Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

3,
Yana zaune a unguwar hotoro GRA.

Daddy ya Yana da nutsuwarsa da girmama mutane, Nan ya amince Masa da ya bashi rukayyah. Allah yayi Miku Albarka.
Ameen! Cewar Abbas.


Abbas yaji dadin ganawa da mahaifin rukayyah, sukai ta yabon shi shi da Nasir, har Yana ce Masa
Kayi dace da sueuki nagari.

Nan suka tafi cike da farin ciki.

Momy kuwa da taji labari kamar zatai HAUKA,
Da kyar akai ta lallashinta ta akan ta amince ba'a jayayyah da Abinda Allah yayi.

Ta Amince akan zata kafa Masa dokoki akan yarta, kafin aauren.


Ta saka aka kirawo shi akan cewa bazai hada ta da kishiya ba Kuma xata dole zaibi Al'adar su ta Yan maiduguri duk Abinda ake na Al'ada sai yayi, Kuma ita zata nemo irin gidan da za'a saka yarta a ciki.


Bai Musa Mata ba duk da a zuciyarsa kawai daurewa yake Yana karfin halin bin ta Amma tuni ya gama surewa da halayyar surikarsa, don dai Yana kaunar Rukayyah ne, Amma a zuciyar sa kan Sanya Masa shakku akan abinda zai iya biyo baya duk da ya yasan ita rukayyah Bata da wani Hali na kyama.





Wannan kenan




Ki biyo ni don sanin waye Abbas?




By

Ummu Ameer
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
KISHI KO HAUKA
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€






Story & writing

By

Ummu AmeerπŸ’ƒ








Page5⃣





Abbas dan danbatta ne dake a jihar kano, haifaffen can ne, mahaifinsa Mallam muktar da mahaifiyarsa haj. Binta, duk yan danbattan.



Sai dai tin Abbas yana d shekaru 5 a duniya mahaifinsa y bar duniya ya rasu, ya bar haj binta da yara 5 maza 2 mata 3.




Da sadiya itace baba, sai karima, sai Fatima, Sune matan, maxan kuma Abbas shine babba sai mustapha, autan kenan.


Mallam mUktar kafin ya rasu bashi d wata sana'a saita kiwon shanu, yana fita da shanunsa kiwo. Suna d Dan rufin asiri daidai gwargwado, matan bai saka su a makarantar boko ba sunyi dai na addini dai dai gwargwado.

Amma yaci burin yaransa maxa zasuyi karatu boko. Abbas yana pri.1 Allah yaima Mallam muktar rasuwa, inda matan kowacce tana dakin mijinta.

Haka haj. Binta ta tsaya tsayin daka ta jajirce da tarbiyar yaran nata da kuma burin cikawa Mallam burinsa na yin karatu.

A alokacin da y gama karatun sakandire alokacin ne ya koma gdn cousin dinsa Wanda yake a matsayin yayanasa da Mallam d babansa uwa daya uba daya, shi yayi karatu boko mai zurfi, yana da matarsa Amina d yaransu hudu, habibu da bashir d sadiq, sai karamarsu Asma'u, a unguwar hotoro.


Tin rasuwar Dan uwansa yaso y karbi Abbas d mustapha a wajen innar, amma fur taki tace abin Sai yai mata yawa gashi ba Mallam kuma n yara haka ya hakura Ya bar Mata su, amma yana zuwa lokaci zuwa lokaci yana musu Alkhairi.


A wani zuwa d yayi alokacin jarrabawarsu t fito y samu kyakkyawan sakamako, shine ya nemi Alfarmar inna ta barshi y tafi da shi domin ya samo mai admssion hakan kuwa akayi tare suka tafi da shi.


Nan da nan ya samu admission a A b u zaria, Inda yake karanta medical doctor, Ya maida hankali sosai kan karatunsa ko yaushe cikin karatu gashi kuma da hazaka yai fice a makarantar "Dan boko" Wasu friends dinshi Ke kiransa sbd son karatunsa.


