Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bai ganta ba ya Kira Taki dagawa, ya koma wajen Maryam aka Basu suka taho komai normal.


Suna Isa tace ina ruakyya yace Shima Bai sani ba,yazo ya duba Bai ganta ba ya Kira Bata daga ba, tace Abban mufid bansan Ina Zama silar matsalarku naganta cikin damuwa tunda muka taho,rabu da ita ... .


Can gida ya kaita wajen ummi yace in ya gama zai zo ya dauketa....







Muje zuwa


*By*


*Ummu Ameer*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻






*Story & written*



*By*



*Ummu Ameer*💃




*Page* 3⃣2⃣




"""""Rukayyah kuwa ba inda ta zame sai gidan wata kawarta da sukai school tare, tana zuwa ta hau kuka farida kawar ta ta hau tambayar lfy kike kuka,me ya faru ..?

Ita dai kukanta take sai da tayi Mai isarta sannan ta kwashe komai ta fada Mata da irin zaman da suke ....ai tun kafin ta karasa farida tace Amma kin badani wlh ...kina mace tana mace sannan har ki Bari ta fiki tasiri a zuciyarsa ...Ashe Baki da wayo ko kadan, Ina ganinki Yar gari Ashe kallon kitse nake wa rogo.....

Rukayya tace to me ake so nayi ? Nayi iya kokarina wajen ganin na janyo hankalinsa gareni Amma kamar ingiza shi akeyi...Kuma duk da haka ba haka na zauna ba, in maganin ya fara tasiri Bai jimawa ajikinsa sai kiga an koma gidan jiya...Ina tunanin malaminta yafi namu karfi....


Wata bazawarar dariya farida ta saki tare da tashi ta karasa kusa da ruky ta dafa kafafarta tana cewa "ke da baki shirya ba kika kwaso Mai Mata haj.ruky?

Ai ya kamata ace kinsan komai akansu kafin ki aureshi, ki San wacece matar kisan wane matsayi take dashi a wajensa kisan irin soyyayar da yake mata, sai ki San irin aikin da ya kamata ki Fara akansu tun kafin ki shiga gidan, Kinga da kinyi haka komai zai zo Miki da sauki Kuma da bakiyi facing ol dis problem ba...at least Kya samu saukin wasu abubuwan.


Ruky tace hakane wlh duk banyi wani tunanin ba,idona ya rufe akansa, banyi tunanin zan samu wata matsala daga gareshi tunda muna son junannmu...kawai matarsa ce ta shiga tsakaninmu.

Yanxu me shawara tunda har ynx Ina da sauran dama.....

Farida tace kinganni nan a cikin gidan nan sai abinda nace wa mijina shi akeyi hatta da provisions na Abinci a bangarena yake sai abinda Naga damar bayarwa ko Bai Isa ba, Basu da damar tambaya....ke hatta da girki in Banga dama ba sai yayi 2-3 wks Bata girki a gidan nan,in banso ba sai yayi kwana da kwanaki baiga fuskarta ba, gashi ni bani da kowa a gidan kinsan matsalata ai tun muna sch. So ynx likita ya tabbatar bazan iya samun ciki ba...Kuma hakan bai canza komai ba daga gareshi...ruky Tai saurin katseta da cewa ke kuwa wajen wa kike zuwa har kika samu wnn nasara haka....murmushi farida tayi tace kin faye gajen hakuri...ruky zan gaya Miki.


Tace ba inda nake zuwa a ynx Amma naje dai kafin na shigo gidan a ynx ba inda nake zuwa sai basirata....ruky tace bangane ba?


Farida ta kwashe duk irin kissa da makirci da Kuma magungunan mallaka da take amfani dasu duk ta fadawa ruky ...ruky kuwa mamaki ne ya cika ta Jin irin wanna shedanci na kawarta ....


Nan itama ta karanta mata duk irin Wanda zata Fara Yi a cikin gidanta ...Aiko ba karamin farinciki ruky tayi ba tace da Ina dake Amma na tsaya Ina wahalar da kaina....har magungunan ta hada Mata. Tai Mata godiya sosai sukai sallama akan cewa itama farida zata kawo Mata ziyara tazo taga wnn kishiyartata...




