Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, acan din xuwa safiya...



Nan suka Mata fada sosai ita kuwa a lokacin ta Fara dawowa hayyacinta ga matsananciyar nadamar Abinda tayi...suka ce ta koma gidan gobe sai su tafi...jiki a sanyaye kanwarta ta kamata suka shiga cikin gidan.



Shima Abbas din daki ya shiga, Amma Yana fargabar Kar haukan nata ya Kara tashi, da ya tuna Kuma akwai Mai tsaro a waje sai ya Dan sake...ya zauna yai dressing din wajen data yankeshi Yana yi, Yana tunano abinda ya faru, yace da tuni ta sheka ni lahira, Allah ya kubutar Dani.

Nan dai ya zauna don ba tunanin bacci a wnn Daren abinda ya faru ne ke ta Masa yawo akai ga wani matsanancin ciwon Kai kamar zai fashe, sai Allah wadai da irin wnn zafin kishi nasu yake, sai ynx ya tabbatar da Abinda ake fada akan Yan garinsu masu kashe miji har lahira akan kishi..



Can kuwa ruky kuka take kamar ranta zai fita ganin ynx ba wani sauran Zama tsakaninsu da Abbas rashin hakuri da bakin kishinta ya jawo mata nadama, da danasani, tana fadin ynx me zan cewa mummy da wane idon zan kalleta...



Aisha ce ke lallahinta tana fadin ki daina kuka don kin rabu da wnn Mara mutuncin ke Baki ga tozarta ki da ya yayi ba, har kike bakin cikin rabuwa da shi, tace wlh Ina son shi, Ina sonshi, tayaya zan iya rayuwa ba tare da shi ba ..Aisha cika ta tayi don takaicin maganar rukyn tace wlh kin bada Mata...Kuma ynx xan Kira mummy in Gaya Mata duk Abinda ya faru, tace karki kirata don nasan Abbas zai yafe min zai barni muci gaba da rayuwa, nasan Yana sona shima bacin raine, Bari naje na Kara bashi hakuri ...Aisha ce ta kulle dakin tace wlh ba inda Zaki kina fita zan Kira mommy...ba yadda ta iya haka ta koma ta zauna tana kukan nadama, ta dauki Khadija ta rungume ta, tana fadin kiyi hakuri 'yata nice na janyo miki rabuwa da Abbanki sbd zafin kishina, na rabaki da Abbanki domin kuwa matukar na bar gidannan ba yadda za ai na barki a gidan, sbd kece farincikina bazan iya Koda kwana 1 ba tare dake a kusa Dani ba, sai Kuma ta fashe da kuka, itama Yar uwartata sai da tayi musu kwallah, ta janyo yayarta ta rungumesu suna kuka.




Can Maryam kuwa itama ta kasa runtsawa ko kadan, taso ganin Abbas din Amma akace Tai hakuri xuwa safiya, tunda qlau yake ...ba yadda ta iya haka ta hakura,tana Mai tausaya Masa halin da ya shiga, gashi ta mance wayar a gidanta, ita batace ma ga inda take ba, tunda aka Fara wnn tashin hankali...a zaune ta kwana cike da fargabar ko wani abun zai biyo baya, duk da an Gaya Mata duk yadda ta kasance ...



Tun asubahi ruky taje tana ta buga dakin Abbas da dai ya tabbatar ita ce sai yaki budewa har ta gaji ta Fara cewa Abban Khadija kayi hakuri ka gafarta min wlh nayi nadama abinda nai, kayi hakuri ka bani dama ta karshe ...shikuwa cewa yayi axuciyarsa lallai tana da karfin halin tunkararsa da wnn maganar, tsabar rashin kunya ne ma.

Bai saurareta ba, ta karaci surutunta ta koma wajenta, tana shiga taga Aisha ta gama hada Kaya a akwati, tai wa Khadija wanka, ta hada musu duk abubuwan bukata, Zama tayi shirif jiki ba kwari ta kalli Aisha tace nifa ba inda zani, nasan zamu sasanta kanmu, ki daina wnn Shirin ...Aisha dubanta tayi da mamaki tace kinsan mekike cewa kuwa tace nasani...