A can bangaren inna ko dama tana gama d hawan jini kuma in ya tasar mata kamar bazata yi ba, wani tasar Mata da yayi wajen wata guda tayi asibiti har tasa mustapha ya kira Mata Abbas a waya tai ta yi masa wasiyyah da ya kula d dan uwansa ko bayan ranta domin tana jin ciwonta ba na tashi bane, hankalinshi ya tashi sosai domin yana jin innarsa a ransa domin mace ce mai hakuri da juriya da kaunar yaranta ta su ajikinta ita dai burinta tagansu cikin farinciki ko yaushe.


Kafin ya iso inna tace ga garinku' hankalinsa ya matukar tashi da rasuwar mahaifiyarsu, nan sukai ta kukan rashin inna aka rasa mai lallashin juna shi da mustapha.


Haka aka dauki gawarta zuwa gida aka kaita makwancinta na gaskiya, bayan share zaman makoki na bakwai Yayan nasu yace mustapha y shirya su tafi, babbar yayarsu wato sadiya taso a barshi a gurinta amma yace tai hakuri zai dinga kawo su lokaci xuwa lokaci.




*************************
Bayan tafiyarsu ne shi kuma Abbas y koma school, amma duk ya canza bashi da abinyi said kika abokan shi suyi ta lallshinsa suce addu'a kawai zaka dinga yi mata mai makon kuka.

A kwana a tashi har ya dangana ya fawwala ma ubangiji, amma yana Mata addu'a sosai.

Haka rayuwa ta dinga tafiya, idan anyi hutu y koma gdn yaya sule, suna zaune cikin walwala a gidan domin Ha Amina mace ce mai kirki da mutunta mutane ta dauke su kamar ita ta haifesu ba abinda suka nema suka rasa.


A kwana a tashi har Allah yasa y kamala karatunsa, ba tare d bata lokaci ba kasancewar kwarewarsa a fanninsa yasa y samu aeki a hospital din da yai practical.
Akth. Aminu kano taaching hospital kano, a fannin yara". peaditric".


Shikuma mustapha a alokacin y shiga buk Bayero university kano yana karanta geography.

Ku dai biyoni don jin labarin
KISHI KO HAUKA....










By


Ummu AmeerπŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
KISHI KO HAUKA
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€





Story &written

By


Ummu AmeerπŸ’ƒ




Kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu.. Uxuri ne yai yawa.





Page6⃣



Akwai wata rana Abbas yana hanyar sa ta zuwa wurin aeki, a titin maiduguri road Wasu yammata zasu tsallako Titi shi kuma yana y danno motarsa ji kake 'kiiiiiiiiiiiii" y sautin taka burki sakamakon wadannan yammatan da suka tsallako, jira suka su ji motar ta bugesu, sun makale juna sun rufe ido har ya fito daga motar y karaso inda suke basu sani ba su dai sun Riga da sun saddakar.




Qamshin turarensa ne ya doki hancinsu tare d min motsin mutum sukai hanzarin bude idonsu, a lokaci daya, shi dariya ma suka bashi, ganin yadda suka kankame juna cike da tsoro, amma azahiri a fusace ya fito daga motar domin sun saka shi a fargaba don baiyi tunanin motar bazata taba su ba, Allah ne kawai ya kiyaye.

Kallonsu yayi tare da cewa ba kwa gani ne kuka tsallako, kuna ganin mota ta taho?

Daya daga cikinsu wadda kana ganinta tafi dayar razana tace don Allah kayi hakuri wlhy bamu kula ba shiyasa.. Itama dayar ta bashi hakuri. Shi kam tuni hankalinsa yana man wadda ta fara masa magana tun da ta fara magana ya ji sautin maganar tata ta shige shi a take yaji wani yarrrrrr, saboda zazzakar muryar ta, dubansu yayi yace ba komai amma don Allah ku dinga kula in zaku tsallaka titi kunji.

