Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻






*Story & written*




*By*




*Ummu Ameer* 💃





*Page* 4⃣0⃣







Hakanan rukayyah ta hakura ta saduda ta kwantar da hankali, Amma har ynx bata taba yi Masa zancen ko Maryam na da ciki ba, hasalima Bata son tuna hakan sbd tana dadewa cikin bakincikin hakan...sai dai itama ta dauki aniyar daukan cikin , dama tana allura Amma shi kanshi Bai sani ba, a boye takeyi, sbd ta nuna tana son Yi yace a'a Yana da illah, Amma Taki Jin maganarsa sbd a lokacin tana cin karenta babu babbaka, a lokacin Bata da niyyar sake haihuwa kusa sai ta huta, ta mori rayuwa, Amma tunda ta kyallara idanuwa akan cikin maryam, ta sake tunani..


Shiyasa ynx tace bazata Kara zuwa ayimata ba...



Maryam kuwa ciki ya Kara girma sosai don a yadda take cikinta baya wani girma sosai, Amma wnn tunda ya Kai 7month sai kace kafin gobe ta haihu, yayi girma ba kadan ba, gashi yayi Mata nauyin da Bata taba Jin irinsa ba, wani zubin har kirjinta take Jin cikin, gashi ko tafiya da kyar take yi don nauyin cikin gashi Sam Bata iya rike fitsari don in Bata hanzarta ba ma kafin ta Kai toilet ya zubo mata.



Har scanning suka Kara yi don tabbatar da lfyr cikin aka tabbatar da lfy shi normal, har sex din ya fada musu cewa baby girl ce.....hakane yasa tun daga hospital din suka biya sayen kayan baby girl, komai pink suka siya takalma ne, bandana har da gown masu kyau da tsada, haka suka dawo da Kaya niki -niki, ko da suka dawo rukayyah na leken su ta window ana ta shigar da Kaya, anan ta tabbatar da lalai ta kusa haihuwa ...ga bakin cikin kayan da aka dinga shiga dasu ...tace ko Khadija Bata samu haka...duk da itace dama tace a basu da kansu zasu siya,suka je sukai son ransu suka saya masu arha, shi kuwa baya sayan Abu Mai arha sai ya duba tsadaddu masu kyau sannan ya dauka, shiyasa in yaran suka Sanya Kaya kowa sai ya dinga Santinsu wai Ina suke samun kaya haka masu kyau...



Sai da taga wucewarsu har da Maryam taga katon cikin take gabanta gashi tayi wani haske kamar baturiya..Bata karasa kallonta ba don bakinciki ta koma ta zauna...




*******. ******. ******


Yanxu Kam ruky ta shiga hankalinta sbd ynx Abbas baya raga Mata ko kadan, sbd yaga haukanta bana karewa bane, ta dauka tsoronta yake ji..ynx Kam baya daukan shashanci...shi yasa ta nutsu ta rage haukan nata, ta nuna Masa cewa shine gatanta shine rayuwarta bazata taba rayuwa bashi ba, ta Saba da kulawarsa...




Maryam kuwa wani irin ciwon kafa take fama dashi in ya Fara yi kamar ranta zai fita don azaba, ko da suka je hospital aka ce nauyin babyn ne ya danne Mata cikin, sai dai tayi hakuri har Allah yasa ta haihu lfy...Amma tana Shan wahala sosai ...



Ranar wata laraba ciwon kafar ya takura Mata kamar me, gashi Yana gidan ruky...maryam kuwa ta kasa jure azabar ciwon sai wani irin nishi take kamar me nakuda duk ta fita hayyacinta don ana Jin saitin shi har waje ...kamar a mafarki Abbas yaji sautin ya farka a firgice ya kasa kunnenshi Yana jiyowa kasancewar a falo take ta kasa kwanciyar a daki, itama hafsa Jin motsi. Maryam din ne ya fito da ita,dake tana gidan tinda cikin ya tsufa dama ba iya wasu aikin take yi ba...tana kusa da Maryam din tana Mata sannu, sai ganin Abbas sukai ya shigo a firgice yace lfy hafsa me ya sameta tace wlh kafar ce ta matsa Mata da ciwo tun dazu ganin halin da Maryam ke ciki yace bari in fita da mota kawai muje Asibiti, cikin sauri ya fito da motar, ya dawo suka kaita mota tare da hafsa...Jin karar motar Abbas ne ya farkar da ruky, ta duba taga bashi a gadon Aiko ta mulmulo wani katon ashariya tace ni za'a ci wa Amana haka ta fito harabar wajen daga ita sai Riga da wandon bacci, wando iya gwiwa sai karamar rigar baccin kanta ba dankwali, kafin ta fito ya figi motar da gudu...

