Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma ya kasa ma magana, sai faman safa da marwa yake a dakin.


Sai da nutsuwarsa ta samu sannan ya dauki wayarsa ya Kira daddy ya shaida masa Abinda rukayyah ke Shirin yi, yace daddy Ina ganin ko za'a kaita ai Mata rukiyya ko tana da wasu mutanen akanta, Amma a gaskiya lamarinta ya Fara bani tsoro, Abu Bai taka Kara ya karya ba, Amma ta dauki zafi ta Hana kanta sakat...daddy shiru yayi don yasan ba wani abinda take dasu, kawai zafin Raine irin na uwarta, in ransu ya baci su maida kansu mahaukata, har illata kansu sukeyi, Amma in haka ne ko Bata gadawa yaranta Abin arxikiba, ya fada a zuciyarsa, dogon ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce, kayi min Alhlfarma kayi hakuri, nasan irin hakurin dakakeyi Amma don Allah Kara min wani, gobe in Allah ya kaimu zanzo in sameta zan yi maganin haukanta, kayi hakuri kaji...

Abbas yace Allah ya kaimu..sai ka zo, Amma a zuciyarsa baiyi niyyar barinta ta Kara kwana a gidan ba.



Zamanshi yayi Bai Kara komawa wajenta ba, ya rufe gidan ya shiga wanka, ya Dan sake samun nutsuwa, sannan ya kwashe abinda ya faru ya Gaya wa Maryam, tace kayi Kara hakuri Abban mufid jarabawarka kenan kayi kokarin cinyeta kaji ...

Gyada Kai kawai yayi haka taita Masa kalamai masu kwantar da hankali, har sai da taga ta kawar Masa da damuwarsa...


Ruky kuwa kokari take ta ballah kofar ta fito bacin ran ya kalleta ya tafi can wajen matarsa ne yasanyata ta tattaro karfin da take dashi ta buga kofar Aiko sai ga kofa a kasa dake Bata karfe bace, ta fito kamar wata zakanyar dake farautar nama...ta nufi wnn tsakanin da ya raba tsakaninta da gidan Maryam, ta nufi wajen a guje.....





*Muje zuwa*



Taku



*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Story&written*


*By*



*Ummu Ameer* 💃




*Page* 4⃣6⃣






""""Tana zuwa wurin ta hau buga wajen tana kazo ka bude ni, wlh ko nai na tayar da hankaiin Yan unguwar Nan gaba daya, bugawa take ba kakkautawa, dama tsakanin da akai musu kofa ce Amma ba karfe ba, Kuma ba'a shiga ko fita ta wajen sai dai a zagaya ta can baya...da ta daddage ta saki karfinta ga kofar sai ga kofar a akasa...

Suna jin karar balla kofar ya tashi a fusace kafin ya iso gareta, ta dauki wani katako ta rafka Masa a goshi, kan kace me jinin ya Fara malala a gurin, Maryam na ganin haka ta zuciya ta nufeta a kufule, Abbas yai saurin fizgota, ya rike ta Yana fadin me zaisa ki tunkari wnn mahaukaciyar so kike ta illata kine, so take Daman ta samu damar illataki tunda ke kika tsole Mata ido...Cike da bacin rai tace ka barni in nuna Mata ba tsoranta nake ba, haka kawai taga ana kyaleta ne, shiyasa take wnn iskancin.

Ganin jinin dake xuba a goshinsa yasa ta Kara zuciya zata koma wajen ruky, ya Kara riko ta, yace me hakane bansanki fa da wnn halin ba, karkice Zaki biyewa wnn karyar...Jin sunan da ya kirata ne yasa ta Kara yunkurin Kara zuba Masa katakon, hannunsa yasa ya fixge katakon ya wurga ta gefe guda, da alama kuwa taji jiki don kasa yinkura tayi ta zube tana rige kwankwaso, Amma bakinta Bai rifu ba, sai binsa take da Allah ya Isa mugu kawai, so kake ka kasheni ka huta ko, to wlh sai na dauki fansar abinda kaimin..


