tsira da mutuncin sa yana cikin tunani yaji ta sake fitowa da kukanta bai ankara ba yaga ta bud'e kofar parlor ta fice da sauri ya tashi yana bin bayanta mota yaga ta dauka tsaye yai yana hard'e hannunsa yasan ba wannan 'kauyen zataje ba tunda batasan hanya ba bazai wuce gidansu zata ba shi kuwa hakan ma zai taimaka masa wajen warware matsalar sa juyawa yai yana komawa parlon ya d'au wayarsa amma harta fasa masa screen bai damu ba ya zauna yana sake danna kiran wayar Nafisan domin hakan ma yana rage masa wani zafin😳.


'KAUYE🏕️
____A babban dandalin garin inda yake cike da samari da 'yan mata kowa da abinda yake sayarwa Indo tana zaune a gaban kayan sayarwata tayi tagumi naban tausayi hankalin ta baikan kowa tayi zurfi a duniyar data fad'a na tunanin wannan baud'dd'iyar rayuwa da take karasowar Dauda kenan ganinta da abin sayarwa yasa yaje inda take yana cewa.

"Indo".

Da sauri Indo ta d'ago a razane tana kallon sa fuskarsa murtuk lullu'be da 'bacin rai yace "amma me nace dake jiya? bance karna sake ganinki da kayan tallar wannan matar ba wato taurin kai ya hana kiji magana ta ko"?.

Sunkuyar dakai Indo tai tana goge hawaye muryarta na rawa tace "kayi hakuri dan Allah yaya Dauda wallahi ba laifina bane idan banzo ba duka na zatai".

"Ta dake ki tayi hauka ne"? ya fad'a a tsawace har saida Indon ta tsorata da sauri tad'an matsaya baya tana fashewa da kukan tashin hankali da damuwa tace "kayi hakuri" mi'kewa yai yana cewa "shikenan tashi muje gidan" jiki a sanyaye ta mike tana d'aukar kayan suka tafi jikinta sai tsuma yake tasan yau kam ta shiga uku ta lalace kila kasheta ne kawai Asabe bazatai ba a gidan nan yau hakan ma dan tasan tana morarta da babu abinda take mata tasan yau saidai tai kwanan kabari mus zata kasheta har lahira kuma ubanta baida farcen sosa baida ikon cewa 'kala ta kashe banza suna shiga Asabe tana shirin kulle kofar d'aki zata fita anguwa ganinsu yasa taja ta tsaya tana cewa.

"Malam lafiya zaka shigowa mutane gida kai tsaye ba neman izini"?.

Bai kula Asabe ba sai juyawa dayai yana kallon Indo wacce ta ra'be acan baya jikin katanga ga alamar firgici bayyane a fuskarta yace "ke zonan" karasowa Indo tai da sassarfa tana tsayawa a bayansa kad'an saboda tsoro cikin tsawa yace "jeki aje mata kayanta a gabanta" matsawa Indo tai jiki na 'kyarma take kokarin sau'ke katon bahon tallar abincin dake kanta rawar da hannunta keyi yasa bazata iya ri'kewa dakyau ta sauke ba a tsautsayi ya su'buce ji kake tassss baho ya fad'o abincin ya zube miyar ta zube sannan bahon ya tsage zaro ido Asabe tai tana cewa "kan bala'i amma yaron nan da 'karfin hali kake to wallahi bari kaji saika biyani dan ko uwarka Aliyah bata isa jadani ba balle kai karamin alhaki d'an marar kunya fitsararre bashi kaci saika biyani bazan d'au asara ba" bai ko kalli inda take ba ya juya yana cewa Indo "muje" da gudu Indo ta fita a gidan tana kuka sannan ya kalli Asabe yana cewa "ke kuma ki kuka da kanki na rantse da Allah kafin nabar garin nan saina saita miki zama zanyi maganinki tunda ke ba mutuniyar arziki bace"

"Aliyah da Balah neba mutanen arziki ba d'an marar kunya".