Nan ta tsaya tana takaici, tare da cixon yatsa....dubanta takai ga kofar shiga gidan Maryam ta ga hafsa tsaye a bakin kofar cikin matsananciyar damuwa...karasawa tayi wajenta kamarabin arziki tace ke Ina yayarki sai da hafsa ta dau mintina kafin ta amsa Mata tace sun je asibiti, maimakon ta jajanta sai cewa tayi Ashe za'a ga tashin hankali a gidan nan, ta nan Kuma ta bullo da makircin nata tsakar dare zata dauke min miji tsabar makirci to wlh sai na nuna mata ko ni wacece munafukar banxa masu bin bokaye...


Hafsa sbd takaicin shirmenta komawa ciki tayi ta maida kofa ta rufe cike da tausaya yar'uwarta wnn mahaukaciyar kishiyartata ....





Haka ta karaci shirmenta ta koma ciki taga ba maijinta, ta zauna zaman jiran dawowarsu...taso ta kirashi a waya sai Kuma ta ga wayar tasa a gida ya manta ...

duk a karfe 3na dare....


Koda isarsu hospital Dr. Ya tambaya watannin cikin suka Gaya Masa 8m da kwananki, yace a shiga da ita metron zasu duba ta, ko haihuwa don wani lokacin ta kanzo a haka da ciwon kafa, yace haka ma wata patient tayi Kuma ana dubawa akaga haihuwace.

Bayan an duba aka tabbatar da cewa ba haihuwa bace, Dr. Yace sai dai ya basu magingunan da zasu taimaka Mata wajen rage Mata radadin ciwon, haka akayi har allura akai mata, suka taho Kuma cikin ikon Allah ta samu relief, don ynx ma da kanta take takawa, daxu kuwa ko tafiyar Bata iyayi sai daya riketa tana dingishi...





Suna Isa gida yace ta danci wani abu tasha maganin, ya Bata tea Tasha kadan ya Bata magunguna, yace ta shiga wanka ko taji dadin jikin nata...daga Nan ya wuce wajen rukayyah lokacin assalatu tayi...

Yana shiga yaci karo da mutuniyar a zaune ta cika fam kamar ta fashe don haushi don idonta kaf akan dawowarsu....


Yana shigowa ta tashi ta Sha gabansa tana yau dubunku ta cika munafukai Azzalumai kawai maciya amana....a fusace ya daga hannu zai zabga Mata mari sai Kuma ya tuna baya ....ya fasa Amma ya dinkule hannu Yana huci kamar Zaki....ita Kuma ganin hakan sai ta samu karfin gwiwar ci gaba da rashin kunyar tana fadin dake ni tana tura Masa jikinta ka dakeni nace in ka Isa Dan halak ne kai, shi kuwa ranshi ya gama baci karshe da munanan kalamanta, ta cigaba wlh yau da ka Kara tabani sai na kullah maka sharrin da bazaka iya fita ba, wlh sai kotu ta rabamu da Kai.. jaka aka kawo maka ko tinkiya ..aikin banza kawai Kuma itama sai na nuna Mata cewa ruwa ba sa'an kwando bane kawai ka goya Mata baya tana yiwa mutane Abinda taga dama...ganin ya wuce tuni ya barta a wajen yasa ta bishi dakin tana bugawa ya bude ya Sanya key, yai Mata banza, sallah yayi ya kwanta domin bacci ne a idonsa sosai.

Itakuma gajiya tayi da bugawa ta zame kasa ta zaman dirshan a wajen tana kuka ...ta fara tuno mommy tace nasan da Baki tsame hannunki a kaina ba da ban Zama wukantata ba a gidannan, Nan ta Fara kuka tana Kiran mommy kiyi hakuri ki yafeni na gane kuskurena wlh na tuba...

Nan ta karaci kukanta har gari ya karasa wayewa, yai wankansa ya shirya tsaf ya fito zai wuce aiki, itama data ga uwar Bari tashi tayi tai wankanta Amma batayi break fast ba, ita a dole an Mata laifi, shi Kuma ganin tana bacci ne yasa Bai tasheta ba, Kuma Bai dauka Abin ya Kai haka ba, shiyasa ma ko wayarsa bai dauka ba.


Yana fitowa Bai saurareta ba, Khadija kawai yaiwa wasa yai fice, tana ji tana kalloh, tace lallai wannn shine karfin hali ga duka ga Hana kuka ...



**********************
Bayan kwana 2 da faruwar haka, basa mgn da Abbas baya cin girkinta itama Kuma ta Dena yi, wai harda fadin ka hutassheni.



Ranar daya koma gidan Maryam a wnn Daren ma kafar ta Kara tsananta Mata Batai bacci ba, ita da shi, yace ta tashi suje hospital tace ka kyaleta kawai tunda sunce sai na haihu zan daina ji ciwon....haka suka kwana zaune zuwa asuba Kuma sai ciwo ya koma Mara ta Fara Jin ciwo kadan kadan, Amma ba sosai ba, ganin hakan yasa tace suje Asibitin ko wani abun ne , Amma Bata kawo haihuwa ba, sbd ciwon ba Mai tsanani bane.

Ta shirya da kanta suka fita zuwa asibiti, Kuma a lokacin sai ciwon kafar ya dauke, suna Isa Asibitin suka ce zasu duba ko ta Fara labour, Aiko ana duba ta suka ce ai ga kan baby nan..haihuwace, ita kanta abin ya Bata mamaki sbd bata Jin ciwo a lokacin ko kadan.
Ta saba ita data ke dogon labour,inko hakane ta godewa ubangiji.


Nan da Nan aka fada Masa ai haihuwa ne maza a kawo kayan haihuwa...Shima mamaki yayi don baiga alamun nakuda ba.


Cikin sauri ya koma inda ya aje motar ya fito da akwatin kayan dama tuntuni an shiryasu, indai ta shigar watan haihuwa komai kintsa shi take sai su aje a motar shall incase sai gashi kuwa hakan yai tasiri...ai kafin ya kawo kayan sai Jin kukan baby yayi,Yana kaiwa akace ta haihu ta haifi baby boy...yai murna sosai yace ikon Allah, sbd ya tunaa scanning ance mace ce, gashi komai na Mata ne sai wani set, na overoll unisex, ai mamaki Bai gama shi ba, yaji guda ana 'yan2 ne twins ol boys, Nan aka dinga rige rigen Masa Albishir ai twins ne maza kyawawa inji wata nurse take fada masa, hmm farin cikin a gurinsa ba'a magana, Baki yaki rufuwa kamar gonar audiga, baisan sanda ya nufi dakin da gudu ba, akai saurin dakatar da shi ..yace don Allah ki barni inje ingansu plz ..akace kayi hakuri in an gyarasu sai ka shiga kaga abinka, tunda duk suna cikin koshin dasu da mahaifiyarsu....


Haka ya hakura ya kyalesu, farncikinsa kuwa yaki boyuwa mutane sai taya shi murna suke yi..Shima har ya bugawa yan'uwa da su ummi kowa sai murna yake bare da suka ji ance lfy suke gabadayansu.



Amma Bai fada was ruky ba...


*To ruky hassada ga Mai tabo Taki*🤷🏻‍♀






To reader's ku biyoni don Jin Yaya ruky zatayi idan ta samu labari..



Muje zuwa

*Ummu Ameer* 💃.




















