Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a idonta cikin rawar murya tace sbd nayi imanin shine addinin gaskiya sbd adalcinsu da mutuncinsu da taimakokon juna tun ina yarinya karama nayi imani da Allah na kuma yadda addinin musulunci shine addinin gaskiya,

Alhamdulillah, mungodewa Allah yanxu xan baki Kalmar shahada kafin nan zan fada miki rkunnan musulunci da kuma ahikanshi imani, addinin musulunci addinine na amince da salama da taimakon juna da kaunar junanmu, rukunann musulinci ya kasu kashi biyar Wanda dolene sai ka amince dasu xaka shiga addinin Allah

1 shahadatu an LA ilaha illalha wa'anna Muhammadan rasulullah

2 tsaida sallah

3 bada zakka

4 yin axumin watan Ramadan

5 da xiyartar dakin Allah .

A keeda ta muslunci tushenta shine imani da Allah, da mala'ikonsa, da littattafansa, da manxanninsa, da kuma ranar lahira, da yadda da akddara me Kyau ko mummuna

Lallai wannan magana da kika fadamin ta cewa tun kina yarinya kikai imani da cewar addinin Allah shine addinin gaskiya sai kika tunamin da hadisin manxon Allah (s.a.w) daya ke cewa, maa min mauludin illa yuladu alal fidrah, babu wani abin haihuwa face an haifeshi da imani ga Allah, fa abawahu, har sai iyayensa yuhawwidani au yunassiranihi aw yumajjisanihi, sun kasnce yahudawa ko banasare ko majusawa,
Wannan ba abin mmk bane dan dan malaman tauhidi sun kawo wannan, fa inna kulla maklukin kad fudira alal imani bi kalikihi min gairi sabqi tafkeer au ta'alim, Allahu akhbar, haka Allah ya ke halittar kowa da imani dashi batre da wani tunani ko koyarda shi ba, Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah. Ikon Allah ya wuce komai dan shiyake shiryarwa kuma shi yake fidda haske daga cikin duhu, baiwar Allah duk kin amince da hakan ? Cikin gwarin gwiwa tace eh Malan na amince, yai murmushi yace to Alhamdulillah, zan fada miki Kalmar shahada kamar yanda nai miki bayani afarko, duk abinda na fada sai ki maimaita Ash'hadu an la ila ha illallah ta bude baki da murna hade da imani harshen ta ya karye taji wani irin abu ya rufe mata ido da kyar tayi kokarin juya harshenta ta kasa bata San lokacin data mike tana kakari tana son maimaita wa gaba daayansu sukayo kanta luuuu tai kasa kafin ta karasa kasa ya khaleel ya riketa yana jijjigata dif yaga idonta ya rufe numfashinta ya tsaya cak cikin tashin hnkli suke jijjigata





By
*Ummee Garkuwa*
For comments
08037251895
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



47&48

A matukar raxane ya khaleel yake jijjigata da karfi yana kiran sunanta Malan ya mike yana mmkin al'amarin ya kalli idonta yaga yana motsi yayi ajiyar xuciya naya dan yagane inda matsalar take dukkamsu hnklinsu na kanta musamman Momy da ruby, Malan ya kalli ruby yace taje ta debo masa ruwa acikin cuf, da sauri ta tafi, bata dabe ba ta dawo ya amsa ya yayyafa mata bayan yai mata addu'a har yanxu bata bude ido ba, numfashinta ya kawo da karfi idonta arufe yana motsi, Malan yace nayi mmk sosai Ku xauna, Ku kwantar da hnklinku xata tashi babu abinda yafi karfin addu'a xama sukayi xuciyoyinsu cikin dimuwa, har yanxu tana hannun khaleel yakasa sauketa gani yake yana sauketa wani abun xai kara faruwa da ita,
Malan yace, dama tana da wata matsala ne ? Jikin Momy asanyaye tace gaskiya ban Santa da matsala ba lfy lau take, yayi Jim yana juya xancen yace to xata tashi inshaa Allah xuwa kuyi hkr idan ta tashi ta samu nutsuwa xamuji daga bakinta, kuma akwai wasu tambayoyi da xammata in shaa Allah xamuyi wa tubkar hanci, kada Ku damu, ya mike tsaye ya mikowa Ruby sauran ruwan addu'ar yace sukara shafa mata duk yadda ake ciki suyi waya kafin ya tafi sai da ya kuma yi mata addu'a ya khaleel ya dauketa, so Momy suka bi bayanshi ya sauketa a dakinta jigum sukayi hade da xuba mata ido ransu ajagule