A fusace ya nunata da yatsa yana cewa "kada ki kuskura ki sake zagarmin mahaifana wallahi zanyi 'kasa 'kasa dake a gun nan"🙊.

"Inka fasa yin 'kasa 'kasa dani baka haifu d'an halak ba".

Shigowar Balarabe ganin Dauda ga Asabe tsaye sai huruwa take yace "a'a lafiya waye wannan haka ba Dauda bane d'an gidan Malam Balah mene haka meyake faruwa?

Ba'kin ciki ya gama cika Asabe ganin yadda Dauda ya jawo mata asara ta kalli Balarabe tana cewa "wallahi bazan yarda ba gurin mai gari zanje yanxu nakai kararsa a mana iyaka haka kawai zai shigo min gida kai tsaye ya zageni yasa wannan matsiyaciyar yarinyar Indo ta xubar min da abinci ta fasa min baho sannan ya ri'ka fad'a min magana son ransa".

Kallon Dauda Balarabe yai yana cewa "kaga jeka abinka Dauda kyale kawai".

A masife Asabe tace "ya 'kyale kawai meye kake nufi a barshi ya tafi kaine zaka biyani"?.

Kai Balarabe ya d'aga "eh zan biya ki Dauda jeka".

Dauda yaso magana amma ya share kawai ya fice a gidan yana jan tsaki mai karfi wata uwar harara Asabe ta sakarwa Balarabe tana cewa

Kace ya tafi ko saboda bakai yaiwa asara ba to wallahi bari kaji yau saika biyani sannan tunda ka goyi bayansa duk wata wahala da Indo take yi a gidan nan kaine zaga ka dawo yi ka gane"?.

Jikin Balarabe yana rawa yace zanyi komaye kinsan yaron nan da zuciya badan Allah yasa naxo ba kikai kuskuren masa wani abu saiya nad'a miki duka babu ruwansa".

"Uban wa zai nad'awa dukan aiko yau da yaga hauka ganin idonsa dan wallahi saiyài kwanan bayan kanta kuma hakan ma ba ha'kura naiba bari naje gidan Aliyan itama wata tsinanniyar nasan itace ta turoshi yazo yaci min mutunci".

Dakatar da ita balance yai da cewa "Asabe karki je gidan mutane da rana tsaka ki kyale xanyi aiyukan da Indo d'in takeyi da".

Tsayawa Asabe tai tana juyowa tace "ai wallahi Balarabe sai naje na kaddamar mata da nima bani da mutunci ba'a ta'ba ni na barta ta kwana lafiya sannan kafin na dawo ka share gidan ka wanke wadancan kwanuka ka kyara gurin da shegiyar 'yar taka ta xubar min abincin ka sakewa raguna na igiya🙊 ka xuba musu dusa ka d'ora min sabon girki" tana fadin haka tai waje fuuuuu sauke ajiyar zuciya Balarabe yai yana kallon abincin dake zube a kasa kafin ya fara tattarawa.

Sauri Asabe keyi kamar zata tashi sama haka ta afka gidan malam Balah babu sallama suna zaune harda Dalah ga Indo tana kuka Dauda yana musu bayanin abinda yake faruwa tana xuwa babu wanda ya lura da ita ta sha'ki Indo tana cewa .

"Kee taso min nan mu tafi dan gwafar ubanki matsiyaciya munafika kukan uban me kike yau saikin biyani asarar da kika jamin".

Duk d'agowa sukai suna kallon Asabe wacce ta kama Indo da karfin tsiya tana janta harda mari ba zato taji itama wani lafiyayyan mari ya sauka a kuncinta a gigice ta saki Indo tana dawurwuri domin Dauda akwai zafin hannu marin ya tsarata ihu ta saki tana cewa.

