Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi nace masa wani fa'kirin mabaracin qauye ne ya taso ya dawo nan da yaga barar bazata kaishi ba ya 6uge da sana'ar tumatur".

A tare suka kwashe da dariya Bara'atu harda doka kafa cike da jin dad'i tace "yauwa yar albarka nagode miki da baki nuna kanin ubanki bane balle ya taimaka masa ko ya ri'ka masa alkairi baki sani ba idan ya biyo layin hummm Habubakar a birni share Nafisa zanga uban dazai tara ya dawo dashi qauyen muna nan muna jiran dawowarsa a tsiyace kamar yadda ya tafi kada ki damu kinji kedai kisa ido sosai ki tabbatar kinsan sirrin dukiyar Nurain kinji" to Umma saida safe Nafisa tace Bara'atu dake Shirin mi'kawa Ilyah wayarsa tace.

"To Nafisa mu kwana lafiya amare mutanen binni uhm ana can ana jin dad'i nifa tun ranar ta tambaye ni wai yaya bikin Salma anyi nidai nace mata a'a bansan miyasa aka d'aga sosai ba".

Ta'be baki Ilyah yai yana cewa "tunda ita ce ta nace sai Adamun nikam ina ruwana ranar ma saida na samu fa'kirin uban nasa akan zancen auren amma cewa yayi wai na kara musu lokaci wallahi abubawan har yanxu sun rasa yadda zasuyi babu kud'i maganar da nake miki a yanzu kam Adamu baya gari wai ya tafi neman kud'i kona sadaki ya samo".

Kai Bara'atu ta jinjina tana cewa "hum'um ni dama da Maimuna zataji shawara ta da sai Salma ta had'a kayanta ta tafi gurin Nafisa ko wata biyu ta samu idan akai sa'a itama sai kaga ta samu miji acan ta huta zaman wahalar da take nemawa kanta domin auren irin su Adamu matalaunta wanda talauci ya gama samun gurin zama a jikinsu bala'i ne amma tunda tana sonshi bazata ga haka ba".

Kai Ilyah ya murgina yana cewa ''nikam ba ruwa na ainace idan ya kasa ri'keta bazan taimaka mata dako lomar abinci ba tunda ta yarda ai shikenan ga fili ga mai doki sannan da kike maganar wai ta had'a kayanta ta tafi gurin Nafisa so kike taje suyita wannan shegen fad'an nasu acan tasa Nurain ya sakota kinga an 6ata biyu ko ita bata auru ba taje tasa an sako wacce tayi"..

Zaro ido Bara'atu tai tana cewa "kuma fa haka ne gara da Allah yasa kayi wannan hasashen da wuri nikuwa har nasa araina Maimuna tana dawowa daga tafiyar nan zan fad'a mata tona fasa kowa yayi zamansa a inda yafi so nasan ko yanzu Nafisa tazo tafi qarfin raini bata da sa'ar gwaji a garin nan"..........

Shiru Salma tai duk abinda suke fad'a tana jinsu sun manta tana d'aki kuka kawi takeyi mara sauti tana share hawaye kuma abinda tasa a ranta shine zata auri Adamu koda ace kullum saiya fita ya nemo da aci zata zauna dashi zaman lafiya yafi zama d'an sรคrkรฏ.


Batun Nafisa Kam suna gama waya ta gyara kwanciya tana kunna kallo a waya Nurain ya shigo bedroom din yana kallonta yace.

"Ok na d'auka kinyi barci da naji shiru kizo kici abincin sun gama miki" jiki a sanyaye Nafisa ta mi'ke kamar zata fashe da kuka ya juya yana fita tana biye dashi batai tunanin sunan nanba ta d'auka suna ajiyewa zasu tafiyarsu qamewa tai ta'ki karasowa ganinsu zazzaune suna mata wani kallo.

"Kije kici abincin sun gama".

Shiru Nafisa tai cikin zulumi kafin ta d'aga kafa da'kyar kamar mai ciwon cinya ta fara tafiya taje ta zauna duk hankalinsu suka maida kanta ta yadd Nurain bazai fahimci komai ba bud'e kuular tai a bisa dole taga abincin d'an mitsitsi da'kyar in zata koshi juyeshi tai duka a plate tasa cokali amma me lomarta daya tana taunawa da sauri ta fito dashi cike da azaba ga yaji ga qarnin d'anyan kifi ga shinkafa d'anya dagowa tai tana kallon su wata uwar harara suka zuba mata duk su hud'un wanda ba arziki ta d'auke kai daga saitinsu tanajin idonta na kawo hawaye tsabar yaji.