Toh mungode suka fada a lokaci guda tare da rike hannun juna, har sun fara tafiya yace makaranta zaku je ko, suka eh!

Yace to in ba damuwa ku shigo na sauke ku.
Lokaci guda suka kalli junasu da alamun tambaya,

A'a mungode xamu samu Dan sahu ynx, ba yadda bai yi ba kememe suka ki shiga ba don komai ba Sai nasihar mafinsu kan hana su shiga motar Wanda basu sani ba.

Haka ya hakura yace wadda ya kurama ido wadda ta fara bashi hakurin ta bashi no. Ta fiir taki Sai kawartata ce ta bashi, yace kunki yadda na sauke ku a school ko? Kunga hanyace tunda naga f. G. C zaku da idan nai dropping naku Sai nawuce office.

Tace ba komai wlhy mungode ynx xamu samu abin hawa, haka ya hakura sun rabu akan zai kira no.



Maryam da zainab kawayene, a unguwar tarauni gidansu wajen kasuwar tarauni dake a jihar kano, gidansu kusa da kusa ne, kawayene kuma aminan juna school dinsu daya, wato f. G. C kano dake unguwa uku, nan suke zuwa suna final year a halin yanzu suna xana waec ne.

Akwai shakuwa mai karfi a tsakani domin kullum in basa gidan su zainab to suna gdn su maryam.

Basu kai 18 ba a shekaru, maryam doguwa ce ba can ba tsaka tsakiya tana da dan haske amma ba sosai ba, yana da kyawu dai-dai don Sai ka yi Maya kallon tsanaki zaka fahimci irin kyawun nata, tana da hanci tare d Dan karamin Baki kamar an dasa mata, Sai fararen idanuwata sexy eyes in ka kalli idanuwan Sai kayi tsamanin barci take saboda yalwar gashin idon da take dashi wato "eye lashes ga zazzakar muryar in tana magana kamar me rera waka..
Iyayenta duk yan Asalin garin kano ne kuma mahaifnta da mahaifiyarta auren xumunta ne cousin's ne.

Alh kabiru ma'aikacine a WRECA, manager gidan ruwa ne, mutumin arxiki ne shima yana zaune da kowa lfy kuma y iya mu'amula da jama'a.

Ummi shine sunan da suke kiran mahaiyarsu suna da yara 5, hudu maza namiji 1.

Sun bawa yaransu Tarbiyyah sosai don yaran kam a unguwar har kwatance ake da su a unguwar wurin tarbiyyah, da girmama na gaba, suna zuwa islamiyyah don ko waccensu kafin suyi candy suke sauke qur"ani mai girma.

Aisha ce babba, wadda suke kira da hanan sbd sunan kakarsu t wajen uba taci sai Amina itama Amira ake kiranta, sai maryam itace ta uku said hafsa sai autan ummi khaleel.
Suma yaran sun taso da matukar kaunar yan'uwansu domin in suka ga daya cikin damuwa duk sai hankalinsu y tashi.

Alh kabiru yana da rufin asiri gwargwado mutum ne mai xuciyar yi akwai wadatar zuci.
Ya aurar da yara biyu aunty hanan da aunty Amira, sai maryam da take daf da kammalawa secondary sai hafsa tana junior section, said auta dake primary 3.
Alh kabiru mutum ne mai ra"ayin karatun boko domin yaransa ma sai sun kammala karatun jami'a yake aurar da su.

Maryam kuwa a halin ynx masoya sun mata caaaa da xarar ta fita to ba'arasa maau kyasawa amma ko kadan bats bash fuska, duk da shi a tsarin mahaifinta bai basu damar saurarar samari ba saboda karatun da Ke gabansu.
Duk da dai dokar tana neman faduwa a kan maryam saboda yawan Samarin dake sintiri akanta, tana da farin jini ne sosai, ganin maneman auren nata kowanne da gaske yake kuma direct wajen iyayenta sun neman ixini shi kuma ya basu hakuri akan cewa karatu zatayi, har ya fara jin kunyar fada musu hakan.

