Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya farkar da Maryam daga daddadan baccin da takeyi, itama a tsorace ta tashi cike da fargaban me yake faruwa cikin wnn Daren haka....


Tashi tayi ta je daidai saitin da take Jin Kiran da yake tace Abban mufid lfy ...yace ki zagayo ki shigo ba lfy Maryam

Rukayyah ce!

Ya Fadi cikin mawiyacin Hali ....

Tace me ya faru ne ka Gaya min Mana yace ki shigo kawai xuwa yayi ya bude kofa Maryam ta shiga gidan tana shiga taga rukayyah a kwance kamar matacciya a kasa ..

Innalillahi!

Tace me ya sameta Abban mufid haka ..cike da tsoro yace ba wnn ba Maryam ki diba kiga kamar Bata numfashi....


Tsugunawa tayi akanta ta Sanya yatsa a bakin hancin don Jin ko tana numfashi ..tana sawa taji tana numfashi, tace kawo ruwa da sauri tana numfashi cikin sauri ya je ya debo ruwa a cup har Yana Shirin faduwa ya yayyafa mata Nan take ta sauke wata irin ajiyar zuciya...Amma Bata bude ido ba,,,,,

Shi ko ba abinda yake sai hamdala da Bai Zama sanadiyyar rayuwarta ba...don gabadaya ya gama tsorata ya dauka mutuwa tayi shi yasa ya kasa komai ya Kira Maryam tazo ...duk ya wani fita hayyacinsa lokaci daya, tare da nadamar Sanya hannu akanta da yayi dama ba halinsa bane Bai taba dukan matarsa bare wasu ita ma din ta kaishi makura ne duk yadda yaso ya kaucewa hakan sai da ta janyo ya bugeta...yana Kara godewa ubangiji da Allah yasa Abin ya tsaya anan, har ya Fara hango kanshi da laifin Wanda yayi kisan Kai ...


Maryam na tsugunne kusa da ita, ruky ta bude idanuwanta ta sauke su kan Maryam ta waiga ta hango Abbas a can gefe Yana maida numfarfashi...🀣 Namiji da tsoro ...


Mikewa tayi tsaye ta kalli Maryam sama da kasa kallon raini ta Kai ganinta ga Abbas, ta watsa musu wani mugun kallon Wanda sai da Maryam din ta tsorata, tayi shigewatta daki...


Maryam na ganin haka tace Abban mufid bari na tafi tunda ta farka ...kasa magana yayi kawai gyada Mata Kai yayi ta fita cike da mamakin Abinda ya hadasu haka....tace maganinsu kenan suna zaune lfy su janyo ma kansu bala'i .




Maryam na fita ya shiga dakin wajen ruky da ya sameta a zaune a kasan carpet din dakin tana kuka ....karasowa yayi kusa da ita yace kiyi hakuri ba son Raina na dakeki ba, na kasa controlling kaina ne a lokacin sbd bacin rai ...itako abin nema ya samu har da wani kara sakin kuka Mai ban tausayi...


Sai da ya tabbatar da ta hakura sannan ya tashi ya shiga toilet don dauro Alwala kasancewar har an Fara Kiran sallar asuba ...


Tana ganin ya shiga toilet ta tashi ta fashe da dariya tana fadin Ashe zan iya wasan kwaikwayo..

Ashe dama Yana kaunata Bai nuna min ne kawai, ji yadda ya wani rikice sanda na fadi...sai yanzu nasan irin kaunarka garani,,,,,


Nan kuwa Bata San tashin hankaline ba ya dauka kisa yayi shiyasa ya gigice Yana kiranta a haukace....


Tana Jin motsin fitowarsa ta ci gaba da kukan karya ...shiko harda Kara wani lallashinta Yana Bata hakuri yace taje tayi Alwala. Ta tashi da kyar irin wadda Tasha wuya dinnnan.



Shikuwa tashin hankalin da ya faru ne ya manta duk hukuncin da yaso yi akanta don bazai jure wnn haukan nata ba Bai San Abinda zatayi gaba ba Kuma.

Wnn abinda ya faru ne kawai ya janyo rugujewar shirinsa akanta ...

