Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaggawa yai airport dan ya kagu yaxo gida ya tahumi munafukar yarinyar nan azzaluma macuciya barauniya 





10:00pm ya iso 9jaa sai wajan 11 ya isa gida dare yayi haka yaita sintiri da ga bangarensu xuwa cikin gida da kyar bacci ya kwashe shi 



Tunda wuri yadda ta saba ta fito dora musu break fast sbd kwananta 3 ba agidan ba tana wajan jinyar David suwaiba ta tarar a kitchen din suka yiwa juna murmushi suka gaisa suna girkin suna hira kwatsam suka ganshi akansu daga shi sai dan gajeran wando dama al,adar mazan kenan yawo da kana nan kaya kowanne irine da sauri ta kalleshi atsorace take gaishe shi ya kura mata ido yarasa tana ina xai fara tambayarta sbd xuciyrshi da take akufule miko min tee ya fada yana huci da sauri ta bude flask ta xubo masa a cup ta mika masa ya kalli tee din yana jujjuyashi ahannunsa ya watso mata shi cikin zafin nama ta goce duk da haka sai da ya samu gefen kafadarta ta kwalla kara sbd xafin da taji ya nuna ta da yatsa sai dai yakasa cewa komai sai girgiza kai kawai yake yakaiwa iska naushi da hannunsa yai tsaki me karfi ya bar wajan da sauri hade da ajjiye cup din hannunshi nesa da kitchen din su ya xauna yana tunanin hanyar da xai bullo mata abinda yabashi mmk dakiyar daya ga tayi cikin gwaninta da yaudara kamar basu hadu da ita a Dubai ba duk yadda akayi yarinyar nan bakar shedaniya ce bai kamata kai tsaye ya damketa ba kamun kazar kuku ya kamata yai mata xaibar wannan a cikinshi cikin lokaci kalilan zai mata mugun kamu binciken wacece ita xai farayi ya alkawarta sai yago dalilin zamanta cikin gidansu 



Kuka takeyi sosai suwaiba na bata hkr kiyi hkr Jennifer wayeshi ? Cikin kuka take bata amsa dan gidan nan kanin ya mahboob ranar da aka kawoki ya tafi Dubai dama tuntuni baya kaunata suwaiba dan kawai addininmu ba daya ba ta kuma fashewa da kuka kiyi hkr Jennifer kin San kowanne kalan mutun da halinsa nikaina naga kiyayyarki sosai a kwayar idonsa kuma na fuskamci bashi da tausayi ko imani dan me imani baxaiyi abinda yayi ba bakomai suwaiba komai yana da lokaci addua suwaiba tacigaba dayiwa jennifer tana tofawa a inda ta kone inshaa Allah wajan bai tashiba kiyi hkr ki koma daki daki zan karasa girkin kai jennifer ta girgixa kibari mu karasa tunda kin min addua Allah ya saka miki suwaiba na fuskanci kina da adalci da daraja dan Adam in sha Allah xakiyi albarka arayuwarki dan mamana tana fadamin mutane masu kyawawan hali da daraja muatane yanuwansu masu adalci da biyayya ga ubangijinsu suna albarka arayuwarsi kin dace dan wannan halin mamana ta fadamin baiwace Wanda sai mai rabo ubangiji yake bashi murmushi suwaiba tayi hade da kura mata ido cikin xuciyarta tana adduar Allah yasa kina da rabon musulunci Jennifer kalanki da nutsuwarki da kamanninki irin namune Allah mai iko tana mamakin kasancewarta cikin wannan halin Allah y shiryaki Jennifer shirin addinin musulunci bayan sun gama suka jeresu a dining sannan suka koma daki sukayi nasu break fast din suna hira jefi Jefi Jennifer na duba konewar da tayi abinda ya bata mmk kokadan koniyar bata tashi ba ta kalli suwaiba tana murmushi suwaiba kinga ikon Allah tafashash shan ruwan xafine fa amma kinga koniyar bata tashi ba suwaiba ta saki fuska baxata tashiba jennifer na miki adduar annabi Ibrahim alaihis salam lokacin da aka jefashi cikin wuta duk irin wutar da ta tabaki kowacce irice in kikai saurin yinta kika tofa ta tofa yanda bata illata annabi Ibrahim alaihis salam babu abinda xatai miki ko da yarone ya kone shiru Jennifer tayi tana tunanin wani abu Wanda babu Wanda yasan menene ciki kuwa har da ni ummee🤔






