Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€





*story&written*


*By*



*ummu Ameer* πŸ’ƒ





*GODIYA MAI YAWA DA COMMWNT DINKU, ALLAH BAR ZUMUNCI* 🀝









*page* 1⃣7⃣







""Bayan isowarsa gida yayi ta knocking ba'a bude ba, motar ya koma ya dauko spare key din ya bude gidan ya shiga, ganinta yayi a kwance kan 3seater, tana bacci, da alamu baccin bai dade da kwasheta ba, murmushi yayi a zuciyarsa yace Allah sarki wiffy, nasan da bacin raina kika kwanta, lekawa yayi daki inda yaran suke suna bacci, gyara musu kwanciya yayi, yai musu Addu'a, ya sumbace su a goshi yace gudnyt my lovely kids.

Fitowa yayi falon ya tarar bata da niyyar tashi, key din motar sa ya dan sa mata a kunne yana mata susa da shi, firgigit ta farka tana subhanallahi, ka bani tsoro wlh, sai ya yanxu ka dawo daga wajen amaryartaka, ai nazaci can zaka kwana ta karashe maganar da wullah masa harara, ta mike xata shige daki ya janyota ta xauna a cinyarsa, yace wlh baby Motana ne ya samu matsala wajen 2hrs na bata akanta, ba wai da gan-gan nai ba, ayimin afuwa, tace Amma nai ta kiranka kaki picking, why?
na bar wayar ne a mota.
Shikenan! Ta bashi amsa.

Muje kan dining kaci Abinci ba musu ya bita tai saving nashi, yace lallai in tana so yaci sai ta bashi, hakanan ta ringa bashi, yana ci yana santi, har ya koshi, tace ya Amaryar?
Yace tana gaisheki, sun dan taba hira daga bisani suka je suka kwanta.




*washe gari*

Ranar Alhamis kenan itace ta Kama Ranar kamu, 'yan danbatta ma sun taho bikin a Ranar, gidan yaya suka sauka, sai daga baya ne sauran 'yan'uwan suka leko gidan maryam din ta karbesu hannu biyu, kuma ta burgesu ganin ba wani damuwa da ta sanya aranta, akasin wasu matan da in Ana bikin mijinsu ko kallon arziki ba suyi yan'uwan mijin suna ganin kamar su suka Sanya shi. Hirarsu sukai tayi har wajen la'asr, Amma anty sadiya tana can gidan yaya bata karaso gidanba.


Angon ne yayi waya da misalin karfe 5:pm, yace zai zo ya kaisu gidan amaryar kamu, jimawa kadan sai gashi ya fara dauko aunty sadiya da matar yaya, sai yayar mahaifinsu da sauran yan'uwansa.



Suna isa ya sauke su ya nuna musu gidan ya wuce daman mota 2 sukai, da ta yaya sai kuma tashi yace zaije ya dawo, suna shiga gidan sun tarar da gidan makil da jama'a sai shagali suke, suka bayyanah kansu cewa dangin ango ne sunzo kamu, ba wani tarbar arziki da sukai musu sai wani kallon wulakanci suke musu, kowa sai binsu yake da kalloh, suna ta yin yarensu, aka kawo musu wata jallof fara fat da kuma zobo an kullah a leda don wulakanci, sannan suka ce suyi hakuri tuni an yi kamu, itako aunty sadiya an sa rai za'aje aci kaji, ba karamin haushi ta ji ba, haka suka dauko jiki suka fito jiki a sanyaye, sauran yan'uwansa na fargabar abinda Abbas ya debowa kansa, don ita uwar amaryar ma ko kula su bata yi ba, sai wani kallon kyama take musu, tana mai jin haushin 'yarta da ta kwaso musu tarkace, dogon tsaki tsaki ta ja tayi shigewarta daki, sai aunty salma kanwar momynce ma ta sauraresu.