Farida tare sukai sec.sch.da ruky,dama farida tun suna sch. Bata da kunya gashi Bata tsoron kowa ba wani kyau ne da ita ba, tana da haske shine ma ya fito da ita ga son kwalliya a cika fuska da su eye shadow da eye liner kamar aljana.

Alh Auwal indabawa shine mijin nata Yana zaune da matarsa lfy da yaranmu 4 biyu maza biyu mata, ga matar kyakkyawar gaske bafulatana ce kamar ita Tai kanta, sun taso cikin kaunar juna da mutunta juna.

Kwatsam ya debowa kansa ruwan dafa kansa don farida tun kafin ta aureshi ta gama da shi Kuma gashi mutum ne da yake sake da addu'a da rashin maida hankali ga ibada itama matar Abin Yana damunta tana iya kokarinta wajen ganin yana maida hankali ...

Haka akai auren ta shigo gidan da gadara ..cikin kankanin lokaci ta gama da shi,ya zamo tsoron shiga wajen uwar gidan yake kiri-kiri Yana ji Yana gani wajenta ya gagareshi...sai ya tambayi izini a wajenta sai ya tambaya kusan sau 5 take barinshi ya shiga...

Ita Haj.bilkisu (uwar gidan) Bata sake da addu'a tana iya kokarinta da ba don haka ba ma sai Abin yafi haka...kullum cikin tsayuwar dare take Akan Allah ya karya duk wani tuggunta.






******* **********

Rukayya kuwa da matsanancin farinciki ta koma gida....tare da karfin gwiwa har da kiransa a waya ta bashi hakuri akan tafiyar da tayi yace dama ke kikai kidanki kikai rawar ki ...ya wuce sai a kiyaye gaba....tace tnx baby it won't happen again....sukai sallama tana kashe wa ta saki wani ihun farinciki tana tsalle wai komai yazo karshe.....garin tsallen Bata ankaraba ta takewa Yar tata kafa Tai ta kuka kamar ranta zai fita, Ashe targade tayi...hankalinta kuwa ya tashi sosai ga murna ta koma ciki....


Sai da ya dawo suka kaita wajen Mai gyara yarinyar kuwa Tasha wahala sosai Shima uban sai da ya tausaya mata ruky kuwa kuka shabe-shabe tana taya diyarta ....

Bayan sun dawo yace wai garin yaya kika Bari tai wnn raunin Tai Masa karyar wai tana rarrafe ne Bata San tana bakin kofa ba shine ta taketa....yace Allah ya kiyaye gaba Amma a dinga kula .....





Jingine duk wani shiri tayi a gefe sai Khadija ta warke sbd tana Jin tausayi yarta sosai ....



*To masu karatu muje zuwa shin ruky kuwa zata samu nasarar akan Shirin da takeyi ...hausawa dai na cewa in wani yayi rawa an bashi kudi wani duka
zai Sha*




Taku


*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Story & written*



*By*



*Ummu Ameer* 💃

*Godiya dubu ga masoya Ina jin dadin comment naku domin shi ke Kara min karfin gwiwa...ngd sosai* ❤





*Page* 3⃣3⃣






'''''’'''sai da akayi sati guda sannan Khadija ta samu sauki, shiyasa ruky ta jingine komai sbd kulawa da diyarta sbd ba karamin damuwa tayi da ciwon nata ba, tana tausaya mata sosai, tana matukar ji da ita kamar me, Bata son ko kuda ya taba ta...wannan daliline yasa ya aje duk shirinta waje daya tace ba abinda yafi lfyr yarta gudan jininta ....







Ranar Asabar a ranar ta tashi da aiwatar da Abinda suka shirya da farida......



Tun wajen 11am aka shiga kitchen ana shirya abinci ta zage iya karfinta ko tasamu ta inganta ya cinye tas kamar yadda yake a wajen Maryam ...ta gwada irin na Maryam Amma baiyi irin nata ba...don kin ciyuwa ma yayi Kuma ya gane Sarai na Maryam take son kwaikwaya yai ta dariya a zuciyarsa yace girman Kai ya Hana a koya...