1:30pm suka gama lunch suka kai musu dining sannan suka dawo daki suwaiba ta wuce toilet tayo alwala ta tada sallah Jennifer na satar kallonta ta fuskanci suwaiba tana da ilmin addini daidai gwargwado sannan tana aiki dashi dan akwai son yin ibada akan lokaci tanayin komai nata anutsu sabanin sauran yan aikin su Sa a da hadiza da ko shiga harkarta basayi tunda suka San wacece ita novel ta janyo na Hausa tana dubawa na suwaiba ne tagane tana son karance karancen litattafan Hausa in dai sungama ayyukamsu ta idar da sallar ta dauko musu nasu abincin Jennifer ta sakko tasa hannu tana kallon suwaiba tai addua sannan ta fara cin nata bayan sun gama ma sai da tayi abin ya birge Jennifer sallamr hadiza sukaji sannunku yanmata masu hadin kai to kuxo masu gida suna nemanmu a babban falo da murmushi suwaiba ta mayar mata da to yanmata marasa hadin kai muna xuwa dariya Jennifer sukayi ita da hadizan sannan ta bar dakin tana mitar wai suwaiba ta fiya mai da kurji ciwo 





Gaba dayansu ma aikatan gidan suka taro a babban falo dady da Momy ne a ciki kusa da shi ya khaleel ne hnklinshi akan waya yana danne dannenshi Jennifer tarasa me yake dannowa da kullum baya gajiya tun xuwansu wajan babu wacce ya dago kai ya kalla cen gefe zahra ce rike da lpad itama tana game Rubayya hnklinta na kan tv sarkin kallon series films 



Yayana sunnunku da xuwa daddy ya fada da sauri dukansu suka kalleshi cike da mmkin kiransu da yayi da yayanshi ya aiki ? Ya tambayesu cikin hadin baki suka amsa da alhamdulillah babu wata damuwa dai ko ya kuma tmbyr su babu damuwa dady to masha Allah na tarakune sbd jibi dukanmu nida iyalina xamuje umara saudiyya kowacce xata koma gidansu ajibin sai mundawo dan 2 weeks kadai xamuyi ma aikatan mu maza su zasu kula da gidan banda Ku mata yaxaro kudi masu yawa yararraba musu sukayi godiya sosai sannan ya sallamesu kowacce acikinsu murna take banda jennifer da take cikin damuwar rabuwa da yan gidan suna fitowa sukai karo da mahboob ya harareta suwaiba tasaki hannunta tai gaba ita kuma ta tsaya tana kallanshi itama ..kinsan fushi nake dake ?? Ya tambayeta tayi dariya a a Yaya mahboob bansani ba shiyasa na fda miki dan na fuskanci bakisan ina fushin dakeba xo muje garden hira xamuyi ta xaro ido aikinfa ? Baxa kiyi ba ya bata amsa yana kallonta ta kwabe fuska kar nabar suwaiba shiittt ! Ya katse ta hade da Sa yatsansa daya abakinshi muje aikinta ne itama tabi bayanshi bata soba akan dadduma suka xauna cikin grass idon shi akanta Jennifer menene yake damunki kwana 2 dinnan naga kamar kina cikin damuwa ?? Shiru tayi tana tunanin amsar bashi dan tasansa da bin kokwkwafi hakane David ne bashi da lfy yana fama da sicler idan ta tayar masa hnklinmu na tashi duka sbd muna son yaron rashin lfyr nasa yana takura masa Ayya! Ya fada cikin tausaya kuyi hkr kuyi masa addua Allah ya bashi lfy amin ta fada jibi xamu tafi umara naso ace tare muka tafi wani daliline me karfi yasa baxa mu tafi tareba amma next in shaa Allah tare xamu tafi murmushi tayi dan tasan dalilin shine kasancewarta Kristan ne hira sosai yai mata cike da tsari kasancewar Sa dan tsara zance ya dauko wayarsa sukayi photo tare kala kala dakyar ya bar ta tashiga gida yna fadin shi baigaji da hirar ba tana shiga cikin gidan taci karo da ya khaleel a tsaye hannuwansa cikin aljihu ya jefa da kallon da ya saba yimata Wanda takasa fassarashi 