Tashi Mimih tai tana cewa "bari nadan sha kayan marmari a gurin Aunty na" ta karasa maganar a wayance tana zuwa dinning d'in ta zauna Nurain hankalinsa nakan TV baisanma abinda suke ba.

Zama Mimih tana kallon Nafisa tare dayin kasa da murya saboda Nurain tace.

"Ke dabba abincin namu ba dad'i ne aina d'auka dabbobi basu san daidai ba komai aka basu zasuci dan haka maza yanzun nan ki cinye wannan abincin kafin na hallakaki gobe" ta karasa maganar tana zare mata ido da sauri Nafisa taja plate a bisa dolenta ta fara tura shinkafar da'kyar tana runtse ido su Meelat suna zaune suna kallonsu ta gefen ido dariya na cinsu batare da Nurain ya ankare ba Nafisa ta cinye wannan abinci sannan ta bata juice tare da cewa ta shanyeshi tas haka ta kar'ba tana xubda hawaye ta shanye ta kuma hanata bud'e baki tai shid'ar yaji kawai ta nuna mata kofar bedroom da sauri Nafisa ta shige da gudu cike da azaba agigice dan taje ta samu ruwa tasha yar dariya Meelat tai a hankali tanaiwa Mimih jinjina da hannu kafin suka mi'ke suna cewa.

"Ya Nurain saida safe".

Shikam sai lokacin ma ya lura babu Nafisan a gurin amma bai kawo komai ba tunda dama sanda ya shiga yanxu ma saida ya tasheta ta fara barcin dole da tsoron kada suyi girki taci shiyasa a ransa yayi zaton ko barcin zata koma.

Batun su Mimih kuwa suna fita suka fara 'bab'baka dariya suna shewa har part d'in zainab suka fad'a mata ga abinda ya Nurain ya musu sumaga abinda sukaiwa Nafisan ta'be baki zainab tai tana murmushi batace komai lallai ta yarda da Nanah da tace mata iya meelat da Mimah sun isheta balle ga Mimih da Meenah humm tana zaune ta sani zasu kora Nafisa karkara basai tasa baki ba.

MALAM HABU
Yau Aisha tana gidan Asma'u sakamakon jiya bata da lafiya suna asibiti acan suka kwana ta haihu yau da safe mace da namiji๐Ÿ˜‰ A'i da Binta suma suna can iya Saude ce a gidan domin malam Habu da sukaje asibitin ganota tare da Amatu suka dawo yadau kwandunan tumatur dana attaruhu su albasa da tattasai ya fita dasu da yake titi ne kad'ai ya raba tsakanin gurin sana'ar sa da gidansa yana ta baiwa mutane kayan miya ko zama baya samu yayi Amatu tana zaune a gefen bencinsa na zama tana d'inki hularta harta kusa kasheta.

Wata ba'kar kyakkyawar mota mai 'kirar range Rover ce ta parker a gefen titin sai 'kyal'kyali take baka ganin wanda yake ciki saidai na ciki ya ganka, tooo Bari mu le'ka muga waye a ciki.

Ajeeb ne ri'ke da sityarin motar yana kallon Ameer wanda shima ke kallonsa da mamaki yace.

"Ajeeb lafiya naga ka tsaya"?.

Kai ya d'aga masa "eh lafiya wani abu na gani bari nazo ko kazo muje tare".

"No jeka dawo ina jiranka" Ameer ya fad'a yana jingina bayansa da kujera tare da rufe ido.

"Ok bari na dawo bani minti biyar" fita Ajeeb yai yana zuwa gurin Malam Habu da sallama daidai ya gama baiwa kowa suka gaisa yana cewa.

"Dan Allah wannan 'yarka ce"?.

Kai Malam Habu ya d'aga "eh 'yata ce".

"Ok ka bani dama nayi magana da ita anan a gabanka dan Allah"?.

Nanma kai Malam Habu ya d'aga masa yana cewa "ba damuwa bismilllah".

Cikin girmamawa Ajeeb yace "nagode sosai" kafin ya juya inda Amatu take yana gyara tsayuwarshi yace "am wannan hulan na saidawa kike''?.

Kai Amatu ta d'aga "eh na sayarwa ne".

