Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayo, dariya sukayi dukansu idonsu akan juna yaja hancinta,
"ina son hancin nan naki da wannan dankaramin lip din,
sajenshi ta shafa itama
"ina son sajen nan naka daya k'arawa fuskarka kyau
" lol ba dole ki so D'an kyakkyawa Irina ba,
dariya tayi ta k'ara shafo sajensa ya khaleel kai fa Na musamman ne,
lumshe ido yayi
" nasani beautyna amma meyasa kika wahalar dani ?
xaro ido tayi ta Na mmk,
" yaushe zan iya wahalar da ruhina,
kwashewa yayi da dariya ya k'ara mannata da jikinsa alaman yaji dad'in maganar ta,
" lokacin da kika ce dole akai miki akan aurena
da sauri ta rufe mishi baki tana dariya,
asanyaye yace,
" beautyna kin wahalar dani kin san a ranar banyi bacci ba ? sbd tunani na yanda nake sonki haka kike sona nasan ba dagaske kike ba amma duk da haka sai da Na shiga tashin hnkl shiyasa Na sauke komai Na furta miki Kalmar da bantab'a furtawa y'a mace ba,
ke ta dabance ina miki kallon yarinya ashe ke boss ce kinfi gingimari girma, dariya ta kwace mata da shagwaba tace,
" ni gsky ba gingimari ba ce
maimaitawa yayi,
" ni gsky ke gingimari ce, mik'ewa tayi daga jikinshi ya xuba mata manyan idanuwansa yana kallon wuyanta xuwa k'asa wajan k'irjinta tunowa tayi da sauri xata nemi riga, da sauri ya dawo da ita jikinshi,
"a haka nake son ganinki,
kallonshi tayi tana jinjina kai,
d'aga mata ido yayi had'e da kanne d'aya,
"mmkin me kikeyi ?
d'an karamin murmushi tayi
" ina mmkin wai Kaine kk mgn haka kai da nasani shiru shiru baka da aiki kullum sai danna waya,
dariya yayi sosai harda kyakyatawa,
itama dariyar tayi
" plx ya khaleel wai me kk dannawa awaya,
dariya Yakuma yi yana kallon fuskarta,
" oho nima fa ban San me nake dannawa ba,
ware ido tayi tasa hannu ta rufe bakinta sbd dariya,
"oho fa kace,
d'aga mata gira yayi
"abinda nasani idan kina kusa dani bana iya yin komai duk wani motsi tamkar kina motsawa da xuciyata,
kin San akwai ranar da ina bincike awaya muna falo duka garin kula da motsinki nayi formatting d'in komai ban sani ba,
gaba d'ayansu suka tuntsire da dariya,
tana dariya tana mgn
" meyasa toh ban ga alama ba ?
tab'e baki yayi
" ina ganin kin yi karama da soyayya dani
ta harare shi da wasa
"toh yanxu fa ?
"kin xama gingimari
dariya tayi had'e da shigewa jikinsa
" shiyasa naga kana cije leb'en k'asa kullum sai kace min ina da abin cewa ? ko kina da damuwa ?
wata dariya yayi had'e da d'agota daga jikinsa
ya ja hancinta
"beautyna yau kina tuna da kenan kinsan me nake so kice ?
girgixa kai tayi tana kallonshi fuskarta d'auke da murmushi,
" ina so kice ya khaleel I love u,
dariya tayi sbd yanayin da yai mgnr sai da ya sirantar da muryarsa,ya harareta da wasa,
" kika k'i fad'a kikaita wahalar damu bayan nasan kina sona,
ina mmkin ki sosai yanda kika iya rik'e abu a xuciyarki da haka yanmta sukeyi da sunjawa Kansu aji beautyna ke ta dabance a jinki yana birgeni daurewar da kikayi kika jira furtawata ya k'ara miki k'ima da daraja a idona,
far tayi da ido
"kaida jira kk ince ina sonka ? ta murgud'a baki,
xaro ido yayi
" sorry beautyna nina isa koda nace ina sonki ma haka kika d'unga jamin class kika sani cikin wani mugun yanayi ga tsiwa da kika tsira a time d'in
beautyna kin axabtar da xuciya ta lokacin sosai coffee kawai nake iya sha ya k'arasa da harararta irin Hararar wasa,
" sorry ya khaleel d'ina,
kwantar da kanta yayi k'irjinsa
" plx beautyna kada ki k'ara axabtar dani gaba dan kikai min komai xai iya faruwa dani,
" shafa cinyar hannunsa tayi ta lumshe ido tana jin mugun sonsa,
" ya khaleel wahalar da kai wahalar da xuciyata ne tayaya mutum xai wahalar da xuciyar sa ?
k'ara manneta yayi ajikinsa
" baxaiyiyu ba beautyna Allah ya nuna min ranar da xangan ki d'auke da ajiyar babyna a cikin nan naki
" muryarta a sanyaye tace amin,
" kin San lokacin Dana fara dakon soyayyarki axuciya ta ?
girgixa masa kai tayi,
" tun lokacin dana fara ganinki a wajan maman david, kin tuna ranar,
" nasani mana baxan manta ba,
" ina son Na ganki kusa dani shiyasa Na ke kiranki kullum ki kawo min coffee,
ina son naga motsinki kusa dani kada ki b'oyemin komai nasan kina sona kema shiyasa nake waya da Jidda kuma ina ganin sauyawar fuskarki,
alaman kina kishi Na
duk da haka in kikai wani abun a time din xuciyata tai ta waswasin any'a kuwa kina sona ?
bakya nemana idan bani nace kixo ba sannan ba kyamin mgn sai dai Na wuce ki wuce,
Na yadda da wannan ke ta musamman ce,
gani tayi xai yi tone tone ta waske had'e da janyo bargo
" ya khaleel bacci xanyi, janye bargon yayi "ba yanxu ba sai mun gama hira, ta zaro ido
" mundad'e muna hira fa kalli agoga ya kalla 2:40 ya d'an xa ro ido dare yayi ya had'ata da jikinsa kafin mu kwanta kiyi min gud nyt,
kiss tai masa a goshi shi,
ya tab'e baki
" ni d'anki ne daxa kiyi min kiss a goshi ?
dariya tayi tai masa a kumatu,
" anan xakiyi ya nuna mata leb'enshi,
batayi musu ba tayi Dan bacci takeji bayan ta masa ya lumshe ido ya k'amk'ameta ajikinsa sukayi baccin tare kamar xasu had'iye juna