          Saudiyya 


Sun sauka lfy kwanansu 3 da xuwa haisam yana masallaci yna dawafi bayan an idar da sallar axahar ya fito dan yaci abinci yana sauka daga lifta karf idonshi ya sauka akanta tana sanye cikin dogowar riga Arabian gown suna tsaye da wata mata fara irin farin 9ja me kiba babbar mace mgn suke tana dariya ta riko hannun matar ta sumbata sukayi hugging din juna sannan tabar wajan da sauri yana tsaye ya kasa mgn mmk sosai da firgici ya kamashi da sauri yabi bayanta kafin ya cimmata tashige cikin mutane bat tabace masa da sauri ya dawo inda yabar daya matar batanan ya bige kanshi hade da fadin oshcc!! Meyake faruwa ne kasa ya dunkule hannunsa yana dukan tafin hannunshi da shi da gudu gudu ya bi wani wajen karaf yaci karo da wata ta hnkdashi hade da fadin baka da hnkl ? Cikin tsawa da sauri hnklinshi ya dawo kanta ya zaro ido yana mata wani irin kallo tayi tsaki tana masa kaskantaccen kallo mahaukaci ne kai ?? Irinkune sakarkaru da kuke tafiya bakwa kallon gabanku mahaukaci kawai tafada tana cigaba da tafiya ta dago yatsanta tana karkada masa nunin gargadi bai farga sai da takusa ficewa da ga masallacin sannan ya furta jennifer !! Akufule yabi bayanta da sauri 





            By 

          *UMMEEYY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍





            13&14 


Jikinta a sanyaye ta wuce ta fito daga kitchen din tabi hanyar dakinsa ta bude ta shiga da sauri ta sauke idonta kasa daga shi sai gajeron wando jikinshi ba riga kanshi sunkuya yana danne dannen waya ta wuce toilet dinshi ta wanke tana mmkin yadda ta ganshi ko kunya bayaji mgn taji kasa kasa yanayi ta matso kusa da kofar toilet din ta tsaya ............. Jidda ki daina wadannan maganganun akaina kin kasa fahimtata yayi dariya....ki fahimci soyayyata mana oh! Kwantar da hnklinki babu ya macen daxan iya so acikin xuciya ta kina ganin zan iya son wata bayanke ?.......... Fitowa jennifer tayi daga toilet din da sauri ta fara gyra dakin ya cigaba da wayan kamar bai son da halittar mutun a kusa dashi ba .......... Kina bukatar kulawa ta ?? Nima ina bukatar hakan sosai yayi dariya cikin nishadi ....xaki fara ko ?? Ni gsky ya khaleel kaxo kd yafada ashagwabe da alama kwaikwayon muryarta yayi ya kuma yin dariya sosai ...... Yau fa dady yadawo kin San baxaiyiyu nabar dady naxo ba sorry kada kidamu kina son maimaici ?? Kinfi kowa sanin matsayinki kanwata matata ah ! Kinjiki da wata rigima toh zan fada my love my everything ..... Tsayawa cak jennifer tayi takasa karasa aikin ranta yayi masifar baci hawaye na kokarin fito mata ya kalli yanayin da take ciki yai murmushi hade da cije leben kasa yadai Jennifer ???? Ya tmby ta idonshi akanta tayi shiru tarasa me xata ce masa OK xaki iya tafiya ya nuna mata kofa da hannu jikinta asanyaye ta taka kafarta da kyar xata fita hawayen da ya makale ya xubo da gudu kinga "" ya tsayar da ita da sauri ta goge hawayen ta waiwayo wayarsa yake dannawa kina da wata damuwa ne ?? Ya tmbyeta ah ah ta bashi amsa ta fice daga dakin hawaye ya cigaba da xuba daga idonta me yasa yake mata irin wannan tmbyr ?? Koda yaushe tmbyrsa kenan kina da damuwa ?? Idan tana da damuwa xai iya mata maganinsa alhali yana son wata ?? Xata hadiye damuwarta koda kuwa xata xame mata ciwo baxata iya sanar da shi Sirrin xuciyarta ba ita kadai tasan damuwarta tagane inda ya khaleel ya dosa akan me zai dinka tmbyr ta damuwa ??? Gabanta ya fadi ko yana lura da sauyawar da takeyi inya na waya ? Xata yi kokarin controlling din kanta ta kwanta tana ta sake sake xuciyarta kamar madaci 