"Ok yanzu wannan d'in zatai nawa"?.

Daina d'inkawa Amatu tai tana kallon hular tace "zata iya takai dubu biyar ko shida ko kuma dubu shida da d'ari biya hawa hawa ce".

"Ok mu gani" Ajeeb ya fad'a yana kar'bar hular ya fara dubawa tayi kyau sosai kalolin zaren su fito amma yafi so ayi musu iri daya su shida mai Martaba mai girma Alhussain da su mi'ka mata yai yana cewa.

"Ina son kimin irinta guda shida duka iri daya ki fad'a min kud'in a nawa zakiyi"?.

Shiru Amatu tai zuwa wani lokaci tace ''tunda da yawa kake so zaifi sau'ki ka biya kud'i sayo yanki da zararrika saidai kawai ka biya kud'in d'inkawa idan a haka zaka saya gaskiya da tsada"..

"Ok bari to nakawo miki kud'in sai kiyi mini lissafin abubawan" to tace ya juya yana d'auko kud'i a mota Ameer baice masa komai ba tunda yaga hular da yake d'agawa maybe a kanta sukai magana komawa Ajeeb yai tayi masa lissafi tas ya d'au kud'in ya biya harda na d'inkin kowacce zata d'inka masa akan dubu uku da d'ari biyar sannan yace.

"Idan kin gama taya zan sani sai nazo na kar'ba"?.

"Bani da waya saidai kasa numbar a wayar babana ta fad'a tana mi'ka masa karamar tecno kar'ba yai yasa mata har zai juya ya sake tsayawa yace.

''ina fata anan anguwar kuke"?.

Kaita d'aga "eh anan muke ga gidan mu can" ta karasa maganar tana nuna masa kallon gidan yai kafin yace "ok sai naji ki dan Allah kiyi d'inki mai kyau kuma ki gama da wuri domin ta angwaye ce" to tace masa sannan ya juya yaje ya shiga mota suka wuce.

Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tana kallon kud'in iya ladan d'inkin ta dubu ashirin da uku guda shida banda Wanda za'a yo musu sayayya tun yace a matse yake ta biki ce saidai ta raba musu ita biyu Binta daya A'i daya Saude daya Aisha daya safi gamawa da wuri..........

Katse mata tunani malam Habu yai da murmushi akan fuskarsa yace ''masha Allah mamana kullum d'inkin ki qara haskuwa yake gashi yanxu an baki kud'i a hannu tun kafin kiyi Allah ya kara basira da tsayuwar hannu".

Itama Amatun murmushi tai tana cewa "Amin baba nagode da addu'a bari naje na shirya yanzu na sayo kayayyakin saina rabawa su umma kowa d'aya mufi saurin gamawa " ta fad'a tana mi'kewa to mamana Allah ya tsare min ke saikin dawo ya karasa maganar yana binta da kallo harta shiga gida yana matukar son yarinyar nan a rayuwarsa baya iya had'a son da yake mata da kowa.

Ajeeb suna tafe a hanya Ameer ya kalleshi yana cewa "kai kud'in me ka baiwa wannan budurwar kuma ai banga ka sayi hular bako"?.

Kai Ajeeb ya d'aga "eh ban saya ba guda shida nace tayi iri daya sabida bikinka kaida Shaukiyyah" dariya Ameer yai wai da gaske kake harda Asad kenan ka tabbata zaisa hular".

Kafad'a Ajeeb ya d'aga "oho masa shiya sani idan baisa bama matsalarsa ce basai in zaizo bikin naku ba tunda mugun d'an rainin hankali ne".

"A haba meka mayar da Asad d'in zai zo man Kaine dai zakayi taka tsantsan karka kulashi kuzo kuna dambe ana biki ga ba'ki kuyi abun fad'a".

Dariya Ajeeb yai yana cewa "Asad ga'bo kenan ko kadan yaron nan baida hankali kasan kwanan baya cewa yai sai yayi retire zaiyi aure".

Da mamaki Ameer yace ''retire dai kai haba da wasa yake"?.

Kai Ajeeb ya girgiza "kai wallahi bada wasa yake ba Asad yadda yake d'anye aka barshi da gaske yake har zuciyarsa sai yayi retire zaiyi aure kuma wai hakan ma biyu yake rabawa zaiyi ko bazai yi".

"Kuma kai kana ganin su Abba zasu barshi"?.