Some hours letter

Har dare bata bude ido ba gaba dayansu suna dakinta kowanne ranshi ajagule haisam da mahbobb duk sunyi cirko cirko kowanne da abinda yake sakawa uban gayyar kuwa ya rasa kalar tunanin da xaiyi addua'a yake xabgawa ubangiji Allah ya tashi kafadun jennynsa, Malan Dr Ahmad Sani ningi ya dawo, har dakinta sukaje, cikin mmk yace wannan abu da muni yake nayi mmkin rashin bude idonta, Momy tace wllh Malan babu me kwanciyar hnkl acikinmu, mun rasa wane kalan tunani xamuyi kan mu ya daure tamau kwata kwata jenny bata tabayin irin haka ba, wani irin tari Jennifer ta fara yi da atishawa me karfin gaske idonta a rufe take yinsu, hnklinsu yadada tashi addua malan yai mata sannan ta daina sai kuma hamma, girgixa kai haisam yayi Momy kuyi hkr akwai abinda muke boye muku nida Jennifer amma yanxu dolene kusani jenny plx ki gafarceni yaxama dole su mom su Sani sbd awarware matsalar jikin khaleel ya fara rawa wani kishi mai karfin gaske ya taso masa ya cikumi wuyan haisam cikin fada da tsawa yace me ye atsakanin Ku Wanda kuke boyewa ? Menene ? Araxane Momy ta mike cike da mmkin khaleel din, kana lafiya kuwa khaleel ? Kasa keshi, cikin fada da jin haushi yace mom plx ki kyaleni, tayaya xasu munafunce mu su kintsa wani abun batare da sanin mu? Kasa keshi nace ! Da karfi yasakeshi har sai da haisam yai baya, ran khaleel ajagule gani yake ko soyayya suke shida ita, to me sukeyi ? Wani irin yanayi Mara fisaltuwa yaji shi aciki,
Momy tace muna jinka haisam girgixa kai haisam yayi cike da jin haushin dan'uwansa ya kwashe lbrin komai ya fada musu jinjina kai Malan yayi hade da fadin ikon Allah, kunga inda babbar matsalar take, lallai sihiri mai karfi na bata da kauce hanya hade da babaken jinnu ajikin yarinyar nan dole anemo sauran yan uwanta ayi musu magani gaba dayansu, wani irin shock khaleel yaji hade da danasanin cukumar haisam da yayi yana son jenny shi bakone asoyayya ya kasa controlling kishi mai xafi daya ta so masa, Momy tace amma haisam kunyi yarinta sannan kunyi kuskure, kuyi abu Ku kadai batare da sanin babba ba gobe dadynku xai dawo yanxu xan kirashi a waya na sanar dashi komai, ubangiji Allah ya kawo mana dauki wannan lamari da sarkakiya yake idan kana duniya xakaga abu kaji shi kuma kala kala,
Malan yace mutane ne iri iri marasa tsoran Allah da sai kaunar duniya basa taba tunanin xaman kabarinsu basa tunanin yaumul hisaab duniya kawai sukeso cikakken me imani ne yake tuna Allah adukkan lamarinsa Ku ga ikon Allah kuji wani xalunci, araba yaya har guda uku da mahaifiyarsu da mahaifinsu da danginsu a watsasu a duniya sbd bakin xalunci ba abarsu haka ba sai da aka jefesu da mugun sihiri na kiyayyen junansu ta tambadewa, innalillahi wa inna ilaihi rajiuun, an raba musu kawuna waccen a Dubai an hadata da bakin asirin daxata lalata rayuwarta waccen a saudiyya itama an hda ta sihirin rashin kunya wannan a 9ja an hada ta da kafuri, subhanallah, amma sbd kudura da kuma iko na Allah subhanahu wata'ala sai ya hada kawunan su duk da mugun sihirin da akai musu na har abada baxasu hadu ba, Allah kenan mai yadda yaso, ya girgixa kai fuskarsa cike da tausayin jenny ya kalli fuskarta, Allah kadai yasan halin da iyayensu suke ciki, musammn mahifiyarsu, Yaya uku ris ! Ita wannan yan biyu aka kwana arba'in aka rabasu da nonon mahaifiyarsu, bata gama ficewa daga radadin batansu ba ta kuma haihuwa still aka kuma sace yar, na tausaya musu duka daga su har iyayensu, ya mike xuwa gobe duk yadda ake cike na dawo kafin nan nasan Dr bashir ya dawo Allah ya bata lafiya, ya fice yana jinjina al'amarin suma haka suka tashi jikinsu asanyaye suka fita khaleel yana xaune awajan ya kura mata ido tausayin halin da take ciki da kuma soyayyar ta mai karfin gaske yake ji tana xagaye ilahirin sassan jikinshi da kyar yatashi ya barta hade da tofe ta da addu'a


