Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne yake sama-sama, kamar zai dauke, yace tun yaushe?tace tun bayan tafiyarka, yace ta ta shirya su tafi Asibitin.


Komawa yai wajen Maryam ya shaida Mata zai kaita asibiti Bata da lfy,tace Allah ya sawwake ,sai kun dawo!

Ya shirya ya fito da motar tare suka tafi da Yar aikin ta rike Mata yarinyar, suka wuce Asibitin da take zuwa.


Kasancewar Asibitin bashi da Wanda ya sani shiyasa suka dauki lokaci kafin a dubasu, ko da aka dubata sun gano jininta ne ya hau sosai har Dr, na tambayarta me ta Sanya a rai har ya janyo Mata jininta yai irin wnn hawan gashi ba wani shekaru ne da ita masu yawa ba, fada yai Mata akan ta rage tunane-tunane, shima yai wa Abbas din fada akan a dinga kiyayewa don Allah, sannan suka saya magunguna suka kama hanyar gida, shima a hanya har nasiha yai Mata akan ta rage Sanya wa kanta damuwa, ba komai ne yake Zama damuwa a rayuwa ba, Amma ke Abu Bai Kai ya kawo ba, ki maida shi gagarumi a wajenki, ki daina plx, ki dinga yin hakuri da rayuwa ki daina wahalar da zuciyarki.


Tace duk abinda ya sameni Abbas kaine, kullum kokarin cuxguna min kake, yace a'a kike dai cuxguna ma kanki, duk yadda zanyi in kaucewa abinda zai shiga hakkinki Ina yi, Amma bakya gani...



Tace ai shikenan Basu koma gida ba, sai 3:30 na dare, Koda suka Isa ma Bata barshi ya koma can ba, sai wani Nishi take tana langabewa, ga patient, hakan yasa ya bita gidan yaita kwantar Mata da hankali, da Kuma sanyata Tasha magungunan, sannan yai Mata sai da safe, a lokacin har 4na asuba tayi.


Itakuwa Yana fita ta tashi tana murnar yau tayi nasarar ruguxa musu wnn daren, Daman a zahiri rashin lfyr karya take, sai Kuma gashi an aunata jini ya hau, tace Daman indai a irin wnn lokacin ne, zan dinga auna b.p ai wataran ma sai zuciyar ta buga..sbd ba abinda yake tayar Mata da hankali kamar Daren da ba na girkinta ba, tana dorawa kanta wahala....

Tace yau nai wining, Maryam you missed Dix night...ta fada tana murmushin mugunta.

Koda ya Isa Daman ya rufe gidan ta baya, shiyasa ma Bai tsaya knocking ba, ya bude ya shiga, har an fara Kiran assalatu, Yana shiga dakin ya tarar tayi nisa a bacci, Bai tasheta ba, ya shigo toilet yai wanka, sbd shi ka'ida ne inda ya dawo daga asibiti, Wala inda yake aiki ko wani sai ya yi wanka yake samun nutsuwa ya dauro Alwala ya Fara gabatar da nafilfili, sannan daga bisani ya wuce masallaci.

Itako tin shigowarshi tana ji, Tai pretend kamar tana bacci..

Yana fita ta tashi Tai wankanta Tai Alwala, tazo Tai kwalliyar cikin doguwar Riga na material , ta shiga gudanar da Ayyukan data Saba yi..Koda ya dawo Tai Masa sannu da zuwa yace shine kikai baccin ki Baki jira na dawo ba, tace na jiraka kasan bacci barawo bansan sanda ya saceni ba, Bata nuna Masa damuwarta ba, na Daren da ya Kai basu dawo ba, har ma tanbayarsa tayi ya Mai jikin yace da sauki, yace b.p dinta tane yai high, tace Allah ya sawwake...

Tace in na Bari ya gane Raina ya baci,. Ai ta samu abinda take so, don tasan da gayya ta bijiro da fitar, tuni ta gane nufinta.


