Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka kallesu hjy murja ta girgixa kai tana murmushi aranta tace "yara kamar su cinye kansu dan soyayya"
kai tsaye wani b'angare tayi dashi na gidan d'aki na musamman ta kaishi suna shiga ya janyota jikinsa suna dariya cikin murna tace,
"nida man nasani jikina ya bani kana kusa dani"
shafa cikinta yayi ya ware ido
"nifa ajiyata naxo na kula da ita bazan iya xama bana shafa lafiyar ajiya ta ba"
wata iriyar dariya tayi.
"ni kuma fa wato ma ajiyar ka kabiyo naga alamar kafi son ajiyar nan taka dani"
ta fad'a tana k'ok'arin ture shi jikinta,
"ah beautyna kada kiyi kishi da ajiyata"
ta tabe fuska had'e da turo baki,
"ba dole ba tunda kafi sonta dani"
dariya ta bashi dan yana son shagwabar ta.
"kin san ke ta musamman ce awajena ajiya ta ma ta dabance,
fad'amin banbanci tsakanin ta musamman da kuma na daban "
far tayi da ido.
dariya yayi
"ina sonku duka beautyna"
ya sunkuya dai dai saitin cikinta ya d'age rigarta da sauri ya d'ago kai yana kallonta
"beautyna kinga ajiyata ta fara girma ko?"
shafa cikin nata tayi.
"ni ban gani ba"
d'agowa yayi ya shafa wuyanta daya ke kyalli da hasken fatarta
"zaki min bayani anjima"
ta xame jikinta
"bari na kawo maka breakfast"
dawo da ita yayi jikinsa,
"noh ! ni da wani abu daban nakeso nafara breakfast dashi"
tsura masa ido tayi ta shafa sajensa.
yana shirin mgn ya ji bakin shi cikin nata ta sha cikin yanayi najan hnkl tuni ta rud'ashi ya k'ank'ameta yana maida mata martani cikin rikicewa dan baiyi tunanin xata iya hakanba

kafin wani lokaci sun rikita kansu tuni lbr yasha banban da sauri ta yakice kanta ya kuma dawo da ita ta kwace da kyar tayi nesa dashi.
"kayi hkr ya khaleel kayi breakfast ka huta tukunna"
idonshi a rine yake kallonta
da kyar ya iya d'aga kansa.
"ina sonki beautyna"
itama yanayinta asauye tace.
"ina sonka sosai ya khaleel"
ta fice daga d'akin idonsu akan juna.

tun aranar suka tafi wajan siyayyarsu tare suka tafi da ya khaleel yana lik'e da ita motsi kad'an sai yace"ki kula fa kin san akwai ajiyata a jikinki"
murmushi kawai takeyi sai dare suka dawo a d'akin shi ta kwana hannunshi rungume da cikinta wai baxai iya kwanciya shi kad'ai batare da hannunshi na tab'a lafiyar ajiyarshi ba

kwanansu biyu yau suna shirin gobe xasu wuce india dan dubai ne last inda xasuje.

tana tashi taga 9 miss cal d'in ya khaleel ta d'an xaro ido sam tamanta da wayar na silent ta kira wayar tajita akashe ta ajjiye ta nufi b'angarensa a kulle ta tarar da k'ofar gabanta ya fad'i tabbas tafi kowa sanin ya khaleel bai son ya kira waya ak'i d'agawa jikinta asanyaye ta dawo falo tana tunanin ko ina yaje?


wasa wasa har yamma ya khaleel shiru tun tana iya daurewa har ta kasa abinci ma kasa cinsa tayi suna shirye shirye tana gefe tayi ta gumi tana kallon wayar ta lokaci xuwa lokaci tana kiran numb d'insa
duk ta jita akashe ji takeyi kamar ta fasa ihu dan tuk'ik'in ba k'inciki.
duk sun kula da yanayinta tun safe kasa daurewa hjy murja tayi sai da tambayeta
"jannat me ya farune ?"
kamar zatayi kuka tace,
"ya khaleel tun safe bai shigo ba kuma baya b'angarensa na kira wayarshi a kashe"
xuba mata ido sukayi sulthana tace,
"toh ina ya tafi"?
girgixa kai jannat tayi
rubayya tace
"ko ya ce miki xaije wani wajan?"
girgixa kai ta kuma yi
zahra tace,
"ku kwantar da hnklinku baxai b'ata ba fa ina ga wani wajen ya tafi"
jidda tace,
"ikon Allah gsky da wuya ya khaleel ya kashe waya"
hajiya murja data ke binsu da ido ta dawo kan jannat da idonta yake kan waya,
"jannat kinsa fa namijine dole xaiyi sha'awar xuwa wani wajan ki kwantar da hnklinki xai dawo kinji"
kai ta d'aga mata


