Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruky tayi tace zan jarraba Amma Abin da kamar wuya ...wai gurguwa da auren nesa .



Farida ta tashi tare da fadin atoh! Ya rage naki inkin bi shawara kanki ...ni dai Kinga tafiyata, ruky Tai Mata godiya ta rakata har gate din gidan sannan ta dawo tana dawowa ta hangi Abbas ya rungumo Maryam suna picture, ba yaran ahannunsu ma sbd sunyi tare dasu tun dazu. Har wani style suke sai kace masu pre-wedding pictures sunyi matuakar kyau ba kadan ba, hakanne ya Kara tunxura ruky ta kwasa a guje don bazata iya kallah ba....tana shiga Tai kacibus da Yaya babba tace lfy kuwa Yar Nan?

Ruky ko kallaonta batai ba, ta shiga dakin ta Sanya key sai faman huci take kamar wacce taga wani bala'i, don kukan ma kasa yinsa tayi duk da ta maida shi sana'a don kusan ko yaushe acikin yinsa take , Yaya babba tabe Baki tayi tace wnn yarinyar fa na fahimci ba diyar arxiki bace, kaji Ina Mata mgana ma ko ta kaina Bata bi ba, tabdijan !



Sum-sum ta fice ta koma can bangaren Maryam.


Mejego Kam da kyar ta samu ta zille da wnn pic da ake tayi yaki karewa, ga Baki na jiranta aciki, sai da wata abokiyar wasansa tace Kai kyaleta haka Nan da hoton Nan kabi ka nanike Mata tun dazu ka fakaice da hoto...yace to sa'idinawa Ina ruwanki? A barni in Sha iska...ya fice sumi-sumi dashi.



Taro Kam Alhamdulillah ansha Baki gida ya cika da mutane, wadanda ma Basu taba xuwa ba sunxo sunan twins, sunsha kayan barka, Kuma anci an sha, an tashi taro lfy.



Ruky tana can ta kulle kanta a daki ana ta bugawa Amma shiru Taki budewa, sai kusan magriba ta fito idon Nan yayi jajir kowa ya fahimci kishine ke addabarta, kowa sai fadin albarkacn bakinsa yake akanta...Basu Kara sirewa da ita ba sai da ta tazo falon cike da tsiwa ta tsaya agabansu tana fadin wlh aje a gyaran bandaki tayaya zaku shiga ku Bata min sannan ku barni da gyrara . .ta fada cike da rashin kunyar...kuma a lokacin harda Yaya babba da sauran yan'uwa , har wata daga cikinsu ta tashi zata zazzago Mata rashin mutunci Yaya babba ta ruko ta, yi hakuri bazamu biye Mata ba, kuruciya ce. ...kuruciya fa kika ce inji me Shirin yin masifar wane kuruciya ce anan bayan Saida ta gama girmanta a gida ta rasa mashinshini, shine ta makale wa Abbas, sannan zata zo tana yiwa mutane hauka. Don nasan rufarsa sukai Don a hankalinsa bazai kwaso Mana wnn shirgin ba...ruky kuwa naji an Mata tatas ta fashe da kuka ta shige daki, Yaya babba tace me yasa ba kyajin magana ne Asabe sai da nace ki kyaleta kika ki, tace kyaleni in nuna Mata ba tsoransu ake ba, Ina sane da Abinda suke yi mana, cin kashin ya Isa haka


Yaya babba janyo su tayi tace su wuce su tafi wajen Maryam mu bar Mata gidan, Asabe tace akan me gidanta ne, ko kuwa da shi aka kawo ta, Yaya babba tace ki dai taho nace ko, suka dunguma suka koma wajen Maryam,, sannan suka dunguma sai gidan yayah suka ce sai da safe don acan zasu kwana.




Abbas kuwa bayan sun tafi ya shiga wajen ruky, Yana ta buga kofa, tana ji Taki budewa ya gaji ya koma wajen Maryam.dakinsa ya shiga ya kirata sukai ta hirarsu Yana yabon kyan datai kamar sabuwar amarya...


