Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba hummmmm yana ji yana gani suka turo shi waje suka fece da adedetar😵 jiyai hajijiya na d'ibansa yana ganin duhu da'kyar ya samu ya zauna yana kifa kansa zuwa wani lokaci jin ya dawo daidai ya mi'ke cikin wani irin yanayi yanzu daya zai kalli Alhaji Musa mutumin dayai masa halacci ya mayar dashi tamkar d'an uwansa na jini ya bashi komai ya yarda dashi fiye da yadda ake zato innalillahi wa Inna ilaihi raji'un😭 tsabar ba'kin cikin daya tsinci kanshi a ciki baisan sanda ya fara tafiya da kafa ba yana gani biyu-uku hudu-biyar idansa yayi dishi-dishi haka ya dawo gida jiki a mace ya tarar kowa idonsa biyu babu wanda yayi barci sakamakon rashin ganin dawowarsa kan lokacin daya saba amma a yadda ya shigo musu yasa duk suka mi'ke a rud'e suna tambayar sa lafiya basu sake gigicewa sun shiga d'imuwa ba sai lokacin da yace musu ya had'u da 'barayi su kar'be masa adedetar harzai taho gida suka tareshi ya kaisu Gaida ashe silar mashin din ya fita daga rabo ne.

Tabdijan sunyi salati sunyi sallallami harda masu kuka a ranar basu iya runtsawa ba kowa ya shiga d'aki dai kawai amma suna zazzaune akan taburmi ne har asuba sukai sallah gari ya waye ganin shiru bai dawo musu ba yasa sukai tunanin ko ya tafi gurin Alhaji Musa ne ya fad'a masa halin da ake ciki.

Batun malam Habu kam yaje kofar gidan Alhaji Musa yasa mai gadi yayi masa sallama dashi amma shima Alhaji Musan a yadda ya ganshi yasan ba lafiya shi har yayi zaton ko wani ne ya rasu a cikin iyalansa da sauri ya tareshi da tambaya.

"Malam Habu ina fata dai lafiya na ganka sassafe haka ga wani yanayi a tattare dakai meyake faruwa ne"?...

Sauke kai malam Habu yai cike da kunya da takaicin ta Ina zai fara fad'a masa ga abinda ya faru da adedetar sa zaiga sakensa bazai iya fuskantar sa da maganar ba har saida ya sake tambayar sa sannan da'kyar ya iya fad'a masa abinda ya faru har hawaye na taruwa a idonsa wajen bayani.

Saidai abinda ya bashi mamaki daya gama fad'a masa sai yaji yayi shiru bai tanka ba haryai tunanin ko ransa ne ya 'baci amma daya d'ago sai yaci karo da murmushi akan fuskarsa yana kallon malam Habun da mamaki tsantsa ya'ki 'boyuwa a tare dashi yace.

"Haka ne malam Abubakar naji jawabinka kuma na gamsu sannan nad'au 'kaddara Allah ya mayar min da dubunta karka damu ba kaine mutum na farko wanda aka kar'be adedeta na a hannunsa ba inada yara masu min hayar Napep zasukai su arba'in amma maganar da nake maka an 'kwace min Napep yafi qarfin a kirga tun ina lissafawa harna gaji na daina tunda bashi da amfani lissafin dama haka ne dole wata rana in kana da kaya jarrabawa ta shigo ciki sai kaga abinda zai sameka ya samu kayanka babu damuwa malam Habu zuwa nan da karfe goma idan na shirya zuwa office zanyi maka magana muje store ka sake d'aukar wata Allah ya kiyaye gaba su kuma masu kwacen Allah ya shiryesu".

Malam Habu yaji matukar dad'i sosai kuma ya yaba dakyan zuciyar Alhaji Musa baiji kwanciyar hankali da sanyi aransa ba tun jiya sai yanxu da yazo sukai magana ko abinci bai samu jiya yaji ba da dare yadda aka kawo masa shi yana nan a rufe a d'akinsa humm da harya fara tunanin da yadda zai biyashi kud'in adedeta😥 .