har dare kusan k'arfe goma shiru bai dawo ba jannat kasa daurewa tayi tasa kuka sosai breakfast kawai tayi bata ci lunch da dinner ba
ba yadda hjy murja batayi da ita akan taci abinci tak'i ci sai kuka.

sunyi kiran duniyan nan wayarshi akashe. xugum sukayi a falo suna rarrashinta.

muryarshi asanyaye yai sallama suka xuba masa ido.

jikinsa sanye cikin jessy kayan ball farare hannunshi rik'e da jaka k'arama ta kayan da ya fita dasu cikin k'asaita yake tafiya cike da jin k'arfi tamkar matashin sadauki.
dariya sulthana tayi tace,

"oyoyo majunun lailah"
kallonta yayi ya kauda kai.
dariya sukayi dukansu hajiya murja tace,

"wannan ai sunfi majnunun laila k'araso nan ya khaleel kayi laifi"

fuskarshi asake ya k'araso ya xauna kusa da jannat da kanta yake a b'oye jikin cinyoyinta.

sulthana tai karaf tace,
"haba majnun meyasa kabar lailanka cikin rashin sanin inda kake?"
wani kallo yai mata.
kama bakinta tayi,
"aw ashe fa tsoronka nakeji kai d'inne wllh idan ka b'ata rai tamkar sadauki awajen ya'ki umma ni dai na gudu dan wllh tsoron idon ya khaleel nake" tana tafiya gudu gudu tana maganar.

dariya sukayi suna kallonta sum sum
suma suka bi bayanta dan sunga fuskar tashi ba wasa.
hjy murja ta kalleshi tana dariya
"majnun yau kayi laifi ka tafi ka bar laila cikin wani yanayi,
ka ganta nan breakfast kawai tayi yanxu ta gama rusa mana kukan ita ya khaleel,
tun safe sai yanxu?
gata nan ka rarrashi kayar ka dan kai kad'ai ne xaka iya sauke wannan fushin ni dai na bi bayan y'ay'ana"
ta mik'e tayi b'angaren su.
shiru ba wanda yace wa kowa komai shi kam tunaninsa ta ina xai fara lallashinta?

ita kuma tunaninta ko har yanxu fishi yakeyi sbd bata d'aga wayanshi ba?

yana k'ok'arin yi mata mgn
cikin sanyin murya tace,
"kayi hkr nasan kaimin wannan horon ne sbd ban d'aga wayanka ba."
katseta yayi ta matsowa kusa da ita kamar xai shiga cikinta.
yasa hannu ya d'ago fuskarta baiyi tunanin xatayi saurin bashi hkr ba jannat ta wuce tunanin shi wajan hkr da saukar da kai akansa
"wannan salon naki yana sani jinki tamkar kece ni,
ngd wa Allah daya bani matar da baxan wahala akanta ba duk abinda nakeso kin karance shi kin kuma iya shi,
na fahimci biyayyarki pure ce original kina yin komai ne sbd biyayya ga umarnin Allah da biyayya ga mijinki wacce hakan ne xai kaiki samin rahama daga Allah,
ngd wa Allah da yai min baiwar samun mace irinki mai hikima mai tsoron Allah,
ni yakamata na baki hkr kafin nayi mgn kin rigani,
wannan ya isa yasa naji bana son kasancewa da kowacce mace aduniya irinki,
"kiyi hkr beautyna ban kyauta ba, nasani amma ba zan kuma ba"
ya k'arasa had'e da rungomata jikinshi,
ya fi 30 mints yana rarrashinta had'e da wasu maganganu masu dad'i haka yai k'asa da kanshi wajan lallashinta bai barta ba sai daya ga tana dariya.

