Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fito shima ya shiga.
Bayan ya fito suka gabatar da sallar, ya danyi mata tambayoyi game da addini kuma ta bashi amsa yaji dadi sosai da ya sameta mai ilimin addini, yai musu addu"ar samun zaman lafiya tare da zuri'a na gari, bayan kammala sallar ne ya janyo musu tray din naman da milk, ya zuba bashi a cup, itama ya zuba mata da kanshi ya dauka zai bata ta kauda kai wai ta Koshi, nan ko yunwa ce Ke kwakularata, amma ta kafe bazata ci ba said da kyar da ta ga ranshi ya baci sannan ta fara kurbar milk din shi ya dinga bata saida ya tabbatar da ta koshi sannan shima yaci nashi, ya gashi ya kwashe kayan ya maida su kitchen.


Yana fita ta shiga toilet, Tayi wanka ta shafe jikinta mayuka masu laushi da turaruka masu tayar da hankali, ta dauko rigar baccin da ta saka amma duk ita ji take kamar ta cire kamar rashin kunya ne hakan, daga karshen dai hijab ta dauko ta sanya bisa rigar barcin.
Shima Abbas din Dakinsa ya shiga domin yin wankan bayan ya fito ya sanya turare mai dadin qamshi tare da sanya singlet da boxer said ya dora jallabiya akai sai yai fes da shi, Abbas dogo ne amma yana da dan kauri tare da faffadan kirji yana da yana da Dan haske ba sosai ba yana da kyau dai dai misali ga sajen dake zagaye a fuskarsa gwanin sha'awa, yana da kwarjini da cikar kamala, yammata da yawa suna kawo tayin soyayyrsu amma duk ba wacce tai mai sai maryamunsa.

Y kashe fitulun dakin tare da janyo kofar ya kashe komai na falon ya wuce dakin amarsuuu. Yana shiga ya sameta a zaune a gefen gadon har ta fara gyangyadawa, hura mata iska yayi a fuska firgigit ta tsorata, yace wannan zumbulelen hijabin fa baby ba kyajin zafi yai saurin daga kai duk ta tsorata da shi, ango kuwa tuni ya gama rikirkicewa tare da zumudin wannan dare, tashi yayi ya kashe wutar dakin ya nufi gadon tare da janyo ta ta fado jikinsa....

dole dae nima fitowa nayi, domin iya abinda xan iya gani kenan.





""""""Fadin farincikin Abbas bai misaltuwa a wannan dare sai faman addu'a yake mata tare da Sanya mata albarka, wani irin Sonta ne ke kara ratsashi yaji dadin samunta yadda ya kamata tare da samun nutsuwa.


Da asuba ya tashi ya shiga wanka, a toilet din dakin bayan ya fiyo ya taimaka mata wajen hada mata ruwan zafi ta gasa jikinta, ba karamar wuya ta sha ba, domin kuwa har tsoronsa take tare da wata matsananciyar kunyarsa ko hada ido bata yadda suyi, sai da ta gama gasa jikinta ta tabbatar da duk wata gajiya ta sake ta sannan ta fito tai gabatar da sallah sannan ta shirya cikin wani material doguwar riga ta Dan yi silent make -up ta yafa Dan karamin mayafi akanta ba karamin kyau tayi ba.

Shima Dakinsa yaje ya shirya cikin kananan kaya sun masa kyau ya feshe jikinsa da turare sai qamshi yake tashi, kasancewar sa ma'abocin turare. Ya shirya tsaf ya nufi wajenta tana Dakii a zaune ta kasa fitowa,
Shiga yayi ya sameta a zaune gefen gado ta kimtsa dakin tsaf, tsugunawa tai ta gaisheshi Ina kwana kanta a kasa ruko hannunta ta yayi suka sake gaisawa lfy lau my lovely wiffy!
Yai ta mata godiyar rike mutumcinta da ta kawo gidan aurenta. Ruko hannunta yayi suka fita falon kan dining ya ajiyeta ya shiga zai hada tea kenan sai suka ji knocking yaje ya bude daya daga cikin yaran gidan yaya ne aka aiko shi da break fast, ya amsa yai godiya, farfesun kayanciki ne da irish&egg da yaji source da akayi da kayan lambu sai kunun gydar da sha madara, daman shi ma'abocin kunun gyada ne, zuwa yayi ya kawo plates da cups ya zuba musu yace da kanshi zai bata tace da kanta zataci bata wani sake ba ta dan tsafura amma tasha kunun sosai.

