Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Muhammad kad'ai afalom sai sambatun da tv takeyi sallama taji a tsorace ta amsa

y'anmatane matasa suka shigo gidan su hud'u masu kama d'aya tsoro yak'ara kamata suka gaisheta a d'ad'dari ta masa ganin kamar tana jin tsoro sosai yasa babbar cikin su yin murmushi muryarta asanyaye tace
"sunana khadeeja Garkuwa wannan k'anwata ce sunan ta Zainab Garkuwa da Halima Garkuwa wannan itace k'aramar mu Rumaisa Garkuwa mu k'an nan Aysha Garkuwa ne"

sai yanxu tasamu xuciyarta ta sanyaye cikin murmushin da bai kai xuci ba tasake suka fara hira sosai dan ta fuskanci suna da hankali duk da yara ne hira sosai suka ye suna cikin hiran ya khaleel ya shigo tayi mmkin ganinsa ganin ya shigo yasa suka mik'e xasu tafi jannat tadakatar ta shiga d'aki ta had'o musu kayan kwalliya dan taga yaran y'an son kwalliyane sukayi gdy suka tafi

jigum tayi tana kallon k'ofar d'akinsa wata xuciyar tana taje ta rarrashe shi wata kuma tana hanata na ita fa macece tajawa kanta aji kartaje ta bari har sai yaxo inba haka ba sai ya rainaki ya xaci ma ke kika damu ko ke kike sonshi xugum tayi tarasa abinyi da sauri ta shiga d'aki ta d'auko carfi tana xkirin da duk yaxo bakinta ta kwanta tana xikirin ta tashi jikinta asanyaye qur'ani ta d'auko ta fara karantawa

tana karatun tana jin xuciyarta kamar an wanke mata ita ajjiye qur'anin tayi tana jin muguwar hud'ubar xuciyar ta karkije tayi a'uxiyya tayi addu'ar korar shaid'an ta shiga d'akin yana xaune yana kallon News kallo d'aya yai mata ya kauda kai

haushi ya kamata irin kallon dayai mata ta daure dan mafarkin jiya ya bata tsoro kusa dashi ta xauna tarasa ta ina xata fara mgn korar shad'an tayi dan tasan shiyasa mata waswasi muryarta tasanyaye ta fara magana

" nasan ban kyauta ba .. amma nayi cikin rashin sani....nasan na b'ata mk kayi hkr na janye waccen maganar Allah ya sauke ni lfy "

shifa dama ya damu matuk'a dan shi kad'ai yasan axabar da yasha na rashinta kusa da shi
kwatsam xuciyar shi tafara kai kawo
"kar ka hkr ka gasata tukunna dan yarinyar tagama rainaka banda rai nin wayo tace xata xubar da ciki ? wannan taxama mashirkiya ka kyaleta inda hali ma ka wanka mata mari ka koreta daga kusa dakai tuban muxuru tayi my b ma ta xubda cikin tunda tace sai ta xubar"

dafe xuciyar sa yayi da hannunsa yana juya zancen daurewa yayi ya kori shaid'an yai addu'a sannan yaji xuciyar sa tasaki kafin ya kuma jin wata xigar ya janyota jikinsa muryarsa asanyaye

" kin kyauta da kika gane kuskuren ki har kika janye sab'awa mahaliccinki,
rayuwa ta gaji hk xo mu xauna xo sab'a shi shaid'an babban burinsa rusa xaman lfy musamman ga ma'aurata dole ma'aurata su tashi tsaye suyi yak'i da shaid'an idan har suna son zaman lfy idan har yai nasara akansu tofa sun shiga uku dan basu babu farin ciki,
ya xama dole mu tashi tsaye beautyna mu yak'eshi tunda har yai nasarar samana jin haushin juna"

lallai sai yanxu tai tunanin hk data biyewa xuciyar ta da yanxu tana nan ranta ab'ace tada saukar da kanta tunda itace k'asa dashi sannan ita ta b'ata masa gashi yanxu tana jin farin ciki sosai

