Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai faman girmanta take tayi mulmul ba ruwanta...hatta da ita ma mommy ta rage kulawar da take Mata,duk da dinbin kaunar da take ma yarinyar..kawai dai tana yin hakan ne don rukayyah taji haushi ta canja ra:ayinta...Amma ta fahimci ko gezau, ta fahimci idon ta ya rufe,Bata Jin maganar kowa...



Abbas kuwa tuni ya gama gyara,Kuma ba laifi tsarin da akai mata yayi kyau itama,sai dai wajen Maryam Nan ne gidan.

Duk Abinda mummy ke yi da tsanar da take nuna masa,duk kwashewa take tana fadawa Abbas, *don HAUKA* ko soyyaya ce ko meye ita ta sani, duk da cewa Shima ya sani..



Lokacin da ya gama gyaran ma har daukarta yayi ya kaita ta gani,ya Yana Amma ta nuna inda take bukatar gyara ... Ba yadda baiyi ta shiga ta gaishe da Maryam taki,sai Khadija dake hannunsa ya shiga da ita wajen yan'uwanta itama Maryam din ta dauketa tai Mata wasa.



Bayan sun gama ya maida su gida dama ita da wata cousin dinta ne Aisha, itace ma ke Mata fada akan kin shiga wajen Maryam din da batai ba..





Daddy kuwa ya yanke hukuncin sanar da mahaifiyar mommy sbd tana mutunta shi, Kuma ta San halin yarta sarai, tasan iriin zaman hakurin da yayi da ita,ko da suka rabu cewa tai tayi asarar miji bazata Samu kamarsa ba,wnn ne yasa take mutunta shi sosai...





Ai kuwa haka akayi, takanas ya shirya ya tafi maidugurin Tai masa tarbar mutunci,bayan sun gaigaisa ya kwashe duk abinda ke faruwa ya sanar Mata ranta ya baci,tace wato yadda taiwa kanta sagegeduwa shine take so taiwa yartata..Aiko Bata Isa ba...ta bawa daddy hakuri,sannan tace zata shirya taje har gida ta sameta...yayi godiya yai Mata Akhairi taita godiya sukai sallama ya yafi...




Bayan kwana 2 Haj. Babar mummy ta shirya sai gidan mummy, rukayyah ma Tai murna da zuwanta domin itama tana Shirin Kai karar mimny haj.tace ai abinda ya kawoni kenan mahaifinki ne yaje ya Gaya min duk halin da ake ciki..rukayyah Tai ta murna tasan matsalarsu tazo karshe don tasan mommy tana Jin maganar hajiyarta....tana matukar shakkarta.


Bayan Haj. Ta huta ta samu yarta Tai ta Mata fada akan mummunan kudirin da ta sa aranta...tace Kuma ta gaggauta janye wnn ra'ayin tun kafin ranta ya baci...taso musawa mahaifiyartata,Amma sanin halin haj.ta sbd Bata da wasa ko kadan,duk da itama ta zuba mulki a gidan mijinta kafin ya rasu..


Mummy tana ji tana gani aka Sanya ta janye kudurinta, Amma tace ba hannunta a ciki bazata sake shiga sha'aninta ba,ko matsala ta samu karta Fara dumfararta da duk wani Abu da ya shafeta..har kukan bakinciki mommy tayi ga haushin taje ta Kai kararta wajen wadda tasan sai taci galaba akanta...ranta ya baci sosai Anty batulu dama na gidan sai Kara zugata takeyi akan ta zame hannunta akan lamarin rukayyah in ba haka ba sai bakincikin su,ya kasheta...




Rukayyah kuwa wnn Rana ko bacci bataiba, don farinciki,har ta bugawa Abbas ta shaida masa yace Allah ya tabbatar Mana da Alkhairi....




________________________


Rukayyah kuwa ynx ba abinda ke ranta sai hanyar da zata bi,domin ta Kama shi a hannu ta juya shi son ranta..ta kwace mijinta tun kafin ta koma gidan....


Hakane yasa ta Fara shige da fuce don ganin ta sameshi yadda yake so Kar a samu mtsala kamar yadda ta faru a baya.....