"Wayyo Allah shikenan ya makanta ni na daina gani ruwan idanuna ya tsiyaye na shiga uku wallahi bazan yarda ba saina had'aka da hukama yau sai an mana iyaka".

Ba wanda ya kula iskarta saida marin ya saketa ta dawo daidai ta kalli Aliyah tana cewa.

"Aliyah kinyi asarar haihuwa Dauda ba d'an halak bane cikin shegensa kikai tsinanne ne kuma wallahi bari kiji ku jira sammaci saina d'auko muku 'yan sanda".

Dariya Aliyah tai tana kallon yadda Asabe ke huci tace "maza sauri ki d'ebo bataliyar sojoji ba 'yan sanda ba mutuniyar banza kawai ki jira karshen ki ai Daudan ne daidai dake wofantacciya kawai".

"Au haka kikace akan d'an kine ya mareni? zakuwa kuga yadda ake sharri indai ni ce Asabe ki jirani zan baku mamaki"tana fadin haka tai waje da sauri.

Tashi Dauda yai zaibita Aliyah ta dakatar dashi "Dauda Ina zakaje karka bita ka 'kyale ta" shiru yai yana kallon hanyar kofar gidan kafin yace "ba ita zanbi ba zanje gurin mai gari ne".

"Mai gari kuma me zakai masa"?.

"Ina so zan koma Osun ranar litinin ta sama magana zamuyi dashi daku da kuma ita wannan matar"

"Amma maganar me kenan Dauda wacce zakuyi da mai garin tunani na damu zaka fara shawara ko kafin kaje gurin sa"?.

"Eh daku ne kawai zanje na sanar masa abinda ya faru tsakani na da wannan matar sannan a mata iyaka da indo ba ita ba ita bazata sake zama a gidansu ba har abada saidai taje da yawo shine kawai abinda zance idan mai gari bai iya maganin matsalar ba zamuyi gaba zuwa ofishin 'yan sanda".

"Amma Dauda da ka bari babanka yaje wannan maganar ta manya ce".

Kafin Dauda yai magana malam Balah ya mi'ke yana cewa "eh muje tare nima wannan abubuwan sun isheni haka" ficewa sukai Fatima dake gefe kusa da Indo tace.

"Allah yasa ta d'ebo yan sandan ma da 'karyarta da 'kare idan wani baiyi kwanan bayan kantar ba ita tayi dan wallahi nima 'yar shedace irin cusgunawa Indo ta tayi balle azo kan abinda tai miki baba Dalah haaah Allah yakai damo ga harawa in baici ba yaci tsinannan duka takai 'karar mana daga haka a tafi kotu ta gani idan batai zaman gidan yari ba shima baba Balaraben ai duk laifinsa ne".

Murmushi Dalah tai tana cewa "ke yarinya ce Fatima bazaki fahimta Balarabe bayin kansa bane tilas yake komai fatana kawai Allah ya kawo karshen abinda tai masa kowa ya gane gaskiya daga lokacin da duniya ta juya mata baya a sannan ne zatai kuka da idanunta babu mai sharewa tayi ihu da kururuwa babu mai jints balle ya bata agaji kuma nikam nawa ai nabarta da Allah alhaki ma ya ishe yana nan lodi lodi wanda ta d'eba idan nabi a sannu Ina zaune zanga sakayyar sanyani cikin damuwar datai ke kuma Indo karki damu insha Allahu kamar yadda kikace bakya son Iluh bata isa tilasta kiba indai kina son Dauda zansashi ya d'aga tafiyarsa sai anyi bikinku inya ga da damar gurin zama acan ya tafi dake idan babu ya barki anan".

Ita dai Indo batace komai ba sai ido take gogewa sakamakon hawayen da ya'ki daina zuba amma dai tayi farin ciki kuma koda ma ace bata son Dauda aita aureshi balle meye aibunsa😝.