"Oho waya sani sai lokacin yayi nima dagewa zanyi na samu matar aure a had'a nawa da naka Annur tunda shima d'an uwan Asad d'in ne ya'ki fitarwa sai suma suyi tare yarinyar nan Khaldiyyah tana shan wahalar soyayya da Annur zai tausaya mata daya amince ya bata lokacin sa kuma tana da hankali da nutsuwa Allah ko duk ta fisu nutsuwa".

Had'e rai Ameer yai "no malam sa munjaye cikin maganarka banda wife d'ina Shaukiyyah dai ta fita" dariya Ajeeb yai yana cewa "oh masu amarya sorry fa aina manta ne".

"Yanzu na tuna maka ko"?.

"Haka Allah dai yakai mu da nisan kwana musha walwali tunda dai wannan shine karo na farko da za'ai biki a masarautar dole a bada mamaki a xubar da dollars Naira zatai kuka ina Annur banker ranar tasace" dariya sukai tare Ajeeb daidai yayi horn a kofar gate din shiga masarautar na farko aka bud'e musu suka wuce zuwa ciki suna cigaba da sake tattaunawa.

Ajeeb dake kallon Ameer yace "amma nima fa Ameer har naji wani abu game da yarinyar nan".

"Wacce yarinya kenan"? Ameer ya tambaye shi cikin rashin fahimta.

"Yarinyar da nasata d'inka mana hula".

Zaro ido Ameer yai ''haba dai mutumina wai da gaske kake"?.

"Kwarai Ameer da gasken gaske amma dan Allah dagani saikai kada ka fad'awa kowa ka bari na gama yanke shawara duk abinda zuciyata ta yanke min idan na samu Abba mukai magana shikenan sai kowa yaji fatan zakai min wannan alfarmar"?.

Kai Ameer ya d'aga masa "ok Ajeeb kada ka damu ai kallon farko naga kamar yarinyar zatai hankali".

"Ba kamar bane Ameer akwai nutsuwa a tattare da ita wannan shi yaja hankalina ba komai ba kyan abun ace irin matar da Asad zai aurace saita saitashi ya dawo hanya".

Dariya Ameer yai yana kallon Ajeeb yace ''kai kam duk wata kalan magana ka iya yanzu da yana kusa kila da yanxun ku fara sana'ar taku ta fad'a duk da gaskiya ka fad'a".

Parking Ajeeb yai suna fitowa yace "hum Ameer kaidai 'kyale kawai zanje nayi tunani idan har yarinyar akwai alkairi a tattare da ita Allah ya tabbatar min" Amin to Allah ya yarda Ameer ya fad'a suna yin 6angarensu.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE ๐Ÿ˜˜.
See you tomorrow morning.

โœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธโœˆ๏ธ
๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš๐Ÿš
๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ๐Ÿ›ฌ
๐Ÿš€๐Ÿš€๐Ÿš€๐Ÿš€๐Ÿš€๐Ÿš€๐Ÿš€๐Ÿš€
๐Ÿ›ซ๐Ÿ›ซ๐Ÿ›ซ๐Ÿ›ซ๐Ÿ›ซ
๐Ÿ›ฉ๏ธ๐Ÿ›ฉ๏ธ๐Ÿ›ฉ๏ธ๐Ÿ›ฉ๏ธ
๐Ÿ›ฐ๏ธ๐Ÿ›ฐ๏ธ๐Ÿ›ฐ๏ธ
๐Ÿ›ธ๐Ÿ›ธ
โœˆ๏ธโœˆ๏ธ
โœˆ๏ธ

TYPING๐Ÿ“ฒSun, Sep 1โ„ข/24 6:30AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR๐Ÿ’‹.

๐Ÿ‘‘Mรช kรขmรขr sรขrkรฎ๐Ÿ‘‘

โœ๐Ÿป Mrs Al'ameen Ahmad ce๐Ÿ˜˜

______________๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_______________________โœ๐Ÿฝ
______________________________๐Ÿ‘†๐Ÿป
๐Ÿ’ซANNUR WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ’ซ HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY.


69~AL-AHDU
The Indivisible
70~AS-SAMAD
The Eternal

33~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin Sahibul siradul musta'kimi.