"hakane ya khaleel Allah ya rabamu da sharrinsa Allah yai mana tsari dashi" ya amsa da "amin"

ranar cikin farin ciki suka yini suka kwana suna nuna missing d'in junansu

kwanaki satittika watanni biyu suka wuce wato yanxu cikinta wata biyar cur jidda ta haihu ta haifi d'anta namiji me kama da fulani sak dan kamarsa d'aya da babansa nan da nan dangi suka cika gidan zahra ma taxo da cikinta wata uku ita da ammy da ya mukarram da ysuf xuka xo sai sati na xagayo wa aka sawa d'an sunan dady Bashir anyi shagali kam dan abokanan mugun gaye sun xo na cen kauyan su sunyi irin nasu shagalin da wasan da sukeyi idan ammu su haihuwa .

ranar sunan hjy Nabila taja jannat gefe tana bata lbrn Hindu mahboob ke sonta ta k'e k'ashe k'asa tace bata so sam wai abin sai yai yawa asalima ita bata son auren xumunci dan ita mahbobb wane awajan hjy Nabila ranta asoshe take mgnr
" ni har mmk take bani tunda aurenta ya mutu da hafiz take gidansu mahboob d'in kuma yace yana so ta k'i Dadyn naku yace ba mai mata dole shi kuma Abbanku yace ko tana so ko bata so sai ya d'aura auren y'ar'uwar ku ce kuyi mata fad'a"

"umma kwantar da hnklinki zan mata mgn komai xai wuce Allah ya xab'a mata abinda ya fi alkairi"

ta amsa da "amin"

wata d'aya da sunan jidda jannat ta kira hindu kan mgnr ta da mahboob
"Hindu meyasa bakyason mahboob ?"
"nba sonsa bane banayi bana son auren zumunci ne kawai wllh ina son sa sai dai hkr dannyi yanxu ma na turawa dady wanda nake so"
xaro ido jannat tayi

"waxaki aura to"
"wani ne sunansa Auwal"

"haba Hindu ya mahboob d'inta fa ?"

kallon jannat d'in tayi ta girgixa kai
"jannat abun yayi yawa ke kina auren khaleel sulthana na auren haisam sannan ace dole sai na auri mahboob? yes dukanku ba dole akayi muku ba asalima ku kuka had'a kanku amma baxan iya ba iya taku ta isa ni mahboob wana ne yayana ne baxan iya auren shi ba idan kuma damuna xakiyi da mgnr xanyi tafiya ta dan ban son maganar"

"hmmm Hindu kenan Allah shi ya had'a ba wani ba idan Allah yai mijinki ne ya xakiyi?"

shiru hindun tayi jannat d'in na mata nasiha fur tak'i sauraron ta dole ta kyaleta

ba ajima ba akasa ranar hindu da Auwal mahboob da meenat budurwar sa duk wata biyu kwanci tashi har wata biyun ta cika suka fara hidimar biki zahra taxo da cikinta d'an wata 6

ana sauran 1 week a d'aura aure
Hindu na kwance wayarta tai k'ara tana dubawa taga Auwal d'inta tai murmushi ta d'aga suka gaisa had'e da d'an tab'a hira kamar yanda suka sa ba bayan sun gama wayan bata kashe ba tana tunanin ya kashe ta ajjiye wayan ta koma ta kwanta kanta na dai dai inda wayan take taji surutun su Auwal d'in tana k'ok'arin kashewa maganar data ji sunayi ne yasa ta d'auke wan numfashi

hankalinta yai masifar tashi mmk da haushi da takaici ya dirar mata lokaci d'ya taji tana mugun danasani

*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:45 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

127&128
*Ummee Garkuwa*

wata murya ta bata sani ba taji ana mgn
"Auwal kai fa shege ne wai da gaske kake y'ar gidan Adam ched'e ce ? nasan ka mak'aryaci ne idan kuwa yarinyar y'ar shi ce gsky kayi babban kamu ka kamo mana k'aton kifin daxamu dink'a cin kitse"

"zauna nan d'an iska wallahi nayi mmkin yarinyar nan data soni bata son ni d'in shege bane aureta xanyi kaga nima nan gaba afara kirana Auwal ched'e hahahh"

"tasan kuwa kana da mata?"

