Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫

PROMISE OF THE HEART 💔


✍🏻M SHAKUR

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


1️⃣
~UK~
Tundaga nesa take leke babban building din datake dumfara tana bin uban tulin cars din wajen da kallo kaman akwai abinda take nema kafin daga bisani idanuwanta su sauka kan wata white Bentley car, gashinan kar kar ko alamun a single dust babu ajikin motan, ajiyan zuciya tasauke ahankali murya chan kasa tace “Alhamdulillah he’s still around” sanan tashiga sauri takarasa gaban wajen da ake kira da Cozy, harzata saka hannu tabude kofan tashiga tadanyi jim tsaya kafin ahankali tabi jikin ta da kallo tana sanye dawani white jeans daya kamata tsam dawata yar dark blue top mai shegen kyau wacce da kadan tasauka daga kan cibiyanta, saidan gyalen data yana kanta white shima dayamata kyau sai gashin kanshi dakenan kusan rabi awaje anmata kalaba da attachment kanana dayamata kyau shima, hannunta rikeda wasu books guda biyu dakuma phone nata kirar iPhone 13, sai wata yar karaman jakan datake rataye da ita, ajiyan zuciya takara saukewa kana ganinta kasan she’s nervous sanan ahankali tasa hannu tabude kofan wajen tashiga ciki.


Hadaden eatery ne and bar mai shegen kyau, babu wasu mutane dayawa awajen wayanda suke wajen yawancinsu turawa ne fararen fata maaikatan wajenma fararen fatane hakan yasa zaka gane wajen na bature ne, ahankali take tafiya tanabin wajen gabaki daya da kallo da gefen idanunta, kafin takarasa gaban kanta taja kujeran wajen ta zauna sanan tasauke books dinta agabanta da wayanta, daidai baturen Bar attendant din yakaraso yana kallonta yace “what can I get you miss” dan waigawa tayi kaman tana neman abu awurin tace “Pierre Zēro Rosé please, two shot” ganin duk tana maganan ne batare datama kalleshi ba yasa yace “gotcha” sanan yajuya yakoma yadauko wine din datai order yazuba mata a cups guda biyu sanan yadawo gabanta ya ijiye yace “here we go” dan juyowa tayi da sauri takallai sanan tasauke jakanta da sauri tadauko kudi taba shi tace “keep the change” kafin ma yay magana tasake juyarda kanta tana bin mutanen wajen da kallo one after d other…..


“Kai Zayn look” wani hadadden chocolate guy daga tachan karshen babban falon wajen da aka cikada kujeru ne kowa na zaune yana abinda yake yataba wani kyakkywan thick farin guy dake zaune kan kujera ya lumshe idanu pipe din shisha na bakinshi yana zuka yana fitarda hayakin ta hanci, yana sanye da riga da wando both black na LV, farine shi kal yanada cikan jiki dayake rigan dayasa short sleeve ne hakan yafito da kakkauran murdadden hannunshi, irin guys dinan ne masu manyan gabobi dakuma murdadden jiki, dudda idanunshi a lunshe but idan ka kalleshi bazaka so kadauke idanunka ba dan yanada wani irin kyau kaman mace, lips dinshi sunyi wani kalan masifan ja kodan shishan dayake shane oho, yanada dogon hanci siriri dayazauna akan fuskanshi gwanin ban sha’awa, sai gashin giranshi baki sidik kuma acike yanada tabon salla agoshi sai gashin kanshi baki sidik shima dake kyalli sun nannade kaman na buzu sanan gawani kwantaccen saje a fuskanshi Masha Allah, koda ace shiyay kanshi bazaiyi kanshi da wanan kyau dinba ballema bashi yayba.