Burinta Kuma ya Fara tasiri,don ynx Abbas jinta yake sosai a ransa,ji yake Yana Mata wani irin so,duk yabi ya damu akan ta dawo ...ita Kuma tace ya Kara Mata lokaci...tayi hakan ne don ta gama gudanar da duk wani Shirinta akansa...kuma duk wani shiri da takeyi a Alhajihunsa ne,shi Kuma idonsa ya rufe ko me ta tambayeshi cikin barin jiki yake yi...har wata malama dake yin lecture akan Mata taje ta hada Mata magunguna masu tsadar gaske...


Sai da ta tabbatar da ta gama kamashi a hannu ta ko ina sannan.. aka sa date din daxata tare sai da tasa ya cika Mata akwati biyu da nata da na yarinyarta da Kaya masu kyau...




Ranar Asabar itace ranar da rukayyah zata koma gidan Abbas ya rage saura 3days kenan yau....



Bangaren Maryam Kuma ko wane shiri take yi.....?



Sai min hadu a page na gaba ......








*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
KISHI KO HAUKA
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻










*Story&written*


*By*

*Ummu Ameer* 💃








*Page* 2⃣8⃣






Bangaren Maryam kuwa ta dage da addu'a Allah yasa hakan ya zame musu Alkhairi gaba daya..ita kanta tana mamakin wnn dokin da yake akan Maryam...don ko lokacin da zai aureta Bai yi haka ba..


Bata wani dorawa kanta mugun kishi ba..sbd ta San za ai haka ballantana an Dade ba'a hadu ba....ita dai kawai addu'a tasa a gaba sbd itace takobin mumuni..



Shi yasa bata damu kanta ba, ta wahal da zuciyarta...matsala daya ce ke damunta wato karamin cikin dake jikinta Wanda ko Abbas Bai San da shi ba...Kuma Yana wahal da ita sosai..


Amma duk da haka batai sake da gyara kanta ba, dama Kuma ita ko yaushe cikin gyaran take ..sai dai ba kowanne take amfani da shi ba sbd cikin da ke jikinta,akasari Daman da kanta take hadawa cikin sauki ga Kuma aiki...


Ta fannin jiki da kwalliyarta ma ba abinda ya canza ...dama ita ciki Bai hana ta gyaran jiki sai dai kawai canji yanayi na masu juna 2 ..Wanda in ba'a daure ba shi ke kawo kaxantar da rashin gyara..





___________________

Rukayyah kuwa shiri take kamar wata sabuwar Amarya ta zage sosai ta Sha gyara ..a ganinta abinda Maryam keyi kenan ta gama sace xuciyar Abbas...yake rawar kafa a kanta ..Bata San cewa ba maganin Mata ne kadai ke saka mallaki zuciyar miji ba..in Zaki Sha duniyar Nan matukar Baki da tarbiyyah,ko rashin iya kula da miji,da rashin iya girki,da dai ire-iren wadannan abubuwa da Kuma Mai gaba daya *hakuri* to babu tasirin da Abinda kike Sha zai yi ko da Yana yi to wadannan abubuwan da kika rasa sai sunfi tasiri, shi yasa ynx Mata suke ganin in dai ta Sha gyara to Bata da matsala da miji..




Duk wnn shiri da ruky keyi mommy Bata ko shiga harkarta ba, ido kawai ta zuba Mata.

Ranar da za'aje jere ma gidan ba Wanda ta Kira a fanninta sai kawayenta da kanwarta, da ita kanta ne suka je suka shirya abinda zasu iya..sauran Kuma sai Abbas din ne ya karasa shiryawa..kayan ma ba duka ta bayarba,wai a Ina xata aje, taji ance ai daki ne daya sai karamin falo..abinda ya Kara sa tsani auren.




Ranar Asabar da daddare aka dawo da rukayyah gidan Abbas,tare da kannen daddy da Kuma matar daddy, sai kanwar rukayyah,mommy cewa Tai ba Wanda zai taka kafarsa xuwa gidan a danginta, ba arziki suka rabu.



Bayan sun kaita sun Kara yi musu nasiha akan su dinga hakuri da juna, sannan suka ce akai su wajen Maryam, don su musu nasiha su zauna lfy..har rukayyah akace suje Taki zuwa sai da kanwar daddy Tai Mata fada sannan suka shiga wajen Maryam.