**********
Karfe uku da rafi na dare yana xaune yakasa runtsawa alwala ya dauro ya fara jera na filfili zumbur ya mike hnklin nakan yaje ya duba ta ya kalli agogo ya girgixa kai ina dare yayi, tun yana iya jurewa har sai da yaji ya kasa ya fito daga dakinsa ya nufi cikin gidan bangaren inda take ya bude kofar dakinta xaune ya sameta tayi tagumi ya xuba mata ido, atsorace ta dago kai ta kalleshi wani irin sonshi taji yana ratsata ta sunkyar da kanta cikin sassanyar muryarshi taji yace ke! Dago kanki ta dago kai tana kallon kwayar idonsa da take fur babu alamun jin bacci atare da ita, akwai abinda yake miki ciwo?, sanin halinshi da tayi na bai son mgn da alama yasa ta budi baki da kyar tace ah ah
Sanyin dadi ya xiyarce shi baisan lokacin daya lumshe idanunsa ba, da sauri ya bude ya danci mur wai shi bai son raini, karta gane yana mugun sonta, kin tabbata? ya jefeta da tambaya, na tabbata ta mayar masa da amsa, asanyaye yace masha Allah, yakamata ki kwanta ki huta dare yayi sosai cikin wani yanayi na musamman tace tohh! Ya matso kusa da ita ya janyo bargon lullubarta ya kalli fuskarta, oya kwanta, ta kwanta ya lullubeta da bargo sannan ya fice ta murgudawa bayanshi kallo sannan ta runtse ido plx ya kahaleel kana son hauka tani da wannan salon naka, da kyar ta samu tai bacci


Tun kafin yakarasa dakinsa yake jin dadyn jennyn Sa ta farka yanayin daya ganta ciki tayi kyau duk da tana cikin damuwa oh ! Jenny ta musamman ce ! Komai nata na musamman ne ina sonki jenny plx kema kina sona ki daina wahalar damu kice kawai kina sona, baxan iya yadda kike so ba Sam ! Aa shiga daki nutsuwa ta musammna yasamu kansa aciki bai San lokacin da yai murmushi yasa hannu ya shfa sajensa a hnkl ya furta, nine mallakin ki ni zan mallake ki nafi kowa dacewa da in xama naki ina sonki jenny yana nan xaune har akai kiran sallar farko yatashi yai raka'atainil fijr sannan ya tafi masallaci



************
Washe gari gidan tsit babu annuahuwa kowa ka kalla a damuwa yake da kuma tausayin rayuwar Jennifer tana kwance adaki wayar ta tai kara bata son numb din ba ta daga muryar sulthana taji, oyoyo Anty jenny munyi missing dinki,
Cikin farin ciki tace nima haka, kuna lfy ? Hmm Anty jenny ba sauki,
Dariya jenny tayi sulthana kinsan me kikace kuwa ?
Tsaki sulthanan tayi cikin fada tace me nace ?
Murmushi Jennifer tayi naji kince Anty shiyasa nayi mmk,
Hello jenny Hindu ce
Oh ! Hindu kin amshi wayar ne ?
Da fada tace ko bakaya bukatar jin muryarta kinji nace nice sai kin wani maimaita taja tsaki,
Daga cen gefe taji sulthana tana cewa dallah Malama bani wayata idan kin matsu ki kirata da taki mana,
Hindu tace baxan kiraba da taki nai niyyar yi fitsararriya nan danan suka fara fada kashe wayar Jennifer tayi hade da tagumi ita da yan'uwanta an maidasu makiyan juna koma waye yai musu wannan xaluncin bai kyauta musu ba, karara motoci taji da sauri ta tashi ta leka dady ya dawo ta fada hade da rike kirji komawa tayi ta xauna mutum adali mai tausayi da karamci