"mahaukaci ne ni xan fad'a mata ina da mata ? naiwa kaina asara bata son komai akaina ba kuma baxata sani ba ni dai nasan har ga Allah banda arxik'in gidansu wllh baxan sota ba naji fa lbrn ta tab'a yin aure kwana 3 auren ya mutu sannan ance ma yarinyar karuwa ce ta dad'e tana karuwanci da larabawa a dubai kai k'ar she ma kasan baxan b'oye maka komai ba wllh y'ar damfara ce kasan waye ya fad'a min ? k'anin matar da ta auri mijinta shiya bani labarinta ful,
da na aure ta tasan komai akaina tace xatai min hayaniya nima intada nawa b'allin kin fad'a min ke karuwa ce ? kaga dole tayi shiru,
hhhhh abokina sama taka Allah yai min arxik'i kuma dole kusamu naku"

"kai yanxu da hnklinka xaka auri y'ar damfara Auwalu?"

"ai nima babban d'an damfaran ne tunda nima damfare ta zanyi ita da ubanta ni banda mu wllh koka d'an bana sonta kud'in su kawai nakeso dana samu sakin ta xanyi,
d'an xaman danayi da ita na fuskanci bata da son hayaniya so wannan yana sa inajin tausayin ta shiyasa baxan wani d'au dogon lokaci tare da ita ba"

takaicine yahanata jin k'arshen maganar ta kashe wayan had'e ta fa shewa da kuka ta dad'e tana kukan sannan ta shi da sauri ta tafi gidan su a falo ta tarar da Abbanta yana duba jarida ta xauna had'e da sama sa kuka

da sauri ya ajjiye jaridan yana tambayan ta lfy dan bai son abinda xai tab'a masa y'arsa cikin kuka take mgn

"Dady kabani 10 millions dan Allah"
jim yayi yana kallonta hannunsa yasa akanta

"Hindu me xakiyi dasu?"
"akwai muhimman abinda xanyi dasu Abba"
ta kwashe lbr ta fad'a masa tagumi yayi maganganun yaron su sosa masa rai amma ya xaiyi ? k'addara ce ba son ranta ba gashi yanxu ammata gori

check ya d'auko ya rubuta kud'in ya mik'a mata ta amsa had'e da ajiyar xuciya
"Abba xuwa xanyi na bashi tunda dan su yake sona amayar masa da komai nasa nafasa aurensa xan bashi wannan ne dan yarage masa rad'ad'in abinda xaiji ko kad'an bana son akan abin duniya wani yaji haushi na"

Abba kamar yai kwalla ya ce
"shikenan Hindu Allah yai miki albarka Allah ya baki wanda ba xai goranta miki ba"
ta amsa da amin ta fice yabi bayanta da kallo yana girgixa kai.

ta kirashi awaya yaxo suka gaisa cikin walwala da sakin fuska tana duba check d'in ta bashi ya amsa yana mmk ta fad'a masa taji komai ga wannan ta bashi kyauta ta wuce tai tafiyar ta kasa xaman gidan tayi tayo gidan jannat

tana xuwa tasawa jannat kuka ta dad'e tana rarrashin ta sannan ta bata lbrn komai jannat ta girgixa taji kuma dad'i da Allah yasa sukaji hakan
"ina son mahboob lokaci ya k'ure min Allah yabani miji nagari abin ma ni yafara ban tsoro ko wanne ba sa'a ?"
"kiyi hkr Hindu komai daga Allah ne Allah yayi ba maxajen ki bane Allah ya baki nagari"

tadad'e agidan hindu sannan ta tafi tana tafiya jannat takira Abba tafad'a masa hindu da bakinta tace tana son mahboob yaji dad'i yasa musu alvarka

ranara d'aurin auren duka mahboob aka bashi matan sai da aka fara d'aura auren shi hindu sannan aka d'aura dana meenat yaji dad'i sosai sbd yasami abinda yakeso ita kanta hindun tayi mmk dan bata sani ba sai da aka d'aura

anyi shagali anyi bikin al'adu kala kala an kuma kashe nera anyi watsi da ita fatanmu Allah ya basu xaman lafiya haka akayi shagalin bikin jannat na jan tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe.

