Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji musa nasan kayi mmkin kiran gaggawar da nai maka sbd jibi ne ranar da ta kama daurin auren Ibrahim da jidda,
kuka danjuma yasaka Alhaji kataima kamin,
dady ya xuba mishi ido cike da tausayawa, ya kalli umman jidda da harara,
sai kiyiwa mutane bayanin abinda kikayi,
sunkuyar da kanta k'asa tayi hawaye na xuba kunya sosai takamata tarasa ta ina xatai bayanin wannan abin kunyar,
ya daka mata tsawa a firgice ta d'ago kai jikinta na karkarwa wani b'akin ciki mai xafi ya tokare mata kirji,
sam takasa bud'ar baki tayi mgn,
cikin kuka hjy Aisha yayarta ta fara mgn xuciyarta akarye, kayi hkr yaya bashir kuskure ne da kuma kad'dara, shekaranjiya ne mukaje wajan wani malami akan ana so jidda ta mallake Ibrahim, tayi jim cike da danasani muryarta k'asa k'asa had'e da kuka ta cigaba,
shine yai aiki mai karfi ya bamu yace ta xuba masa a abinci ko a lemo in dai yasha to sai yadda tayi dashi dan ko uwarshi tace kada ya kara gaisheta baxai k'ara ba xata maidashi kamar d'anta sai abinda tace,
salati Alhaji musa yayi ya cire hula yana girgixa kai gumi yaji ta ko ina,
momy ma salatin tayi hawayen farin ciki ya sauko mata na Allah ya mayar musu da mummunan k'udirinsu,
jannat ma hamdala tayi ta godewa Allah xuciyarta cike da tsoron Allah, hajja kuka tasaka tana yiwa yarta mugun kallo,
hadiza ina bak'in cikin mugun halinki yanxu ko makiyinki xaki masa haka ? balle Ibrahim daya ke d'anki ? innalillahi wa inna ilaihi raji'unn kin cuceni hadiza kin gama da rayuwarki,ya khaleel daya ke kusa da ita ya riko mata hannu plx hajja yi hkr ki yi shiru, ta rik'e hannunshi sosai sannu khaleel kayi hkr kaji nasan kana da tausayi da imani da taimako shiyasa Allah yake tare da kai, d'aga mata kai yayi, ki daina kuka hajja,
tabe baki dady yayi yana yiwa hjy hadixa mugun kallo cike da tsanarta,
kinga yadda Allah ya nuna ikonsa ko ? Allah baya barin xalunci, Ibrahim d'ankine hadiza idan kin maidani d'an'uwanki kaf d'inku kun tsani firdausi mahaifiyar shi wai ta shanyeni, yar bin bokaye ce da malamai yanxu tsakaninku waye mai bin bokan ? tunda yaran nan suke xaune cikin gidan nan kuke xaginsu kuna aibatasu kuna ce musu yan asiri sbd kawai sun rab'eni,
sam bakwason kowa ya rab'u da jikina,
wannan shine babbar sakayya daga ubangiji yanxu sai ku gane abu d'aya duk wanda yake xaune dakai da kyakkyawar xuciya ubangiji baxai baka sa'ar ka cutar dashi ba,
Alhaji musa ya kalli dady,
Dr bashir yau yaxama dole na fadi abinda ke raina akan hadixa da y'ata hauwa'u ka gansu nan babu wanda na isa dashi hauwa'u ita kadaice mace tilo da Allah ya bani amma sai na shafe wata ko shekara ban sata a idona ba danayi mgn uwarta tace min tana gidanka bawai zan hanata xuwa gidanka ba amma amatsayina na ubanta yadace ace duk inda xataje a fad'amin, amma sbd ammai dani buje dantofi ya jinjina kai ban isa ba sai dai na xuba musu ido, hadixa ta rabani da yan'uwana tace duk mak'iya nane
Dr bashir na fad'a maka hakane dan kagane wannan kad'an daga cikin mugun hali irin na hadiza ta xamemin masifa bala'i a ratuwata narasa yadda xanyi da ita,

