Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naga rawar kai,
Cikin shagwaba sulthana ta mike tana dire diren k'afa ni fa nafasa aurenshi ta hau sama da gudu gudu,
Cikin wasa momy tace dawo,
Dady ya k'arasa dawo amaryarmu,
Dagudu sulthana tak'arasa hawa sama tana dariya,
Mik'ewa haisam yayi xai bita,
Mahboob ya rik'o hannunsa haba guy bi a hnkl mana,
Fincike hannunsa haisam yay"
ba ruwanka,
Dady yace kyaleshi yaje kada xuciyarshi ta fasa kirjinsa ta fito,
Suka had'a ido da khaleel sukayi dariya a tare, komawa haisam yayi ya xauna kunya ta kamashi ya mik'e yabar falon,
Rabon da suyi farin ciki irin wannan har sun manta sun da d'e suna wasa da dariya da tsokane tsokane har aka kira sallar la'asar suka mik'e dukansu



Tana idar da sallah ta jingina jikin gadonta lumshe ido tayi fuskarta d'auke da murmushi turo k'ofar d'akin yayi,
Ta bud'e ido ta kalleshi da sauri ta mik'e ta k'arasa kusa dashi had'e da fad'awa jikinsa,
K'ankameta yayi yana jin sautin fitar dariyar ta wani farin ciki Na musamman ya xiyarce shi haka yakeson ganin jannat d'inshi cikin walwala da annushuwa, ta dad'e ajikinshi yana shafa bayanta sannan ta xamo suka kurawa junansu ido hancinta yaja,
Beautyna yau rana ce ta musamman,
Far tayi da ido
" hakane ya khaleel
Hannunshi taja ta xaunar da shi gefen gadon ta ta xauna kusa dashi tana kallonsa,
"Ina jina kamar sabuwa nagode wa Allah ta kalleshi kamar xatayi kuka tasa hannunta a kirjinsa ngd mk ya khaleel kai Na musamman ne arayuwata, hawaye ya sauko mata sbd kai ne ummul aba isin canxamin rayuwa daga duhu xuwa haske ngd maka ya khaleel kuka ya kufce mata ka so ni lokacin daya kamata a k'ini ka taimaka min lokacin dana ke neman taimako,
Rungomata jikinshi
Muryarshi asanya ye yace jannah ! Meyasa kikeson b'ata farin cikinki ?
Yau rana ce ta musamman awajan mu, kada ki b'ata farin cikin ki da wannan tunanin babu gdy a tsakaninmu kada ki kuma godemin Allah shine abin gdy, k'ara kankameshi tayi,
" tayaya xuciyata xata rayu batare da taka ba ?
Da sauri ya xamota daga jikinshi
Wow ! Beautyna maimaita abinda kikace ? Kunyace ta kamata ta b'oye fuskarta a kirjinshi,
Yasa hannu yana shafar gadon bayanta,
sulthana ta bud'e k'ofa ta shigo da sauri jannat tai k'ok'arin janye jikinta k'am taji ya rik'eta,
Xaro ido sulthana tayi tana in ina tace,
" ah ah yi hkr ta juya da sauri ta fice,
Dago kai jannat tayi had'e da turo baki,
" kaga fa sulthana ta gammu,
Tab'e baki yayi to menene ?
Kefa matata ce,
K'ara turo baki tayi
Hancinta yaja "gyara bakin kona gyara shi yanxun nan ,
Da sauri ta saki fuska suka kalli juna sukayi dariya ta kaiwa kafad'arshi duka kad'an
Accchh ! Ya fada had'e da dafe wajan da ta kaiwa duka "Sai Na rama
Matsawa tayi had'e da xaro ido,
Ya dawo da ita jikinshi,