Yace Masha Allah gaskiya anyi taro sosai don ba'a taba cika kamar haka ba, ko don sbd Yan 2 ne kinsansu da farinjini, tace lallai Kam Masha Allah, an Yi taro sosai, Kuma an Kare lfy.




Yace Allah ya kawo wasu twins din Mata, wata shekarar..ya fada da zolaya....


Tace haba dai ai na gama, haihuwa fa ba sauki ...


Yace to meye nee haihuwar, ba gashinan ba, kamar Baki Yi ba, wazece ma kece mejegon sai faman kyalli kike kina haskawa kamar zahra a cikin taurari...


Hmmmmm tace tare da tashi ta zuba Mai sauran snacks din da drinks da kuma naman da aka soya sannan ta zuba wa Maryam ta bashi in zai tafi ya Kai mata.


Sai da yayi kusan awa 2 suna ta hirarsu, sai itace ma ke tuna Masa akan ya tafi kar ruky Tai fushi...Amma sai ya basar sbd Bata San ma ynx rufe gdn tayi ba,sbd shi bashi a cikin mazan dake kawo zancen kishiya kamar yadda wasu mazan suke duk Abinda ya hada su, da daya sai ya fadawa daya, sbd a ganinshi hakan Bai kamata.


Sallama yai Mata kamar Kar ya tafi har Yana cewa shifa gaskiya ta barshi ya dinga kwana da yaransa Yana Jin duminsu a jikinsa gaskiya.



Ko da ya koma wajen ruky zuwa yayi ya tarar da gidan a hangame alamun Bata ko ina a bude yake yai mamakin hakan, shiga yai ya duba ko Ina Amma Bai ganta ba, ya Kira wayarta Bata dauka ba, yace Ina Kuma taje cikin Daren Nan haka, ya bugawa anti Salma y tambayeta ko taje tace batazo ba.

Itama Anty Salman ta tambayi mommy tace Bata zo ba, Kuma tace ko tazo ba dai gidana ba wlh, tunda na kafa Mata sharadi, Kuma ta Amince taje tunda mijinta ya finiii.


Janyo kofar yayi ya rufo gidan ya shiga yai wanka yai kwanciyarsa.

*****************


Tun asuba text dinta ya shigo tace masa na fuskanci Kora kake min da hali a gidanka, don na fahimci wani Abin ma da gayya kake yinshi, to ka sani duk halin da na fada Kai ne sanadi, Abbas bakin cikinka ya kusa sa zuciyata ta buga, duk Abinda ya faru da ni kasani Kaine sila, sbd haka Naga ya dace in baku waje kasha iska....



Yana gama karantawa Kuma sai jikinsa yai sanyi, duk da yasan ita take Sanya kanta a ciki, Abu Bai taka Kara ya karya ba, ta maida shi babba.


Reply yai Mata Yana tambayarta tana ina?


Ta bashi amsa da cewa tana gidan wata kawarta farida, shi Bai ma San gidan ba, balle farida.yace Tai Masa kwatance zai zo su tafi anjima..


Gidan farida taje tun jiya Amma Bata gaya mata gaskiyar rashin hakurinta ne ya fito da ita ba, sai tace wai ji tayi gidan ya gundure ta, gashi ba kowa shine tace zata zo ta kwana gb sai ta wuce,farida kam Sam Bata yarda da Abinda ta fada Mata ba, don tasan halin ruky rashin hakurinta ne ya Hana ta Zama, binta tayi a haka itama, suka Sha hirarsu..kasancewar mijinta Bai kasar..ita kadaice a gidan...




Kasancewar wkend ne ranar lahadi bayan Abbas ya tashi ya shirya ya shiga wajen Maryam Bai nuna Mata Bata Nan ba, daga bisani yace zaije ya dawo.

Tace Allah ya tsare hanya .

Tace Ameen.



Kwatancen da Tai Masa ya bi har xuwa gidan farida baisha wani wahala ba, kasancewar mijinta sananne ne a unguwar,. Yana Isa y kirata a waya yace y iso, tace y shigo yace a"a kawai ki fito sauri nake.