Suna fita suka ganshi ya dawo suka shiga mota suka wuce a hanya ne daya daga cikin yayunsa tace nikam Abbas me ya kaika kwasowa kanka irin wadannan mutane da basu san mutumcin dan Adam ba, wata acikinsu ta Kara da fadin ai ka ci gaba da kula da matarka Domin samun kamar maryam da wuya, daga ganinta Kasan ta fito gidan tarbiyya kayi dace da matar kwarai ka riketa amana ga hakuri yarinyar arxiki, yace gaskiya kam maryam ta dabance tana da hakuri, itako aunty sadiya ta6e Baki tayi ba magana.

Yace anty wani abun sukai mukune, suka a'a Amma dai gidan ba karamci a cikinsa.


Hira sukayi tayi har suka ISO cewa sukai ya wuce da su gidan yaya karsu takura musu, ga yara karsu isheku da kiriniya.



******* ****** ********
Bangaren gidansu amarya kuwa Mommy ce a daki ita da aunty batula, mommyn na gaya mata wai ita wlh Addu'a take Allah ya kawo sanadin da auren nan zai ruguje na tsani auren banso ko kadan, duk cikin yarana ba mai taurin kai irin Rukayyah da taji maganata da ba a kai ga haka ba, aunty batulu tace ai sai dai ki hakuri yar'uwa, abinda zamuyi ynx shine mu gina diyarmu, shine kawai
Kwafa mommy tayi,
Aunty batulu tace taso muje cikin jama'a kar azo Ana neman uwar amarya. Fitowa sukai da kaya iri daya suka sanya ita da kawar ta, suka cigaba da gudanar da shagalinsu na kamu, ita amaryar ma bata san cewa dangin Abbas sunzo ba, kuma tasan halin mommy da kyar in bata yi musu halin nata ba. Yau kuma amaryar sanye take da wani tsadadden lace, pink Riga da zani tayi karamar buba mai dogon hannu ta dora zanin akai sai blue head ta aka jera masa stones da takalmi blue sai irin maficin da amare ke rikewa, an mata make-up, tayi kyau ba laifi.
Dama tun safe sukai waya yace bazai samu xuwa ba, sai dai Ranar dinner.






Yau juma'a itace Ranar dinner tuni dama Abbas ya bada odar komai da komai a inda za'ai dinner din, na mutum 150.

Ba yadda baiyi ba akan maryam ta shirya suje Amma kememe taki tace ba inda zani.

Karfe 7:30pm tuni an fara kwasar kawayen amarya da sauran yan 'uwa xuwa wajen, amaryama ango take jira ya iso su tafi, tayi kwalliyah cikin wata doguwar riga orange color head dinma haka, rigar tana jan kasa.

Ango kuwa yana can shima ya shirya cikin wani tsadadden boyel fari, sunyi masa kyau ya feshe jikinsa da turare mai qamshiii, maryam tace kayi kyau angon Rukayyah, yace ita Kadai, tace a yanxu ba, ai mu namu ya wuce, yace a wajenki ba, Kiran amarya ne yai ta shiigowa tun yana dauka har ya daina waii Ana ta jiransa, maryam tace muje na raka ka mota ka tafi, yau ma har mota ta rakashi sai dai yau da abokanasa guda biyu a motar suna ta yabawa madam din tashi ta burgesu da rashin nuna kishinta, sauran abokanan nashi kuma duk sun wuce daukan kawayen amarya xuwa wajen dinner.


Suna isa ya kira ya iso, aka taho da amarya aka bude mata bayan mota ta shiga kusa da angonta, sai Yusuf dake jan motar sai Ahmad dake kusa da shi,


Wajen dinner ya cika a haka ma an hana wasu shiga sbd in baka da gate pass, ba zaka shiga ba, uwar amarya da kawayenta ma duk an hallara sunyi ankon lace blue ita da kanennta da batulu itama aunty nusaiba matar babansu taje, Ana ta gudanar da programs din da suka shirya, an yi hotuna amarya da ango sunsha pic, ko wanne sai ta kwanto jikinsa, sun dauka, sunyi da uwar amarya da kawayenta, bayan ciye-ciye da akayi an taka rawa inda amarya da ango suka fito, amarya ta zake sai rawa take tana rike da hannun ango, shiko ba wata rawa da yayi shi kunya ce ma ta kamashi ga surukarsa itama ta zake da kawaye sai rawa suke Ana musu liki, fita yayi daga filin rawar yaje ya zauna yana mamakin surukarsa, wayewa ko zamani?