Komawa gida yai ya fad'a musu suma sai lokacin suka samu kwanciyar hankali daga nan aka fara gyara gyaran gida mai girki ta d'ora abun kari yan makaranta kowa tai shiri bayan sun karya suka tafi domin yanxu Hajiya tace su ri'ka bari idan su dawo a school sai suzo gurin aikin tunda itama da safen bata nan tayi office saidai ranar weekend ne suke zuwa tun safe sukai daidai lokacin zuwa islamiyyah saisu mata sallama su tafi.

TANKO/MUDI🏕️
Zaune suke gaban boka wanda idonsa ke rufe sai surutai yake suna sauraronsa saidaya gama kafin ya bud'e ido yace.

"Ina jinku da me kuka zo yau"?.

Kallon juna sukai suna jinjina kai Tanko dayai gyara murya yace "ran boka Hambuwa ya dad'e dama matsala ce ta sake kawo mu yauma kamar kullum duka dai akan wannan mutumin wancan siddabarun dakai masa ya sameshi mu kanmu shaida ne mun gani da idanuwanmu a tsiyace ya dawo gida bai shigo dako naira biyar ba hatta abokinsa wanda suka tafi tare saida abun ya shafeshi to yanzu kuma ana cikin haka rana tsaka ya tashi yabar gari shida iyalansa bamusan inda ya tafi ba boka tsoron mu kada muje mu saki baki kwatsam mu ganshi ya dawo qauyen sannan ya zama mai arziki shiyasa muka zo gurin ka zamu baka komai da kake so amma kada ka barshi ya ri'ke koda naira biyar tasa balle ya tara wani abu wanda zaiyi alfahari dashi muna so kasa duk abinda ya ta'ba koba nasa bane abun ya narke ya zama dai komai yayi masa zafi bamaso yaji dad'i har karshen rayuwar sa".

Kai boka ya jinjina yana cewa "kun taki sa'a kunzo a daidai lokacin daya dace domin maganar da nake muku a halin yanzu ma yana cikin kwanciyar hankali dajin dad'i a inda yake babu abinda ya nema ya rasa komi a wadace yake".

Zaro ido sukai cike da firgici Mudi dake girgiza kai yace "inaa boka hakan bazai ta'ba faruwa ba jin dad'in nasa nadan lokaci ne bama so ya sake koda d'igon murmushi ne a rayuwarsa a sanya masa ba'kin ciki da rashin sukuni har abada sannan ka tura masa aljani shed'ani ya d'ora masa masifu iri iri kada ya barshi ya huta kuma hatta wadannan 'ya'yan nasa kada a barsu suyi aure boka haka muke so".

Ihu boka yai yana cewa "an gama za'ai komai yau kamar yadda kuka bu'kata zai shiga damuwa da 'kunci har abada sannan za'a dad'a masa rariyar hannu komai zai ta'ba saiya narke baza'a barshi ya sake ba".

Kai Tanko ya d'aga "yauwa boka Hambuwa hakan nake son ji ko hankalina zai kwanta amma taya za'a ce malam Habu zai yi arziki ina raye tabd'i humm wallahi bazan bari ba so nake komai ya sa hannu akai ya zama kamar ansa wuta ya 'kare abunda ya tara a zuwansa boka ka tura aljanu su 'koneshi sannan me zamu kawo maka abun ladan aikin"?..

Dariya boka yai yana cewa "babbakakken bunsuru shi zaku kawo kullum tsawon wata d'aya shine ladan aikin".

Kai Tanko ya d'aga "shikenan boka za'a fara kawowa daga gobe wannan ba matsala bace tunda muna da kud'in mu bamu da damuwar komai bamu rasa komai ba mu taka kowa mu murtsuke ba yadda aka iya damu mun zama gagarau nan gani nan bari d'umamen mayya😨 tashi mu tafi Mudi boka saika ganmu gobe da babbakakken bunsurun ka🐏 za'a kawo maka shi tun yana kan zafinsa kamar yadda kaima kake mana aikin mu da d'umi d'umi" Tanko yana gama fad'in haka suka tafi suka bar boka yana surkullen aikin asirin dazai yi musu wanda zai aikashi kan malam Habu😥.