Ko da isarsu ta amshesu hannu biyu cikin sakin fuska,Kuma ta kawo musu abin motsa Baki,Suka gaisa ..Amma rukayyah ko gaisheta batai ba sai harararta take taga want kyau da ta Kara yi Mata akan sanin da Tai mata...and cikin ya Kara mata kyau da haske ta Kara cika..


Tasa hannu tana ta karbi Khadija tana Mata wasa,sai a lokacin ne ta Dan sake taga tana yiwa diyarta wasa..ita ko Bata taba daukar ya'yan ta ba balle Tai musu was..a zuciyarta tace makirci ne da kissa ..


Su gwaggo da Anty nusaiba sukai musu nasiha akan su hade kansu su zauna lfy...Maryam tace insha Allahu ... Sukai Mata sallama suka tafi..ta rakasu har waje,sunji dadin yadda ta mutuntasu sukace ai da ganinta Bata da matsala ..suka kara yi Mata fada ta cire kishi a ranta su zauna lfy fa kishiyarta...sukai musu sallama suka tafi...


Ruky kuwa sai rawar Kai ake an dawo gidan Miji...wasu Riga da siket ne ajikinta duk kirjin a waje..shayarwar da take yi ne suka ciko..Amma siket din sai kace an daurawa muciya zani...

Sai faman karairaya ake wa mijin..Shima din sai wani rawar Kai yake Mata..


Bayan sun dawo ya Kira rukayyah wajen Maryam ya Kara yi musu nasiha,akan su zauna lfy..tana sane da yadda yake ta rawar kafa akan rukayyan...bayan ya gama sukai Mata sallama, ya dauki abinda zai dauka a dakinsa yai Mata sai da safe...sai wajen ruky...





Muje zuwa


*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻




*Story&written*



By


*Ummu Ameer* 💃






*Page* 2⃣9⃣






"""Maryam kuwa tun fitarsa daga wajenta ta kasa samun nutsuwa kishi ya tashi ...ya Hana ta sakat,duk yadda taso ta kawar da Abin a ranta ta kasa tana Jin motsin su,dake duk waje daya ne kawai dai hanyar shiga can ne yayi ta baya Amma duk Abinda ake anaji..


Zuciyarta sai faman bugawa take kamar ta fashe..sai addu'a take bacci ya dauketa take ..Amma fir bacci ya dauke a idonta ..data tuna mijinta suna tare da wata ko ta danji wani motsi sai taji wani Abu ya tsaya Mata a rai...tace sanda suna can ba abinda ya dameta...


Haka dai taita juye-juye dake bacci barawo Bata San sanda yai gaba da ita ba..Amma sai kusan 3am na dare..


Can wajensu rukayyah kuwa an kwashi soyayya an Dade ba'a hadu ba..


___________________

Washe gari bayan ya dawo daga masallaci yai karatun qur'ani kamar yadda ya Saba ..wajen 7aam yaje ya bude gidan daga Nan ya wuce wajen Maryam yaji ya suka kwana..A wnn ranar ta kasa danne kishinta da ya shigo ta amsa Masa sallama Bata Kara bi ta kansa ba ..ta shige kitchen don ci gaba da hada break fast..gashi duk gidan ya dumame da kanshin girki ..qamshin ne ya tashi ruky daga bacci..don tun kafin ya fita masallaci yake ta tashinta Taki tashi ..gashi ya tsani wnn lalacin da take da shi Kuma ya lura Bata canja Hali ba..tana farkawa taga ba miji..ta leka ko Ina Bata ganshi ba..sai muryarsa ta jiyo a wajen Maryam..tace kan ubancan.. wnn mutumin Bai daina halinsa ba kenan ..Bari yaxo wlh baxata yiwuba ..matukar Yana San zaman lfy..

Ga haushin ta karade musu gida da qamshi...tana tsaye tana jiran shigowarsa da taji alamun ya shigo Tai saurin shiga toilet..Kar ya sameta har ynx Bata shiga ba.



Maryam kuwa a sanda ya shiga wajenta ta gyara ko Ina da wankanta dama ita tun asuba take yin wankanta Tai sallarta,wani lokacin ma ita ke tashinsa daga baccin..


