Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba hada inuwa daya da kishiya wlh, mayaudari kawai.. Yasan ba zai iyaba ya debowa kansa, ruky kuwa sai kuka take tace Allah ya isa.. Tsakani na da Abbas ya cuceni yaci amana ta, Allah sai ya saka min..

Mommy tace wnn kuma duk abinda yai miki ke kika jawa kanki ba, abinda nai ta hango miki kenan kika rufe idonki akansa, ai ga halacci nan yana ta binki dashi...



Washe gari da safe ta kira shi a Waya tace suna jiran takarda in ba haka ba kuwa ya jirayi sammaci a kotu..

A zuciyarsa ko yace ai ba sai ta kai ga kotu ba, cikin ruwan sanyi zaku samu..

Itako tuni ta katse wayar ta, sai faman bala'i take ita kadai kamar tababbiya..

Rukayyan ma duk ta tashi hankalinta ya gagara samun nutsuwa, sbd tana son mijinta amma bata jin zata iya zama da kishiya.. Kishiyarma wadda ta gama mallake mata masoyi, ta hana shi ganin kowacce da gashi sai ita! Ina bazai yiwu ba da ta kasance bora gara ta hakura da shi har abada.. Wata zuciyar kuma ke zugata idan na barshi ai dadi zata ji na barmata shi..

Idan ko haka ne sai na bi duk wata hanya da zai canja ra'ayin hadani da munafukar matarsa..

Ta kasa samun nutsuwa itace buge bugen Waya wa yan'uwansa wai yaci amanarta ya yaudareta ya karya mata Alkawarin da ya dauka tun kafin aurensu, har yaya ta kira yace tayi hakuri zai samu Abbas din komai zai daidaita insha ...

Sai a lokacin ta ji sanyi a ranta sbd tasan Abbas yana jin maganar yaya baya ketare maganarsa..


Bayan sun gama magana da Rukayya ya bugawa Abbas in ya tashi daga office ya biyo yana son ganinsa, yace toh.


Itama maryam tana cikin fargaba, don kwata kwata ta kasa samun nutsuwa tunda ya bujuro da wannan lamarin, amma dake tana da Saurin fahimta yai ta lallashi da ban baki yace insha Allahu ba abinda zai jiyo baya sai Alkhairi.. Ta kwantar da hankalinta ba abinda zai canja haka nan ta hakura ta mika lamuranta ga ubangiji, don tasan ko bata hakura ba ma ba canja ra'ayinsa zaiyi ba in ya kafe akan Abu daya bai canjawa..


Yaje ya sami yaya sun tattauna akan batun inda Abbas din ya gaya masa Alfanun hadawar da zaiyi, ba yadda yaya bai yi ba amma ya kafe akan ayi hakuri a kyalleshi shi yasan inda ke masa yoyo!

Hakanan yaya ya hakura ya kyaleshi yace toh Allah ya sa haka shine Alkhairi a gareku baki daya yace Ameen!

Har gidansu Rukayyan yaya suka je shida amininsa, amma mommy ta rufe ido tace ta gama magana in bazai fasa hadasu guri daya ba, to ya sakar mata yarinya..

Da yaga bata da shirin saurararsu sukai tahowarsu cike da mamakin wannan suruka ta Abbas, ko me ya kaishi kwasowa kansa irin wadannan mutane!

Inda Abbas din Yace gara kawai ya sawwake mata tunda haka suke so... Yaya ya hana shi yace ka zamo mai juriya a rayuwa jarrabawa ce Allah yake maka kayi kokari ka cinyeta..


Haka dai ake ta fafatawa shi ya tsaya tsayin daka magana ba fashi ba Abinda zai canja... Suma su mommy sun kafe diyarsu bazata zauna da kishiya ba.. Sai dai ya saketa..


Magana har taje gun mahaifinta ransa ya baci da abinda suke ita da mahaifiyarta, yai ta yi mata fada akan lallai ta gaggauta komawa gidan mijinta kafin ranta ya baci, mahaifiyarta ko ta hana tace ai ba shi zai zauna miki da shiba, ya kyaleta itama tana da iko akan yarta..