Suka d'ai suka San yadda sukeji a xukatansu




Ranar alhamis tunda sassafe suke xaman jiran kiran sarki dukkan su suna had'e waje daya, kowa ka kalla cike yake da annuri, shiru shiru sarki bai kiraba har akayi sallar la'asar gaba d'ayansu jikinsu yai sanyi jannat da sauran y'an'uwanta kamar su fashe da kuka shi kanshi dady jikinshi yayi sanyi ya fara jin ba dad'i yana feeling din wasu abubuwa da shi kad'ai yasansu, sunyi jigun a falo wayar dady tai k'ara gaba d'ayansu suka kalleshi,
Sbd gaggawa ko duba number baiyi ba,
Muryar abban A.K Garkuwa yaji
Dr gamu nan muna jiranka kaxo kaida y'ay'anka,
Kashe wayar dady yayi yana kallonsu Ku tashi mutafi,
Da murna suka mik'e suna Allah Allah suga fuskokin iyayensu mota suka shiga suka d'au hanyar gidan sarki


Basu b'ata lokaci ba suka isa jannat da sulthana da Hindu tuni jikinsu ya hau rawa sunajin wani yanayi Na musamman falon ganawa da manyan bak'i suka shiga sarki suka gani da Abban A.K Garkuwa da shi kanshi Prince A.k,
Cikin biyayya suka gaishe da sarki da murna had'e da walwala sarki ya amsa ya kalli prince " jeka kira min su gaba d'ayansu,
Cikin gaggwa ya mik'e ya fice daga falon
Rawar da jikinsu jannat yakeyi ya k'aru suka k'urawa k'ofar falon ido suna kallon isuwar iyayensu,
Bai jima ba ya dawo tare da mutane su hud'u mata uku manyan mata d'ayar turata ake a keken guragu me shegen kyau kamar Na xinare sai Adam ched'en shine farkon shigowa, lokaci d'aya jannat ta mik'e tsaye tana kallonshi kamarsu daya karaf suka had'a ido jikinshi yai masa wani mugun shock, da sauri ya shigo sulthana da Hindu ma mik'ewa sukayi bai kula dasu ba sbd suna cen gefe jannat ce take xaune facing din kofa,
Cikin matukar raxana Adamu ched'e ya nuna jannat da hannu idonshi yayi jaa
" wannan jini nace jikina ya bani tsokata ce,
Dai dai lokacin da sauran matan suka k'araso suma idonsu kan jannat ya sauka wacce take tura tsohuwar a kid'ime ta k'araso da gudu tana kuka, wannan y'atace ta rungomata jikinta had'e da tsurawa fuskarta ido araxane cikin masifaffan kuka tace AFRAH ! wannan afrah tace


