Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban tsoro



Kansa ya dafe yana jin haushin taimakonta da yayi lokacin daxata fadi daya Sani kyaleta yayi ta fadi yaja tsaki kaxama datti munafuka mayaudariya yana nan xaune yana sake saken yanda xai bullo mata har yanxu yarasa ta ina xai fara a haka har akayi isha'i ya wuce masallaci yai sallah ya dawo gida kallo yafara yaji duk ya fita kanshi ya kashe ya kwanta yana tunanin wannan tunkushash shiyar matsalar ta Jennifer a haka bacci ya kwashe shi

Ganin shi yayi cikin wani daki mai duhu sosai yanda ba ya iya ganin komai can haske ya bayyana ya ganta tsaye da bakaken kaya da bindiga babba tana mishi murmushi meyasa kk son sanin ko ni wacece ?? Ya kalleta da mmk ina son insan mekikeyi a gidanmu ?? Ta bata rai xuwa nayi in kasheku araxa ne ya kalleta wani laifi muka aikta miki da kikeson ganin bayanmu ?? Babban dalili ne ina son daukar fansan iyayena da kuka kashe min su yanxu xan kasheka suma inkashe su Ta nunashi da bindiga .......a firgice ya farka ya hada gumi sosai yana ajiyar xuciya sai yanxu ya fahimci mafarki yayi me ba tsoro tashi yayi yana tunanin mafarkin yarasa me xaiyi laptop ya janyo yana duba abinda ya dace yayi istargram ya bude yana dubawa ya ga mahboob ya dora pix dinshi da Jennifer mutane da yawa sunyi liking suna xuxuta Kyan hoton ya duba yaga pix din yau kwana 3 da dorashi comments yake bi yana jin haushin xuxuta kyan Jennifer da sukeyi idonshi ya sauka kan wani comment da yagani ....kai menene hadinka da SULTHANA??? ya xare ido yana kallon comment din sulthana ?? Kanshi ya daure da sauri ya duba profile na mutumin daya ga sunashi Elmustafha ya duba yaga abinda yake son gani sauka yayi saga IG din yana jin dadin abinda ya gani dan xai tai maka masa sosai dabara ta fado masa yayi murmushi ya kwanta yasan Sam shida bacci kuma sai ya gano wacece jennifer ??



Washegari da safe bayan sunyi break fast sun fito shida mahboob haisam ya kalli mahboob am mahboob ina son kabani laptop dinka da kake chat oh ! Tana daki na wullar da ita kasan kwana 2 dinnan dady ya bani aiki na kula da sababbin ginaginan shi ban sami lokaci na duba social network ba hamdala haisam yayi yanxuma cen xan wuce jiyma fa sai 6 na adawo yau ban San ma lokacin da xan dawo ba ya wuce sai na dwo OK Allah ya dawo da kai lafiya kai tsaye dakinshi ya wuce ya dauko laptop din bai sha wahala ba dan yasan code dinshi ya bude istargram yana jin fargaba dan baisan mai xai tarar ba test ya gani masu yawa da notification
Test din ya bude wani test ya fisgeshi na Ammar ibn Muhammad ..hi guy meya hdaka da Hindu ?? Kasan wacece ita kai gaggawar goge pix din nan idan kuwa ba haka ba xakayi nadama kuma xaka Sa kanka cikin tashin hnkl