Shiyasa yau ta zage ta hada duk wani abinda ke Sanya girki dandano da qamshi...tuwon shinkafa tayi da miyar agushi,kasancewar ta fahimci Yana son kalar Abincin a gidan Maryam in tayi shine ta gwada Amma Ina kwata-kwata tuwon Bai dahu ba aka tuka dama haka take yin tuwanta fa shinkafa batso -batso Bata Bari ta dahu ta tuka ga ruwa aciki Bai tsane ba...sai yayi wani shakakaf, a hakan ma ta gyara ganin yadda na Maryam take nata kamar sakwara, miyar ma haka ayita agushin daban ruwa daban ba kyan gani ....

Sai juice din da ta hada Masa Wanda a ciki me ta Sanya Masa maganin barci Yana Sha zai Fara bacci....


Ta gama komai tana jiran dawowarsa ta gyara ko Ina yau ..itama ta Sanya turaren gidan Yana ta qamshi...Amma da ga turaren ga burner Amma kiwa ta Hana ta kunnawa, yau Kam ta zage don tun safe ake a tsaye Kuma ba karamin jiki taji ba...duk ta gaji abinda Bata Saba ba....




Koda ya dawo gidan ya Fara shiga wajen Maryam kamar yadda yadda Saba ...wadda cikinta har ya Fara fitowa ya mata kyau ...ya sameta tsaf da kwalliyarta hakama gidan tsaf cikin baya Hana ta gyara kanta ko kiwar gyaran gida ta Riga ta Saba ma in batayi ba Bata Jin dadi.



Bayan sun gaisa yayi wa yaransa wasa ya danyi mintuna sannan ya wuce wajen ruky....



Yana shiga wajenta yaji qamshi Yana tashi an gyare ko Ina tsaf ....Yana shigowa aka wani tafi a guje akai hugging dinshi tana masa shagwabar tayi missing dinshi ...shi dai duk ya cika da mamakinta tun a waje ya Fara ganin changes ...shi kuwa da Bai shiru da Baki in yaga sabon Abu ko akasin haka yace toh sabon salo kenan yaushe kika canza haka lokaci daya....ta wani langabe Kai tana cewa haba baby! Dama can haka nake ...murmushi yayi ya dauki Khadija Yana Mata wasa ba dadewa tayi bacci dama bacci takeji ta kwantar da ita ...ita Kuma dama wasu kaya ne ajikinta mini skirt da wata half vest tazo ta zauna kusa da shi ta Fara aiwatar da shirinta sai da ta gama rikirkitashi da salo salo na kissa Wanda Bata taba Yi Masa ba....ai tuni suka Lula duniyar ma'aurata, dama tayi amfani da wnn maganin da farida ta Bata...Aiko ya Mata aiki sbd taga aiki ba kadan ba...


Bayan sun samu nutsuwa ya shiga toilet yayi wank ya Sanya jallabiya ya fesa turare ya fito yace zai shiga wajen Maryam zai kulle gida tace haba baby! Baka ci abinci ba saka fita haba zo na baka kaci ka koshi sai kaje...


Zuwa tayi ta janyo hannunsa ta zaunar da shi ta zuba Masa abinci Yana Kai loma daya ...ya furzar da shi kallonsa tayi cike da bacin rai tana cewa bansan ranar da zaka Fara cin girkina ba kullum nayi kace baiyi ma ba...adalchi kenan ?



Shiko har da wani janyo ta ta kwanto a kirjinshi Yana wani lallashinta wai tayi hakuri wlh Yana iya kokarinsa wajen ya ga ya ci Amma sai ya kasa....kiyi hakuri ki gyara kinji...

Dagowa tayi daga jikinta ta ce to ga juice din kasha ta zuba Masa cikin glass cup ita ta bashi ma abaki dake yasha sanyi Kuma ba laifi yayi dadi duka ya shanye tas....


Aiko Nan ta saki wani murmushi....Nan take kuwa ya Fara ...layi kan kace me bacci ya daukeshi.da dai ta tabbatar da cewa yayi nisa ...ta saki dariyar mugunta tace ai sai kaje wajen Maryam din tace Dani kike zancen....