🚶🚶🚶🚶🚶
Tafiya dai tafiya sakewa Malam Habu adedeta baifi wata takwas ba tsautsayi ya sake shigowa ciki wani mai mota ya bugeshi ya fad'i adedetan ta mammokad'e ya d'an samu ciwo kad'an a jikinsa mutumin ya bashi ha'kuri sannan ya kaishi asibiti ya biya kud'in maganin ya sake daukoshi ya dawo dashi gida ganin yadda yake da iyalai yasa mutumin bayan ya koma gida ya kawo masa kayan abinci masu yawa harda taimakon suturu masu tsada duk da kunce ne amma bazaka ta'ba cewa an sasu ba sai tashin kamshin turare suke umm kayan alhazawa malam nan ma dalilin wannan abu malam Habu yayi samuwa a gurin wannan mutumin ya dagoshi Sosai harda jari ya bashi.

Dan haka daya warke yacewa Alhaji Musa kada ya sake bashi adedetar sa domin shi dama sana'a bata kar'beshi ba yana ta'ba kaya ake samun matsala yanzu wacce sana'ar zai kama Alhaji Musa ya bashi shawara kawai ya saro kayan shago zai bashi kwantaina ya zuba ko Allah zaisa ya dace.

Haka malam Habu yai yaje yayo sarin kaya mai yawa ya cika kwantainar fal kuma kamar wanda yai Kiran kasuwa haka jama'a ke rubibin shagon saidai fa ba'a ci nisan zango ba shago yayi hayam babu kaya ba kud'i kamar ansa wuta an 'kone malam Habu ya shiga rud'u sosai ganin bashi da damar yai sana'a ta gari yayi bakin ciki ya kara.

Alhaji Musa ya sake bashi jari a karo na biyu duka dai sai an fara abu ciniki caf caf kamar gaske sai kud'i ya narke daga nan nefa abu yayi yawa komai malam Habu ya ta'ba saiya narke damuwa goma da ashirin ta dameshi dan haka Alhaji Musa yace yasan wani malami ya shirya suje gurin sa su gani ko saka hannu ne farko malam Habu bai amince ba yace ba saka hannu dama ya dad'e idan ya ta'ba abu saiya zama babu kamar mai rariyar hannu daga baya ya yarda suka je yayiwa malamin bayanin komai abinda ke damunsa da rayuwar dayai a bayan domin malamin ya tambayeshi da fari yaya mu'amalarsa da iyayensa sun rabu lafiya yace masa eh dan haka malamin yace to indai ba hakkin iyaye ne ke bibiyarsa ba akwai wani abu a kasa zai masa istahara zuwa nan da jibi su dawo zai fad'a musu komai godiya sukai masa suka dawo gida haka malam Habu yayita zulumin Allah yasa dai lafiya gabadaya ya hana kansa sukuni Allah Allah yake su koma yaji meke faruwa dashi.

Bayan kwana biyu Alhaji Musa ya d'aukeshi a motarsa suka koma kamar yadda malamin yace masu su dawo saida suka gaida dashi suka samu nutsuwa sannan ya fara koro musu bayanin abunda ya shigewa kowa duhu harda shi uban gayyar (malam Habu).

Yace musu tabbas akwai 'boyayyan abu a jikin malam Habu tun shekarun da suka wuce a baya an turo masa muyagun mugayen baka'ken aljanu masu had'ari sun shiga jikinsa duk wata damuwa da tashin hankali su suke sakashi a ciki sihiri akai masa dasu asiri akai masa wanda aka hada da gashin kansa akai shiyasa asirin bazai ta'ba barin jikinsa ba saidai in mutuwa yai amma hanya d'aya za'a iyabi a kawar da komai hanyar itace za'ai kokarin rabashi da aljanun a masa magani asirin yabar jikinsa domin shed'anun zamansu dabam asirin ma zamansa dabam kowanne yayi mugun karfi da tasiri a jikinsa saboda shekarun da aka d'auka abun nacin jikinsa fitar da aljanun yana da wahala saboda kafurai ne kuma masu taurin kai shiyasa za'a fara da karya asirin tukuna idan an dace sai a dawo kansu insha Allahu komai zaizo karshe za'a fara bashi magunguna yana yi kuma kada ya tsallake koda rana daya yabi umarnin maganin zai dace sannan malamin yace shi baya kar'bar abun sadaka sai anyi an warke dan haka sukai masa godiya daga ranar ya fara aikata duk abinda malamin ya bashi ya kuma bashi addu'o'i kala kala safe da yamma yanayi ba tsallake.