innalillahi wa inna ilaihi raji'un lokaci daya dady da hajja sukayi hajja ta k'ara rushewa da kuka , da kyar khaleel ya rarrasheta tayi shiru,
sai a yanxu dady ya tabbatar da hadiza ba k'aramar makira bace gdy yaiwa Allah daya tsare d'ansa daga makircinsu,
cike da jimami dady ya cigaba da mgn,
aikin gama ya gama khaleel Allah ya tsareshi daga wahala baici abincin ba cikin tsautsayi ya bawa danjuma ya nuna danjuman daya ke arab'e yaci abincin sai akayi dacen shima sunanshi Ibrahim,
dalilin haka ya shiga wani mayuwancin hali na kaunar jidda har yana ikirarin muddin aka hanashi xai iya kashe kanshi ya kasheta,
xaro ido hajja tayi hade da murmushin yake tace alhamdulillah Allah nagode maka,
Alhaji musa shima murmushin takaici yayi ya kalli danjuma, kwantar da hnklinka d'ana na baka auren ta kuma yau yau dinnan xa a d'aura maka aure da ita, wani ihu jidda ta kurma hajja ta kai mata rankwashi,rufewa mutane vaki makira ba uban da ya isa ya hana wannan d'aurin auren haka ba wanda ya isa yace baxa d'aurashi ayau ba, ngd maka musa nagd mk musa, haka akewa mutane masu mummunan xuciya ta fashe da kuka, wllh ban wa hadiza wannan tarbiyyar ba cen y'an bariki suka b'atamin ita Allah ya shiryar min dake, kuka hadizan take sosai dana sani na xiyartar ta ta ko'ina,
Alhaji musa ya kalli danjuma fuskarshi na nuna tausayinsa,
kana da sadaki a hannunka ?
asanyaye danjuma ya shafo aljihunsa dan bashi da kudi sai wasu yan canji, da sauri ya khaleel yace xan biya mishi sadakin,
dan shi ya fi kowa farin cikin wannan hadin waskewa kawai yake yana nuna ya damu amma xuciyarsa cike take da farinciki,
danjuma
ya kalle shi ngd oga khaleel
Alhaji musa yace ka katuro wakilinka
kana da mata ?
kanshi a k'asa yace mahaifina ya rasu sai mahaifiyata datake xaune da matata acan garinmu gexawa,
nan garin bani da kowa idan kuma xa'a jira wakilan nawa zan kirasu awaya, dady yace in dai wakiline zan zame maka Allah ya baku xaman lfy,
nagode dady,
kada kadamu danjuma kaima kazama namu tunda xaka auri yarmu,
Alhaji musa yace kana da inda xaka ajjiyeta ?
girgixa kai yayi jikinshi asanyaye sai dai gidanmu na gado na cen gexawa d'aki biyu ne anan matata da mahaifiyata suke xaune,
Alhaji musa yace nabaka gidane da yake rijiyar xaki nan kano ku xauna aciki,
idon danjuma fal hawaye yake gdy,
dady yace zan canxa maka aiki kadawo companynmu Allah ya baku xaman lfy,
fashewa yayi da kuka lokaci daya Allah ya axurtashi ta dalilin wannan auren yai gdy sosai, hajja tace saura waccen ja'irar ta nuna zahra, dady ya gallawa xahran harara itama cikin satin nan zan aurar da ita ga duk wanda na ga dama sbd itama na fuskanci wani irin hali gareta, da sauri hajja tace bakin hali kai,
kai dai baka dashi uwarta ma bata dashi xama da wannan ta nuna hadixa yasa tana k'ok'arin komawa ita sak Allah ya shirye ku addu'ar da xan muku kenan, zahra ta fashe da kuka hajja tabige mata baki yi mana shiru munafuka,
Alhaji musa ya kalli agogon hannunsa inshaa Allah yau ana idar da sallar axahar za'a daura auren ya mik'e tsaye dady yayi addu'a suka tashi ya khaleel ya mik'e shima had'e da kiran danjuman yabi bayansa dakinsa yaje kayan shi da dady ya dinko masa sbd bikin shi da jidda set 30 ya d'auko ya had'a masa da hula da takalma harda agogonsa wannan dady ya siyo masa ya bashi, danjuma gashi nan aje ayi hidimar biki dasu, gdy sosai danjuman yakeyi, shikam ya khaleel farin ciki fal ranshi shiyasa ya had'a kayan da aka siyo masa dan d'aurin auren ya bada su dan ko kallonsu bai son yi tunda Allah ya rabashi da alak'a k'ai