abinda yakeso kenan yaga dariyarta tuni ya saki shima
"meyasa kika wahalar min da kanki da kuma ajiyata?"
murgud'a baki tayi,
"bayan kai ka wahalar damu"
kiss yaiwa kumatun ta.
"ai min afuwa tashi muje na baku abinci kuci na kuma k'ara baku hkr"
ya mik'ar da ita tayi luu xata fad'i ya rik'eta cak ya d'auketa yai b'angarensa da ita.

abinci ya bata taci yana bata yana k'ara rarrashinta har taci ta k'oshi sai da tagaji da rarrashin ta turo baki,
"nifa ya khaleel nace maka na hkr"
"toh bari naji ajiyata ma ta hkr dan na san fushin har da ita,
itama fushin take dani"
kallonshi kawai tayi dan ya daina bata mmk
rigar ta ya kama yana k'ok'arin cirewa.
xaro ido tayi
"menene haka?"
kallonta yayi
"ina son bawa ajiyata hkr na kuma k'are mata kallo tunda ga sama har k'asa"
kafin tayi mgn har ya k'arasa cire ta duka

washegari suka bar Italy
india suka wuce nan ma kwanan su uku suka dawo Dubai anan sukai kwana biyu jannat kam tasha tarairaya da kulawa ko agaban waye baya shayin kula da ita ba kuma ya barin tayi nesa dashi ko tafiya xasuyi motar su daban idan suka sauka hannunshi cikin nata wai yana taimaka mata tunda yanxu ba ita kad'ai bace akwai ajiyarsa.
itakam mmkin ta sam tarasa gane inda ajiyar ta shi take.

bayan sun dawo aka kawo lefensu duka kowacce jakar akwati 36 kaya masu kyauta nagani na fad'a.

k'ayyade k'ayatuwar kayan wani sabon babine na daban ka fasaltasu da kanka. Alhaji Adam ched'e ne ya had'a lefen sbd yace shine tukwicinsa amatsayin shi na uban angwaye.

kwana uku da dawowarsu akafara shirye shiryen biki an tsara komai da irin hidomin da xa ayi day one ranar farko ta hidimar itace wacce anty safiyya ta shirya k'anwar momy ranar barebari sbd su barebari ne suna kiran ranar da:
*Wushe-Wushe* shine traditional day nasu wanda amare da k'wayensu xasuyi shiga irinta kanuri da mazajensu xa'a k'awata wajan da makad'an gargajiya irin nasu achashe da yiwa wajan ado da k'amshin turare mai dad'in gsk aci abinci na gargaji biski da burabusko da *banderu* waje yayi kyau sosai dan anan cikin gidan sukayi.
kowa ka gani yana cikin nishad'i da annushuwa gida yacika dam da dangin ched'e kyawawan yanmata dan gin hjy Nabila ma ba abarsu abaya ba ga dangin dady suma datasu gudunmawar wannan yana wane wannan sunyi rawa da lik'a manyan daloli.

motsi kad'an jannat tayi yana mata mitar tabi a hnkl bai son ta matsawa awajiyar shi.

yana lik'e da ita kamar cingam su sulthana an sami abinda ake so da sun faki idonsa su tsokane ta wai mai cingam ko suce majnu nun laila su kansu iyayen sun jinjina shak'uwa da soyayyar jannat da khaleel momy har mamakin sauyawar shi take duk irin miskilancin sa lallai ta yadda mace na sauyawa mijinta rayuwa.

*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍


105&106
*Ummee Garkuwa*
day 2 shine ched'e day wanda duk wata y'ar danginsu in ta tashi aure suna wannan al'adar ta filani ango da amarya suna shiga irin ta amaren filani haka aka yi abubuwa na al'adar filani aka sha nono aka yanka shanu masu yawan gaske suka kira masu wasannin al'adun filani akayi wasa abin gwanin ban sha'awa akayi lafiya aka gama lafi

3 shine akayi agidan sarki goggo fulani ce tace suxo nan suyi dan suma duk aka tashi bikin y'ar gidan sai sunyi wannan budirin na kamun amarya wannan ne babu angwaye ya khaleel da kyar ya bar jannat wai bai son mutane su jagwal gwala masa ajiyarsa basu dawo gida ba sai dare.