Haka Abbas ya bige da bacci Akan kujera Bai San duniyar da yake ba...shiyasa ta Fara morarsa Yana dawowa sbd tasan zai dauki lokaci kafin ya dawo dai2





Maryam kuwa ta baza idanuwa Abbas Bai shigo ba...gashi elham tana fama da ciwon ciki...sai kuka take tayi, ta kirashi yafi a kirga Amma ba'a dauka ba...sbd ruky ta Sanya ta a silent Kuma tana ganin Kiran da akeyi




Da dai Maryam taji Shiru ta aika mufid ya kirawo Abbansa yace elham ce ba lfy ...Amma da ya zo ya Gaya Mata sai tace dallah can tafi ka bani wuri kace bacci yake....



Yaro ya fita cike da tsoron tsawar da tayi Masa,yaje ya fadawa mummyn shi, ranta ya baci sosai ga dare yayi tace gashi ba dama in fita ba da izininsa ba...ya zanyi kuka ta Fara Yi tana ya Allah ka taimakeni ya Allah ka kawo min mafita...




Itako ruky tana can ya bugawa farida ai aiki yayi tana ta mata godiya ...farida tace ba komai kedai kici gaba da kokari zakisha mamaki....







Tofah

Ki biyo ni don Jin yadda zata Kaya....



*Taku*

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻




*Story&written*



*By*



*Ummu Ameer* 💃







*Page* 3⃣4⃣










""""""Maryam taje ta duba
magungunan dake gidan Amma ba na ciwon ciki, ga yarinya na ta murkususu, ta rasa inda zata Sanya kanta, zuwa tayi ta dauko cup da ruwa ta Mata tofi aciki ta Bata ta sha.


Cikin ikon Allah sai bacci ya kwasheta alamun ya lafa Mata.

Sai alokacin ta samu nutsuwa ta Fara tunanin ya akayi Abbas ya kwanta baizo sunyi sallama ba,,,,

Kuma Bai kulle gida ba,,,?
Kuma yaki daukar wayarta ?
Sannan an aika ta koro yaro ,,,,,

Anya kuwa lfy?
Ta tambayi kanta


Tana Nan zaune tana jiran shigowarsa shiru...wata zuciyar tace kije ki gani ko lfy?

Wata zuciyar Kuma na Hana ta sbd ta fahimci tun ranar da suka fita tayi tafiyarta ta daina shigowa gidan Bata kula yaran, shiyasa itama ta fita a harkarta....sai ynx ta gane gaskiyar wadanda ke gayamata ya bi ahankali ta gane kawai zuwa tayi ta bugi hancinta,,,Kuma dake Allah na tare da Mai gaskiya Allah Bai Bata ikon aiki da Shiba ko tayi ma Bai yin tasiri...


Ko da Maryam taga har 12 na dare ya wuce tashi tayi take ta kulle gidan ta rufe ko Ina na bangarensu ,,,cike da fargaba a zuciyarta don zuwa ynx ta Fara tsoron rukayyah Bata son wane abin take kullawa ba kuma.





******. *******

Washe gari har wajen 7na safe Abbas Bai farka ba da taga Abin yayi yawa Kar asiri ya tonu shine ta tasheshi ya tashi cikin magagi alamun baccin Bai sake shi ba...sai a lokacin ta tuna ta zuba kwayar ne da yawa ...a haka dai ta takura ya shiga toilet yayi Alwala yazo Yana sallar Amma kana ganinshi kasan bacci ne Bai ishesba Yana idarwa ya Kara komawa...tace na shiga uku....karfa a gane abinda nayi,,,,





Maryam kuwa hankalinta ya tashi sosai tana ta tunanin ko lfy?

Gashi ta shirya su mufid zuwa sch.amma shiru har ynx Bai taba irin haka ba.....


Ganin 8 ta kusa tace Bari ta je ta tambaya ko lfy..


Hijab ta Sanya ta nufi bangaren rukayyah ...



Sallama taitayi Amma shiru kamar ba kowa a ciki...sai da aka kusan 5mint sai gata nan ta fito sanye da wata gown sleeping dress ta barbaza gashni kanta ba ko kunya ta tunkarota a haka..dake Saida ta leka ta ga me sallamar sannan tayi wnn Shirin ..