Koda ya dawo bangaren rukayyah kuwa Yana Jin sanda ta shiga toilet sai alokacin ne zatai wankan ,balle ko breakfast da Bata ma Fara Shirin yi ba..tsoki yayi a zuciyarsa yace dama Mai Hali Bai fasawa...







**** ****. *****

Kwana 2 yayi a wajen rukayyah,ya dawo wajen Maryam ...


Ranar da ta fita girki kusan zaucewa tayi sbd tsabar kishi..ji tayi dama ta bar gidan in girkinta ya zagayo ta dawo...a ranar kasa yin komai tayi a gidan ko abinci Bata dora ba,wnn Kuma halinta ne in dai ba ta da girki tun acan gidan da ta Fara Zama,batayi sai ranar girkinta ko waye a gidan sai dai asha complex ko indomie kiwar girkin take...




Da daddare kuwa da yaje sallama tsiro da wani makirci tayi taki bawa Khadija nono,Kuma tasan shi take bukata ..hakane yasa taita kuka,ko da yazo ya tambayeta Mai ya faru tace itama batasani ba sai faman kuka takeyi..ya karbeta yaita jijjigaya yarinya kuwa yinwa na cinta sai faman ihu take ..sai da ya kusan 1hr daga sallamar da Bata wuci 10mins ba ...sai da tasan ta kunna Masa wuta.... tukun ta amsheta tace Bari na Bata Tasha ko tayi shiru..sbd tasan shi akwai kulawa da yara Kuma ya iya rainon..tasan bazai iya tafiya ya barta a wnn halinba shiyasa ta kunno da wnn salon..don ba kowa ne ke son rainon yara ba, wasu mazan ma in suna kuka yaran ficewa suke su bar gidan..


Yai mata sai da safe ya tafi ...itako zuciyarta fari Kal...



Maryam kuwa da taga shiru Bai dawo ba..a zahiri ranta ya baci..Amma da ta tuno halin ta,ba ynx ta Fara haka ba..sai ta saki ranta ko da ya shigo ma Bata wani nuna Masa komai ba..Kuma dama ita ko laifi yayi Mata Bata nuna Masa a lokacin sai daga baya ta nuna Masa rashin jin dadin abinda yayi..balle Kuma ynx ga kishiya a kusa ta Yaya zata Bari ta jiyo wata baraka daga garesu...duk Tai masa abinda ta Saba..ba tare da nuna Masa komai ba..ga wani kyau da yaga ta karayi Masa ..Wanda Bai lura da hakan ba sai ynx...Nan da Nan wani shaukinta ya kamashi...ga wani cika da ta karayi..sai wani mayataccen kalloh yake binta da shi..sai kace Wanda Bai taba ganinta ba...yace ranki ya Dade wai menene sirrin ne Kinga wani kyau da kike yi kuwa..murmushi kawai tayi.

Don ma a kwanankin nan yana Dan samun matsala daga gareta Bata cika son bashi hakkinsa ba har fushi yayi da ita ..shi Kuma cikin yanayin da yazo Mata da shi kenan duk sauran ciki Bata samu matsalar Nan ba..akasari Kuma Mata sukan fuskanci haka in cikin Yana karami Amma in ya fara girma sukan dawo normal.


A wnn Daren ne Kuma ta Gaya Masa tana da ciki..yaji dadin sosai har Yana cewa ko yara nawa zata haifo Masa bazai gajiya ba..sbd ta iya santalo kyawawan yara ..tai murmushi tace masu Kama da Kai ko..yace wane ni ai ke suke biyowa saidai su dauko wasu abubuwana.


Sai ynx ya gano dalilin da yasa take gudunsa kwana 2, sbd cikin da take da shi...yasan dama masu ciki suna samun wnn matsalar.

Suka kwanta cikin farin ciki da annashuwa Kuma yaji dadin kasancewa da ita a daren..duk da itama rukayya yaji canji a wajenta ..Amma bazai taba hada su daya da Maryam ba,Yana alfahari da ita sbd ita ta daban ce a cikin Mata..tuni ta mantar da shi komai..


