Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hargitse hannunta rik'e da d'ankwalinta fuskar ta cike da frin ciki tana dariya.


nan ta xauna suka hau hirar yaushe rabo basu dad'e ba zahra ta shigo tana dariya da mmk suka rungume junansu dake basu koma ba tun xuwan da sukayi

jannat take tmbyr ta
"ina ya mukarram d'in ?"
"da kyar muka rabu yanxun nan wai ba xai shigo ba sai anjima
wai wanne biki akeyi yau ? nayi nayi ya mukarram ya fad'a min yak'i"

suma xaro ido sukayi jannat tace
"biki kuma gsku ban sani ba "
suma d'in basu sani ba sulthana tace
"mu xuba musu ido magani"
nan suka cigaba da hirarsu akan irin soyayyar da mazajensu suke musu su kam sunfi mmkin
danjuma dan wayewar sa ta shammace su yanda suka kula jidda kam nacikin jin dad'i da soyayya mai k'arfi

shigowar hindu da mahboob daya kawo ta ne ya katsesu cikin farin ciki suka rungume juna mahboob ficewa yayi wai ana jiransa xai dawo anjima hira suka cigaba dayi jidda tana baxu lbrn xamanta da mijinta

"maza basu da kunya akan matayensu kunga yanda Ibrahim yake min agaban innarsa da kishiyata? soyayya kamar me haka innarsa ma na sona bakuga yanda suke kulawa dani ba, matarsa ma yarinya ce irin auren k'auyen nan anty take cemin tunda na girme ta,
da ita ake had'uwa ake nuna min soyayya tana da hkr bata damuwa ko kad'an,

dai dai gwargwado yana kwatanta adalci ni kam sai gdy ga Allah dan yanxu baxan iya rayuwa babu Ibrahim ba sbd ya shagwab'a ni da yawa"
dariya sukayi sulthana tace

"munga alama kam ni har mmkin haisam d'ina nake baya iya nesa dani ko ina xani k'afarsa k'afata kulawa ta ban mmk ko cikin gida,
dai dai da toilet sai ya bini shekaranjiya da mukaje gidan momy tana son muyi sirri ya kafa ya tsare yak'i tafiya yana kusa dani kamar xai shige cikina ko kunya sai da momy ta gaji tace muje ciki sulthana kai kuma ka xauna anan ya biyo mufa har d'aki momy tace futa ka bamu gu sirri xamuyi dady ne ya rarrashe sa yace kayi hkr xo mu fita kasan mata da sirri da kyar ya fice momy tace oh yaran nan ! bamu gama sirrin ba ya dawo wai mutafi gida .."
dariya sukeyi dukansu jannat tace

"yanxuma da kyar ya fice bayan kun kwashe 1 hour awaje daga rakiya"

Rubayya tace
"maxan yanxu kam abarsu nifa hajiyarsa ce min tayi Rubayya kiyi ta hkr dan Allah ya had'aki da naci kullum yana gida baya iya kyakkyawan motsi sai kina kusa dashi k'annansa har wasa suke min wai ina mannau d'inki alhmdllh danginsa na sona nayi dacen suruka da k'annan miji bani da wata matsala sai Hamdala"

zahra ta girgixa kai cikin dariya tace
"ni matsala ta missing d'in ku amma kunsan larabawa da kula tari wannan innayi ammi da Abbu kamar suyi me,
sun dink'a cemin sannu sannu
haka dangin sa cikin kulawa dani suke, shi kansa ya mukarram Ammi sai ta koreshi da fad'a

office kafin yaje sai ankusa k'aramin yak'i kusan kullum sai ya makara sai da Abbu yace tare xasu d'ink'a tafiya mu kam mun dace Allah ya datar da y'anmata masu burin yin aure"

hindu kamar xatayi hawaye tace
"amin ni kuma banyi dace ba ranar da aka kaini dayaxo mukayi hira ya fice yabar min gidan ban kuma ganinsa ba sai bayan kwana 3 shida matarsa tace min
hindu kada ki b'ata rayuwar ki da b'acin rai kibar min mijina nawa ne ni kad'ai kiyi hkr kije ki sami wani take tasa ya sakeni saki ma har uku !"
tak'arsa da xubar hawaye tausayinta ya kamasu jannat tace