Sai ga ta sunfito da farida, tazo suka gaisa da Abbas, Amma tunda ya ganta kawai yaji Bata kwanta Masa a rai ba, vaison alakarsu da ita, Kuma Bata taba bashi lbr ta ba.


Sallama sukai Mata suka tafi, a hanya yake tambayarta Ina ta samo wnn Kuma, tace kawata ce tare mukai sch. Da ita yace Kuma ki rasa inda zakije sai gidan kawa ki kwana?

Yace karki sake plx bana so...

Tun a hanya suka sulhunta kansu bazakace ma wani Abin ya faru tsakaninsu ba.




Kuma ba Wanda yasan ma tayi yajin sbd tun jiya ba Wanda ya kuma shiga wajenta.

Ganin haka yasa ruky Kai ya fasu ...
Sai kuma aka bude sabuwar soyayyah .


*To Anya kuwa ruky zata Bari ta dore*




Muje xuwa



*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻






*Story & written*



*By*


*Ummu Ameer* 💃






*Page* 4⃣3⃣







Su ruky kwana 2 shiru an Sami yanda ake so...shiru kake ji, duk da cewa Bata Jin dadin zuwan da yake wajen Maryam ya dade, gani take tunda ta Bata girki ai ashikenan,haka dai taita dannewa, data ga Abin ba sauki, sai ta sameshi Tai Masa magana, Abban Khadija a gaskiya fa bana Jin dadin abinda kake min, tace ta bani girki, ya kuma za ai ka dinga shiga tana rike ka, da kisisina gaskiya banso, in Kuma girkin take so ai bissimillah, Amma bazata barni da wahala ba Kuma ita da rike miji ba...


Shiru yayi na wasu seconds ya dubeta da mamakin kalamanta a zuciyarsa yace ashe Bata canza halinta ba, dubanta yayi Rai a bace yace kina nufin don ta Baki girki bazan zanje ni in duba lafiyarsu ba, kawai don Kar ranki ya baci...in kin gaji da girkin ba matsala sai na koma can din ai ba wani abu bane...

Tana jin ya Fadi haka ta Fara a' a ni bance na gaji ba, a zuciyarta tace yadda nake jin dadin kasancewar sa tare Dani b zanso ya koma can ba ynx..ai Kaine sai ka shafe awowi acan kamar bazaka dawo ba,


Yace na dauka kin gaji ne da sai in barki ki huta...


Murmushin karfin hali tayi a zuciyarta tace ai sai na gama kamashi a hannu ya mance da wata Maryam tukunna...



Haka ta tsara cewa zata bi duk wata hanya domin ta ga Abbas ya dawo gareta sannan ya mance da duk wani Jin dadin dayake samu daga gareta..


*Anya kuwa*?



itama ba azaune take ba, Daman sai da aka Mata dinki, Yana warkewa ko ta Fara shiga ruwan magarya da bagaruwa, da ta fito Kuma Tai tsuguna kan garwashi à na kanumfari, ga shi tana kokarin cin duk wani abinda zai dawo Mata da Abinda ta rasa, dama ita ko ba kishiya Bata wasa da kanta, balle Kuma ynx ai sai abinda yai gaba, shi kansa aduk sanda ya koma mata sai ya mata jinjina Yana fadin ita din dabance a cikin mata, domin ko yaushe zam-zam yake jinta, shi yasa Bata wasa ko kadan da kanta, gashi ko hakan ya janyo Mata daraja ta musamman.


Yau kwananta goma Sha daya da haihuwa, Hassan ya tashi da wani irin zazzabi sai kuka yake, Abbas cikin tashin hankali yace ta shirya su yi maza su je asibiti, sbd yaga ma idon yaron ya canza kala zuwa dorawa, cikin tashin hankali ta Sanya hijab suka tafi...


Kasancewar sa likitan yara, Shima Kuma a bangaren yake direct ya wuce da su can S.C.B .U dake cikin Asibitin mallam, Da taimakon wani abokin aikinsa Dr.mahmud ya taimaka Masa wajen gwaje -gwajen Don a tabbatar da matsalar tashi, Nan da Nan akai sun gano joundice ne, yai masa karfi a jiki, sbd haka dole sai an canza jini...