Amma zai Kara Bata damar ko zata canja...Kuma Yana ganin girman mahaifinta sbd Yana iya kokarinsa akanta wajen Bata shawara ta zauna lfy a gidanta ...gashi duk sanda ya Kai kararta wajensa ita yake bawa laifi baya goyon bayanta ko kadan.





Bayan ya fito tai sallah komawa baccin da Bata Sami yi ba tayi.




Bayan yayi wanka ya shirya ya tafi Kai su mufid sch.

Amma kana ganinshi kasan Yana cikin damuwa..Yana Mai ganinshi laifinshi wajen kawo wadda take Shirin tarwatsa mishi rayuwa sai ynx ne ma yake nadamar dawo da ita da yayi dama kawai ya musu abinda suke so ita da mahaifiyarta.a wancan lkcin



Rukayya kuwa cikin doki da karfin gwiwa ta tashi tana hada break fast, tana tuno yadda plan dinta yai tasiri a wajen Abbas ...na sanin irin matsayin da take da shi...a wajensa ynx


Bayan ya dawo ta gama shirya breaakfast dinta suka je suna ci, Amma tana sane da yadda taga ynx ba walwala a fuskarsa...

Tace lfy kuwa naji ka shiru...Ina ta magana ba amsa?


Yace ba komai Amma fuskar har ynx ba walwala

Tace Ina so ka gafarta min Abinda ya faru jiya wlh Nima bacin Raine Kuma na kasa controlling dinsa Amma kayi hakuri ka yafe min insha Allahu bazan sake Yi makamancin haka ba...har da tsugunnawa a kasan kafarsa tana bashi hakuri. Ganin ta dameshi yasa yace "ya wuce!


Ta tashi tana Masa godiya!

Tea kawai ya iya Sha, ya tashi zai wuce aiki, yai Mata sallama ya tafi wajen Maryam itama sukai sallama...




Muje xuwa


*Ummu Ameer ce* πŸ’ƒ

πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»






*Story& written*



*By*


*Ummu Ameer* πŸ’ƒ






*Page* 3⃣7⃣






""""Har yanzu rukayyah Bata San cewa Maryam na da ciki ba,,, sbd Bata da girman ciki, Amma dai duk da haka ya fito...Kuma Shima Bai fada Mata ba.




Rukayya kuwa ba farincikinta Bai misaltuwa taji dadin yadda Abbas ya nuna damuwarsa akan halin da ta shiga a gaban maryam,tasan yanxu itama zata gane irin son da yake Mata..don duk tana Jin abinda yake faruwa duk Abinda yayi tana jinsa, sannan ta fahimci mugun matsoraci ne🀣zata Yi amfani da wnn damar....


Har farida ta fadawa abinda ya faru ...tace Ashe kema shegiyar kanki ce, ai gara da kika tashi tsaye in kika tsaya Sanya zakiga Sanya hajiya...sukai sallama cike da farinciki a ranta.




Abbas kuwa ko da yaje office kusan kasa komai yayi Yana ta tunanin abinda ya faru har ynx ya kasa cire Abin a ransa shi yasa ya wuni ba walwala a tare da shi.

Yana zaune a office friend dinshi ya shigo Dr Yusuf ya shigo daukan ruwa a fridge kasancewar fridge dinshi ya lalace,yai ta sallama shiru Abbas yayi nisa a tunani ...sai da ya Dan yarfa Masa ruwa a fuska yayi firgigit ...yace Dr. Me kake tunani ne Abokina haka Ina ta magana ka yi nisa a tunani ....ko Mata 2 sun Fara caja maka Kai ne?


Ajiyar zuciya ya sauke yace Kai dai bari Yusuf jiya Naga hauka a gidana ...Yusuf yace wane irin hauka Kuma ?


Abbas kwashe duk Abinda ya faru yayi ya fadawa yusuf, har da sauran matsalolin da suka faru kafin wnn.

Yusuf yace ai dama na Gaya maka zaka Yi kuka da wadannan mutanen sbd Basu da kyau akan kishi ...ko da yake kaddara ce da Kuma rabo, ni Daman ban goyi bayanka ba akan auren Nan tunda muka je da Kai Naga yadda mum din ta take behaving na San akwai mataala, a lokacin don ka yi nisa ne shiyasa na kyaleka ...kana zaune da matarka Mai hankali da hakuri yar gidan manya ka debowa kanka ruwa....