wanka sukayi suka xauna jannat tace,
"wannan day day d'infa ya isheni"
d'an k'aramin tsaki sulthana tayi
"ni kaina na gaji sosai wllh nagaji"

hindu tace,
"gobe xamu huta sai kuma jibi"
zahra da take a kwance tace,
" naji dad'in hutun nan na gobe dan ni kaina nagaji daurewa kawai nake"
rubayya ta girgixa kai,
"na jinjinawa amare haka kowacce amarya take shan wahala da hidima?"

wayar sulthana tai k'ara sai da tayi ajiyar xuciya ta duba screen d'in wayar d'an k'aramin murmushi tayi ta d'aga
"ok toh ina xuwa"
ta kashe wayan tana k'ok'arin mik'ewa jidda tace,
"oh sarkin tsokana yanxu fa kikaje kin gaji amma dake kece lailan majnun kin manta da gajiyar xaki tafi wajan ya haisam"
dariya sulthana tayi

ta nuna jannat
"kinga laila ya khaleel shine majnun ni babu ruwana kin san ya haisam in bai ganni ba baya iya munshari"
dariya sukayi rubayya tace
"wato munsharine baxai yiba ba bacci ba?"
kafin ta fita wayar jannat tayi k'ara lokaci d'aya suka kalli wayar suka kwashe da dariya sulthana tana dai dai k'ofa tace
"oyoyo ga majnun taso muje dan nasan kiranki yake na jinjinawa ranar yau jannat ta kwashe rabin yini ba tare da ya khaleel ba,
yanxu haka in kuka bibiya d'ank'aramin xaxxab'i ya kamashi na rashin ganin jannat d'insa"

girgixa kai jannat tayi ta mik'e bata tanka musu ba har tafice daga d'akin tasan halinsu sarai kan wannan lik'ewar daya khaleel yake mata suka maida ita kakarsu kullum cikin tsokana.

washegari ba ayi komai ba suna hutu amma gidan d'ank'are yake da mutane ana hidimar bikin ranar kam amare da angwaye suna cen wani b'angare na gidan suna hira cikin nishad'i prince A.k Garkuwa ne yace wai yau yinin angwaye da amare dan haka yini xasuyi suna hira cike da farin ciki amaren suke tsokanar sa su basu tab'a jin akwai yinin amarya da ango.

jidda tana gefe ranta ab'ace yanayinta sauran amaren suka kalla jannat ta kasa daurewa tace
"anty jidda menene? ki saki ranki mana"
ajiyar xuciya jiddan tayi

"jannat kalli Ibrahim"
sulthana tace "me danjuman yayi?"
d'an k'aramin tsaki taja
"kwalliyar shi xaku kalla"
ware ido sukayi suna kallonshi yasha shadda irin ta jikin angwayen yayi kyau ya murmure sbd bai son ya b'atawa jiddan sa rai ko mgn ba yayi sunyi mmkin yanda lokaci d'aya ya koma d'angayu haka da wuri.
zahra ta girgixa kai
"mungani Ibrahim ya yi kyau sosai mashaa Allah kalli yanda yake kyalli "
tsaki jiddan tayi ak'ufule tace,
"baku ga glass d'in daya saka bane? wannan uban glass kamar na kutare haba"

rubayya ta tab'e baki "ni banga aibun glass d'in sa ba kin fiya maida k'urji ciwo,
idan bkyaso kice ya cire mana"

test ta tura masa,
yana gani da sauri ya cire glass d'in yana kusa da mahboob komai nasa irin na mahboob haka sukayi hirar su cikin nishad'i da farin ciki

washegari gari akayi lunch aka kira masu kid'an kwarya aka cashe sosai gwanin ban sha'awa

ranar juma'a aka d'aura musu aure kan sadaki dubu d'ari shida shida dan dady cewa yayi sauk'ak'a sadaki shine albarkar aure ubangiji Allah ya albarkaci wannan auren

ranar aka kira matashiyar malamar nan mai fasaha da ilmin addini malama *Maryam Garkuwa*
dan taiwa amare wa'axi akan aure har da ma iyaye da y'anmata.

tafara jawabin ta cikin muryarta mai sanyi da jan hankalin mai sauraronta :
assalamu alaikum warahmatullahi wabara katuhu.