Sai kusan 12pm aka tashi ya maida amarya gida shima ya wuce yayi ma friends din shi godiya da ban gajiya, dama bai gayyaci yan'uwansa ba ko daya.






Ranar asabar AKa daura auren Dr. Abbas mukthar danbatta. Da Rukayyah usman. A masallaci. Akan sadaki naira 50k.

Kuma aranar ne za'a kai amarya gidan mijinta, itama maryam a Ranar har da shirya walima ta gayyaci kawayenta da yan'uwanta. Kada mai karatu kaso kaga yadda ta hadu cikin wani tsadadden code lace red, tayi kyau ba kadanba don ko amaryar sai haka kasancewar ta iya dressing ko yaya ta sa kaya yana amsar jikinta, anci ansha a wajen walima inda mai lecture da aka dauko tai tayi musu nasiha mai ratsa jiki, tare da shawarwari akayi ta Mata godiya.



Su Aunty Aisha ma wato yayun maryam sun yi Mata nasiha da shawarwari da kuma addu'oi da zata dinga yi, kuma suna ta yabon kanwar tasu ta burgesu bata dorawa kanta bakin Kishi ba.


Gidan Amarya kuwa sai a lokacin ne ake mata jere itama ba laifi an mata kaya gwargwado, duk da wasu abubuwan shi aka dorawa yi.

Tuni motocin daukar amarya sun ISO gidansu amaryar Ana ta divan mutane.

*mu hadu gobe insha Allah*






*By*

*ummu Ameer* πŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€







*story&written*


*By*



*ummu Ameer* πŸ’ƒ








*page* 1⃣8⃣







"""An kai Amarya gidan Angonta, cikin wata laffaya green color ta Sanya ta sanya Riga da wando a ciki, ta sha kwalliyah sai da aka turara kayan da turaren kaya, gidan cike yake da mutanensu basu da niyyar tafiya. Itako Amarya ta kosa angon nata ya bayyanah.




Can wajen maryam kuwa itama shigar Riga da skirt tayi na atamfa yellow mai ratsin green, kayan sun Mata kyau ba kadan ba, itama tana tare da kawayenta da sauran yan'uwanta sai makota, sun tsaya domin su karbi amarya, a tunaninsu za'ai fara kaita gidan uwargida kamar yadda aka saba, ko da Abbas din yaima 'yan'uwanta magana akan su fara kaita wajen abokiyar zamanta, cewa sukai ai ba itace ta auro musu diyarsu ba inda zasuje, in ita amaryar ta ga dama taje daga baya, ko kadan Abbas baiji dadin haukan ba yana mamakin rashin halin dattako irin na wadannan bayin Allah, shiko ba inda ya tsaya sai gidansa wajen uwar yaransa, Dama Already ya sanar mata a waya amaryar ba Zata samu xuwa ba, sai daga baya, tace ba damuwa ai kasan kowa da irin tsarinsu, itama ta sanar da wadanda ke jiran tarbar amaryar kowa ya Kama gabansa, zainab ko taso ta tsaya ta ga amaryar, haka nan ta tafi sai da ta Kara lallashin maryam da ban Baki, domin ta fuskanci ta fara shiga wani yanayi.
Duk an watse a gidan daga ita sai hafsa sai 'yar yayarsa khadija kusan sa'ar hafsance jininsu ya hadu shiyasa suka kulla abota da juna, sune suka tsaya Domin taya maryam din kwana.