Har Abbas ya bugawa yaita bashi hakuri akan abubuwan da suke faruwa yace ba komai daddy kar ka damu komai zai daidaita..

Yana matukar respecting dinsa sbd mutum ne mai dattako Albasa ce bata yin halin ruwa ba..

Haka ya hakura ya zuba musu ido tunda ya fahimci ta biye wa mahaifiyarta, shima Abbas din kyalesu yayi..


Itako mummy tuni ta sanya an kwashe kayan rukayyan daga gidan shima yaje ya kwaso ragowar tarkacensa ya kulle gdn ya basu mukullan gdn.





Tofa masu karatu zamuga waye zai yi wining tsakanin Abbas da su mommy...




*ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻







*story&written*



By



*ummu Ameer* 💃







*page* 2⃣5⃣






""""Dukansu sun kafe akan magana daya kowa ya tsaya Akan maganarsa, da mahaifin rukayyah yaga Basu da niyyar bin umarninsa ya zame hannunshi daga ciki, sai daga baya ne kuma ya sami Abbas din akan cewa indai akan gida ne, to yaje ya sami gida mai kyau su zasu dauki nauyin biyan kudin haya, Abbas yace masa kayi hakuri daddy nima ba gagarata sukai ba kawai dai Ina son hada Kan iyalina ne waje daya.. Da dai daddy yaga ya kafe ya hakura ya kyaleshi, daman kuma kafin ya fara yi ma Abbas din magana sai da ya fara yima ruky, tace daddy dama matsalar kenan in dai ya janye ra'ayinsa xan koma amma ni bazan zauna da matarsa ba, saboda ta Riga ta asirce shi abinda tace shi yake yi.. Yace ya isa haka nan ki dinga yiwa mijinki kyakkyawan zato.. Kar ki debo halin mahaifyarki.. Toh tace masa sukai sallama..



Ko da rukayya taji labarin yadda sukai da daddy ranta ya matukar baci ba kadan ba, tace sai ynx na fahimci bawan Allah nan ba kaunata yake ba, neman hanya yake da ita, lallai kuwa Abbas ya cuceta gashi ya barta da ciki, Waya ta masa tai masa tas ba irin rashin mutuncin da batai masa, kuma tace in ya isa dan halak ya gaggauta aiko da takarda... Ranshi ya baci da kalamanta, ya harzuka sosai don har ya fara ayyanah sakin tuno da nasihar yayansa da kuma darajar mahaifinta take ci, in ba haka ba da tuni ya yarda kwallon mangoro ya huta da kuda..





Daga karshe suka hakura suka kyaleshi shima haka, sai da cikin ya kai 9month ne suka turo masa list din kayan haihuwa, cikin gadara suka rufe ido ba tausayi sukai masa list na mugunta tun daga Kan kayan baby har na fitar sunan mejogo, ko da ya gani yasan suna sane suka shirya wnn muguntar, shiko cewa yayi Abinda naga zan iya shi zanyi...


Ya sayi duk Abinda ake bukata daga Kan baby zuwa ita mejogo kuma ba laifi ya yi bajinta, domin shi duk abinda zai siya tsadadde ne, komai hassada sai an yaba, amma dake sharri suke binsa da shi sai cewa sukai ai kaya Basu yi ba, yace yayi abinda zai iya.. Aiko mummy ta kira ba ko kunya har da su zagi wai matsiyaci in ba kaddara ba, ai diyarta tafi karfinshi... Shiko katse kiran yayi don bazai iya jurewa ba, idonshi ya kada yayi ja don bacin rai.




Har tana cewa in ba kaddara ba, Ina Ke Ina hada zuriya da wnn dan kauyen.. Shiyasa tun farko naso ki zubar da cikin kika ki yadda.. Ai gashi nan ya barki da wahala..