Abbas yace duk wnn ya wuce tunda aikin gama ya gama ni kaina sai ynx nake nadamar Kara auren da nayi gashi nai rashin sa'a, wlh ni auren ya fita a Raina ...



Yusuf yace ai dole kaganni Nan kwata-kwata bani da ra'ayin mace 2 Kuma kada kayi tunanin wai bani da matsala da matata, da Mai ra'ayin ne da tuni na yiwa safiyya kishiya Amma duk da wnn bantaba sha'awar Kara wata ba, duk da su Haj. Sun so na Mata ko ta shiga hankalinta akan rashin mutuncin da takeyi..Amma fir naki sbd nasan wata matsalar xan karawa kaina in suka zamo su 2 maimakon a samu sauki.



Kaidai kawai ka ci gaba da hakuri, Kuma ka dage da addu'a Allah ya hada kansu ita Kuma ya yaye Mata zafin kishi...in Banda ma Abin rukayya, ai Maryam ce ya kamata tayi wnn kishin ba itaba.Allah dai ya kyauta Ameen!
Abbas yace tare da mikewa Yana saka laptop inshi a jaka da sauran tarkardunsa, tare suka fito daga Asibitin Daman Shima Yusuf din ya tashi tun dazu,sukai sallama kowa ya nufi motarsa suka tafi.





Bayan ya koma gida yaje wajen ruky kamar yadda ya Saba, Fara zuwa wajen wadda Bata da girki ya shiga fuska ba yabo ba fallasa itako sai wani rawar Kai takeyi..bayan wasu mintuna kadan ya wuce wajen Maryam ya sameta a kwance cikin wani mawuyacin Hali...da gudu ya karasa inda take Yana tambayar lfy kike kuwa...Amma Ina ba Baki sai karkarwar zazzabi take har hakoranta na karo da juna,yace Amma me yasa baki gayamin halin da kike ciki ba Maryam?
Kinsan illar zaxxabi ga Mai juna 2 kuwa? Shine kika zauna da shi har haka Yana maganar kamar zaiyi kuka miryarshi na rawa...sbd yasan hatsarin zazzabi ga masu ciki, cikin tashin hankali yace wa kanwarta da tazo gidan tai maza ta dauko Mata hijab su kaita hospital.


Da taimakon hafsa kanwarta suka taimaka Mata ta shiga motar don kuwa tana Jin jiki ga wani zazzafan zaxxabi kamar turirin garwashi ga ciwon Kai kamar kan zai cire don Bata taba ma irin wnn zaxxabin ba.




A guje ya figi motar da wani irin gudu kamar zai tashi sama, Kuma motsi kadan zai ce sannu, itako ba Baki don Bata ma San Wanda ke kanta ba...



Bai tsaya ko Ina ba sai Asibitin da take Awo da sauri yai Kiran nurses suka taho da wheel chair aka dorata akai tare da hanzarin shiga da ita dakin ganin likita aka dorata akan gadon dake cikin dakin Shi kuwa Abbas Yana rike da hannayenta har da kwallah...sbd tausaya matan da yayi Kuma ga fargabar kar yai affecting din babyn cikin.


Dr. Ya Masa tambayoyi game da cikin ko dama ta Dade tana yin zaxxabin? Yace wlh Bata taba yi ba sai yau, Nima Ina dawowa na ganta a cikin wnn halin, Kuma ga dukkan alamu Bata dade da farawa ba,


Nan da Nan aka Sanya Mata drip sannan aka Debi jininta don gwajin malaria n typoid, shi kuwa Yana rike da hannunta Yana Mata sannu duk da ba iya amsawa take ba.


Rukayya kuwa ta kira ya Kai sau 20 Amma ya kasa picking...

Itako tana gani sanda suka fita daga gidan rike da Maryam din, yanayin da ta ganshi a ciki ya tabbatar Mata da cewa Maryam dince ba lfy..Kuma shine ko ya Gaya min zai fita ga wani irin tashin hankalin da ya shiga sai kace ce Masa akai ta mutu tsaki tayi tace aikin wofi kawai..ga takaicin kin daga wayar ta da baiyiba.