Bayan ya huta yasa aka kira masa Jennifer dan tun jiya yaji lbrin komai yayi mmk hade da ta ujjibi kanta akasa ta sunkuya ta gaishe shi ya tambayeta ko tana jin wani ciwo a jikinta, tace ah ah, suna xaune haisam suka shigo shida su hindu da sulthana dady yace su hau sama kafin malan yaxo kaf gidan sunyi mmkin mugun kamar da sukayi da juna xuciyoyinsu cike da mmkin wannan lamari dakin Jennifer ta kaisu a ya tsine hindu take kallonta, kinji haushi jenny ki tare gidan mutane matsayin Yar aiki, kafin jenny ta bata amsa sulthana tace taxi Wanda yake yawon dabanci, akufule hindu tace, kema wata tarbiyya gareki ? Tarbiyyar da bakya ganin darajar kowa duk tsufan mutun yarone awajanki,
sulthana ta hararesu duka naji tunda ba dabanci da kwacen kayan mutane nake ba sannan ni ba arniya bace,
Kwankwasa kofa akayi khaleel ne ya shigo bai kallesu ba idonshi akan jenny, fuskarshi a daure yacewa jenny,
Kin shafa wannan ruwan addu'ar ? A a ta bashi amsa dauko ki shafa, toh tace masa batare da ta mike ba, nop ki tashi ki shafa yanxu ina kallo sbd yanxu malan zai dawo ta dauko ruwan tashafa a furkarta, yace yayi Kyau sannan ya fice, hindu ta tabe baki shi kuma wannan dan xafin kanfa ?
Sulthana tace sai wani hura hanci yake kamar barren soja amma fa ya hadu, hindu tace kirar jikinshi taimin kana ganinshi kasan yana ji da kansa ina son maxa irinshi cikin jin haushi jenny tace to malamai ya isa haka ! Murguda baki sulthana tayi wllh baxa a hanamu yaban me Kyau ba karar wayar jenny ce ta katse su Momy tace su sakko kasa dukansu suka sauko malan ma yaxo ga dady, malan yace sannunku bain Allah suka amsa da yauwa, Jennifer ya kira sunanta wanne irin mafarki kikayi jiya, a hnkl tace gani na nayi cikin wani katon rami, kina yin irinshi ko jiya kika fara ?
Tunda na mallaki hankalin kaina nake irin wannan mafarkin, da sauri hindu tace, wllh nima haka, irin shi nakeyi,
Sulthana ma tace nima haka irinshi na keyi, kafin ta karasa suka ga jenny ta dungura numfashinta ya dauke idonta arufe amma yana motsi da sauri sukayi kanta hnklinsu atashe daki suka kaita

***********
Malan suka kebe shida dady daya khaleel malan ya jinjina kai Dr bashir ! Yakira sunan dadi, akwai matsala gagaruma makarin sammun jikin yarinyar nan shine ta auri musulmi, gaban dady ya fadi shi kanshi khaleel wani mugun shock yaji girgixa kai malan yayi wani shedanin aljinine ajikin yarinyar nan baxai barta ta karfi shahada ba muddin ta auri musulmi xai kyaleta dan shi baya son aure asalima hana wa yake shiwa ? Dady ya tmby shi aljanin malan ya bashi amsa, dady yace toh malan yarinyar nan ba yata bace shari'ah bata amince da haka ba, a a Dr bashir malan ya katseshi a ina iyayenta suke ? Ba Wanda yasani, sannan lalura ce ta taso muhimmiya da kuma uxiri, xa ajira ne har sai anga iyayenta sannan xa a fiddata daga cikin duhu ?, in dai yarinya ta amince magana tayi sannan su marinka ba musulmai bane amma dole xa a fada musu ajiyar xuciya dady yayi, yana jinjina lamarin khaleel kuwa tuni gumi ya jikeshi sharkaf, malan yace muddin kana da Wanda ka yadda dashi da kuma addiminsa da tarbiyyarsa a daura mata aure dashi, hakane malan ina dasu dan naga tasu taxo daya da mahboob Dana ba matsala na hadata dashi danna San baxata kiba hamdala malan yayi Allah yaska da alkairi Dr bashir kayi jihadi Allah ya biyaka murmushi dady yayi bakomai da na kowa ne shikam khaleel suman xaune yayi wani abu yaji me dafi da xafin gaske ya sokeshi da karfi jin an ambaci mahboob xa a. Bawa jennyn Sa 😭😭😭😭


By
*Ummee Garkuwa*
F[truncated by WhatsApp]
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