ana idar da sallar axahar aka d'aura auren danjuma sani gexawa da amaryarshi hauwa'u musa kan sadaki nera dubu d'ari biyar wanda ya khaleel ya biya sbd farin cikin daya keji ko miliyan nawa ne xai iya biya Allah ya rabashi da jidda bai tab'a jin soyayarta aransa ba yana kulatane kawai sbd yar'uwarsa ce, wani vangare na xuciyarshi yana wa Allah gdy akan tsareshi da yayi da makircinsu yau jinta yake kamar sallah



tunda saka bar falon hajja take ta musu fad'a da nasiha,
hajiya amina da hjy Aisha da umman jiddan lokaci d'aya suka fita hayyacinsu dan sun bala'in kad'uwa da abinda ya faru lokaci d'aya Allah ya nuna musu ishara hajja tana xubar da hawaye tace,
kun bani mmki dukanku, kun xubar min dak'imata ngd wa da ubangiji da yasa mahaifinku bai ga wannan masifar ba duk irin soyayyar daya nuna muku da yanda ya koya muku kaunar juna, ace har daya daga cikin xai yi yunkurin cutar dan daya innalillahi
da kyar momy ta lallasheta tayi shiru, ta kamata tai bangaren ta da ita sbd rashin lfyr ta ba'a son ranta ya dink'a b'aci,

hjy amina ta kallesu nikam wannan abin yasa ni dana sanin da bantab'a jinshi ba hawaye ya sauko mata sbd haka hajja take xubar mana da hawaye nayi nadama, haka suka dinka tattaunawa a tsakaninsu kowacce tana dana sani k'arara



daki jannat ta shiga ta xaune gefen gadon ta tagumi tayi tana tuna abin kamar mafarki ko shirin film lallai Allah shine mai kare bayansa abincin da ta fita tabar shi adakin ya khaleel ashe bashi da maraba da tarwa tsa farin cikin raywarta ? tasaki ajiyar xuciya sulthana ta shigo jikinta asanyaye tana xama hindu ta biyo ta, sulthana tace wai naga drimer mai ban mmk,abinda ya bani mmk ba wannan ne karo na farko ba lokacin data fara barbaden ni naganta na sauya abincin, sbd bata daddara ba sai da ta kara ni wllh banso asirin ya tsaya akan danjuma ba naso ace wani tutturna baki mai katon ciki da katon baki da mummunan fuska ta samu danjuma dayake bafillace me kyau da yaji wanka murjewa xaiyi, hindu tace, kina da matsala sulthana wananna fa ishara ce kiyi addu'a kawai daga Allah yake ba awajan dan'adam ba, murguda baki sulthana tayi
eh kaikayine ya koma kan mashekiya,
knocking door sukaji a hnkl aka bude kofar suka kalleta jikinta asnyaye ta karaso kusa da su fuskar ta tasha kuka, cikin rawar murya tace anty jannat plx ki ya femin nayi danasani sosai yanxu na tabbatar da dan'uwa suna ya tara wani dan 'uwan naka bashi da abin nema sai jin ka wulakanta wani baren sai ya kaunace ka kaunar da dan'uwanka bai nuna maka ita ba, ki dubi halin da umma taso saka ya khaleel wai ahaka kanwar dadynmu ne, ta fashe da kuka yanxu na gane ku yan'uwane na yadda ku yafemin plx,
ayatsine sulthana tace munji anyafe atashi a k'ara gaba saura ke dan kema sai kinga naki isharan wanda ya tuba dan wuya ba lada, hindu tace, me ye haka sulthana ? ba inda xata dan duk duniya in banda ku bani da wata bayan su, jannat tace bakomai zahra Allah ya yafe mana gaba d'aya, kasa tashi tayi dan kunya ce ta kamata yara kanana sun fita hnkl tasan ko kad'an su jannat ba sa'anninta bane da kyar ta mike jikinta ba kwari ta fice xuciyrta cike da xullumin itama wa xa'a daura mata aure dashi ?



momy tana komawa d'aki ta saki ajiyar xuciya tai hmdl tun farkon soyayyar jidda da khaleel ba so take ba sbd halin uwarta cikin ikon Allah sai gashi Allah ya raba, ta d'ago hannu sama tanawa ubangiji gdy kan tsare mata danta da yayi wayarta ta dauko ta kira kanwarta hjy safiyya ta bata lbrn komai sun dad'e suna hira suna jajanta lamarin sannan sukayi sallama ta tashi ta dauro alwala tai sallar la'asar



da daddare gidan tsit kowa ka gani da abinda ke damunshi
jannat tana zaune gefen gado sulthana tana kusa da ita hindu na xaune kan stool suna hira,
sallama tayi suka amsa mata da mmk suke kallonta, gaba d'ayanta asanyaye take idanuwanta sun kumbura sbd kuka fuskarta tayi jaa ta xauna kusa da jannat ta kalleta tayi wani mugun murmushi kana kallonsa kasan na bak'in ciki da takaicine,
jannat kinga yanda Allah yayi dani ko ?
girgixa mata kai jannat tayi,

kada kice hk jannat wannan abin daya sameni ishara ce babba, dan wannan ya xame min babban darasi wasu guntun hawaye suka sauko mata, ta kare mata kallo, ina mmkin yarinya karama dake amma kin san rayuwa tunda dad'ewa nasan ya khaleel yana sonki,
xaro ido jannat tayi,
plx ina son ki bani shawara dan ni yanxu daga jiya xuwa yau na dauki wani babban darasi arayuwata,
rik'o hannunta jannat tayi, ki daina kuka anty jidda komai kika gani daga ubangiji yake gaba d'aya rayuwar nan a tsare take gun Allah ki godewa Allah kina da iyaye suna gabanki kina kallonsu kina da rabin jin dadin duniya, jidda ta share hawayenta, hakane anty jannat ina son kibani shawarar yanda ya khaleel yake sonki duk da na san rik'akk'en ra'ayi irin nasa,
jim jannat tayi tana tunani a sanyaye tace anty jidda kema kin san shi sai dai mutuna sar da juna dan duk wata mace tasan da wannan,
*biyayya*
itace ke saurin jefa kauna axuciyar mutun idan har xakiyi biyayya ga wanda yake sama dake to tabbas xai k'aunace ki k'auna bata wasa ba,
rashin biyayya shi ke kawo kiyayya da tsana axuciyar mutun
meyasa xakiga wasu matan suna kula da kansu da tsabtace jikinsu da shan magani dan gyara da iya abinci duk wani abu na jan hnkl ta iya tana ganin ita ta cika mace lokaci d'aya mijinta ya kuntata mata yai mata abinda inkikaji sai kinyi mmk, idan kika binciketa sai kinga ne bata masa biyayya amma fa tana kyautata masa
akwai banbanci sosai, duk yadda kike kyautata wa mijinki muddin bakya masa biyayya tofa kyautatawar nan abanxa take,
misali ko baki da miji kina da kanne acikin k'annanki duk wanda yafi miki biyayya kinfi sonshi kinfi son ki kyautata masa haka ma ayayanki wanda yake miki biyayya kinfi kaunar sa haka dangantaka take arayuwa mata plx adage da yi miji biyayya kada ki manta Allah da kansa yace da ace xa ayiwa wani sujjada bayan ni dana umarci mata taiwa mijinta,