Koda Maryam taji labari kuka ta Sanya tace shikenan Hassan don Allah karka tafi ...kuka take sosai Mai ban tausayi gashi ta shaku da yaron don kuwa har yafi Hussain kuzari,ita gani take bazai tashi ba,ta Yaya za ai wa jariri wani canjin jini...


Sai da Abbas ya fahimtar da ita tukun yace aikinsu ne arana sai suyi ma yara kusan goma Kuma duk su tashi garau ai juyen jinin shine samawa yaron lfy, ki kwantar da hankalinki ba abinda zai Sami Hassan dinki kinji mmn twins ya shafa Mata habarta tare da goge Mata hawayen fuskarta, ya lallabata ta samu nutsuwa ya kaita office dinshi ta zauna acan bayan an dauki jininta za'a tantance blood group dinta. Kuma sungano 0+ne shima nashi Hassan din haka.


Nan da Nan aka Basu gado Kuma don tuni an Fara Masa aikin, ita Kuma aka kaita can amenity ita da Matar dake taimaka Mata da rainon, Koda taje dakin kasa komai tayi duk jikinta yai sanyi sai addu'a take Allah ya bashi lfy ya tashi kafadunsa.


Sai wajen 11 na dare Abbas ya shigo dakin yace har anyi ba wata matsala insha Allah zuwa gobe ma, zasu tafi gida.. Alhamdulillah tace Tai wa Allah godiya.

Yace Bari ya koma gida yaje ya dauko musu abubuwan bukata da Abinci, tace to Allah ya kaika lfy, ya tafi.




Can kuwa ruky ta Kai kololuwa wajan bacin rai duk da ya sanar da ita inda zasu Amma sai ya je ya zauna, nufinsa acan zai kwana sbd akanshi aka fara haihuwa kenan, ganin har 1 na dare Bai dawo ba, gashi wayarsa a kashe...tana ta ita wlh bazai yiwu ba, ya za ai su dinga Raina Mata hankali.

Tana zaune tana mita sai gashi ya dawo don sai da ya Fara Kai duk abinda za a bukata cikin boot din motar sannan ya shigo y Gaya mata, halin da ake ciki...

Yana shigowa tace lfy sai ynx, ya fada Mata lalurar yaron Amma ko ajikinta Bata nuna damuwa ba, sai ma cewa tayi ynx to me kake nufi? Yace zan koma na Kai musu kayan da suke bukata ne, sai na dawo...zare idanuwa tayi cike da mamakin zancen nasa tace kana nufin cikin Daren Nan zaka koma, tace gskya ka Bari kawai da safe ka Kai musu ynx dare yayi....wani banzan kallo ya bita da shi ya juya yai ficewarsa ya barta Nan gurin a tsaye.


Wani takaici ne y lullubeta ta ciji yatsanta Tai kwafa ta shige daki tare da fadin zaka dawo ka sameni, sai dai ayita ta Kare yau na gaji haka ..



Koda ya koma Asibitin sai da ya Fara zuwa wajen Hassan yaga yanayin shi Kuma Alhamdulillah aiki Yana kyau sannan ya wuce ya kaiwa Maryam kayan sai da ya sa ta agaba taci Abincin sannan ya tafi yace ta dinga lekawa wajen Hassan lokaci zuwa lokaci, sannan sukai sallama yace da safe in ya Kai su mufid sch.zai taho.tace Allah ya kaimu.



Sai karfe 3na dare ya koma gida yaje wajenta zai Gaya Mata zai kwana da yaran tunda mommynsu Bata nan, duk da akwai hafsa Amma gara ya kwana da yaransa, dama haushinsa take ji kamar me, tabe Baki tayi taja tsaki, tayi komawarta daki, shi Kuma ya koma can wajen yaran duk da sun yi bacci, adakin shima wanka yayi ya kwanta bacci.