Tazo ta wuce ta gabansu ta shiga ta dauki yarta a gidan tace wlh, ba Wanda zai bacci a gidan nan, in Kuma ka musa mu zuba.ta fada tana jijjiga jiki,kamar farin shigar hauka...


Jan Maryam yayi suka koma wajensu, har sun yi nisa ta jefo musu wnn katakon Allah yasa Bai samesu ba....

A zuciye ya dawo ya fixgo ta Yana fadin ke mahaukaciya ki barmin gidana ynx Nan kafin nai danyen aiki akanki ya fada don bacin rai har karkarwa hannunsa yake, idonsa ya birkice ita kanta sai da ta tsorata da yanayin nasa, tana tsoron karya furta saki, Amma dake zuciyarta ta bushe alokacin sai cewa tayi ba inda zani, Zama daram wlh, ni da Kai mutu ka raba....ya katseta da fadin ki fita nace ai ba da gidan kika zo ba....


Tace wlh ba inda zanje in ma kana tunanin haka to gara ka daina Batawa kanka lokaci...juyawa tayi ta janyo rigarsa ta baya tana wlh fa ba inda zakaje sai dai mu kwana anan dukanmu Amma ba Wanda zai runtsa.. a lokacin 12saura na dare,


Da dai yaga Bata da niyyar fasa haukan Kuma Taki fita a gidan sai ya damkota yana Shirin fitar da ita ta karfi, amma ta tirje Taki motsawa, shi kanshi Yana mamakin wnn karfinta haka shiyasa wani lokacin yake tunanin ko ba ita kadai bace.

Amma duk da haka dake karfin Namiji ba daya da mace ba, sai da yayi nasarar janta zuwa bakin gate ya bude kofar kenan Yana Shirin wurgata wajen sai ga makocinsu ya fito sbd Jin hayaniyar dake tashi tun dazu a gidan makocin naci, shiyasa ya fito sbd hakkin makotaka.


Yace subhanallahi Dr .lfy me ke faruwa haka? Shi bacin rai ma da kunyar Abin kunyar da ta janyo Masa ya Hana shi cewa komai ita Kuma sai ta fara kuka tana fadin kagan shi Nan wlh ba abinda yake min sai musgunawa da rashin Adalchi tsakaninmu, yayi ta wulakantani a gaban matarsa, ya raba ni da iyayena na biye Masa sannan Kuma ynx yake son juya baya, kawai don na nemi in kwaci yancina a gidan, tunda na shigo gidannan kullum da bacin rai nake kwana, in nai Masa magana yace in bazan iyaba, in tafi ai ba rikeni yayi ba, yaje yasa an toshe min mahaifa, ya bar matarsa tana haihuwa ni baison hada zuriya Dani....

*Kaji sharri irin na ruky*


Makocin najin haka yace ya Isa haka baiwar Allah, kiyi hakuri ki koma cikin gidanki, zamuyi magana da maigidan naki...tataso Tai saurin komawa ciki...ba inda ta dosa sai bakin kofar data karya tana fadin to bakar munafuka fito, maganin naki baici ba, Ina Nan daran Zama ynx na Fara, ni da shi mutu ka raba, ba inda zanje sai dai ke ki fita ki barni, so kike in fita in bar Miki shi, dama hakan kike so, to ki canza batu don Abu kazakazanki Yar masu bin bokaye, haka taita shirmenta Amma Maryam Bata tanka Mata ba, Sanya key tayi a kofar ta rufe tana ambaton ubangiji ya yaye musu wnn bala'in....



A can kuwa Abbas kwashe duk Abinda ya faru yayi ya Gaya masa, Kuma ya tausaya Masa don yasan halinsu na mugun kishi, hakuri ya bashi akan don Allah Kar ka yanke hukaunci cikin bacin rai ka jira mahaifinta ya zo goben tukun Kar yace baka ji maganarsa ba, Abbas yace na gaji da halinta ne wlh, shiyasa naso in yarda kwallon mangoro in huta da kuda, makocin yace kayi hakuri munsan kanayi ka Bata dama mahaifinta yazo goben.