49&50

Girjin shi yaji yana xafin gaske tamkar ana babba ka masa wuta numfashinshi da kyar ya ke iya saita shi,
Malan ya cigaba da cewa, Dr bashir na jijina maka irinku mu keso Ku yawaita aduniya masu taimako dan Allah, masu jajircewa akan d'a koba nasu bane Allah ne kawai xai biyaka da mafificin alkairi bakomai malan shi d'a na kowane baxaka ki mutum ba koda yaka sance ba addininku daya ba, sbd bakasan gaba, malan ya mike xan wuce Dr duk yadda ake ciki muyi waya, amma maganar auren nan in son samune kada ya wuce satin nan, murmushi dady yayi cikin gwarin gwiwa bakomai malan ko gobene ashirye muke,
Shima malan murmushin yayi hakane Dr Allah yasanya alkairi, ka tamvy ta bakin yarinyar ko tana da abinda xatace, insha Allah xanyi haka nagd sosai, malan ya tafi yana zabgawa dady addu'a ta samun rahama,
Saukar da numfashi dady yayi ya kalli khaleel,
khaleel ? Yakira sunanshi, khaleel ya kuma maimaitawa a tsorace yata bashi hade da girgixashi khaleel ! Da kyar ya iya bude ido ya kalli dady, cikin raxana dady yace meya sameka ? Kirjina dady yana min xafi ina jin xuciyata kamar xata fito, subhanallah khaleel ! Sbd me ? Yanxu yanxu fa lfyr ka kalau, mikewa khaleel din yayi tamkar xai fadi dady natafi daki zansha mgn da kyar ya iya mgnr,
Dady binshi yayi da ido yana mmkin ciwon nashi yanxu yanxu ace ana tunanin xuciya kamar xata fito ya salam ! Meya sami yaron nan farat daya haka ?? Haka ya cigaba da tunane tunane ko xai danko dalilin cutar babban nasa daya keso tamkr namaa tsoka daya a miya


*************
Kai tsaye dakinshi ya wuce shi kadai yasan yadda ykeji aransa abude ya tadda dakin ya shiga ciki a wahalce ya xauna kan 3 siter dinshi sai da ya xauna sosai sannan ya kula da sagir daye xaune yana kallonshi,
Sagir ! Yakira sunanshi, ya cije lebenshi xan rasa jenny ta,
Xaro ido sagir yayi, cike da mmk yace ban fahimta ba khaleel, da kyar khaleel ya bude baki cikin wani mugun yanayi na bakin ciki da bacin rai,
Dady xai bawa mahboob auren ta,
Subhanallah ! Sagir yace sbd me ? Ya tmby khaleel din daya runtse ido yanajin kansa kamar ana cakamasa kibiya, sbd yace tasu tafi xuwa daya,
Da mmk sagir yace to khaleel yanxu meye abinyi hnklina yatashi nikaina bana so karsa jenny, tsaki sagir yayi duk kai ka janyo wannan tashin hnklin taurin kanka ne yajamaka,
Kwfa khaleel yayi bana son fda plx kabarni naji da abinda nakeji shi kadai ya isheni, idan narasa jenny narasa dukkan farin ciki na rayuwata bana jin xanyi aure, dan konayi wacce na aura baxata taba jin dadin xama dani ba, kallonshi kawai sagir yakeyi dan ya kasa mgn, ina son jenny naso na aureta na reneta na bata ilimi ta goge da rayuwa har xuwa lokacin daxata mallaki hnklin kanta yanda xata iya rayuwar aure dani, da inaji ajikina jenny ta wace, yanxu tana so tafi karfina tayaya dady xai gane jenny itace mahadi na farin cikin rayuwata ? Dafe kansa yayi cikin mayuwancin hali har abada bazan daina son jenny ba,itace macen dana kalleta yanayi na sauya ita kadaice macen dana fara so har nake tunanin rayuwar aure da ita sagir kasan ya akayi jasan Jennifer?
Girgixa kai sagir din yayi,
Kwanciya khaleel yayi hade da tsirawa cillin din dakinsa ido