Bayan sun kammala break fast ne ya ja ta ya Nuna mata ko Ina na gidan, suka dawo falon suka zauna ya kai musu tashar m.BC 4, ya jawo kusa da shi kamar wani zai kwace masa ita, aiko tuni bacci yayi gaba da ita fuskarta ya kurama ido yana kallon kyakkyawan idanuwanta da gashin ido ya rufe shi ba karamin kyau tai masa ba da baccin, gyara mata kwanciyar yayi har da dauko abin rufe ya rufeta.




***** **** *****
Sun gudanar da amarcinsu cikin so da kaunar juna ji yake kamar kar ya koma aiki hutun yayi kadan ya zauna yai ta kula da amaryarsa.




*muje zuwa*

*ummu Ameer ce*πŸ‘Œ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€




*story&written*

*by*


*Ummu Ameer*πŸ’ƒ





*page*πŸ”Ÿ



"""""Wata uku kenan da aurensu maryam ta Kara haske da tare da cikowa, kana ganonta kasan amarci ya karbeta kowa sai yabon ango yake akan ya iya kiwo.

Sosai Abbas yake ji da maryam ko office ya je cikin kiranta yake lokaci zuwa lokaci, Itama kuma tana kokarin kyautata masa duk wani abinda tasan zatai ta burgeshi tana kokarin yi, Ko ta fannin girki ne duk abinda tasan yana so to sai ta kware basirarta wajen yi mai yadda yake so.
Ta fannin kwalliyah ko ba'a magana domin gwana ce kuma ta hadu da miji mai son kwalliyar, ko yaya tai make-up sai ya yaba har da tukwici, haka ma ko girkin ne in dai tayi sai ya yaba, yana Alfahari da ita wajen girki wannan ne yasa bai shakkar kawo friends dinshi cikin gidan, in dai suka zo to haka zasuyi ta yabon girkin nata, har da kyauta. Shikuma kai ya fasu an yabi Abin Alfaharinsa, haka ta fannin tsafta ma ba daga baya ba wnn kuma kamar gado ne domin ko ummi mace ce mai tsaftar gaske, duk sanda ka shiga gidanta ko Ina tasss yake so wannan training dinta shi yasa yaranta basu da matsalar kazanta a gidan aurensu.
Babu yadda za'ayi ka shiga gidan maryam baka ji qamshi na tashi ba ita ko yaushe cikin qamshi gidanta yake ko girki ta ke to qamshin girkin daban na turaran gidan daban, wannan ne yasa ta sace masa zuciya gabadaya ya gama sakankancewa da ita ya mallaka mata kansa baba daya, ko bako ne yaje gidan sai ya fito yana yabon soyayyarsu suna burge mutane.

Duk inda Zata shi ne yake kaita da kansa kuma ya jira in yana da uxuri ko saidai ta hakura da fitar. Har danbatta ya kaita wajen 'yan uwaansa sunji dadin ganinsu sosai, amma anty sadiya babbar yayarsa bata wani sakar mata fuska ba, ganin irin rawar kan dake yi akanta, gani take kamar ta asirceshi ne, sauran yanuwansa kuwa sun nuna Mata kauna sosai ta saki jiki da su har ta nemi a bata yar diyar yayarshi ta biyun tai hutu a wajenta, haka kuwa akayi tare suka taho da ita amma shi baiso hakan ba.



Ranar wata asabar ne lokacin yana gida hutun wkend maryam ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki tunda safe take ji kadan-kadan yana lura da ita duk yanayinta ya canza ba walwala a tare da ita duuk yabi ya rude yana tambayarta meke damunta tace bata Jin dadin jikinta ne duk ga kasala, yace tun yaushe tace tun last 2days amma dai yau har da ciwon ciki tunda nai breakfast yake ta min ciwo.. Ta kare maganar cike da shagwaba kamar xatai kuka, yace amma babyna shine Baki fada min ba kina barmin jikinki yana ta wahala Har tsawon kwana 2 karki sake kinji koya kika ji wani changes a jikinki just tel me, okay! Gyada masa kai tayi, maza dauko hijab muje hospital shi kuma yace bari naje na dauko key.

Bai zarce da ita ko Ina ba sai asibitin STANDARD hospital dake nan tarauni bai kaita asibitin da yake ba saboda yasan delaying dinsu, kuma shi standard din nan gidan yayanshi suke zuwa indai bukatar asibitin ya taso.