Ganin baida niyyan amsashi yasa Mamu ya fizge pipe din shisha dake bakinshi yace “kafara ko ina maka magana kamin banza” ahankali yabude idanunshi dasuka wani lumshe sukai yaushi da idanda zai kalli mace dasu sai lissafinta yarikice sanan yazubasu kan Mamu kaman ance yay magana dan dole yace “what”? Dan murmushi Mamu yayi da hannu yamai alamu yace “look over to the counter ga budurwanka chan, stalker dinka tazo sai kallon ka take wlh, haba Zayn kaiko bazakaji tsoron Allah ka kula yarinyar nan koda sau daya bane tunda dai ta kasa maka magana for morethan 2months yarinyar nan kullum binka take tana stalking naka tana kallonka u know she really really likes u waikai maisa kacika wulakanta mata ne eh? Anyway I don’t blame you ni wlh in mace ne banmaga abin so ajikinka ba mutum dukgaka nan kalan asibiti farin fata kalan cuta, duk baku da karfi” dan murmushi yayi dan yasan Mamu so kawai yake yajashi suyita surutu this afternoon shikuma baida time dinan, hannunshi yamikamai alamun yabashi shishi shi, ijiye pipe din shishan Mamu yayi kan table din gabansu yace “Ya isheka hakanan gashinan duk idanunka sun chanza launi, munada lectures yanzun nan fa I think in the next 5min” dan tsaki yaja yasa hannu yadauki pipe din shisha yacigaba dasha abinshi yana daddanna wayanshi yana hura hayakin ta hancinshi batare dayama daga kai ya kalli inda Mamu yacemai yarinyar nan takeba Mamu nabinshi da kallo yarasa yanda zaiyi yaraba Zayn da shisha, shima bawai bayasha bane no but occasionally yakesha, shiko Zayn zai iya wuni yanashan shisha hakanma yasa baya iyacin abinci sosai, ganin yasake lumshe idanu yasa Mamu yaja tsaki yamike tsaye yace “dalla Malam wuce mutafi” bude idanunshi yayi dasuka dan kankance sukaija sanan ya watsama Mamu harara kafin ahankali ya ijiye pipe din yamike tsaye dogon namiji ne nagaske, budadde sanan kuma cikakke irin mazan nanne da ake kira da burin mata, car key dake kan table din yadauka yana rikeda wayanshi yay gaba abinshi batare daya cema Mamu komi ba yay hanyar kanta.


Tundaga nesa ta hangoshi ya dumfaro gaban kanta, duk taku daya dazaiyi saita jishi har kirjinta yana amsawa, tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin dayakeyi dayake neman sata ta haukace sabida sonshi ya lullube mata hanci ganin ko’ina najikinta yadau kyarma yasa ahankali tasa hannu tadauki cup na drink dinta takai bakinta still tana kallonshi ta gefen idanunta daidai ya iso ya tsaya dab da ita dasauri bartender din yazo yace “u done sir” bai amsashi ba yasa hannunshi a wandonshi yaciro wallet dinshi yabude yana kokarin zaro kudi ko kadan batasan drink din yamakai saman hancinta ba tsabagen yanda take kallonshi kawai numfashin dazata shaka ta shaki wine din wani irin mahaukacin shakewa tayi dabama tasan lokacin data saki cup din akasa ba tana wani kalan mahaukacin tari wine nabin hancinta suna fita idanunta sunyi ja kwalla yacikasu dawani kalan sauri daga Bartender din harshi suka juyo suna kallonta dasauri Bartender din yataho ta saitin gabanta yace “sorry Miss” dudda tarin datake kokarin danne tarin take tana kakalo murmushi dan wanan kwafsin haka har ina baki tabude zatai magana wani tarin yakara sarkaketa wine din na fitowa daga bakinta yana diddiga akan white wandonta duk yay staining sabida Jan wine ne, kaman daga sama taga wani clean white handky agabanta kamshin da ajikin mutum daya tall a duniyan nan takejin kamshi taji yana fitowa daga hanky ahankali tadago kanta sama tanabin Tundaga handkerchief din dakallo harzuwa white hannun dake rikeda shi zuwa kan fuskan Zayn dake kallonta in the eyes, wani sabon bugawa zuciyanta yashiga yi hannunta har rawa yake tasa takarba zatakai kan fuskanta dan sharewa shikuma yajuya ya ijiye kudaden dayariga yaciro daga wallet dinshi yadaura kan kantan yajuya yawuce batare daya kara bata second look ba, ahankali ta janye handky dagakan bakinta tabishi da kallo harsaida yabace ma ganinta sanan tasauke ijiyan zuciya kafin ahankali tasauke kanta tana kallon handky din ko kadan tama manta inda take rungume handky tayi akirjinta tana murmushi sosai.
[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 PROMISE OF THE HEART 💫

ALKAWARIN ZUCIYA 💔


✍🏻M SHAKUR


2️⃣

Murmushi Bartender din yayi inda sabo yasaba yasan yanda yarinyar nan ke crushing on that guy like hell, not just her da many other ladies ma, sabida guy dinan cinikin dasukeyi yanzu a eatery dinan is mind blowing, dazaran ansan yana ciki yammata zasu fara tururuwa suna shigowa from no where so koshima he’s happy for her at least yau yakulata, he hope suyi relationship dudda guy din dumping yammata yake anyhow kaman trash kuma ko ajikinshi dan yasan yanda suke binshi, he just hopes wanan will not be one of his victims, dan yana using babes kaman yanda yake using pen na rubutu idan yagaji da wanan ya yar yadauki sabo.


Tadade awajen ita kadai sai murmushi take tana daddaura handkerchief din akan fuskanta tanajin dadi daga bisani wayanta yashiga kara, dasauri ta kalli wayan ganin Juliana Munari ke kiranta yasa dasauri tadauka tana murmushi sosai tace “Hi Babe ya” daga tachan bangaren wata yarinya tace “ina apartment dinki amman bakinan Ayshu where are you? Ba tundazu muka gama lectures ba” murmushi tayi sosai tace “ina Cozy” dan jim Jully tayi tace “for Godsake Aisha when will u get sense? Eh, look at the way Kabeer ke binki Ayshu yaron nan loves you like a mad man amman kina nan kina stalking wanan heartbreaker da the worst part baimasan kina existing ba” dasauri Aysha tai fari da ido tace “says who, wayace miki baisan ina existing ba? Wlh yasani infect right now ma yanzu haka handkerchief dinshi nake kallo a hannuna it feels warm and smells succulent, OMG it smells just like him wlh, I feel kaman Zayn dina ne anan wajen” shiru Jully tayi saikuma chan tace “Ayshu I am ur friend and I will always tell you the truth, forget that guy he’s nothing but a dream and face the reality face wanda ke sonki ba wanan ba da kowa in our university sunsanshi ba wajen using yammata yay dumping nasu, Ayshu enough of this stalking, sabida yaron nan kin chanza gida kin dawo apartment din dayake, kin biya kudi double of the normal amout sabida acire tenant din dake zaune adakin dakenan directly opposite nashi kinyi parking kin koma compund din, Aysha sabida yanda kike stalking guy dinan kinsan karfe nawa yake tashi, karfe nawa yake fita gym, karfe nawa yake shiga school, sau nake yake da lectures kinsan all his spots, grades dinki kullum low suke karayi sabida soyayyan wanda baisan dakeba ke gabanki kum…” “Jully please enough, allow me to leave my life, ana so by force ne banson KB ki rabudani da maganan shi, kuma zaki gani Zayn will notice me and I will date him” dasauri Jully tace “dating Ayshu bakince min Islam dating babu kyau ba” dan yatsine fuska tayi tace “Jully is because bakisan guy dinan bane saisa, irinsu idan kika basu kanki ne kawai zasu zauna dake, dan gayu ne nafitina kaman ba muslim ba, boko tashigeshi, I want him to be addicted to me kaman yanda yakenan addicted to shisha, I am ready to give him anything, wlh Ina bala’in sonshi, just wait for me, ki dafa mana abinci gani nan zuwa”
tana maganan ta katse waya shiru Jully tayi, at this point zubama Ayshu ido zatayi dan Allah yama Ayshu taurin kai batajin shawara, kuma yaron nan will only break her heart, she will only chop breakfast a hannunshi a nothing will happen yaron da har lecturorin su mata crushing suke akanshi, anyway she just hope for the best.



