Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruguza masa rayuwa.

Hannu ya daga sama yana mai rokon Allah ya bashi ikon cinye wannan jarrabawa da ka yi min.

Dole ya bita ya sameta yana lallashi, da kyar ta hakura ta saurare shi, amma tace ka tsimayi zuwan mommy gobe, gara taxo ta taka maka burki, don nan gaba bamu san me zaka yi ba kuma

Tana ambaton mommy yaji wata mummunan faduwar gaba, baisan dalili ba duk sanda suka hadu da ita wani irin shakkarta yake yi, dama ita fuska ba rahma a tare da ita, don kafin kaga murmuahinta za'a dade, to gara ma in suna tare da kwayenta, bare ma anty batulu.
Allah ya kaimu yace.


Sai a lokacin ne taji Dan tausayinsa, tason in suka hadu da mommy bata masa da dadi ko kadan, shiyasa ma sanda tana gida bata son haduwarsu da mommy, ita kuma gani take kamar uwargidan ta Riga ta gama da shi gara tun wuri aima tufkan hanci, gashi kullum jin wani irin sonsa takeyi yana shigarta, shiyasa bata so ko kadan ya dinga nesa da ita, in aka ce zata fita girki kuwa ranar kamar zatai hauka don kishi.




*washe gari*

Washe gari tunda safe kafin Abbas ya fita office mommy ta dira a gidan, banyan an kawo Mata break fast taci, sa'annan Abbas yazo ya gaisheta, ta amsa a Takaice, ta fara mgana dama ba wani abune ya kawoni ba Akan complain din da take kawo min ya isheni haka, tace kana zuwa gidan uwar gidanka kai zamanka har kaci Abinci acan to wlh bazai yiwu ba, Baka isa ka maida min diya bora ba, in anyi magana kace yara, to in ma yara 100 ne da kai ba abinda ya shafeni, ni tawa na sani dole ne abinda zakai acan ayi anan kana jina, shi dai kawai daga kai yake yi, kanshi akasa.

Sbd haka ya zamo farko ya zama karshe kar in kuma jin wani complain daga gareka, yadda kake kaunar yaranka, haka nima nake ji da tawa, ta fada tare da tashi ta dauki Jakarta ta fice, yace a sauka lfy!
Yar ta bita tana mata a gaida gida, tare da bata wani kulli a Leda tai Mata a rada a kunne. Ta wuce.


Bayan ta dawo ciki ne taje tana masa wata munafukar kissah wai baby kayi hakuri da mommy, haka take, shiko ko tanka Mata baiyi ba ya ce na wuce office, tai masa Allah tsare.


A cikin mota kuwa ba Abinda yake masa yawo akai sai maganganun surukarsa suka ta maimaita kansu a kunnensa, har ga Allah ranshi ya matukar baci, ji yake bata da wani sauran daraja ynx atare dashi, ya fara gajiya da halayesu completely.


Itako sai faman murna take da sakon da mommy ta kawo mata gani take da zarar tayi amfani da wanan magani kashin maryam ya bushe, wani mugun murmushi tayi, tare da fadin yarinya zaki gane kurenki, sai kin koma inda kika fito ne, Abbas da ni kadai yafi dacewa....






*ummu Ameer* 💃🏻
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀





*story&written*


By


*ummu Ameer* 💃🏻






*page* 2⃣1⃣





""""" sai dai kuma Rukayya ta manta da cewa Abbas ba a gidanta yake ba, said daga baya ta tuna hakan, ko da Abbas ya dawo gidan rukayya ya wuce kamar yadda ya saba, yana shiga yadda ya bar gidan da safe haka ya sameshi ynx bacci ma ya tarad tana yi ko qamshin turare babu, kuma ga turarukan nan da ita burjik amma kiwa ta hana ta kunnawa, yana takaicin wannan hali nata, ita bata san hanyar mallakar miji ba sai yadda zata kwace shi karfi da yaji, ba wani matakai da take bi, amma ko kadan shakkarta ya hana ya mata magana, don a zahiri bai son ya mata abinda zai bata mata rai. Amma shima yana mamakin yadda ba ya iya mata magana akan abubuwan da bai kamata ba.