Rukayyah kuwa a wnn dare kasa Zama tayi tunda ya dawo wajen Maryam har labe take taji hirar da suke amma ta kasa sbd Maryam Bata daga murya sosai in suna hira da Abbas ko bama shi ba haka take maganarta, sai dariyar Abbas kawai take ji sama-sama ..ranta ya baci wato dama har dariya yake haka Amma ni sai in Dade ban ga dariyarshi ba...lallai ne wato har ynx da saura na kenan,haka taita labenta har sai da taji Shiru ...alamun basa falon sannan ta zagaya ta daidai saitin dakin Maryam taji Shiru..ta zagaya ta saitin dakin Abbas sannan Taji motsinsu..tace lalai ita har turaka ne ma da su...haka ta kasa kunne ko xata Dan ji wani abun shiru..Bata ji komai ba sbd an rufe dakin ga karar A.c ta hana ta Jin komai..hakanan ta hakura itama ko barcin kirki Bata samu yi ba..sai kusan asubahi maimakon Tai sallar ta kwanta sai ta yi baccinta..har Abbas din yazo yayi ta kwankwasa kofa Amma shiru ..tayi nisa a baccin...yayi komawarsa can...






Muje zuwa


*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻







*Story & written*


*By*


*Ummu Ameer* 💃






*Page* 3⃣0⃣


*Kuyi hakuri da rashin jina kwana 2, sabgogi ne sukai yawa...ngd sosai da kulawarku* 😘


"""Ko da Rukayyah ta farka taga kusan karfe takwas na safe,Amma Abbas Bai shigo ba, ranta ya baci sosai, hakanan ta tashi jiki a sanyaye ta shiga toilet..sai a lokacin zatai sallah, bayan ta idar ta dawo falo ta zauna ta cika fam da Abinda Abbas yai mata,jiran shigowarsa kawai take ta zazzaga Masa bala'i... sleeping dress ce a jikinta don ko wanka batai ba.


Tana Nan zaune ita Ba ga wankan ba,balle gyaran gida ga shi har ynx Abbas Bai shigo ba...

Sai karfe Tara ya shigo,yai sallama ko amsa masa batai ba, Yana ta magana Tai masa shiru..yace wai lfy na shigo Ina ta magana Baki tanka min ba? Me Kuma ya faru ..ai bazaka San Abinda ya faru ba tunda a tunaninka daidai kayi..wai yaushe ne xaka Fara kamanta adalchi a tsakanin mu..ko yaushe kana kokarin fifita uwargidanka akaina..ta Yaya kuwa kake tunanin samun zaman lfy a gidanka? Idan kana wajena,kana tashi tun kafin gari ya karasa wayewa kake shiga wurinsu,Amma ni sai ynx ne kake shigo min sbd baka damu da mu ba...wlh bazai yiwu ba Ina ji Ina gani na Zama wulakantattiya a gidan Nan ba, ya Zama dole ka canja tsari...

Shi kuwa tsayawa yai Yana kallon ikon Allah na gajen hakurinta...yace na shigo kina bacci shiyasa na tafi kar na katseki ..

Tace meyasa baka tasheni ba?

Yace Am late idan na dawo mayi maganar...yai mata sallama ya tafi,binshi tayi da idanuwa ko Allah kiyaye batai Masa ba...

Yana fita ta durkushe a wajen ziciyarta na tafarfasa, a ziciyarta tace har ynx da saurana akan mutumin nan,tana mamakin irin soyayyar da yake Mata ...a tunaninta ita yafi cancanta ta samu wnn soyayyar, tunda itace Amarya .


Nan da Nan wata dabara ta fado mata, akan ta kwantar da Kai ta shigewa Maryam yadda yadda zata saki jiki da ita domin ta gama sanin duk wani sirrinta domin ta gano abubuwan da take Masa da kuma sanin sirrin zamantakewarsu..



Cikin sauri tai abubuwan da zatai ta shirya tsaf ta nufi wajen Maryam ...

Ko da Maryam ta ganta har sai da gabanta ya Fadi tayi tunanin ko rashin kirki ne ya kawo ta....Amma sai ta ga fuskar ta a sake cikin walwala .....Maryam Tai Mata iso zuwa falo suka gaisa har tana tambayar Ina yara sun tafi sch.ko?

Maryam tace eh!