Wuraren 6 ta shigo gidan, kana ganin gidan kasan na mugun yaran masu kudi ne, elevator ta shiga zuwa floor dinsu sanan tawuce Dakinsu tana kallon nashi dakin datana gani tasan baidawo ba daman baya dawo da wuri kullum sai 11 ko 12 nadare kuma kullu yaumin bata iya bacci saitaga dawowanshi wata rana tai kuka duk randa zai dawo da mace wata tana kuma tai murmushi, the truth is baifiye neman mata ba, wani zubin zaiyi 2month baidawo dakowace mace ba wani zubin kuma saiya dawo da mace zasuyi kusan kwana uku ko hudu tare saikuma shikenan bata kara ganinta dudda batasan dalili ba but kawai haka take gani, kuma baka taba ganinshi da babe din dabataci sunanta babe ba, duk tana tunanin nan tana tafiya ne tana kaiwa gaban Dakinsu tabude kofa tashige ciki tana ihu kitchen tafada tawani irin rungume Jully tana nuna mata handky tace “Jully look” murmushi Jully tayi tana kallon handky sanan tace “Ya akayi yabaki handky shi” nan tabata labarin from A to Z tana murna, murmushi Jully tayi tace “nidai jeki wanka kizo muci abinci dan Jerry zaizo yadauken” gira daya Aysha tadaga mata tace “Iyye love birds” tai maganan tana wucewa bedroom nata tashiga sanan ahankali ta ijiye handky kan pillow dinta tareda shafawa sanan tawuce ta shiga wanka agurguje tana fitowa tazo sukaci abincin tare sanan Jully ta shirya ta wuce abinta, komawa tayi ta kwanta kan gado tadauki handky tana kallon shi kafin ahankali tace “Zayn! I love you so very much Zayn” rungume handky tayi akirjinta tsamtsam tanaji kaman shita rungume, ahaka bacci ya kwasheta 11 dot na bugawa ta bude idanunta tsam shi kanshi gangar jikinta yasaba da stalking nashi, fitowa falonta tayi tai hanyar window ta ta tsaya dayake wutan dakin akashe ne ta tsaya tana kallon kofarshi tana tsaye awajen kam wajejen 11:30 saigashi ya shigo yana tafiya nan cikeda isa akuma hankali tundaga wajen saida kamshin dayake yadaki hancinta bude kofanshi yayi ya shiga sanan ya maida yarufe kafin ya kashe wutan falon, murya chan kasa tace “good night My love, asuba tagari” sanan ahankali tasauke window blind din tajuya takoma daki ta kwanta saikuma kaman wani abu yafado ranta dasauri ta tashi tadauki handky tafada bayi ta wan ke shi tsaf sanan ta shanya tafito tazo ta kwanta, shida dot tabude idanuwanta agurguje tafada bayi tadauro alwala tafito sallan ma agurguje tayi bama ta tsaya cire hijabin ba tafito ta daga window blind ta tsaya jikin window dan 6:30 dot yake fitowa tafiya gym, tana tsaye saigashi yafito cikin kayan workout gajeren wando da singiletin Riga da safa da canvas, cinyanshi tabi da kallo amunmurde kaman na yan wrestling sanan yaja kofan dayake da pin suke bude kofan yawuce yana jogging yatafi abinshi murmushi tayi ahankali sanan tace “good morning baby na” sanan tajuya handkerchief din tadauka tai ironing nashi, sanan ta shiga wanka tadade sosai abayin sanan tafito tana ganin 8 saura da sauri tawuce wajen window Wuraren 8 yashigo yana zufa murmushi tayi dasauri tajuya tashiga ciki wani hadaden short gown ta saka daya sauka daga guwiwabta da kadan pink yamata kyau Wanan Karan batasa dankwali ba sai turaren data feffesa sanan tai parking gashin ta in a stylish way sanan ahankali tadauki handky tana kallon kanta agaban madubi ahankali tace “Ya Allah kadaurani akanshi” sanan ta zura slippers dinta tawuce tafita falo ahankali tabude kofa tafito daga