Tace to ma wai me take damunta?Kar dai ace ciki ne da ita? Inko hakane Akwai matsala...tashi tayi tsaye tana ta zagaya dakin tana safa da marwa....






Muje zuwa



*Taku*


*Ummu Amear* πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»





*Story & written*




*By*




*Ummu Ameer*πŸ’ƒ





*Page* 3⃣8⃣






Sai bayan awa 2 sannan Maryam ta dawo hayyacinta, Abbas kuwa cike da farinciki yace sannu maryam, ya jikin?
Tace da sauki!
Ya taba kanta yaji ba zazzabin ma, hamdala yayi tare da godewa ubangiji.

Motsawa tayi alamun tana son tashi zaune taimaka Mata yayi,sannan ya cire Mata robar ruwan da aka Sanya Mata sbd ya kare.


Sai faman Nan -nan yake da ita motsi kadan yace sannu ba dai wani Abu ko?
Tace eh!


Shima Dr. Da ya shigo ya yi murna da ganinta kamar ba ita ba, yayi wa Abbas murna.
Yai Mata tambayoyi ko akwai sauran abinda ke damunta? Tace babu.
Sannan ya nuna Masa result din, malaria ce Tai Mata mugun kamu.


Yace ikon Allah Kuma Bata fashin kwana cikin net.
Dr. Yace hakane Daman sai dai aci gaba da kula sosai kasancewar cikin dake jikinta anyi sa'a ma Bai shafi babyn ba,
Abbas yace Alhamdulillah
Thank you Dr umar!
Insha we shall do as u said!

Dr ya rubuta Mata magunguna masu kyau na malaria, sukai sallama yai musu fatan Allah ya kiyaye gaba, shi Kuma Abbas ya rungumo matarsa ta kishingida jikinta a jikinsa suka tafi, Dr. Kuwa sai murmushi yake sbd a gaskiya sun burgeshi Kuma ya Mata murna samun miji kamar Abbsa 'caring husband' gashi sun matukar dacewa da juna..





Haka suka fita kowa na binsu da kallo, har zuwa inda yai parking ya zaunar da ita sannan ya zagaya ya shiga suka tafi...

A hanya ya tsaya ya saya Mata fresh milk, da shawarma, da carton din maltina.

Sai sannu yake Mata duk hankalinshi na kanta har suka iso gida ...

Lokacin karfe 1na dare, ruky kuwa kamar jira aka Bata ta kasa zaune ta kasa tsaye ta Hana kanta bacci, sai taga dawowarsu, kafin isowarsu sai da ta shiga toilet sau uku sbd fargabar ko cikin ne...


Tana Jin karar shigowarsu kuwa ji tayi kamar ta je ta tambayesu me ya sameta sbd gajen hakuri.
Lekawa take ko zata iya gane wani alamu na masu ciki, Amma Ina Bata fahimci komai ba.

Haka ta hakura ta zauna tana jiran shigowarsa ta tambayeshi..



Shi kuwa Abbas jinya ta sameshi shi ya hada Mata ruwan wanka ya taimaka mata ta shiga wankan, haka dai yai ta Bata kulawa ta musamman, yara kuwa tuni sun Yi bacci suna ta tambayar hafsa Ina mommynsu tace sunje anguwa zasu dawo ynx.. a haka dai sukai bacci cike da kewar mahaifiyarsu.


Abbas kuwa har zai kwanciyarsa, sai ya tuna da Kiran wayar ruky, ya shiga ya sameta a zaune ba alamun bacci,yace lfy baki bacci ba har ynx?

To wane bacci zanyi baby? Naga ka fita a tashin hankali wai meya faru ne ka fita bako sallama yace Maryam ce ba lfy wlh?

Har da Dan zaro ido cike da kissa tace Allah sarki me ya sameta haka?
Yace malaria ce ta kamata sosai!

Bata San lokacin da ta sauke ajiyar zuciyaba tare da hamdala!
Yace lfy!

Tace har naji dadi ba wani mugun ciwo bane da ya tsaya kan malaria Allah ya sawwake
Yace Ameen !

Ni zan koma sai da safe
Kuma gobe ki shiga ki duba jikinta.

Ta yatsina fuska batare da ya ganta ba, a fili kuwa sai tace Allah ya kaimu...