By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



79&80

Asanyaye Jidda ta kalli jannat ngd anty jannat nagane rayuwar ma gaba dayanta tana tafiya ne akan biyayya, da babu ita baxa a xauna lafiya ba, ta mik'e hawaye Na xuba, inshaa Allah xanyi aiki da ita, ta kalli su sulthana ngd k'annena ta fice daga d'akin,
Sulthana ta kawo wani gwauron numfashi,
Oh ! Duniya kenan lokaci d'aya Jidda ta koma abin tausayi, tabani tausayi sosai,
Hindu tace, shiyasa idan xaka gina ramin mugunta ka gina shi daidai kai, mace mai ixxa da ji da kai irin Jidda itace take xubda hawaye a gabanmu,
Jannat tace, hmmn ikon Allah kenan abinda kk tunanin baxaiyiyu ba cikin kudirar Allah sai kaga ya faru, damb'ashe shiyar mace irin Jidda ace ta auri danjuma,
Ta jinjina kai ni kaina Na dauki babban darasi abinda ke baka tausayi wataran xai baka tsoro, Allah ya karemu daga sharrin shaid'an, wayarta tayi k'ara tana dubawa taga ya khaleel tana d'agawa yace ta kawo masa abinci wunya yakeji, ta mik'e sulthana ta kwashe da dariya ai maxa kai idan ba haka ba kuma ayi biyu,
Hararar ta jannat tayi ta fita, tana sauka kasa suka ci karo da mahboob daya shigo
"Anty jannat nemanki nakeyi ya fada yana dariya,
taxaro ido mahboob Allah yasa lfy,
" haisam ne ya aikoni wajanki, ta ware ido haisam ?
gyada kai yayi kamar xai tun tsire da dariya,
Akan sulthana wai ki bata hkr yanxu ta daina kulashi,
Lokaci daya sukayi dariya dukansu,
" ni Na isa yaxo da kanshi ya lallasheta,
Xama mahboob yayi akan kujera, abinfa ya dameshi sosai, ki taimaka ina son nai mata mgn Ina tsoran karta taramin jama'a,
Dariya suka kumayi,

"Shikenan xan mata,
"Yauwa anty jannat, ta wuce tana murmushi
Kitchen ta shiga ta had'a masa coffee ta d'ebi abincin ta nufi b'angaren sa sallama tayi ya amsa ta shiga, yana xaune akan kafet yana kallon news,
Ta sunkuya ta ajjiye abincin tacire hijab dinta ta gaishe shi ya amsa yana kallonta,
Ta xuba masa coffee ya amsa yana shaa, ta koma gefen shi ta yi shiru tana tunanin abinda ya faru,
Ya gama sha ta xuba masa abinci yana ci yana kallonta, ya fahimci jikinta asanyaye yake, ya janyota jikinshi, tayi lamo,
"Beautyna me ya sameki ??
Muryarta a sanyaye tace masa ba komai,
Dariya yayi,
"Kina tunanin ankusa rabani dake ko ?
Da sauri ta xamo kanta ta kalleshi,
Daga mata gira yayi,
Ta koma kirjinshi hade da sakin ajiyar xuciya,
Har sai da yaji,
Dad'i yakamashi ya k'ank'ameta ajikinshi, yana jin kamar ana k'ara mishi soyayyarta,
a hnkl ya sa bakinshi daidai kunnanta,
" Allah yana tare damu babu Wanda ya isa raba wannan soyayyar ki kwantar da hnklinki,
Yana rad'a mata mgn yana shak'ar k'amshin turarenta daya keso,
Lumshe ido tayi tana addu'ar Allah ya kuma tsare mata ya khaleel dinta, ya xame dankwalinta yana shafar gashin kanta,
Ta xame jikinta daga nashi ta mik'e tana k'ok'arin saka hijab,
Mik'ewa shima yayi yana kallonta da manyan idanuwansa masu kama dana mai jin bacci,
"Ina xaki tafi ? Ya fada Kamar Wanda vaison ta matsa daga kusa dashi,
Kanta ta sunkuyar katsa,
" zan koma d'aki,
Kusa da ita ya matso sosai,
"Meyasa kike son rabani da ke ?
Da sauri ta kalleshi idonta cikin nashi,
" a'ah ya khaleel,
"Sheet! Ya fada hade dasa Dan yatsanshi kan lip dinta,
Bana son ki dinka gujemin nafison Na dinka Jinki a jikina kin kasa fahimtar irin son dana ke miki ni nagaji da wannan rab'e rab'en cikin week din nan xa ayi biki mu koma gidanmu Na damu da yawa,
Ta shagwab'e fuska tana kallanshi
" nifaa..... Ya katse ta,
"Kefa me ?
Ta rausayar da kanta,
"Nifa ba gudunka nake ba, ya kalli karamin lip dinta daya ke matukar so
Janyota yayi jikinsa,
Muryarshi asanyaye yace,
" idan bakya guduna yau anan xaki kwana,
Arikice ta xame jikinta
" ya khaleel ....... Bakinta taji cikin nashi kyam ta tsya har sai da ya gaji ya tsaya Dan kanshi hade da kura mata idanu muryarshi asanyaye yace I extremely love u jannahh ! Hannunshi cikin nata, kunya ta kamata ta sunkuyar da kai ya kalli dogon wuyanta xuwa kirji ya cije lebe,
Yasa hannu ya shafo cikinta daya ke ashafe kamar ba'a xuba abinci,
Dai dai kunnanta ya rad'a mata nakusa ajiya anan ya fad'a da murmushi,
Murmushi itama tayi tasa hannu ta rufe fuskarta ya sa hannu ya tallabe fuskarta hade da xame hannunta suka kalli juna tai dariya a kunyace ta fad'a kirjinshi, lokaci daya sukai ajiyar xuciya dukansu da kanshi ya dagota daga kirjinsa ya dauki hijab dinta ya sa kamata,
Ta juya dai dai bakin kofar shi ta tsaya tana masa wani shu'umin kallo, da mmk yake kallonta ta bude Dan k'aramin lip dinta
" I extremely love u ya khaleel da sauri ta fice,
Zo ! Zo ! Jannah,
Ina ta fice tana dariya,
K'ofar ya tsurawa ido yana jin kamar ya bita ya had'iyeta,