Bayan sati biyu ta haifi yarta mace tasha wuya sosai don har an fara tunanin yi mata c.s Allah ya sa ta haihu da kanta, tace wa mommyn kar a gaya ma Abbas don ta Riga ta cire shi a rayuwarta bai cancanci zama uban yarinyata ba,

Mommy tace uban wa zai dauki nauyin biyan kudin asibitin ai kwandala ba zan kashe akan yarinyarsa ba, domin asibitin da ta kaita haihuwar ba karamin tsada ne dashi ba, tana sane ta shirya muguntar..



A take ta kira wayarsa ta shaida masa ta haifi diya mace, kuma ya gaggauta zuwa Ana nemanshi a hosp. Ta gaya masa asibitin da suke.


Yayi murna kwarai da jin haihuwar sbd yana da son yara, amma da ya tuna halinsu sai farincikin sa ya ragu.

Ya sanarwa da maryam itama tai masa murna da fatan Allah ya raya.. Tace elham anyi kanwa ko.


Tashi yayi ya kintsa ya shirya domin zuwa asibitin amma duk ranshi ba dadi sbd yasan sai ya fuskanci bacin rai daga wajensu, haka nan ya tafi jiki ba kwari.. Ya dan tsaya yai masu siyayyar abinda yasan zasu bukata.


Yana isa asibitin ya hadu da kanwarta tai masa jagora izuwa dakin da suke a lokacin mommyn bata nan, ta fita waje.. Ya sameta kwance babyn kuma na kusa da ita.. Ya karasa ya dauketa yana ta murmushi, yai mata huduba da sanya mata suna khadijat, itako ko kallon shi batai ba, yana tai mata sannu da jiki amma ko tanka masa batai ba, ita adole fushi take da shi..

Bayan wasu mintuna mummy ta dawo tare da shaida masa yaje ya biya bill za'a sallamesu ynx, yace toh, fita yayi yaje aka bashi bill an caje shi kudi mai yawa ba yadda ya iya haka nan ya biya, yace su zo ya sauke su a gida. Suka fara harhada kaya suka tafi..

Bayan isarsu ma haka ta Kara cajar shi kudi wai ko da bukatar wani Abu ya taso a zuciyar shi ko yace ko baki fada ba zan bayar.. Yai musu sallama ya wuce, ya gaya musu sunan yarinyar...




Bayan kwana uku yace wa maryam ta shirya ya kaisu suga baby...shiru tai na seconds sai can ta amsa da toh! Ji tayi tana fargabar zuwa sbd tasan rashin kirkinsu ba abinda baza su iya ba.. Kuma ma tunda da Abbas din zasu ai da sauki, ta tashi ta shirya cikin wata super red fa mayafinta red tai matching colour, tayi kyau sosai don bazakace ma ta haihu ba, yar caras da ita, suka tafi a hanya suka tsaya tace zata sai kayan barka, ya mika mata kudi ta shiga ta debo kayan babies masu kyau wajen 5colours har da du takalmi masu kyau 2pear ta hado da atamafa guda daya..


Suna isa gidan a falon suka sauka sai bayan kusan 30 mins sannan mommyn ta fito ta tsaya daga bayan kujera suka gaisa fuska ba rahma, sai faman wurga musu harara takeyi.. Ta koma ciki tace tana zuwa saida aka kuma wata 30mins sanna n rukayyah ta fito rike da jaririyar ta zauna suka gaisa da maryam din amma fuskarta a hade ba walwala, sai Abbas dinne ya gaisheta ta amsa a dakile ya amshi yarinyar ya mikawa maryam ta amsa da fara'a tana cewa tubarkallah kuwa da girmanta Allah ya raya. Abbas ya karba ya mikawa Abbas yace ga kanwarka nan, yaro ko sai washe baki yake yaga sabuwar baby..
Mummy tana fitowa taga jarirya a hannun mufid tai Saurin karbarta tana cewa wnn wane irin wauta ne zaku dauki new born ku bawa karamin yaro don ba ke kika sha wahalar haifota ba tai tsaki ta shige ciki rike da babyn.