By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



81&82

a kid'ime take sbd rikicewar da tayi,daya matar itama da sauri ta k'araso kusa da jannat cikin wani masifaffen yanayi ta rungumota jikinta had'e da fashewa da kuka mai tsuma rai, Adamu ched'e kasa mgn yayi wani farin ciki ya keji wanda bai tab'a jinshi ciki ba, tsohuwar matar da take xaune kan keken guragu,tana wani irin kuka ta mik'e a duk'e tana taka k'afar da kyar ta k'araso kusa da jannat tana surutu mai cike da ban tausayi,
"ashe kafin na mutu Allah xai nuna min jiko kina ashe ina da rabo ?ashe bak'in cikina ya guje daga yau ? wannan ranar taxama ranar cikar farin cikina innalillahi wa inna ilaihi raji'un, la ilaha illallah, subhanallah Allah shine abin gdy, tana fad'a tana wani irin kuka mai had'e da gunji,
hawayen kafi ciwon xuciya ciwo adamu ched'e yayi hawayen ido daya tal,duka wajan xuba musu ido sukayi,
da sauri ya kalli sauran mutanen cikin falon har idonshi ya kai kan su sulthana da hindu da suke ta uban gunjin kuka, a kid'ime ya xaro ido cikin wani mugun chock da ta ujjibi da sauri ya k'arasa kusa dasu yana kallon su cike da mmk, araxane yace "Aysha fateema ?had'esu yayi ajikinsa yana salati da k'arfi yana hamdala,
"Alhamdulillahi bini'imatihi ta tummusalihun, Allah ngd maka, narasa y'ay'a lokaci d'aya kabani har guda biyu, sannan karaba ni dasu ba tare da sun mutu ba ka kara bani kuma still kara bani da ita batare da ta mutu ba, yanxu kuma ka dawo min dasu lokacin da banyi tsammani ba ka axurtani da baiwar ka Allah kaine abin gdy Alhamdulillah,yana surutun ne sam bai san me yake fad'a ba sbd kid'ima da firgici na ban mmk, da rarrafe d'aya matar tak'ara sa kusa da hindu tana gunjin kuka,
"ashe ba afra kad'ai bace y'ay'a nane suka dawo gareni plx idan mafarki nake kada atashe ni akyaleni nayi ta yinshi ina jin dad'in ganinsu a mafarkin har mutuwa ta taxo ta riskeni kada ku tasheni tana rarrafen tana wannan maganganun masu karya xuciya,
itama tsohuwar da rarrafe ta nufo su jikinta na mugun rawa,
tana fad'in "nabilata ba mafarki bane hawayen da muka shafe shekara sha tara munayi ne yaxo k'arshe k'uncin mu ya k'are ayau b'akin cikinmu ya yanke,
d'aya matar da sauri ta mik'e a daddafe bari na xo na tab'a jikin y'ayana masu albarka yan baiwa babu abinda xamuyi wa Allah sai gdy addu'ar da muka shafe shekaru munayi yau ta amso hasbunallahu wa ni'imal wakeel, alhamdulillah Alhamdulillah,
duk wan da ya kallesu sai ya xubar musu da hawaye dan sanbatu kawai sukeyi suna kuka mai gunji da wani irin sauti na ban tausayi,sam sun manta a inda suke,
dady ta maza yayi yagoge guntun hawayen daya sauko masa, shi khaleel kasa jure ganin kukan jannat yayi ya karasa kusa da ita yana lallashinta, sam bata jin me yake fad'a gaba d'aya hankalinta nakan iyayenta da danginsu,
sarkine yai gyran murya dan shi kansa xuciyar sa ta karye momy kuwa tuni ta biye musu suna kukan tare su rubayya da zahra ma kukan suke cike da tausayi mai narkar da xuciya, mahboob da haisam ma xuciyoyinsu akarye suke
gyaran muryar da sarki yayi shi ya fara dawo da hnklinsu suka fara nutsuwa har suka fahimci inda suke dan sun manta sbd yanayin dasuka tsinci kansu ahnkl cikin karyewar xuciya sarki ya fara mgn dan yaga alamar aka dad'e ana wannan maganganun da koke koke tabbas kowa na gurin sai ya kuka,
" alhamdulillah ! Alhamdulillah ! Allah shine abin gdy dan shiya dawo mana da farin cikinmu da yaranmu garemu shekara goma sha tara ana cikin k'unci da damuwa da b'acin rai da tashin hnkl lokaci d'aya kuma Allah ya dawo mana dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba shin baxa kuyi mamakin ganinsu atare lokaci d'aya ba ? wannan wata baiwa ce ta musamman daga rabbil ixxati daga ubangiji mai rahma mai jin kai, yaran nan an sacesu daban daban amma Allah da ikonsa ya dawo mana dasu a tare a had'e alokacin da xuciya ta cire tsammani alokacin da jikkunan mu suka xama tamkar basa tare damu sai ubangiji mai hikima ya dawo mana da jikinmu da farin cikinmu kai Allahu akhbar ! lallai shine gwani sarki mai hikima akan komai mu kuma gode masa da wannan falala da baiwa da albarka da yai mana,
Allah mun gode maka,
ya yi shiru sannan yaci gaba da bayani " adamu nasan kai da mahaifiyar yaran nan a yanxu kun sami kwanciyar hnkl wanda baku tab'a tsammaninshi lokaci d'aya ba cikin wannan ranar acikin irin wannan yanayin shin tashin ku a yau ko asatin nan kun tab'a tunanin Allah xai nuna muku fuskokin y'ayanku cikin wannan sigar ?
fashewa da kuka hajiya na nabila tayi " kokad'an ranka ya dad'e,
shikam adamu girgixa kai yayi dan ya kasa mgn sai yarfe hannu da yayi,
murmushi sarki yayi,
"Allah kenan aduk lokacin da ubangiji ya hanaka abu ka gode masa dan idan ka gode masa to tabbas gaba kad'an xai maka wata hamshakakkiyar baiwa da bakayi tsammanin ta ba lokacin daka fidda rai, wannan shine babban misali addu'a bata fad'uwa k'asa banxa kai tayinta kada kagaji ubangiji yana jinka kuma ya na amsa akwai wahalar da xai yanke maka ita wacce xata xame mk baiwa da farin ciki nan gaba,
ga bayin Allahn da suka had'a maka y'ay'anka adamu su baka lbrn komai,
