You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
haka suma mahaukata suna da ita."
Wayyo Allah na, na faɗa a raina da sauri na fara ƙoƙarin kwace kaina. Amma ina haka ya danne ni, tare da niman kwayar idanuna.
"Hammah don Allah tashi kaji, ya hakuri ka tashi bani da karfi irin naka."
Kamar wanda yaji abinda na faɗa mishi sai gani nayi ya tashi a hankali, tare da janyewa daga jikina, da sauri na dira a gadon ina niman hanyar fita waje, ai kuwa ya biyo Ni.
Allah ya hada ni da bindi, domin duk inda nasaka kafa yana biye dani, har niman faduwa yaƙe idan yana bin bayana, haka na dafa mishi abincin duk da babu dad'i domin har yanzun ban iya girki ba, kuma dai sai a hankali baki daya rayuwana ban tab'a shiga cikin al'amarin girkin Inna sosai ba, ina yi amma ba wai ina nufin na iya bane. A'a Kawai ina yi ne sabida kar na mutu da yunwa.
Ina juye mishi na zuba nawa na fara ci, kamar yadda nake ci. Rike hannun shi nayi sabida nashi cin a haukace ake yinta, ina ci ina nuna mishi. Haka shima yake ci a hankali yana kallona.
Har na gama ci na sha ruwa sai cin nashi yaƙe, kuma abin da j fahimta shine bai san koshi ba, yayi ta durawa kamar yaro karami,dauke filet din nayi, wani irin narke min yayi da fuska sai da tsigar jikina ya mike min, ina ganin kwayar idanun shi cike da wani irin maiko, yana tara kwalla.
Murmushin jin dadi nayi tare da cewa.
"Kaga idan kaci kadan sai kasha ruwa, sai ka bar inda iska zai shiga, fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, a raba ciki kashi uku daya abinci daya ruwa daya kuma iskar da zaka shaka, idan kuma ka nace sai ka cika cikin ka ina zaka samu inda zaka sha ruwa?"
Kura min ido yayi yana me lashe bakin shi pink dashi, kurawa bakin idanu nayi gasu da wani irin fadi dai dai misali. Ga gashin bakin da ya zaga bakin, sai karan hancin shi, dara daran idanun shi masu matukar kyau da haske.
Mik'ewa nayi zan tafi ya riko hannuna, juyawa nayi ina kallon shi.
"Kana son wani abu ne?"
Shiru yayi yana kallona, a hankali na janye hannuna daga nashi. Ina barin kitchen yana biyo ni. Da sauri na fice kamar dama haka yake jira, sai ji nayi ya fad'i a bayana nima na fadi, ina jin wani irin yanayi a jikina, juyawa nayi na ina kallon shi, sai zare ido yaƙe.
"Tashi a kaina babu kyau kaji" kamar wanda ya san ma'anar haka ya mike da sauri, yana me d'agani. Kafin na Fahimci nufin shi ya dauke ni cak. Ya wuce dani sama, yana zuwa bakin kofar ya kwala Ni da kasa ji kake timmmm. Yayi wucewar shi cikin dakin abinshi.
"Dalla dube shi basamude a gurin zaka karya min k'uguna."
Na fada ina jin kwalla a cikin idanuna. Ganin ban taso ba ya kuma juyowa zai sintume ni da sauri na tashi ina zare idanu.
"Yanzun ka makani da kasa kace zaka kuma daukata ai ko daga birnin mahaukata irinka nake na zan yarda ba balle daga birnin masu hankali na fito."
Na fada ina mishi mugun kallo, tsayawa yayi.
"Kuma ka bar kallona katon kawai"
Da sauri ya sunkuyar da kanshi, karasawa nayi gaban shi, tare da tsagalgale shi da masifa, ina yi da baƙi, hannun nayi, wato d'ago kai yayi tare da kallon bakina. Sannan ya fashe da kuka. Zaro idanu nayi ina kallon shi.
"Toh kayi hakuri" na fada mishi ina mi d'age kafana ina share mishi kwallar da yaƙe, murmushi yayi tare da kai hannun shi kan hanci na, yaja da karfi zunzurutun mugunta.
"Auchewww! Kaga mugunta sake min hancina.....