Tashinta yayi daga baccin da take yi ta mike ta shiga toilet ta wanke fuska, sa'annan tazo yai masa sannu da zuwa, suka taba hira sama-sama yace zai tafi, nan ta shiga jan hankalinsa wai don ya dauki lokaci bai tafi ba, itama ta hada masa bom wajen maryam, mace akwai makirci, sai da yai wajen 2 hours sannan ya tafi, ita anfi xama qalau ranar da ba girkinta ba, sbd tafi samun damar yin makircinta a lokacin.




Bayan ya isa gidane tun a waje yake jiyo qamshi na tashi, har wata nutsuwa ya samu, tare da sauke ajiyar zuciya yana mai Alfari da ita, dabance a cikin sauran mata, yana shiga ya sameta zaune a falo tana kallo tana jin shigowarsa tai Saurin zuwa tarbarsa tana masa sannu da zuwa, yace yawwa uwargida sarautar mata, murmushi tayi ko kadan ba bacin rai a fuskarta na jimawan da yayi bai dawo ba, kuma bata tambayeshi dalili ba, daukar elham yayi yana Mata wasa shiko mufid yayi bacci, yace rago bai jirana in dawo yai baccinshi, tace wlh tun daxu yake ta jiranka da sunanka a Baki yai bacci, Allah sarki my boy! Zuwa inda yake baccin yayi yana shafa masa kai yai kissing dinshi.


Itako karbar jakar hannunsa tayi da ledojin
Ta ajiyesu, tace ga ruwan wanka can na hada maka, yace tnx my lovely wife, Allah ya miki Albarka duniya da lahira!
Ameen tace

Sanann ta bishi domin taimaka masa, bayan ya shirya da taimakonta, yai sallah isha'i sannan suka fito domin cin abinci, rike yake da elham a hannu ya zauna Kan dining dorata yayi a cinya yana bata abincin, tace husby karfa ka bata da yawa taci daxu sosai, yace ai ba abinda zai mata tunda tana ci sai abata, tace oh elham Baki gajiya da cin abinci ko, yarinya kuwa har da daga kai Alamar eh!, suka kyalkayale da dariya, haka suka gama xin abinci, cikin farincikin da annashuwa daka gansu kaga masoyan da suka yi nisa da kaunar juna.


Shi kanshi baya samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai ranar da yake gidan maryam, tana iya kokarinta wajen kyautata masa, kuma ba wai bata kishin bane, tana yi amma na nutsuwa, domin nuna zazzafan kishi akan namiji ba shine solution ba, asali ma shi yake kawo zubewar kima da daraja, ko da ace wani abin yayi a cikin lumana sai ki gaya masa kuskurensa, kuma wlh zai gyara, kuma hakan zai jawo miki wani matsayi na musamman a zuciyarsa, maryam tuni ta gano tana jan ra'ayinsa ne, ya bata lokaci a wajenta, in ya dawo tai tunanin ko soyayyarta ta hana shi dawowa da wuri, shiyasa ko kadan bata taba nuna masa bacin rai ba, da dai fa itace, tai tunanin kowa ma haka yake.




Bayan Rukayya ta karbi girki ne, tai ta fama da rashin lfy, bata iya komai ko da suka je hosp. An tabbatar tana da juna2, na wata 2,farinciki a wajenta bai misaltuwa zata samu zuri'a da Wanda take kauna Faye da komai, shima ba laifi yayi farin ciki domin mutum ne mai kaunar yara, tun daga lokacin fa sabuwar kazanta tai sallama bata yin komai kullum wai ba lfy, hakane yasa aka samo mata wata dattijuwa tana zuwa tayi mata aikace2 sai ta tafi, to da taimakon yar aikin ne ma gidan yake samun tsafta, kuma wani lokacin kannenta na gidan bazata saka su suyi ba.