flat dinshi sanan kaman wacce abi yafashewa aciki tai hanyar dakin shi kirjinta na daukan uku uku tawuce gaban dakinshi tadade atsaye kafin ahankali ta danna door bell, ankai kusan 5min kaman bazaa budewa farat aka bude kofan gabadaya dasauri tadaga kanta suka hada ido wani irin faduwa gabanta yake tana kallonshi yana daure da bathrobe ajikinshi kirjinshi duka abude gashin kirjinshi akwance ruwa nabi sai karamin towel a hannunshi yana goge kanshi da alamu daga bayi yake, da mamaki yadan kalleta batare datai magana ba, lips dinta har rawa yake sanan ahankali tadaga hannunta dake rikeda handkerchief din murya chan kasa tace “ahhhhhmmm dama, dama, I brought your handkerchief back ne” tai maganan tana wani irin nishi sama sama kaman numfashinta sai dauke, kirjinta nawani irin racing, this is the first time take ganinshi ahaka, ganin still kallonta yake ba yabo ba fallasa kuma bai fasa abinda yake ba wato sharekanshi da karamin towel din dayake rikedashi, yasa taji wani bala’in fargabanshi na cikata jin baice komiba dakyar tadaga hannunta tamai pointing kofan dakinta dake kallon nashi tace “actually that’s my flat, yanzun nan naganka shine nace uhmmm bari nakawo ma” dan yatsine fuska yayi amugun wulakance ya kalli handky datake mikamai tundazu har hannunta na neman sagewa yace “I don’t need it, discard it” yaja kofan zai maida yarufe da sauri tace “uhmmm wait please” chak ya tsaya yana kallon fuskanta da fuskanshi dababu alamun rahama akai face dinshi looking kaman zai maketa, tagefenshi taleka tana kallon indomie da taga yafito dashi zai dafa yacika ruwa a babban pot yazuba albasa aciki ya fasa kwai aciki ruwan na kumfa sosai, dan murmushi tayi cikeda shakkanshi tace “are you trying to cook indomie”? Yana kallonta still a bala’in wulakance yace “uhn” kaman dole akace yay maganan, murya chan kasa cikeda shakkan abinda zatace tace “that’s not how to, lemme cook it for you p…..please” wani kalan wahalallan tsaki yaja ko kunyanta baijiba yace “banso” sanan yay slamming door din on her face batare dayama jira maitake shirin cewaba, kuka taji yazo mata wuya tadaure tahanashi fitowa tadade ahaka awajen sanan ahankali tajuya tawuce takoma dakinta zama tayi tana kallon handkerchief din tama rasa meke mata dadi, tunda take bata taba shakkan wani namiji ba sai wanan menene shi? Jibeta fa tanada kyau babu namiji da bazata iya daukemai hankali ba shi waye, enough of all this, tashi tayi fuu tai kofan tabude tafice sanan direct tai dakinshi ta danna door bell baa wani dauki lokaci ba wanan karan tabude kofan koyana expecting wani ne oho, churus ya tsaya ganin yarinyar dazu, wani irin faduwa gabanta yayi ganinshi dagashi sai dogon wando na Jean da Riga a hannunshi dabai Riga yasaba yanada wani irin broad chest ga cikakken shoulder parts garai, kasa magana tayi saiwani kalan kallon kirjinshi datake lips dinta na rawa tana kallon dark aroelas dinshi, ahankali tace “l…..l….ove……you…..Z….Zayn” Tundaga sama har kasa yake kalleta sanan yace “ke kikama kanki” wanan Karan wani slamming kofan yayi on her face saida yataba goshinta ahankali tajuya kaman an kashe mata yaran ciki tawuce side nata ta zauna dirshan akasa, tana zaune awajen taji fitowanshi yafice, kiri kiri kasa zuwa class din datake dashi tayi sabida yanda komi baya mata dadi.
[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫


PROMISE OF THE HEART 💔


✍🏻M SHAKUR



3️⃣

~Nigeria~
Wata babbar mace ce doguwa chocolate skin tsaye cikin wani lafiyayyen hadadden kitchen ginin zamani, tana sanye dawata doguwan rigan Atampa mai kyan bala’i ga kallabi daure akanta da kana gani kasan daura dankwalin kawai tayi amman hakan baihana kwantaccen black gashinta dake gauraye da farare lekowa ba, tana tsaye agaban wani hadadden babban gas a kitchen tanama wata yar aiki dake juya basmati rice a tukunya dawani wood spoon magana sukaji wata zazzakan murya dake ratsa zuciya na y’a mace ta kwala ma matar uban kira. “Mama nadawo, nakawo miki wasu kawayena ki gansu” wani irin kwashewa da dariya yar aikin dake juya abinci a tukunya tayi takalli Matar da aka kira da Mama datai tsaye kawai tama rasa ta cewa tace “Hajiya wlh tun ina iya kirga yawan kawayen Khairy harna bace a kirgan” kwafa kawai Matar da aka kira da Mama tayi tace “karasa juya abincin sai ki kwashe a warmer Ladid…..” bata idasa maganan ba aka kara rangadamata kira da wanan zakakkiyar muryan kaman ana busa sarewa. “Mamaaaa kina ina zoki gansu” dafa goshinta Matar tayi cikeda takaici tace “Allah nagode maka dakabani wanan yarinya, ina ganin Ummulkhairy ce zata bani hawan jini aduniyan nan” tai maganan tana fitadaga kitchen din ta hanyar bude kofa tafice, tana fitowa dining tai kicibus da yammata kusan su tara a zazzaune kan lafiyayyun kujerun falon suna maganganu suna hira suna kallon lafiyayyen hadaden falon dayaji Cubana furnitures, ganin Matar da kallo daya suka mata suka gane itace mahaifiyar Khairy yasa duk suka zubo daga kan kujerun cikeda girmamawa duk suka gaidata. “Mama ina yini, Mama barka da rana, Mama ina gajiya” lafiyayyen murmushi ta sakin musu tana karasowa tsakiyan falon tana bindi da kallo daidai tace “Masha Allah sassannunku da zuwa yammata yakaratu”? Kafin subata amsa wata kyakkyawan budurwa yarinya chocolate skin color, yar doguwa bachan sosai ba dabazata wuce 20yrs, skin dinta nawani kalan glowing fuskanta babu ko kuraje guda, tanada dan dogon hanci yet kuma dan karami dan diss afuskanta but fitacce, tanada manya manyan pure white eyes, idanunta are very big sunada wani kalan adorable spherical shape that is just damn gorgeous, dan kana kallonta the first thing dazasu fara daukan maka hankali a fuskanta are her big white eyes, ga eyelash dinta dogaye bakake cikakku, hakama gashin giranta, tanada goshi wanda kusan yarabu biyu ne rabi duk gashi ne dayake nan baki sidik sun kwanta daya karama fuskanta wani kalan kyau dan zaka dauka buzuwa ce sai dayan rabin kuma fatarta ne dayataho har gira, tana sanye da dogon rigan atampa itama da dan kwalinta akanta, tawani buga uban ihu da saida falon ya amsa gabadaya. “Mamaaaa” yanda ta kwala mata uban kiran nan yasa mahaifiyar nata tadago da kanta tareda juyowa ta zuba mata idanuwanta kurii irin na jama’a yaya zanyi da wanan yarinyar ne? Wani irin washe baki Khairy tayi cute saitin white teeth dinta suka bayyana tashiga saukowa daga stairs din dagudu kaman ba ita Mamar kema kallon zaki ganeba kawai tawani irin fada jikin Maman nata tana ihu sosai tana rawa ta kankame Maman kamkam. “Wayyooo Mama wlh nai missing naki, inata nemanki nadauka kin fita ne har hankalina yatashi ashe kina kitchen, Mama tun safe yau banganki ba awa nawa yanzu bansaki a idona ba karfe biyar fa, nai kewanki Maman mu, Mamana, I miss you Mommy Ummulkhaiyr” tai maganan tana kara kankamet Mama cikeda tsananin murna, dudda yanda Mama ke mugun kule da ita saida tai murmushi har cikin ranta duk

Please Login or Register in order to submit comment