washegari da safe suka had'u dukansu a dining sukayi breakfast y'an uwan dady suna ta kiranshi akan ya dawo suna son ganin y'ay'ansu da safe yace su jira Dan bai basu lbrn yanda akayi yaran suka dawo gida ba baxai je ba har sai dady ya xo tukunna suxo tare


dady ba suxo ba sai wajan 11:00 sukaxo tare da Jidda Dan rigima tasa masa akan yaka wota wajan y'an uwanta ta gansu yabar su ummanta agida sbd har yanxu basu San lbrn komai ba kuma shi dadyn bai fad$a musu ba ko nan ma da xasu da jiddan bata San komai ba, shiyasa koda suka xo take ta mmkin komai tana ta ujjibin meye had'in su jannat da way'annan hamshak'an mutanen,
suma su jannat sunyi murna da ganinta,
basu Dad'e da xuwa ba suka tafi can main house dinsu ched'e estate taron da suka gani ya basu mmk Dan yaransu ta manyansu sunci ado abinka ga Fulani kyawawa sunyi kyau sun gyara wani babbn falo sun k'ayata shi tamkar masu wani had'ad'dan biki cike da mmkinsu muke kallonsu duk yawan nan Nasu ba bare kowa ka gani dan'uwane ko ba'a fad'a ba Kamannin su kusan d'ayane Dan hancinsu iri d'ayane da idanuwansu haka suka k'ayata wajan suka d'inka gabatar da Kansu awajan su jannat bayan sun gama dady ya kwashe lbrn irin rayuwar da y'ay'ansa sukayi nan da nan waje ya rud'e da hayaniya babu abinda suke sai aibata da tsinewa Wanda ya jefa rayuwarsu ga halaka da kyar hayaniyar ta lafa wasu ma kuka suka sa suna mmkin rashin imani Na wanda ya aikata wannan D'an yan aikin,