Washe gari da wuri ta gama aikinta ta koma daki sababbin yan aikin da akayi suka shigo dakinta da fara'a ta tare su suka xauna suna hira suka fada mata sunayensu hadiza da Sa'a kefa meye sunanki ?? Sunana jennifer ! Suka xaro ido suna mmk da ta'ujjibi tasan mmkin sunan suke da kuma ta'ujjibin batai kala da sunan ba tunda ta fada musu sunanta jikinsu yai sanyi sukai shiru da hirar da suke karshe ma suka fita daga dakin nata ta kalli gefen dakin nata tana girgixa kai ita kadai tasan yanayin data ke tsintar kanta inxa ta fadi sunanta Sa'a ce ta shigo kixo Momy na kiranmu a falo ta mike tabi bayan Sa'a a falo ta tadda Momy da hadiza ta gaishe ta cikin fara,a Momy ta amsa kinga yan'uwan naki ko jennifer ?? Eh Momy hakane zan raba muku aiki hadiza ke xaki dinka share share da goge goge kafin sauran da xasu tayaki su karaso ke kuma Sa'a wanke wanke xakiyi da gyaran daki kema akwai mataimaka inaga anjima xasu iso kudinga yi tare jennifer kina bangarenki dai na girki girki kawai xaki dinkayi kema akwai mai tayaki in shaa Allah xuwa anjiman dai xaku gansu sallama akayi ya haisam ne shida ya khaleel da daddy suka shigo falon aladabce suka gaishesu cikin sakin fuska dady ya amsa sai alokacin jennifer ta kalleshi kamarshi daya da ya khaleel ya wuce bangaren hajjo ya khaleel ya bishi ya haisam ya tsaya ranshi a bace Momy ki bawa dady hkr bana son xuwa Dubai din nan mahboob ko khaleel suje me kk so nace haisam ? Bafa dadewa xaka yi ba kwana 3 ne fa kacal mezaka yi ?? dabaka son xuwa babu ruwana , ohhhh Momy !! Ina son gama wani muhimmin abune inda kaje ka dawo sai ka karasa plx Momy kisa baki kutashi kuje jennifer haisam nifa na gama mgn suka mike da sauri musamman Jennifer da tun shigowarshi ta matsu ta bar falon 