Shiko sai cizon yatsa yake na missing din wnn Daren gashi yau a gidan ruky yake, zuwa lokacin kuwa yara tuni sun tashi daga bacci, itako ruky ta sanya idanuwa da kunne taji bala'in maryam, kamar yadda ita ta Saba, amma shiru kake ji, Abin Bai Mata dadi ba, ba haka taso ba, da safe ma ya shiga ya duba ya jikin tana Jin shigowarsa ta Kara wani langabew tana Nishi sama-sama, yai Mata sannu sannan yace tayi breakfast ta Sha magungunan tace tohh!


Komawa yayi breakfasat ya shirya fita office, har kofar ta rakashi kamar yadda ta Saba, har zai tafi ya dawo yai Mata rada a kunne, duk yadda Nima naso inji banji ba...sai dariya kawai Naga tayi shikuma ya kanne Mata ido, tai Masa Allah ya kiyaye!
Yace ameen my sweet wify..

Ta koma cike da nishadi a ranta,da alama taji dadin radar da yai mata.




Shima zuciyarsa fal da nishadi, har yayi nisa ya mance Bai shiga yai wa Yar rigima, sallama ba, sai kawai ya dauki waya ya kirata ta yace Tai hakuri ya makara shiyasa Bai shigo ba..bataji Dadi ba Amma ba yadda ta iya tunda yau itace ma da girki, tace Allah tsare sai ka dawo.yace Ameen.




Duk da ba yadda taso abin ya kasance ba, Amma duk da haka taji Dadi sosai, wnn ne yasa ta ware tana cike da farinciki a ranta, ga shi Kuma yau oga nata ne!


Hakane yasa ta zage tana ta shirye-shiryen tarbarsa, don itama yau shiri take na musamman tayi koyi da Maryam, an gama shiryawa tsaf ana jiran dawowar yallabai...







Muje

*By*


*Immu Ameer* πŸ’ƒ


πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»






*Story & written*



*By*


*Ummu Ameer* πŸ’ƒ





*Page* 5⃣0⃣





"""""Sai bayan magriba ya dawo ya shiga wajen Maryam daga bisani ya dawo gidan ruky, da fara'arta ta tarbeshi, yace ya jikin tace da sauki yace kin Sha maganin tace eh!



Bayan ya gudanar da duk abinda ya Saba yi, ta kawo shi dining, ya Dan tsafura Abincin yace ta kawo Masa tea yasha, Yana Sha suna taba Hira, Khadija na hannunsa ita Kuma sai sai daukansu take pictures , sbd ta samu ta Dora akan dp dinsa don Maryam ta gani, ta zata tata kawai ake wa haka...



A wnn ranar dae sun kasance cikin walwala da farinciki dama ita ke Bata zaman, sai ana zaman lfy ta bujuro da rigimarta,


Amma a zahirin gaskiya hankalin shi na kan Maryam duk kewarta ta dameshi, bare da yaje sallama kusan kasa controlling din kansa yayi, haka Nan ya dawo da matsanacin kewarta...


*********** **********

*UNFORGATABLE DAY*😭





Washe gari ma sun tashi cikin farinciki, ya gama duk Abinda zaiyi ya mata sallama yace zai fita daga nan zai Kai Maryam gida yawon arba'in


Zare idanuwa tayi tace what,?
Yace yes!

Tace wlh bazai yiwu ba, ta Bari sai ranar girkinta yace sbd me, tace abd yau girkina ne ko ka manta ne in tunasar da Kai?

Yace Ina sane, yace Amma rukayyah wlh kin faye son kanki da yawa, kin manta Randa na kaiki Asibiti muka kusan kwana acan, amma Maryam ko daga Kai batai ba, Amma shine kike fadin haka...


Tace wnn ai larura ne, kaima gashi ka fada asibiti...ita kuwa fitar nishadi ne, sbd haka kawai ta bari ranar girkinta, ganin ta hakikance da gaske take yace ke Bari kiji, wlh ba abinda zai Hana ni fita da ita, tace ni Kuma nace baka Isa ba, yace to zamuga wai zai nasara, yasa kafa zai fita Tasha gabansa tace, sai ka canza magana zaka fita a gidannan, ganin haka yasa shi ya wancakalar da ita gefe yace Allah ya wadan wnn halin naki,, nonsense!

Kuka ta Fara Yi da karfi kamar karamar yarinyar da aka duka, tana wlh indai ka fita da ita ban yafe ba, Allah ya Isa!


Tana gani suka fitan, Kuma Bata fasa kukan ba, har suka fice daga gidan, sai da tayi Mai isarsa tukun sannan ta tashi ta shiga, kamar ta Kira no mummy Kuma sai ta fasa, kawai sai ta Kira kanwarta, Aisha tazo gidan, ta Gaya Mata abinda ya faru, dake kanwar ma ta fita zafi akan rukyn sai ta shiga zugata wai wlh an Raina Miki hankali, in Banda ma kin maida kanki wata iri har yaushe zasu Fara Miki haka, ai wlh Anty ruky idan nice Basu Isa sumin haka, kece ma da kika nace masa, sai da mummy taso ta hadaki da Dan gidan Alh.dala, inda Zaki je kiyi abinda kika ga dama Amma kika ki, kika nacewa wnn da ba shi da wani arxikin azo a gani, ni ki tsaya kiga Wanda zan kawo a matsayin miji...ruky tace ya Isa haka Nan ke kanki kinsan Ina son Abbas kuma son da nake masa ne yasa nake zaune da shi, Kuma ni a gaskiya bazan iya rabuwa da shi ba, sbd mijin da kowacce mace zata so mallaka ne , ga kulawa, ga kyautatawa iya gwargwado gashi ya iya soyayyah, matarsa ce kawai take Mana katsalandan, sbd haka wlh nasha Alwashin sai ta bar gidan Nan..😳






Haka dai yar'uwarta taita zugata har tana cewa in suka dawo kizo mu shiga muyi Mata dukan tsiya muga uban da zai tsaya Mata shegiya kawai..ruky tace ke so kike ya koreni kenan,ki dai kawo wata shawarar...


Nan sukai ta saka wancen kunce wancen, har bayan magriba shiru basu dawo ba, itama Maryam duk ta damu Kar ya jawo matsala tunda ba girkinta bane, data Kira shi sai yace wlh abokinsa ne yaxo daga ibadan zai kaishi masauki sai ya dawo, yace kinsan Kuma an Dade ba'a hadu ba, muna Nan muna ta kwasar hira.

Tace to ka dai hanzarta don Allah kasan yadda muka barota a gidan.yace insha Allah zan taho ynx tace Allah ya tsare hanya...


Acan kuwa ruky ranta ya gama baci, tun tana sa ran karfe 7 har 8 tayi ga kuma 9...

Aisha tace kawai ki debo kayanki kizo mu tafi, ki barmasa gidansa, yaga kin nace Masa shi yasa yake wahal dake, ruky tace ba inda zani, wato ta samu ma Abinda take so,ai so take na bar Mata gidan, ni kuma Zama daram, ba inda zani...


Aisha tace ai shikenan Kinga Zaki iya ne....wlh da nice ...hmmmmm ta girgiza Kai Tai kwafa da sai sun gane kurensu...haka suka zuba idanuwa suna jiran dawowarsu, Kuma Aisha ta Hana ta buga Masa waya, wai ai shi ya kamata ya nemeta..