Kusan wata uku nan ma aka ci amma asirin bai karye ba har malam Habu ya d'ago daga lamarin kamar abun wasa rana tsaya yana tsaye yaji hajijiya tana d'ibansa karshe ya fad'i kumfa na fita a bakinsa yana wata irin kara jikinsa na kakkarwa yana harbe harbe tun safe har dare kusan kwana yai yana buge buge harda haya'ki ne ke fita ta hancinsa sai wajajen asuba sannan jikinsa ya saki ya zama kamar gawa shiru jikinsa yayi laushi kuma sanyi qalau dukkan matansa da yayansa suna kansa suna masa addu'a suna share hawaye haka suka je kowa yai sallah suka sake dawowa kansa nan ma bai farka abun yanata basu tsoro kuma dama malamin yace kada a tasheshi saiya tashi da kansa ganin abun ya zarma tunaninsu yasa dole suka nemo Alhaji Musa yayi waya da malamin ba'a dad'e ba sai gashi yazo ya du'kufa a kansa da karatun al-qur'ani da addu'a nan wani sabon kururuwa da buge bugen ya tashi yana mummurd'ewa yana gwara kansa a bango can malamin ya mike yana zuwa inda yake ya kamashi da karfi ya daidaici tsakiyar goshinsa ya fara tofa masa addu'a da tsakiyar kansa a hankali jikinsa yake saki yana yaushi can ya zube a jikin malamin karasa kwantar dashi yai yana fita a d'akin da murmushi a fuskarsa yace sihirin dake jikinsa ya gama ficewa dukka dalilin da yasa sukaga bai farka ba wani asirin akayo masa kwanan nan kuma shima tare da aljani aka hada to alhajinin ne ya ri'ke dukkan sihirin ya hanusu fita shiyasa da ya kama barci bai farka ba amma yanxu ko minti talatiin bazaiyi zai tashi kuma kada wanda ya fad'a masa ga abinda ya sameshi suyi shiru malamin yana gama musu jawabi ya tafi.

Suna zaune a waje sai ganin Malam Habu sukai ya fito yana kalle kalle kamar wanda yai batan kai cikin basarwa Binta tace.

"Malam lafiya ko buta kake nema"?.

'Dan shiru yai yana kallon ta zuwa wani lokaci yace "eh Ina take na duba bata d'aki na kuma duk sauran kayana ma ban gansu ba ina kuka kaimin"?.

Murmushi tai tana cewa "ayya yi hakuri Malam dama mamar gida ce tace d'akinka yayi datti zata gyara maka idan suka dawo daga makaranta itace ta fara fito da komai".

Kai ya d'aga "au shikenan to aina d'auka ko sune suka fito da kansu daga d'akin" ya fad'a yana d'aukar buta yai hanyar bayi dariya Binta tai tana cewa.

"Kiji dan Allah wai kaya su kawo kansu waje uhm malam kai jama'a Allah dai ya rufa asiri Allah yasa a dace dauran tsinannun da suke kansa ma su fice mu huta ashe bada banza ba komai malam ya ta'ba sai kiga babu komai yayi sai kiga wayam duk abubuwan hannunsa suka kare komai ka d'auka ka bashi saiya narke ashe asiri ne a jikinsa.

'kwafa A'i tai tana cewa "ni abun tambayar ma anan shine wanne mitsiyacin ne yayi masa asirin a garin"?.

"To A'i wa zakace gari da yawa kuma bakasan iya ma'kiyan kaba sai kiga wanda kake tunani bashi bane wani ne dabam dan haka babu abinda xamuce fatanmu Allah ya taimaki Malam damu ya rabashi da shed'anun da suke jikinsa ko ma samu zaman lafiya".