nan da nan waje yai tsit sbd muryarta ta tayi tasiri wajan kunnuwansu suka amsa tai addu'ar bud'e taro tafara jawabin ta:
"wannan wa'axi ne akan aure da kuma halin da rayuwar mu take ciki wato mu mata,
Alhmdllh shi aure sunnace ta manxon Allah annabinmu annabi muhammad sallallahu alayhi wasallam,

da yawan y'anuwana mata kuna d'aukan aure kamar yanda kuke kallo a film ko kuke karantawa a novel,
kada kubari wannan yai tasiri acikin xuciyoyinku Aure bauta ne bautar Allah subhanahu wata'ala sannan xaman lafiyan sa shine *Biyayya*
dayawanku kun san wannan kalmar ta iyaye da kakanni wato *Yi nayi* *bari na bari*
abaki kam akwai sauk'in fad'a wajan aikatata akwai aiki babba wannan kalmar kakannin mu suke amfani da ita wajan yiwa kowacce mace nasiha musammn a dai dai wannan lokacin,
shin yaya biyayya take ? ta yaya xaki xama mace mai biyayya?

hanyoyi ne da yawa ga kad'an daga ciki:

tun farko kisa ranki cewa aljannar ki kike nema xakiyi komai dan Allah sannan ki kauda kanki ki kuma maida mijinki wani babban mutum mai k'ima da daraja
awajenki
ki bashi kwarjini awajanki
kiyaye abubuwan da suka shafeshi sannan kiyaye aikata abinda baya so idan ya umarce ki da abu idan har ba sab'awa Allah bane ki gaggauta yinsa

kada kiyi tunanin ai mijinki na sonki kuma mai hkr ne xaki takashi son ranki baxai damu ba,
idan ya kyaleki kina ganin Allah xai barki?
waya fad'a miki soyayya tana d'orewa babu kyautatawa juna?

duk irin son dayake miki muddin kina masa abinda kika ga dama wllh sunanki sorry koda baya miki mgn k'imarki tana raguwa awajensa haka baki da kwarjini ko misk'ala xarratin asalima kallonki yake mara tarbiyya mara ilmi duk kuwa yawan ilimin naki ya xama abanxa tunda baxaki masa biyayya ba bakya girmamashi balle in ya hanaki ki hanu

idan kuma kina tak'ama da kyau ke kyakkyawace dan haka bari na juya shi son raina ai ko yasakeni baxan rasa mijin aure ba,
waya fad'a miki xaki cuci mijinki Allah ya barki ?
hak'k'insa ya d'inka bibiyarki kenan duk inda kikai aure baxaki tab'a jin dad'in mijin naki ba
ak'arshe ma haka xai ta axabtar dake duk da kyannaki
sbd hak'k'in waccen mijinnaki da kika axabtar wanda kika raina bakya masa biyayya na bibiyarki,

mata mu girmama aure mu girmama maxajenmu muyi musu biyayya dan shi xai kaimu ga samun rahamar ubangiji kada kiyi tunanin kin karanta novel kinga yanda mijin yake tsananin son matarsa take takashi tana wulak'anta shi amma yana bibiye da ita dan haka nima bari na gwada nawa mijin inga yana sona,
ikon Allah shin kin manta tunanin wata kika karanta ?
k'irk'irar wata ne kinsan ya tsakninta wacce ta rubuta da nata mijin ?
tayaya xaki had'a rayuwar ki da rayuwar novel? rayuwar ki daban wacce kika karanta daban kiyi k'ok'arin d'aukan abu mai kyau kibar wanda kikasan hnkl baxai d'auka ba

matsayinki na mace wacce xata xauna a k'arkashin wani ki maida kanki mai sauk'in kai mara kafiya mai jin tsoron b'acin ran mijinta

babu abin kunyar da yawuce ki maida mijinki tamkar d'anki tayaya xakiyi rayuwa ke kike juya wanda ya dace ya juyaki ? kina ganin idan kina juya mijinki rayuwa kike mai kyau? ba kya tunanin wanne irin kallo y'ay'anki xasuyi miki ? kina da abinda xaki cewa ubangjinki ? subhanallah !