a kid'ime suka kallesu dukansu, adamu ched'e ya girgixa kai ya cije lebe sam yarasa wanne irin kalan harafi xaiyi mgn dashi cikin girgixa kan ya fara mgn dan muryar shi ma sai da ta canza
" ban san wacce irin gdy zan mk ba kayi min abinda duk yawan tarin dukiyata batai min ba dole na jinjina maka kaxama mutum mai k'ima da daraja a wajena ka xama mutun na musamman wanda baxan manta tulin tarin alherin da kaimin b duk wanda ya kalli yaran nan yasan sun sami gata kasa k'arasa wa yayi dan muryar shi rawa ta farayi tabbas in ya cigaba da mgn xai iya kecewa da kuka, da sauri abban A.k ya dafa kafad'ar shi yana girgixa kai,
a hnkl adamu ya sauke ajiyar xuciya yana magana jikinsa asanyaye,
" kabeeru ina jina cikin yanayin da bantab'a jinsa ba ashe farin ciki iri iri ne ? yau nake tantance yadda kake jin sa arayuwa, zan iya yin komai dan tabbas ina jin bak'on al'amari na musamman atare dani,
hajiya nabila cikin kuka tace,
" bawan Allah kayi mana gata wanda muka kasa yiwa kanmu duk yawan dukiyar mu da yawan danginmu shekara sha tara kenan ana bincike ba'a gano komai ba amma cikin ikon Allah ka dawo mana dasu lokaci k'alilan, kuma dukansu, da sauri d'aya matar tasa gyalenta tana share mata hawaye tana kuka,
" anty ki daina kukan nan yau fa ba ranar kuka bace a wurinmu rana ce ta musamman na Allah ya kawo mana farin cikinmu Allah ya had'amu da yaranmu,
tsohuwar da suke tare ce tayi wani guntun murmushi ta kalli momy,
"baiwar Allah nasan ke kika xamewa jikokina uwa keda bawan Allahn cen mijinki bamu da bakin da xamu iya biyanku ko gd muku sai dai kawai muce,Allah ya.... ta fashe da kuka Allah ya biyaku,
sarki ne ya gyar murya,
"dr bashir Allah yai maka Albarka Allah ya raya maka xuri'a Allah ya albarkaci rayuwarka da xuri'arka lallai kayi namijin k'ok'ari na jinjina maka ina son ka kwashe labarin rayuwar yaran nan mai ban ta ujjibi kafad'awa iyayensu,
jikin dady asanyaye dan muryarshi ma sai da tayi mugun laushi sbd tausayi suna kukan yana rayawa aransa ace shine a irin yanda suka samu kansu tabbas xai iya yin fiye da abinda sukayi,
ya fara da gdy ga Allah sannan ya kwashe labarin komai ya fad'a musu,
kamar ya xugasu suka kece da sabon kuka na ban mmk,
sarkine yace,
"ku dakata ! ku dakata kukan ya isa haka Allah xa mu gode masa,
" hjy na nabila ta kalli jannat datake gefe guda tayi ta gumi,
"y'ata xo nan xo kirabu da jikina plx kixo na ji guminku duka a cikin jikina,
jannat tana xubar da hawaye ta girgixa kai tana wa uwar wani kallo wanda ya bawa kowa mmk,
" baxan iya xuwa ba naganku tabbas ku iyayena ne amma har yanxu xuciyata bata dai daita da tunanin yadda muka tsinci kanmu ba,
sulthana da sauri ta fincike jikinta ta matsa kusa da momy hade da sakin wani sabon kuka,
"momy kina jinsu wai sune iyayenmu kalli irin kukan da sukeyi dan muji tausayinsu su sam basu ji namu ba shiyasa suka watsar damu a bola momy ki kalli irin rayuwar da anty hindu tayi ita da Jennifer wai muna da iyaye masu sanmu wllh ban yadda ba tayi dariya wacce tafi kuka ciwo ta kalli jannat " anty jannat kinji fa kin yadda ?
irin dariyar da sulthana tayi irinta jannat tayi
" ina fa zan yadda nifa kallonsu kawai nakeyi, cike da mugun mmk suke kallonsu,
hindu itama xare jikinta tayi tana dariyar wacce tafi kuka ciwo,
" baxan iya yadda ba fa sam shekara nawa ina cikin kunci da masifa lokaci d'aya na yadda da ta tsuniya ta yaya sulthana jannat ?
mik'ewa sulthana tayi cike da tsiwa da rashin kunya,
" ko kunya bakuji ba kuke kiranmu y'ay'anku wanne laifi mukai muku kuka kasa xama tare damu ? idan ma sace mu akayi tayaya kukayi sake har hakan ta faru ? kaina fa bai d'auki wannan ba, khaleel ne yace " sulthana meyasa kike haka ne iyayenki nefa,?
xare ido tayi
" iyaye ? su wa din ? iyaye xasu watsar da y'ay'ansu abola ? kasan yadda mukeji kuwa ta girgixa kai tan xubar da hawaye masu k'una kada kace komai dan bakasan xafin rabuwa da iyaye ba,
kwatsa mata tsawa yayi,
" ya sheki iyaye ba abin wasa bane ba kowacce mgn ake musu ba,
itama tsawar tayi,
"plx ya khaleel ! dan kaga ina tsoranka kada ka shiga wannan maganar kabarni dasu kamanta wahalar da Jennifer da hindu suka sha !! ?
kallonta kawai sarki yayi yai mata alama ta xauna,
a tsorace had'e da kid'ima ta xube a wajan tana kuka mai ban tausayi, tsohuwar nan da sauran matan suka sa kuka tsohuwar ta rarrafo ta rungume sulthana yi shiru jikata bamu da laifi a b'atanku sanadiyyar rasaku sandin xamana kan wannan keken shekarata goma sha takwas ina xaune akanshi sbd bak'in cikin rasaku, waccen ita ce mahaifiyarku, tunda kuka bace take rashin lafiya sai yanxu inaga xata warke,
mahaifinku rabonshi da dariya tunda aka rasaku waccen hajiya murja matar babanku ce tafi shekara tana suma ayanxu haka tana da ciwon xuciya sanadiyyar b'atanku munfiku bakin ciki da damuwa kiyi hkr yanxu kuwa xakiji komai abakin hjy murja matar babanku,
a daddafe hjy murja ta iso kusa dasu ta janyosu jikinta inshaa Allah xakuji lbrn ku mai ban ta ujjibi da mmk idan sarki yai min ixni,
gyran murya sarki yayi,
" nayi miki ixini murja
muryar ta asanyaye ta fara


CHED'E FAMILY
wani babban dangine wanda yayi fice afadin kasar nan harda kusan duniya fulani ne su usul, Alhaji yahaya ched'e shine mahaifin adamu yana da tarin dukiya wacce tasa sunanshi yayi fice a duniya yana da mace d'aya hajiya zainab ched'e wacce take y'ar'uwa awajansa sai d'ansu guda d'aya tal da suka haifa shine Adamu ched'e wanda suka dauki son duniya suka dora masa kasncewar shi kadaine hajiya zainab ita da mijinta suka haifa,
sun so suk'ara samun haihuwa amma Allah baiyi ba musamman hajiya tana son y'a mace arayuwar ta dan ko lokacin da tana da cikin Adam addu'a ta dink'ayi Allah ya bata mace cikin ikon Allah kuma ya bata d'a namiji ya taso cikin gata da soyayya taban mmk kasancewar shi kad'aine duk da gatan daya samu hakan baisa ya xama fand'ararre ba sbd iyayensa tsaye suke a kansu da kuma kulawa ta dangi dan atare suke xaune waje d'aya ched'e estate nan cikin g.r.a basa xama ararrabe sbd kansu a had'e yake komai nasu acikin ched'e estate yake, hakan tasa suke kula da junansu da tarbiyyan y'ay'annsu,
adamu mutun ne mai tausayi da taimako da son y'an'uwa uwa uba mai son addini, dalilin dayasa yai fice cikin dan ginsu kowa na sonshi da nan nan dashi a kullum burinsu su kyautata masa Allah yasa ya kai mun xalin aure nan da nan dangi sukayi caa kowa yana so yabashi y'arsa sanadiyyar hakan rikici ya fara k'ulluwa dan kowa gani yake adamu da y'arsa ta dace tun abin ana yinshi a b'oye har takai takawo ana gaba da jin haushin juna hakan tasa mahaifin shi Alhaji yahaya ched'e ya tara yan'uwanshi dukansu yai musu nasiha sannan yace,
"Adamu ba yaro bane yana da hnkl da ilmin da tunanin da xai zab'awa kansa wacce ta dace dashi yanxu fa ba xamanin da xa'a xab'awa yaya abokan rayuwar su bane ku barsu su xab'awa kansu dukkannin mu nan jini d'ayane xuri'a d'ayace har abada muna tare babu mai rabamu kuyi hkr nabawa d'ana damar ya xab'i duk wadda yaga ta dace dashi kuma kuyi hkr ku bari y'ay'anku su xab'i wayanda suka dace dasu,
haka dai yai musu nasiha suka gamsu jikinsu asanyaye suka watse bayan sunyi addu'a