***** ******* ******

Washe gari Abbas Bai fita office da wuri ba, ya tsaya Yana kula da Maryam sbd Bata son shan magani sai ya takura Mata tukun take Sha.



Karfe 11 na safe kuwa sai ga ruky ta shigo bangaren Maryam fuska ba yabo ba fallasa Bata Sami kowa a falon ba, taita sallama sai ga hafsa ta fito ta gaisheta ta wani amsa ya wulakance tace Ina matar gidan?
Hafsa tace tana daki Bari na kirata!


Hafsa taje tayi knocking kofar Abbas ya leko tace Anty rukayyah ce tazo yace kice tana zuwa.

Ta dawo ta Gaya Mata tana zuwa ki zauna ..

Sai alokacin ta zauna a kujera sai bin falon take da kallo, dake zuba daddadan qamshi, a zuciyarta tace ko Ina take samun wadannan turaruka masu qamsh oho!


Jin karar kofa ne yasa ta maida hankalinta ga wurin, wani irin razana tayi da Abinda idonta ke gane Mata Maryam ce ta fito sanye da doguwar Riga irin me roba din nan ga ciki a gaba, Wanda akalla zaiyi 7month, Nan take ta rikirkice hankalinta yaso gushewa, har sai day Maryam tace lfy kuwa ?

Sannan ta wayance tace oh! na Dan tafi tunani ne, suka gaisa da Maryam Tai Mata ya jiki, Amma har alokacin ba'a hayyacinta take ba, sai Kara bin cikin take da kallo, a zuciyarta tace lallai ma Abbas ya cika minafiki.

Ko 5mint batayi ba tace zan tafi sukai sallama Maryam ta rakata har bakin kofa,sannan ta koma daki wajen Abbas dake Shirin fita office..

Yace har ta tafi tace eh!
Yace to wify! Ni zan tafi don Allah Kisha magingunan akan lakaci plx! zan dinga kiranki in tym din yayi.
Tace zan Sha wlh.
Kissing din cikin yayi tare da shafa shi yace my baby zan tafi aiki take care !

Dariya tayi tace waya fada maka yanaji?
Yace ai kece Baki sani ba ,Yana jina amsawa ne dai sai ya fito ko my baby ?


Dariya sukai gabadaya ta karbi jakar hannunsa ta rataya ta suka fito falon kana ganinsu kaga masoyan Asali..har bakin kofa ta rakashi yace ya Isa haka Kar a wahal min da baby tace au ni Kuma fah?babyn ka kasani..yace wane ni?
Har da ke ya fada tare da lakuce mata hanci.

Tace husby na Ina godiya da irin kulawarka gareni ba abinda zance sai dai Allah ya saka da Alkhairi ya kare min Kai a duk inda kake ya Kuma barmu tare har Abada!
Yace Ameen uwar ya'yana Kuma Abin Alfaharina.

Ngd sosai da wnn addu'ar.

Sukai sallama cike da kaunar juna .



Me zai faru?Ashe ruky idonta da kunnenta akansu, wata Yar bula ta samu take lekawa duk sanda Taji su anan din...

Haukacewa ne kawai batayi ba jikinta sai karkarwa yake sbd tsabar kishi, tsigar jikinta na tashi...idonta ya daina gani ta fita hayyacinta
*Oh su ruky da lekan asiri an lekowa wa Kai da jiyo wa Kai tashin hankali*πŸ€”



Abbas sai sallam yake Amma Bata ji ba, Bata a hayyacinta kwata kwata ga tashin hankalin cikin da ta gani Abu goma da ashirin...





Muje zuwa




*Taku*


*Ummu Ameer* πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»






*Story &written*


*By*




*Ummu Ameer* πŸ’ƒ





*Page* 3⃣9⃣







""""Sallama yake tayi Amma Bata San ana Yi ba, shi kanshi ta bashi tsoro, ganin lokacin da ya dauka Yana ta sallama Amma Bata ji ba, sai da yazo Yana facing dinta yace "rukayyah"me hakane?sannan tai firgigit, yace meya sameki tun dazu Ina ta sallama bakijini ba?
Tunanin me kike haka?

Kallon shi tayi cike da raini ta buga tsaki Tai shigewatta daki ta barshi Nan tsaye da mamakinta,Yana cewa wanna matar ba'a kwana 2 cikin zaman lfy da ita sai ta bijiro da wani Abin kuma?