By
*UMMEEY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




43&44


Kallon shi sukeyi xuciyoyinsu cike da mmkin ganin su haka da sauri Jidda ta juya tabar wajan zahra ta bita murmushi yayi hannunsa rike dana jenny yai wajan Momy cikin farin ciki yace Momy jenny taxama Yar ki ya ruko hannun Momy ya mika mata hannun Jennifer Jennifer taxama tamu ta fada min tana son ta musulunta fuska Momy ta saki hade da fadin alhmdllh nagode wa Allah rungume jenny tayi ruby ma takara so ta rungume ta naji dadi sosai ta ruko hannunta sukai cikin gidan xuciyar Jennifer tass da ita duk da tana cikin kunci Momy tace zan kira dadynku na fada mishi zansa khaleel yanxu yaje ya taho da Malan Dr Ahmad Sani ningi yaxo ya baki Kalmar shahada da duk abinda ya kamata dai toh Momy ngd a a karkiji komai Jennifer kin zama tawa ina jinki kamar yata Momy ta mike bari na hau sama ruby ta taso kusa da ita ina cikin farin ciki jenny yau xaki karbi Kalmar shahada murmushi tayi itama nima haka ruby xuwa anjima kinxama mu mun xama ke ta mike itama bari naje nayi wanka nagaji itama mikewa Jennifer tayi ta shiga dakinta aciki ta samesu kowacce fuskarta a daure zahra ce ta rufe kofar Jidda cikin kuka nan gidan kune ? Shiru tayi dan bata da amsar bata ke wacc e irin munafukan yarinya ne ? Zahra da take a tsaye ta janyo akwatin kayan jenny tace yanda kikaxo haka xaki koma yau yau din nan kibar gidan nan tunda bana ubanki bane cikin kuluwa jenny tace dole na bar muku gidanku dan nima nagaji da cin mutunci barina gidan baxai xama karshen rayuwata ba duk da ina talaka to xuciyata ba talaka bace ta janyo akwatinta ta fito ba kowa a falo gab da xata fita ta hango suwaiba da sauri ta karaso jenny me ya faru hawaye ya sauko mata suwaiba masu gida sun koreni su wa ?,zahra da Jidda salati suwaiba tayi jenny ta juya ta bar gidan



******* **********

Gidan hindu ta sauka tana ta ruko jakarta hawaye na xuba a falo ta tadda sulthana tana kallo ta wullar da jakar kayanta ta shiga daki tana kuka sosai ta fada kan gado ta rushe da kuka sulthana ta biyo bayanta ta tsaya bakin kofa tana kallonta tana kuka karaso wa kusa da ita tayi ta rike mata hannu xatayi mgn itama kukan ya kufce mata kiyi hkr jenny haka Allah ya kaddara mana dole mu dauki wannan kaddarar jarabawa ce daga ubangiji Allah muyi hakuri mu cinye akwai kyakkyawar rayuwa nan gaba Allah baya jarabtar mutanen banxa hindu ta fito daga wanka ganin suna kuka yasa itama ta karaso kusa dasu ta rungumesu duka dolene muyi kuka dan munga rayuwa kuyi hkr yan uwana addu'ace mafitar mu dai dai lokacin haisam ya shigo sunyi matukar bashi tausayi ya tsaya yana kallonsu xuciyar shi a raunane jenny ta kallesu baku San me nake jiba ni kadai nasan irin feelings din dana keji yanda kikeji hk kowa yakeji hindu tace tana share kwalla a xuciye jenny tace kuma sai kin min fada ? Sulthana ta hararesu hade da yin tsaki ta nuna Jennifer jenny kike ko jinnu sunanki ya dace dake jinni cike da jin haushi jenny tace ke kuma ifrituwa what ? Ifrituwa ? Dariya hindu tayi kun radawa kanku sunan da ya dace daku ifritu ta kumayin dariya yadace da ke ta nuna sulthana akufule tace ke kuma kwankwamai mikewa hindu tayi ta nuna sulthana da yatsa wacece kwankwamai ? Itama mikewa tayi kece kwankwamai wani abun xakiyi ? Haisam ne yace dasu ya isa haka kuna bani mmk yanxu yanxu fa kuka gama kukan halin da kuke ciki baxa Ku taba zama lfy waje daya ba oh ya rabbi ya rike kai sulthana ta Matso kusa da shi sorry ya haisam bai amsa ba jenny naga akwatin ki a falo me ya faru ? Masu gidan ne suka koreni xaro ido yayi bangane ba ? Zahra da Jidda ya salam ! Sbd me ? Suna zargin muna soyayya da ya khaleel janyo stool yayi ya xauna al'amarin ya khaleel dinne da daure kai kinsan haka ya taramu nida mahboob yai mana warning mu fita harkanki ban gane ba ya haisam ya girgixa kai eh shiyasa kika ga mahboob ya dan canza miki ni kaina banda nasan Jidda xai aura zanyi tunanin ko sanki yake lumshe ido tayi ina addu'a Allah yasa kada zargina ya tabbata jenny jikin Jennifer a sanyaye ta tashi inaga ba Ku fahimce shi bane murmushi yayi ki tashi mu koma gida kiyi hkr ni kaina wani Sa in inna kalleki inajin kunya da kuma nadamar abinda nai miki a baya ya haisam kabar tuna baya komai ya wuce ni kai ne kaxame min fitila wacce tasa nasan wacece ni abu daya nake so kai min kanuna Sam baka son inda nakeba koda zakaji suna cigiya ta yai shiru plx ya haisam shikenan xanyi yadda kikso ya mike xanje gida dan Allah ki kula da kanki kada kuyita fadace fadace murmushi tayi baxanyi ba yana kokarin fita sulthana tace ya haisam ba sallma OK hindu zan tafi sai na dawo kwafa tayi ba hindu bace sulthana ce cikin ko inkula yace OK ya fice



****** *********
Momy ta fito daga daki tai dakin jenny taga wayan ta sauko kasa ta duba falo bata ganta ba tai kitchen nan ma bata nan hnklinta ya tashi taxa gaye gidan kaf babu jenny kai tsaye dakin khaleel ta nunfa tana kwala masa kira ya fito ina Jennifer ? Momy Jennifer kuma ? Cikin tashin hnkl Momy tace ban ganta ba da sauri ya fito daga dakinsa yai cikin gida ba inda bai duba bai sameta ba yasalam ! Momy meyasa Jennifer zata bar gidan nan ? Abinda ban saniba kenan khaleel da sauri yai dakin su suwaiba ya tadda ita ta hada kai da gwiwa tana kuka ina Jennifer ? Ya tambayeta cikin tsawa sun koreta ta bashi amsa tana kuka suwaye ya fada cikin karaji zahra da Jidda ya juyo cikin bacin rai a babban falo ya gansu me yasa kuka koreta ? Yana fadan ne kamar xai dake su a tsorace zahra ta gudu bayan Momy tmbyr Ku nake ! Ya xaro belt Jidda ta tsure kayi hkr tasa kuka ina jin kishin ganinka da ita baxan iya jurewa ba OK ya fada kinyi mgn sbd ansa ranata dake ko ? To NAFASA ! Baxan aureki baki San darajar mutun ba baxan iya rayuwa da mutumin da baya daraja kanshi bare ya daraja na wasu khaleel ! Inji Momy meyasa ka rude hk ? Dole na rude Momy !! yanda ya fadi mgnr yasa kowa ya tsorata dan baita ba irin wannan fishin ba ya fice ranshi a bace daki ya shiga hade da rike kirjinshi sbd zafin daya ke masa yana fidda numfashi a hnkl yace jenny ina sonki ! Meyasa kika gujeni ? Kin San irin halin da zan fada na rashinki kusa dani ? Azabtar dani da kikeyi da soyayyanki bai isheki ba har sai kin nesanta kanki dani meyasa ? Kece rayuwata farin cikina kece mace ta farko Dana fara so yana mgn kamar tana kusa dashi nasani kina sona gardamar ki ta hana ki fadamin muyi rayuwa ingantacciya ? Ban taba cewa ina son wata ya mace ba ban saba ba yan mata sun sabar min da cewa su suke sona why ke baxaki fadamin ba ya dauki ruwa ya sha yai hmdl tayaya da girma na in ce ina son karamar yarinya irin jenny? Baxan iya ba meyasa xuciyata taso ta ? Kin xama memin tauraruwa me matukar haske plx plx plx kixo ki fadamin kina sona jenny starshine oh ya rabbi ! Soyayyar ki xata xauta ni laptop dinsa ya janyo ya bude pix dinta ne akai Wanda sukayi ranar Sa ranarsa da zahra murmushi yayi gardamarki starshine xata Sa na auri wata bake ba alhali ke ce xabina dole na takura miki ki furtamin da kanki kina sona ya kurwa lip dinta ido ya lumshe ido ya tuno lokacin da yai kissing dinsu tsikar jikin Sa ta tashi ya rungume hannayensa starshine rashinki kusa dani baraxana ce ga rayuwata kwankwasa kofa akayi dakyar ya amsa suka shigo zahra da Jidda xubewa sukayi kusa dashi kayi hkr ya khaleel xamuje mu dawo da ita shiru yai yana kallon pix din jenny yana sauraron su OK naji zahra ta mike Jidda ta matso kusa dashi ya dakatar da ita no no ! Tashi ki bita bana son hayaniya ta mike sweet heart kayi hkr kada ka fasa aurena naji naji jeki ta juya jikinta asnyaye ka janye mgnr ?, plx kitafi nace plx ya khaleel na janye shikenan ngd ta fada sannan ta fice ya saki numfashi I love u starshine


*************

Bayan kwna biyu

Tana kwance akan 3 siter tana kallon pix dinsu dashi nayi missing dinka Mr coffee ina sonka yanda kake so nayi ne baxan taba yi ba tana mmkin irin abubuwan daya ke nunawa takasa gane me yake nufi shin shima ba Santa yakeba ? Meyasa yake hana maxa su kulata xuciyarta ce ta tunasar da ita Mr coffee yana sonki kamar yanda kike sonsa yana kishinki ba a kishin mutun batare da soyayya ba yayi kissing dinki dariya ta kufce mata ta shafa lip din da yatsunta hkn yana sona kara taji na kida sosai da sauri ta mike hindu ce ta karo volume na wakar film din fan tana rawa a kufule jenny ta dauki remote din ta rage da sauri hindu tace meye hakan ? Dalla bani bazan bayar ba tunda ba gidan shedanu bane sulthana ta fito daga kitchen hannunta rike da plate da acinci a ciki tace xaku fara ? Jarababbu kin San inda jarababbiya take mikewa tayi kada a kuskura a fada min a binda zai tunxirani dan zan iya aika aika hindu tace wanne sakaren ne xai xauna kiyi masa wani abun ? Tsaki jenny tayi ba mmk dan ke Yar masara mutunci ce OK naji amma ai ba arniya bace ni ko ? Hindu tace amma ke tabbatacciyar fitsararriya ce sulthana ta harari hindu harda au kaxa a cin danko Yar daba kawai hindu ta dauketa da mari dai dai lokacin da ya haisam ya shigo duka sulthana ta kaiwa hindu tsawa ya kwatsa musu haba kullum abu daya Ku xauna Ku sasanta kanku hawaye ya xubowa hindu al'amarin mu bana sasanci bane haisam kawai kai mana addu'a ta wuce daki sulthana ya haisam sannu da xuwa bari na kawo mk ruwa a a ki barshi ya fada hade da xama kusa da jenny jenny akwai matsala fa ? Ta kalleshi tame ? Har yanxu hnklin kowa atashe yake sbd batanki kiyi hkr ki dawo office zan wuce naga yakamata na karaso na fada miki kiyi hkr ki koma gida ya khaleel ko fitowa bayayi daga daki plx jenny kiyi tunanin abinda ya dace anjima zan dawo na mayar dake sukai sallama ya tafi


Jin ya ambaci khaleel yasa ta kasa jurewa ta kira suwaiba da murna ta daga oyoyo Jennifer kin barmu cikin wani hali ki dawo dan Allah hnklin kowa ya tashi Mr coffee ma duk sonshi da coffee sai da ya daina sha sosai abinci ma inna kai mishi baya ci kullum cikin fada kinga kuwa yanda hnklinshi ya tashi dadi sosai ya kama Jennifer ta kashe wayan xuciyarta na axalxalar ta akan ta koma gidan da sauri ta shiga daki ta janyo akwatinta dama tagaji da fadace fadacen su itada yan uwanta zata fice daga gidan sulthana tace ke kam baki da aiki sai yawo da jaka ba kyanan bakya cen ? Ke kuma baki da aikinyi sai gulma da shiga abinda bai shafeki ba nabar muku gidan jarababbu Ku cinye kanku hindu tace ala raka taki gona waxai damu tsaki jenny tayi ta fice cike dajin haushin su zama dasu yasa tazama masifaffiya


Bata bata lokaci ba ta iso gidan a cen garden ta hango shi xaune yana sanye da wando 3 quarter da riga blue gefenshi ruwan cway ne tunda ta shigo ya xuba mata ido taji dadin ganinshi kai tsaye falo ta shiga dukkansu suna xaune sunyi jigum ganinta yasa Momy ta mike cike da murna da farin ciki Jennifer ta fada hade da rungumeta ina kikaje ? Kika daga mana hnkl tunda kin dawo alhmdllh ruby ta dauki jakar kayanta muje daki kiyi wanka ki huta kanta akasa ta mike har daki ta kaita ruby idan kin gama hutawa muna falo ta fice ta kalli dakin yana nan yanda ta barshi bude kofar akayi ya shigo gabanta ya fadi ya rufe kofar hade da rungume hannayensa ya xuba mata kyawawan idanunsa masu Kyau da haske fuskarshi a murtuke




By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




45&46

Ya xuba mata ido yana kallonta ranshi abace cikin muryar tsawa kadan yace daga ina kike ? Shiru tayi kanta akasa , ya matso kusa da ita dago kai ki ban amsa , ina kika je ? Asanyaye ta abshi amsa gidanmu . girgixa kai yayi , naje gidanku Maman David tace bakije ba, gabanta ya fadi , tarasa ydda xatayi gashi ya tsareta da manyan idanuwansa,
Naje gidan yayata ne. Tabashi amsa tana addu'ar Allah yasa ya amince, ina kenan ?? Ya kuma tambyrta muryarta na rawa ta amsa
Hotoro, Ok dago kanki ki kalleni
A kunyace ta dago fuskarta kwarjinin fuskarshi yasa takasa jurewa tai kasa da kanta, hannu yasa ya dago da fuskar ta ta xubawa kyakkyawar fuskarshi ido, shima idonshi akanta yana kallonta , kin San irin yaran da suke barin gida batre da wani dalili kwakkwara ba ?? Kai ta girgixa masa, nop kiyi magana, Asanyaye tace bansani ba,
Kwafa yayi yaran dabasu da tarbiyya,
Xaro ido tayi atsorace
Daga yau in ba dady ko Momy ne sukai miki mgn kada ki kuma varin gidannan jina jina? Kai ta daga hade da fadin naji zan kiyaye, Yayi Kyau, ya saki fuskarta sannan ya xuba hannayensa a aljihu, ki kiyaye.
Inshaa Allah zan kiyaye,
Ya fice daga dakin tabi bayanshi da kallo tana murmushi hade da jin dadin ganinshi ta fuskanci ya rame kadan,