Abbas yai Masa sallama ya koma ciki, tana Jin shi ya taho Tai saurin shiga daya dakin da Bata balla kofar ba, ko kallon inda take baiyi ba, ya wuce wajen uwargidansa, ya sameta itama a cikin damuwa na abinda ya faru, ya Bata hkauri akan ta yafe masa shi ya jefa su cikin wnn halin, har Yana xubda hawaye, tasowa tayi tazo kusa da shi tana fadin don Allah ka daina zubda hawayenka akan wnn matar kayi hakuri da jarabtar da Allah yayi ma, kaita addu'a Allah ya kawar d dikkan sharrin dake cikinsa.


Haka dai taita lallashinsa daga bisani, yai treating din wajen, da ta fasa Masa,kusan a zaune kuwa suka kwana sbd Yana tsoron kar ta shigo musu da wani makamin, shiyasa ko runtsawa Bai yi ba sai da har garin Allah ya waye....






Muje zuwa



Taku

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Story &written*




*By*


*Ummu Ameer*💃





*Page*4⃣7⃣






""""Washe gari, Ruky tashi tayi da nadamar Abinda ta aikata, kamar ba ita Tai hauka ba jiya, a zahiri in ka ganta bazai Kai tunanin cewa zata iya aikata abinda take yi ba, Nan kuwa zuciyar kafirai gareta, tashi tayi ta hau gyaran gidanta da kanta duk ta gyara abinda ta hargitsa na fashewar Kuma ta kwashe ta xubar ,ta zage tukuru tana aikin gidan ko don taji daddyn nata zaizo ne oho!



Har wajen karfe 9na safe Abbas Bai shigo ba, hakan kuwa Bai Mata dadi ba, anata wautar...


Da ta ji shiru sai ta dauki waya ta kirashi Bai dauka ba, har ta gaji ta hakaura, taci gaba da aikinta, kamar gaske, bayan ta gyara ko Ina tai wankanta Tai ma Khadija.



Bai shigo gidan ba, sai da ya tabbatar da isowar mahaifinta wajen karfe 10:30 na safe, ko da daddyn ya Isa gidan shima yayi mamakin ganinta kamar ba ita akace ta aikata wani abinba, tai murna sosai da ganin mahaifinta, sai rawar jiki take wajen kawo Masa abubuwan ci da na Sha, shi kuwa sai kallon ta yake da mamaki, har Yana zargin ko dai ba gaskiya ya fada Masa ba, Abbas din, Yana Nan cike da mamakinta sai ga Abbas din ya shigo, ya tsugunna ya gaisheshi ya masa ya hanya.


Shima kanshi yayi mamakin yadda yaga rukyn, kamar ba ita Tai rashin mutumci jiya ba, gashi yaga ko Ina tsaf ta gyara gidan kamar ba Abinda ya faru....haka dai ya samu wuri ya zauna a kasan carpet din itama tazo ta zauna ta daya gefen, tana satar kallon shi ta kasa-kasa, kamar wata mumina.


Bayan shiru ya ratsa na Dan wani lokaci, daddy ya Fara magana yace

Rukayyah bana Jin dadin Abinda kike aikatawa a gidan mijinki, kinki kwanatar da hankalinki ki zauna lfy, kullu yaumin cikin hayaniya, haba ban tsammanin haka daga gareki ba, sbd ada, na sanki da kyamatar irin wnn halin, Amma gashi ynz kin tsunduma kanki tsundum a ciki, nasiha yai Mata Mai ratsa jiki, daga karshe yace Kuma matukar ta sake aikata haka zai zare hannunsa akanta tunda ya fahimci taurin Kai ne da ita.


Itakuwa harda fashewa da kuka Mai shiga rai tazo ta tsuguuna gaban shi tana Mai neman ya yafe Mata bazata Kara yi, ba, shi dai Abbas binta yai da kallon mamaki.


Shima Nan ta zo gabansa akan ya yafe Mata bazata sake yin makamncin haka ba.

Shiru yai Bai amsa Mata ba, ganin idon daddy akansa yasa yace Allah ya kiyaye gaba. Har da cewa ngd baby!