Banyan sunje suka samu wata Dr. Hauwa daman sunsan juna tana aiki a AKTH in ta tashi daga nan da gama sai ta wuuce can standard din ranar wkend kuma tun safe take zuwa.

Bayan sun gaisa ne yake ce mata ya kawo madam ne tana fama da ciwon ciki, nan tai mata tambayoyi na masu ciki, sannan akai p.T test, an tabbatar da cewa tana da cikin wata uku, ajikinta farinciki wajen Abbas bai misaltuwa, Dr. Hauwa tai masa murna sannan ta batashawarwarin da ya kamata tayi don kula da lafiyarta da na babyn, itama kam murna da tsoro ne suka hadu mata a zuciya domin tunda ta taso take tsoron haihuwa sosai a rayuwarta gani take kamar bazata iya ba in tazo haihuwa mutuwa zatai, ganin Wasu da suke haihuwa ace ai garin haihuwa wance ta rasu, shine take ganin kamar itama hakane... Lol.. Kuruciya

Tun daga hospital din kada kaso kaga yadda ya tattara duk wata kulawa akanta, da suka zo fitowa a hospital din ma rungumo ta yayi a jikinsa sai kace irin wadda ta galabaita dinnan ya wani shawabata itako Dama abin ne ya samu tai luf a jikinsa ya bude Mata motor ya zaunar da ita, ya zagaya ya shiga suka nufi gida, Wasu had kallon su suka tsaya yi a asibitin saboda sun burgesu wasu kuma na taya ta murnar samun miji mai kulawa irin wannan.

A motarma ma duk hankalinsa yana Kanta gabadaya, yana tambayar ta ko cikin ya daina tace eh! A Hanya ya tsaya ya siyo mata pizza Da burgar saboda yasan tana sonsu sosai kusan duk sanda zai dawo gida saiya siyo mata.


Tun daga ranar ya Kara dora soyayyarsa AKan maryam Da unborn baby dinshi, ya hana yin wani aikin Da zai wahalar Da ita ko abinci cewa yayi ta bark zai dinga taho musu Da takeaway in zai dawo tunda a gidan ya samo musu wata dattijuwa baba larai tana yin aikace aikacen gidan, har avincin ma tanayi amma yace shi Sam bazai ci avincin mai aiki ba saidai nata gudun kar Ya takura mata yasa yace zai dinga taho Da shi, ita kuma tace a'a ai yin girkinsa ba zai gagareta ba.




*muje zuwa*


By

*Ummu Ameer*πŸ’ƒ

More comment more typing...
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€

*godiya mai yawa gareki yar'uwata ta kaina kinfi kowa son book dinnan Allah ya bar zumunci*


*Story&written*

*by*

*Ummu Ameer*




*page* 1⃣1⃣



Haka maryam tai ta fama da laulayin ciki sai dai abin ma yazo mata da sauki tunda bata amai da zubda miyau, abin da yafi damunta ma ciwon ciki kuma Ba waikullum ba sai dai rashin Jin dadin bakinta da bata yi da kasala da tayi dan aiki kadan sai ta gaji, Abinci ma komai dadinshi da ta fara sai ta kasa ci hakan yasa ta danyi rama sai haske da ta Kara yi tare da kyawu.

Abbas kam Indai yana gida bai barinta tayi komai ya dauki son duniya Ya dorama ma unborn baby dinshi haka zaka ga yana tayin magana da shi kai kace amsa masa yake yi, Kullum addu'ar shi Allah ya sauke ta lafiya tare da dokin ganin ranar da zai zama daddy.

A lokacin da cikin yai 4month ne ta fara zuwa awo zuwanta na farko akai mata scaning domin ganin lafiyar cikin, kuma ba wani Matsala komai normal tare da yin gwaje-gwajen da tabbatar da lafiyar ita kanta mai cikin, kuma Alhamdulillah shima normal sai magunguna na Karin jini da calcium aka bata.

Shima tunda cikin ya kai 4month haka yake siyo mata kankana kullum sai tasha domin shan kankana ga mai ciki yana wanke baby kaga jikinshi fresh da haske in ka haifi baby, maltina ma carton-carton yake siyo mata kafin wani ya kare ya siyo wani shima yana Kara jini ko da haihuwa aka xo yi to bazata samu matsala jini ba, sai dai in ya zo da matsala na bleeding.