Washe gari sai da ya kusa makara sbd Bai Sami isasshen bacci ba, a gurguje ya shirya yaran shi ya masu wanka da kanshi ya shirya su tsaf, hafsa kawai break fast tayi musu, ya tafi kaisu sai tanbayarsa suke Ina mommy da su Hassan yace suna asibiti in sun dawo daga sch. Zai kaisu su gansu.



Ko da ya dawo ya shirya yaci abinci, sbd ita bayi ta yi ba, ta Hana kanta sukuni tun jiya, shi yasa tace ba zatayi ba, yaje can Maryam din ta bashi.


Ko da ya shirya zai tafi ya shiga yai Mata sallama, tace ai wlh kafarka kafata duk inda zaka Ina biye da Kai ta fada tana Shirin Sanya hijabin ma duk ba a goge ba,ko wanka ma batayi ba, ta Suri takalmin zaman gida ta Sanya ta Riga shi fita da yarinya a hannu ko wanka itama Bata Yi Mata ba, tana fadin haka kawai kun Raina min wayo ka dinga fita da ita Kuna Shan soyyayrku, ni Nan kun barni jiran gida,


Magana yake Mata Yana ki dawo, ki Bari ki shirya in zan Kai su mufid sai muje, gaba tayi ta Riga shi shiga motar, ta zauna tana surutai kamar tababbiya


Mamakinta kawai yake Anya kuwa tana d cikakken hankali? Ana ta Mara lfy tana wani shirmenta banza, ta Sanya zargin wofi a ranta, a fusace ya shiga motar ya figeta da wani mahaukacin gudu, kamar zai tashi sama, ko kallaonta Bai yi ba, bare ya tanka mata.ta gama kular da shi, ga haushin shigar da tayi don tsaf za ace house girl ce....kawai don ta tozarta shi ta shirya hakan , kwafa yayi yace in kinsan wata, ai Baki San wata ba....





Muje zuwa


*Ummu Ameer ce*💃💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻







*Story & written*




*By*



*Ummu Ameer*💃





*Page* 4⃣4⃣





*Addu oin ku sun iso gareni masoyana nagode kwarai Allah ya bar kauna* 💓💓💓




""""" Ko da isarsu Asibitin,bayan yai parking, shammatar ta yayi, yai saurin fita daga motar ya Danna security na motar yai fita ya barta a wajen, sai faman buga glass din take,shiko ko a jikinsa, direct wajen Hassan ya wuce kasancewar ba guri daya suke ba, da Maryam dinba da Dan tazara.


Yana shiga ya sameshi sai wutsil- wutsil, yake gashi garau baka ce shi akai wa juyen jini ba, zuwa yayi ya dauko shi yayi duk binciken da zai yi na tabbatar da yasamu lfy, kuma Alhamdulillah ba sauran wata matsala, yace zuwa yamma ma kawai zasu tafi.




Bayan ya gama da Hassan ya koma motar ya dauko musu breakfast ya kunna motar Yana kunnawa Tai saurin fitowa sai faman hararar shi take, tana fadin ai kome zaka min sai na bika .... Ko saurarta Bai yi ya fito da Abincin da sauran wasu ledoji ya rufe motar ya wuce can Amenity inda take, itako tana biye da shi a baya...

Shiko godiya yai ga Allah, da Bata Sami binshi cikin s.c.b.u dinba, sbd abokanan aikinshi suna wurin.

Sai sauri yake Kar ta cimma shi ta ga room din da zai shiga, Don yadda take dinnnan yasan zata iya komai a gaban mutane, sauri yayi ya shiga dakin ya rufe, dake shine ba farko, itama sai gata sai faman diri- diri take tana kokarin shiga, sai security tace ya lfy madam? Ina Zaki ta Fadi tare da tokare hanyar shiga, sbd ka'idarsu ce ba'a Bari a shiga sai 4na yamma, sai Mai jinyar kawai ko mijin.


Ruky kallonta tayi da raini tace kamarya? Sbd ita Bata San ka'dar Asibitin ba, sbd Bata zuwa Nan din, Wanda take zuwa daban.


Security ta taso pa hasile ganin irin kallon rainin da ruky take mata, tace who are you ana Miki mgn kina kokarin shiga wajen wa zaki? Na Gaya miki ba Wanda zai shiga wurin Nan sai 4 tayi aha!


Ruky tace ai sai ki Hana ni in gani kinsan ko ni wacece Zaki hanani shiga wajan mijina, ko Zaki ce baki San Dr. Abbas danbatta ba?


Security ta kalleta ta jefeta da wani kallon raini, tana tunanin Bata san matar Dr. Ba, Zatai mata karya, Kila ma house girl ce, tace a Ina kika Zama matar Dr. Bayan matarsa na ciki, babynsu ba lfy.


Ruky tasowa tayi zata shiga tana kokarin bangaje security, ita ba abinda yafi Bata haushi ganin tana Bata Mata lokaci, Bata shiga ta ga uwar da suke ba, ganin haka yasa ta zuciya, tana kokarin hambare security, itako tana ganin haka ta tattaro karfinta, ta wullah ta gefe.


Abbas tunda ya jiyo sautin muryar ruky ya garzayo d sauri gudun karta jawo Masa Abin magana, Yana zuwa ya taradda sai zagin security take, itako Tai shiru bazata biye Mata ba, sbd intace zata biye Mata sai ta ballah ta, shiyasa tai shiru ta kyaleta, shikuwa Yana ganin haka yai hanzarin karasowa yace wa security ai tare suke, tace kayi hakuri sir! Kasan dokar wurin shiyasa ban barta t shiga ba, yace no problem.



Yayi gaba tana biye da shi yasan dama bazasu barta ba, shiyasa yai saurin shiga, ya barta a baya, ynz Kuma ganin zata Tara Masa mutane yasa ya shigo da ita tunda ta Zama jaraba....Abin nata ma ya wuce hauka .


Suna shiga dakin itama ta shiga, ganin Maryam Tai ta Kara wani kyau kana ganinta kasan tana cikin kulawa d kwanciyar hankali, hakan ya sosa Mata Rai, ta dauka zata ganta cikin wani hali, shiyasa itama, Bata damu da shigar da tayi ba, sbd taga yawanci Mata in suna jinya a asibiti, shikenan sai su maida kansu marasa lfyr, wasu ko wanka ma gagarar su yake, maigida yazo ya taradda su kacha-kacha wai sbd tashin hankalin rashin lfyr...


Ita kanta sai ynx ta Fara Jin kunyar kanta akan shigar da tayi danasanin shigowa... Itako Maryam sanda taga ta shigo dariya ce, taso kufce Mata Tai saurin kawar da Kai gefe ta rufe Baki,


Mutuniyar kuwa ana hakince akan kujerar da aka tanada don Baki cike da takaici ta shigo bako sallama balle ta Gaishe su, Tai kicin-kicin da fuska, sai Maryam dince ta gaisheta, tace Khadija ammata, tana Mata wasa, ganin da tayi kamar in taci gaba da Zama zata kara wulakanta yasa tace ka tashi mu tafi, tai hanzarin fita a dakin.


Abbas yana fita yace Bari in maida matar can gida Kar ta jawo min wani Abin,don Naga ta Fara fita hayyacinta.


Tace Allah ya kiyaye hanya, yace ameen ynx xan dawo insh allah, ya fita itakuma tuni har ta Isa ga motar tun kan y iso ya bude motar ta shiga, suka dauki hanyar gida,tace kana nufin wait gida zaka maida ni, wlh nifa duk inda kasa kafa sai na saka, bazaka bige da rashin lfy Kai ta cin amanata ba...ganin Abin nata da gaske ne, yasa wata dabara ta fado Masa yace to muje in kaiki gida ki wanka sai in jira ki mu tafi ko kuwa, tace yayi! A takaice.