Shi kuwa Abbas zuwa ynx ya fara gajiya da sintiri tsakanin gida biyu, ya fara tunanin hade matansa waje daya, duk da yasan ba karamin Abu ya debowa kansa ba ta bangaren ruky da mom dinta, yana sane da tsarinsu na rashin son kasancewa da kishiya gida daya, domin sai da sharadin aka amince da aurensu, shi kuwa ganki yake rashin kasancewarsa da yaransa waje daya, yana rage shakuwa tsakaninsa da yaransa, wani lokacin sai sun yi bacci, zai dawo hakane yasa yake ganin gara ya hada su waje guda, domin hakane zai sama masa nutsuwa, shima ya huta da sintiri..



*tofa masu karatu kuna ganin kuwa hakan me yiwuwa ce a wajen rukayya da mommy*


Ki biyoni don jin yadda zata kasance.....



*ummu Ameer ce* 👌🏻
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀








*Story&written*


*By*


*ummu Ameer* 💃🏻






*page* 2⃣2⃣






A kwana a tashi cikin Rukayyah sai girma yake lalaci kuwa sai abinda yai gaba, gashi sun koma sch. Abubuwa sun Kara kacame mata, rashin hakuri da bakin kishinta kuwa, sai abinda ya karu, domin kuwa kusan yajinta uku ynx, wani sabon salo ta tsiro da shi ko kuwa uwar ce ta kirsa mata, oho! Don ynx suna yin Abu da Abbas bai taka Kara ya karya ba sai tayi tafiyarta.

Ranar da ta fara yi kuwa watarana ce tace tana so ya kaita taga maryam, kuma dama gulmace zata kaita take taga wadda yake rawar kafa akanta, bai musa mata ba yace ta shirya su je, ta shirya cikin nadin laffaya blue ta sanya flat shoe sai yar powder da ta shafa, ita bata cika son yin make-up ba. Dama ranar girkin Rukayyan ne.


Shi kuma tuni ya buga mata cewa Amarya zata zo su gaisa, tace Allah ya kawoku lfy!

Ta hada mata lemon kwakwa, da Abarba snacks kuwa Dama bata rabo da yinsu ko da yaushe kaje gidan. Ta sanya wata Doguwar riga mai igiya ta ciki, ta daura mayafi akanta kalar rigar tai kyau.


Jin karar motar sa yasa yara suka nufi gun daddynsu, a guje suna masa sannu da zuwa, itama yace wa rukyn anty sannu da zuwa, tace yawwa ba tare da sakin fuska ba, daman ya taba zuwa da shi gdn har yake tambayar dad dinshi wnn wacece yace ita ma momyn kace, sau tari ma in zai kaishi sch. Itama in a ranar tana da lecture, yana biyawa ya dauko ta sai ya fara sauke mufid daga nan sai ya wuce ya sauketa a makarantar.

Suna isowa ya dauki elham tare da mika mata chocolate din da ya siyo musu sai mufid kuwa tuni ya shiga gida yana Kara fadawa momynshi ga dad da dayar mom dinsu, tace to sannunsu da zuwa.