A haka ne har suka hadu da Dr.Abbas, a wajen tsallaka titi, kuma tunda yai tozali da ita yaji ya kamu da kaunarta, kuma bai taba soyayya da wata mace ba.

Tunda ya je office yaje office ba abinda yake said daman tunanin maryam, Wanda sai ynx ma yake tuna bai tambayi sunan ta ba, dukNo da dai ya amshi no.
Nan take yai dialing no. Yaji "switch off"
Nan ya tuna fa Ashe school fa suka tafi shi yasa wayar akashe...




By

Ummu AmeerπŸ’ƒ
: πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€



*story*& *written*

*by*


*ummu Ameer*πŸ’ƒ





Page7⃣




Bayan su maryam sun dawo gida daga school ne, tana zaune tana cin abinci, wayarta ta hau ringing.

Bakuwar number ta gani had xatai picking sai ta fasa, saboda ba kasafai take amsa no da bata sani ba, haka wayar tai ta ruri har ta gaji daga karshe ma tasa ta a silent.

Amma a xuciyarta tana zargin wannan mutumin da ya kusa kadesu wajen tsallaka titi, da ya fado Mata a rai sai ta dinga jin faduwar gaba.

Amma itama haka ta wuni tana tunaninsa tare da kwadayin son Kara ganinsa kuma cikin ikon Allah shine kadai a cikin masu sonta take jin wannan yanayin akansa.
Har barci yai awon gaba da ita.

*************************
Bangaren Abbas kuwa yinin wannan rana ya kasa samun nutsuwa so yake ya sake jin zazzakar muryarta tare da sake ganin kakkyawar fuskarta, haka ya wuni duk ya canza Hatta da friends dinshi sai da suka tambaye shi KO lafiya take yace ba komai.

Haka ya hakura ya koma gida cike da rashin samunta a waya, gashi yai rashin sa'ar tambayar kawarta nomber ta.




Washegari zainab ce a gidansu maryam, tai sallama ta hadu da ummi a kitchen tana hada breakfast ta tsuguna ta gaisheta, '
ummi Ina wuni'
Lfy lau zainab
Ya ummantaki take
Lfy lau wlh tace ma a gaisheki. Ina amsawa cewar ummi, ki shiga tana ciki mutuniyar taki tana shiryawa.
To ummi!

Tana shiga ta same ta adaki a gefen gado tana kokarin Sanya safa akafarta, oh! Maryam kullum nazo sai na jiraki kinsan yau paper safe muke da shi kuma kinsan halin invigilator's din nan basu da kirki in suka ga anzo late suyi ta embarrassing din mutane.
Maryam dai said dariyar masifar zainab take, tace to haj. Fada yi hakuri Ai na gama breakfast dinma idan ma dawo naci, ta dauki Jakarta sannan ta day wayarta daomin ta kasha, sai ta massage ya shigo kamar haka


"Assalamu Assalamu, Da fatan min tashi cikin koshin lafiya? Na kira ki jiya kin ki ki picking, I think KO don Baki san number bane, to Abbas ne Wanda kuka hadu da shi a hanyar ku ta zuwa school, don Allah kiyi kokarin amsa kira na idan na kira, Domin isar miki da wani muhimmin sako.
Ngd daga
Daga Dr. Abbas Danbatta"

Nuna ma zainab wayar tayi ta karanta, karbar wayar tayi ta kashe tace muje ma karasa maganar a hanya mun yi late, fitowa sukai daga dakin suka yi wa ummi sallama tace bazaku tsaya ku karya ba, maryam tace said mum dawo ummi wlhy mum makara, tace to Ai shikenan Allah ya bada sa'a sai kun dawo!
Suka amsa Amen!
Said min dawo.