Karfe 9:30 na dare suka iso, suna ganin haka Aisha tace wlh ko barazana ce ki Masa kice tafiya zakiyi, sai ta bi shawarar ta, suka shirya Kaya a akwati Yana shigowa tace abinda kake so kenan yau zan bar maka gidanka, yace me yayi zafi haka, ya Kai dubansa ga Aisha wacce sai jifanshi take da harara, sai yai maza ya fita ya rufe kofar don Kar ta fito, tana ganin haka ta Fara bubbugawa ita da yar'uwarta da dai suka fuskanta baya wurin sai ta zagaya ta dauki jug na glass ta jefa ta wajen Maryam tana fadin wlh in baka bude min ba, sai na yi muku danyen aiki, tana fada tana Kara jefa kofunan glass, su Maryam suna neman hanyar kaucewa jifan nata, Aiko tana jefo na karshen saura kiris ya fada kan mufid...Abbas na ganin haka ya fita bangaren a guje cikin matsanancin bacin ran da Bai misaltuwa, ita kanta Maryam sai da ta tsorata da ganin yanayinsa, ya bude kofar ya shiga a fusace zai zabga Mata Mari kenan Aisha tace kul wlh kasake ka tabamin yar'uwa sai mun kulleka jaka aka maka? Ruky kuwa ta dauki wani kofin zata kwala Masa yai saurin bige hannun ya janyota yace ki barmin gidana ynx nan,tirjewa tayi tace ba inda zani ta fada da karaji, wlh ba inda zani fita, ganin ta hakikance har kanwar na fadin ki bar Masa gidan meye acikin gidan. .tace bazan fita ba....


Aiko sai cewa yayi kije na sake k...Bai karasa fada ba, tai wata irin Kara tare da ashariya kan ubancan ni ka saka ? Hahhhhhhh Ashe yau za ai gawa uku a gidan nan, ta fada tare da wullar da dankawalinta ta ruga kitchen a guje da zummar dauko wuka...tana fadin wlh tunda ka sakeni babu wata Yar iskar da ta Isa ta zauna a gidan Nan wlh sai na kasheka na kashe kaina sannan... ..Maryam kuwa na can kafafuwa suna rawa πŸ˜‚Jin ance za ai gawa uku...shi kuwa tana shiga kitchen din yai saurin kulle gidan ya koma ya cewa Maryam ta shiga daki karsu fito, zai San Abin yi...tace mun shiga uku Abban mufid wata irin mace ka kwaso Mana ta fada cikin tashin hankali, shi dai sai cewa yake kiyi hakuri komai yaxo karshe, ki kwantar da hankalinki karki fito kinji, tace Abban mufid don Allah karka fita karta kashe min Kai ta fada tana kuka ta riko shi, yace ba abinda zai sameni ki koma kawai, Yana shiga ya sameta da wukar a hannu ta dumfaro shi gadan-gadan, yai saurin rike hannunta suka hau kokawa tana wlh tunda ka sake ni sai na kashe ka,ka rabani da kowa bani da kowa sai Kai sannan kace ka sake Nan ta Kara wani yinkurin...Maryam dake jiyo Abinda ke faruwa jin dif anyi shiru yasa ta kurma ihu Wayyoh Allah ta kasheshi .......




To Nima dai hannuna karkarwar yake, tashin hankali ya Hana ni karasawa...ku biyoni don Jin yadda ta kasance....





*By*


*Ummu Ameer*πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»





*Story & written*



*By*


*Ummu Ameer* πŸ’ƒ




*Page* 5⃣1⃣






""""" Shirun da Maryam taji shiya tabbatar Mata da cewa lallai ta kashe shi ko Tai Masa wata illar, kuka ta dinga yi ta nufi kofar fita,duk da taji a kulle take, Amma tana gwada sa'ar ta ko Allah zai sa ta bude....Amma Ina ko alama, haka dai taita kuka tana Allah ya kareshi daga sharrin wnn mahaukaciyar matar..Allah yasa ba wani abin Tai Masa ba.

Ganin haka yasa baba sa'a (Mai taya ta renon su Hassan) ta kamota ta zaunar da ita tana lallashinta, tace Haj. Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, insha Allah ba Abinda zai sameshi...tace Allah yasa...Bata rufe Baki ba kawai sai ganin ruky sukai akansu kamar Aljana Maryam na ganinta ta tashi zata gudu sbd Bata da maraba da mahaukaciya
Kai a bude ta barbaza gashi, kafar duk tayi Kura daga ita sai vest iya cibi.. da wando..Maryam daga nesa da ita, take fadin me kikai wa mijinah?, Ina kika kaimin shi...?ruky wani banzan kalloh Tai Mata ta dumfareta a fusace wai saita Gaya Mata dalilin daya sa, ta shiga tsakaninsu da Abbas har ya sake ta, don tasan ba yin kansa bane ita take haddasa duk Abinda yake faruwa...Maryam tace kije na barki da Allah Kuma in nice na zalunceki Allah ya saka Miki, dama alokacin ba komai a hannun rukyn, Maryam na gama fadin haka ruky tace haka kika ce? Sai kuma ta kwasa a guje kamar wadda Tai mantuwa taje dauko abinda ta manta, ita da baba sa'a suka bita da kalloh,suna mamakin wai ya akayi ma ta shigo bayan ko Ina a rufe yake,,,

Ashe wnn kofar da Tai musu tsakani wadda ta ballah kwanaki, duk da dai an gyara Ashe ba'a saka key ba, Maryam na ganin haka Tai maza ta dauko key ta murda, jiki na rawa don bata aminta da fitar da Tai ba, da kyar in ba wani makamin ta je daukowa ba...


Baba sa'a tace haj, gara kije ki sanar wa makotanku, abinda ke faruwa sbd ba'a San me take Shirin aikatawa ba Kuma ynx, Bai kamata muyi shiru ba, ko sa taimaka mana, tace haka ne baba, Bari nai saurin barin gidan...spare key din gidan taje ta lalubo taxo ta bude kofar ta baya wacce ita kanta rukyn Bata San da ita ba, tai hanzarin fita ba tare da ta dauki yaro ko daya ba, sbd tasan ita take Hari don ta tasan ita ta tsolewa ido, cikin sanda ta bar gidan ta shiga makotansu tana buga kofa alokacin 12 na dare sai faman buga kofar take tana waige ko rukyn ta biyo ta, sai da akai kusan 5min sannan maigidan ya fito shima cike da tsoron Mai buga musu gida a wnn lokaci, sai da ya Dan leka ta wata kofa ya ga Mai bugawar sannan ya bude Yana tambayar Maryam din lfy kuwa?

Tace ba lfy Amaryar Dr. Ce ta kasheshi tana fada tana kuka tace ynz haka ni take bi, wai sai anyi gawa uku..don Allah baban Khalil ka taimaka ka duba min halin da yake ciki...shi kanshi ya tsorata da jin haka, yace shiga ciki Bari naje naga Abinda ke faruwa , amma wnn wace irin mace ce haka, Allah ya kyauta...cikin hanzari ta fada gidan ta samu matar gidan a falo itama Tai jugum domin duk Taji abinda Maryam din ke fada ...tace zo mushiga ciki Maryam ta janyota suka shiga daki, ta koma ta Sanya key a kofar falon gudun Kar su ganta kwatsam a gidan..ita dai Maryam sai kuka take tace ni wlh tashin hankali na shine bansan halin da Abbas yake ciki ba, don wnn matar ba abinda bazata iya yi ba...matar tace insha Allahu ba abinda zai sameshi, tace maza ne da kwashe -kwashe Kuna zaman lfy su kwasowa kansu bala'i ynx Ina amfanin wnn don Allah..


Ashe wnn shirun da Maryam taji, yankarsa tayi a hannu ganin zata Kara wani yunkurin, yai saurin kaucewa tare da barin wurin a guje ya fita daga gidan tabi bayanshi itama a guje, ganin ta hakikance kisan take son yi, ya tsorata matuka, yace kafa me naci banbaki ba, itama ta kure gudu, Yana gudu tana binshi, daga ita sai wnn rigar iya cibi da wando, ba dankwali, Yana gudu Yana Fadi a xuciyarsa lalle ba makawa wnn Bata da hankali, ganin ya Mata nisa sosai yasa ta tsaya tana haki tace wlh duk inda kaje sai na bika na hallaka ka, ba abinda zai canza kudurina, Kuma wlh ba wata nadamar da zanyi, juyawa tayi ta koma hanyar gida, sai ga kanwarta da ta biyo bayanta ta rike ta suka koma, duk Yan unguwa na kallonsu don ma wasu sun yi bacci, wasu Kuma hayaniya ce ta fito da su, su ganewa idonsu abinda ke faruwa, wasu har video suka Fara dauka don tabbatar da shaida idan har ta aikata kudurinta, sai faman tsinewa halinta ake.