Tun daga kofar gidan ta fara sanin ko wacece maryam domin ko Ina ta kallah tsaf da shi ga wani qamshi mai dadin ji, bata Kara raina kanta ba, sai da ta shiga falon, a zuciyarta tace ngd wa Allah da ba itace ta fara zuwa gidana ba, ai sai ta raina ni, sai a lokacin itama ta fara ganin laifinta na kiwa, ita ba yara ba, ga mai yaran ma amma gidanta yafi nawa kyan gani, zazzakar muryar da ta ji tana cewa zauna mana sis rukayya ita ta dawo da ita hayyacinta, ai nan da nan ta Kara kaduwa da ganin haduwa a wajen maryam, sai faman kallonta take, ba ko kyafta ido, ita ko mijinta ta tsugunna tai masa sannu da zuwa, bayan yan seconds, ta dan samu nutsuwa, ne suka gaisa maryam fuska a sake, bata wani nuna mata komai ba, amma a zuciyarta dannewa tayi ganin husbyn ta da wata matar sbd wnn shine karo na farko da suka da ta gansu tare, ita kuwa mutuniyar tuni fuskarta ta canja ita da bata iya danne Abu, bayan gaisuwar ne ya hada su yai musu nasiha, inda yace maryam ga Rukayyah, ke kuma rukayya ga maryam Ina fatan zaku bani hadin kai wajen gudanar da adalchi tsakaninku, ki hade kanki tamkar yan'uwan juna, Ina muku fatan Alkhairi gaba daya,
Maryam tace insha Allahu, Allah ya bamu ikon kyautata maka, yace Ameen, ita kuwa ruky tunda ya fara magana ko uffan bata ce ba, domin tuni ta gama raina kanta, ga kishin wai Abbas ya zauna kusa da maryam kamar itace da girki zai wullah masa harara take amma bata bari sun gani ba, yace rukayya baki magana ba, tace bani da abinda zance.

Maryam ta cika mata table, da kayan makulashe, tace bissimillah, ruwan kawai ta sha a kayan da aka kawo mata, duk inda maryam tayi dai binta fa kallo take tana mai jin haushinta, sbd maryam duk inda mace take ta kai, mai diri fa kyan siffah ga kyau ga nutsuwa, itako Rukayyah irin siraran matan nan ne da siffar jikinsu take mai kama da muciya, sun tafi 1 ba gaba ba baya, itama bakace amma ba can ba, tana da nata kyawun amma bata Kama kafar maryam ba.


Ba yadda ba ai da ita ba taki cin komai, shikuwa gogan tuni ya bude ciki sai faman kwasa yake hankali kwance.

Ruky kuwa tuni ta gama kuluwa da shi, yau ga zahiri ta gani daman tasan nan yake cin Abincinsa, shiyasa in takawo masa sai yaci kadan yace ya koshi, ba shiri ta mike, tashi mu tafi, tace masa, shiko yana ganin yanayinsa yasan akwai gwarama, nan da nan ya cika fal da tsoron abinda zai biyo baya, ya tashi ya shiga dakinsa ya kira maryam domin tambayatta ko da wani abin tace ba komai yai Mata godiyar tarbar mutumcin da tayi mata, tace ba komai ai kafi karfin haka a gurina, ya bata hot kiss a kumatu, sukai sallama y fita, ruky kuwa tuni tayi gaba, tunda taga sun shiga daki, yaran nasa kuwa ko irin jansu ajiki dinnan bata yi ba, suna fitowa suka ga ba ita, cikin sauri ya bita, ita kuwa tsayawa tai tana kallon ikon Allah!
Tace ko sallama bata tsaya munyi ba, ni da ya kamata nai kishin mijin ita takeyi, karfin hali! Don tuni ta gane ba abinda ke yawo da ita sai kishi, bata iya danne kishinta.


A mota ya sameta sai faman kuka takeyi, yace lfy ba sallama sai ki taho haka akeyi?
Dago fuskarta tayi cikin bacin rai tace bansani ba, maci amana kawai, dama ka kawoni ne don ka nuna mata ni ba kowa bace a wajenka, nayi nadamar aurenka, kasan kana matarka, mai yasa ka Kara yin aure, eyehh? Tambayarka nake?