.
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Story & written*




*By*




*Ummu Ameer* 💃





*Page* 4⃣1⃣




* I really appreciate ur comments masoyana Allah ya bar kauna*😘





''''''''' cikin kankanin lokaci lbrn haihuwar Maryam yaje kunnen 'yan'uwa da abokan arziki...ruky kuwa ba labari....sbd ko da taga sun fita Bai Gaya Mata ta Kara Jin haushi wai ya fita Bai sanar da ita ba shiyasa Taki kiransa, Shima Kuma Bai Kira ba, Yana sane da Kiyayyar da take da cikin Daman shiyasa yaga Bata cancanci taji ba...



Shiko Abbas Yana makale da yaransa ya dauki Hassan din Hussain din Kuma na kwance kusa da Maryam, sai kallon yaran yake cike da kauna Yana yiwa Allah godiya da wnn kyauta da ya masu, yaran jajir dasu kamar larabawa gasu lafiyyayu dasu, sai faman sannu yake mata ganin haihuwa yara 2 a lokaci daya, Yana kuma jinjina Mata tare da godewa ubangiji da ya Basu kyautar da basuyi zato ba...


Sai daukansu hoto yake har da ita mejegon sbd in ka ganta bazakai tunanin ma itace ta haihu ba, garau da ita...sbd Bata ma taba Jin karfin jikinta ba a haihuwarta ba kamar wnn, har tana cewa Abban mufid kaga ikon Allah ko?
A scanning suka ce baby girl, sai ga twins boys...yace ikon Allah ne kawai sai kiga wani lokacin Allah bai Basu ikon ganin dai-dai ba, hasashe ne kawai.


Tace to kayan fa? Na baby girl da muka kwaso? Yace anjima zan canzo masu.




Kan kace me yan'uwa da abokan arziki da suka ji lbr duk sunxo asibitin, har su ummi da Abba sunxo ganin jikokinsu, murna a cikinsu kamar me...





Sai wajen karfe 5na yamma aka sallamesu suka taho gida...tare da yayar Maryam da ta dauki Hussain Maryam Kuma na dauke da Hassan.





Ruky na zaune jiran dawowarsu don ko kadan batai tunanin haihuwa bace, tana zaune taji karar motarsa ta tashi don yin leken da ya zame Mata jiki...



Me zata gani...?

Maryam ta haihu? Mamakinta Bai kare ba,sai da ta ga yara 2 daya a hannun sis din Maryam 1 Kuma Abbas ya dauka, kara goge idonta tayi Wanda take tunanin yana Mata gizo, Amma hakan dai take Kara gani...wata zuciyar tace to ko dayan na waccan ne tana nufin Yayar maryam.


Sai tace Anya Kuwa.... tana Nan tsaye cike da wasi-wasi a zuciyarta har suka shige suka barta cikin duhu...


Kasa zaune tayi tana ta so ya shigo ta tambayeshi...zuciyarta sai dukan 3 take yi.


Ba jimawa kuwa sai ga Abbas ya shigo dauke da wani irin farincikin da ta mDade Bata ganshi a ciki ba, Nan ciki ya Kara durar ruwa, sbd son Jin gulma ko gaisheshi bata Yi ba ta hau tambayar haihuwa tayine me ta Haifa? Ta tambaya cike fa fargaba,
Yace wlh kuwa mun samu karuwa Maryam ta haifi twins Kuma duk maza lafiyyayu, ya fada cike da doki da farinciki Mara misaltuwa..


Wani irin zare ido tayi tana cewa me? Ya Kara maimaita Mata..Bata San lokacin data saki wata Kara ba, tana cewa No! Tare da zubewa kan kujera shirif jiki a mace.


Ta mance shaf Yana wurin...yace No what!

Sai a lokacin ta dawo hankalinta ta wayance da rike ciki tana cikina Abbas ciwo Wayyoh cikina....sai ta kwasa a guje ta shige toilet cike da tsoron Allah yasa bai ganoni ba....


Shiko tana shiga yai murmushi ya ganota tsaf ba tun yanzu ba, ficewa yayi ya koma can wajen Maryam.