๐ŸŒ„ THREATEN๐ŸŒ„
Episode 69&70
GIDAN NURAIN
________Nafisa na kwance akan gado tana sharar barci taji an bango kofa a tsorace ta tashi zaune kafin ta farga Mimah da Meelat sun d'ago ta suna yin waje da ita har saida suka kaita garden kafin cike da mugunta suka saketa tass ta fad'o a hanzarce ta mi'ke domin batasan me zasuyi mata ba tana mi'kewa Mimih data karaso ta hankad'a ta gaba ta kifa ta sannan kafin ta d'ago ta watsa mata kayan wankin dake hannunta aka tana cewa.

Mimah kuje ku d'ebo naku dama saboda ke dabba ce mara hankali an fad'a miki hutu kikazo? hummm ri'ko kunnen ta tayi daidai su Meelat su dawo da himilin kaya a hannunsu harda na Nurain Zainab da Amnah da Auta wasu kayan ma ba'a sasu haka suka mutsurttsuka su sukai squeezing kawai dan su hanata zama.

Mimih dake ri'ke da kunnenta tace "ke jakar inace muna barci kina barci ke kin isa ki had'a sa'a damu tab ashe kwana kusa zaki gangara lahira domin saimu kasheki mun kashe banza babu Mai tuhumar mu miya faru saboda dama abinda ya dace dake kenan ugly girl kawai".

Ta karasa maganar tana tureta meelat dake tsaye tana jijjiga tace "hum bari kawai Mimih ni harna rasa ma me zance akan wannan bagidajiyar bulkumar yarinyar kamar wanda tunanin ta ya fara gushewa a fad'a Mata magana ta'ki ji aiko wahala zatasa ki fahimta ga ruwan fountainโ›ฒ can yana zuba kije ki d'ebo ki wanke mana Kaya sannan idan kin gama ki zauna sai sun bushe tas ki linkosu dama abinda ya kawo ki birnin kenan 'yar matsiyatan qauye masu son zuciya".๐Ÿ˜ HUMM 'DAYA KENAN SU ILYAH AN FARA SHAN TSINUWA

Shiru Nafisa tai jikinta na rawa kamar mazari ko wacce kid'a ya ratsata cikin mamaki Mimah tace "kin wuce kin d'ebo ko sai nayi shot dake da'ki'kiya kin tsaya kinyi wani saroro ya qawar bora kina kallonmu munyi kama da tsofinki ne ko bakyar jin hausa zaki wuce ko saina fasa miki wannan ru'bab'ban bakin da ha'kora sunyi ja sun mutu tsabar tsananin qazanta ba'a musu brush".

Da sauri Nafisa ta wuce har tayi nisa muryarsa na kakkarwa 'kafafunta ma haka tsabar tsoro tace "Ina sabulun"?.

A fusace Meenah tace "yana gidan ubanki shegiya bagidajiya kuma idan kin gama kizo kiyi moping a falo sannan ki gyara bedroom d'in Aunty Zainab kuma saura kiyi mata sata yau a gidan nan na gidan yari saiya fiki jin dad'i sai munyi miki faca-faca da jini" tana kaiwa nan fuuu suka bar gurin haka Nafisa tayita tsoma kayan a ruwa tana d'aurayesu babu wanda aka saka a ciki wankakku ne saida ta gama ta d'auki bokitin ta nufi parlor ta manta cewa sunce ta tsaya ya bushe tana shiga duk sun hud'un suka daka mata firgitacciyar tsawa wanda da gudu ta juya cikin firgici jikinta yana rawa taje ta shige cikin wasu flowers masu duhu ta 'buya domin ta d'auka sun biyota.๐Ÿ˜ฃ NAFISA ANYI AUREN BIRNI ANATA SHAN DA'DI Kร‚Mร‚R YADDA AKE SO.

Kusan kullum Ajeeb saiya Kira Amatu yace ta gama hular yazo kar'ba a sati daya ya dameta har gajiya tai tace masa da wahala ya karasa mata lokaci sannan tadan samu salama har suka kammala bai sake kira ba sai ranar sunan yaran Asma'u ta kirashi tace masa yazo bayan sallar la'asar ya kar'ba.

Hum suna fa yau an gwangwaje an zubar da kud'i a gidan Alhaji Musa haka ya musu takwara shida Hajiya Aisha za'a ri'ka kiransu Imam da Imaan a gajiye Amatu suka dawo gida ita da Aisha saidai sakamakon ita Aisha yau tana da ba'ko yasa suna shiga gida bata zauna ba tahau hidima saurayin ta zaizo daga sabuwar qofa sunansa Safwan Amatu ce ta tayata suka gama komai harta manta da cewa Ajeeb zaizo kar'bar hula tana zaune a kofar d'akin Binta Malam Habu ya shigo da sallama yana cewa.