Sun gyara mata ko Ina sun turareshi ko gidan Amaryar sai haka.

Shikuwa Abbas da wani wanda zai dinga yi masa gadi ya taho kasancewar ynx ba ko yaushe zai na kwana agidanba, yana isa ya nuna masa masukinsa, ya kuma bashi amanar kular masa da gida, yana shiga gidan bai tadda ita a dakinba, sai su hafsa a zaune suna kallon Arewa24, gaisheshi sukayi, ya amsa yace bakuyi bacci ba, sukace eh!

Tunda bai gantaba anan ba yasan tana daki, direct ya shiga ko da ya shiga a zaune ya sameta tana latsa wayar hannunta Amma kana ganin yanayinta kasan tana cikin wani hali, sallama yayi mata tace sannu da xuwa, yace yawwa my wiffy, zama yayI sun Dan taba hira yana mai kwantar mata da hankali, itako tuni idanuwanta sun cika da hawaye tana tunanin yadda Zata fara wata sabuwar rayuwar, mijin da yake mallakinta ita kadai a yanxu ya zama mijin mata2.
Ganin dare yanayi ne ya kasa tafiya, tace husby ka tashi ka tafi dare yana yi, shiko dama ya kasa fadi ne, tashi yayi yaje inda yaran suke bacci yai musu Addu'a ya fito yaje dakinsa ya dauki wasu daga cikin kayansa da dan abubuwan da zai bukata ya zuba a wata trolley, ya kashe wutar dakin ya janyo kofar shima ajikinsa duk sai yaji wani iri! Duk jikinsa yai sanyi itako dama tana zaune inda ya barta tuni ta fara kuka, shima baisan sanda kwallah ta fara zubar masa ba a Sauri ya karasa inda take yana lallashinta, rungumeta yayi yana lallashi kamar yarinya, yace kiyi hakuri baby Nima ba yadda zanyi ne, am very sorry!
Ki gafartamin halin da na sanya ki ciki, nasan kin yi iya kokarinki wajen kiga kin danne damuwarki Domin ki faranta min, nayi miki Alkawarin ba abinda zai canja daga gareni, kiyi min Addu'a Allah ya bani ikon adalci tsakaninku, matsayinki na nan daram a xuciyata, sai ma karuwa yake sbd kyawaqan halayenki, rufe masa Baki tayi tace ya isa haka tashi ka tafi karka shiga hakkinta, tare suka fito ta rakashi bakin kofa sukai sallama, ya hugging dinta tare da manna Mata kiss, sannan ya tafi sai da ya ya tabbatar fa lafiyar komai na gidan ya kulle ya tafi...,.





Can gidan Amarya kuwa amarya ranta ya gama baci da rashin isowar ango har yanzu, tasan kuma yana can wajen matarsa tsaki tayi tace illar auren mai matar kenan.














Bai je da kowa ba shi kadai ya tafi wurin amaryarsa gudun kar ayi wani abin magana, aikuwa da isarsa gidan ya tarrada sauran 'yanuwanta a gidan wai taya Amarya kwanaπŸ€” yana shigowa suka bishi da guda sa'annan wasu kawayenta 2 suka Hans shi shiga wai sai ya banda kudin sayan baki, hakanan ya fito dash ya basu baima kirga ba, yana shiga ya sameta ta rufe fuska da laffayar da ta sanya, sallama yayi, ta amsa masa, yaita magana tai shiru ita adole fushi take yaje yai zamansa wajen matarsa, yace, ko maganar ma sai na saya amarsu, tace kaida ka tafi can ka manta amaryar taka, yace ayimin afuwa!
Tace anyi tare da bude fuskarta.
Yace bark na watsa ruwa ko na samu saukin gajiya,
Tace gaskiya kam, bayan ya fito ya sanya jallabiya saukai sallah suka ci naman da ya taho dashi, daga bisani ya je rufe gidan. Ba abinda ya shiga tsakaninsu sbd bakin dake gidan, amma bacvinau sukai manne da juna.