Haka suka tafi a hanya ne maryam ta gaya Mata kiran da Abbas yai mata bata daga ba, tace gara na ja masa Aji! Maxa said da aji,
Zainab tace in aka ja da yawa ai ya tsinke. Don na fahimci wannan bawan Allah ya samu waje a zuciyarki, murmushi Tayi tace ba haka bane kawai dai Ina jin faduwar gaba a duk sanda ya fado min a rai, zainab tace sonshi kike yi,
Maryam tace daga faduwar baba sai so?
Alamun su ne AI, cewar
Zainab, tace amma don Allah in ya kiraki ki dauka jan ran yayi yawa.
Haka sukayi ta hirarsu har suka isa school din.




***********************
Bayan sun dawo zainab bata tafi gida ba sai da ta tabbatar da maryam ta amsa kiran Abbas, Domin suna kunna wayar kamar jira yake a kunna kiransa ya shigo.

A kunyace take wayar kasancewar wannan ne karo na farko da ta fara yin waya da saurayi, anan yagaya Maya abinda me ransa kuma shi da gasket yake ya kuma nemi izinin zuwa ya fara ganawa da iyayenta, ta amince masa, sun Dan taba hira daga karshe yace ta bawa zainab, suka gaisa tare da yi mata godiya don yasan da taimakonta a yiwuwar al'amarin.
Sunyi sallama Akan gobe zai gana da iyayenta.




Washe gari Abbasa ya gana da iyayenta tare da neman izinin zuwa wajen maryam. Ton fah! Abinda Abban maryam ya furta a zuciya kenan domin wannan ba shine Karo ma farko ba, amsar da yake bawa sauran *ba yanxu ba* amma tun shigowar bawan Allah nan yai man kwarjini, kuma shi kanshi ya fara kunyar su Akan hakan, yai doguwar ajiyar zuciya, yace mallam Abbas ko?
Ae haka ne.
To ba komai na baka izinin zuwa in had da gaske kake kuma azahirin gaskiya ire-irenku sunzo min da irin wannan batu amma amsa daya nake basu karatu xata yi yanxu ba aureba, har na fara jin nauyin gaya musu hakan, kasancewar duk yan'uwanta sai da suka kammala karatun jami'a nake aurar da su.
Amma inKa amince zaka barta tayi karatu to ba Matsala.
Abbas yace Abba ba Matsala indai wannan ne damuwar ka, domin nima Ina da ra'ayin karatun.
Yaji dadin kalamansa soaai yai masa addu'a tare da fatan cika Alkawari. Sukai sallama ya tafi.

Abbah ya yaba da nutsuwar Abbas Sosai gashi da kwarjini da kamala.
Ya zayyana ma ummi duk Abinda ya faru tsakaninshi da Abbas itama taji dadi sosai Domin bata son wannan ra'ayin yarinya sai ta gama karatu ai aure.
Nan ummi take tambayarshi to kaji ra'ayin yarinya ne?
Yace to ai ita ta bashi izinin zuwa.
Murmushi tayi tace ai zance ya kare.

Itako daman tana nan alabe tana Jin hirar su ummi, tana ta fargabar kar Abbanta ya hana shi xuwa kamar yadda ya saba, jin hirar iyayen nata ya sanya ta farinciki,
Had kanwarta hafsa tana tambayarta anty maryam wai me ya faru ne naga kina ta farinciki?

Ba komai hafsa Ina murnar gama paper mu na karshe ne,
Hafsa tace to Allah ya bada sa'a.
Ameen! Inji maryam


Tin daga nan soyayya ta kullu mai karfi tsakaninsu magana har ta kai ga magabata sun shiga maganar anyi "baiko" sosai suke junansu.




An Sanya ranar aure, ranar aure wata uku masu zuwa shiko Abbas ji yake kamar sun yi masa yawa, yana matukar jinta a ransa gashi da tsananin kishi, in suna tare KO tari tayi kada kaso kaga tashin hankali a wajensa.