Ruky kuwa bata fito ba, sai da ta tabbatar da baya Nan ta fito tana goge xufar data cika Mata fuska kamar wadda Tai wasan dambe, tana fadin yau na Banu ni ruky Yan 2 ta Haifa ...tabdijan ai shikenan Kashi na ya bushe mun gama Zama Bora ni da diyata, Maryam ta gama samun wuri a zuciyarsa....yadda nake masifar son twins Amma ace matar da nafi tsana itace ta Haifa masa su...shikenan ynx Kuma sai abinda yayi gaba....

Har ta janyo waya zata Gaya wa mommy sai ta fasa sbd har ynx mommy Bata Bata fuska ko xuwa tayi daga gaisuwa Bata Kara shiga sabgarta, saidai suyi ta hirarsu da kanwarta Aisha.


Sai tai dialing no. Farida tana dauka ta Fara Bata labarin kishiyarta ta haifi twins duk maza...cike da mamaki farida tace da gaske? Tace wlh ynx Nan suka dawo daga asibiti, ruky tace wlh danaji lbr kusan zaucewa nayi don bakin ciki...farida tace name Kuma Kinga gara ma ki saduda ki dauke kishinki akan haihuwarta gashinan kinxo kina kyashi tana d ciki sai gashi Allah ya Bata kyautar 2, tace kawai kema ki addu'a Allah ya baki twins din tunda so kike ki Zama mama...ta karashe maganar da dariya.


Tace wlh Nima Ina bala'in son twins da Allah zai bani a haihuwar farko Kinga shi kenan na gama...ruky tace dakata da Allah na fuskanci ynx kin canza tunaninki akaina in ba haka ba, nakiraki ki tayani jaje kina min wani soki burutsu.. .


Farida tace kamarya ...so kike nace ki kashe su ko me? Ni Banga dalilin d zaisa ki damu kanki akan haihuwarta ba, sbd matarsa ce, in Kinga kema kin shirya zazzago Masa ne bissimillah Mana waya Hana ki...ni wlh bana dorawa kaina wnn wahalar ba abinda zaisa ni damuwa da haihuwar kishiyata...ni dai barni da Kama miji da kuma makirci na, don ni bama zan Bari har yaje gareta ba, balle haka ta faru, in ma ta faru to ko ajikina tunda bani zan haifar Mata ba, ita zata ji ajikinta ..


To gara ma ki cire wnn a ranki kici gaba da gudanar da Abinda kika fara,in kuma kema kin shirya haihuwar ne to Allah ya baki Yan 4.

Rukayya tace bazaki ganeba, shikenan kawai ...farida tace sai munxo suna ta fadi da zolaya . Ruky ta kashe wayar tana tsaki...






Tunda akai haihuwar ruky Bata je taga twins ba, ba yadda baiyi da ita ba, sai tace to zan shiga, sai lokacin shigar yayi sai tace wai cikinta na ciwo..har akai kwana4 da haihuwar, Kuma kullum a gidan yake kwana, sbd tunda Maryam ta haihu ta nemi alfarmar ya koma wajen rukayyah har Allah yasa yaran sun dan kwana 2, sbd abubuwan suna mata yawa duk da hafsa tana gidan ga Kuma wata da aka kawo Mata don taimaka Mata da rainon yaran, ga kuka in wnn ya Fara sai wnn Shima ya kama, sai duk ta rikirkice.

Haka Nan ya hakura ba don yaso ba, itakuma ruky da farko kin yarda tayi tace sai ynx da tasan Bata da mamora ne zata turoka, to bazan yarda ba, nima aikin yawa yake min, har ya zuciya zai koma Kuma sai ta lallabashi ya dawo tace ai dama ce na samu da zan gama kamashi kafin ta warke...



Sai ana gobe suna ta shiga gidan Jin ance Yan danbatta zasu xo yau, Kar azo a Dora Mata laifi yasa ta shiga, ko da ta shiga ma ko daukan yaran Bata yi ba, har an dauko Mata sai tace barsu kawai na gansu daga Nan...duk da Bata daukesu ba Amma ta hango su yaran tubarkallah son kowa..Bata jima ba ta tashi ta tafi...Maryam batai mamaki ba da Abinda ruky tayi tasan zatai fiye da haka ma..sai sis dinta dake dakin ce tace haka kishiyartaki ke da bakin kishi haka, bako Kara..take bayyana shi a fili?
Maryam tace haka take wlh kinsan kowa da irin nashi kishin...sis din nata tace wane irin kishi hauka dai..waye bashi da kishin? Ai dannewa ake musamman ma agaban kishiyar, Amma ita shine nata ya fito fili a bayyane...