Bangaren maryam kuwa bacci gagararta yayij a wannan dare sai faman juyi take sai kusan 3na dare bacci barawo yai awon gaba da ita.








Washe gari da safe ya shirya tsaf zai je kai mufid school, tace baby wai Ina kake shirin zuwa da safennan, yace zan kai mufid school ne, adawo lfy tace, tayi tayi komawarta daki cike da jin haushi, tana shiga kuwa tace aiko bazai yiwu ba, ya bari in yana can ya dinga kaishi amma hakan ba mai yiwuwa bane.




Bayan fitarsa ne yan'uwanta ke tambayar Ina zashi haka ta fada musu inda zashi, zugata suka hau yi wai sai ta yi da gaske wannan matar ta gama dashi in bahaka ba ya za ai yana nan ace lallai sai je ya kai taro makaranta, ita me takeyi uwar da bazata kai shi ba, haka dai sukayi ta zugata, daga nan kuma wasu daga cikinsu suka hau hada breakfast.



Yana isa gidan ya tarradda an gyara gidan tsaf ko Ina fes sai qamshi ke tashi, ko gidan Amaryar ma ba sharar da akayi balle kunna turare, itama maryam din tayi kwalliyarta, daman ita ka'idane da asuba take wankanta tayo alwalarta, bata taba bari ya fita ba tare da kwalliyarta ba, mufid yana ganinshi ya tafi aguje ya rungumeshi yana Tambayarshi daddy Ina kaje banganka ba tun jiya yace, ai gani yanzu, dauki bag dinka mu tafi sch.
Hannu ya mikawa maryam suka gaisa yace Ina fatan ba wani matsala, babu tace masa, lakuce mata hanci yace really? Daga masa kai tayi yace ok zan kaishi sch. Anjima zan dawo tace Allah ya kaim

By

Ummu AmmerπŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€





*story&written*


*By*


*ummu Ameer* πŸ’ƒ




*page* 1⃣9⃣






Bayan duk bakin dake gidan sun Tafi, daga Amarya sai angonta, Amarcinsu suke ci hankali kwance, Amma ko kusa maryam tayi mata zarra, inda kuma duk wani abinda suka shirya a kansa yake tasiri a hankali akansa, don ma mutum ne da baya sake da addu'oi, ga addini, kuma tsayayyen namiji ne, amma duk da haka a ynx wani irin so yaji yana Kara yi mata idonshi ya rufe akanta, tunda ta fara girki rufe ido kawai yake yi yana ci, gudun kada ranta ya baci, ga rashin tsafta, sbd mugun son jiki ne da ita, ita dai barta in ta gyara kanta shikenan, hatta da bed room dinsu wata ran haka take yini sai ya mata magana sannan ta gyara, an saba da rashin aikin tun agida, abubuwa yai ta gani kala-kala kawai daurewa yake yi, a daddafe yai sati guda kamar yadda aka saba, amma kullum sai ya je wajensu maryam ya duba lfyrsu da ta yaransa, safe da dare, haka kai mufid sch. Kullum ba fashi, Randa zai bar wajen Amaryar kuwa naga kirsa da kisisina dauke hankalinsa tai tayi da salo na kissa da yaudara wai ita bazata iya Kwana ba tare da shi ba, da kyar ta samu ta sake shi da sharadin sai ya dauko mata kanwarta da kuma junior, haka kuwa akayi sai da yaje ya dauko mata su, bashi ya bar gidan ba, sai kusan karfe 9 na dare.