Abin ya sosa masa rai yace ta tashi su tafi suka mika kayan da ta kawo sukai sallama, suka tafi cike da bacin rai..


A hanya yaita bawa maryam hakuri tace karka damu ba komai ai duk Wanda yai nagari kansa.. Itama tai ta kwantar masa d hankali kar ya sa damuwar su a ransa jarabawa ce.



Ya fadawa yan uwansa na danbatta yace ba sai sunzo ba, sbd akwai yar matsala amma anty babba ta kafe wai akan me matarka ta haihu kace basai anzo ba, duk yadda yaso fahimtar da ita amma taki wai gasunan zuwa Ana gobe suna, haka nan ya kyaleta tace ai ba gayya zamuyi ba mu uku zamuzo, yace sai kunzo.



Ranar suna tun safe yaya babba aka taho gidan Abbas dake a gidan yaya ta kwana ita da dayar yayar Abbas sai kanwar mahaifinsu, yace ai ba ynx suke sunan ba sai yamma.


Maryam ma tai kwalliyarta kuma tai musu lafiyayyen girki ta kawo musu sai godiya suke mata amma banda yaya babba sai faman habaici take mata wai takori Amaryar sbd bakin KISHI ta kalailaye miji...
Suna ta hana ta amma taki ji..

Sai maryam din sukai ta bawa hakuri tace ba komai amma har ga Allah ta gaji da wnn munanan halaye da take mata kuma bata taba fadawa Abbas ba, ita dai tasan tana iya kokarinta wajen kyautata mata.


Karfe 5 na gamma Abbas yace su fito su tafi tace ita uwargidan taka bazata bane ko kishi ya hana ta zuwa.. Yace ai munje tuntuni.
Tabe baki tayi suka tafi tai musu Allah kiyaye!








*ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻




*Godiya Mai tarin yawa masoyana Ina jin dadin karfin gwiwar da kuke bani,Nima Allah ya bani ikon faranta muku*
Luv u ol😘


*Story&written*




*By*



*Ummu Ameer* 💃







*Page* 2⃣6⃣






"""Suna hanyar zuwa gidan suna Abbas ke tuka motar da Yaya babba sai anty ..da Kuma kanwar babansu goggo turai sai matar Yaya.


Yaya babba ce ke tambayarsa wai me ya hada ku da amaryar taka ne ko kuwa makircin matarka ya koreta..

Yace ba ruwan Maryam ..duk Abinda ya faru su suka so..tai saurin katse shi da ai Bata da laifi a wajenka sbd ta gama da kai ..shanyayye kawai ..

Matar yaya tace Anty Baki San abinda ya hadasu ba fa, ba ruwan Maryam ta kwashe duk Abinda ya faru ta Gaya Mata..Aiko Yaya babba tace to me zai sa ka hada ta da wannan makirar matar taka ai da gaskiyarta ..ba zai yiwu ba kaje ka dawo da matarka gidanta ita kadai ..kaje ta kitsa maka shiyasa ka kafe sai ka hada su to bazai yiwu ba.


Yace Anty ai na Riga na gama magana Kuma ba gudu ba ja da baya,in taga zata dawo su zauna fyn in Kuma sunga haka suka zaba shikenan...

Iyyeh! Yaya babba tace ah lallai malamin Maryam ya iya aiki sai ta je ta Kara masa kwarin gwiwa,dama ai bazata barka ka zauna da wata mace ba, sai ita shafaffiya da Mai...


Haka dai taita sumbatunta ita kadai ba Wanda ya kula ta har suka isa gidan su Rukayyah,yai parking a kofar gidan yace su shiga shi zaije ya dawo in sun gama zai zo ya daukesu ...



Suka shiga cikin gidan sun tarar da mutane cike da gidan, aka kira musu mejego ta taho da baby a hannunta, ba laifi ta amshesu sama-sama,ba yabo ba fallasa, an kawo musu abinci da Bai zai ishi mutum 2 ba balle su hudu,mommy kuwa ko kallon inda suke batai ba.