idan kikayi sake kina ganin kin fi k'arfin ya juyaki xuwa xaiyi ya auro wata my b ma wacce xai auro bata kaiki ba kinfita komai kin fita wayewa kinfita iya girki kinfita iya kula da shinfid'a kin fita kyau

bai hana ta kwace miki miji sbd ta fiki biyayya ta fiki tsoron b'acin ransa tafiki sanin darajarsa tasan sama da ita yake dole ta yi masa biyayya ta kyautata masa

ke kuma kije kiyita jin kanki wata kiyi ta jan class bak'in ciki yai miki illa
sannan kuma Allah baya tare da ke tunda yace kiyi kin k'i kiyi

biyayyar miji Allah ne yace ayi yaxama dole tiles kiyi wa mijinki biyayya kin k'i yi bakya tare da Allah bakya tare da mala'ikun rahama shikenan komai xai cab'e miki kirasa gane kanki ki kuma rasa gane kan mijinki

muji tsoron Allah muyiwa maxajanmu biyayya koda shi yana cutarki ki barshi da Allah ki dage da yi muku addu'a kina mishi addu'ar Allah ya shirya miki shi,
in shaa Allah Allah na jinki yana kuma ganin duk irin xaluncin dayake miki xai kuma saka miki dan Allah baya barin hak'k'in wani akan wani idan kina son ki juya mijinki juya wa ta hankali da ilmi to kiyi masa biyayya ki kyautata mu'amalarki ki tsabtace jikinki ki gyara kanki sannan ki dogara ga Allah a kullum ki d'ink'a neman d'auki daga Allah inshaa Allah tunda kina tare da Allah shima ubangiji yana tare da ke.
sai mgn akan gyara:


*maganin ni'ima*
hmmm subhanallah ! y'ar'uwa kin san kanki kuwa ? kin san illar shan maganin mata ? kada kiyi tunanin shan maganin mata shike k'ara ni'ima bari in baku wani misali:

kina shan kunu cup d'aya arana idan kika sha xaki k'oshi xakuma ki dad'e bakiji yunwa ba, wataran sbd jin dad'i kin d'auko kunun nan naki cup d'aya xaki sha sai kika ga bari ki k'ara masa ruwa yanda xaiyi afki sai kika xuba masa ruwa cup biyu ya xama cup 3 kinga kunun nan xai tsinke ya koma gashi nan dai amma fa yayi afki ki ka d'ibi cup d'ayan nan da kike sha kika sha ba ki dad'e da sha ba kika ji yunwa sai kika k'ara shan cup d'aya kika ji kin k'oshi ba'a dad'e ba kika kuma jin yunwa kika shanye ragowar sauran cup d'aya take kika ji kin k'oshi ba'a jima still kikaji wunya,
ranki dole ya b'aci dan dole ki nemi wani abun ki kuma ci tunda wannan yawan nashi baisa ya gamsar dake ba duk inda abinci yake dole ki nema kici inba haka ba kuma yunwa tai miki lahani

toh haka maganin mata yake ajikin mu idan kika sha bafa wata ni'imar yake k'ara miki ba a'ah takin nan dai wacce Allah ya baki ita

ita yake tsinkarwa tayi ruwa ta taho da gudin tsiya amma fa baxata tab'a gamsar da mai gidanki ba yanda kika sha wannan kunun kika k'oshi lokacin da kika sha daga baya kikaji yunwa shima haka xai kasance dashi ba shi da gamsarwa ko kad'an ko ya gamsar to na iya wannan lokacin ne baxa a dad'e ba xaiji sai a hnkl

ko yaya amfison ki xauna da natural test d'in da Allah ya halicceki da shi dan shi wannan natural d'in shine yake gamsarwa domin shine na ainahin ba fake ba

akwai maganin da suke gyara wajen sune kayan marmari su kam gina jikinki xasuyi sannan su tsatstsafo da test d'inki da kuma wasu magangunan way'an da suke marasa cutarwa

shi kanshi maganin ba wai ki yi ta shanshi ko yaushe ba ki d'ink'a amfani dashi sama sama sbd anfison original pure test d'in da Allah ya halicceki da ita shiyasa xakiga duk yanda kike gyara jikinki da maganin mata masu tsada bai hana mijinki yai miki kishiya idan akayi sa'a

batayi wa kanta illa da shaye shaye ko tushe tushe ba sai kiga hnklinshi ya koma kanta duk da ke d'in kinsha maganin mata kina liking dan ni'ima bai hana kiga yana rawar k'afa akan wata,