To kice kema Indo umm😂 dama dai kin 'kyasa🙈 kawai daga umm sai umm uwar gulma tayi cikin shege 😁😀😃😄.

Suna zaune a gaban mai gari suna masa tsari saiga Asabe itama tazo da Balarabe yana binta su'kuri-su'kuri a bayan ganin su yasa ta had'e rai tana cewa "au har kunyo gaba dan munafirci aida kun aika an kirani sai ayi komai ina gurin indai ba sharri kuka taka ba kunzo kun fad'i karya da gaskiya to wallahi mai gari bazan yarda ba sai an dawo da shari'ar nan baya".

Kallonta mai gari yai yana cewa "ke kam Asabe baki da hakuri baki zo da sallama ba sai hayaniya zauna muyi magana a nutse ai suma d'in ba komai sukace ba dama yanxu nake shirin aika Laminu ya kiraku keda malam Balaraben".

Ta'be baki Asabe tai irin bata gamsu da abinda yace ba kawai ya zurata ne tace "au duk da bakai tunanin a kiramu ba sai daka ganmu zaka tsiri borin kunya Toni ba zama ya kawo niba kawai nazone na sanar maka zanje na d'ebo wa wannan shegen yaron hukuma kar kaji karar jiniyar mota kace waye ya d'ebo yan sanda baka sani ba nice yau sai anyi ya'ki a garin nan" tana fad'in haka zata juya mai gari yace.

"Dawo Asabe karki d'ebo yan sanda zoki zauna nayi muku sharia idan na gagara da kaina zan dauko yan sandan yanxu idan kikaje bada sa hannuna ba akwai matsala dole zasu bukaceni ni kuwa matukar bakiji magana taba sukazo neman ba'asi zance bansan komai ba".

Jin abinda yace yasa Asabe dawowa dole ta zauna Balarabe ma ya zauna kusa da ita sai 'kar-'kar yake da ido kamar idon 'kwar'kwata duk kunya ta rufeshi dan yasan a garin nan babu wanda baisan shi mijin tace bane".

Gyara zama Mai gari yai yana kallon dukkansu yace "umhum mu fara ta kanka ina jinka malam Balah meya faru"?.

Kafin yai magana Asabe tace "bangane kana umhum mu fara ta kanka ba Malam Balah ina jinka meya faru dama dashi zamuyi shari'a da d'ansa ne 'karar d'ansa na kawo bashi ba dama shi yasan abinda ya faru a tsakanin mu ne a tunani na ni zaka tambaya wannan shari'a ce tsakani da d'an sa".

Kai mai gari ya d'aga "eh haka ne Asabe kinyi gaskiya" maida hankalin sa yai kan Dauda yana cewa "kai Dauda meye ya had'aka da Asabe matar Balarabe tana matar aure har fad'a ya had'aku"?.

Wuf Asabe tai har tana 'kwaruwa wajen cewa "amma ai nice babba ni za'a fara tambaya"?.

Kai mai gari ya girgiza "a'a bake za'a fara tambaya ba banzo kanki ba tukuna jira yanxu da Dauda nake, domin shi ya fara zuwa kai meye ya had'aku".

'Dan shiru Dauda yai kamar bazai bada amsa ba takaici ya gama cika shi sai kuma yace "d'azu nabar gida kamar da wasa ina zuwa dandali naga Indo da 'katon bahon tallar abinci a gaban ta tayi tagumi sai tunani take haka kawai yarinyar 'karama zata d'ora mata hawan jini shine na tambaye ta banace karta sake d'aukar kayan tallar wannan matar ba da kukanta tace idan bata d'auka ba dukanta zatai sannan ga wahalhalu da take dora mata nayau dabam na gobe dabam alhali ba itace ta haifeta ba bawata tsiyar take bata ba nikuma shine nasa Indon ta dauki kayan abincin mukaje tare har gidan nace a aje mata a garin saukewa bahon ya fad'o ya fashe nace Indo tabar gidan muka tafi gidan mu tare muna can sai gata ko sallama babu ta shigo ta d'aga hannu ta shararawa Indo mari ta kama janta 'kababa wai saita bita nima na mareta akan haka ta taho kawo ni 'kara".