*_🤣🤣🤣🤣🤣 Mahaukaci kenan, sorry wallahi mun fasa Chakwakiyyar rashin wutar lantarki 🤣🤣🤣 Wallahi sai a hankali domin kuwa ban san iya adadin lokacin da zamu dauka kafin mu samu wutar ba, so please zaku ji Ni shiru idan kunga update toh wallahi mun sami wuta ne idan baku gani ba sorry nagode sosai da ta'aziyar da kuka min Allah Yasaka da Alkhairi nagode sosai_*
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1099088650?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4lwvUq4CDNgGO6G8hSqWOpKF0xTz1GVp6y7Sxeme%2Fg5OCwGdT5AJbfyarf93zolA7FBbhl2FOh%2FpFU0pdrB84Lq2xdZkHArH%2Bvs7uiWokSFzxRJ27Z5Ikm4Ezg7evEig
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA SHA BIYAR.
"Sake min hancina!" Na maza na kwace kaina a hannun shi ina lailaya hancin nawa, kamar zanyi kuka. Harara shi nayi tare da cewa.
"Maza zauna a nan na shiga ban daki na yi wanka." Na nuna mishi inda zai zauna na shiga ban dakin.
Sai da na shirya sannan na fito, na same shi yana zaune kwayam.
"Kayi hakuri kaji na Barka kai ɗaya a daki."
Bai kula Ni ba, kamar yadda ban saka rai zai amsa ba, haka na cigaba da uzurin gabana, ban kuma bin takai shi ba, domin abubuwa da zanyi na maganin shi yana dayawa, dan haka na shiga haɗawa ina kaiwa ban daki nasaka shi ya cire kayan shima da kokuwa, haka na samu ta cire na fito na kira Hammah Malik yazo yayi mishi wanka Tunda suka fara yaƙe rawan sanyi.
Har suka gama ya fito, na shafa mishi addu'o'in, sannan ya kwanta, ban yi tsammanin zai yi barci haka ba, sai gashi yayi dan haka ma na fita na barshi a dakin nayi sallah, ina idarwa na kuma leko shi, ina dawowa na samu bai farka na, dama Baba ya gaya min zai ta yawan barci.
***
Kasa zama yayi ya kasa tsayuwa. Kallon Mutallab yayi sannan yace mishi.
"Kasan me? Ba zan iya boye maka abinda yake raina ba, amma wallahi ina masifar kaunar Almamoon" ya faɗa a sanyayye, yana kallon yadda Mutallab ya sake baki, mik'ewa yayi zai fita Ansar ya riko hannun shi.
"Don Allah saurarre ni mana" fauce hannun shi yayi yana zare mishi ido.
"Shika min hannuna, da alamu ka haukace? Ba banza aka yi ta muku kallon masu soyayyar jinsi ba, ashe da gaske ne soyayyar jinsin kake ina zaka kai..."
"Dalla ka min shiru, ka bude banzan bakin ka sai maganar banza kake yaron nan mata maza ne!" Ya fada da karfi, zaro idanu Mutallab yayi tare da had'iye yawun.
"Kasan me yasa na gaya maka? Saboda ina son Yaron ne kuma zan taimaka mishi ayi mishi aikin ya tsaya a mace, wallahi ina masifar kaunar shi. Please my Friend kai ɗaya ne zaka taimaka min shi yasa na maka maganar please"
Ajiyar zuciya yayi yana kallon shi, Kafin yace mishi.
"Ban san me zan ce maka ba, amma na tausaya maka. Kuma idan na boye maka yadda rayuwa take yana da hatsari, idan yaron nan yana son ganin shi a mace falillahamdu idan kuma ya fison ganin kanshi a matsayin mata maza TOH karka tirsassa mishi ayi abin da zai saka kowa damuwa."
Riko hannun shi yayi sannan ya ce mishi.
"Na sani, amma abin mafi alkhairi shine a dawo dashi jinsin da ya fi karfi idan aka ce lallai sai an jira ra'ayin shi ba zai yarda ba." Shiru yayi na wani lokaci kafin ya cigaba da cewa.
"Tukun kasan inda yaron nan yaƙe? Kasan a inda yake rayuwa? Yana tare da dan primer minister ne, kuma abin takaicin tunda yagan shi ya makale mishi.
Wallahi ina tsoron kar yaje a lalata goben shi! Ina tsoron kar abin duniya yasa a lalata mishi mutuncin shi, don Allah ka taimaka min ta yadda zan shawo kanshi."
Shiru Mutallab yayi yana gyada kai kamar kadangaren da ya sha rana.
"Yaushe kenan zamu hadu da Almamoon din, tunda kaga kun kusan komawa makaranta?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanun shi yana kallon yadda Almamoon shi zai koma da yan nonuwa a kirjin shi yana takun kauna a dakalin zuciyar shi. Tashi yayi zaune yana faɗin.