"Mamana kin manta yau kika cewa yaron nan ya dawo ya kar'bi hulunan fatan kun gamasu duka ko gashi a waje yana jira"?.

Mi'kewa Amatu tai tana cewa "eh baba na gama na manta yau zai zo bari na kawo masa ina zuwa yanxu".

"To kiyi sauri" malam Habu ya fad'a yana fita daga Amatu ta fito da ba'kar leda a hannunta tana saka babban hijab har qasa yake ja sannan ta fice yana tsaye jikin mota yau shi kad'ai yazo yaci wanka um abun ba'a cewa komai idan ana sallah ba'a magana karasawa tai da murmushi a fuskarta tayi sallama tana cewa.

"Ayya yi ha'kuri dan Allah Ajeeb ko? ga sa'kon ka duba ka gani sunyi"?.

Kar'ba Ajeeb yai yana d'orawa a saman mota sannan ya d'auko d'aya yana dubawa caf gaskiya d'inkin ya d'inku kamar da inji kuke yi Amatullahi ni harna fara kokwanton anya da hannu kukeyi"?.

'yar dariya Amatu tai tana kallon hular tace "wallahi da hannu ne idan ka duba zakaga biyu sunfi d'inkuwa sosai sun matsu nice nayi sauran kuma umma tace da sauran".

Kai ya d'aga "ok ba damuwa wanda suka fi d'inkuwar sai a baiwa su Abba amma nace kinsan inda ake rufawa"?.

"Eh shima rufin munayi ai bansan harda shi kake so da yanxu nayi maka nakai an wanke".

"Nawa kuke rufin"?.

"Guda d'aya dubu d'aya".

"Inda ake wankin fa"?.

"Eh gaskiya nan bansan nawa bane saidai idan na tambaya sai baba ya kiraka ya fad'a maka".

"Ok shikenan nagode sosai Amatullahi bari na tafi gashi idan kin rufe kin kai gurin wankin sun fad'a kud'in ki kirani ki fad'a min".

"To insha Allahu Ajeeb zan kira sai an jima" kar'ba tai ta juya dasu shima ya shiga mota yabar gurin.

Saboda tasan zai iya kiran Malam Habu yace kota tambayo yasa washe gari Aisha ta rakata suka tambaya ta kirashi ta fad'a masa a ranar suka rufa takai gurin wankin tace mesu yace ayi musu sitati sosai aiko sunyi mugun kyau data kar'bo saida taje har gurin Asma'u ta aro babbar waya tazo ta d'auki photonsu dare Ajeeb yazo kar'ba humm abun mamaki abun bazata saida suka gama zancen hula ya bata kud'in harda ihsani karshe yace yana son zasuyi magana mai muhimmanci har Amatu ta tsorata da taga yayi mata serious face๐Ÿ˜ ta d'auka wani abu ne sai kuma taji ya furta mata kalmar SO๐Ÿ’“๐Ÿ™Š abinda bata ta'ba kawowa a ranta ba aiko yana rufe baki ta girgiza masa kai bata iya cewa komai ba da gudu ta shige gida Ajeeb yayi mamaki har yayi wani tunanin dabam daya koma gida gashi yanzu sun ware babu abinda zai sake tambayar ta balle ya Kira wayar malam Habu yace a bata.

Kwanaki kusan goma daya kasa ha'kuri ya kira malam Habun dole yace dan Allah ya had'a shi da Amatu zasuyi magana tunda taji Malam Habu yace mata yaron nan dataiwa hula ne gabanta ya fad'i itafa harta manta dashi da'kyar ta kar'ba jiki a sanyaye ta shiga d'akin su ta zaune tambayar ta ya farayi wai abinda ya fad'a Mata ne bata nemansa sannan ya yaji muryarta ta canza ta fad'a masa meye laifi a ciki dan kawai ya fad'a Mata abinda ke ransa amma indai dan haka ne ta kwantar da hankalinta ya bari sai tayi tunani ya bata lokaci bai jira tace masa komai ba ya kashe kiran tagumi Amatu tai ita yanxu ya zatayi tsakani da Allah wannan saurayin ba sa'an aurenta bane bataso tasa kanta a damuwa ta fiso ta auri talaka daidai da ita wanka zai riketa da kima ya ri'ka ganin darajarta bataso tayi aure inda za'aga kud'i tabi tunda duk wanda yahau motar kwad'ayi zai sauka a tashar wulakanci amma xatai tunanin sannan zata fadawa mahaifanta duk abinda suka yanke saita kirashi ta fad'a masa.