sbd yafi samun abinda yake nema agun wancen ke kam sai yawa amma bamai gamsarwa bane

kwanaki naga wani posting dayake ta yawo a social net d'in nan wai mijinta ya mutu daren auren ta sbd tasha maganin mata,
suna ganin ko ni'imar ce tayi yawa shiyasa yakasa hkr ahaka har ya mutu ko kad'an ba haka abin yake ba ta xama mai yawane ba gamsarwa bai samu abinda yakeso ba dole ya k'i hkr

mu taimaki kanmu mu gujewa shaye shayen magangunan nan mubar kanmu da wanda Allah ya haliccemu idan ma xamu k'ara duk da ance duk kyanka ka k'ara da wanka to musan wanda xamu sha .

babu babbar illahr ma irin matsi tushe tushe kinsan me wannnan tushe tushen yake haifarwa ?
infection
PID
daga nan kuma sai cancer

shiyasa xakiga kina fama da infection kiyi ta magani ba sauk'i tayaya xakiji sauk'i alhali kina wa kanki babbar illah kin damu wajan da ba ason ki fiya damunsa ?

kin matsa wannan kin matsa wancen dole kina so sai kin birge mai house ki kashe kanki ki birge mijinki

akwai hanyoyi da dama da xaki bi wajan birge mijinki ba sai kin cusa wani abu agabanki ba kisha nasha

kada ki yadda da maganin matsi ki sha nasha kawai dan wannan matsin yafi komai masifa yafi komai illah yafi komai illahta mace kiyi hkr da wannan matsin ko shi misk Aisha radiyallahu anha a wata sau d'aya take amfani dashi dan ta tsabtace wannan k'arnin na jinin haila

ke kuma kullum sai kinyi amfani dashi ko kuma bayan kwana biyu

wannan wajan baya buk'atar wani k'amshi ko wanne irine ki barshi yanda Allah ya halicceshi muddin xaki tsaftace shi to wllh kin huta

sai tsarki da viginal soap da yawa wasu matan suna magana akan tayaya xa'ace su daina wanke wajan da sabulu to ya xasuyi da dattin wajan?

yaxama dole ki daina amfani da ruwan sanyi idan baxaki iya dafawa ba ki tafasa da yawa da safe ki juye a flask inkika tashi amfani dashi ki d'iba ki sirka da kinje alwala dole dai xakiyi tsarki kafin kiyi tsarkin ki wanke lokon da kike ganin xaiyi datti ki wankeshi tass da wannan ruwan dumin sannan kiyi tsarki .

arana kin wanke wajan sau biyar duk kika tashi tsarkin alwala ki wankeshi tayaya xaiyi datti?
ko ke kike wanka sau biyar arana ya xaki koma ?

shima wannan wajan haka yakamata ki kula dashi ba yadda xa'ay datti yasamu mafaka dole wajan xai kasance atsabtace
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍


107&108
*Ummee Garkuwa*
ki kiyaye kanki kafin lokaci dana sani ki kare lafiyar jikinki da kanki ubangiji Allah yasa mudace.

sai kula da uwar miji da dangin mijin:
duk dana san kun sani bari na tuna muku,
kin san darajarar da Allah ya bawa uwa ??
kinsani son xuciya ne ya mantardamu kada ki kuskura ki had'a kanki da uwar mijinki sbd tafiki nesa ba kusa ba
matsayinku ma ba d'aya yake ba

kowanne mahuluk'i ba sai mijinki ba anfison ka kula da iyayenka fiye da kowa.
musamman uwa duk da cewa kowa matsayinsa daban

kula da uwa dolene rashin kula da ita kuma tab'ewa ne asalin tab'ewa mu d'auko hadisan nan na cikin riyadussalihin akwai dogon hadisi wanda yake sananne agun kowa mutanen da suka shiga kogo dutse ya rufe dasu d'aya daga cikinsu yai tawassali da wannan y'ayansa da matansa da iyayensa duk suna jin yunwa da ya samo abinda xasu ci duk da yabar y'ay'ansa k'anana suna kukan yunwa haka ya juya ya fara kaiwa iyayensa sai da sukaci suka k'oshi sannan ya kaiwa

Please Login or Register in order to submit comment