      Dubai 


Sanye yake cikin kayan sanyi rungume da jakarsa ya fito daga airport din waya kira Yusuf plx kaxo ina airport ya kashe wayar Sam baya jin dadi ranshi abace yake sbd dolen da akai masa akan tafiyar ba yadda baiyi da dadyn shi akan ya daga tafiyar yaki yadda Yusuf dinne yaxo haisam ya bude motar ya shiga ya kalleshi haisam ? Meya faru ne ? Gobe birthday din meeena oh ! Yusuf ya taka birki kana tare da meena dinne ? Inafa tana 9jaa ya bashi amsa yana Sosa haba to meyasa kabarta Baku taho tare ba tana fushi dani kawai dady ya kwafsa min yaimin dole sai naxo dubai haba ana shiga rayuwar mu fa yusuf yace oh ! Gsky dadyn Ku ya kwafsa maka sorry pepper iyayen namune ba yadda xamuyi dasu me xakayi ne anan din meeting ne ya bashi amsa dai dai lokacin da yai parking suka sauka daga motar gidane babba me Kyau gidansu yusuf kai tsaye suka shiga gidan yai wanka ya kwanta sbd dare yayi ga gajiya da bacin rai 




Washe gari yaje meeting din hk suka gama ya dawo kan gobe xasu kuma yin wani meeting din tare da wasu larabawa da sai goben xasu xo yusuf ya daukeshi xa su koma gida kan hanyar su takomawa suka tsaya dai dai shopping malls yana son yin siyayya tare suka shiga ya tsaya duba perfumes harbi suka sukaji na gun gaba tsawa sukaji everybody nil down gaba dayansu sukai kasa kaba afada ba yasan yan fashine yana kokarin kwanciya karaf idonshi ya sauka akanta tana sanye da riga da wando bakake ta rufe idonta da glass bakake hannunta rike da gun bullet grum wani shock yaji hade matukar mmk da ta'ujjibi da sauri ya mike yana nuna na ta da yatsanshi je.... Je... Jennifer ?? Ta cire bakin glass din tana mishi wani irin kallo cikin in ina ya cigaba da mgn me..me..mekikiye anan? Daya daga cikin yan fashin yanuna shi da gun din hannunsa xai harbeshi don't kill him ! Ta fada tana kallon shi let's go plx guyz ta fada hade da daga murya yana kallon lokacin da suka dauki akwatunan waajan da gwalagwalai suka fice da sauri yana kallonta tana kallonshi itama har motarsu ta bace daga wajan da sauri yusuf ya karaso wajan Sa are u OK haisam !? Idonshi akan window yana kallon titi da mmkin wacce ya gani kana hauka ne yusuf ya fada jikinshi na rawa da sun harbeka fa ?? Shi kam gaba daya hnklinshi baya jikinsa Jennifer !? Sunan yake maimaitawa aransa Jan Sa yusuf yayi dai dai lokacin da police sukaxo ya bude masa kofa shiga mana yusuf ya turashi motar sannan ya xagayo ya shiga ya tada ita da gudu yabar wajan 












By 

           *UMMEEEY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




17&18

Da sauri yabiyo bayanta cikin rashin Sani ya ture wata tsohuwa ta fadi dolenshi ya dakata ya dago tsuhuwar yana bata hkr sbd yanda ta balbaleshi da fada haka ya samu da kyar ya lallashi tsohuwar yai hanyar da Jennifer tabi da gudu dugu cen nesa ya hango wani matashin balarabe sanye cikin uniform ya bude mata murfin mota tashiga hannunta rike da waya tanayi kafin ya karasa motar ta ja da gudu ta bace masa ya sauke numfashi yana. kallon inda motar tabi hnklinshi atashe ranshi yakai kololuwar baci jikinsa asanyaye ya koma masaukinsu yarasa kalar tunanin daxaiyi dan al,amarin yfara bashi tsoro wacece Jennifer babu yadda xa ai ya yadda ba itabace dan tanayin mgn muryarta ta tabbatar masa da itace yasalam ! Meyasa take aiki a gidansu ?? Shi dai yasan Jennifer Kristen ce meya kawota saudiyya masallaci wajan ibada ?? Me ya kaita Dubai aikata mummunan aiki na fashi da makami ?? Anya kuwa xai iya bari yai mata kamun kaxar kuku ???? Ina baxan iya ba !! Yafada cikin huci da daga murya duk ranar da yakoma 9ja tofa sai tafada masa mummunan kudirinta akansu gabanshi ya fadi kodai Yar bincikece ??? To akan me xa a bincikesu alhali dadynsu ba mugun mutun bane mai aikata laifi ?? Wata ke bincika ??? Taya xa ai Yar bincike ta aikata fashi da makami ??? Ohhhh!!! Ya dunkule hannunsa ya naushi tafin hannunsa dashi baxaiyi yuba ! Jennifer wacece ke ?? Meyasa kika shiga rayuwar gidanmu ??? Shifa dama duk da ba kare mata kallo yayiba yasan Sam yarinyar batai kala da yare ba kokadan gaba daya xubinta na Hausa fulanine gumi ya rufeshi duk da sanyin a.c dake sanyaya dakin hk ya dinka sambatu hade Da gudire mummunan abinda xaiwa jennifer sai ta fada mishi wacece ita ?? Me yakota gidansu??