*by*

*ummu Ameer*πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€



*story&written*

*By*

*Ummu Ameer*πŸ’ƒ




Page8⃣




***shirye shiyen biki ake tayi, domin saura sati biyu kenan, ango saboda doki tun ya rage 1month, biki ya aiko ma amarya invitation, shi ji yake kamar ya janyo ranar.

An kawo lefe akwatuna 2 set pink&blue, an zuba kaya na gani na fada aciki komai yayi sai fatan Alkhairi ga ma'auratan.
Maryam kuwa ta shiga busy, domin kullum gyaran Jiki na amare take zuwa gidan wata hajjagana dake da zama a unguwar zoo road tayi fice wajen gyaran amare.
Aikuwa amarya tasha gyara Jiki sai kyalli take, yadda Kasan fatar jarirai, ango kam duk ya Kara susucewa akan amaryar tashi.


*************************
Yau saura satin daya a daura aure duk sun gama rabon invitation cards da taimakon ango amarya ta kaima duk friends dinta invitation domin cewa yayi bai yarda garin raba I. V ba amaryarsa ta kode ba sannan a gane masa mata, duk gidan da ya kaita sai ya jira ta fito sannan su tafi wani wajen kuma, amma duk fitar da Suke da zainab suke fita, tare suke gudanar da shirye-shiryen bikin.


"""Bangaren amarya kuwa tuni an mata jere a gidanta dake hotoro amma da taxara tsakaninshi da gidan yayan shi, shi ya gina gidanshi gidan ya tsaru ba laifi amma falo ne babba, sai kitchen a falon da kuma 3 bed room sai kuma farfajiya wadda in ka shigo gate din gidan zaka gani wacce zata dauki motoci biyu. Ba wani girma ne da shi sosai ba amma ya tsaru abin sai Wanda ya gani, wajen dining din tafi daukar hankali wani decoration da akayi da wani labule mai duwatsuna ga wata cupboard a gefe an jere plates da cups, duk wani glass cups da tea cups har da roses guda hudu daya biyu a sama biyu a kasa har da wani colour Daga cikin cupboard din dake bayarwa a ciki daga sama da blue da pink da kuma red, daga kasan dining din kuma an sa carpet purple n white har kujerun suma purple ne hatta da fentin falon ma haka yake, gida yayi kaya sunyi masha Allah.


A yaune dandazon jama'a aka shaida daurin Auren "mukthar usman Danbatta da kuma maryam kabir Muhammad"
Kada kaso kaga ango Baki yaki rufuwa friends dinshi na tsokanarshi, har cikin gidan suna shiga akai musu pictures da iyayenta amarya da amaryar tare da kawayenta, tayi kyau ba kadan ba, domin kwalliyar da akai mata tayi mata kyau sosai domin kwalliyar ta canxa mata kama kamar ba ita ba, gashi da ta gifta wani daddadan qamshi Ke tashi irin na turara jiki dinnan.

Bai bar gidan ba sai da ya samu ganinta yana shaida mata wai Dama su tafi yanzu tunda an daura aure daga baya azo ganin amarya? Ko babynah ya wani maze a dole shi da gaske yake, aikuwa wata dariyace ce ta kufce mata, har saida wushiryarta ta fito, tace haba husby! Ka fiye gajen hakuri duka awa nawa ya rage mu kasance tare a gidanmu, husby, din da ta kirashi ne ya Kara narkar da shi domin ji yayi kamar itane ta hallici kalmar saboda dadin sunan, dubansa ya kai ga hannunta da yasha jan lalle da kuma Baki zanen yayi matukar kyau yace muga hannun, ta boyeshi cikin mayafin data yafa, kwatsam sai ga zainab tace ohhhhh nan kula taho kuke soyewa hakane daman in asking yaxo gaban goshi tafi zafi dama, ango duk kunya ta kamashi yana soda keya yace to baby sai na kira ki take care! Ya fada mata tare da kanne mata Ido daya...
Ya tafi wajen friends dinshi dake jiranshi a waje, suma haka suka yi ta masa tsiya, daga nan suka wuce reception.