ranar talata adamu yana b'angarenshi akwance mahifinsa ya shigo dakin ya sameshi akwance idonshi a bud'e cike da kulawa yakalleshi,
" Adamu lafiya kake ?
mik'ewa yayi daga kwancen yana murmushi "Baba lafiya nake,
"toh alhamdulillah ka shirya anjima kad'an xaka rakani fada wajan sarki,
" toh baba,
ya fice yana fita yashiga toilet yai wanka ya sa manyan kaya yayi shiga irin ta mahifinshi wacce yake so fararen kaya abinka ga farin mutun kayan sukai masa kyau sosai bayan ya gama ya je babban falon su ya tadda mahaifinshi da mahifiyarshi suna hira, ta d'ago kai ta kalleshi
" oh dannan,
da ke bata kiran sunanshi,
"ina xakaje haka ?
" kodai xakaje wajan y'ata surukuta ne ?
dariya sukayi shida babansa,
" unguwa xai rakani wannan d'annaki inaga matsoracine yakasa fidda mata,
"baba adai tayami da addu'a
murmushi baban yayi,
" Adam addu'a dolece taxama dole ko bamu haifa ba dole miyiwa y'ay'an dangi dana musulmai Allah yai maka albarka Allah yabaka mace ta gari shida hjy suka amsa da, "amin,
hjy tace "nidai in an fita yau adawo min da lbrn surukata, suka fice suna dariya bayan tayi musu addu'ar Allah ya dawo mata dasu lfy


By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



83&84

basu b'ata lokaci ba suka isa gidan sarki falon shi suka isa na tarar bak'i kasancewar akwai babbar sanayya atsakaninsu cikin girmamawa da biyayya suka gaishe shi ya amsa had'e da sakin fuska,
suna cikin gaisawar sarki yai bak'i dan'uwan shi wanda baya k'asar yaxo shida iyalinsa matarsa da y'ay'ansa hud'u biyu maza biyu mata,
bayan sungama tattauna abinda ya kawosu sukai sallama da sarki da bak'insa suka taho kan hanyar su ta dawowa Adam yakasa daurewa har sai da yaiwa babansa maganar,
" baba kasan wannan wanda ya shigo fadan sarki ?
"a'ah adam ya akayi ?
sosa kansa ya farayi yana murmushi,
"naga babbar y'arsa ne naga kamar tana da hnkl,
dariya baban yayi
"d'an nema kafad'i mgnr ka kai tsaye kasan dai ni ba surukin ka bane,
dariya shima adam din yayi
"baba da gaske nakeyi ina ga tazama surukarku idan zan samu,
cikin murna baban yace,
"Alhmdllh haka akeso inshaa Allah gobe zanje na tambayo lallai ashe dai hajiyanka da gaske take tunda tace fitar yau axo mata da lbrn surukarta gashi xa a je mata dashi ubangiji Allah yasa adace,
cikin xuciyarsa ya amsa da "amin