A take Aisha ta Kira no mummy ta Gaya mata duk Abinda ya faru...mummy tace yayi kyau ga abinda nake jiye Mata nan, Kuma ba dai gidana ba wlh..Aisha tace ai tace ba inda zataje wai zasu sasanta ,mummy tace Bata wayar, ta Mika mata Nan ta hau ruwan Bala'i tace in kika Bari gari y waye Baki bar gidan Nan ba, zakiga abinda zani Miki wawiya shashasha kawai...ruky ta cillah wayar tana kuka tana fadin ni ba inda zanje.


Ganin ta dage bazata bar gidan ba, yasa aka sanar da yan' uwanta abinda ya faru, aka ce suje su taho da ita daga gidan...


Daddy ma Koda yaji labari ransa ya baci sosai na yadda Saida ta kashe auren sannan taji Dadi, cewa yai ba ruwanshi shima ya zare hannunsa akanta.


Koda gari ya waye Abbas fita yayi ya bar gidan, ya gayawa Maryam karta dawo sai sun tafi rukyn.



Wajen 8na safe anty Salma da mijinta da wata yaruwarsu suka zo gidan, suka tambayi Aisha abinda ya faru..ta kwashe komai ta fada musu, Anty Salma tace kinga abinda nake Gaya Miki ko gashi Nan ai kin yiwa kanki akan banzan kishi da Bai da amfani, kin guntule auren naki kin huta, tana jin Anty Salma ta Fadi haka ta Kara fashewa da kuka tana fadin don Allah anty ki sa Baki ya maida ni, wlh bazan iya Zama da kowa ba sai shi, ki bashi hakuri ya maida ni, Anty Salma tace ni bazan iya ba, ba dai haka kike so ba, kinsanu kuma ai shikenan.



Nan mijin Antyn Salman yace a Kira Abbas din aji ta bakinsa, ko Allah zai sa a dace. ...Anty Salma tace wlh ba wanda zai zauna da Mai irin halin wnn kisan Kai fa Tai niyyar yi, sannan Kuma mu tikasta Masa Zama da ita, ni ba hannuna a ciki, in zaka gwada bissimillah, shiko Kiran Abbas din yayi, yace shi baya kusa ,sai da kyar ya bashi hakuri akan yaxo, sannan ya taho ba don yaso ba, donshi ya fita ne har sai ta bar gidan ya dawo.



Koda rukyn taji zaizo Dadi taji..har da Kara kintsa kanta



Bayan isowarshi ne, ya gaishesu, mijin Antyn ya bukaci ya Gaya Masa Abinda ya faru, ya Gaya Masa komai, suka ce gaskiya rukyn CE da laifi, Bata kyautaba, sannan yace Amma Abbas tunda har tayi nadama muna rokon ka Kara Bata dama, insha Allah zata canxa....Abbas yace ai ynx aure ya Kare tsakanina da ita domin kuwa saki uku 3 nai Mata..ruky najin haka ta kwallah wani irin Kara ta tashi ta nufi Abbas din kamar zakanya...









*True lyf story*



Muje xuwa


*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Stiry& written*


*By*


*Ummu Ameer*💃





*Page* 5⃣3⃣




"""""Cakumarsa tayi tana fadin wlh baka Isa ba, tunda ka tsinke igiyar aurena da Kai wlh da Kai da Matar taka sai na hallaka ku, wlh muddin Ina Raye kuda farinciki har Abada...