Washegari suna dining dukansu break fast sukeyi kana kallonsu kasan har yanxu basu gama wartsakewa daga abinda ya faru ba wayar dady tayi k'ara yana dubawa yga bak'uwar number
Ya d'aga sallama akayi ya amsa yana naxarin me muryar,
Murmushi dady yayi cike da murna yace,
Mashaa Allah ngd sosai inshaa Allah anjima kad'an Ina nan tafe a gagguce ya gama breakfast d'in yana jin dad'i sosai ya kira khaleel su xo su tafi tare ya shiga mota khaleel ya shiga wajan driver suka fice daga gidan


Ya kalli dady ,
" dady ina xamu?
Da fara'a dady yace gidan sarki xamu ya dawo jiya,
Shima khaleel din murmushi yayi hade da jin dadi da gudu yake Jan motar Dan ya matsu suje wa sarki da buk'atarsu,
Basu b'ata lokaci ba suka isa abban A.K Garkuwa ne yai musu jagora falon sarki daya ke ganawar sirri da mutane,
Cikin girmamawa suka gaishe da shi ya amsa cike da kulawa,
A hnkl sarki yace,
"Dr bashir anbani sakon kana son ganawar sirri dani ina fatan dai lafiya ?
Sunkuyar da kansa dady yayi cike da biyayya,
" hakane ranka shi dad'e naxo ne kan wait muhimmiyar mgn akan Alhaji Adam ched'e,
Sarki yace
" toh ched'e lafiya dai ko bashir ?
" lafiya lau ranka ya dad'e akwai yaran da suke gidana y'anmatane guda uku muna binciken iyayensu sai aka tabbatar mana da y'ay'an shi Alhaji Adam ched'e be
Da sauri sarki da abban A.K Garkuwa suka kalli dady
Sarki cike da jindad'i yace
" Alhamdulillahi ai bama sai anbincika ba tabbas y'ay'ansane Dr bashir yau shekara goma sha tara muna binciken inda yaran nan suke,
Wannan tafiyar tawa umara bayan naiwa katsata addu'a da jahata sai da na rok'i Allah akan ya bayyana mana su, gashi kuma Allah ya karb'i addu'armu Alhamdulillah , Allah mungode maka,
Dady daya khaleel suma hamdala sukayi duk da b'acin ran da dady yake ciki sai dayaji ya kau farin ciki sosai yakeyi,
Sarki yace
" Dr ya akayi ka tsincesu haka ahad'e bayan ararrabe aka sacesu ?
Nan dady ya kwashe lbr ya fad'a musu,
Sunyi mmk sosai,
Sarki yace aje ataho dasu ya gansu nan da nan aka tura fadawa da driver