Maryam murmushi kawai tayi tace hmm Allah dai ya kyauta Aunty..tace ameen dai.



Zuwa yamma gida ya cika da yan'uwa Yan danbatta, har da su Yaya babba tace ita ai a wajen ruky zata kwana...bayan an gaisa din wnn karon ta rage Kiyayyar Maryam a ranta ko don taga ta haifi Yan 2 ne oho! Don da farinciki ta shigo...tana manne da yaran.


Bayan sun gama gaisawa ta tafi wajen ruky ita datawagarta su biyar...suna shiga gidan ruky ta karbe su hannu 2, kasancewar Yaya babba mutuniyarta ce..

Tana ji sunce ai anan zasu kwana Nan take ta dauke wuta Tai dif duk sun fahimci hakan, sai ta Fara inda inda tana cewa ba isasshen waje ai Anty...eh ba komai ai sai muyi kwanciyarmu anan. Ruky na Jin haka ta tashi ta shiga daki tana kunkuni wai wlh bazasu sani wahala ba, ni ba da haihuwa ba, sai a barni da wahala wlh bazan iyaba . Tana cikin maganar sai ga Abbas ya shigo Yana lfy na ji kina magana ke kadai ?

Sai tace wai su Yaya ne zasu kwana anan shine Naga kuma ba wadatataccen waje....yace badai ki Fadi masu hakan ba ko?

Sai Tai karyar eh!

Yace kyalesu Mana yau dai 1 tunda ba anan zasu dawwama ba, haka Nan ta hakura Amma bata so ba, don ma kawai suna dasawa da yayan ne inba hakaba wlh ba Wanda zata Bari ya kwanar Mata. Abincin data kawo masu plate 1 ko mutum 2 bazai Isa ba.


Hakanan suka hakura sai daga baya wata daga cikinsu ta amso musu a wajen Maryam....Aiko ta Sha zagi wajen su, suka ce wnn matar da ita kadai ce wajen Abbas ba Wanda ze ziyarceta, gaskiya baiyi dace da matar kwarai ba wlh...itama Yaya taji haushi domin kuwa harda kawayenta daga ciki ta taho dasu, Kuma ta kunyatata a gabansu...Amma dake har ynx Bata cika ganin laifinta sai ta basar kawai...2 daga ciki kuwa fir kin kwana sukai suka koma wajen Maryam, suna ai ga Yar mutunci anan...




*******************

Washe gari ranar suna gida tun safe ya cika da mutane, sunyi shawara akan a bar musu sunansu wato Hassan da Hussain. mejego ta sha kwalliya kamar ba me jego ba, sai kace amarya don musamman aka dauko Mai make -up tazo tana Yi mata, Shima ango ba baya ba, anyi order abinci kala-kala kamar gidan biki, duk inda mejego tayi sai wani kyalli take,..ruky kuwa kasa shigowa tayi don bakinciki, sai leke ...sai da farida tazo ta takura Mata akan su shiga itama don taga me jego da yaran, kwalliya farida Tai Mata itama ta Sanya wata super Riga da siket.ta yafa mayafin kayan orange, suka shiga gidan...ai Bata Kara sirewa ba sai da taga Maryam cikin wani dankararren lace Wanda kana gani yasha kudi ba kadan ba, ya amshi jikinta sosai tayi parking din kanta a tsakiya an Masa doughnut, an daura Mata dankwali irin me Hawa Hawa din Nan kamar amarya tayi kyau sosai...da ruky ta ganta kasa magana tayi, sai farida ce ta gaisheta Tai Mata barka dake ita tafi ruky iya duniyanci ta wani saki jiki kamar tasan Maryam har da daukan baby's din tana fadin Masha Allah, yara kyawawa, Aiko ruky ta wani balla Mata harara.