Tsaki A'i tai tana cewa "ai wallahi Allah ya isa tsakanin mu da koma waye yayi masa haka ya cutar dashi damu ya rabashi da dukiyarsa ya hana yar sana'ar da zaiyi ya ri'ke mu komai ya ta'ba babu muna ganin laifin sa humm Allah ya tona asirin wanda yai masa haka ya tagayyara shi".

Da sauri Saude tace "Amin A'i dan gaskiya ta takin an cutar damu sosai an zalunce mu amma Allah yasa hakan ya zama mana taki sannan shi sharri dan aikene duk wanda ya aikoshi koma waye gashi nan yau zai koma kansa Allah ya sauwake" Amin sukace ganin Malam Habu ya fito daga bayin yasa sukai shiru da maganar suka d'auko wani zancen saida yai alwala ya tafiya masallaci suka d'ora a inda suka tsaya.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘
Tnks so much I really appreciate it masoya.

Sai mun sake had'uwa see you next time,😉 we will meet again🤗.

TYPING📲 FRI Aug30/24 08:18AM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋.

🎆✨ME KAMAR SARKI✨🎇

Story nd written
✍️Mrs Al'ameen Ahmad ce.

__________________________________
______________________
_______________
💫ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASS💫
Haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake.

63~AL-QAYYUM
The Guardian
64~AL-WAJIDU
The Perceiver.

31~Allahumma salli wa sallim wa barik ala sayyidina muhammadin sayyidi Ahlul jannati.

🌄REACTION ND RIDICULE🌄
Episode 63&64
🏕️ QAUYE🏕️
________Zaune su Sadi suke a majilasarsu ana hira Tanko ya kalleshi yana dariya yace "Sadi ya mutumin kuwa malam Habu kana jin labarin sa ina ya tafi gudun hijirar ne ko saudiyya dan nasan acan sai yafi samo kud'i shi kuma naga qarfi da yaji so yake saiya dawo da arzikinsa humm isa tana wahalar damai kaya kara yana can yana ihu bayan hari bari da zamuga a yadda zai dawo mana garin da borin kunyar ba'a shigo da ko biyar ba harda d'iban mata da 'ya'ya kuyu-kuyu waishi gamai 'kaura hahhhh lallai ayi mu gani ai labari yazo mana da gudu ka bishi bayan gari kana kukan ya dawo gida shikuma ya'ki saura kaima nan gaba kadan za'a ga ka shirya kabi bayansa tunda naga gasa kake dashi ko ya fad'a maka inda zaije ne daga baya kaje ka sameshi"?.

Had'e rai Sadi yai cikin takaici yace "ban sani ba inace ku kuka dama kusan inda yake kuje ku binciki inda ya tafi tunda matsuwa kukai ku sani na rasa wanne irin qahon zu'ka suka kafawa malam Habu kamar wanda yai muku wata tsiyar duk girman qauyen nan babu wanda kuka sawa ido dan masifa sai shi haba aikin banza kawai" Sadi ya karasa maganar a fusace yana jan tsaki.

Kallon juna sukai cikin mamaki kafin Mudi yace "kai Sadi! kai Sadi!! kai Sadi!!! sau nawa na kira ka? Ya fad'a yana kallon sa ganin yayi danza dashi yaci gaba.

"Sau uku na Kira ka a matsayin gargad'i ina maka kashedi daf da duka ka iya bakin ka ka iya harshenka idan kuma ka'ki zakaga abinda ake Kira da jaki sha duka tunda naga kaima kanka a toshe yake".

Wani irin kallo Sadi yayi masa yana cewa "dama ka ta'ba ganin inda dabba ta had'a kanta da mutum ne"?.

Zaro ido Mudi yai ba arziki ya kalli Sadi yana cewa "miye abinda kake nufi da maganar ka waye dabban kenan"? Yai tambayar a fusace.