ba'a d'auki wani dogon lokaci ba suka dai dai ta kansu sai dai an samu matsala daga wajan dangin yahaya ched'e fur suka k'i yarda da auren akan baxaiyiyu ya auro musu bare ba duk tulin danginsu ace babu wacce tai masa, suka dink'a k'aramar mgn suna aibata rashin dacewar abin, ran Alhaji yahaya ya b'aci ya tarasu duka yai musu fad'a had'e da nasiha ya kuma ce babu wanda ya isa ya hana auren Allah ne ya had'ashi, ganin yanda ranshi ya b'aci yasa suka amince dan suna gudun b'acin ranshi suka saki komai akayi auren mai ban mmk,
auren Adam ched'e da amaryarsa Nabila Idris sarki,
amarya ta tare nan cikin ched'e estate tasamu soyayya da gata wajan y'an uwan mijinta yanda suke sonshi haka itama suke nan nan da ita,
kwanci tashi asarar mai rai sai da suka kwashe shekara goma da aure batayi ko b'atan wata ba hakan ya dami dangi sosai akayi ta rokon Allah akan Allah ya bashi haihuwa hajiya Nabila da surukarta Hajiya zainab sunfi kowa damuwa dan kullum atafe suke k'asashe daban daban ana duba hajiyan Nabila duk inda sukaje amsa d'aya ce bata da matsala Allah ne dai bai kawo ba kwatsam Allah ya dauk'i ran Alhaji yahaya ched'e sakamakon y'ar rashin lfy ta sati biyu, mutuwar ta gigita kowa dan kaf arewa babu kamarsa haka danginsa kamar suyi me basu da yadda xasuyi ubangiji ya amshi abinsa haka akai zaman makoki xuciyar kowa akarye akayi aka watse akabar iyalanshi da azabar rashi ba kad'an ba,

sanadin mutuwar baban shi yasa komai na kasuwancin mahaifinsa ya dawo kansa shiyake kula da komai
komai yanayin shine batare da jin dad'i ba abubuwa masu yawa sun tunkushe masa ga matsalar danginsa da suka sashi a gaba da sai ya k'ara aure ga mutuwar mahaifinshi sannan ga babban jigo shine rashin samun magaji abun ya had'u yai masa yawa yarame kana kallonsa kasan yana cikin tashin hnkl shi sam bashi da burin k'arin Aure tunda yasan matsalan rashin haihuwan ba daga wajansu bane Allah ne kawai bai basu ba

abin duniya ya ishe hajiya zainab ga rashin mijinta ga matsalar da danginta suke son takurawa danta hakan yasa ta tarasu ta samu su kuka tace sam bata yadda ba. d'anta da matarsa basu suka hana kansu haihuwa ba Allah ne bai basu ba su kyale shi yaji da abu biyu dan uku yai masa yawa, da kyar dai ta shawo kansu dan rigimammune haka dai suka hkr suna matukar jin haushi akan sunk'i yadda da mgnr su


kwanaki suka wuce sati ya shigo ya wuce haka watanni had'e da shekaru sai da suka shafe shekara 20 sannan Adamu ya k'ara aure ya auri SAKATARIYARSA, abinda ya bawa kowa mmk, akayi sa'a bata da fad'a sai d'an karan mutunci da biyayya dan soyayyar da take nunawa hajiya Nabila da surukarta yasa kowa yake sonta ciki kuwa harda shi kanshi Adam dan yana son uwargidansa da mahaifiyarsa suna xaune lafiya xama na biyayya murja tana matuk'ar girmama su, basa kishi ko kad'an kowa yana son kowa idan ma ba amfad'a maka ba baxaka taba tunanin kishiyoyi bane kwatsam baiyi wata da auren ba uwargidansa ta sami ciki, wohoho karkaso kaga farin cikin wajan dangi biyu dangin ched'en da dangin hjy Nabila kowa son cikin yake gata na duniya hjy Nabila tasameshi surukarta hjy Zainab kamar ta had'iyeta hakama kishiyarta hajiya murja da ita akaita renon cikin har ya kai wata tara hajiya Nabila Allah ya sauketa lafiya ta haifi y'an biyu mata, yasalam hajiya zainab kamar ta had'iye yaran abinda takeso Allah ya bata shi kanshi adamu

Please Login or Register in order to submit comment