Ruky dai ba magana don ko gaisheta batai ba, sai daga baya Maryam ta tuna basu gaisa ba, sannan ta gaisheta, ta amsa da kyar fuskar Nan ba annuri, ga kishin kashe kudin da akai kamar yau aka Fara haihuwa a gidan, a zuciyarta tace lallai Abbas ya Raina min hankali Amma zamu hadu...ganin farida ta zake da yawa yasa ruky tace tashi mu tafi...suka Mika Maryam ta cikawa farida take away aleda Tai Mata godiya suka tafi....suna fita farida tace Kai Amma gaskiya yaran nan Masha Allah kamar in sace su. ...wlh sun bani sha'awa, harara ruky ta bata, tace wlh kin bada ni kawai kina shiga sai ki zake ki hau surutu ..mtsss tayi tace ni ban ma fahimceki ba? Meye amfanin yin hakan ...farida dariya tayi tace wlh kina bani dariya Baki iya zaman duniya ba, so kike in biye Miki agaban kishiyar in nuna kishina don HAUKA ?
Lallai da sauranki shiyasa har ynx Baki nasara akansu ba, sbd gajen hakuri da rashin iya danne kishinki tabdi wlh da sauranki ruky ...

Ruky a fusace tace ba wani nan gsky ni banji dadin abinda kikai ba ...tace to kiyi hakuri bazaki Kara ganina ma agudanki balle kimin haka..ta fasa rain bace.

Ganin ran farida ya baci ta janyota tana fadin yi hakuri besty nah, muje ba haka nake nufi ba, hannunta ta riko suka shiga cikin gidan tace muje ki yi min wata lecture....





Muje zuwa


*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻





*Story& written*



*By*


*Ummu Ameer* 💃





*Page* 4⃣2⃣





Suna shiga cikin gidan ta jata daki ta Sanya key gudun Kar wani ya shigo ya shammace su...


Dukansu Zama sukayi a gefen gadon suna fuskantar juna, farida tace wlh kin bani haushi har na Fara tunanin fita harkarki tunda baki daukan shawara...ruky tace kiyi hakuri kawata wlh idona ne ya rufe kinsan ni akan kishi...



Murmushi farida tayi tace Banga laifinshi ba, akan abinda yake Miki..ko kinsan Namiji ba abinda ya tsana ga mace kamar nuna tsantsar kishi akansa, ko zakiyi ma to karki Bari ya gane hakan sbd matukar ya fahinci haka akwai matsala....kinganni nan duk zafin kishina Ina iya controlling dinshi ban taba nuna Masa shi ba, bantaba nuna Masa Kiyayyar matarsa a fili ba..inkinga yadda nake nuna kauna agabansa akanta Abin sai ya Baki mamaki ..shi yasa shi Kuma ya dauki yadda da Amana y doramin ynx ko wani ne yace Masa zan Yi abinda nake a bayan idonsa bazai yarda ba, ke wani lokacin ma Nike bashi shawara akan ya Dan gyara halinsa akan matarsa Nan ko Bai San nice silar komai ba, shiyasa nace Miki ni ba boka ba mallam kawai basirata ce ke aiki.

Amma ke na fahimci kina da gajen hakuri ga shi Baki iya danne kishinki ako ina, kinje wajen Mata ko magana Baki Mata ba, kin nuna kiri-kiri kishin yaran kike, kuma na tabbatar Shima kin nuna Masa hakan,sannan kike tunanin har ki samu matsuguni a Zuciyarsa, sannan Nima kike so in biye Miki mu Zama mahaukatan gabadaya...


In Zaki canza taku ki canza tun wuri kafin lokaci ya kure Miki ki daina nuna tsanarta a gaban mutane duk da dama ba zancen so ga kishiya Amma ki iya takunki sai kiyi galaba, itama din ai ba sonki take ba, Amma na tabbatar Bata taba nuna Miki a fili ba, sbd iya kissa kin zauna yarinya karama tafiki wayo....


Hmmmmm doguwar ajiyar zuciya

Please Login or Register in order to submit comment