Kallon Asabe mai gari yai yana cewa "Asabe anyi haka"?.

Huci Asabe keyi tunda tasan duk abinda ya fad'a a kanta babu karya haka akai amma saita waske da cewa "nifa ba wannan ya kawo niba abincin da yasa ta 'barar min zai biyani da kuma marin dayai min a gaban munafikan iyayen nasa suna gani babu wanda ya hana sannan abu na 'karshe dole ya bani Indo ta koma gidan mahaifin ta tunda yana raye bai mutu ba kuma ba cewa yai bazai ri'ke 'yarsa ba".

Kallonta mai gari yai "ba wannan na tambaye kiba cewa nai haka ne abinda ya fad'a"?.

Cikin son yin jayayya Asabe tace "amma mai gari..............

"A'a ki bani amsa eh haka ne ko a'a ba haka bane"?.

Kamar mai ciwon baki da'kyar tace "eh haka ne abinda yace".

Gyara zama Mai gari yai yana cewa "madallah yanxu abunda zan fara fad'a shine ke Asabe kin mari Indo ke kuma Dauda ya rama mata ya mareki shikenan babi babi sannan kince abi miki kadin ya shigar miki gida babu sallama yana zage zage bai kyauta ba tanan amma fa wani hanzari ba gudu ba kema haka kika shiga musu gida ba sallama kina zage zage tanan ma babi babi sai maganar Indo ba kece mahaifiyar taba ba kece mahaifin taba dan haka baki da wani iko a kanta sai abinda mahaifin ta yace ina jinka Balarabe wannan 'ya da ake gwarama a kanta 'yarka ce dukkan mu nan bamu da iko akanta sai abinda ka yanke muna sauraron ka"?.

A firgice Balarabe yace "iye mai kace mai gari"?.

Da mamaki mai gari yace tunanin me kake Malam Balarabe cewa nai za'bi yana gareka akan 'yarka sai huluncin daka yanke gyara ne nawa shin Indo zata dawo ne taci gaba da zama a gidanka ko kuma zataci gaba da zama a gidan malam Balah"?.

Shiru Balarabe yai jikinsa yana rawa muryarsa ma haka da'kyar yace "me me megari to ni mezamce meye nawa a ciki"?.

"A'a yane me zaka ce kawai amsa ce guda d'aya zaka bayar eh na amince taci gaba da zama acan ko a'a ban amince ba 'yata ce ta dawo gidana komai kace yayi daidai ikonka ne".

'Dagowa yai yana kallon Asabe wacce ta zuba masa ido tana sauraron abinda zaice harara ta zafga masa da sauri ya d'auke kai yana cewa "ta dawo gida na"?.

Farat Dauda yace "ban amince da wannan amsar ba mai gari harararsa tai ka sake tambayarsa"?.

Kai mai gari ya jinjina domin shima ya gani yace "malam Balarabe ka fad'i abinda ke ranka ba abinda Asabe take soba idan kuma ba haka ba zan yanke hukunci da kaina".

"Ta dawo gida na zan ri'ke ta" Balarabe ya sake fad'a muryarsa na rawa.

Kai mai gari ya jinjina yana cewa "shikenan dai naga kamar yanzu baka cikin nutsuwarka abar shari'ar sai nanda kwana biyu idan ka yanke shawara saiku dawo kuje kawai" mi'kewa sukai sunai masa masa sallama da godiya suka tafi Dauda yasa a ransa cikin kwanakin biyun nan zai had'a komai tunda da kud'i a hannunsa zaiyi sadaki da sauran abubuwa akwati kuma idan sunje Osun ya had'a mata acan.