Ko da Maryam ta ganta ranta ya baci sosai Amma bata Bari ta gane ba, ta gaishe ta amsa mata a yatsine har da cewa wai lfy da sasssfe haka ko tashi masu gidan basuyi ba...

Maryam tace dama naji shiru ne tunjiya banji shi ba na Kira ma ba'a daga ba shiyasa na zo inji ko lfy ...


Wani kallon raini Tai Mata tace ai ba kullum ake kwana a gado ba haj.yau da gobe ya Fara gajiya da sintiri wajenki...shiyasa yai kwanciyarsa nima Kuma Naga hakan shiyafi cancanta ...Amma lau yake ba wani Abin, sai a Kara gaba ....





Maryam juyawa tayi cike da takaici zuciyar ta tana Mata radadi....


Lekawa tayi taga makotansu da suke sch. Daya da su mufid tace don Allah su tafi tare daddynsu ne bashi da lfy


Suka shiga motar suka tafi...


Zama tayi akan kujera kalaman rukayyah na dawo mata akai...tana mamakin halin maza Bata taba tunanin haka daga gareshi idan har hakane tabbas yaci amanarta ya karya Alkawarin daya daukar Mata ,,,,,




Sai zuwa kusan 10na safe Abbas ya watsake ya farka da salatin ganin lokacin da ya Kai Yana bacci ...Wanda Bai taba yin haka na tun kafin yai aure...mamakine ya cika Masa zuciya yadda akai haka t faru ....sai ga ruky ta shigo tana cewa wai me ya faru babynah tun jiya kake ta wnn baccin tun jiya?


Bai tsaya Bata amsa ba yai hanzarin shiga toilet


Itako rufe Baki tayi tana dariyar mugunta...


yayi wanka ya fito ya shirya a gaggauce tace ya kake Shirin fita baka Yi breakfast ba yace na makara me yasa baki tasheni ba kinsan Ina da abubuwa agabana ga Kai yara sch.


Tace nayi iyakar kokarina wlh Amma Ina tashinka sai ka koma bansan me ya sameka ba ..kasa ni cikin damuwa Nima.


Yace sai na dawo kawai ynx dai na makara zuwa tayi ta bashi hot kiss sannan tare da wata irin kissa da saida taso kashe Masa jiki...

Yace kyaleni in tafi sai na dawo ....tace take care baby ,,,,



Fita yai da sauri kamar zai tashi sama ya shiga wurin Maryam dake kwance kan 3seater tana ta tunane2 ko breakfast batayiba duk da motsin da cikin ke Mata kamar zai fasa ya fito .don yinwa, Amma hakan baisa ta tashi don cin wani abu ba.



Kamar daga sama taji muryarsa yana sallama tare da qamshin turarensa saurin rufe ido tayi don ya dauka bacci take yi .

Key din hannunsa yasa Yana Mata wasa a kunne
Tai saurin razana ta mike, tana ganinshi tai tsaki ta koma ta zauna yace morning wify!
Ta amsa a takaice



Yace kiyi hakuri wlh bansan me ya faru ba,tunda na dawo bacci ya daukeni sai kace Wanda yake maye ban farka ba sai kusan after 9








Dagowa tayi ta kalleshi ta ga kwayar idonshi ba karya a zancensa ta gasgata zancensa.

Amma Bata Yi saurin nuna Masa ta yadda ba, tace Allah ya kyauta


Yace Ameen!

Yace Ina su mufid din waya kaisu ?

T
ace tare da su khaleel neighbour dinmu suka tafi

Allah sarki yace!

Sai na dawo ma karasa maganar am late!
Tace Allah ya tsare hanya...
Yace Ameen ya fita





A mota kuwa yana tuki Yana ta tunani wnn lamari Anya ba wani Abin yasha ba da har yayi ta wnn baccin ...Nan ya tuno lemun ya Sha Kuma tun bayan nan Bai sake sanin komai ba...ya tuno duk abubuwan da suka faru bayan dawowar shi daga office, da irin changes din da ya gani a tattarre da ita ...

Yace ya Zama dole in Sanya ido akanta domin kuwa Yana zarginta akan faruwan hakan....