Shikuwa fakar ido yayi ya wullah mata harara, don har ynx haushinta yake ji, Koda ma sun ci gaba, da Zama baya Jin zai Kara sakin jiki da ita, girmanta da kimarta duk babu su wajensa.

Daddy kuwa yaji dadin yadda suka sulhunta kansu, da Kuma nadamar da tayi, yai musu sallama ya tafi, tare da Addu'ar samun zaman lfy.


Har waje suka rakashi, bayan sun shigo taga Yana kokarin komawa wajen Maryam, hannunsa ta riko, ta sakalo shi ta hade da nata, tana cewa don Allah ka gafarta min, wlh nayi nadama, dama bacin Raine Kuma na kasa controlling dinshi, Amma ynx na gane kuskurena, kayi hakuri ka Kara bani wata damar...plxxxxx ta fada har da wani kwantar da Kai a kafadnshi, shi kuwa da dai ya tuna Abinda tayi jiya,sai ya fixge hannunsa yayi tafiyarshi ciki, ya barta Nan a tsaye.



Haka ta dauki jiki ta koma ciki, jiki ba kwari, zuciyarta na Gaya Mata cewa tayaya za ai ki aikata irin wnn mummunar Abin, sannan ki yi tunanin samun kansa ta sauki, ai sai kin zage..


Wata dabara ce ta fado Mata, ta dauko mayafinta ta shiga wajen Maryam, taita sallama taji Shiru sai ga Abbas din ya fito, yace lfy?
Murmushi tayi tace nazo na bawa Maryam hakuri akan abinda ya faru...

Wani kallo ya bita da shi na raini, ya Koma ciki, ya fada Mata wai rukayyah ce tazo Baki hakuri... ita kanta tayi mamaki da Jin hakan, sai Kuma ta Dan yi dummm na wani lokaci, sai ta yunkura ta tashi, yace Ina Zaki?tace zanje wajenta mana.

Yace kyaleta kawai...tace in mun kayi haka bamu kyauta ba, tunda har ta gane kurenta ai sai muyi mata afuwa, mu zamo masu saurin yafiya, tunda itama har tayi saurin nadama, kaima ina rokon Alfarma ka yafe Mata, shiru yayi na wasu lokuta, a zuciyarsa yace lallai Maryam na da kyakkyawan hali, na rashin rike mutum a ranta, tabbas shine shaida domin kuwa ko akansa ya Isa ya gane wnn kyakkywan halin nata.


Tashi tayi ta fita, ta sameta zaune akan kujera, yau ita ne ta gaisheta, bayan gaisuwar tace nazo ne in Baki hakuri akan Abinda ya faru jiya, wlh bacin Raine da sharrin shaidan,kiyi hakuri insha Allahu haka bazai sake faruwa ba...

Maryam tace lah ba komai, Allah ya yafe Mana Baki daya, tace Ameen.

Daga bisani sukai sallama, ta koma wajenta.


Koda Maryam ta shiga daki ta Gaya Masa yadda sukai, shidai kawai jikinshi Bai bashi ba, Yana tunanin ko wani makirci take so ta kullah, Amma sai ya barshi a zuciyarshi, yace Allah ya kyauta, yai Mata sallama ya wuce office.


To wnn tuban da ruky tayi ko me dorewane???




Taku

*Ummu Ameer*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻






*Story&written*



*By*



*Ummu Ameer*💃


*Page* 4⃣8⃣





""""Bayan kwana 2 da faruwar haka, rukayya ta karbi girki, duk da har yanzu ba wani sakewa da ita yai ba, ita kuwa ta dage wajen ganin ta janyo ra'ayinsa, ya yafe Mata, Amma Ina yadda take tunanin Abin ba haka bane, wnn karon Abbas ya dau zafi..



Kwata-kwata ya canza Mata ita kanta da ta San haka ne zai biyo baya da batai ba...a haka yai kwana 2 a gidan Amma ba wani walwala ko sakin fuska daga gareshi.



********. *********


Bayan 2wks da faruwar hakan har ynx zaman nasu ba dadi...ba Abinda batai Masa ba ganin ya sauko Amma ina.