Itako maryam Ana can Ana ta shirin tarbar miji tun yamma, amma shiru abin ya sosa mata rai, kuma taki kiran wayarsa, bashi ya iso gidan ba sai kusan 10 na dare yara kuwa tuni sunyi bacci har sun gaji da jiran daddynsu, taci kukanta ta koshi, har ta fidda rai zaixo, sai ga horn din shi, dama duk sanda ya dawo sai yayi horn su kuwa yaran suna jin horn din shi zasu tafi a guje suna daddy oyoyo! Wata ran ma har da ita ake zuwa tarbarsa, tana jin horn dinsa tai sauri ta gyara fuskarta da powder ta Kara fesa turare, fitowa tai ta zauna a falon tana jiran shigowarsa, sallama yayi ta amsa tare da yi masa sannu da zuwa, fuskarta ba yabo ba fallasa amma bata wani sakar masa fuska ba, sai Abin hannunsa da ta amsa, yace baby, yau ba kiyi hakuri wani uxuri ne ya rikeni, shiyasa nai dare, shiru tai masa ba amsa, gajiya yai da surutun, ba amsa, yace Ina yarana? tace sunyi bacci, ayyah banso sukai bacci ba naso idonsu biyu mu sha hirarmu, ita kuwa juya kai tayi ta tabe Bakii azuciyarta tace Baka so ganinsu bane, Dakinsa ya wuce ta bishi, ruwan wanka ta zuba masa tare da madarar turaren da ta saba sanya masa a ruwan wankan ta ajiye masa towel, tuburewa yayi wai adole ita zatai masa, itako kememe taki, daga karshe ma fita tayi adakin, hakanan ya shiga Yai abinsa ya fito ya shirya, cikin singlet da boxer, yaje ya sameta tana zuba masa abinci a plate, aiko ya zage ya kwashi gara yaushe rabonshi da cin abinci mai dadi haka, itama tai mamakin irin avincin da ya ci ta zaci ma bazai ci ba ko ya kwashi na Amarya, yana ci suna hira. Yana ta yabon girkin.




Washe gari tun sassafe Rukayyah ke ta kira wai ai ya kamata gari na wayewa ya kira ya ji lfy ta tashi, amma gashi har ynx baizo ba, hakuri ya bata yace zai kai yaro makaranta ne ynx anjima zai xo, azuciyarsa yace wannan yarinyar ta fiye mita wlh.



Bayan yai wanka yai breakfaast, yace Maya zaije gidan Amarya daga nan zai wuce office.

Yana isa gidan ya taradda ba shara agidan balle kunna turare, ita kanta ko wanka ba tai ba sleeping dress ce ajikinta ko breakfast batai wa kanta ba. duk da cewa mutum ne mai tsafta ko tsinke baison ganin adakI, bayan sun gaisa ne, sannan ta hau shirin yin wanka, shiko yana mamkinta, maryam tai mata xarrah ko kadan ma basu hada hanya ba, ko 30min baiyiba yai Mata sallama ya wuce office.




Haka rayuwa taita tafiya Abbas yana kokarin yin adalchi a tsakaninsu, kowacce yana kokarin bata hakkinta, sai dai wani irin shakka da tsoronta yake ji, duk abinda ta gaya masa ya zauna daram. Amma hakan bai hanashi yin adalchi ba, yana kokarin ganin ya sauke nauyin dake kansa.




Bayan wata guda da auren matsaloli sukai ta kunnowa daga wajen Rukayya wai ranar girkinta gidan matarsa yake zuwa yaci abinci inta girka nata baici, haka zata saka shi gaba taita kuka, sannan in ya tafi can ranar girkinta sai ya ga dama yake dawowa, ita inde ya fita ya dade a waje to ba abinda take zargi, sai gidan uwargidansa ya tsaya Wanda a zahiri wasu lokutan uxuri ne yake masa yawa, ita fa ko yaushe cikin korafi take, Wanda baisamun haka wajen maryam bata taba kai masa wani korafi akan Amaryarsa ba, bata dorawa kanta wahala ba, duk da cewa taga salo irin -iri da wasu sabbin dabi'u daga gareshi. Wanda tasan dama hakan zata faru, duk inda miji yai aure to ko Amaryar buxuxuce dole sai Kinga rawar kai wajen mijin saboda anyi sabuwa dole ayi doki, amma in akayi hakuri na Dan lokaci ne, kamar ace mutum yayi sabuwar Riga ne zaki ga kullum cikin son sanya ta yake amma daga baya sai kiga an koma ma tsohuwar sbd ingancinta har tafi sabuwar, so, dole ne sai an daure, an kau da kai, sai ya kasance in yazo sallama wajenta da dare Allah-Allah yake ya koma kar ranta ya baci, kana ganin yanayinsa kasan ba'a hayyacinsa yake yi ba, koda maryam ta fuskanci hakan addu'a ta shiga yi masa akan Allah ya yaye masa halin da yake ciki.