Ranar lahadi ne da yamma Momy ta ce ya kai wata abu Yar aikinsu kasuwa xatai mata siyayya bayan sunje yai parking dai dai bakin kasuwa wajan kofar gidansu inda mamansu take sai da abinci yana xaune cikin mota ya hango baban avokinsa da ya rasu xaune cikin rumfan murmushi khaleel yayi dan mutumin yana da matukar kirki tun suna yara abokin nasu ya rasu amma khaleel bai manta da shi ba dan yana xuwa gaishe ahi lokaci xuwa lokaci futawa yai daga cikin motar yana sanye da wando 3 quarter da riga maroon ta dan kamashi kadan hannun shi rike da mukullin mota yayo rumfar wajan Baban abokinsa ganinshi yasa mutumin yin dariya hade da fadin sunanshi, khaleel d'ana kana duniya ? Dariya shima khaleel din yayi hade da sunkuyawa baba barka da yammaci,
Yawwa khaleel tashi ga benci nan xauna ya gida ya aiki ya iyayen naka? Mikewa yayi ya xaune hade da fadin suna nan lafiya baba,
Mashaa Allah khaleel har yanxu dai ba iyali ko ?
Kai khaleel ya sunkuyar hade da murmushi ankusa baba,
Af kullum amsar kenan ankusa ba, to ubangiji Allah yasa,
Khaleel ya amsa da amin
Shiru Baban yayi, duk lokacin Dana kalleka sai na tuna da khamis, Ubangiji Allah yaji kanshi da rahma,
Amin baba,
Karasowa tayi tai musu sallama suka amsa kan khaleel akasa bai kalleta ba ta mikawa baba plate na abincin daya siya ta juya xata tafi baba ya kirata, Jennifer xo ki tambayi khaleel me yakeso? Dago kansa khaleel yayi suka hada ido gabanshi yaji ya fadi da karfi wani abu yaji yam tundaga kansa har dan yatsan kafansa da sauri ya sunkuyar da kanshi muryarta yaji me matukar dadi, me xa'a kawo maka ? Girgixa mata kai yayi hade da kara kallonta mmk sosai abin yabashi ganinta yayi adire kyakkyawa Sam batayi kala da sunanta ba aslima shi yafi ganin kamarta da Hausa fulani a hnkl a hnkl gaban nashi ya rage faduwa mmkin kansa yake baba na cin abinci yana mishi hira shi kam hnklinshi nakan sabon sauyin daya samu kansa ciki bai taba kallon mace duk kyanta da tsarinta yaji wannan yanayin yanayi wa mutane kwarjini yau shi akaiwa kwarjini yarinya karama hnkl ya kallo bangaren da take xaune akan benci cikin runfar nesa dasu kadan karantar yanayin da ta ke ciki yayi sbd ya karanci sanin yanayin halayyan dan adam tana da nutsuwa sannan tana cikin damuwa haka kawai yaji tausayinta ya kamashi, kwala kiran sallah akayi, araxane yaga ta kalli inda kiran sallar yake fitowa gaba daya ta bada nutsuwanta akan sauraren kiran sallar mmk sosai ya kama khaleel bai tsure da mmkinta ba sai da suka debi ruwa arumfar tasu shida baba suka fara alwala kura musu ido tayi tana kallon alwalar kana gani kasan alwalar birgeta tayi jinjina kai khaleel yayi ya mike Abu ya hango ta nufosu tagama siyayyar yace ta shiga mota ta jirasu xasuyi sallah xuciyar cike da mmkin yarinyar da kuma tunanin son taimakonta suka shiga masallaci

Bayan sun idar da sallah sun fito shida baba ya kira Jennifer xai biya kudin abincin daya ci da sauri khaleel ya xaro kudi ya tambayeta nawane kudin tace 500 ne ya bata 1k ta tafi kawo masa changy yace ta barshi baba yai gdy shikuma khaleel din ya shiga mota dai dai lokacin da Maman david takara so wajan baba Jennifer tace wai a bar changy? Gyda kai baba yayi bani na biya ba khaleel ne dan gidan Dr bashir na g.r.a xaro ido Maman David tayi, hee ! Baba meyasa baka kirani nayi gaisuwa ba ? A kamfanin babansu fa Baban David yake gadi kamfinsu na takalma ai mutanen kirkine baba, Allah ya saka angode ta wuce tana mmkin ganinshi ana sbd tasan dan manyan mutane ne


*****************
Wasa wasa kullum khaleel ya xauna bashi da aiki sai tunanin yarinyar nan ba yanda baiyi ba ya share ya kasa da kyar akai 1 week da kyar ya samu ya xakulo dabara sbd yaji daxu Momy tana anemo mata Wanda ya iya girki kafin bikin Abu yaxo da yamma ya shirya ya nufi unguwarsu kai tsaye rumfar Maman david yaje bai samu Jennifer anan ba sai Maman david din yatarar ga mamakinsa yana xuwa yaga Maman David da sauri taxo wajanshi dan ta ganeshi sannu da xuwa oga amsawa yayi sannan ya xauna ta gaishe shi da girmamawa ya amsa shima tace me xa a baka yayi Jim ya dago

Please Login or Register in order to submit comment