Amma tana shakkun Anya kuwa babu wani nufi a tattarre da ita ...wata zuciyar Kuma tace ki daina wnn tunanin watakila ta gane gaskiya ta dauki hanyar Zama lfy ....Nan da Nan ita ma Maryam ta saki jiki da ita suna ta hira...Amma in Maryam ta kawar da fuska sai ta jefa Mata wata muguwar harara, sbd a hirar da suke tayi iya kokarinta na gano wani aibu ko cikas Bata gano ba,a tare da ita,ta ko Ina Maryam tayi Mata zarra.....


Tana gidan har Azhar a gidan taci abinci, har kitchen din tabi ta wai zata taya ya aeki....tayi haka ne don ta ga irin sinadarin da take amfani da shi a girki...da spices da curry, taga tsantsar tsafta,domin kuwa taga ko tsinke Maryam Bata Bari sai ta dauke ....Bata barin datti ko kadan a waje.


Rukayyah kuwa gani take hakan wahala ne me zaisa mutum ya Kare a wahala ba hutu ko yaushe cikin aiki ....tace wlh bazan iya ba.



Ba ita ta bar gidan ba sai da Abbas ya dawo, ya Kuma ganta a gidan ...Shima a zuciyarsa ya zargi wani Abu a tare da ita,ya San a kwai abinda ya kawota...tana ganinshi Tai saurin barin sashe don bazata iya jure ganinsu ba.....








Kuyi hakuri da wnn bani da isasshen lokaci ne shiyasa....



Taku

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI ko HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻






*Story& written*


*By*


*Ummu Ameer* 💃



*Page* 3⃣1⃣





Haka rukayyah tai ta amfani da wnn damar na shigewa Maryam don samun abinda take nema...ta danne kishinta na dan wani lokaci.


Akwai watarana da Abbas suna hira da Maryam take ce Masa ni Kam Abban mufid Banga wani hali na ki a tare da rukayya ba,domin ynx ta sauke komai ta bada hadin Kai an zauna lfy....yace ki dai bi a hankali,ba komai Zaki sakar Mata ba .... itako xuciyarta ta gama aminta da ita gani take rukayyah bazata sake yin wani abu makamancin na baya ba...*Maryam ta manta ko Bata San da ba'a Aminta da kishiya ba...komai Jin dadin zaman da kuke*



'yanuwanta ma sai da sukai Mata magana akan tabi a hankali don wasu kishiyoyin ba Abin yarda bane...ita dai jinsu kawai take Amma a tunaninta ba abinda zai biyo baya....





Sai da tayi wata guda a haka, Kuma Bata San cewa Maryam na da ciki ba...


Amma itama Maryam din tana da wayonta domin kuwa ba komai ne ta Bari rukayyan ta sani ba dangane da zamantakewarsu.


Ba Abinda ya fi tsayawa rukayya arai irin yadda taga ya dauki son duniyar Nan ya Dora Akan su mufid sosai yake nuna musu wani irin so da kulawa ....kasancewarsa caring father, ko tari sukai duk sai ya wani kidime ya rikesu Yana musu sannu, Kuma ko a gaban waye baya kunyar nunawa yaransa kulawa ...wannan ne yasa rukayya ta Kara tsanar Maryam da yaranta.


Domin ynx ko kula yaran Bata yi..kwanaki kuwa ta danne halinta ta Dan jasu a jiki dama na munafurci ne...


Sai Abu na 2 da ta fahimta a tare da shi kwata-kwata baya nunawa Khadija irin soyyayar da yake ma sauran yaran...wnn Kuma ba laifin shi bane sbd yarinyar akwai kiwa in ba su mommy da ta taso a gidansu ba,Bata yadda da kowa Bata shaku dashi ba tun farko yayi iya kokarinsa ganin ta Saba da shi Amma har ynx Bata Saba da shi ba,Amma Yana iya kokarinsa kawai dai rashin godiyar Allah ne...


Kuma sauran yaran tun suna jarirai kusan shi ke rainonsu in dai Yana gida,sai dai in suna bukatar abinci ne zai kaiwa mahaifiyarsu,sun shaku da shi gaskiya fiye ma da ita mahaifiyarsu.


Wannan dalilin ne yasa rukayyan ta dinga cusa Masa yarinyar ta karfi...da ya shiga gidan in ba girkinta bane sai ta manna Masa ita wai ya tafi da ita aeki takeyi,tun yarinyar na ki, har ta fara sabawa da shi Amma ba kamar sauran ba, sbd yasan takan yara sosai.



Ta fannin girki kuwa duk idon da ta Sanya akan yanayin girkin Maryam,in taje zata gwada ba ya taba yin kamar na Maryam din don sau tari ma kasa ci yakeyi ....duk sanda yaki ci kuwa ba zaman lfy kwana kuka wai taga in a gidan Maryam yake zagewa yake ya cinye tana sane da shi,Amma ita ta wuni tana yi don ta faranta Masa yaki ci...a ranar ko bacci gagararsu yake sbd bala'inta.

Har cewa yayi taje Maryam din ta koyawa Mata ...tace Allah ya kiyaye tunda ta Kai ga Abincin ma baka Jin dadin na kowa sai nata....


Duk da cewa har ynx tana aiki akansa Kuma Yana tasiri..sai an danyi kwana 2 sai Kuma ya sakeshi...sai a Kara himma.


Cikin wani ikon Allah duk Abinda takeyi akansa baya shafar Maryam din, don har ynx Bai canza Mata ba,a ko yaushe darajar ta karuwa take a wajensa Kuma ko da wasa Bai bata dama ta Raina ta ba.sbd zuciyarta kyakkyawace Bata da mugun nufi...ga Kuma addu'ar da Bata sake da ita. Ta dauketa da zuciya 1.


Hakan da rukayya ta gani abun ya tsaya Mata duk yadda taso ta ga wata baraka ko ta gansu a ruwa Bata gani ba, tana bakin cikin ganinsu cikin nishadi da mutunta juna,ita ba abinda takeso ta gani illa ta ranar da zai Fara wulakanta Maryam ....ta Zama ba komai ba a wajensa ya zamo ita ke iko da shi.




****** ***** *******

Akwai wata Rana Abbas zai Kai Maryam Asbiti zata Fara Awo, shine rukayya tace ai itama fita zatayi, dama Kuma girkin rukayya ne, yace ta Bari sai gobe..ba yadda baiyi da ita ba Amma Taki ita a dole sai ta fita, sai da Maryam tace ka kyaleta Mana taje...sannan ya barta Amma ba don yaso ba,. Sbd ya na sane da Abinda take duk ranar da ta fahimci Maryam zata fita sai ta bijiro da ta ta fitar...shikuma ganin akwai Mata 2 a gida Bai dace ace gabadaya sun fita ba.


Sun gama shiryawa tsaf sun fito rukayya Tai hanzarin shiga gaba,har tana tuntube sauran kiris ta Sha kasa, maryam tace hankali dae...shikuwa Abbas tabe Baki yayi....


Ko gaisheta rukayya batai ba,sai Maryam din ce ta gaisheta sai faman wani kimbura take ita a dole an shiga hakkinta ya fita da ita ranar girkinta,Kuma Yana sane da Abinda tayi wnn tasa ko kula ta baiyi ba,sai faman zuba take zancen da ba kan gado sai dai yace eh ko a'a, Aiko ba karamin kuluwa tayi da hakan ba,ya gama kunyatata a gaban kishiya...daga karshe ma Maryam din yace wa mmn mufid lfy kuwa kinyi shiru ko jikin ne, tace a'a .

Haka yaita janta da hira,rukayya kuwa takai kololuwa wajen bacin rai tai danasanin biyosu..kamar tace ya sauketa a wajen, haka dae ta danne Batai Masa magana ba, har akazo hospital din ya fito ya budewa Maryam mota ta fito tace wa rukayya Allah kiyaye ta amsa a dakile ya leka ta window yace Yana zuwa...Tai Masa banza.



Tare suka shiga ciki,sai da Maryam din tace ya koma Kar rukayya Tai ta jiransa yace ai ta ga zata iya sai da nace ta Bari gobe ta fita takiji...kinga bani da laifi.


Dake duk yasan likitocin Basu wani Sha wahala ba, anyi duk wani abinda ya dace ayi na masu Awo,suna jiran result ne na text din da akayi ya leka wajen ruky yaga ba ta cikin motar....ya duba ko Ina

Please Login or Register in order to submit comment