Ranar wata Sunday ta sa masa rigima kan lallai sai ya kaita gida, shi kuma in ba zuwa hospital ba bai fiye son tana fita ba, haka ta sa shi a gaba tana masa kuka, a dole ya amince yace ta shirya su je, nan taita murna ta tashi da sauri had tana shirin faduwa yai saurin tallafo ta yace yace Kinga ni ko zaki wahal min da baby, shi yasa ban fiye son kina yin wasu abubuwan ba.

Tace wato kai ta babyn ka ma kake yi ba ni ba ko shikenan ai, ta kare maganar da shagwaba kamar wata yarinya, murmushi yayi ya lakuce mata hanci yayi yace tun yanzu har kin fara KISHI da babyna. Murguda masa Baki tayi tana masa dariya ta shige tai saurin rufe kofar, yace zaki fito ne yarinya.

A hanya suka tsaya a wani super market sukai danyi ma su ummi siyayya daman ka'ida ne duk sanda zasuje sai ya tafi da wani Abu basu zuwa haka, yana kyautatawa wa yan'uwanta, tare suka shiga yace ta zabi abinda ya dace.
Da isarsu yace karki dade just 30min, zanje gidan yaya indawo sai mu gaisa ki gaishe su sai da ya bude mata motor en har da riketa wai karta fadi sai da ya tabbatar da ta shiga sannan ya tafi tare da manna mata kiss a kumatu.

Tana shiga gida sai murna bare ummi da tai missing dinta kullum da ita take kwana take tashi a ranta, duk da kusan kullum sai sunyi waya, kowa yai farinciki da ganinta gashi sunga ta Kara kyau sosai sun yaba sosai da ganinta, sai alokacin ummi ta lura da juna biyun dake jikinta, ko hafsa da taje tai mata kwana biyu da bata da lfy duk basu gane ba, nan itama ummi tayi ta nan-nan da ita, Abba shima yayi farincikin ganin yar tasa yai ta shi musu Albarka, ko Abincinta ma ummi daban tai mata, tace ita tuwo takeso miyar kuka ummi tace sai dai tai mata miyar ugwu sai yafi amfani a tare da ita, haka kuwa tai mata lafiyayyen tuwo da miyar ugwu kuma tas ta cinye tana ta santi.

Sai bayan la'sar ya zo daukarta ya shiga suka gaisa da ummi sukai tai mai godiyar kula da diyarsu shima ya ji dadi sosai da add'ar su, ganinsu yake kamar iyayenshi yana matukar ganin girmansu yana Alfahari da samun surukai masu dattako kamarsu.

A hanyar su ta komawa yace su je BABY DREAM CENTER, su fara siyan kayan baby tace kai husby tun yanzu bamu sani ba fa ki me samu haifa yace ai unisex samu saya, haka suka shiga duk abinda ya mash sha'awa sai yace a dauka.

Bayan sun dawo ne daman ta taho masa da tuwon ummi yaci ya koshi shima yai ta santi yana cewa Ashe ummi ce ta koya mata girki masu dadi yai ta shima ummi Albarka.

Tashi tai tace bari naje na Dan watsa ruwa a jikina yace to bari na zo na cuda ki, tace a'a barshi na gode saboda tasan abinda zai biyo baya, itako yanazu kwata kwata abin ma ya fita akanta kawai dai tana daurewa ne tana kokarin bashi hakkinsaBy gudun jefa shi cikin wani hali.

Tana kokarin jure bukatarsa amma bata so tun sanda ta fara laulayin cikin, shima kuma yana tausaya mata duk da kasncewarsa mabukaci sosai.


"""""Haka suka kasance cikin so da kaunar juna tare da kulawa ta musamman ga cikin dake jikinta, yanxu kam cikinta ya kai 9month, ga cikin da girma sosai kamar na twins, ko bacvin kiraki bata samu ga motsin cikin kamar zai fasa mata cikin sau tari motsin ke hana ta bacci, shima barcin kaurace masa yake, zuwa yanxu sun gama hada komai haihuwa suke jira, hafsa ma tana gidan ko da wani abin ya taso in baya nan.

Ranar litinin da daddare misalin 11 daya na dare ta fara jin ciwo tun tana daurewa har ta kasa yace kawai ta tashi su tafi asibiti tace ya bari dae ciwon yafi haka duk ya wani rude ya kASA zaune ya tsaye, haka tai ta fama sai misalin 3 na daren suka tafi asibitin Mallam Aminu kano, direct akai shiga da ita labour room, yana kokarin binsu suka bana shi ya tausayi mata matuka.