To tsakanin miji da Mata sai Allah, sai da ruky tasan yadda tayi amfani da kissa yaudara ta janyo hankalinshi ya sauko daga fushin da yake da ita. Sun shirya an bude sabuwar rayuwa.


Maryam kuwa na can ta dage wajen Kara gyara kanta fiye da na da, ba yadda baiyi ba, a koma ruwa Taki yadda, ta ci burin sai tayi arba,'in tunda ynx ba ita kadai bace, har fushi yake da ita, sai dai ta kwantar Mai da hankali ta wani fannin.



Su ruky kuwa ynx ta dage wajen kokarin ganin tana danne wnn zaxxafan kishin, shiyasa kwana 2 shiru..gashi ynx ba kwayar Hana shi zuwa wajen Maryam, sbd akwai wata Rana Yana neman wata takarda ya gano shi, ko da ya gani daukewa yayi ya zubar, sannan yayi tirrr da halinta ya gane nufinta akan kwayar..Kuma yai shiru Bai Gaya Mata ba.


Shiyasa ya Sanya ido akan duk abinda take yi a gidan, Kuma ya daina Shan duk wani drinks da zata hada da kanta. Tun daga lokacin ta Sha jinin jikinta ta San tabbas ya gano wani abin,,,




Mummy kuwa tun da taji labarin wai ana neman rukayya, tayi yaji...sai jikinta yai sanyi, ta Fara ganin kuskuren zare hannunta da tayi a kan diyarta, duk da cewa itama ta watsa mata kasa a ido, Amma duk da haka ya kamata ta San halin da yarta take ciki.

Kanwar rukyn ta tura gidan ta je ta bugi cikin rukyn ta fada Mata damuwarta...


Aisha ta shirya ta tafi gidan rukayyah, rukyn kuwa ba karamin dadi taji ba da ganin yar'uwarta, sbd tana son zuwa Amma mommy ta Hana su.


Sai dai ba wani Abin aje a fada da Aisha ta gani ko taji daga gareta, ba yadda Aisha batayi ba, ganin taji damuwar Amma Taki fadan komai, tana tsoron kar ta guntule Mata igiyar aurenta.

A wnn lokacin ne Kuma yai dai-dai da arba'in din Maryam yara sunyi kyau gasu da kibarsu Abin sha'wa ga kamar da suke sai ka kula sosai zaka iya gane su...


Ranar da ya Kama arba'in din kuwa kada kuso kuga gyara ta ko Ina wajen maryam, ansha Jan kunshi ga kitso an Mata shi ya zubo gadon bayanta, ga wani fresh da fatarta ta Kara sai sheki take ga taushi kamar fatar jarirai, ga Abubuwan saukar da ni'ima ta tsumu sosai,ita kanta tasan ta gama hadewa.

Ranar kuwa yai dai dai da ranar da zata karbi girki, hatta da Abincin da aka shirya Masa na musamman ne, gidan ma ya Sha gyara na musamman, bed room dinsu kuwa yasha turaruka masu sanyaya rai da saukar da nutsuwa, an Sanya new sheet, tare da fesheshi da turarukan qamshi.


Wasu kananan Kaya ta Sanya wanda suka amshi jikinta sukai Mata das, kamar don ita akai kayan,Riga da wandon ne rigar ja, sai wandon bluei Wanda yasha adon stones ta gefe amma Bai sauko kasa ba, hakan ya Kara bayyanar da kyawun kunshin kafarta, ta saki gashinta har bayanta, ta Sanya sarka Mai beads Mai ratsin ja da blue haka ma Abin hannunta, ansha make up Wanda yai dai dai da tsarin shigar da tayi, in ka ganta ma bazakai tunanin ta haifo yara haka ba.ga wasu shedanun turaruka da ta shafa kala-kala bazaka iya tantance ma qamshin ba,
Haka ma madarar turare shafe ko Ina tayi na jikinta da shi tun kafin ta Sanya kayan..