Shiko tuni idanuwansa sun yi jajir da bacin rai, da mamaki ya kalleta, yace ni kike gayawa haka, an gaya maka kayi duk abinda zakai, tuni zuciyar sa ta fara ayyanah masa abubuwa da dama akanta, ace kanwar kanwarsa ta dinga gaya masa irin wadannan kalaman, ko daga murya maryam bata taba yi masa ba, bare irin wnn rashin kunyar, shiru yayi ya kasa ma magana don bacin rai, motar yaiwa key, ya figeta da wani mahaukacin gudu, tace mallam kada ka sake ka maida ni gdnka, don wlh bazan kwana a gidanka ba. Bai saurareta ba ya ci gaba da gudu kamar zai tashi sama, suna isa ta buga tsaki ta juya zata koma titi, bai hana ta ba, yana kalloh ta hau napep, shi kuwa cikin gidan ya shiga yana isa ya zauna Kan 2seathet, domin jin kansa na wani sarawa yakeyi, sai fadin inna lillahi wa'inna raji'un kawai yakeyi, tare da tunanin abubuwa barkatai game da wnn baiwar Allah yana tunanin lallai boye masa halinta tayi domin ya fahimci ta fara zama mahaifiyarta.


Yaso komawa wajen maryam, amma gudun kar tai zargin wani Abu yasa y hakura, yai kwanciyarsa.

Washe gari da sassafe ya fita, ya je daukan mufid Kana ganinshi kasan akwai damuwa a tartare da shi, amma gudun kar tayi masa katsalandan yasa taii shiru da bakinta
Kuma yace ta hada masa breakfast ya tafi da shi, nan ma kamar tai masa magana, tai shiru ba musu, ta hada masa, ta san dai tabbas da matsala, ganin bai gaya mata ba, itama tai gum da bakinta...

Yana fita wayar momy ta shigo wai tana son ganinshi ynx2 yace yana da patients in ya sallamesu zai zo... Bata jira wata mgn ba ta katse wayar...

Ta saka diyarta a gaba, sai faman masifa take mata, da farko cewa tai duk abinda yai miki ke kika jawo da kika nace sai kin aureshi, daga baya kuma sai tausayin yartata ya kamata ta hau tambayar kina amfani da wadannan abubuwan da na baki, tace eh!
Tace taurin kai ne da shi kenan zanyi maganinshi, zaizo ya sameni dani yake zancen...

Nan kuwa bata san mutum ne da baya sake da kare kanshi da addu'oi ba, ga matarsa da take hana kanta bacci wajen kai kukanta gurin ubangiji.

Duk da dai akwai wadanda suke tasiri akansa,

Bayan ya tashi daga office direct gidan ya nufa amma wnn karon zuciyar sa a dake take domin ya fara daina jin shakkarsu a shirya yake da koma me zai faru ya faru...






*ummu Ameer ce*👌🏻
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀






*story&written*



*By*


*ummu Ameer* 💃🏻






*page* 2⃣3⃣





Yana isa gidan ya aika ace musu ya iso, akace ya shiga, a falon ya tarar da su mommy, da anty batulu, sai Rukayyah zaune a kasan carpet, tayi wani firki2 da ita.


Sallama yayi anty batulu ta amsa masa, mommy kuwa tana hakince akan kujera sai jifansa da harara takeyi, bayan ya gaishesu ne, sa'annan anty batulu ta fara yi masa mgn akan abinda ya faru tsakaninsu da Rukayyah, haduwa sukai da mommy sukai masa cin fuska, har suka ce in ya ga bazai iya ba, ya bata takardarta, ai bashi kadai ne autan maza ba, ruky ko naji an fadi haka, tace mommy bafa shi yace na taho ba, nice na taho da kaina, shutup! In nasake jin bakinki sai ranki, ya baci shashasha kawai, Ana nema miki yanci kina shirmen banza.

Shi dai tunda suka fara shirmensu baice uffan ba, baisan me yasa ko da yai shirin maida musu martani bai iyawa, bai saba ba, ko kadan baijin zai iya jayayya da ita ko akasin haka, tunda shi daga gidan tarbiya ya fito sun san mutumcin mutane.