************
Dakinsa ya koma ranshi yai mishi dadi na ganin ta dawo gida ya ga abubuwa da yawa afuskarta, tayi missing dinshi, murmushi yayi kadan, kofar aka bude hade dayin sallama mmk ya kamashi ganin Wanda ya shigo hannu suka bawa juna, sagir ? Yaushe ka dawo ? Ba sanarwa? Dariya sagir din yayi, jiya na dawo,
Hamdala khaleel yayi kaxo a time din Dana ke bukatarka, xama yayi ya kalli khaleel man naga ka rame kadan me ya sameka, kallon sagir din yayi da mmk, rama ? Ya maimaita, kana mmk ne sagir ya tmbyshi hade da janyo laptop din khaleel ya bude pix din jenny akai, sagir yace wow, wannan wacece? Ina kasamo kyakkyawa haka ? Karka cemin komai akanta nasan da Jidda aka saka maka rana, plx khaleel ina kamun wannan,
Bata rai khaleel yayi bai bashi amsaba, ta hadu matsalar kawai karama ce, amma nayi mmkin ganin pix din nan sbd nasan wannan ba tai kama da danginku ba, aslima yanda nasanka banajin xaka iya son karamar yarinya, shiru yayi khaleel bai amsa masa ba sbd ya kulu, dago kai yayi ya kalli khaleel yaga yayi kutukutu, shekewa da dariya sagir din yayi lallai fuskarka ta tabbatar min da son yarinyar nan kake, ya kuma kallon pix din wow ! Kyakkyawar fuska manyan ido, karamin baki, ya isah haka sagir, bana son maza su dinka yaba min ita, bana so da mmk sagir yake kallonshi, menene dan na yabi mai Kyau, ranshi bace yace ban hanaka ba itace kawai bana so ka yaba, rufe laptop din yayi, abokina me ya sameka ?? Jingina yayi da jikin kujera sagir ina son Jennifer,
Jennifer? Sagir ya maimaita, Kristen ce ita ? Suka hada ido khaleel ya daga mishi kai, haba khaleel duk matan Hausa Fulani ? No ! Sagir, ya daga mishi hannu, kasan hakan ba haramun bane, dan tana Kristen bazan ki aurenta ba addinina bai haramtamin ba, idan na aureta kamar nayi jihadine, ajiyar xuciya sagir yayi hakane khaleel, kwafa khaleel din yayi ba wannan bace matsalar,
Taurin kai gareta taki ta sanar min tana sona, da sauri sagir ya kalleshi khaleel wai har yanxu kana nan da wannan tunanin naka? Wani kallo khaleel ya wurgawa sagir, kana ganin zan canzane? Naja ra'ayin yarinyar sosai kuma tana sona taurin kanta ya hana ta fadamin, dariyar shakiyanci sagir yayi, khaleel wato kai na daban ne mgn daya kake baka canxawa, tayaya karamar yarinya xata yi maka abinda manyan big gals irinsu nabila, amatullahi, jidda, suka kasa ? Murmushi yayi ina son Jennifer sosai ban San yadda akayi hakan ta faru ba, bakayi mmkin fada maka hakaba? Wata irin dariya yayi sagir mmkin ne yasa nabawa zancen serious, wai shin ya akayi kake sonta ? Kai da kace sai dai mace ta soka ? Bazan iya tunawa ba kawai na tsinci kaina cikin tsananin sonta, itama tana sona bazan iya gane waye yafi son wani tsakanin mu ba,
Khaleel mafita kawai kacewa yarinyar nan kana sonta,
What ? Sagir ni din ?? Ina bazan iya ba banta ba yi ba bakuma zan fara akan karamar yarinya ba, kasani sagir ban taba cewa budurwa ina sonta ba su suke sona, ban yadda da wannan tsarin ba xuwa wajan mace kace kana sonta sagir babban raini ne, ka ja ra'ayin yarinya da dabaru taxo da kanta sbd takasa jurewa tace tana sonka shikenan, lol khaleel kana nan da halinka kai din na manyan yara ne irinsu Jidda, Nabila, wai ina Nabila ne ? Tsaki khaleel din yayi ina ga ko tana Singapore ne ? Meyasa baka son yarinyar nan,
Iska ya fitar daga bakinshi bazaka ganeba Nabila bata da kamun kai dalilin dayasa nake son jenny yarinya ce karama akansu bata kaisu ilmiba har yanxu a 0 label take wannan year din tagama secondary fa amma tafisu aji da kamun kai babu jan ra'ayin da man mata ba amma har yanxu takasa ce min tana sona yai tsaki bana son mace ta dinka hauka akaina koda tana masifar sona nafison ta dinka Jan aji haka nakeso, hakane khaleel wasu matan soyayya tana Sa su manta kansu, yanxu ya xakayi da auren Jidda ka Jennifer ? Gyara xama khaleel yayi yace jenny is too young kona aureta yanxu renonta zanyi, dariya sagir yayi ko kuma ita tare neka ba, dariya shima yayi kasan dai zahra itace autar mu ko ? To nesa ba kusaba ta girmi jenny, kaga dole sai reno, sagir ya buce da dariyar keta ina jiye mk abu daya ranar da yarinyar nan xata rikita ka, wani kallo ya jefa wa sagir anfada maka ni mayen matane irinka kajira kaga abin mmk nan da wata daya zata furtamin tana sona da kanta, wata dariyar sagir ya kumayi, ko kuma kai ka fada mata kana sonta ba, sagir bana son iskanci kaifa shege ne tayaya da girma na da ajina zancewa yarinya karama ina sonta ? Kana ganin xan sauya ne yadda nake ? Kaxuba ido xaka sha mmkina,
Sorry abokina yanuna idonsa wannan shine nawa, amma fa kasani soyayya ba'a yi mata alwashi,
Tsaki khaleel din yayi ya janyo musu wata hirar



***********
Bayan ta fito da ga wanka ta sauya kaya Momy tashigo dakin jenny kin shirya ? Eh Momy, OK in shaa Allah anjima malan Dr Ahmad Sani ningi xai xo kamar yadda muka tsara xai baki Kalmar shahada,
Wani dadi ya kama Jennifer, toh Momy ina jiranshi, tare suka jero suka sauko kasa babbn parlourn gidan suka xauna, Jidda da zahra suna aika mata harara, ta lumshe ido bata damu da kiyayyrsu ba sam dan tasan rayuwa baxta yiyu kowa ya sokaba dole akwai makiya, suna nan a falon suna hira jefi jefi ya khaleel yai sallama shida wani babban mutun gaba daya falon suka mike suka gaishe shi cikin farin ciki da fara'a ya amsa ya xauna yai sallama suka amsa masa,
Wacece acikin ? Suka nuna ta kanta akasa, baiwar Allah meyasa xaki musulunta ? Hawaye ya taru

Please Login or Register in order to submit comment