Satinsu biyu cif a saudiyyan suka dawo gida shikam haisam gaba daya hnklinshi nakan yadda xa'ai Jennifer ta cigaba da xama agidan su ranar da suka sauka ma'aikatan gidan mata basu da dawo ba mazan kawai suka tadda



Washe gari da safe ya fito daga daki sanye yake da 3 quarter da riga body Huck fara Sol ya hango inuwar mutun a kitchen da hanxari yayi wajan bayanta ya hango tana aiki sosai duhun mutun ta gani da sauri ta waiwaya atsorace taja baya yanayin da ta ganshi ya tsorata ta ya xuba mata ido yana mata wani irin kallo durkusawa tayi sannu da xuwa Yaya haisam cikin ladabi andawo lafiya ?? Allah ya karbi ibada shiru yai yana naxarinta yarinyar nan kuwa ba shedaniya bace ?? Yanayin yadda tai masa mgn ya matukar basa mmk kamar ba itace ta tsare shi da xagi a masallaci ba kee ! Ya fada akausashe wacece ke ?? Araxane ta kalleshi hade da mikewa tana kallonshi alamar bata fahimci tmbyr tashi ba tmbyr ki nake yi ! girgixa kai tayi ban fahimci tmbyr ta ka bane ta fada kanta akasa OK ! Ok ! Xaki fahimta yana fada ne tmkr zai kai mata duka munafuka ! Azzaluma barauniya ! Nafiki hatsabibanci kafura ! Koda yake shedancinki ya wuce duk me karancin tunani zan miki kyakykyawan rukon da xaki kasa kufcewa sai kinyi Dana sanin yaudarar mutane OK ! Nafahimce ki kinyi hkn dan ki xautani kisani cikin tunani ?? Atunaninki karamar kwakwalwa gareni irin taki ?? Kijira nawa hukuncin dan ubanki bakin kafuri ! Da sauri ta kalleshi ya wuce fuuuuu yana huci ko kadan batayi mmk ba asalima tana jiran fiye da hk xan gani haisam idan kai me babbar kwakwalwane kamar yadda ka fada ina gidanku babu abinda xai fiddani har sai burina ya cika koda kuwa xaka dinka yankan naman jikina