Bai bita ba, yasa Kai yai
Ficewarsa da takaicinta...

Tana Jin ya fita wani bakincikin ya sake rufe ta, ta fashe da kuka tare da lalubo wayarta ta Kira daddy tana Gaya Masa wai wulakancin daya ke Mata yai yawa ynx in Bata da girki ko zuwa baya yi wajenta sai ya ga dama sharri iri-iri Tai ta Yi Masa...


Tsakanin uba da 'da' sai Allah sai tausayin diyarsa ya kamashi a karo na farko yace tayi hakuri zai Masa magana...sukai sallama .



Tana gama kiransa ta Kira farida itama ta Gaya Mata cikin da Maryam ke dashi...dariya farida tayi tace shugabar masu kishi ke Kuma Ina ruwanki da cikinta ba matarsa bace, taitayi Mana ai Nan da Nan zakiga ta tsofe, sai kace akuya..ke in Banda shashanci ma ai dadi Zaki ji.... rukayyah ta katseta da cewa wani irin dadi Kuma ta Riga ta gama zazzago Masa yara ya Riga ta mallakeshi Baki ga yadda yake nuna ma yaran kauna ba, kamar akansu aka fara haihuwa, ko Khadija bata samu wani soyayyarba daga gareshi, hakuri kawai nake Ina kyaleshi sbd ba yadda zaiyi jininsa ce ko Yana so ko baya so....Kuma Baki ga wani irin kulawa da yake Mata ba, kamar me haihuwar fari ko ni bansami wnn gatancin ba, sannan Kuma in zauna Ina kallo ba wani mataki da zan dauka...farida tace wane mataki Zaki dauka ai aikin gama ya gama tunda kince ma ya Kai 7month ko?
Tace zai Kai..
Kuma ga munafurci ko da wasa Bai taba Gaya min ba.

Farida tace Kinga ki bar wnn zancen ni Banga wani abin tada hankali ba anan ai kin Mata zarra ta Nan tunda ke haihuwarki 1 Kuma ba dainawa Zaki ba ynx kika Fara Kila ma ki dinga haifo 2 tinda so kike ki Tara Masa yara...ta karashe maganar da tsokana.tace karki wani dami kanki don wnn ,ke dai kawai ki cigaba da samawa diyarki matsayi na musamman a zuciyarsa.
Haka dai suka dauki lokaci suna waya daga karshe sukai sallama.

Amma ko kadanba haka taso ba, taso ta goya Mata baya su San abinyi akan cikin, sai aka samu akasin haka sbd ita farida Bata dauki haihuwa wani ba, ita a ganinta ai haihuwa ma tsofar da mace takeyi shiyasa dama ita a tsarinta ko da Allah yasa ta haihu to bazata wuce 2 ba, sbd ta morewa rayuwarta ....a nata tunanin.




Itako rukayyah Bata dauki shawarar farida ba, sbd idan ta barta tana ta zuba Ya'ya ai ta Riga da ta kwace mijin, shi yasa take ta tunanin wata hanyar Kuma.



Daddy kuwa Kiran Abbas yayi yace rukayyah ta Gaya min Abinda ke faruwa don Allah dai kaci gaba da hakuri Kuma kayi kokarin kana kamanta Adalchi tsakaninsu don samun zaman lfy a gidanka...
Yace insha Allah!
Sukai sallama
Yace me Kuma ta hada min wnn munafukar yarinyar, har zai kirata ya fasa sai ya koma gida ya sameta..




Sai da yayi kwana 2 a gidan Maryam cikin kwanciyar hankali da kaunar juna, Bai so ba ma zai bar gidan sbd ynx jinta yake kamar me... A bed.




Rukayya kuwa tun rannan ba magana suke ba, ita a dole tana Jin haushi yama Maryam cikiiii....karfin hali kenan

Randa zai dawo gidan kuwa Bata wani wahal da kanta ba, wajen gyara shi ba, tunda tace ko tayi ba tasiri yake ba*A tunaninta da gajen hakurinta ya Hana ta cin ribar zaman aurenta*


Amma dai yau ma ta Kara hada Masa zobo ta Sanya Masa kwayarnan Bata mance da ita ba, ita dai tana Jin haushin shigar da yake wajenta ranar girkinta...