Bayan sun baro gurin mai gari ganin Asabe tayi wata hanyar dabam sai sauri take yasa Balarabe cewa "Asabe ina zakije".

Cikin fusata Asabe tace "inda ka aikeni d'an zomomuwa🙊 d'an sakaliya zaka wuce kaje ka gyara min gida ko saina juyo na sauke dukkan fushina da wadancan tsinanun suka d'ora min a kanka"?

Bai sake ce mata 'kala ba ya juya sakalaf sakalaf jiki ba laka ya kama hanyar gida yayin da Asabe ta wuce zuwa gidan malam Garba a kofar gida bakin shagon kwanan samari irin aljihun zauren nan ta samu Iluh d'an garuwa yana zaune da baronsa a gabansa ya Kira yarinya mai awara yana saya da sauri ta karasa tana cewa.

"Kai Iluh naxo muyi magana".

'Dagowa Iluh yai ganin Asabe yasa da sauri ya du'ka yana cewa "ashe babah ce sannu da zuwa ina kwana"? Ya gaida ita amsawa tai da fara'ar mugunta a fuskarta ta kalli gabas ta kalli yamma babu kowa a layin d'an kasa tai da murya tana cewa.

"Kasan me nake so dakai yanzu a yau d'in nan basai gobe ba kayi shiri maza ka koma garin ku gobe ka bugo sammako kaida iyayenka wajen neman auren Indo nayi maka alkawari zanyi ruwa nayi tsaki a baka ita kaji"? .

Kai Iluh ya d'aga cike da murna dan shima dama a matse yake ya aureta a yanxu dan tun ranar da yaje gurin ta sau daya ya harbu da sonta da sha'awar ta musamman da yaga tana da kayan aiki😳🙈 (Innalillahi wallh fans ba ruwana🤭).

"Ka jini ai ko"?.

Kai ya d'aga yana cewa "eh babah insha Allahu ayau kuwa zan tafi gobe innata da baffana zasu zo" yana rufe baki Asabe tace "yauwa d'an albarka maza tashi kayi shiri ka tafi nima bari na koma na sanarwa ubanta cewa zaka turo" tana fad'in haka tabar gurin yayin da Iluh ya mi'ke yana shiga shagon ya soma d'ura kayansa a leda da mai wanki da marar wanki ko wanka baiyi ba 'kafarsa duk kasa haka ya fito yana shigar da baron cikin gidan malam Garba yai musu sallama ya d'au hanya su kansu sun d'anji mamakin tafiyarsa amma babu wanda ya tambayeshi".

Batun Asabe bata koma gida ba sai dare kusan karfe goma a kofar d'aki ta samu Balarabe yana zaune gurun ya zuba tagumi tsaye tai a kansa tana shewa wanda yasa a firgice ya d'ago yana kallon ta itama shi take kallo cikin hasken farin wata tace.

"A lallai Balarabe akan lamarin wannan shegiyar 'yar taka Indo shine kake neman hana kanka sukuni? hummm nayi maganin abun gobe karkaje ko'ina ka tsaya a gida ka shirya tarar ba'ki".

Muryar Balarabe kamar yana mura sakamakon dad'ewa dayai bai magana ba yace "su waye zasu zo"?.

'Daki Asabe ta wuce tana cewa "iyayen Iluh d'an garuwa naje na sameshi d'azu nice nasashi yaje gida ya turo su nan da karshen watan nan a gama komai" tana rufe baki Balarabe ya dafe kirjinshi sakamakon jin bazatar datai masa gabansa ya fad'i harsai da ya saki salati zuciyarsa na harbawa baice mata komai ba ya share wani d'an 'karamin hawaye daya zubo masa wanda baisan na meye ba sai yanzu yake jin takaicin kansa da haushin kansa da yakai tallar 'yarsa a masallaci baisan meya sameshi ba yana son 'yarsa amma bashi da wani iko a kanta kome zai mata na muniya bada son ransa bane abun na damunsa a raisa ya rasa ta inda matsalar take sannan haka nan yaji baya kaunar baiwa Indo wannan d'an garuwar fatansa Allah yasa Dauda yaji yazo ya samu Asabe dan yasan shi kad'ai ne zai iya taka mata burki a yanxu ya mike da'kyar yana shiga d'aki.