Ruky kuwa dama kamar ita ta haihu tana irgen kwanakin, ga qamshi girki da na gida ya budade ta, tun daga lokacin ta kasa samun nutsuwa, har shiga gidan tayi ta ga irin kwalliyar da tayi, lokacin Abbas ya fita masallaci ta saci kafa ta shiga, ta fake da cewa wai tazo Mata murna, lokacin tana daki Maryam har zata fito ta koma ta Sanya xumbulelen hijabi baka iya ganin me ke jikinta, sai kunshin da kwalliyar fuska, hakan kuwa ya sosa ran ruky, tace don bakin Hali ma bazata Bari a ga me ta Sanya ba, ganin hakan yasa tace zan koma. Maryam Tai Mata godiya ta rakata kofar fita.


Ruky kuwa ta dawo da takaicin rashin ganin shigar da Maryam tayi.




Shi kuwa gogan tunda ya kyallara ido akanta ya gagara samun nutsuwa sai wani Nan -nan yake da ita kamar wata sabuwar Amarya, Yana manne da ita Yana shakar qamshin da ya gama rikirkita shi, A ranar dai komai santin shi ya dinga yi...

A Daren ranar kuwa abin ba magana domin kuwa jinta yayi kamar wata sabuwar Amarya, yasa mata Albarka yafi akirga.


Ruky kuwa Abin ya tashi kasa bacci Tai a wnn Daren, har labe tayi ko zataji wani Abin Amma ba Abinda ta iya ji.


Dan wahala ko bacci kasa yi tayi, kishin ya tashi ta kasa samun nutsuwa,,,,,


Washe gari kuwa Bai shiga wajen ruky ba da wuri, Maryam ta gama sukurkuta shi, sai da zai fita office ne ya biya, ya sameta ta cika fam gaisuwar ma Bai Samu ba, yai ma Khadija wasa wacce a lokacin tana dabo koyon tafiya, Sam Bai damu da rashin kulashin da batai ba, har yazo zai fita tace Ina da magana da kai, yace tin shigowa ta, Baki tashi yi min magana ba, sai ynx da nazo fita ki Bari idan na dawo mayi maganar, tace Sam Bata yarda ba, ynx take son suyi maganar,,,

Ganin ta hakikance tana Bata Masa lokaci, gashi ya Riga ya makara yau, kawai yasa Kai yai tafiyarshi, ya barta Nan tsaye da bakin cikin rashin saurarrarta, mayafi tai saurin daukowa ta rufe gidan ta bishi har bakin motar Yana Shirin tayar da ita, tace tunda kaki saurarata, muje ka saukeni a gida bana jin dadi, banson kadaici yace a'a ba inda zakije ba ke kike da ikon fita aduk lokacin da kika so ba, ki Bari sai na Baki izini tukun, ya fada tare da Shirin Jan motar tace nace maka bani da lfy, Amma bazaka iya tsayawa ka tambayi abinda ke damuna ba, kake Shirin tafiya, tunda ba damuwar ka bace ko?


Tace tun jiya ban yi bacci ba, sbd zazzabi da ciwon Kai ....yace Allah ya sawwake zan taho Miki da magani in na dawo, ya tashi motar ya tafi, ta tsaya Nan gurin da takaicin rashin samun nasarar Abinda taso yi, wai ita a dole sai ta ja ra'ayinsa sun dauki wani lokaci, don hakan ya sosa ran Maryam, ko ta bishi su fita, don tasan matukar Tai hakan Maryam bazata ji dadi ba, tunda tasan girkinta ne, shi Kuma kamar yasan kudurinta, shiyasa baya biye Mata.


Haka dai ta koma gidan kafa ba kwari, Amma duk ta bi ta damu kanta, tunda ya fita take doka Masa Kira wai zazzabin ya dameta, Bata iya Abu kaza, tun Yana dauka har ya gaji ya daina daukar ita kuwa Bata fasa Kiran ba.

Shi kuwa tunda yaje office ba abinda yake tunani sai abinda ya wakana a Daren jiya tsakanin shi da maryam, jinta yake sosai a ransa, har Allah Allah yake ya koma gidan ....itama sai turo Masa zafafan text take wadanda suke Kara rikirkita shi.