Suna Isa gidan ta shiga da saurin don ta hanzarta ta shirya karta Bata Masa lokaci, shikuwa mukullan gidan ya diba, tsaf ya saka Aljihu, Yana ganin ta shiga wankan ya saurin fita ya kalleta ta baya....ya shiga mota ya tafiiiii





Muje zuwa



*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻







*Story & written*



*By*


*Ummu Ameer*💃




*Page* 4⃣5⃣



""""A hanya kuwa tunanin wnn halin na rukayya yake, Yana tambayar kansa Anya kuwa Bata da wani matsala akanta kanta ko kuwa tsabar kishi ne yai Mata yawa? Haka dai yaita sake-sake akanta har ya Isa Asibitin. Bayan ya huta Daga bisani ya koma kan aikinsa.



Ruky kuwa ko da ta fito a toilet ta duba Bata ganshi ba, ta ga ya kulleta ta baya...wani irin ashar ta mulmulo, tace ni zai rainawa hankali,ni zai mayar shashasha? Lallai yau zan tabbatar Masa da bani da hankali a KISHI...


Haka dai taita buga kofar kamar zata balla daga baya Kuma ta shiga kitchen ta hau farfasa abubuwa, tana fasawa tana kuka, haka ta farfasa kayanta ta hargitsa komai na gidan kamar wancan Karan. Data gaji da haukan taga ba Mai jinta, ga yarta sai kuka take Taki sauraranta, da kanta Kuma ta natsu sbd gajiyar da jikinta yayi ga baccin da batai ba, tun jiya, daukan Khadijan tayi suka shiga daki suka kwanta.





Acan Asibitin kuwa tun karfe 4 aka sallamesu har ta dauki hassan din zuwa can inda take, suna jiran Abbas ya tashi aiki su tafi.




Sai karfe 7na yamma suka dawo gida, hakan kuwa yayi dai- dai da farkawar ruky daga baccin daya saceta, aiko da dai ta tabbatar da sune suka dawo Kuma har da Maryam, Nan ta Dora daga inda ta tsaya sai faman ashariya take binsu dashi sannan Kuma tace wlh indai Bai bude ta ba, sai Tai Masa danyen aiki, shiko Yana jinta sai da ya gama duk Abinda zai yi, sannan ya nufo wajenta, duk da cewa har ynx Bata fasa abinda take ba, na ashariya da farfasa abubuwa, Yana dumfaro wajen ya ji abinda take a zuciyarsa yace ikon Allah ita Kuma irin nata kalar bacin Rai kenan, Aiko in Bata shiga taitayinta yau za'ayita ta kare, na gaji da wnn haukan, bazai yiwuba ya fada cike da bacin Rai....



Yana Isa ya bude da mukullin dake jikinsa, tana ganinshi ta cafko shi ta cakumi wuyansa tana faman bugun kirjinshi, tana fadin na tsaneka Abbas na tsaneka, ka cuceni , ka rabani da yan'uwana, da iyayena, na biye maka kaci amanata, sai Allah ya saka min,. Bazan yafe maka ba, shidai Yana tsaye Yana ganin ikon Allah runtse idanuwa shi yayi yana ambaton ubangiji, wai yau shine yake auren irin wnn matar wadda Bata da tarbiyyah, Bata San daraajar aureba, A fili ya furta Allah kaine ka jarabceni ya Allah ka bani ikon cin jarabawarka....


A lokacin kuwa ita ta nufi kitchen tana wasa wuka, wai gara ta kashe kanta ma ta huta da wnn bakin cikin...Jin karar wukar ne ya maida hankalinshi ga Abinda yake ji a guje ya karasa ya sameta ta hakinkance tana wasa wukar ta dauka kenan zata aza bisa cikinta, yai saurin cimmata, ya anshe wukar da karfi,ya zabga Mata Mari a kumatu, Nan suka hau kokawa, tana kokarin amsar wukar tana kabani na kashe kaina sai ka huta da jarabata, tunda na zame maka jaraba, ganin ta gama fita hayyacinta yasa ya janyota ta karfi ya jefata cikin daki ya kulle dakin ya dauki khadija, ya kaita can wajen Maryam, sai faman huci yake Maryam na tambayarsa lfy?

Please Login or Register in order to submit comment