Shiru haihuwa har asuba, ba labari hankalin shi yai matukar tashi ya sanar ma da su ummu da gidan yaya aikuwa ba bata lokaci sai gasu sun iso har da Abbah.



Munai miki fatan Allah raba lfy maryam.

*by*

*ummu Ameer*πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€





*page* 1⃣2⃣




"""""Hankalin ummi ya matukar tashi ganin irin tsawon awannin da diyarta ta dauka duk da tasan daman haihuwan fari wasu kanyi doguwar nakuda, amma duk da haka ta tsorata ganin duk yaranta itace ta haihu a shekarunta, ganin cewa sauran da sai sun gama mallakar hankalinsu, gani take kamar tai kankanta, addu'a kawai take tayi ba kakkkautawa akan Allah Ya sa ta haihu lfy, shima Abban yana zaune yai jugum shima sai addu'a yake Mata a zuciya, *lallai maryam yar gata ce ga ummi ga Abba, ga husby.. Lol..*

Shi kam Abbas ya kasa ma zama da yaga an fito zai nufesu da sauri yana tambayar *ta haihu*?
Suce da saura, sai da Abba yai masa magana ya samu nutsuwa ya zauna Addu'a zai mata, ta sauka lafiya, yaya ma
da matanshi sun tausaya mata.



Sai da misalin karfe 9:am
Aka zo musu da Albishir din ta sauka, ta haifi *baby boy* Wata nurse ce tazo da Abishir din kada kuso ku ga farin ciki a wajen family din nan, Abbas ko daga hannu sama yayi yana ta fadin Alhamdulillah yana ta godewa ubangiji, hat da tukwici yaima nurse din, yana kokarin binsu suka ce ya dakata in an gyara babyn za'a miko masa abinsa sai tsiya suke masa na dokin shi.

Abba ma sai murna sai kace shine jikansu na farko, ummi kuwa an bata damar shiga don ta kintsa ta, tana shiga ta ganta da gani ba karamar wuya ta sha ba, ta nufe ta cikin Sauri tare da daukan babyn, tana tai Mata sannu, tace wannan babanshi ne sak, Rungumeshi tai tana masa addu'a.

Banyan an kintsa babyn aka kawo ma mahaifinshi rungumeshi yayi a jikinshi yana jlin wani irin son yaron aranshi bakinshi yaki rufuwa, yai masa huduba da sanyama yaron sunan mahaifinshi wato, *muktar*, ya kaiwa sauran yan'uwa suna masa murna kowa cewa yake kamarsu daya, abokanan aikinshi ma duk sunzo sunga baby sai pictures suke ta yi tare da babyn, suna cewa like father lyk son amma ya fika haske, jajir yake babyn kamar bature.


Banyan wasu awanni aka sallamesu ummi ta nemi da abata maryam domin tai wankan jegon a gida, fafur yaki yadda a tafi da ita, Abba yace a kyaleta a gidan mijnta a samu wadda zata je ta kula da su da jaririn.


Haka kuwa akayi suka wuce gida aka ce za'a kawo inna, kakar maryam wadda ta haifi ummi, duk da daman hafsa na gidan.


Bayan sun dawo tai wankanta tsaf da ita kamar ba ita ta haihu ba ta ciko tai bul-bul da ita, shiko yana zaune yana rike da babyn a hannunshi a gefen gadon, yace baby nah ba abinda zance da ke sai godiya kin Haifa min santalelen yaro zanso duk shekara ki dinga haifomin irinsu... Jifanshi tai da harara tace lallai kam tunda ba wuya ko???? Yace ba gashinan ya wuce ba. Bai bar dakin ba har sai da inna ta iso sannan ya fita.


*******************
Maijego ta samo kyakkyawar kulawa a wajen inna ta mata wankan jego yadda ya kamata, hatta dinkin da akai mata ya fara warkewa duk da cewa cin abinci ingantaccen shine jegon ba wai wankan ruwan zafi ba, shima anayi amma saffa-saffa.


Ranar suna 'yan'uwa da abokan Arxiki sun halarta gida ya cika makil da abokanan arziki angon karnin ma a ranar bai fita ba wai da shi za'ai taron yan'uwasa na tayi masa tsiya yace naji dae.

An gudanar da shagalin suna lafiya maijego tasha kyau kamar amarya ansha make-up, sai canja kaya take na gani na fada, shiko duk inda ta gifta idonshi na kanta, sai hotuna suke tayi tare da shi ya wani rungumota ita kuma tana dauke da babyn, abin sha'awa.