Shiko Abbas Bai tsaya ko Ina ba, sai division dake basu da nisa ya shiga Afujajan ya Kai musu report din abinda yake son faruwa, suka shigar da case din, Daman sun sanshi, Suma sun jajanta masa, suka ce ya Dan samu nutsuwa sai suje gidan,yace na samu yallabai kawai muje a fitar min da ita a gidana na Riga na saketa ba wani sauran Abu tsakanina da ita, ga iyalina bansan halin da suke ciki ba, karta je ta far musu.


Bayan dawowarta daga bin Abbas din data yi shine ta afka wa maryam tana tuhumarta da cewa ita ce silar faruwar komai, wnn fitar da tayi aguje kuwa komawa tayi ta dauko wukar ta afkawa Maryam, Amma tana zuwa ta tarar kofar a rufe gam, an kulle sai jijjigata take iya karfin ta, ganin an kusa ballah kofar baba sa'a ta fashe da kuka tana fadin shikenan kashinmu ya bushe ..a guje taje ta dauki Hassan ta goya ta dauki usaini a hannu ta fita ta inda Maryam ta fita a guje tana la'ila ha'illallahu jama'a ku taimaka zatai kisan Kai, kicibus sukayi da baban su Khalil Wanda ynz ya gama waya da Abbas ya shaida masa Yana Raye police station yaje ya Kai report gasu Nan ma a hanya zuwa gidan.


Yana ganinta a wnn halin yace baba lfy? Gata can tana can tana Shirin ballah kofar Kuma wlh wukar ce hannunta ta fada a gigice, yace me ?
Shima ya tsorata ainin, yace kiyi sauri ki Kai yaran ciki mamansu tana gidana, ni Bari nai hanzarin debo sauran yaran, ... haka baba sa'a taita bugawa su Kuma sun daukan rukyn CE Basu bude ba Saida tace Haj. Nice kuyi hanzarin budewa yara na kawo miki tana can tana Shirin ballah kofar da wuka a hannunta cikin hanzari suka bude suka karbi yaran tana kukan wnn bala'i ko a film Bata taba ganin irin haka ba, tana Basu ta koma cikin hanzari don debo sauran yaran, sai ga Abban su Khalil ya dauko mufid, yace kiyi hanzari ki dauki macen ta kusa ballah kofar..ta dauko ta kenan sai ga kofa kasa ta shigo a fusace da wuka a hannu... Baba sa'a Tai hanzarin buya jikinta sai rawa yake sauran kiris fitsari ya zubo Mata don tsoro, ruky kuwa ba inda tayi da wukar sai dakin Maryam, ta bankada kofar da karfi, ta shiga tana waige waige Bata ga kowa a dakin ba, har wardrob da karkashin gado Bata ganta, ba yaran ko daya a ciki...


Baba sa'a kuwa tana gani ta shiga dakin Tai saurin barin gidan cike da tsoron karta cimma su, Tai saurin shiga can gidan tana fadin wlh hajiya ke take nema, tana ballah kofar dakin ki tayi da wukar tana dubaki, tace wlh da tasamu daya ayaran Nan sai ta hallaka wani, karbar elham din Maryam tayi tana kuka tace na sani ai tinda ni take zargin na rabata da mijinta..

Makociyar tata tace oh wnn masifa Dame tayi Kama...Amma gsky wnn ba Imani a tattare da ita ko kadan...


Anan baba sa'ar take shaida musu Abbas Yana Nan da ranshi, police station yaje sun taho ma gidan ynx. .hamdala Maryam tayi tare da godewa ubangiji daya tserar dasu daga gareta.




Acan gidan kuwa ba inda Bata duba ba, Bata ga kowa ba, tace tabbas guduwa sukayi, Amma ta ina? Ta tambayi kanta, ganin Bata samu kowa ba, yasa ta fito waje tana dubawa ko zata ga inda sukai Amma ba Wanda ta gani, A haka bbn su Khalil din ya cimma ta yace haba baiwar Allah me yayi zafi haka kike Shirin aikata irin wnn danyen aikin? Wanda zai saka ki nadama daga baya..tace wlh ba nadamar da zanyi bayan na kashe shi..mutumin daya rabani da kowa, na bashi dukkan kaunata Amma ya saka min da saki, wlh ba abinda zai hanani kashe shi...A'uxubillahi sai kace ba Yar musulma ba kike wnn kirarin ...yace ki taimakawa kanki ki aje wnn wukar ta hannunki domin matukar hukuma ta kamaki da ita kin kade...tana Jin hukuma sai Kuma ta tsorata sbd ta tsani Yan sanda balle kwanan prison..ni ko nace Ashe haukan nata na karya ne..Amma sai ta dake Bata nuna Masa tsioronta ba har taci gaba da fadin bazan fasa kudirin da na dauka ba...hango mutanen da suka dumfaro su Tai saurin wulla wukar bayanta, ta danne da kafa, shiko Abbas karasowa yayi da sauri Yana fadin gata Nan yallabai ku tafi da ita, bana bukatar ta Kara koda mintuna a gidana...




Muje zuwa



*Ummu Ameer ce*πŸ’ƒ

πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»




*Story & written*


*By*


*Ummu Ameer* πŸ’ƒ





*Page* 5⃣2⃣




*** Kuri-kuri Tai ta idanuwa tunda taji ance wai a tafi da ita, ganin suna Shirin arresting dinta yasa makwabcin sa ya Dan ja Abbas din gefe yace Masa, kayi hakuri kar ka Bari su tafi da ita can,kayi hakuri zuwa safiya sai su kwashe kayansu su tafi, kaga ko ba komai da yarinya tsakaninku Bai kamata ba, kamar tozarci ne ko ya kagani..

Abbas zaro ido yayi yace in barwa zuwa safe ai Banga Abinda zaisa ta kwana a gidan Nan ba, bakasab kudurin da take da shi ba ne akaina, sai kuma in kyaleta don bansan ciwon kaina ba...


Ruky kuwa ganin sun dumfarota ta xube kasa a gurin tana kuka, wai wlh nayi nadama, dama bacin raine ..kuka take sosai sai kace ba ita ta gama kirarin kisa ba, har tana Basu hakuri tace, kunga ba komai a hannuna, tun daxu nayi nadamar Abinda nayi, ta juya kan Abbas ta hade hannu biyu tana rokonsa ya gafarta mata, tayi nadama, tana rokon ya gafarta Mata Kar ya Bari su tafi da ita...shiko ko ajikinsa yace dolenki ki bisu ba abinda zai hanaki kwanan cell!


Kuka take sosai ganin haka daya daga cikin masu tafiya da ita yace oga Ina son magana da Kai..Abbas yabishi suka yi gefe yace oga Ina ganin tunda bamu da hujjar kamata bamuga wani makami a hannunta ba, Kuma Naga alamun nadama a gareta Ina ga kawai gara ka barta zuwa safiya sai su tafi, kaga shi kanshi case din zai iya Kara zama wani Abu daban ga tonon asiri kowa sai yasan me ya faru, Kuma a matsayinka na babban mutum Bai kamata ai ta yawo da maganar ba, in yaso zan bar mutum 1 Wanda zai zauna har gari ya waye gudun Kar wani Abu ya biyo baya...ko ya kagani?

Dogon azuciyar zuciya ya sauke yace amma Sam ban yi niyyar barin ta, ta kwana anan ba, da kyar dai ya Amince da hakan da taimakon makocinsa,, sannan suka ce Maryam din Tai kwanciyar

Please Login or Register in order to submit comment