Kowa sai wani kallon wulakanci suke musu suna ganin ya wulakanta musu yar'uwa ya yaudareta,har habaici suka zo har gaban su suna yi wai ke ruky ma in Banda Abinki ma me ya kaiki hada jini da wadannan kazaman da basu da wani kyakkyawan asali,ai kinfi karfin mai mota sai Mai jirgi,Baki dace da Matar kanana ba, sai govenors ko yaran sarakuna ,Amma kin tashi kin kwaso Mana yuyuyu..


Cikin fushi ta dakatar da su da fadin haba Anty fanna me haka, ynx kin kyauta kenan abinda kukai...

Shashasha shi yasa yake gara ki kamar tayar Keke har wani kareshi zakiyi mutumin da ya gama tozarta ki a idon duniya ..ba wai kareshi nake ba Amma ai abinda kuke be dace ba ko...


Tashi sukai suka bar wurin har da tsartar da yawu wai wari suke..

Su matar Yaya kuwa tuni ransu ya gama baci da wnn can fuskar cikin bacin rai suka tashi zasu tafi ..taita Basu hakuri akan abinda yan'uwan mommy sukai, ko abinda aka kawo musu ma Basu ci ba dama waina ce kwaya 3 sinasir 1 da wata miya da Bata fi ludayi daya ba,sai nama 2 acikin miyar,Amma don jaraba Yaya babba nema take ta sa hannu taci naman don rashin zuciya,sai da goggo turai ta daka mata tsawa tace meye haka ne!

Sannan ta hakura ta ajiya ba don ya so ba,shine rukayyan tace ko ajuye muku ku tafi dashi Sika ce Alhamdulillah min gode sai da Maryam ta tai Mana Mai rai da lfy Mika fito..tana ji an ambaci sunan makiyarta ta daure fuska har da jifansu da harara ba tare da sun gani ba.


Tai musu Allah ya kiyaye..har sun tafi sai Yaya babba ta Kira Rukayyah tace zasu magana suka Dan kebe inda ba mutane tace Mata dama hakuri zan Baki kiyi hakuri ki dawo gidan mijinki,duk da nasan ba laifinsa bane laifin wnn munafukar matarsa ne,Amma kanina Yana matukar kaunarki baya cikin nutsuwa tun daga lokacin da kika barshi kullum bashi da magana sai ta amaryarsa,shiyasa Naga ya dace in sanar dake matsayinki a wajensa wlh mijinki Yana matukar kaunarki, ba yin kansa bane...🤔 Oh su Yaya babba girma ya fadi da karya.... itako an tabo Mata inda yake Mata kaikayi Nan ta washe Baki a zuciyarta tana cewa ai nasan Abbas Yana masifar Sona matarsa ce ta shiga tsakaninmu Amma tuda hakane Suma yan'uwansa sun gane zata gane kurenta sai na kwace mijinah...Yaya babba ce ta katse Mata tunaninta da cewa to Bari mu tafi Amma ki kula kinji kiyi tunani ki dawo gidan mijinki.


Tace ngd Anty Allah ya saka da Alkhairi Kuma naji dadin bayaninki zan yi tunani, har da ciro kudi 3k ta Bata tace asai goro ..ta karba cike da farincik Abin nema ya samu..sukai sallama ta tafi..su matar Yaya kuwa tuni sun gama kuluwa da ita har sun gaji da jiranta ..tana isowa suka Yi kanta kowa sai cewa yake abinda tayi Bai dace ba ita Bata kishin dan'uwanta akan wulakancin da sukai musu...


Tace yo ma Zama manyan banza Abu ya faru bazamu sulhunta su ba...goggo tace ai Basu dauko hanyar sulhun ba,ki dai canja wnn halin naki gaskiya na rashin kishin Kai ..haka dai suka sakata gaba kowa sai fadin Albarkacin bakinsa yake..tace naji za'a kiyaye!

Amma karku Gaya Masa wulakancin da sukai Mana Kar ya Kara kullatarsu ko kuwa...