"ki gdw Allah dan hakan shi ya fi miki alkairi Allah yabaki wanda ya fishi "
suka amsa da
"amin"
suka tashi gaba d'aya suka shiga kitcean suna k'ok'arin shirya lunch

bayan sungama sunyi sallah sun ci abinci suna hira har akai kiran sallar la'asar suka katse hirar sukaje sukayi sallah suka cigaba da tattauna lbrn hjy murja jidda tace
"shiyasa nake xaune lfy da tawa kishiyar ina gudun hak'k'in wani akaina Allah ya kare mu da xaluntar wani"
suka amsa da
"amin"
ya khaleel ne yai sallama ya shigo sulthana cikin tsokana
"oyoyo ga majnun "
d'an garamin murmushi yayi dan sulthana sam bata tsoranshi
"oh ! ashe fa tsoranka nakeji" ta kama baki sauran su ka gaishe shi ya amsa ba yabo ba falla gab da xai shiga d'aki yace
"ya xanyi dake sulthana tunda kin mai da ni k'aramin kakan ki"
dariya suka yi dukansu ya kira jannat ya bata wasu kayan na daban yace ta canza wani shegen yadi ne mai kyau sosai kamar material maroon colour an masa landing da fari sai head fari da farin sark'an gold nan da nan da shek'a kwalliya dasu tana mmkin me xa'ayi shima ya shek'a nashi adon da farin yadi shigen na ta amma shi mai kauri ne suka fito fess da su kamar ranar dinner wayam taga falon ba su sulthana hannunta ya rik'e suka fito harabar gidan taga ank'awata shi da decoration maroon da white su sulthana ta hango kowanne yana kusa da mijinsa ta kalleshi da mmk

"ya khaleel wai me akeyi ?"
janyota jikinsa yayi a hnkl ya rad'a mata a kunne
"birthday d'ina "
xaro ido tayi tana kallonshi ta b'ata rai
"shine baka fad'amin ba?"
"ina son baki mmk ne dan ke zan taya murna khaleel d'inki ya k'ara shekaru"

murmushi tayi rik'e da hannunta suka k'arasa wajen.

wajan xamansu na musamman suka xauna basuyi wani gayyata ba family memmbers d'insu ne kawai sai masu pix da vedio danjuma Ibrahim ne yai jawabi dan shi yagabatar da komai cike da birgewa ya birge kowa da barkwanci akayi nishad'i sannan suka mik'e xasu yanka cake waje ya rud'e ana wak'ar birthday

"happy birthday to u !
happy birthday to u !
happy birthday ya khaleel ! happy birthday to u ! "

ya yanko cake ya bata ta amsa tana k'ok'arin yankowa sukaji muryoyin da ya basu mmk hajiyarmu ce da hajja da momy da ammy da hjy Nabila suka taho suna tasu wak'ar birthday d'in

dariya sukayi dukansu da mmk haisam yake kallon hajja
"hajja harda ke ?"
ya mutsa fuska tayi
"eh harda ni kun maidamu tsoffi baku gayya ce mu ba toh mun kawo kanmu"

mukarram ya harari yusuf daya ke b'uya cikin gyalen hajiyar mu
"nasan wancen parrot d'in ne ya fad'a musu"
ya nuna yusuf
hajiyarmu tace
"koma waye munxo mu yanka cake"
dariya sukayi cike da nishad'i suka yanka cake akayi wasa da dariya masu photuna nayi shike da nishad'i suke hira dukansu kamar baxasu rabu ba.

*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:45 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER
✍✍✍

*na sadaukar da wannan page d'in ga y'an group d'ina Jennifer novel group da Hausa and English novel group da kuma y'an group d'in basma y'ar lele da kuma Ummu khamal novel group and all readers da writers ngd sosai Allah yabar xumunci*

123&124
*Ummee Garkuwa*
basu bar wajen ba sai bayan magrub suna cike da nishad'i sannan suka koma gidajensu

4 days ago
da safe Abba ya kira wayan ya khaleel yace suxo gida shida jannat a firgice suka je tunanin su ko wani abun ya faru

a cen suka tadda dangi sun cika gidan hafiz ne ya kawo hjy murja yana kuka itama hjy murjan na kuka duk ta ya mutse cikin sati d'aya ta koma wata iri kamammnin ta sun canz idan ba kyakkyawan sani kai mata ba baxaka tab'a shedata ba.

jannat na kallonta gabanta ya fad'i tausayin ta ya kamata abinka ga xuciyar mai imani Abba cike da jimami xuciyar shi na cikin rud'u da damuwa yace

"wannan ishara ce da ixna !, nayi mmkin cikin 1 week ace kamar murja ta koma haka, babu kamannin ta ko kad'an,
baxanwa kowa dole ba kafin nayi mgn bari kuji abinda ya kawo ta wajanku"

muryar ta arikice kana jin muryar kasan sai addu'a idanuwanta sunyi k'ulu k'ulu wuyanta ya sirance ga k'asusuwanta birjik kamar ka k'irga

"ku.....ku......kuyi ....yii..... min afuwa..
ku....... ya..yaa ..... fe...feeee..... min....."
da sauri hindu idonta cike da hawaye tace

"na ya fe miki umma tuntuni Allah ya yafe mana xunuban mu dukan mu"

sulthana kasa magana tayi ta xuba tagumi tana kallon hjy murja tunani barkatai takeyi
tasan hjy murja ta cucesu ta xaluncrsu ta kuma k'untata musu yanxu kam xuciyoyinsu sun karye da ganin halin data ke ciki meyasa ita bataji tausayin su lokacin da suna cikin taraddadi ? meyasa taraba su da iyayensu tun suna kwana 40 aduniya ? shin ita bata da irin wannan imanin ? hmmm tabbas imani baiwa ce daga rabbi idan baka da shi bakaji dad'in hali ba.

dangin ched'e ma shirun sukayi suna jimami shekara 20 suna fad'a da junansu ta xuba musu gaba da jin haushin juna uwa uba taraba su da d'an uwansu ta sace musu y'ay'a tun suna da 40 days a duniya any'a xasu kyaleta ?

hjy Nabila xuciyarta ta karye ita yanxu bata da sauran bak'in cikin rayuwa amma har yanxu akwai wani mugun d'aci na musammam data keji aranta akan murja sbd cin amanarta da tayi uwa uba yaudarar da taimata da tsantsan butulci any'a xata iya

suna cikin wannan halin na tunane tunane hjy murja tayi wani irin kaki da kyar ta tofar da uban gudan jini kafin kace me rai yai halinsa ta mutu basu sani ba

hafiz ne ya kula yai salati da k'arfi yana jijjiga ramamman jikinta araxane suka mik'e suna kallon gawarta dangin ched'e suka mik'e had'e da fad'in Allah yaji k'anta xasu tafi Abba yace su tsaya ai mata sallah suka ce ina baxasu iya ba sum mata dai addu'ar Allah yaji kanta asalima gawar ta ta tsoro take basu fur suka tafi kad'anne suka tsaya

wasa wasa suma sauran suka gudu Abba yarasa yadda xaiyi da kyar ya lallashi hajiyarmu tai mata wankan gawa wai gawar tana wani irin wari mara dad'in ji

tun safe har k'arfe 5 na yamma Abba yana rarrashin danginsa akan xuso aimata sallah akaita fur sun bujure ransa yai masifar b'aci yarasa yadda xaiyi da gawa surukan sa ma su haisam guduwa sukayi dangin ched'en sun sugaxu kada suyi

cike da jimami dady yake kiran wayan su off ya jinjina abun wannan wacce masifa ce haka ? tun aduniya ma ace ana gudin gawarka ? sallah ma mutane sun k'i yadda suyi maka to me xaka je katarar a cen ? shedar mutane shedar samun rahama

kuka Abba yasawa dangin sa ganin hakan yasa su kaxo suna k'unk'uni malan dr Murtadha Garkuwa Abba yasa yai musu wa'axi da jikinsu ya sanyaye suka ce sun yafe mata tun da Allah yana san me yafiya Allah ya yafe musu akai mata sallah aka binneta xuciyoyinsu akarye

suma su jannat duk wa'axin akai musu suka yafe mata suna kuma neman mata gafara awajan Allah suna addu'ar suma Allah ya yafe musu

haka aka gama xaman makoki na kwana 7 aka watse .

6 months later
cikin jannat ya girma sosai haihuwa ko yau ko gobe tana shan kulawa sbd ya khaleel yace kada ta wahalar masa da ita da kuma ajiyarsa

ranar litinin tun safe take jin bayanta na ciwo kad'an kad'an haka mararta na murd'awa jefi jefi asitin da suka saba xuwa sukaje dr ta duba ta tace ba haihuwa bane juye nan haihuwar sai nan da 1 week ko kwana goma suka dawo gida dan shi ya khaleel shi ya matsa suje sbd ita ciwon bai uxxira mata ba.

suna dawowa gida ya tafi wajan maman yusuf (maman david)
ya amsowa jannat teb'a tunda sukaje gidan taci ranta ke so y'ar aikinta tai mata taci taji sam bai mata ba ita lallai irin na maman yusuf d'in takeso.

yana tafiya ciwo ya dawo d'anye tasha ruwan rubutun da momy takawo mata tun cikin yana wata 5 kamar ta k'ara ciwon ba shiri ta kira mak'ociyar ta nos Aysha Garkuwa tana xuwa ta dubata taga haihuwar ce gadan gadan cikin mintuna ta haihu bayan tasha axabar ciwo da ita kad'ai tasan shi tana haihuwa taji kamar an xare mata ciwon haka Aysha Garkuwa ta gyara d'an ta goge d'akin ta d'iban mata ruwan xafi a toilet d'inta jannat d'in ta shiga ta shek'a wanka.

kafin wani lokaci sun gyara ko ina gida ya d'au k'amshi gsky Aysha Garkuwa nada kirki sosai.
jannat hannunta rik'e da d'anta tana kallon shi kyakkyawa kalar mahaifinsa

xuciyar ta fal farin ciki mara fisaltuwa Allah ya axurta ta da baiwa na wannan sunkucecen yaron suna hira jefi jefi Aysha Garkuwa na mata hira ita kam xuciyar na kan d'an da Allah ya bata

sallamar ya khaleel sukaji cike da d'auki ta amsa yana shigowa idonshi ya sauka kan jaririn dake hannunta

cikin rud'ewa yai wajanta yana kallonta cike da mmk yarasa me xaiyi fuskarshi a washe

Aysha Garkuwa tace "congratulations kasamu k'aruwar d'a namiji Allah ya raya"

cikin kid'ima da wani irin farin ciki da bai tab'a tsintar kansa ciki ba yai wata irin tamabaya

"da gaske nine me wannan d'an ? Yanxu nima ina da d'a ? d'ana na cikina Alhamdulillah "

ya rungume d'an ak'irjinsa yana jin kansa tamkar yau shima ya diro duniyar

murmushi Aysha Garkuwa tayi ta sulale ta bar gidan dantaga abin nayine

tsurawa jannat ido yayi yana kallonta ta k'ara wata k'ima da daraja awajansa yana kallonta kamar ya cinyeta dan so.

"beautyna kece kika haifamin d'a ? "
yafad'a muryarsa asanyaye dan shi kad'ai yasan irin farin cikin daya keji

itama tsura masa ido tayi tana jin sonsa na musamman na k'ara bajewa a cikin jikinta
"Alhamdulillah jannah nagode wa Allah da yai min wannan baiwar"

janyota jikinsa yayi ya had'a da jaririn ya rumgume yana jin farin cikin da bai tab'a jinsa ba
xamewa tayi tana kallonsa
"kafad'awa su momy da mama"

d'ansa rungume a k'irjinsa ya d'auko waya momy ya fara kira tana d'agawa yace
"Albishirin ki momy"
dariya Momy tayi tace
"goro"
"sai fa kin bani tukwicina dan albishirin na musamman ne"
"xan baka kai dai fad'amin"
"yau kin xama kaka kinyi jikanki na farko kixo kiga jikan ki "
kama bakin ta tayi
murna da farin ciki ya cika mata xuciya wullar da wayan tayi ta d'auki gyale a falo suka had'u da Dady
akid'ime yake tmbyr ta

cike da farin ciki ta fad'a masa abinda ya faru hamdala yayi cike da murna Allah ya sauke ta lafiya tare suka je kan hanyar xuwansu ya kira Abba da shima tuni khaleel d'in ya fesa masa.

cikin lokaci k'alilan gidan ya cika tam da dangi kowa ka gani na cikin nishad'i hakama angon k'arnin khaleel daya kafa ya tsare yana rik'e da sabon babynsa tun su hajja da hajiyarmu na tsokanarsa har suka ga yana k'ok'arin wuce gona da iri dan k'in fita yayi sai da momy ta kira Dady suka fita tare da kyar.

haka suka cigaba da d'an biki dan kullum sai anyi shagali jika na farko agun Alhaji Adam ched'e dole kam ayi bidiri sabon baby yaga gata da soyayya duk wanda ya d'aukeahi da kyar ya ke iya ajjiyeshi a haka har nanar suna ta xagayo yaci sunan sa muhammad wohoho ! anyi b'arin nera ranar kam dan duk wani iyalin attajiri na 9ja burinsu aci taron sunan nan dasu bayan angama taron suna Abba da dady suka shirya nasu waleeman na daban wanda abokanan su sukai wa muhammad kyaututtu ka na ban mmk washe garin suna kuma k'ana nan yaran familyn ched'e suka shiryawa Muhammad nasu shagalin na daban a Ni'imal hotel Muhammad d'an dan gi duk wani yaro ko yarinya na dangin ched'e da kalar nashi gif d'in abin abin birgewa sati cur aka kwashe ana xabga walima kamar baxa adaina ba.

Muhammad wanda suke kiransa da sunan sa kyakkyawan yaro lafiyayye mai kuxari yaro mai farin jini tunda aka haife shi gidansu bai rabo da mutane na son ganin shi

watan ta bakwai da haihuwar Muhammad da yamma Haisam ya kirata sulthana tana asibiti tana na k'uda ita da ya khaleel suka tafi hnklinta atashe

suna k'arasa wa suka tadda rubayya da itama take jan tsohon cikinta dan sunyi tunanin sai ta riga sulthana haihuwa hajja da hajiyarmu da momy da hjy Nabila na asibitin haisam da hnklinsa baya jikinsa dan shi ta sulthanan sa yake,

aiki yaxo ga ma'iya haka taita salati dan nak'udar ta d'anxo da jinkiri salati kawai take tana kiran sunan momy cikin ikon Allah ta haihu ta haifi y'arta mace haisam kam bai kula da y'ar ba shi dai burinsa yaga sulthanan sa garam sai da aka gyarata yaga lfyr ta lau sannan ya dawo kan babyn yana murna kamar xai had'iye ta

ya rik'e y'ar ya k'ura mata ido yana murmushi shi kad'ai yasan meya keji aransa hajja tagaji ta ya mutsa fuska

"haisam abamu y'ar mugani ko ?"
marairaicewa yayi

"hajja ki bari nagama kallonta "
kama bakin ta hajja tayi
"oh ni Hafsatu ! xamani "
momy ce ta karb'e y'ar tace
"tafi ka bamu waje"
"momy plx har yanxu bangane dawa take kama ba,
bawa hajiyar tagani"
hajiyarmu ta amsa tana wa y'ar wasa
"ai nafita kyau dan kowa ya kalli wannan jar y'arta ka ya ganka ba sai ance taka bace"
dady da Abba ne suka shigo suna murna da jin dad'i Allah na axurtasu da jikoki.

nan da nan asibitin ya cika da dangi dan su kansu likitocin sun san y'ar dangi aka kwantar

*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:45 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER
✍✍✍

*jinjina ta musamman gareku my group ADO DA KWALLIYA da kuma group Zama na Amana Umar Dalha and cweetjidda habibty*

125&126
*Ummee Garkuwa*

ranar aka salla mota sbd ita da yarinyar ta suna cikin k'oshin lfy
suna komawa gida da daddare akai musu waya Rubayya ta haihu ta haifi d'anta namiji rana d'aya kenan suka haihu da sulthana amma ita Rubayyan da daddare

rana d'aya akai shagalin suna sunyi gagarumin taro anyi wadak'a da mony kayan rabo kam duk xalamar mutum sai ya gaji y'ar sulthana taci sunan hajja Hafsat d'an Rubayya kuma sunan baban prince A.K Garkuwa wato kabeer.

sati biyu da sunan su sulthana da Rubayya
jannat ta tashi da zazzab'i mai zafin gaske ga tashin xuciya duk abinda taci sai ta dawo dashi hnklin ya khaleel ya tashi sosai ya kaita asibiti aka bata magunguna suka dawo gida bayan kwana biyu xaxxab'in ya dawo su ka koma asibitin akai mata test tana da ciki wata uku.

abin ya bata mmk shi kam khaleel murna yake sosai tun akan hanya ta had'a rai tana kallon d'ansu Muhammad me wata takwas yaro me kuxari da lfy dan har yana mik'ewa tsaye b'ul b'ul da shi ko kad'an bata son abinda xai tab'a lfyr d'an ranta b'ace suka koma gida asalima haushin ya khaleel takeji daya ke murnar cikin wanda take tunani shi sam baya ganin abinda xai faru suna komawa gida kai tsaye d'akinta ta wuce

tahad'a kai da gwiwa tana tunani mai xurfi ranta ab'ace.
d'akin ya shigo hannunsa rik'e da Muhammad daya ke bacci kusa da ita ya kwantar da shi ya xauna inda take had'e da janyo ta jikinsa

"beautyna har yanxu zazzab'in ne ?
kiyi hkr xaki warke ...."

tureshi tayi daga jikinta ta matsa nesa dashi tana masa wani irin kallo still ma tsowa yayi yana k'ok'arin rarrasan ta
"kwantar da hnklinki jannah ! inshaa Allah..."

afusace cikin fushi ta katse shi
"ka kyaleni ! sam raina bai son cikin nan ! ka kalli Muhammad baka tunanin halin da xai kasance idan ya sha ciki? zubar da shi xa'ayi ......."

da k'arfi cikin fad'a yace
" firdausi !wa ya isa ya xubda cikin nan !? babu shi sai Allah wllh ! wllh ! kada ki fara dukansu y'ay'a nane ina sonsu kada na k'arajin wannan maganar"

"dama dole kace haka tunda bakai kake d'auke da cikin ba ba ajinkin ka yake ba kuma sai na zubar ba zan haifeshi ba dolene kayi duk abinda xakayi ..."

"xakiga abinda xanyi dan sai na d'au babban mataki duk shegen likitan daya xubar dashi wllh sai na d'aureshi ke kuma ! xakiga abinda xan miki muddin kika tab'a cikin nan..."

ya wurga mata wata uwar harara ya fice
durk'ushewa tayi awajan tana kuka sosai xuciyarta na ingixata tana jin haushin ya khaleel sam wannan rashin adalcine kaso d'an da baka samu ba karasa wanda kake dashi ?
ina ita bazata iya ba

daren nan kam babu wanda yai bacci kowanne xuciyar shi na masa k'una uwa uba kewar juna dan wannan shine karon farko da suka raba wajan kwana

wasa wasa sun shafe kwana 7 babu me kula juna asalima yanxu ya khaleel sai 12 na dare yake dawowa gida tun bata damuwa har hakan ya fara bata tsoro ga kewar shi da ta addabe ta