Aunty sadiya kuwa sai wullah harara take ko picture ba ai da ita ba, in an kirata tace tana xuwa, sai taki xuwa.

Anyi taro an watse duk yawancin dangin nasa can gidan yaya zasu kwana, sai da aka gyara gidan tsaf kamar ba ai taro ba an turare gidan da qamshin turaren wuta.

Bayan ta yi wanka an ma babyn Wanda suke kira da mufid, ta daukeshi zuwa dakin abbas kasancewa da sauran mutane a dakin, kuma shi ka'ida ne da daddare yaron a hannunsa yake sai zai kwanta zai mayar da shi wajen mahaifiyarsa, a zaune ta sameshi Akan wata kujera da ke cikin dakin ta mika masa Shi ta nemi waje ta zauna, a kan gado, karbarshi yayi yana sorry my boy an wahal min da kai ko? Kasha hannun mutane. Tace ai an masa wanka yanxu zai ji dadi, ido ya kafeta da Shi yace baby Kinga wani kyau da Kika Kara yi kuwa? Dama in an haihu haka ake Kara yin kyau, taso wa yayi ya xauna kusa da ita yana wani mata wani irin kallotare rungumota jikinsa yana fadin wai yai missing dinta sosai ya kosa, tureshi tayi ta nufi kofa tana masa gwalo tace duka yau fa satinmu daya amma had ka fara korafi, tasowa yayi aiko tai maxa ta fita ta rufe kofar tana masa dariya, sai ga inna tace auuu dama can kika tafi Ina ta nemanki yaran zamani ba kunya.. Tace inna yaron na kai masa fah..

Tace muke maza kici abinci ace maijego ta kai had wannan lokaci bata ci abinci ba, tace inna ai yau ne kawai aka kai haka fah.. Ta fada da shagwaba, ita shagwabar ma ta zame mata jiki, ko Ina yinta take.



Watansu daya mufid yai kiba sosai kamar Dan wata uku gwanin sha'awa, ga yaron da farinjini ko asibiti suka je ai ta son yaron, Abbas kuwa tuni an bude shafin wani amarcin tun kan ai arba'in gyara kuwa tun bayan suna take seatbath da bagaruwa da ganyen magarya da tafito wanka kuma ta shiga tai turaran kanumfari, ba tai wasa ba wajen gyara kanta kullum cikin yin juice din fruit ko ta sha kankana da madara ta yanka, shiyasa sanda ta koma wajen oga ta Kara sukurkuta shi sosai.

Banyan arba'in suka ziyarci gidajen yan'uwa da wajensu ummi tunda suka je yana bayan ummi said dai in yana Jin yinwa a bashi ta maida shi bayan.


Sabuwar rayuwa suka bude mai cike da so da kaunar juna in Abbas yana gida shike rainon mufid had goya shi yake a baya in yana kuka, sai ya dauki lokaci mai tsayi yana masa wasa, kusan rabin rainonsa dadyn shine yake, har tsarki saka pamoers, da sauransu ya iya.

Itama maryam tana Alfahari da miji kamar Abbas gani take itace mace mafi sa'a a duniya da tai dacen mijin, ta gama sadaukar da soyayyarta gareshi tana jin sa sosai a ranta, ta ko Ina yana basu kulawa ita da babynsu. Inna ko tun kan ayi arba'in ta tafi tace tunda maijego ta warke ai shikenanπŸ˜„
Sun hada Mata sha Tara
ta arziki sannan suka kaita har gida.



*muke zuwa*


*by*

*Ummi Ameer*πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€




*kuyi hakuri da jina Kwana 2 da bakuyi ba, uxuri ne yai yawa, ngd da kulawa*❀




*page* 1⃣3⃣







""”"sun kasance cikin so da kaunar juna, inda mufid sai girma yake har ya fara rarrafe yaron tubarkallah fine boy da shi.



Shekararsa daya daddynshi ya shirya mashi birthday aka Tara yan'uwa da abokan arziki domin taya shi murnar cika shekara 1, yasha gift sosai a wajen friends din iyayenshi, an sha hotuna abin sha'awa, har da Abbansa akai birthday din duk rabin pictures din yana rike da shi a hannunsa.


A wannan lokaci ne kuma ya samo mata admission a kano poly, diploma a Business administration, duk da cewa

Please Login or Register in order to submit comment