a tsorace suka taho tunaninsu ko ba'a dace ba suna xuwa babban falo inda dady yake da sarki,
Suka gaishe da sarki cikin biyayya,
Murmushi sarki yayi hade da fad'in
Allah Akbar tsarki ya tabbata ga Allah duk Wanda ya kalli y'ay'an nan yasan y'ay'an adamu ched'ene,
Dr ngd maka zan kira ched'en yau yau din nan akan yaxo da gaggawa ina nemanshi gobe ko jibi Dan baxa a baiyana su ba sbd mugayen mutane,
Hamdala dady yayi
" bakomai ranka ya dad'e Allah yakara tsawon rai idan an mana umarni zamu tafi inyaso idan yaxo sai a kiramu,
A hnkl sarki yace
" inshaa Allah Dr katafi da y'ay'anka babu mai rabaka dasu hannu da hannu ka dank'asu gun mahaifinsu Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarka Allah ya tsare maka iyalinka,
Suka amsa da amin sarki yace su tafi jibi su dawo ya kuma gargad'esu da kada kowa yaji zancen suka fito daga gidan sarkin cike da jindadi,


Da murna suka shigo gida a falo suka xauna anata maida bayani dady ya kallesu yaga duk suna cikin farin ciki Wanda bai tab'a ganinsu cikin irinshi ba ya lumshe ido shima yana jin farin ciki Mara misaltuwa cikin farin ciki jannat tace dady,
Suka dago kai duka suka kalleta,
" yau na san yadda farin ciki yake, hawaye ya taro a idonta, na kasa tantance yadda nakeji
ji Na nake kamar sabuwa yau naxo duniya,
Dafa mata kafad'a momy tayi,
Kada ki damu y'ata haka rayuwa take Allah xaki godewa Dan shi yai muku wannan baiwar duk lokacin daka tsinci kanka cikin bakin ciki sai ka gd masa haka inka sami kanka cikin farin ciki ka gd masa sbd shine mai badawa kuma shi yake hanawa,
Ajiyar xuciya Hindu tayi,
Hawaye ya sauko mata,
" hakane momy ni kaina yanxu Na fahmci yadda akejin dadi da farin ciki, Allah shine yai mana wannan baiwar dole mu gd masa,
Cikin farin ciki sulthana tace,
Babu avinda nake jira a yanxu sama dana ga fuskokin su, ko ayanxu alhamdulillah, Allah ya sa na gane ina da dangi da kuma iyaye Alhamdulillah
Murmushin farin ciki dady yayi,
"Masha Allah y'ay'ana Allah yai muku albarka nagode wa Allah daya nuna min wannan ranar ina kara godiya ga Allah ubangiji Allah ya kaimu jibin kamar gobene awajan ubangiji,
Rubayya tace dady, na ji farin ciki mara misaltuwa akan ubangiji ya amshi addu'armu tabbas Allah yana amsar addu'ar bayinsa sai dai kawai jinkiri kuma duk inda yake alkairi ne mukam gashi nan mungani munga yadda Allah yai da jinkirinmu,
Ya haisam ya kalli sulthana yaganta cikin walwala dady ya kamashi hnkl kwance yace,
Dady saura d'aurin auren mu da sulthana,
Dariya sukayi duka falon banda sulthana data b'ata rai,
Dady cikin wasa yace,
Mantawa nayi da an hada jiya anyi Dana Jidda,
Turo baki sulthana tayi, cikin shagwab'a tace,
" nifa dady Na fasa auren ya haisam,
Xaro ido haisam din yayi,
Momy plx kiyi mata mgn ta daina wannan wasan banajin dadi axuciyata,
Momy ta ware ido,
" ba ruwana kun fi kusa na sa baki naji kunya mu dai namu kwasar rawa ne ranar biki,
Kwashewa sukayi da dariya har da dady,
Mahboob yace xanso naga ustaz khaleel yana chasu,
Dariya suka kumayi har tafi ta d'axu shi kanshi khaleel din sai da yayi dariya, ya kalli mahboob yace,
" mai xai hanani yin rawa ranar bikin sulthana da haisam,
Cikin dariya dady yace kamar gaske,
Hindu tace wai ! Sulthana amarya zanso

Please Login or Register in order to submit comment