Ko da ya Isa office ya tarar da patience jindim suna jiran isowarsa, ya shiga da fara'arsa Yana Basu hakurin late din da yayi.


Cikin hanzari ya shiga ya Fara gudanar da aikinsa .








*Taku*


*Ummu Ameer* 💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻








*Story & written*



*By*



*Ummu Ameer* 💃






*Page* 3⃣5⃣










"""" Kasancewar girkinta ne ma yau din haka ta gudanar da komai kamar jiya ta tsaftace ko Ina da dai sauransu yau Kuma zobo tayi Masa bayan ta gama hadawa ta zuba kwayar a ciki Amma kadan ...





Ta gama komai Tai wankanta yau ma wata Riga ta Sanya wadda da ita ma gara babu..sai wani wando iyakar sa gwiwa Bai ma Kai ba ...ta yi parking gashin duk da ba wani yawa ne da shi ba sai ribbom da ta cika, haka ta zauna ta Sanya wani turare da farida ta Bata Wanda aka yi shi don mallaka.



Ta kosa ya dawo shiru har bayan magrib...ba Abbas ta Kira wayar a kashe hankalinta ya tashi ,tace ko dai yana wajen Maryam ?


Zuwa tayi ta leka ba motarsa a parking space ,ta zagaya ta yadda zata ji magana ta wajen Maryam ko Yana Nan taji ba muryarsa sai yara dake wasa.



Haka ta hakura taje tai sallar magrib ta sake gyara make-up din, Khadija kuwa tuni tayi bacci Bata wuce magrib take bacci.



Sai karfe 8na dare taji horn dinsa, ta leka ta window taga shine,Kuma ba inda ya zarce sai wajen Maryam Nan ta Kara Jin haushi da dai ta tuna hadin zobonta Kuma sai ta Tai murmushi tace Kai da Kara shiga sai gobe...


Cikin sauri ta zo ta jere Masa Abincin akan dining,yau kawai snacks Tai Masa ganin tana wahal da kanta Kuma ba ci yake ba..



Acan kuwa Abbas sai da ya kwashe 1hour sannan. Ya dawo ta Kai kololuwa wajen bacin rai Tai ta kwala Masa Kira "Abban Khadija" Abban Khadija " Yana jinta yai shiru ....har Maryam na cewa ka tashi kaje Kar hakan ya jawo wata matsalar yace ba inda zani sai na gama Abinda nake ...Aiko Bai je ba sai da ya gama wasa da yaransa har Saida sukai bacci ..sbd yai missing insu rabonsa da su tun jiya, itama sun Dan yi Hira sama-sama sbd har ynx Bata sakar Masa fuska ba...yana sane da ita ya kyaleta ne sai zuwa gobe tukun sai su fahimci juna ranar girkinta kenan...yai Mata sallama ya tafi cike da begenta sbd ba karamin kyau tayi Masa yau....haka nan ya tafi cike da shaukinta.




Itako rukayyah koda taga ya kusan awa daya acan ai tuni haukanta ya tashi ganin ta Kira Bai amsa ba balle ya dawo, tana ganin ya gama tozarta ta a wajen Maryam ....ai Nan da Nan ta zuciya ta shiga kitchen ta Fara wancakali da kayan dake kitchen din tana fasawa tana kuka kamar mahaukaciya tana ta sambatu "tana fadin ni zaka na wulakantawa don kaga Ina sonka, duk iya kokarin da nakeyi wajen ganin na kyautata na janyo hankalinka Amma a banza...na rabu da kowa sbd da Kai Amma kullum kokarin muzgina min kake ...ke Kuma Zaki hadu Dani ki bar ganin Ina kyaleki kina min shisshigi ba wai tsoronki nake jiba ..wlh sai na dauki mataki akanki ...haka dai taita sambatu Kuma Bata fasa zubar da kayanba hatta da falon ta hargitsa komai na falon, ga wani irin kuka da take kamar zata hadiyi zuciya ....tana tsaka da haukan taji knocking ta san Kuma shine Tai banza da shi taci gaba da farfasa abubiwan fashewa,


Yana tsaye yaji karar fashewar Abu..yace wnn yarinyar kuwa lfy take ...cigaba da kwala Mata kira yayi Amma Bata da niyyar budewa ...sai faman jijjiga kofa yake kamar zai balla, Amma ina Taki saurararsa.