Anty Fatima tace ai gara a Gaya Masa ya San matsayinsa a wajensu ai Allah ya Kara masa Yana zaune lfy ya kwasowa kansa jaraba..Ina amfanin hada zuriya da wadannan marasa mutuncin.. ni ai garama kawai ya sawwake Mata ya huta, goggo tace a gaskiya dai kananan mutane ne Basu da kirki ..Yaya babba Kuma tace hakanan zai hakuri ya dawo da ita zasu Dena ..Anty fati tace ni Yaya wlh bansan me yasa kike rufe idonki akan mutanen Nan ba ai dan'uwanki Zaki tausayawa ..tace yo ai yafi kowa sanin halinsu Kuma ya aura a haka Allah ya daidaita kawai..ita dai bakinciki. Maryam ta zauna ita kadai ne yasa ta ke son ya dawo da rukayyah ta dauki tsana ta dorawa Yar mutane ba gaira ba dalili kawai don ta zamo Mai biyayyah da sanin hakkin aure,shiyasa take gani kamar ta asirce shine ...


Koda Abbas ya iso suka tafi yace ba dai matsala ko ..har Anty Fatima xatai magana Yaya babba ta tabo ta wai kar ta fada ..Shima ya gane akwai wani Abin Amma da ya ga suna boyewa Bai takura musu ba ya kyalesu ...

A gidan Yaya suka sauka,suka ce gobe zasu zo suyi sallama zasu wuce danbatta ..yai musu godiya da sai da safe..


Washe gari sukai wa su Maryam sallama ta musu Alkhairi kamar yadda ta Saba suka tafi...


Amma Yaya babba ta ja kunensa duk yadda za ai yaje ya dawo da matarsa ...ya bita da toh..


Bangaren Rukayyah kuwa ynx ta Fara saukowa akan fushin da take da shi..don kusan kullum sai ta Kira shi a waya..wani lokacin tace tana bukatar Abu kaza Kuma zai je ya Kai Mata sbd yasan hakkinsa ne yayi..a haka Kuma aka bude sabuwar soyayyah don Shima ynx kusan kullum Yana hanyar zuwa ganin babynshi..


Amma da ta tabo shi akan batun ya janye batun hadasu gida daya sai yace Nan fa daya ...


Da dai ta ga ba shi da Shirin canzawa sai ta Fara tunanin sauke ra'ayinta tunda dai tana son mijinta Kuma ga Yar da ke tsakaninsu ..tana ganin gara ta hakura ta je tabi umarnin mijinta,Kuma ya Mata Alkawarin insha Allah u ba wata matsala da izinin Allah yace kece baki fahimci Maryam ba Amma mace ce Mai saukin Kai da fahimta a tunanina in kin kwantar da hankalinki ba abinda zai faru...

Tace sai ta sanar da mommy tukun taji shawararta akai..yace ba damuwa Allah ya sa muji Alhakiri....



Aiko suna gama magana da Abbas ta shaida ma mommy akan ta hakura ta kyaleta ta koma gidan mijinta ..insha Allahu yace ba wata matsala da zai biyo baya...


Mummy sakin baki tayi tana kallon diyarta da mugun mamaki...tace Do u know what ur saying ? Kina HAUKA ne Zaki zo min da wnn batun ..ok kinje ya gama siyeki da dadin bakinsa na yaudara shine kika so Nan Nima Zaki min ? To baku Isa ba wlh Ina so ki Kara shaida masa cewa indai Bai canja kudirinsa ba, Nima ba abinda zai canja nawa ..mu xuba ni da shi shege ka fasa..

Ruky kuwa najin batun mommy ta fashe da kuka ta shige daki da gudu ta rufe kofar ta fada gado tana kuka...sbd tasan halin mahaifiyarta in ta kafe akan Abu daya ..tace ynx shikenan Ina ji Ina gani xata rabani da masoyina sbd ynz ne ma taji tana Masa wani irin so Mara misaltuwa..