sati d'aya da bikin bak'i na shirin komawa zahra taxo gidanta suyi ban kwana sbd gobe xasu wuce suna hira Muhammad yaro mai wayau ya girma sosai dan ba inda baya xuwa da k'afarsa yanxu ma rigima yake shi sai an kaisa gidan abokinsa Abba jannat na rarrashinsa kamar k'ara tura sa take ta kira ya khaleel tafad'a masa yace gashi nan xuwa ya kaisa gidan Abban yana dawowa khaleel d'in ya wuce da zahran gidan Abba tai musu sallama bayan ya dawo ya tadda jannat d'in a dalo tana ta murk'usu su bayanta da marar ta na ciwo bai jira komai ba ya sunkuce ta sukaje asibiti ana dubawa aka ga haihuwa ce

cikin daren Allah ya sauketa lafiya ta haifi y'an biyu maxa kyawawa lafiyayyu cikin daren asibitin ya cika da dangi doctors d'in sun so sallamar ta dan dai dare yayi safiya nayi suka sallamesu komawar da zahra batayi ba kenan sai da akaci suna da su itama dai da cikinta 7 months

y'an biyun sunci sunan Dady da Abba Bashir (fawazz) da Adam (sa'ud) anyi shagali kamar na Muhammad fatanmu Allah ya raya y'an biyu.

watan su fawaz da sa'ud uku zahra ta haihu ta haifi d'anta namiji dangi daya suka shirya suka je saudiyya har da su Abba da Dady

ranar suna tana cikin y'an'uwa suna hira taga kiran wayan ya khaleel ta bar wajan hiran ta fito harabar gidan ta xauna suna waya dashi a lallai sai taxo masaukinsu ya ganta dan tun asuba rabon ta dashi rarrashin sa takeyi sbd tasan muddin taje baxai bar tadawo da wuri ba da kyar ta rarrashesa akan ya jirata xata xo ammafa sai da yamma tana gama wayan tayi ajiyar xuciya tana murmushi
wata zazzak'an murya taji tai mata sallama a hankali ta waiwaya kyakkyawar matashiyar mace tagani me kyau sanye cikin abaya tayi rolling d'in kanta da gyalen abayan hannunta rik'e da jaka madaidaiciya kalan stone d'in abayar ta tunda taxo wajan ya d'umi da k'amshin jikinta.

amsa mata sallamar jannat tayi tana mmk ganin tana mmk yasa tayi murmushi ta mik'o mata hannu alamun su gaisa

"sunana JASRA BELLO MOD'IBBO munxo sunan Zahra ne mijinta abokin mijina ne, naga kema y'ar 9ja ce"

murmushi jannat tayi tana tuna sunan tabbas tasan sunan a kano
"sunana JANNAT ADAMU CHED'E"
ware ido jasra tayi cike da mmk tace

"mashaa Allah tabbas nasan sunan nan a Kano na kuma san sunan ahhh...."
tayi dariya bata k'arasa ba dariya itama janna tayi
"...a ina kika san sunan?"

".... awajan Ummee Garkuwa"
tak'ara sa tana kallon jannat
far tayi da ido
"tabbas hakane a novel d'inta Jennifer ko ?"
d'aga kai jasra tayi had'e da xama kusa da ita
"naji dad'in ganinki jannat dan nima ina son ganin Ummee Garkuwa ina son bata labarin kaina ta rubuta kamar yanda tayi naki"

"karki damu zan had'aki da ita "
"naji dad'i kuwa ki bani numb d'inta yanxu in ban ta kura miki ba"
"ba komai babu takwara ga numb d'in 080*********** "

"ngd sosai jannat bari na kirata mu gaisa tun yanxu dan gsky na matsu mu had'u da ita"

murmushi sukaiwa juna jasran ta sunkuyar da kanta tayi dialing number ta shiga ta d'an jima tana ringing sannan aka d'aga

Ummee Garkuwa:"assalamu alaykum"
Jasrah : "waalaikumus salam, dan Allah ina magana da Ummee Garkuwa?"
Ummee Garkuwa:"en itace ya kike?"
Jasrah:"lafiya lau ya jama'a?"
Ummee Garkuwa:"Alhamdulillah"
Jasrah:"na amshi numb d'inki a hannun jannat Adamu ched'e'