By

Ummu AmeerπŸ’ƒ
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€
*KISHI KO HAUKA*
πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€πŸ™†πŸ»β€β™€






*story&written*


*By*

*ummu Ameer* πŸ’ƒπŸ»




*page* 2⃣0⃣




Akwai watarana ranar girkin Rukayya Abbas yaje sallama da daddare waken maryam, dama duk wacce bata da girki gidanta yake fara sauka in ya tashi daga aiki, a ranar maryam tayi baki, ne kuma daga danbatta suke, yan'uwan Abbas ne, hakane yasa shi daukan lokaci, suna gaisawa da bakin, amma duk da haka hankalinshi duk baya wajen yana ta tunanin abinda zai tarar a wajen Rukayyah, sai wajen 9;30, ya tafi yai musu sallama, amma zuciyarsa cike da zulumin abinda zai Tarar daga wajen Rukayya.



Ita kuwa tana can ta gama kuluwa, har da kiran mommy ta fada mata wai kullum haka yake yi sai ya tafi gidan matarsa yai zamansa inta yi masa magana, yace wai yaransa, aiko uwar ba abinda ya fito a bakinta sai to in ya dawo kar ki sake ki barshi ya shiga gidan ki rufe gidan ki ki kwanciyarki, ni kuma gobe insha Allahu zanxo zan ci masa mutunci, haka dae tai ta kitsa mata tsiya, daga karshe tace koma meya miki ai ke kika siya da kinji maganata da haka bata faru ba.


Yana isowa yai ta knocking taki budewa wai ka koma inda ka fito, shi mamakinta ma yake sbd kwata-kwata bai tsammanin tana da irin wadannan halaye ba, tun lokacin da ta tare a gidansa ya fuskanci duk ba halayen da ya Santa da su bane ta canja ba Rukayyan da ya sani bace kenan boyemin halinta tayi kenan ko kuwa haka take? Ya tambayi kansa, a daaa, har yana tunanin kusan halinsu guda da maryam dinsa na rashin son rigima da biyayya, kawaichi da hankali, kunya, nutsuwa, mutunta na gaba da ita, sai yanzu ya fahimci maryam ce kawai mai wadannan kyawawan halaye, lalle yayi zaben tumun dare.

Yana nan tsaye kusan 30min a wurin har yayi zuciya zai koma, ko tunanin me tayi kuma sai ta bude, wai wallahi kaci Albarcin son da nake maka in ba haka ba.. Kwafa tayi tare da komawa cikin gidan, shi kuwa ko saurararta baiyi ba, amma zuciyarsa fal da shakkarta, har mamakin kansa yake yi.



Shigewarsa yayi daki wanka ya shiga, itako ko bata ko kalli inda yake ba, dama halinta ne indai suka samu sabani to fa a ranar kuntata masa takeyi ta ko Ina, Wanda ko bai saba da wadannan halaye ba daga wajen matarsa ko da bata mata rai yai to hakan baisa ta ki yi masa abinda ya dace, bata tauye shi ki kadan, hakane yasa aduk lokacin da irin haka ta faru shi da Amaryarsa to kwana yake yana shi wa maryam Albarka, tuni ya fara ganin laifin shi ko kuma rashin godiyar Allah da matarsa Mai kokarin kyautata masa ko yaushe amma bai hakura ba sai da ya kawo mai shirin

Please Login or Register in order to submit comment