Hakane ya Sanya ya koma gida da wuri..Koda ruky taga dawowarsa murna taitayi ai ya dawo ne sbd rashin lafiyarta, Yana shigowa wajen rukyn yaje da murnarta ta tare shi, ansha make-up an matse cikin kananan Kaya, sai wani kirsa take yi, Koda ya ganta a zuciyarsa yace to wacce Bata lfy ce da irin wnn iyayin, shikuwa ko Zama ma bashi da niyyar yi, ya tambayi yarinyarsa tace tana bacci, yace Bari na wuce wlh a gajiye na dawo zanje na Dan huta...a take annurin fuskarta ya dauke Tai kicin-kicin da fuska ya Mika Mata ledar magungunan yace sai anjima, a fusace tace Abban Khadija ba kace in ka dawo zamuyi magana ba, yace kinji abinda nace a gajiye na dawo, why not mu Bari gobe in kin karbi girki sai mu tattauna, tace Sam Bata yarda ba, ganin tana Bata Masa lokaci yasa shi ficewarsa, tace wlh bazan yarda ba, ita in tana da matsalar baka tsayawa ka saurareta ne, sai ni da ban Isa ba, sau nawa kake shiga Kai zamanka ran girkina Amma ynz ni zaka kasa sauraran nawa izunin, har waje ta leko tana Abban Khadija! Sai kwala Masa Kira take Bai saurareta ba, ya shige ya gane tsaf kishin ne ya tashi, yace ai Daman Mai Hali Bai canza shi...


Ko da ya shiga ciki a falo ya taddasu suna wasa da yaranta, har da ita, suna wasan buya, sai a rufe ma daya ido in ya Kama mutum to yaci, a haka ya samesu wasan kuwa ya birgeshi, don Basu ma San ya shigo ba, sai da suka ji tafi raf-raf, sbd itama ta buya a bayan kujera, sai suka Fara ihun ganin Abbansu suna daddy oyoyoh, shi kuma ya hau daukan kowa daya bayan daya, Yana ajewa sai akazo kan madam, yace kema taho in daga ki, ta noke Kai Tai Masa nuni da yaran, tunda idonsa ya Kai kanta ya kasa saukeshi, yau shigar Riga da siket na lace tayi Tai daurin dankwali Wanda ya zauna daram kamar gwaggwaro, tayi kyau nesa ba kusa ba,Tai Masa sannu da zuwa ta amshi jakar hannunsa ta Kai daki shima Yana biye da ita a baya Yana yaba irin kyawun surarta, Yana godiya ga Allah da yabashi mace kamar Maryam....ruky kuwa idonta akai tana lekowa ta wata Yar kofa....


Har sai da taga shigarsu daki ta dawo ta zauna tana ta sauke ajiyar zauciya kamar zata hadiyeta, wayarta ta dauka ta Kira no shi alokacin har ya shiga wanka, Koda maryam taga ruky ce sai ta dauka, tace ya shiga wanka Tsaki ruky Tai ta katse wayar tana Allah Allah ya fito ta Kara kiranshi....



To ko Kiran me take Masa oho....???





Muje zuwa


*Taku*

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Story & written*



*By*



*Ummu Ameer* 💃




*Page* 4⃣9⃣












"""""Kiranshi take ba kakkautawa shi Kuma baya tare da wayar suna can dining suna cin Abinci, baiji Kiran ba, Kuma Yana fitowa daga wankan Maryam ta Gaya Masa, yace zai kira, sai Kuma ya mance shaf da zancen wayar.


Sai knocking suka ji anayi, ya tashi ya je ya bude, Yar aikinta ta turo da Bata wuce shekara 11ba wai yazo inji Rukayyah yace kije gani Nan zuwa.sai da ta Aiko sau 2 kafin yaje.


Komawa yayi ya gayawa Maryam zai je yaji ko meye, tace toh!

yana Isa ya sameta tayi wani Afujajan lokaci daya..duk ta sanyawa kanta damuwa tayi wani iri kamar wacce ta shekara tana jinya, dama ita jiki ba jiki ba, ga rashin kwantar da hankali, shima kanshi daya karemata kalloh sai da ya tausaya mata, Yana shiga ta fashe da kuka wai ka kaini asibiti numfashina

Please Login or Register in order to submit comment