Anty Salma ce ta daka Mata tsawa tare da janyo ta daga wajen Abbas tana fada Baki da hankali ne, Zaki dinga wnn furuci, ta wurga ta kan kujera tace koma me ya faru dake kekika jawo, yaro Mai hakuri, in ba ma Shiba a wnn zamanin waye zai kyaleki ki ta wnn haukan ai da tuni ma ya koreki, Amma duk da haka sai da kika kaishi makura, ai kinji Dadi, ki tashi mu tafi tunda ba sauran Zama tsakninku, tana Jin haka tace Anty ba inda zani wlh..ji kake tasss ta shharara Mata Mari tace lallai na yarda ciwon hauka ya sameki, wawiya kawai..ruky najin haka ta shige kitchen ta kulle kanta ta kunna gas wai zata kona kanta, akai akai t bude taki har warin gas din ya Fara fita sosai ta kyassa kenan mijin Anty Salma d Abbas din suka ballah kofar anty Salma ta hau dukanta tana fadin ah lalle dole Abbas ya samawa kansa lfy wa zai jure wnn isakancin naki, tana fitowa Kuma sai tayi toilet Nan ma ta kulle ta kyassa ashanar a soso wai in ya Kama sai ta Dora a jikinta, Nan ma da kyar aka bude, ba Kuma a fasa dukannata ba, Amma ko ajikinta kayan ta dik sun yayyage, tana fadin wlh saina jaza maka bala'in da sai ka Kare rayuwarka a prison...Anty Salma ta riko ta tace ku Kama ta mu Sanya ta a mota wnn tayi nisa karta ballo wa kanta bala'i, mutum 4 ne suka kamata 4,maza 2 Mata 2, Amma yadda kasan ingarman doki, kasa janta sukai ta tirje a lallai bazata bar gidannan.


Shidai Abbas Yana bakin kofa ya tsaya ya harde hannuwansa waje daya Yana godewa Allah da yasa take zuba haukan a gaban yanuwanta...su tabbatar da halinta.


Ruky dai hauka tuburan wani karfi daya zo mata tai wancakali da su, ta nufi gurin Abbas shiko Yana ganin haka yai hanzarin barin gidan ta bishi a hakan duk Kaya a barke yai hanzarin shiga motarsa da yai parking dinta can nesa da gidan.

Tana ganin haka ta juyo ta dawo, ba inda ta nufa sai bangaren Maryam Allah yaso dakunan a kulle suke da kitchen, ta falon ta Fara farfasa abubuwa, tana wullar da komai na wajen, data gama da nan Tai toilet, Nan ma ta fasa na fasawa ta zubar da na zubarwa sai da Tai kacha-kacha da gidan sannan ta fito, Aiko Anty Salma wata sharbebiyar bulala ta je ta samo a waje ta afkawa ruky Amma dake zuciyar ta bushe ko ajikinta, Abin ma ya Fara Basu tsoro ko dai tana da mutanen Nan, zuba Mata ido sukai suna mamakin ikon Allah , Itakuwa wata kwalba ta glass din data fasa ne ta dauko ta yanki hannunta yankar kuwa ba karama ba, Nan jini ya fara bulbulowa sai Kuma ta Fadi ta xube a kasa a sume...kanwarta Tai kanta a guje tana Kiran sunanta, tana jijjiga ta, a haka aka kwasheta sai asibiti...wnn shine silar barinta gidan.




Shikuwa Abbas ba nisa yai ba, can bayan layinsu ya samu ya fake, anan ake gayamasa Abinda ya faru da rukyn yace Allah kyauta.sai da ya tabbatar da sun bar unguwar sannan ya dawo gidan yaga irin barnan da ta Masa a gidan, yace tunda ba wani kika hallaka ba, Allah tsayar Anan.


Nan ya Kira Maryam yace ta dawo sun tafi, shiyaje har kofar gidan ya debo yaransa, suna yiwa juna jajen Abinda ya faru...


Nan suka zage suna aikin harda Baba sa'a suna gyaran gidan, cikin kankanin lokaci suka kimtsa gidan, na gyara ya kirawo masu gyara suka gyara, na zubarwa aka zubar.


A ranar ba inda Abbas yaje Yana gida, masu zuwa jaje na zuwa, Yan gulma na xuwa ganin kwaf..




Rukyn kuwa a Asibitin, tana farfadowa ta ganta a hospital, tana tambayar waya kawo ni Nan, ba Wanda ya kulata,sbd kowa Jin haushin ta yake ,


Ganin haka yasa ta tambayi Aisha wayarta ta Mika Mata, ba Wanda ta Kira sai no Abbas, Tai ta Kira kusan sau goma Bai dauka ba, daga karshe ya tura mata yace Kiran me take wa mutumin da taso hallakawa, kiyi hakuri ki daina kirana, ba wani sauran Abu tsakanina da ke...yarinyata ma zan zo in dauki yata.
Allah ya kaddara saduwa...a take yai blocking no.




Tai ta Kira Amma Taki shiga, haka ta hakura ta Fara zubda kwallar nadamar da Bata da amfani..ita ciwon ma Bai dameta Bata shi take ba.

Su anty Salma kuwa sun gane Wanda take kokarin kira, suna mamakin wnn halin nata, kowa ta bashi haushi a wajen.zuwa can sai ga mommy Afujajan taji ance yarta na asiniti, kasancewar Basu fada Mata Abinda ya faru ba...





Muje xuwa


*Ummu Ameer* 💃


🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻




*Story & written*


*By*

*Ummu Ameer* 💃


*Jinjina Mai yawa a gareki MRS ABUBAKAR Ina godiya da kulawarki a gareni Allah ya bar zumunci*🤝🏻






*Page* 5⃣4⃣



"""Mummy kuwa na Isa Asibitin ganin yarta a wani hali, duk ta lalace kamar ba ita ba, ta Kara Baki..yasa mummy fadin ohhhh! Irin gashin K'umar da yake Miki kenan Amma kikai shiru Kika kasa fada?

To wlh ya saurari sammaci,bazan yarda da wannan rashin mutumcin ba, haka na bashi y'artawa?

Anty Salma tace "Yaya me ya kawo batun sammaci, kawai don tayar da fitina tsaye, kin binciki yartaki da har kike Shirin yanke hukuncin..ai ba shine ya cancanci yaji sammaci ku ya kamata yaiwa haka, Amma sbd sirikin arziki ne da ke, ya kyale maganar, kinsan irin danyen aikin data so janyowa ma kanta kuwa?
Allah ne ya taimaketa da tuni tana "gidan kaso".

Budar bakin mummy kuwa sai cewa tayi and so wahat inta kasheshi, shi din ma ynx ai kiris ya rage ya karasa ta...

Anty salmah kuwa tace haka Kika ce? Mummy tace yes of course!

Mijinta taiwa umarni da ya tashi su tafi, tace na barki lfy..kuyi duk yadda kuka so, tasa Kai Tai ficewarta a dakin.

Ruky kuwa fashewa tayi da kukan nadama, ta fada jikin mummy tana fadin Mummy Abbas bashi da laifin komai, rashin hakurina da rashin bin maganar iyaye ne ya jawo min, ta Kara tsananta kukanta da fadin don Allah mummy kiyi hakuri ki yafemin nayi nadama, Nan itama mummyn kwallah ta cika idanuwanta tana cewa na yafe miki, Kuma nima da laifina Akan zare hannuna da nayi akanki Nima ki yafe min.

Nan sukai ta nemawa juna yafiya akan kurakuran da suka aikata.

Ruky kuwa wata iri ta koma duk ta fita hayyacinta cikin kankanin lokaci, tare da matsananciyar nadama, har tana fadin Ina ma baya zata dawo da tayi amfani da ita wajen gyara kura-kuranta, Amma Ina bakin Alkalami ya bushe, duk Wanda ya ganta a halin da take ynx sai ya tausaya mata.

Zuwa dare aka sallamesu tare da Bata magunguna suka kama hanyar gida.ita Khadija kuwa dama Aisha ta wuce da ita gida tun dazu.


***** *********** *******
Acan gidan su Abbas kuwa sai ynx yaje jinsa free, tunda ya sawwake mata yake Jin kamar ya sauke wani nauyi ne akansa...cikin kankanin lokaci har ya dawo hayyacinsa, a baya kuwa jinsa yake bashi da wata nutsuwa sbd kullum cikin korafi, da kawo fargabar abinda zaije ya tarar a wajenta,.

A Daren ranar ne suna zaune suna hira, tare da jajantawa juna wanna masifar da ta auko gidansu, har Yana Bata hakuri akan ta yafe Masa akan kawo musu tashin hankali da yayi a gidan suna zaman lafiya.

Tace tace ai mutum baya wuce kaddararsa Allah ya Kara kiyaye gaba ya Kuma Kara karemu da kariyarsa.
Yace "Ameen"

Yace ai Allah ya auna arziki da sai dai kuji mummunan labari.

Nan ya Bata labarin gudun da suka rinka Yi, har Saida taga nayi mata nisa sannan ta hakura...Maryam kuwa ta kwashe da dariya har da rike ciki, yace ok! Dariya ma na Baki ko?hmmm ba Dole na ceci kaina ba, Kuma kinsan ni kaina bansan zan iya wnn gudun ba, kinsan mutum in Yana bazai iya ba, to Bata kamashi bane.