๐Ÿ•๏ธQAUYE๐Ÿ•๏ธ
Asabe tana zaune da dare tasha magani kenan ta kwanta taji ana yarfa guda an shigo gidan Aliya ce a gaba ga sauran mata sun rako Dalah mi'kewa tsaye tai ba shiri a zabure tana cewa.

"Me zan gani wannan"?.

Amsa 'kanwar Dalah ta bata "yaya Dalah zaki gani wannan ta dawo gidan Balarabe au bai fad'a miki zata dawo d'akin taba kenan? To ai gashi yanzu da muka zo kin sani ko".

Bakin kofar d'akin Asabe taje ta tsaya tana cewa "wallahi Balarabe bai isa ba banga shegiyar data isa ta bud'e wannan d'akin ta shiga idan kuma akwai wacce takejin ta cika ta gwada"?.

Dariya Balki tai tana kallon Asabe tace "tofa wai matar dake ji da kantace har take fad'a humm kodan zaki aikata Asabe haline a jikin rai amma ki sani maganar wai Dalah bazata shiga d'akin nan ba qarya ne domin ba gidan ki bane auroki akai kamar yadda itama aka auro sannan a gidan kika fara zuwa kika sameta munafirci da ba'kin hali yasa saida kikai silar da aurenta ya mutu shiyasa yanxu dubunki ta cika asirin da kikaiwa Balaraben ne ya karye saiki sake boka domin baki taki sa'a ba".

Zaro ido Asabe tai tana kuka kura ta sha'ki Balki da dambe tana cewa "inji uban waye yace miki asiri nayi masa ya rabu da Dalah halinta ne ya koreta kuma wallahi wannan maganar da kika fad'a min sai kinyi dana sanin ta''.

Ru'kumewa da kokawa sukai suka dake dake Aliyah data kasance babba batai magana ba saboda gudun kar ace itace ta fara sanya fitina sai da taga fad'an bana karewa bane tacewa Dalah ta shiga d'akinta da bismilllah sannan aka raba fad'an da Balki take da Asabe tana kallon Asabe tace.

"Kinga Asabe mufa ba fad'a ya kawo muba amma tunda idonki ya rufa bazaki fahimta ba Allah ya sauwa'ke mu mun wuce" Aliyah na maganar tayi gaba sauran matan suka bita a baya suna fita Asabe ta fad'a d'akin Dalah tana cewa.

"Ke marar zuciya wacce kare ya lashewa kurwa tsabar asaranci ba'a sonki kina cuso kai Saida kikai masa asiri ya dawo dake ko to wallahi bari kiji yau bazakiyi kwanan gidan nan ba bari Balaraben ya shigo naji uban daya bashi shawarar ya dawo dake saiya min bayani'' dariya Dalah tai zatai magana sukaji sallamar Balarabe juyawa Asabe tai ta fice daga d'akin a masife tace..

"Balarabe kaine ka dawo da Dalah gidan nan"?.

Kallonta Balarabe yayi yana cewa "eh nine na dawo da ita".

Yana rufe baki tace "kaine ka dawo da ita da izinin ubanwa"?.

A fusace Balarabe yace "da izinin ubanki Asabe shi yace na dawo da ita ba neman wanda ya bani izini kike ba to shine ya bani izini"?.

Ba Asabe data kusa kifawa kasa ba tsabar tsananin mamakin daya rufeta hatta Dalah Saida ta fito waje taga Balarabe da gaske yayi maganar ko wani ne mai murya irin nasa ganin shine d'in dai yasa Dalah zaro ido tofa nesa tazo kusa akwai wani abu a 6oye kallon Asabe wacce ta daskare guri d'aya tai idonta duk sun fito waje kafin ta jinjina kai tana juyawa ta shige d'aki domin wannan tsakanin sune ba abune wanda ya shafeta ba rabonta da gidan ta dad'e.

Matsowa kusa Asabe tai tana qure

Please Login or Register in order to submit comment