Dariya malam Isyaku dake gefe yana sauraron su yana cewa "haba Mudi shifa Sadi ba dakai yake yada saurin tsarguwa yasan kai mutum akan wanne dalili zaice maka dabban ai wannan ba komai bane koba haka ba Sadi" ya karasa maganar yana kallo Sadi kai ya jinjina yana cewa.

"Kai d'an gari mai kyakkyawar 'kwa'kwalwa shi harya fahimta ina Ina Mudi ai babu wani abu hakan ma ina kana da 'ya'yanka ne" ya fad'a yana sakar masa harara.

'Kwaruwa Mudi yai jin yadda Sadin ya gasa masa magana a gaban mutane yace "me kake nufi"?.

Ta'be baki Sadi yai yana cewa "babu abinda nake nufi indai irinka ne".

Baki bud'e cike da mamakin rashin fahimtar maganar Sadi Mudi yace "irina kuma"?.

Kai Sadi ya d'aga masa "eh ire-irenka nake nufi marasa amfani tozartattu masu yankakken baya gara wani idan baida arzikin komai yana da babban arzikin 'ya'ya wanda wani kuma duk dukiyarsa bai isa ta saya masa koda d'a guda d'aya ne ba dan haka a cikin wadannan mutanen waye matsiyaci mai arzikin 'ya'ya kome arzikin dukiya? Humm Mudi tirrr da halin rashin hankalin wasu mutanen masu kwakwalwa irin ta kifi wanda basa gane komai su duk abinda yazo ransu daidai ne kodan dama biri yana kama da mutum tunda jahilai ne tun farko".

Sadi na rufe baki Mudi yai tsalle ya cukumi wuyan rigarsa yana cewa "ni kake cewa me yankakken baya saboda bani da d'a kuma ka kirani jahili"?.

A fusace Sadi yace "eh na fad'a kai jahili ne Mudi ko karya nayi sannan ba yankakken bayan gareka ba ka fad'a min ko yanxu ka mutu kana da d'an da idan an ganshi za'a tunaka babu saidai idan zance ya tashi a ambace ka dukiyar da kake tunkaho da ita 'yan uwanka ne zasu rabata a junansu su cinye babu wanda zaiyi maka sadakar ko naira biyar balle suyi maka addu'a kenan amma wanda kake magana a kansa talakan fa mai 'ya'ya shine mai babban arziki mai wadataccen baya wanda koda bayan ransa za'a tuna dashi bawan Allah mai kyakkyawar zuciya ko kunya bakwa ji kun d'auki tsana kun d'ora masa ba laifin tsaya ba na zauna wanda yayiku yana kallon ku shine mai hisabi tsakanin ku xaku gani a 'kwaryarku" .

Jin abinda yake cewa yasa Tanko Shima ya daina rabiyar fad'an ya cakumo Sadin suka tarar masa su biyu suna dambe dambe ganin haka yasa d'an uwan dake gurin Sadi Malam Sabo shima ya nad'e qafar wando ya shiga fad'an nan hayaniya da tashin hankali ta 6arke harda yage yagen kaya abun dai saida ya kaisu gaban mai gari akai shira'a mai gari ya tsiga tsaka akai musu iyaka babu su ba Sadi kada wani abu ya sake faruwa makamancin haka domin anan sune basu da gaskiya koma me Sadi ya fad'a musu da badu tsokane Shiba hakan bazai faru ba saida sukai kaca kaca da Sadi dasu Tanko sannan ya samu zaman lafiya a majilasar suka daina kulashi ba su bashi ba wanda yake shiga safgar wani Babu ruwan wani da wani basu sake tunkararsa da maganar malam Habu ba.

Zaune Ilyah yake akan tabarma ya jingina da bango ranar baije kasuwa ba yana gida yana shan iska Bara'atu tana gefensa sai zance suke suna 'bab'baka dariya duniya tasu lahira ko a gidan haya sa zauna😳 Maimuna itakuma taje anguwa su Nafisa duk basa gida sai iya su biyun ya saki baki yana faffad'a mata yawan dukiyarsa da kadarorinsa harda zancen saye gonar malam Habu da gidansa dayai a gurin mutanen nan.