Itako har da tsugunnawa kasa don dariya, tace ka bada maza gaskiya Ina jarumtar mazan? Tace ta gane kafa matsoracine.
Shiyasa.

Yace kedai abar zancen kawai.
Yace shine ke kuma Kika gudu Kika barmun yara, to da ta samesu Baki tunanin komai zai iya faruwa..tace to ai Naga nice danuwarta ba yara ba, shiyasa na bar gidan.

Yace gaskiya hakan kuskurene ki daina..


Bayan sun gama maida zance suka je suka kwanta Amma Saida ya tabbatar da ya kulle ko ina yadda ya kamata, don ya tsorata ainin da halin ruky.




Ruky kuwa acan ta kasa Koda runtsawa Taki cI, Taki Sha sbd tashin hankalin data ke ciki, ga matsananciyar kewar gidanta, in ta kalli Khadija kuwa sai taji wani irin tausayin yarinyar ya shigeta, tace yanxu shikenan zata taso ba tare da mahaifinta ba, Zatai irin rayuwar da tayi na rashin mahaifi a kusa.


Ga wani irin son Abbas din data keji Yana Kara Shigarta, sosai tayi nadama, sai dai nadamar tata Bata da wani amfani a yanxu...


A zaune ta kwana don ko tayi yunkurin kwanciyar Jin zuciyarta take kamar
zata fashe ga wani irin nauyi da kirjinta yai, Bata iya koda kwakkwaran motsi.


A haka ta kwana a zaune,duk da kokarin da Aisha ke Mata na ganin ta cire Mata damuwarta, Amma ko kusa kamar ma karuwa take.

Haka dai ta shiga cikin wani kunci, kowa ya tausaya Mata halin da take ciki, wasu Kuma na halinta ne ya janyo mata, ita kanta sai yanzu ne ta Fara tirr da wannan bakar zuciyartata, da bakin kishin da Tai gado..


Ta dawo silent, kamar ba ruky ba, dama can haka halin nata yake don Bata cika son magana ba.kishi ne ya canza ta.




Muje zuwa


Taku

*Ummu Ameer*💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻



*Story&written*


*By*


*Ummu Ameer*💃






*INA MATUKAR GODIYA GA BUMBUN MASOYANA ADDU'OINKU SUN ISO GARENI BA ABINDA ZANCE SAI DAI ALLAH YA SAKA DA MAFIFICIN ALKHAIRI ALLAH YA BAR KAUNA*❣❣❣


*NIMA INA ALFAHARI DA KU AKO YAUSHE BURINA A KO YAUSHE IN FARANTA MUKU*

*NAGODE KWARAI*
*ANA TAREE*🤝🏻


*MRS ABUBAKAR ina Taya ki murnar fara sabon novel dinKI(*KUN CUNCENI*) ALLAH YASA AN FARA A SA'A AMEEN.


*Page* 5⃣5⃣
*END*


"""Su Yaya babba kuwa da aka ji labari ruky ta Sha tsinuwa wai kaga shedaniyar yarinya, dan'uwanna mu kenan da yake kula da mu take son hallaka mana shi, ja'irar banza kawai ai da an kulleta ta koyi hankali, Ina ganinta kamar mutuniyar arziki Ashe ta iya ta'addanci.


Har gida taxo tai musu jaje, tace ka kyauta da Kai mata saki 3, ai ko a hanya bazan fatan Allah ya hadani da ita ba.

Nan ta roki Maryam gafarar akan halayen da ta nuna Mata, tace Ashe kece yarinyar arziki, tun a sunan Yan biyu ta Fara yin tsiyar ai, to Allah ya raka taki gona, Allah ya Kara hada kawunanku.
Tace Ameen!!!


Nan tace Masa ya je ya karbo yarinyarsa, shikenan ba wani sauran alaka tsakaninsu.

Kwananta 2 ta tafi Maryam ta hada Mata shatara na arziki sai godiya take.