Ko da ya dawo ba wani fuska ya sakar Mata ba, ya shiga toilet yai wankansa, ya gabatar da sallar isha'i, Bai ko kalli wajen dining din ba, balle yai tunanin ci, ita Kuma girman Kai ya Hana ta kiransa a tunaninta ai shi ya kamata ya bita tunda shi yai Mata laifi...hauka kenan.

Ya wani dauki fushi da ita, bayan ita yaiwa lefi shine yake wani wayancewa da borin kunya Kar tai Masa zancen, da ta kalleshi in ta tuno cikin Maryam sai ta Kara Jin haushinsa ...

Ganin Yana Shirin fita wajen Maryam tace mallam ya haka bakaci Abinci ba, kake Shirin fita wani wajen Kuma,ta Sha gabansa ta tare hanyar.



Yace sai kin je kin koyi yadda ake Zama da miji da iya yi Masa magana tukun sai in ci ...Aiko maganar ta Dakar Mata zuciya, tace ni Kake fadawa haka Abbas?
Yace an Gaya Miki kiyi duk Abinda zakiyi na gaji da wnn halin naki I'm tired.

A take tsoro ya kamata a zuciya tace karfa ya sakeni, don wlh bazan iya jure rashinsa ba, bazan iya rayuwa da wani in ba shi ba, gashi taga ya harzuka matuka shiyasa ta ja bakinta tayi shiru ...tana ji tana gani ya fita, Yana fita ta dauki zobon ta zubar a kitchen tace bashi da sauran wani amfani a gareni,in ma yasha ni zai cutar...

Ko da ya shigo ma kasa tunkararsa tayi da wani zancen ya gama duk Abinda zaiyi ya shiga bed room zai kwanta, ranta ya baci sosai da Abinda yayi, bayan ta gama kukanta taga bashi zai fissheta ba,tashi tayi tabi bayansa...ta tura kofar a hankali ta shiga ciki...

Zuwa tayi ta zauna kusa da shi tace ka tashi zamuyi magana da Kai...Yana jinta yai Mata shiru,sai da yaga tana Shirin Hana shi bacci yace Ina jinki, tace ka tashi ka fiskanceni mana,yace kunnene ke ji ai...ta fara magana tana fadin wai don Allah me nayi make kake min irin wnn horon a gidanka?, Ina soyyayar da kake min? Ina Alkawarin da ka daukar min kafin dawowata gidanka,ynx ni na cancanci duk wadannana abubuwan daga gareka?
Rukayyan kace fa Abbas..

Na fahimci kwata kwata baka kaunata, kaunarka tana ga matarka Maryam komai nayi ban iya ba, baka nuna son kamar yadda kake nuna mata, Khadija ma Bata samu soyayyar dakake nuna wa yaranta ba, karka manta yarkace itama, Kuma jininka..

Na fahimci matarka ce take yin asirin da muke samun matsala itace duk ummul aba'insin komai,

Yace dakata karki Kara ambatota da irin wnn kazafin, duk Abinda zamuyi ya tsaya tsakaninmu, ba ruwanki da ita, bana son korafi, tinda nake da ita Bata taba kawo min wani korafinki ba, nasan abinda zatayi,nasan Wanda bazata yi ba.


Nan da Nan wani bakinciki ya turniketa kamar ta hadiyi zuciya.


Sannan ya Kara da cewa batun changes Kuma da kika gani wanna Kuma ke Zaki binciki kanki, ki nutsu ki daina duk wasu halaye da kika son bana so, ki guji abinda bana so, ki fi kowa son Wanda nake so... ki dawo rukayyan da nasani a baya ...ki cire wnn mugun kishin da kika saka wa kanki, don bashi ne mafita a gareki ba.....

In kin canza, Zaki ga canji....

Nan take ta fashe da wani irin kuka...tana cewa ita dama ko yaushe Mai laifi ce a gareshi, baya Mata Adalchi ..ganin Bata da niyyar shiru yasa ya janyota ta kwanta ko tasamu ta barshi yai baccin, itako ganin haka yasa tai luf ajikinsa, Abin nema ya samu...






Muje zuwa




*Ummu Ameer

Please Login or Register in order to submit comment