Ina ba zai yiwu ki kashemin aure ba mummy sai na san duk yadda nayi na koma gidan mijinah..wayarta ta dauka Tai dialing no. Daddy ta shaida masa cewa Abbas ya Bata hakuri Kuma ya Mata Alkawarin ba za'a samu matsala ba ...ta Amince xata koma Amma mummy ta hanani...yace ki kwantar da hankalinki tunda ynx kin gane gaskiya to kamar kin koma gidan Abbas ne,ki kyaleni da mummyn Taki zan dauki mataki akanta tunda ba ita kadai ke da iko da ke ba..zamuje duk inda zamu akan haka..sukai sallama Tai masa godiya.


Farin ciki fal zuciyarta kwata kwata ynx ba abinda take so face ta bude ido ta ganta a gidan mijinta ..daukar Khadija tayi ta rungumeta tana cewa kwanan nan kema Zaki fara jin dumin jikin daddynki Zaki samu kulawa irin ta 'ya da uba kinji my angel!


Ynx 3 month da haihuwarta

🤣🤣🤣

*Su ruky anga uwar bari waya Gaya mata borno gabas take ...*






Muje zuwa ...


*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻






*Story&written*





*By*



*Ummu Ameer* 💃




*Page* 2⃣7⃣






Daddy kuwa Kiran mommy yayi yace ta fidda hannunta akan batun diyarsa tunda tunda Bata dorata akan hanyar da ta dace,in ba haka ba kuwa duk abinda ya biyo baya ita ta jawo....ita kuwa tace ai wlh banga abinda zai sa in bari rukayyah ta zauna da kishiya gida daya ba...ta Riga ta gama Zama da shi muddin bai janye ra'ayinsa ba...wancan karon ka ci galaba akaina Ina ji Ina gani ka bawa Mai Mata yarinyata na kyaleka ..kayi nassara ruguza min tsarina na hakura wnn karon kuwa baka Isa ba wlh ...ba zan taba amincewa da kudurinku ba..gara ma tun wuri ka canja shawara..ita Kuma zata gamu da ni ne...ta katse wayar...


Daddy kuwa sororo ya tsaya Yana kallon wayar da mamakin wnn mugun Hali nata,wato ba abinda ta canxa a hallayyarta sai ma abinda ya karu ...mu zuba ni da ke!





Bayan sun gama wayar da mommy ya Kira rukyn yace ta kwantar da hankalinta komai zai daidaita ...tace ngd daddy Allah ya saka da Alkhairi..Kuma yai Mata nasiha akan ta daina biye wa mahaifiyarta...tace toh insha Allahu zan kiyaye!





Shi kuwa Abbas tunda ya fahimci ynx ruky ta Amince zata dawo ...har ya Fara gyara a gidan ...a yadda ya tsara gidan kuwa wnn falon da kitchen da bedroom dinta duk na Maryam sai dakinsa guda daya,saura 1 bedroom, shi aka barwa Maryam sai ya shigo da wani dan fili akai Mata falonta da kitchen ...sai Kuma dakin ..tsarin da yayi ba lallai ma said sun hadu ba,sai sun so hakan don kofar shiga falon nata ma ta baya akai mata,toilet kuwa each room contain.




Ya zage sai gyara yake inda kuwa mummy ba ta canza ba,akan batunta duk tabi ta tsangwameta a gidan ta daina kulawa da ita har sai ta janye batun komawa gidan mijinta in ba haka kuwa zata cire hannunta a rayuwarta gabadaya...


Itako ta dage komawa ba fashi hakan ne yasa aka Fara zaman doya da manja da mommy d ruky...


Tabi duk gidan wadanda tasan tana Jin maganarsu akan ta hakura ta kyaleta ta koma gidan mijinta ...Amma ta ki sauraran kowa ta rufe idonta ta kafe akan magana daya ... daddy ma ba irin barazanar da Bai yi Mata ba Amma ta kafe ...


Rukayyah kuwa ta shiga tashin hankali Mara misaltuwa,duk ta rame ta Kara Baki ta lalace,ita kuwa Khadija

Please Login or Register in order to submit comment