____________________

Bayan sati guda da rabuwarsu ya tura Mata text Akan ta shirya wa Khadija kayanta zaizo ya dauketa...Nan fa ta buga tsalle tace Bata yarda ba, wlh ba Wanda ya Isa ya rabata da yarta, yace aikuwa Baki Isa ba, shine mahaifinta Yana da iko da y'arsa. Tace wlh ko kotu Bata Isa ta rabani da gudan jinina ba.

Rigima akai sosai akan yarinyar, sun hakikance ita da mummy akan bazasu bayar da ita, duk inda zaije ya kaisu ya je.
Hakanan ya hakura ya bar musu.

Sannan suka yanka Masa wasu makudan kudi da zai dinga Basu na yarinyar duk wata, yace Nan fa daya iya karfina zanyi, in sun Raina su maido Masa diyarsa.

Anan ma ba karamin artabu akai ba, ba yadda suka iya suka hakura, saboda yarinyar ce bazasu bayar ba.

Bayan kwana 2 kuwa yace suxo su kwashe kayansu Yana da bukatar dakunan....

Ruky kuwa naji ance a kwashe Kaya Nan hankali ya Kara tashi, sai kiransa take Amma Sam wayar Taki shiga, sai text ta tura Masa wai don Allah Kar yai Mata haka, ya Bata lokaci su Dan fahimci juna, yace wane sauran faahimta kin manta babu wata sauran alaka tsakanina dake?

Yace zuwa next week kuzo ku kwashe Kaya zanyi amfani da dakuna..hankalinta sosai ya tashi.

Mummy kuwa da Anty batulu da wasu mutane 4 suka je gidan ranar Asabar da Shirin kwashe Kaya itama rukyn tace sai tazo yace karta soma tako Masa gida, mummyn tace tunda ga mahaukaciya ba, kartazo Tai maka hauka ko?

A zuciyar sa yace ai gara ma mahaukaciya tunda ansan itace...Nan ya tsaya ya kasa yana kula da duk abinda sukeyi, ya kulle bangaren Maryam gudun karsu soma shigar mata, don Yana jin suna cewa sai sun Mata dukan tsiya.




Nan dai suka hau parking din Kaya suna yi, suna zaginsu, harda mummy don itace ma kan gaba, wai har tana tunda ka maida diyata bazawara kaima in Allah y yarda sai an wa naka haka, duk Yana jinsu Bai ko tanka musu ba, abinda ya Kara Bata musu rai kenan.

Itama Maryam din ta saitin kofar ta sukai ta binta da munanan zagi suna to Yar masu bin bokaye maganinku yai tasiri sai aje a biya shi, shegiya Yar abukaza kaza Kuma uwar ce da wnn aikin da kanwarta Aisha, girma dai ya Fadi...


Maryam kuwa ko kula su batai ba, itama suna tare da wata yayarta har tana cewa ya za ai ku zuba musu ido suzo har gida suna zaginku, Maryam tace ai in mun biye musu muma min Zama su kenan ki barsu da halinsu kawai,


Haka dai suka kwashe kayan tsaf, bayan sun gama suka hau farfasa wasu abubuwan, suka yi gaba tare da takaicin rashin dukan Maryam ga haushin Bata tanka musu ba, suna fita Abbas ya rufe gate din gidan, ya koma ciki yaga irin barnar da sukai yace tunda ba wani kuka taba ba da sauki, yai tirrr da halinsu na rashin dattako, yai wa Allah godiya da ya raba shi da Kaya..



Ruky kuwa tunda aka kwaso Kaya wani sabon kuka ta bude, zuwa ynx ma sun Fara Jin haushinta, Akan wahal da kanta da take Akan Wanda Bai San tana Yi ba, shiyasa ynx kowa ya fita a harkarta.


Ga daddy shima ya zare hannunsa akanta,yace Kar ta soma xuwa inda yake, haka rayuwa Tai Mata kunci, ta shiga wani hali..ita kanta mummyn Taji zafin rabuwar tasu, sbd tana sane da cewa samun mutum kamar Abbas da wuya, gashi mutum ne Mai kulawa da gidansa akan komai..baya wasa da gidansa.tunda tasan cewa ba abinda zaka nema ka rasa a gidansa na Jin dadin rayuwa..mutum ne Mai zuciya.

Amma sai ta bar Abin a zuciyarta Bata bari an fahimceta ba.

Ganin yarinyarta na Shirin shiga wani Hali yasa ta tattara duk wata kulawa ga yartata don ganin ta dawo Mata da farincikinta. Amma Ina Abin na ruky babba ne har rashin lfy ta kwanta a asibiti tsawon wata guda, kamar bazata yi ba.

Sai da aka hada Mata da addu'oi ta Dan fara marmarowa, aka sallamesu suka dawo gida, ga babban tashin hankalinta hatta takardar da Abbas ya bayar ta sakin da ya rubuta ya Sanya yunkurin kisan kan da take son yine dalilin sakin..domin a zahirin gaskiya da ya furta Mata sakin ba uku yai niyyah ba, ganin irin haukan da ya biyo bayan sakin yasa shi yin ukun yace da ana fiye da haka da yayi..

To ynx shine damuwarta, domin xuwa ynx ta Riga tasan Abbas yai Mata nisa, ta hakura ta rage damuwarta akansa, Amma soyyayar sa kullum Kara karfi take a zuciyarta.kuma tasan duk Wanda yai yinkurin auranta yaji abinda Tai niyyar aikatawa bazasu yadda su kwasarwa kansu ba, ita kanta tasan har yarta ta janyowa domin za'a ce yarinyar Mai yinkurin kashe mijinta ne, ita kanta Yar za:a yi shakkun auranta.




Haka rayuwa ta juyawa ruky baya, ta shiga kunci Mara misaltuwa, ganin haka yasa mahaifinnata ya yafe Mata yace ta dawo wajensa da zama ko ta nesanta da shi...


Haka kuwa akai ta koma can wajen daddyn da Zama, Kuma ba laifi ta Dan samu saukin damuwa, da taimakon Anty nasiba,matar daddyn kullum cikin nasiha take Mata. Kuma Alhamdulillah ta dauka.
Domin ynx ta Fara cire shi a xuciyarta.


Ganin haka daddy ya Sami Mata aiki teaching, tana koyarwa a wata government sch, ko ta Kara samun saukin damuwarta, haka ta Fara koyarwa a makarantar hakan kuwa ya rage Mata damuwa sosai, saidai duk sanda ta tuno Abbas din tana kuka Mai isarta, shi kuwa ba abinda ya shafesshi don baima San halin da take ciki ba.saidai duk wata Yana Mata transfer na Khadija, wani lokacinma, har shopping yake mata ya aika gidansu, shi baima San ta koma wajen daddyn ba.



_____________


Acan kuwa gidan Abbas wata sabuwar rayuwa suka bude Mai cike da so da kaunar juna, ga wata kulawa ta musamman da suke ma juna, sai kacee sabbin amare, ga su Hassan sun girma har suna yawo ko Ina kyawun yaran ya Kara fitowa dik inda suka je sai anyi sha'awar su, shima abbnsu Yana gatanta su, Yana ji da yaran sosai..


Haka rayuwa taita shudawa, suna zaune cikin kwanciyar hankali, Abbas kuwa cewa yai ai shida Karin aure har abada...Maryam kuwa tace hmmmm Allah yasa....


Tuni Maryam ta koma makaranta, inda take masters dinta ynx, sbd Bata da wani nauyin yara domin su hassan ma an Sanya su amakaranta, domin wayo ne da su ga Baki radau sai kace wasu manya, Nan kuwa shekararsu 2.


Baba, sa'a itace har ynx ke kular Mata da yaran don sun Saba da ita, zata barsu a gida ta je ko Ina ba tare da fargaba ba.

Maryam an Kara zama babbar Mata, Kuma duk da haka bazaka ce ta haifi yara 4 ba.sbd kula da kanta da takeyi ko yaushe, kwalliyarta ma, sai abinda ya Karu, shiyasa ko yaushe cikin dokin junansu suke.



Bayan ya kammala gidansa da ya ke ginawa a wata unguwar suka koma, gidan babba ne sosai sama da kasa, tabbas gidan ya Sha kudi.. duk wani abin more rayuwa an Sanya shi, sai zuwa musu murna akeyi, harda wajen shakatawa da aka kayatashi,

Please Login or Register in order to submit comment