Da wuri tagama aikinta ta koma daki tana shiga tai wanka ta canza kaya kwankwasa kofa akayi kafin tai mgn ya shigo fuskarshi dauke da murmushi yana kallanta oyoyo oyoyo oyoyo ya mahboob ya janyo stool ya xauna oyoyo sister nayi kewarki sosai nima HK ya mahboob ta fada tana satar kallonshi jiya naita xuba ido na nemiki na rasa ta rangwabar da kanta banyi xaton da wuri xaku dawo ba andawo lfy ? Lfy ya fada yana tabe baki sai rashinki kawai danayi tayi murmushi rashina kamar vana duniyar ? No nikaina nayi mmk sosai .....sarkin tsari xaka fara tafada aranta......yacigaba bansan nashaku dake haka over ba sai danayi 3 days ban ganki ba na damu sosai har abin yafara bani tsoro kullum cikin tunanin kyakykyawar fuskarki sai na kalli photonki nake jin dadi Jennifer ya kirata ta kalleshi cike da gundira da zancenshi dan ita sam batason namiji me tsara zance yawancin su makaryata ne ...kin shiga raina sosai ban San yadda akai kawancen mu yai tsamari haka ba ya kura mata ido kina da babban fili acikin xuciyata na yadda dacewa kina daya daga cikin farin cikina ke kam kawace wacce zanyi alfahari da ita murmushi tayi shima murmushin yayi kina da Kyau Jennifer kyawunki shine kyawun dake fuxgar duk wani mahluki kyawunki shine asalin Kyau fatana yadda nayi missing aminiyata itama hk tayi kai ta daga masa tana tunanin inama da ya khaleel take wannan hirar look ! Yace cikin daure fuska banson wayo mgn xaki ba daga kai ba kibani lbrn missing dina da kikayi na isa nai maka wayo Yaya mahboob nayi missing dinka sosai ya mahboob dalilin dayasa ma naxo gidanku yau da asuba dan naga yayana ta rufe fuska da hannunta ya tabe bk ngd ya fada hade da mikewa anjima zan dawo OK Allah ya dawo da kai lfy sukayiwa juna murmushi ya fice ta murguda baki jagwab ta xauna kan stool din daya tashi mganganun ya mahboob suna sata gajiya




12:00 tashiga kitchen kamar yadda tasaba dora girkin rana karar telephone din kitchen taji tasa hannu ta daga muryarshi mai sanyi taji kamar baya sonyin mgn ki kawomin coffee ya ajjiye wayar tasaki ajiyar xuciya hade dayin murmushi da sauri ta gama tai bangaren su dan ta matsu ta ganshi sbd dadewar da sukayi basuga juna ba tana xuwa bakin kofarshi taji murya kasa kasa gabanta ya fadi tabbas wya yakeyi da wannan mayyar ! Sam batasan lokacin data kira ta da suna mayyaba ido ta runtse yaukam baxata saurari wayarsu ba da sauri tai sallama idonsu ya sauka kan juna gabanta ya fadi yana xaune akujera 3 quarter ne ajikin shi kalan fari ba riga kukam Allah ya shiryeku da bakwajin kunyar xama babu ishashshun kaya ajjiywa tayi da sauri sbd mgnr da taji yayi ....babyna I love u too...da sauri tajuya xata fita kinga "! Yace da ita tsam ta tsaya ki wankemin toilet ranta yai mummunan baci ta juya jikinta asanyaye tai hnyr toilet din ......ah no babyna ina mgn da maid house din mune kiyi hkr xnxo fa oh ya rabbi ! Allah ya kawomin ke lfy xanyi farin ciki da hakan ki daina mgn karan kanki dan nima nadamu darashin ki kusa dani ........itakam Jennifer bakin cikine ya taru yai mata yawa hk ta wawwatsa ruwa a toilet din ta fito bai kalleta ba ta wuce yabi bayanta da kallo yana dariya kasa kasa hade da cije lebenshi na kasa tana fita tajanyo kofar da karfi ta wuce fuuuu tashiga kitchen suwaiba ta tadda xare ido sukayi dukansu sannan suka rungume juna suna fairin cikin haduwa




Yau takama alhamis dai dai dasatin su ya haisam 2 da dawowa gidan yau ba kowa sai su ma'aikata da suke abangaren su tana kitchen tna aiki suwaiba sun tafi kasuwa da Momy shara ta kwashe tai hanyar da ake xubar da ita taci karo da shi yana mata wani irin kallo ya haisam wacece ke ? Ta kalleshi takasa ce masa komai cikin tsawa ya kuma tmbyrta wacece ke ? Kafin ta ankara ya

Please Login or Register in order to submit comment