tana xaune a falo ya shigo fuskarshi a murtuke ta kalli agogo !2:07 ta kalleshi axuciye take masa tamvaya
"daga ina kake ? meyasa ka dawo yanxu da ka sani acen ka kwana"

jim yayi yana kallonta al'amarinta ya daina bashi mmk ya dawo tsoro yarasa yadda akayi ta iya futsara haka kamarshi babba wannan yarinyar k'arama ta dink'a gasa masa maganganu ? lallai tagama raina shi kaje ka rufe ta da duka tasan kai ba sa'anta bane da sauri ya girgixa kai yana a'uxiyya

bai tanka mata ba ya wuce dan muddin ya tsaya tankamata bai san mai xai faru ba dan xuciyar shi har wani hayak'i hayak'i take sbd b'acin rai

bin bayansa tayi da kallo xuciyar ta cike da xugar da take mata
"lallai ma yarai na miki hnkl ya maidake wata mahaukaciya kina mgn ya kyaleki ki bishi ki faffad'a masa bak'ak'en maganganu"

fuuu ! tabi bayansa kamar ta tashi sama a xaune a bakin gado ta sameshi yana k'ok'arin cire riga rik'e k'ugu tayi tana karkad'a jiki xuciyarta na ingixata

"sbd tsabar rainin hnkl ina mgn ka kyaleni ? wato ka maida ni mahaukaciya ko ? me kake nufi ne ? ciki ko ? nace xaina xubar dashi kayi abinda xakayi"

kamar baxaiyi magana ba ya daure ya rarrashi kansa cikin ko inkula dan ko kallo bata ishe shi ba

"meya shafeni da xubar da cikin da xakiyi ? tunda har kina da amsoshin daxaki bawa ubangijinki in ya tambayeki name kike jiran nawa hukuncin ? ke mai wayo ce wayon naki ya kai ki iya yiwa wanda ya halicce ki kije kiyi duk abinda xakiyi kin san kwanakin daya rage miki aduniya ko ? kina da tabbacin xaki wuce gobe ko jibi ko ? ke kika ba kanki d'an kuma bakya so kinga dole ki watsa shi a bola jibi in kinga dama xaki kuma bawa kanki tunda ke daban kike baxa aimiki tambayar kwanciyar kabarinki ba its good kiyi duk abinda kiga shine dai dai "

axahirin gsky maganar shi tasa mata tsoro amma ta basar ta rasa ma amsar da xata bashi wa'axi yai mata cikin sigar bak'ar magana ta yaya xata amsa masa ?
afusace ta fice tana surutai k'anana k'anana

tab'e baki yayi yana mmkin canxawar jannat d'insa lallai d'an Adam tara yake bai cika goma ba dolene wata rana ya b'ata maka xo mu xauna xo mu sab'a dalilin dayasa yai mata uxiri kenan

d'aki ta koma tayi tagumi tana juya maganganun sa "kina da tabbacin xaki kai gobe ko jibi kin tanadi amsoshin kwanciyar kabarinki..."
gabanta ya fad'i ita da bata da lfy kuma tana son xubda cikin nan

shin inta xubar mai xata cewa Allah ? my b ma baxata sake haihuwa ba .... araxane ta mik'e ta k'urawa Muhammad ido tana son d'anta tana tsoron kar yasha cikin da y'ay'a suke sha suyi ta cuta ak'arshe ma su mutu dafe kanta tayi ya salam ! ya xatayi ? any'a kuwa xat iya xubar da cikin ? tsoron data keji kartaje ma garin xubar da cikin ta mutu alwala ta d'auro ta tada sallah tadad'e tana nafilfili sannan ta kwanta

tana kwance da jarirai guda biyu suna mata kuka tayi tayi su karb'i nono sunk'i asalima jariran hararta suke harara bata wasa ba tarasa yadda xatayi dasu a firgice ta farka cikin tsoro ta janyo Muhammad ta rungumeshi tana fidda gumi baccin da bata koma ba kenan

washe gari bata ga fitar sa ba tayi jigum kewar shi ta isheta uwa uba har yanxu tsoron mafarkin datayi takeyi ita

Please Login or Register in order to submit comment