Washe gari asubar fari ko haske bai gama wayewa ba Iluh ya dira a gidan Balarabe tare da iyayen sa😔 tare dasu akai abun kari😲 farin ciki da murna a gurin Asabe kamar ta xubar ruwa a kasa tasha dan dad'i haka nan akai komai jikin Balarabe a mace kamar mara laka yace a fad'owa Dalah mahaifiyar tace tana da alhakin sani haka Asabe ta hana babu yadda ya iya taya labari ya jewa Dauda a tsegumin gari suna zaune ana tattaunawa sai ganinsa sukai shida Dalah sun shigo gidan zaro ido Asabe tai a ranta tace "to shi kuma wannan yaron uban waye ya fad'a masa har yazo".

"Dawa kikai shawara kike shirin yi mata auren dole saidai kiba da 'yarki Bahijjah domin itace kike da iko a kanta" Dauda ya fad'a yana zaro mata girman idonsa kallon Balarabe Asabe tai wanda ya girgiza kai yana cewa.

"Ahh ya kike kallona? ba nine wanda na gayyatosu ba".

Kai Dalah ta d'aga tana murmushi tace "eh mana babu wanda ya gayyato mu nan".

Sa'kwa'kwa Asabe tai tana kallon ta tace "mene babu wanda ya gayyato ku"?.

"eh a bisa ra'ayin kanmu muka zo".

"Me kenan"?.

"Au ke mekike inace kar'bar auren 'yata kika bararraje kinayi to muma shi mukazo yi saidai kin makara ki sani baki isa ba wallahi lokacin dana d'au cikin ta da wahalhalu baki sani ba na raineta dan haka baki da wani iko a kanta ganin dama tace nace ga wanda zata aura dan haka bari kiji ban amince da wannan za'bin naki ba".

Dariya Asabe tai tana cewa "dama kinji nace ki amince da za'bi na ai na riga na gama magana na basu aurenta nasa rana karshen watan nan maganar na isa ko ina da iko ya wuce aure kuma dole".

Kai Dalah ta jinjina tana cewa "au haba auren Bahijjah zaki ashe to Allah ya bada zaman lafiya idan ankai mana minti zamu zo musha biki mu shari taushe" sannan ta mayar da hankalinta kan Balarabe tana kallon sa shima ita yake kallo zatai magana a bazata taji yace.

"Dalah na dawo dake😲".

Zaro ido Dalah tai tana sake kallonsa da mamaki tace "me kace Balarabe"?.

Da gefen ido Balarabe ya kalli Asabe cikin tsoro da raunin murya yace "na dawo dake d'akin ki kizo kiyi bikin 'yarki da kanki".

A zabure Asabe tace "meee maimaita abinda kace Balarabe dan banji sosai ba ka dawo da ita ina"?.

Dariya Dalah tai tana cewa "ai dama bazaki fahimta ba amma idan kika ganni a cikin gidan na dawo zaki fahimta" maida hankalin ta kan iyayen Iluh tai tana cigaba "ku kuma kunga gaskiya dai ba 'yarta bace zura ku tai a kwalba dan taci kud'inku nice mahaifiyar yarinya bata shawarce niba bansan da wata maganar aure ba asali ma bansan d'anku ba saifa yanzu dana ganshi ni 'yata nayi mata miji dan Allah kuyi ha'kuri fatan ranku bai 'baci ba".

Murmushin ya'ke innar Iluh tai tana kallon Dalah cikin girmamawa tace "ayya karki damu

Please Login or Register in order to submit comment