Ummee Garkuwa:"masha Allah kina tare da mutanen kirki"
Jasrah: " gaskiya kam hakane na amsa ne dan nabaki labarin kaina da kaina rikitaccen lbr mai ban tausayi ban haushi harma da takaici mai abin mmk da kuma soyayya mai karya xukata"
tak'arasa kamar xatayi kuka

Ummee Garkuwa:"tofah bari na gyara xama kin san mu da kibamu naman d'awisu k'ara ki bamu lbr"
dariya tayi jasrah

Jasrah:"kiyi hkr Ummee lbrn baxaiyiyu awaya ba sai na dawo 16 ga watan MAY in shaa Allah"
b'ata rai Ummin tayi kamar tana ganin ta
Ummee Garkuwa:"tohm shikenan Allah ya kaimu lokacin ngd sosai"
Jasrah:"ni ce da gdy zan kira latter ngd sosai byeee"
ta kashe wayan dai dai lokacin da jannat ta mik'e suka jeru tare suna hira suka shiga cikin gidan sunan.

kwanansu tara suka dawo daga sunan zahra da y'arta taci sunan umma Nabila watansu fawazz da sa'ud goma sha d'aya suna tafiya harda gudu ma dan sunyi wayo Muhammad miskilin yaro komai nashi na babansa sak ranar hindu ta haihu ta haifi namiji tunda ta haihu suke cikin hidima sosai hindu suna xaune lfy da abokiyar xamanta meenat suna mutunta juna sati nayi aka sawa d'an suna Abubakar sadik sun sha shagali sosai abin sai wanda ya gani dady da Abba kam cikin murna da godiyar Allah suke ta ko ina Allah na axurtasu da jikoki haka Umma da Momy dangi ya had'u ya cure sun maida kansu tamkar ciki d'aya sun had'a kansu suna kuma k'aunar junansu d'aya baxaiyi abuba batare da shawarar d'aya ba Alhamdulillah komai yayi yanda akeso sukam sai godiyar Allah hindu na kwance tana bawa d'an sadik nono mai gadin su yai sallama wai wani mutum yana sallama da ita da mmk ta fita wanda tagani ne yasa tak'ara sa da sauri kuka tasa
"Baba"
"naam hindu, Alhamdulillah Allah ngd maka dana ganki ahaka najin dad'in had'uwa da iyayenki da kikayi na kuma ji lbrn komai y'ata haka nakeso talatu Allah ya toni asirinta"
"hakane baba amma ya akayi haka ka fito daga prison ?"
jinjina kai yayi
"shareef alhussain ne ya satoni daga cen akan naxo na taimaka masa mu sato wani diamonds a gidan kayan tarihi na dubai d'in nima nagudo nan nasan bai isa yaxo nan yai min wani abun ba,
na tuba yanxu y'ata ba xan koma ko ina ba ina nan k'asata"
hindu na kuka ta cigaba da bashi lbr
nan da nan ta bashi lbrn komai ta kuma kira Abba tasanar dashi da kansa Abban yaxo suka tafi tare sbd ya mutunta shi kamar yanda yaiwa sauran da suka reni sauran y'ay'ansa.

agajiye ta dawo daga kasuwa falo tasa meshi shida Muhammad daya ke baccin agefan sa y'ar rainonta ta ajjiye fawazz ita ma ta ajjiye sa'ud da duk sukayi bacci tana k'ok'arin shiga ciki ya khaleel ya janyota jikinsa hannunsa kan cikinta yana shafawa yana kallonta zaro ido tayi tana kallon sa d'aga mata gira yayi
"yau zanyi wata ajiyar ta musamman dan 3ple zan ajjiye"

ware ido tayi sosai tana kallonsa dariya tayi ta xame kanta a hnkl
"ba ruwana Ummee Garkuwa tana jinka"
tab'e bakinsa yayi
"ina ruwana da Ummee Garkuwa bata son ke matata bace ? ki shirya beautyna yau fa sai na miki kyakkyawar ajiya ta musamman!"

TAMMAT BI HAMDULLAH

abin da yawa ina gaishe da kowa da kowa musamman masu bibiyar Jennifer da kuma way'anda suka bani shawarwari ngd sosai sai mun had'u awani novel d'in
*Ummee Garkuwa*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment