Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaso ta samu tai degree dinta a b.u. k, tunda result dinta yai kyau sosai, Allah baisa ta samu ba. Tayi murna kwarai anyi mata fatan Alkhairi tare da samuun nasara, Abba ma yayi farinciki sosai.



************************

Har sun fara lectures, inda suke fita tare sai ya kai mufid wajen ummi sannan ya kaita sch. Ita kam ta dage sosai wajen karatunta ta maida hankali sosai, tare da taimakon Abbas, ware lokaci yayi yana fahimtar da ita inda take da matsalar fahimta da goyon baya. Ai kuwa bata samu matsala ba tana samun point din da ya kamata.




A lokacin da take shekarar karshe wato N. D2 kuma ta samu wani cikin bayan yaye mufid din da tayi, tana shan wuyar cikin sosai ga karatu, a daddafe ta samu ta kammala karatun, a lokacin cikin yakai watan haihuwa.


Bayan kammala karatun ba dadewa ta haifi diya mace son kowa, farincikin sa bai misaltuwa, yarinya tasha gata ta fannin sittturu da dai duk wani Abu da jaririya yar gata ke mallaka, komai dinta na daban ne, an sanya mata sunan mahaifiyarshi wato, Fatima bintu suna kiranta da elham.

Ranar suna an sha shagalin suna cikin kwanciyar hankali, mufid kuwa ya koma wajen dad dinshi tare suke kwana shine ke masa duk sauran dawainiya, wannan Karon ma inna ce ta kula da su da babyn, saida sukai 1month ta tafi, kasancewar ynx hatta da wanka baby maryam ta iya.


Bayan arba'in Elham ta Kara girma sai dai ba ta kai kibar mufid ba shi yayi kiba sosai don kuwa tana wahala wajen goyashi, ko a hannu yake yana gajiyar da ita, to ita kuma bata da jikisosai saffa-saffah.


Ba abinda ya canza soyayyarsu suna cikin kwanciyar hankali, tana kokarin gyara jikinta bata wasa da kanta, ko ta fannin gyaran gidanta da kwalliyah ma sai abinda ya karu domin cewa tai ita ko haihuwa goma tai bazata daina wa mijinta kwalliyah ba, akasarin matan yanzu kuwa Ana haihuwa daya sai kaga duk sun sukurkuce ba gyara jiki bare make-up a tunaninsu ai komai ya kare tunda ba wani sauran soyayyah.

Duk da cewa suma mazan duk irin kulawa da soyayyah da tattalin miji da suke samu wajen matansu bai hana su Kara aure in suka tashi yi.

Kamar yadda ta faru ga wadannan ma'aurata, maryam ta fuskanci wasu canjin halaye ga husbynta wasu lokutan baya dawowa gida da wuri in ta tambayeshi yace aiki ne yai masa yawa, amma bai canza mata ba ta fannin kulawa da nuna soyayyah, yana sonsu ita da yaranta.

A lokacin ne ya hadu da rukayyah har zance yai nisa, ta kai ga magana aure duk da da farko an fuskanci yan kabulabale daga wajen ita yarinyar da kuma mahaifiyarta kamar yadda na fada a baya.


Lokacin shekarar Elham biyu taji zancen aurenshi taji labarin aurenshi, hankalinta ya tashi sosai tai kuka, shikuwa ya kasa tunkaratta da batun gani yake bazai iya gaya mata ba abin yai masa nauyi sosai, itama wajen matan yaya taji maganar kuma sai da tai ta lallashinta kan cewa ta kwantar da hankalinta mijinta na sonta, ba wai don ya daina Sonta ne zai Kara aure ba, haka dai taita lallashinta.

Itakam duk tunani ya cika mata zuciya ta rasa dalilin da yasa zai Kara aure ta tsayatsaf tai nazari ko Zata gano wani abinda ta gaza masa da zaisa shi Karin aure, amma ta kasa gaza ganowa. Kuma har ila Yau bai fada mata ba, saidai ya fuskanci ta sauya masa ba kamar da ba, duk ta rame, kana ganinta kasan tana cikin damuwa, shima ya fara shan jikinsa ya fara zargin ko ta ji labari, wannan ne kesa shi zulumin gaya mata yana tsoron abinda xai biyo baya.

Aunty sadiya ko da taji labari murna tai tayi wai ai yanzu zai samu yancin kansa wai yarinya tabi ta asirce shi bai ganin kowa sai ita yar karama da ita sai kissa da kinibibi, su kuwa Duran yan uwansa basu ji dadi ba suna ta fadin yarinya mai hankalin da sanin girman mutane, kawai ya jajubo wa kansa kuma Sunji labarin gidan da yarinyar basu da dattako ga tsirfa iri-iri.





Ranar wata juma'a da daddare suna zaune gabadaya a falo tare da yaran yana tai musu wasa suna hawa bayanshi yana musu doki, amma ita ba walwala a tare da ita, shiko yana kallonta Jefi jefi. Tasowa yai ya zauna kusa da ita, yace my luv meyake damunki ne na fahimci kina cikin damuwa ki fada min meyake faruwa ne yana shirin riko hannunta ta fuxge, yace to ynx na gano ni nai laifin ko? Shiru tai masa ta tashi ta shige dakinta ta fada kan gado tana kuka, biyo bayanta yai a zuciyarsa kam yace tabbas taji labari, shiga dakin yayi tare da fargaba mai tarin yawa a xuciyarsa...



*muje zuwa*


*by*

*Ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀




*Story&written*


By



*ummu Ameer*💃







*page* 1⃣4⃣





Tura kofar dakin yayi tare da fargabar mai tarin yawa, a kwance ya sameta ta kifa kanta da pillow, sautin kukanta na tashi kadan kadan, zama yayi kusa da ita tare da dagota ya jinginata ajikinsa tana ta kokarin kwacewa shiko ya matse ta gam ajikinsa, yace babynah wai meye ke faruwa ne kin canza min completely kinsa kanki cikin damuwa 'why'? Dallara masa harara tayi tace ba ka san meke faruwa ba ko?
To tashi ka fita wlh banason ganinka ta fada da ihu, niii yau kike kora adakinki baby?
Tureshi tayi da karfin da bata san tana da shi ba, tare da fadin Abinda yafi hakama zanyima, ta tashi ta mike tsaye tare da juya masa baya, laifin me nai haka, ka tambayi wadda kake shirin kawowa gidanka,
Tashi yayi ya fuskanceta yace ki zauna muyi magana plx, kamo hannunta yayi Zaunar da ita ma shima ya zauna, zuciyarsa yana godewa Allah da yasa abin ya tsaya iya haka, domin kuwa yana jin labarin wasu matan fa insunji za ai musu kishiya suke tada hankalinsu tare da HAUKA iri-iri.

Dubanta yayi yace Ina son ki nutsu ki fahimci Abinda Zan gaya miki, a zahirin gaskiya aure nake nema ba don na gaji dake ba ko kuma don na daina sonki, ko kuma don na kuntata miki, hasali ma wlh har yanzu bansamu macen da nake so kamarki ba, ba abinda kika gaza min kawai dai aure kaddara in Allah yayi ba makawa sai anyi, wlhy bani da ra'ayin mata biyu a tsarina, kawai lokaci daya naji abin a raina, kuma insha Allahu zan kare miki mutunciki babu wani mahalukin da ya isa ya taka ki in kyaleshi, Kina da matsayi na musamman a zuciyata kece zuciyata, bani niyyar wulakantaki balle har wata taga fuskan da Zata samu ta raina min Uwar 'ya'yanah, hakika nasan duk macen da mijinta xai Kara aure tana shiga wani hali, wasu ma har su so kauce hanya, suna jin ciwon abin sosai a arai, Ina mai Baki hakuri ki gafarta min, ki ci gaba da kaunar mijinki tare da faranta min kuma muyi Addu'a samun xaman lafiya gabaki daya, Allah ya sa Alkhairi ne, Allah ya kawar mama da sharrin dake ciki.
Ya kare maganar da goge mata hawayen da ke fuskanta, ya dubeta tare da tambayatta Ina fatan Kin fahimceni kuma kin hakura komai ya wuce, taji dadin kalamansa amma zuciyarta ta kasa yadda da cewa Anya kuwa bashi da wani dalilin yin auren ko ba zai iya fada bane, wata zuciyar kuma tace ai kinfi kowa sanin halin mijiki shi bai boye mata Komai ko wani abin tai da bai ji dadi ba yana fada mata bai barinsa a zuciyarsa ita kuma sai ta gyara, sauke doguwar ajiyar zuciya tayi tare da fadin na fahimceka mijinah Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kuma hada kanmu gabadaya, wata kyakkyawar hug yai mata tare da fadin I know u my wiffy, nasan bazan samu wata doguwar matsala daga gareki ba nasan kina da hakuri da juriya tare da hankalin yan shekaru 40 wannan ne yasa kullum kike Kara shiga zuciyata ngd uwar 'ya'yana Allah ya Kara mana so da kaunar juna tare zaman lafiya mai dorewa har Abada, I luv u tare da manna mata kiss, dubansa tayi tare da gasgakata zancensa tace husby nah Ina maka fatan cika Alkawarin da ka dauka zan taya ka da addu'a domin zama adalin miji, Allah ya sanya Alkhairi. Yace Ameen! Bai bar dakinba saida suka sha soyayyah.


Sun manta da yara a falo, sukuwa yaran sunyi wasa har sun gaji anan bacci yai awon gaba da su, yace very sorry my kids naje Ina lallashin momynku, daukar mufid yayi yaje ya kwantar da shi a dakinsa ita kuma ta dauki Elham.






****** ****** ******
Koda su ummu suka ji labari abin ya dan taba mata zuciyah amma daga bisani ta fawwala wa ubangiji tare da yi musu addu'ar samun zaman lafia yasa kuma Alkhairi ne,

Akwai wata rana da maryam taje gida ummi duk taga ta dan rame ta yi duhu tai ta yi mata nasiha kan ta kwantar da hankalinta ba komai sai Alkhairi shima Abba yai mata nasiha tare da yi musu fatan Alkhairi amma a zahiri yaji tausayin diyarsa, duk cikin ''ya'yan ita Allah ya kaddarawa za a mata kishiya, Addu'a yayi musu.


Zainab ma da taji labari ta taya kawarta kishi, itama tai aure tana da yarinya guda 1, har gida tazo tai ta lallashinta duk da ma ta fuskanci tana da saukin KISHI, don ta fahimci ma bata wani damu sosai ba, tace kawata wlhy Ina tsoron kishiya duk ran da Abdul yace zai min bansan wane irin hali zan shiga ba wlhy domin ko amakota ne naji anyi wa wata kishiya karkiso kiga yadda nake taya su kishi, to bare a Kaina kuma, gaskiya kawata kin burgeni samun kamarki da wuya, tace ai dole in rungumi kaddarata, kinsan Dama shi aure ko wanne da irin matsalar ni dae fatana Allah ya hada ni da ta gari shikuma Allah ya bashi ikon rikemu da amana, wata shewa zainab ta saki tare da tafa hannaye tana fadin yayi kawata Allah ya sausaauta min kishi na kamar naki. Ameen maryam tace. Haka suka yi ta hirarsu har Abbas ya dawo suka gaisa tace ai tafiya zatai ya bata transport ta bata sukai sallama ta tafi, itama tawuce wajen mijinta domin tarbarsa.

Shiko ko yaushe cikin sanya Mata Albarka yake, da godiya ga Allah da ya bashi mace kamar maryam a matsayin Uwar ya'yansa.

Duk wani shirin auren da akeyi bai boye mata komai ba inda shaida mata sauran satin biyu ynx, har gidan da ya Kama haya sai da ya gaya mata kuma ya shaida mata yana sa ran zasu samu fahimtar juna domin itama bata da hayaniya kamar ita kusan halinsu daya, tace Allah yasa.

Ita ma an kawo mata kayan fadar kishiya duk wani Abu da ya sawa Rukayya itama ya sanya mata shi sannan ya canza mata furnitures, ya bata kudi ta sayi duk abinda take bukata.

Itako ba abinda tai da wannan kudi sai gyara domin cewa tayi sai ya kasa tantancewa, hafsa ta sa ta rakata taje ta kwaso English wears na neman tsokan dama ita gwana ce wajen sanya su ko don sunayi mata kyau ne oho! Don ita ka'ida ne kazo gidanta cikin kananun kaya take Da yamma ko dare, Suna mata kyau sosai shima yana son ganinta dasu sbd suna gigitashi, shima da kanshi in ya ga wadanda suka dace d ita yakan sayo mata, Ita duk abinda tasa ma yana mata kyau ta iya daukar dressing.







*ku biyoni domin cigaban labarin*




*by*

*ummu Ameer* 💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀





*Story&written*


*by*


*ummu Ameer* 💃



*page* 1⃣5⃣



*cigaban labarin*

""""""Saura 2weeks biki inda ake ta shirye2 anje an gano gidan amarya, sai da mommy tasa ya samo gida wajen 4 tana cewa bai yi ba sai a na katshen ne yarinyar tace ita yayi mata haka, hakanan ta hakura amma ba don ta so ba Uwar.


Ba karamin gyara yayiwa gidanba domin komai kusan sabo aka canja, gidan kuma yayi kyau sosai da ya sha gyara, gashi da girmansa, babban falo da 3bed room sai kitchen Babba a falon. A zoo road gidan yake.




Amarya kuwa sai gyaran jiki ake mata kusan 1month Ana yi, itama mommy hakanan ta saduda ta hau gyaran diyarta tare da sihirinsu da suke ma 'ya'yansu in sun kusa shiga gidan miji domin kamashi ahannu.


Bangaren maryam kuwa tunda taji labarin mahaifiyar yarinyar ta shiga damuwa domin tana jin labarinsu in suka Auri miji fa to kishiyar ta shiga uku, domin mijin ma shakkarsu suke bare wata kiahiya, inko su aka fara aura to bai isa ya kara wata ba, ko da yayi ma to Zata yi gaba don azaba, duk da ba Dina aka taru aka zama daya ba, don kafin tai aure akwai neigbour dinsu yar maiduguri mijinta zai Kara aure, sbd bakin kishi ta kwance masa burkin mota, sai gawarsa,

Kukanta ta kai wajen mahallicin ta akan ya kawar da duk wani sharrin da ke ciki, ko bacci bata samu sbd nafilfilun da take yi da daddaren gashi ko yaushe cikin Azkar take.




Tuni an rarraba invitations har da na dinner, da farko Abbas din bai amince ba sai da Uwar ta ce ai ya zama dole ya shirya dinner, ba makawa, haka nan ya hakura ya amince ba don yaso ba, yana mamakin wannan karfin hali nata, tuni auren ya fara sure masa yana shakkar abinda zai biyo bayan auren ya na tantama akan ko zai iya jure halayen surukarsa, har fara ganin laifin kansa akan Karin auren da yake shirin yi, ba wani Abu da zaiyi sai ta Nuna bai mata ba, ya fara surewa da lamarin, domin tun kafin maganar tayi nisa ma yaso janyewa, ita kuma yarinyar ta shiga damuwa taita bashi hakuri akan halin mahaifiyarta, tana matukar kaunarsa, domin kuwa bazata iya hakura da shi ba gani take in ta rasa Abbas kamar ba zata samu kamarshi ba tana matukar kaunarsa, ko kiranta in baiyi ba sai ta shiga matsanancyar damuwa. So, halin da zai jefa ta in suka rabu ne kawai yake dubawa, kuma ko ba komai shima yana sonta. Shiyasa kullum yake Alfahari da iyayen maryam samun sirukai masu dattako kamarsu da wuya.



**** ***** *****
Itama maryam bai barta abaya ba, an gyara mata gidanta an yi Mata fenti da sauran gyare-gyare, ranakun biki nata matsowa, sai dai ba rawar kai Abbas kamar na maryam, har friends dinshi ke tsokanarsa wai baiyi Adalchi ba, shiko yace ai duk wani Abu na farko an fi Nuna doki da zumudi.


Gidan Amarya tuni sun fara gudanar da shagulgulansu tun ranar laraba, inda suka bukaci zuwansa amma fir yace yana da uxuri, hakan kuwa ba karamin bata ran amarya yayi ba, ganin irin bacin ran da ya nuna ne yace bayan magriba zai xo, sai a lokacin ta Dan ji dadi a ranta, ko ba komai yaxo yaga kwalliyar da ta sha...

Wata laffaya ta sanya lemon green ta sanya kananun kaya aciki, sai wata tafkekiyar sarka da ta sanya awuyanta ga wata ta sanyae a gaban goshi tayi kyau sai kunshin da ta sha a kafafuwa da hannaye, sai awawaraye duk an kusa cika hannayen da su sai wani takalmi mai tsinin gaske da ta sanya tare da wata karamar purse kamar ball, ta rike a hannunta, suna ta gudanar da Al'adarsu.

Abbas ko sai da ya koma gida YaI wanka Yai sallar magriba, ya shaidawa maryam zaije gidansu Rukayyah akwai program din da sukeyi Yau, sun bukaci zuwana tun daxu bansamu dama ba, shine zanje yanxu ba jimawa xanyi ba, kinji baby, rau-rau tayi da idanuwa a xuciyarta tace yanzu har ya fara zama nata kenan, nan da nan kishi ya turnuketa, sai dai bata bari ya gane ba, ta danne ta ce shikenan husbynah Allah ya tsare hanya, sai ka dawo, yace Yau ba rakiyar kenan binshi tai har bakin motor ita ta bude masa kofar ya shiga ya ruko hannunta Yai kissing dinshi, sannan yace na gode my lovely wife, samun kamarki da wuya Ina Kara godewa ubangiji da ya mallakamin ke, ita ko kawai murmushin yake take yi da bai kai zuci ba domin ta fara kasa danne kishinta ayanxu, tace masa a dawo lfy, sannan ta juya domin komawa cikin gida, tana shiga ta fada kan kujera tana kuka tace daga wannan satin mun zama mu biyu kenan a wajen mutumin da nake kauna fiye da komai Anya kuwa zuciyata zata ita jure ganin Abbas da wata matar, Anya kuwa zan iya! Sai alokacin ne tace dama tana da irin wannan kishin, ta dade a wajen tana ta tunanin abubuwan barkatai, daga bisani ta tashi taje tayi alwala domin gabatar da nafilfilin da addu'o'i ko ta samu saukin halin da take ciki.






*Allah sarki maryam sai munxo dannar kirji.. **😜





*by*

*ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀




*naji sakonku masu cewa bai kamata aima maryam kishiya ba, Ina so ku gane wani Abu readers da kuma writers din tunda nake karatun novel ban taba ganin inda akayi ma tauraruwa littafi kishiya ba sai dai ace ai tursasa masa akai ko makamancin haka, amma ba ason ranshi ba, ni kuma abinda nake rubatawa a littafina kusan abinda yake faruwa ne a zahiri, domin Kuwa mazan yanzu kusan duk irin so da kauna da kulawa da haduwarki wajen gyaran jiki ko shan magunguna duk wannan bai hana su yo miki kishiya kusan ma sun maida abin kamar gasa, a zahiri akwai wadanda basu da ra'ayin mata biyu, wasu mazan kuma kawai ra'ayine suna son suga sun mallaki fiye da mace daya, amma a Hausa novel kullum wannan tauraruwa ita ce farko itace karshe Wanda a zahiri ba shine abinda yake faruwa a cikin Al'umar ba, ni dai fatana mu writers mu dinga kokarin isar da sakonin abinda zai amfanemu Baki daya ta hanyar kawo gyararraki a zamantakewar ma'aurata da masu shirin shiga gidan miji kuma shi wannan Karin aure ba wai yana nufin ya miji ya daina kaunarki bane, duk da cewa akwai mazan da suke da matsala da matayensu ta rashin tsafta ko rashin iya kula da miji ko rashin iya girki ko rashin bawa miji hakkinsa ko rashin gamsar da miji wadannan ma suna taka muhimmiyar rawa wajen jan ra'ayin miji ya kawo miki abokiyar zama, Ina fatan kun fahimceni, ngd*
*Allah ya bar zumunci*🤝





*story&written*

*By*


*ummu Ameer*💃






*page* 1⃣6⃣






"""" Abbas yana hanyar
zuwa gidansu Amaryarsa, amma sai jin wani muguwar faduwar gaba yake, sai "innalillahi wa inna ilaihirraji'un"yake ta ambato har wata zuciyar na ayyana mishi kawai ya koma gida, wata zuciyar kuma na bashi kwarin gwiwar zuwa har zai biya ya dauki abokinshi Yusuf su tafi tare kuma ya fasa gudun kar in-law din tashi tai wani abin maganar da ta saba, yana tuki yana ta sake-saken aranshi har ya iso gidan, tun daga waje yake jiyo qamshin turaran wuta kasancewar Yau ranar turarence, kusan kowa yana dauke da kaskon turare a hannunshi dauke da garwashi aciki, an zuba turaren a ciki ko wane da qamshinsa sai rawa suke suna waka da yarensu, hakan ne yasa daga waje ake jiyo qamshin turaren, can gefe kuma ga wani katon kasko a gefe shi wannan kuma da zarar ango ya bayyana a wurin ake zuba turaren da wata laya a cika, to dazarar anyi hakan tun daga lokacin zai dinga yi mata wani irin so tare da shakkarta.


Kiranta yayi a waya ya shaida mata ya iso, nan da nan ta Kara gyara make-up, ta fito domin shigo da shi ciki, dama a harabar gidan suke ta shagalinsu. Tafiya take kamar tana tauayin kasa ga takalmin data sanya mai tsinin ba iya tafiya tai dashi sosai ba, shiyasa take tafiya a hankali, shiko yana jingine jikin motar ya harde hannayensa,sanye yake da wata dakakkiyar shadda blue tai masa kyau sosai da hularsa itama blue sai faman qamshi yake zubawa, sai murmushi yake mata, itama haka,tuni ta Kara jin wani irin sonshi na Kara shigarta a zuciya tana zuciyarta fal da farincikin ta kusa zama mallakinsa, matarsa kuma Uwar 'yayansa inshaAllah, tana isowa tai saurin jingina da motar tana maida numfashi, yace lfy dai? Wlhy baby takalmin nan ya wahal dani tsiininshi yayi yawa, yace to meyasa kika sanya shi ko so kike ki wahal min da kanki, tace banma yi tafiya da shi ba tunda na sanya Ina zaune kan kujera, bayan sun Dan taba hira tace baby mu shiga ciki hannunshi ta rike suka shiga tun dosowarsu aka kunna wannan turaran na musamman da aka tanada domin shi, sai faman guda suke suna kowacce da kasko ahannu suna binsu suna waka, bayan sun Dan zauna ba dadewa aka fara pictures ko wanne tana makale da shi ta rike shi kamar za'a kwace mata, anan ma saida uwar tace akwai wani dan akwati da angwaye duke zuba kudi yana daga cikin Al'darsu sai da ya zuba kusan 70k Allah ya so ya taho kudi, amma ita yarinyar bata son abinda mahaifiyarta keyi, har wajen karfe goma yana wurin amma duk an watse, sai friends dinta a gurin, shima yace zai wuce gida tace haba baby tun yanzu baka zo fa da wuriba, yace ai dai nazo ko, na fita ko ba sabulu, tace to muje na raka ka mota, tare suka jwra har zuwa gurin motar tashi, ya shiga ya zauna ita kuma tana rike da murfin kofar tace amma baby gaskiya banso zaka tafi yanzu ba, ban gaji da hira da kai ba yace Saura Kwana nawa ya rage duka ki tare a gidana kiyi hakuri kinji luv! Tace to shikenan baby Allah ya Nuna mama wannan rana yace Amiin! Tace amma baby mai yasa baka zo da friends dinka ba, yace suna da uxuri ne shiyasa.
Tace okay!
A gaida gida ka kula min da kanka plx!
Yace insha Allah!
Kunyi kyau Amaryata
Nan aka hau juya idanuwa tare d fadin tanx angonah!
Kunna motar yayi zai tafi itako sai faman daga masa hannu take tana masa bye! har sai da motar ta bace, sannan ta juya Zata koma ciki.

Zuciyar ta fal da kishi aranta wai yanzu Ma haka sauri yake ya koma wajen matarsa shiyasa ya damu ya koma, mtsss tsaki tayi aranta tace Ina tunanin Randa zan budi ido in gansu tare da ita zuciyata fashewa zatai don kishi, Ina ma ace ni ya fara aura da bai isa yayi tunanin wata ba, ni mai ya kaini in ba don son da nake masa ba ma, Ina zan auri mai mata, amma ba komai tunda gidana daban zan samu saukin kishin..

*Anya kuwa*?





Shikuwa a hanya motarsa ta samu matsala tayar motar tai faci gashi duk masu gyaran sun tashi sbd dare ya fara yi, yana tsaye a wajen yana tunanin abinyi, can ya dialing no musa da yake masa gyaran mota, ya shaida masa motaraa tayi faci ya taho masa da spare ya bar tashi gida, nan da nan ko ya garzayo ya taho duk da cewa yana gida alokacin.

Sai kusan 11;20pm aka kammala yace musan ya shiga ya rage masa hanya, azuciyarsa ko baiji dadin delaying din da ya samu ba, don yasan maryam zatayi tunanin ko yana can tare da amarya duk da yasan tana da saurin fahimta, amma shi bai son bacin ranta ko kadan, bashi ya iso gidaba sai to-12.



Maryam kuwa ranta ba karamin baci yayi ba ta Hama kufuluwa tace tun yanzu har an fara haka daga cewa ynx zan dawo had yanzu shiru, gashi ta kira wayar tana ta ringing bai dauka ba, shiko ya aje ta a motar sanda ake canja tayar, kuma ko da ya shiga bai duba ba, itako batai tunanin komai ba sai suna tare soyayya ta debeshi ya kasa picking call dinta abinda ya Kara kular da ita kenan,, tayi kukanta har ta gaji bata san ma lokacin da bacci Yai gaba da ita ba.








*muje zuwa*





*by*

*ummu Ameer* 💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI

Please Login or Register in order to submit comment