Ana ta gudanar da shagalin bikin cikin farinciki da kwanciyar hankali, Amarya tasha kayan gyara abin ba magana sai turarrata akeyi da turarukan qamshiiii.



Da misalin karfe5pm na yamma motocin daukar amare ta iso, ciki har da ango, wai shi da Kansa zai dauki amaryarsa, tunda daga kan kai kudin aure har kai lefe shi yake kawo su, sai ya jira a wajeπŸ˜„


An shirya amarya cikin wani tsadadden leshi dark blue, ya masifar yi mata kyau dinkin ma ya dace da jikinta taui kyau sosai, an turareta da da kayan qamshi, yan uwan iyayenta da iyayenta sun mata nasiha da kuma hakuri da rayuwar aure domin shi aure hakuri ne gabadayansa, sun mata nasiha mai ratsa jiki ta shigeta sosai sai kula take, an kaita wajen mahaifinta shima yayi mata nasiha daga karshen yace nasan ki da biyayya ba abinda kika taba yi mana ina fatan ki dore ahaka, ya kare da Sanya mata Albarka a rayuwar aurensu nan ma kukan taita yi da kyar aka dauketa a wajen, ummi ma daki ta boye tana ta kuka har kannenta na tsokanarta wai batai wa sauran ba.

Kanwar Abba ce ta hana Abbas daukar maryam tace ita zata kaita a motarta su debi kawayen amarya, haka ya hakura ba don ya so ba.


Saida aka sata Tayi addu'a kafin tashiga tare da shiga da kafar dama,tsarin gidan ya burge su sosai kuma sun lura da canja tsarin jeren da akayi, kuma wannan din yafi tsaruwa, an kai amarya har dakinta suna manne da zainab sai faman Kukan rabuwa da juna suke, da kyat aka lallashesu, sannna aka kara yima amaryar make-up kasncewar duk ta bata da kuka, aka Kara fesheta da turaruka, yayyenta ma sun mata fada sosai da kuma wayar da ita akan zaman aure.

Duk an watse daga amarya sai kawayenta yan siyan Baki, ba dadewa sai ga angwaye sin rako ango da ya matsa musu su taho tun daxu suna ta mai tsiya Akan rawar kan da yake akan amaryarsa,

Ba tare da bacin lokaci ba an siya Baki Alan 50,000 abokan ango suka debi kawayen amaryar domin maidasu gida.

Ango kam sai da ya tabbatar da ya kulle ko Ina na gidan sannan ya shiga wajen amaryarsa, tura kofar yayi tare da sallama.......




Ku biyoni domin
*yanzu aka fara*



By
*Ummu Ameer*πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€

*story&written*


By

*ummu Ameer*πŸ’ƒ




*JUMU'AT KAREEM 2 OL MUSULEEM*


*Allah ya bamu Albarkar wannan rana Ameen*

*Ina jin dadin comment dinku Allah ya bar zumunci*🀝





Page9⃣



Sallama yayi bai jira amsawarta ba ya nufeta cikin sauri ganin kukan da takeyi dago fuskarta yayi fuskarta duk ta jike da hawaye,
Yace" baby why are u crying?
Ba kyason ganina?
Girgiza masa kai tayi, yace to "why"
Ni gida zanje.. Ta fada cike da shagwaba, sai alokacin ya gano kukan rabuwa da gida takeyi, lallashinta ya hau yi yace ai zasu dinga zuwa akai-akai, ba wai ta rabu da gidan bane.
Nan ta saki fuska tana murmushi, yace yawwa baby ko kefah, fita yayi daga dakin kitchen ya nufa ya dauko fresh milk tare da kazar da ya siyo ya dauko plate ya Dora tare da cups guda biyu ya nufi dakin ya ajiye kan carpet din dake tsakiyar dakin ya umarce ta da tayi alwala suyi sallah, tashi tayi duk jiki a sanyaye ta nufi toilet din dake dakin ta yo alwala, bayan

Please Login or Register in order to submit comment