ita kanta jidda mmk tayi sosai dajin lbrn Dan sai yanxu taji komai tuni taji kunya tako ina danasani ta kamata irin gorin da cin mutuncin da tai musu ashe su d'in yan dangine dangima babban dangi masu ji da kyau da arxiki Alhaji Adam ya gabatar da dady da iyalinsa da kuma khaleel Wanda yake surikinsu suka jinjinawa dady da ya khaleel suda Kansu sukace dady da yayansa sun xama nasu duk irin yadda suke da kyamatar bare shi kanshi Alhaji yayi mmk amma duk da haka gefe guda Na xuciyarshi mugun haushin dangin nasa yake Dan yana xargin b'atan y'ay'ansa har da sa hannunsu yana tare da sune kawai sbd yan'uwansa ne amma shi kad'ai yasan me yakeji game dasu


by
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



91&92

*Ummee Garkuwa*
kashe wayan jidda tayi had'e da xuba tagumi xuciyarta kamar ta fashe dan bak'in ciki ta d'ago idanuwanta ta kallesu suma kallonta suke,
tayi ajiyar xuciya
" ina danasani arayuwata,
rubayya datake kusa da ita ta amshi wayar hannun jidda ta kashe ta kalleta,
"anty jidda babu kyau danasani sbd komai muk'addarine daga Allah hk Allah ya tsara miki rayuwa ni banga aibun danjuma ba tunda mutun ne shima,
kuka jidda ta saka,
"bazaki ga aibinsa ba rubayya ni nagani uwa uba gidadancin sa tayaya kamata xatayi rayuwar aure da irin danjuma ??
Zahra da ta gefensu ce tayi kwafa,
"nifa anty jidda kina ban mmk ya xakiyi da ikon Allah ? ke kika halicci kanki da xaki xab'awa kanki rayuwar da ta dace dake ? ubangijin daya halicceki ya fiki sanin rayuwar da ta kamace ki, duk abinda ubangiji ya baka toh shine alkairi aruwarka ki rik'e kaddarar Allah hannu bibbiyu ki rungumeta sai Allah ya sauk'a k'a miki ni na ce me ? kina jin abinda dady yace xai aura min duk wanda yaga dama kuma na hkr nasan duk wanda na aura in dai bana sonshi shine k'addara ta kuma shine zab'in ubangijina babu abinda kuka xai miki kwarama ki hkr ki godewa Allah idan kina ganin yai miki gidadanci da yawa kisa dady ya maida shi skul ko h.n.d ne ya k'arasa tunda yayi diploma.
tunda zahra ta fara mgn suke kallonta dan sunga kamar ak'ufule take zance,
y'ake jidda tayi ta sunkuyar dakai
"hakane zahra nasan idan ya koma skul myb xai rage wannan kauyanci kina jin fa irin k'auyancin da yai min d'axu wai sunan shi mugun gaye mtsww,
jannat ce tayi mgn bayan tayi ajiyar xuciya,
" toh menene dan yace sunan shi mugun gaye?
anan ma cikin birni in kikaji wani sunan sai kanki yai ciwo dan takaici skul d'in kawai zai koma sai ki sa masa ido ki janyo shi jikinki ki kula da shigarsa harda yanayin maganganun sa cikin lokaci k'alilan zaki ga ya saki,
hindu ta sauke hannunta daga tagumin da tayi,
"ni ko dan fan san soyayya ba shiyasa nake ganin kamar d'orawa kai wahala ne ?
anriga an d'aura aure tsakanin ki dashi me ya rage miki ?
kibi duk hnyr da kikasan zaki gyarashi tunda yana sonki tsab xai bi abinda kikeso,
sulthana ta mik'e,
"wllh anty jidda ki saki ranki kada ki d'orawa kanki damuwa wani ciwo ya kamaki akan abinda xaki iya maganin sa cikin lokaci k'alilan in dai na miji na sonki ai aikin gama ya gama ubangiji Allah ya hadamu da masu sonmu so na Allah jikinsu asanyaye suka amsa da "amin suna shirin kwanciya hjy murja ta shigo d'akin
"ina afrah, ta rik'e baki oh sorry ina jannat tashi maza kije wajan mijinki zaki barshi shi kadai muje,turo baki jannat tayi ,
"umma bacci nakeji
"jeki cen kiyi baccin
rik'o hannunta tayi,
" ya hkr y'ata kinga babu kyau barin miji shi kad'ai sai ki shiga fushin ubangiji ni kuma baxan so Allah yai fushi da y'ata ba,
dire diren kafa jannat takeyi da kukan shagwaba haka dai hjy murja tai ta lallashin ta har wajan b'angaren shi ta kaita sannan ta juya