Abinda kawai yace shine ayi hakuri, bazata sake faruwa bah, itako tuni ta shiga daki ta dauko mayafinta, don tuni ta fara tsoron kar mommy ta guntule mata auren nata, don a gaskiya tana
matukar kaunar mijinta.

Mummy kuwa tsayawa tayi tana mamakin diyarta, zatai magana anty batulu tace kyaleta, Allah kiyaye hanya.

Sallama yai musu suka tafi....

Mummy kuwa kallon batulu tayi cike da mamakin diyarta tace Ina tunanin cire hannuna a lamarin yarinyar nan, kina ganin abinda takeyi? Sai kace wacce ya asirce, Ana kokarin nema Maya yancin tana hauka!

Batulu tace kyaleta ai namijin ne, namiji dan kunama, namiji takalmin kaya! Namiji buhun kaya! Ki zurata mata ido zaki sake jinsu ne, mazan ynx ma ka tsaya da kafafuwanka akansu ma ya ka kare bare ita da take wulakanta kanta akansa...





A mota kuwa tunda suka fara tafiya ba Wanda ya tanka, da ta ga shirun yai yawa, shine tai ta damunsa da surutu, shikuwa ko tanka mata bai yi ba, har suka isa gidan.


Ko da suka isa gida kuwa, ganin bil hakki fushi yake da ita yasa ya zo ta bashi hakuri, sannan ya saurareta.





Amma da aka kwana 2 sai da ta Kara tafiya har sau 2 amma gdn kanwar mommy ta tafi sai da tai wajen 2wks bai je ba, sai da Antyn ta kira shi, dake ita tana da hankali, ta binciki abinda ya hada su kuma ta gano laifin rukayyah ne, tai mata fada sosai, sannan ta bashi hakuri. Suka tafi....






Bayan abubuwa sunyi sauki ne, domin ya fahimci ta dan canja halin nata, a lokacin cikinta na wata bakwai, ya bujoro mata da batun yana son hada su gida daya da maryam saboda wasu dalilai, abinda yasa bai mata magana ba tun baya, lokacin da sauran kima fa shakkarta a zuciyarsa zuwa ynx kuwa babu, dama a zamantakewar aure "yaji" yana taka muhimmiyyar rawa gurin zubda kima a wajen miji, matakine na farko da yake taka muhimmiyyar rawa wajen rusa kanki, saboda su kansu mazan sun san matsayinki a wajensu, na tona zamantakewar rayuwar aurensu a wajen iyaye, ki bata su, ki shirya su kuma iyaye suna nan da tsanarsa a ransu tunda tun farko kin bata shi a wajensu...
Ga kuma karfin addu'ar da yake yi shi da matarsa, shiyasa ya zamto yanzu ba wani sauran shakka ko makamancin haka a ranshi game da ita, shi yasa ita kanta ynx wani shakkarsa take bata iya yi masa abinda take masa da...

Aikuwa tana jin ya ambaci hada gida batasan sanda ta mike cike da tashin hankali ba, tana fadin Abbas kasan abinda kake fada kuwa? Yace kwarai ma kuwa

Gaskiyane lallai na yadda namiji ba dan goyo bane, ynx na fahimci abinda mommy ke son fahimtar dani akanka..

Ina Alkawarin da kai min tun kafin na amince da soyayyarka Abbas, ynx irin sakayyar da zakai min kenan?

Ko daya yace ba nufi na kenan ba, kawai zuwa ynx ne naga bazan iya jurewa ba, na farko Ina da gidana na kaina kuma wadatacce, nan kuwa haya nake yi aciki gashi tsarin unguwar baimin ba, sannan Ina so na hada Kan yarana da matana waje daya...

Dakata mallam ni ba abinda na tambayeka kenan ba, kasan duk da wadannan me yasa kai min Alkawarin bazaka hadani da kishiya ba, kuma ka yi wa mahaifiyata Alkawarin hakan itama, to wlh tafiya gidanmu zanyi bazan zauna da kishiya ba, sbd matarka ta gama shanyeka sai abinda tace da kai za'ayi, shine ynx ma ta bujuro maka da wannan to wlh bazai yiwu ba ynx nan zanje na gaya ma momy..


Shi dai bai tanka mata ba, yasan dama za ai haka, kuma ko ta tafi yasan ma zata dawo ne...


Shiga daki tayi ta dauko akwati ta bi gidan da kallo, tace masa maci amana kawai ta yi gaba...


Shikuwa a zuciyarsa yace illar yar mace kenan.. Batuna kuma ba fashi....







*ummu Ameer ce* 👌🏻
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻











*Godiya main tarin Yawa masoyan wannan book din Allah ya bar zumunci*



*Story&written*


By



*ummu Ameer* 💃




*page* 2⃣4⃣

Bayan tafiyar ruky, ya debi duk kayansa sai gidan uwargida, dama ko sallama baijje ba sun tsaya hayaniya da uwar kishi...



Ko da ya isa gida bayan ya saba yin abubuwan da yake yi kafin ya tafi, maryam ta ga bashi da niyyar tafiya, tace Abban mufid dare fa yana yi naga baka da shirin tafiya...


Shiru yayi na dan wani Lokaci Sannan yace ba tafiya xan yi ba anan xan kwana...


Sbd me? Ta tambayeshi yace matar gidan ce bata
nan..

Tunda taji haka tasan akwai matsala a tsakaninsu, bata sake tambayar shi ba, yace ta je ta hada masa ruwan wanka, ba musu ta tashi tayi kamar yadda ta Saba...


Bayan yai wankan ya kintsa ta kawo masa tea kamar yadda ya saba sha kafin ya kwanta..

Bayan ya gama ya samu nutsuwa ne, ya gaya mata abinda ke faruwa tsakaninshi da rukayya..


Itama kuwa ba karamin tashin hankali ta shiga ba, da jin zai hada su wuri daya,...

Abinda yasa ita bai fara gaya mata a tunaninsa baza a samu matsala daga gareta ba, kasancewar yasan bata da matsala, Kuma duk abinda Yazo mata da shi tana karbar shi hannu 2 koda ba tason abin a ranta..

Aikuwa tana jin haka tace haba Abban mufid kayi hakuri dae ka barta a can ko don kwanciyar hankalinka, acan dinma ya aka kare balle Kuma nan plxxx ka canja tunani gaskiya domin kuwa nima hankalina yafi kwanciya tunda tun kafin kai auren ka tsara haka..

Yace akwai dalilina na yin haka bana jin dadin yadda bana kasancewa da yarana ko yaushe.. Wani lokacin bana samun ganinsu sunyi bacci, gashi Ina son hada Kan yarana da matana waje daya domin samun nutsuwa, amma ni kenan cikin sintiri tsakanin gida 2, ba zai yiwu ba!



Shiru tayi a ranta tace ai da kafin auren bakai tunanin haka ba sai ynx..

Kuma tasan halinsa sarai in ya dage akan Abu to fa ba mai canza shi..

Itama nan ta barshi a wajen ta nufi daki, tana tunanin wnn gagarumin lamari da ya dauko, tace lallai idan har haka ta kasance to sai ynx ne zata san tana da kishiya..

Tunda wani lokacin ma mantawa take tana da kishiyar domin bata sa ta a ranta ba, ita dae ko yaushe cikin yin abinda tasan zai farantawa mijinta rai take, bata dameta ba ko kusa..





***********************
Itako rukayya ko da ta isa gida ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya mata.. Aiko mummy najin haka tace wlh zamanki da shi ya kare gobe xan aika masa ya aiko miki takardar ki, bama

Please Login or Register in order to submit comment