Cikin matsananciyar fargaba ya Kira no daddy mahaifinta ya gaya Masa Abinda ke faruwa, daddy ya kirata yafi a kirga, sai daga baya ta dauka cikin kuka tace daddy na gaji da wnn auren kullum bacin rai ya dinga wulakantani a gurin matarsa, komai nayi ban iya ba sai ita...na...kafin ta karasa ya katseta Cikin bacin rai shut up!
Rufe min Baki mutuniyar banza da wofi kina so ki dauki dabi'ar mahaifiyarki ko? To zan zame hannuna a lamarinki matukar Baki canza ba...


Kuka ta Kara fashewa da shi ta aje wayar, tana ta maida numfashi sama sama ...karar bugun kofar ne yasa ta tashi a fusace ta je ta bude kofar ta Galla Masa wata hararar da Bai San ta iya ta ba, ganinta da yayi sai da ya tsorata sbd ta wani hargitsa gashin kanta kamar mahaukaciya ga rigar hannu daya ya fita sbd bala'i komawa tayi ta zauna tana cigaba da kuka, yabita da kallon mamaki...

Mamakinsa Bai kare ba sai da ya ga haukan da tayi a falon binta yayi da kallon mamaki itako ko inda yake Bata kallah ba, ya leka ko Ina yaga irin abinda ta aikata...


Bai tanka Mata ba yazo ya Fara tattare na fashewar, ya gyara falon, kitchen dinma ya shiga ya kwashe abubuwan da ta fasa ya zubar ya gyara wadanda zai iya ...Amma zuciyarsa a wuya take fa Ashe haukanta ya Kai ga haka dole ya dauki mataki Nan gaba baisan me zata aikata ba, shi yasa yai shiru Bai kula ta sbd in ya biye Mata a yanzu Abin bazai kyauba...


Itako ganin yaki kulata bakinciki ya rufeta takaicinsa ya Kara kamata, wato Bai ma damu da halin data shiga ba, maimakon yazo ya Fara lallshinta a'a shi ta gyara waje yake Nan ta Kara fashewa da kukan bakinciki...

Shi kuwa ko ta kanta baiyiba, daya gama gyara ko Ina yai wankansa yaje ya Dora ruwan tea ya Sha duk tana zaune. Bai kulata ba itako zuwa ynx takai kololuwa wajen bakinciki.

Tashi yayi ya shiga daki da zummar zai kwanta bayan ya kulle ko Ina.

Tana ganinsa ya shiga daki ya rufe kofa zai kwanta ...tace bacci ma zaiyi ya barni cikin wnn halin ga asarar shirinta da tayi


Sai da ta Bari ya Dan jima da shiga taje ta bude kofar taji a rufe ta jijjiga da karfi kamar zata balla kofar....Yana jinta yai shiru gashi kansa na Masa wani ciwo kamar zai rabe2 .

Da dai ta ga bashi da niyyar budewa, kitchen ta shiga a guje ta dauko tabarya tazo ta Fara buga kofar kamar zata balla ...tana fadin ka bude kofar ko na balla ta ka maidani sakarya bansan me nakeyi ba to ka bude muyita ta Kare eheee..

A lokacin karfe 2na dare ...cikin matsananciyar bacin rai ya bude kofar Bai yi wata -wata ba ya kwasheta da Mari har sau 3 yace ke mahaukaciyar Ina ce Zaki dinga yimana hauka tsakar dare?

Itako tunda Taji saukar zafafan mari a kuncinta ta zube kasa a waje ba numfashi.....



Cike da tsoro ya kalleta yaga abinda tayi ...cikin sauri ya daga hannunta yaji ba motsi ya jijjigata da karfi Yana Kiran sunanta kamat zautacce Amma shiru...





*Ummu Ameer ce💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻







*Story& written*



*By*



*Ummu Ameer* 💃







*Page* 3⃣6⃣






***** Jin Kiran rukayyan da yake cikin tashin hankali ne

Please Login or Register in order to submit comment