sallama tayi ya amsa yana zaune ak'asan cafet yana kallon news hannunshi rik'e da cup yana shan coffee kallo d'aya yai mata ya kauda kai ta k'araso kusa dashi ta xauna had'e da gaishe shi cikin kulawa ya amsa sannan ya kauda kai,
kallonshi tayi
ta yi k'aramin murmushi aranta tace yau miskilancin ne ya motsa, ta jingina jikin bed d'in shi tana kallon tv,
kallonta yayi fuskarshi ba yabo ba fallasa yace,
"baki san wajan zamanki ba ?
far tayi da ido itama fuskarta a d'an d'aure ta ce "ban sani ba ina ne ? ta tambayeshine da mmk,
da ido ya nuna mata cinyarshi,
yi tayi kamar bata san me yake nufi ba,
ya janyota ya d'orata kai ya kwantar da kanta k'irjinsa
cikin muryarshi mai dad'i yace,
"nan shine wajan zamanki da kwanciyar ki,
kanta kawai ta d'aga masa dan ta fuskanci yau miskilancin ne ya motsa bai ce mata komai ba sai bayanta daya ke shafawa,
ajiyar xuciya tayi "lallai akwai shiri agabana zama da miskilin namiji hmm sai ka shirya dole na rabaka dashi ya khaleel !
a haka bacci ya kwasheta ajikinsa,
jin tayi bacci yasa ya d'auketa a hnkl ya ajjiyeta kan gadon yana kallon fuskarta tana baccin ta a nutsu numfashin ta na fita a nutse tamkar idonta biyu ajiyar xuciya yayi ya shafa fuskarta a hnkl kamar mai rad'a ya furta ina sonki jannat !
ya gama abinda xaiyi ya hawo kan bed d'in ya janyota jikinsa ya k'ank'ameta ya rufesu da bargo





washegari da rana maman david da papa da Emanuel da david da john suka xo cike da murnar lbrn da sukaji maman david kuka tasaka Abba ya tarasu duka iyalansa hajiya nabila harda kuka wajan yiwa maman david da papa gdy cikin farin ciki papa da maman david suma sukayi gdyn abinda Abba yai musu yabasu gida anan g.r.a tare da makud'an kud'ad'e da motoci kud'ine masu yawan tsiya tuni suka sa kuka sbd basu tab'a tunanin xasu sami dukiya mai d'umbin yawa irin taba tare dasu suka xauna nan suna hira duk yawanci hirar akan rayuwar jannat ne maman david ta basu lbrn ranar da ta tsinceta da yanda suka rayu hajiyarmu da hjy nabila sai kuka suke sai yamma suka tafi


bayan kwana biyar
ammin sulthana taxo ita da y'ay'anta maxa biyu da mahaifinsu cikin farin cikin sulthana ta fad'a jikinsu tana kuka ita kanta ammin kuka takeyi ita da y'ay'anta dan bak'aramin rashinta sukayi ba suna matuk'ar k'aunarta a babban falo suka xauna Abba ya gabatar musu da kansa da kuma iyalinsa sannan yai musu gdy sosai itama ammy ta gabatar da kanta
"sunana hajiya mariya mahaifiya ta y'ar nan dawakin tofa ce dan mahaifina shine hakimin dawakin tofa,
da sauri hjy nabila ta kalleta tana mmk cikin murna tace
"idan kuwa hakane ke yar'uwata ce dan kakan hakimin dawakin tofa ai d'an gidan sarkine kin ga kuwa duk kakan ninmu d'aya cike da murna ammy tace "tabbas hakane ashe sulthana a hannun uwa ta tashi ba banxa ba tun dana kalleta ranar da na tsinceta naji ina sonta sosai ikon Allah jininka jininka ne wannan shine mijina Abdul jabbar ibn yassar shima balarabe ne amma mahaifiyar shi hausa fulani ce dan y'ar nan 9ja ce adamawa state ga y'ay'ana nan babban shine mukarram k'aramin kuma yusuf suka d'ai Allah ya bani sai kuma macen su uwata takaina sulthana, dariya sukayi hajiya nabila tace " ngd sosai ammy kinyi k'ok'ari kin jure duk wata fitina ta sulthana,
murmushi kawai tayi had'e da girgixa kai
mukarram ne yace,
" ukhty kika tafi kika barni narasa abokin fad'a gsky ukhty nayi missing dinki
dariya babansu yayi
"af dama na fad'a maka duk randa sulthana tayi aure kai ka d'ai xaka ci kanka gashi ma batayi auren ba kullum sai ka mana mitar aje a dawo da ita
yusuf yakatse babansu
"abu nifa na kwana biyu banga fad'ansu ba kace suyi in sha kallo dan in ina kallon fad'an anty sulthana da yaya mukarram ba ruwana da kallon tom and jerry,
dariya sukayi
sulthana ta harari yusuf
"mune ma tom and jerry ko ?
hindu ce tace
"oh sulthana yanxu da wancen yayan naki babba kike fad'a?
kwafa mukarram yayi
" hmm ai ammy ce ta fad'a mata wai ita take bina sakuwa tace shiyasa ta rainani,
yusuf ne ya kuma mgn
"nifa gsky ya mukarram kuyi fad'a da anty sulthana nayi missing kallon fad'an ku,
dariya abbu yayi
"sulthana yanxu ta daina yiwa yayanta fad'a ko sarauniyar ammy ?
gyada kai tayi tana dariya hawaye ya sauko mata ta k'ara shiga jikin ammy tana kuka tace,
"ammy duk wannan gatan da soyayyar da kukai min ace ba ku kuka haifeni ba ?
idan na tuno da hakan ina jinjina abun araina,
share mata hawaye ammy tayi,
"meyasa xakice ba ni na haifeki ba ? kina ji fa yanxu agabanki kakannin mu d'aya da mahaifiyar ki kinga kuwa ke y'ata ce ta cikina dad'i sosai ya kama sulthana tana dariya tace "hakane ammyna
haka sukai ta hira cikin farin ciki da murna


washegari suna falo kamar ko yaushe dangin ched'e suka xo dan su sanarwa da dady gobene gagarumar walimar da suka shirya na jin dad'in dawowar y'ay'ansa gida yak'e kawai yayi yace Allah ya kaimu


Alhaji adam yana xaune a d'akinsa yana duba wasu takaddu na wasu kamfani daya manta dashi wayarsa tayi k'ara bai tsaya duba number ba yad'aga sbd hnklinsa nakan takaddun sallama yayi wata murya mara kan gado yaji ta shek'e da dariya
"waalaikumus salam gawa
gaban Abba ya fad'i
yace "me ?
aka maimaita da
"gawa matacce kana murna y'ay'anka sun dawo ko ? toh mutuwar ku ce ta xo gaba d'ayan ku sai mun tura ku barxahu wannan shine hukuncin dana yanke akan b'atamin aiki da kukayi.
kafin yayi mgn an kashe wayar a tsorace ya mik'e da sauri ya fito harabar gidan ya hango khaleel yana waya da sauri ya k'arasa wajansa abinda yaji yana fad'ane yasa shi k'ara tsorata
"ban gane gawa ba ??
bai ji me suka fad'a masa ba ganin abba yasa ya kashe wayan jikinsa asanyaye,
cikin tashin hnkl Abba yace
" me suka ce maka ?
shiru khaleel yayi
" fad'amin mana khaleel
jikinsa asanyaye yace
" sunce min matacce me yasa na auri jannat dan haka sunana gawa dani da ita da kuma dukanmu
" wani bak'in ciki mai had'e da tsoro ya kama Abba,
da sauri ya kira wayan dady kafin dady yayi mgn yace masa
" dr bashir plx kaxo dukanku kaida iyali akwai maganar da xamu tattauna ya kashe wayan hango jannat sukayi ta durk'ushe tana kuka hannunta rik'e da waya ta ajjiye flask a k'asa da sauri suka k'arasa kanta cikin kid'ima Abba yace "lafiya jannat ?
shiru tayi tana kukan
"lafiya nace kin d'aga mana hnkl
rushewa tayi da kuka cikin kukan tace
"wasu ne suka kirani suka cemin matacciya wai xasu kashemu duka tunda muka b'ata musu aiki muka dawo gida
cikin takaici Abba ya yarfe hannu khaleel ma runtse ido yayi hajiya nabila ce tak'ara so wajansu da gudu gudu hannunta rik'e da waya cikin tashin hnkl take mgn
" meya same ku ? kuna lfy dai ko jannat ce ta rik'e ta lafiya ummee ?
kuka tasa ka
"bana so na rasa ku bana so Abba yace menene ?
"wasu ne suka kirani awaya kafin tak'arasa Abba yace " duk sun kiramu,
ki kwantar da hnklinki nasan ba ke kad'ai bace akwai saura duk xasu kira kowa ina son muhad'u waje d'aya mu tattauna

*dan Allah kuyi hkr readers kwanaki biyar xuwa shida nayi deleting whatsap din duk wacce taimin mgn baxan gani ba tunda na goge kuyi hkr idan kuka ga ban amsa ba kusake yimin mgn sannan dan Allah ina cigiyar bilkisu wacce take posting din Jennifer a fcbk plx kiyi min mgn narasa contacts dina sbd delete din danayi dan Allah kuyi hkr na yau xaku ganshi kadan wllh da kyar ma na[truncated by WhatsApp]
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



89&90

duk abubuwan dasu ka faru xuciyar shi na cike da xargin y'an'uwansa dan tun farkon aurenshi da mahaifiyar su basa so hakama lokacin da Allah bai basu haihuwa ba suka dameshi da sai ya k'ara aure ya auri danginsu,
kallonsu kawai yakeyi dan aransa yanda yakeji da ana sauya dangi da ya sauya uwa uba rigimarsu suna damunshi,

su kam farin ciki suke tayi sun had'a k'aramar waleema anan suke fad'awa Alhaji Adam din cewa wannan kwarya kwaryar liyafa ce suna nan suna shirin hada babba dan sununa farin cikinsu da jin dad'insu na dawowar y'ay'ansu gida shikam yak'e kawai yake musu ya kuma bisu da toh ba yadda ya iya,
yasan bai isa yace ah ah ba yanxu yanxun nan su tada fitina da tashin hnkl haka akayi ta lafiya aka gama
kaf dangin ched'e sunyi wa dady da iyalansa kyakkyawar addu'a,

basu koma gida ba sai wajan 5:00 na yamma agajiye suka koma gida sbd gajiya jidda kam jikinta a sanyaye yake ga azababbiyar kunyarsu datake ji ganin yanda take d'ari d'ari dasu yasa suka d'inka janta jikinsu bayan sunyi wanka suna xaune a d'aki dukansu suna hira hjy murja ta kira su falonta wasu manya manyan akwatuna ne masu shegen kyau ko wanne dank'are da kaya acikinsa tace kowacce ta d'auka anjima xa'a k'aro wasu sulthana tace
"toh kafin mu k'anana mu xab'a sai manya sun fara anty jidda itace babba ki fara,
turus tayi a kunyace tarasa yaxatayi hjy murja dake bata san komai ba da murna tace " plx anty ki dauka mana idan kuma duka kikeso to ba matsala anjima suma aka wo musu,
xaro ido tayi jiddan da sauri ta girgixa kai ta d'auki biyu,
hjy murja ta mik'e tana mgn
" sai nayi da gaske dan naga alamar kunk'i sakin jiki dani nifa mahaifiyarku ce bari ni na xab'a muku tunda kunki xab'a ta janyo akwatunan ta rarraba musu tace,
"anjima xa a kawo sauran tace su koma d'aki baxa su iya d'auka ba xata sa ma'aikata suka wo musu

d'aki suka koma suna hira suna jin dad'in ganinsu tare ba rigima ko tashin hnkl bayan sun huta Alhaji ya kira su babban falo dukansu yace,
"Afrah ke ce babba da kanki xan fara,
turo baki tayi
"dady nifa sunana jannat,
murmushi yayi
" toh jannat ina so ki fad'amin marik'an ki ina son ganawa dasu dukansu,
cikin murna tace,
" toh Abba yanxu ma kuwa,
ya kalli sulthana,
"kema jasrah ki kirasu a waya ki fad'a musu ciki satin nan xansa aje ata ho dasu,
ashagwabe tace
" dady nifa sunana Zainab shi ammina tasamin sunan mamanta shine ta saya da sulthana,
dariya yayi cike da jin dad'i
"ikon Allah kinga sunan jannat kenan a da sunan hajiyarmu,
itama hajiyarmu dariya tayi "to takwarata Allah dai ya ramin ku,
suka amsa da amin
ya kalli hindu sai kuma yai shiru had'e da xuba mata ido itama idonta tane ya cicciko da hawaye da sunkuyar da kanta sai kuma ta d'ago kai kamar xata fashe da kuka,
" Abba ni nawa marik'in yana kurkuku amma ya bani kariya sannan ya gatantani alfarma d'aya nakeso Abba kaimin
da sauri yace, "ina jinki akwai wata alfarma da xaku nema wacce xan kasa yi muku ?
sai dai inbani da yadda xanyi in dai kud'i na maganin alfarmar konawa ne zan miki
mik'ewa tayi "ina xuwa Abba tai b'angaren su bata dad'e ba ta dawo hannunta rik'e da wasu takaddu ta mik'awa Abba ya amsa yana kallon takaddun bayan yagama dubawa ya d'ago kai yana kallon ta cike da rashin fahimtar abinda take nufi,
"Hindu ban fahimci me kikeso ba naga sunan mutum goma da wasu kud'ade,
ajiyar xuciya tayi
"hakane Abba sunan mutanen dana karb'ewa kud'ine ina so abiya su,
"girgixa kai yayi cike da takaicin yanda aka wulakanta masa y'a "kada kidamu hindu ko so kike a ninka musu kud'insu sau miliyan zan musu bare wannan d'an abin da bai wuce ko ke kiyishi da kanki ba,
Ya khaleel ne yai magana,
tabbas wannan shine dai dai dan dama sharud'd'an tuba irin wannan na tsakaninka da mutun guda 4
na farko shine
ka daina aikatawa kwata kwata
sannan kayi nadama akan aikata xunubin da kayi
na uku shine
ka k'udirce aranka baxaka k'ara ai kata shi ba har abada
na hud'u shine ka nemi ya fiyar wanda ka cuta idan ya kasance dukiyane sai ka mayar masa da ita,
haka yayi sosai ubangiji Allah ya yafe mana dukkan xunubanmu jikinsh asanyaye suka amsa da amin ita kam hindu kuka ta saka
mahaifiyarta ta kalleta ta runtse ido tana jin takaici mara misaltuwa hakama hajiyarmu kamar tasa ihu dan takaici tsam hjy murja ta mik'e jikinta asanyaye ta dawo kusa da hindu datake ta rusa kuka muryar hajiya murja asanyaye kamar xata sa ihu dan bak'in ciki ta rungumota jikinta,
"hinduna ki daina kuka kad'dara ce kuma daga Allah take kisani wannan halin da kika tsinci kanki aciki ba da son ranki ba bada niyyanki ba kin san shi addini gaba d'aya yana tafiya ne akan niyya Allah yaga niyyanki banda an rabamu dake da baxaki tab'a tsintar kanki a wannan halin ba baxama kisan da xaman masu aikata shi aduniya ba Allah mai gafara ne da kuma rahma ki daina wannan kukan tunda ayanxu komai ya wuce ya xama tarihi yatafi yaxama kamar ba ayi ba ki daina da mun kanki ki d'inka d'aukan kanki tamkar sabuwa addu'a kawai xaki dage kinji hishma ta ,
ajiyar xuciya hindu tayi, tana

Please Login or Register in order to submit comment