Tuna hakan yasa Bara'atu kallonsa tana cewa "ka tuno min dashi ma wai nikam kasan inda Habubakar d'in ya tafi ne naji kace ranar shine yake buga maka kofa sassafen nan wai yazo sallama kafin ya tafi ko yana tunanin zakaji tausayinsa ne ko ka damu dashi"?.

Ta'be baki Ilyah yai "meye damuwa ta da inda zaije saiya dawo idan bazai dawo shikenan wata tsiyar zai bani Habubakar tsanar danai masa zatasa naji tausayinsa ne kina kallon abubuwan da yaran nan suka ri'ka min a kansa"?.

Kai Bara'atu ta d'aga "tabbas na gani amma naji kace kaine ka saye gonarsa da gidansa ko"?.

"Eh nine saboda na wulakanta shi na ba'kanta masa yaji d'aci a ransa saida na bari yazo ya gama 'kasqantar da kansa a guna na ci masa mutunci nayi masa korar kare fata-fata daga kofar gidana sannan na bari aka rushe gidan kafin naje yana tsaye da d'aurin kayayyakin su a gabansu suna kallon ana ni'ke gidan da babbar mota sannan na sayi gidan a gabansu na biya kud'in ko inda suke ban kalla ba humm yana can wasu sun had'u da bala'i tunda shi ya zama karfa idan ya ra'beka duk arzikinka saika talauce".

Dariya Bara'atu tai harda rausaya kai tana cewa "to ko ya d'auka zaka hanashi tafiya ne kace ka bashi gida da jari shiyasa yaxo maka sallama"?.

'kya6e fuska Ilyah yai yana cewa "waa🙄 nine zan bashi gida ya zauna harda wani jari Habubakar fa? ai wallahi da saidai ya kare rayuwar sa a kan layi har abada Bara'atu baki san yadda na tsani Habubakar akan abinda su Hussaini sukai min ba shiyasa kika ce haka mutumin daya jawo sukaita sakani kuka da ba'kin ciki akan 'ya'yansa har yana da baki magana a gabana humm''.

Murmushi Bara'atu tai tana cewa "to balle kuma ni kana gani dai lokacin da yazo gidan nan da 'yarsa akan kace kila yunwa nake ji na auna masa garin kwaki dan kawai nace masa kaima ka fahimci abinda ya kawo shi gidan neman abinci ne shikenan ya ri'ka zazzaga min bala'i harda marin Nafisa tsabar mugunta".

Cizon yatsa Ilyah yai yana cewa "ai ya mari Allah ya isa akan wannan marin ma nayi matukar jin haushin sa shiyasa komai nake masa da gayya garama daya talauce Allah yasa bazai sake yin arziki ba a duniya duk inda ma yaje yadda ya tafi babu komai ya dawo a tsiyace a firgice".

"Amin Amin" Bara'atu ta fad'a harda shafa hannu a fuska kafin tace "humm bari na mi'ke nima tunda yau nice da girki na d'ora kada rana tayi Nafisa su dawo daga anguwar nan bab gama ba ranta ya 'baci🤔 ai duk laifinka ne kaine ka hanata girki a gidan nan saidai taci ta kwanta hatta wanke wanke bata yimin balle shara" ta fad'a tana mi'kewa.

Murgina kai Ilyah yai yana cewa "eh shalele bazatai girki ta ri'ka 'kaurin haya'ki ba ita da zataje birni idan kuma wanke kwanuka ne ki nemo yarinya d'aya a 'ya'yan talakawan garin nan ta ri'ka yi miki daga yau zan ri'ka bada kud'in amma dai Nafisa bazata ta'ba hura wuta ba ita jikinta ba wahala bane 'yar hutu ce".

Dariya Bara'atu tai harda irin fasa kan nan wai 'ya bazatai aikin wahala ba sannan tace "ai shikenan masu 'ya dan ma kwanan nan zamusha bikin kuma tayi sa'a acan ba aiki zatai ba tunda d'an me kud'i tana daga kwance a mimmi'ke za'ai mata komai

Please Login or Register in order to submit comment