"Insha Allah ranar friday"
Wani irin murna yake ji sabida yana hango yadda zai yi da Almamoon indan Allah ya nufa ya zama nashi. Kuma yadda zai sarrafa santalelen cinyoyin shi,(da gaske ashe su Mom Sayeed da Maman Sadeeq basu yi karya ba hauka kake tuburan team Ansar 🤣🙆🏾♂️😭)
***
Zaune take tana ta haɗa aikan da ka kawo mata daga gidan ministan harkokin wajen tana gani tana murmushin mugunta domin haɗin na musamman ne, dan haka ta kira Babban matakin mai tuka jirgin saman fadar.
"Maza ku shirya gani nan zuwa Maradi zani"
Kashe wayar tayi tare da ɗaukar jakarta tana me jin a ranta shi kenan daga wannan haɗin Insha Allah Mohan Mamman Nasir Aghali ya tafi har abada.
.... Dakin Hajiya Lateefah ta shiga daga bakin kofar ta shiga matse kwallar fuskarta tana faɗin.
"Hajiya yanzun don Allah ba zaki ki ga jikin Mohan ba? Hajiya abinda kike fa Allah"
"Fitar min a d'akina!" Inji Hajiya Latifah, tana nuna mata hanya. Kamar da gaske ta saka kai zata fita.
"Inda yaso ya mutu ko ya rayu, ohon shi" ta faɗa da karfi tare da jin kamar zuciyar ta zata buga dan bata kaunar a kira sunan Mohan a kusa da ita balle kuma sauran Yaranta.
Da wani shu'umin murmushi ta bar falon tana jin a ranta shi kenan ta karewa Mohan Mamman Nasir, zata biya yaron da yake tare dashi kudi na fitan hankali.
Tana fitowa ya hadu da Primer minister, da Manyan yan jam'iyyar shi. Dake tana shirye da ta tozartashi tace mishi.
"Yallabai ina son zuwa na duba jikin Mohan"
Wani irin duba yayi mata tare da cewa.
"Ba yau ba"
Ya cigaba da abinda yake, juyawa tayi tare da komawa gida, har ta nufa gidan ya dawo tana cewa.
"Yallabai sai yaushe?"
"Jibi Insha Allah"
"Dama magani zan kai mishi, kuma yana da muhimmanci, tun da laluran nan hauka ce ai dole a duba lamarin don Allah ka barni na duba shi"
"Ba zaki ba nace" ya daka mata tsawa da yasa ta juyawa da gudu,
Caaa suka mishi da ido, yana jin numfashin sa yana hawa da sauka.
"Yallabai Mohan...."
D'aga hannu yayi alamar baya son jin koda kalma Daya ce daga bakunan su. Mik'ewa yayi yana me d'aga wayar shi ya mikawa Mai bashi Shawara na musamman.
"Ka musu bayani gobe zamu zauna yau bana jin dad'i."
Ya nufi hanyar da zai sada shi da cikin gidan shi. Yana jin kamar zuciyar shi zata buga.
Daga kasar zuciyar shi kaunar danshi yake kokarin tasowa mishi amma kuma k'iyayyar yaron yana kara danne mishi kin yaron.
Yana shiga falon shi ya zube akan sofa, yana jin wani irin kewar yaron a ranshi, amma Yarasa me yasa yake jin zafin yaron.
Chef Judge ya fado mishi a rai, baya mantawa ko wancan juma'ar sai da yace mishi.
"Yallabai munufarka tana da kyau sai dai kuma da na jikinka ake maka yankan baya, sannan ake niman ganin bayanka, Yallabai nasan ba ilimina ya kawo ni nan ba, Allah ne ya kawo ni nan, kai a tunanin ka bayan mun hadu a Saudiya na gaya maka wannan yaron da kuke tafe dashi zanen ƙaddara zata iya raba tsakanin ku.
Kuma kai ma baka manta ba, na gaya maka yaron ka yana da taurari masu karfi da zai hadu da wanda yake da irin taurarin shi da duniyar su. Yallabai Yaron ka yana cikin mawuyacin yanayi wanda a cikin gidan ka aka fara, sai dai kuma Allah yana sane dashi kuma yana sane da kome, idan yaso sai ya kawo mishi dauki kuma ya bashi wanda zai tsaya mishi. Ina tausaya mishi, duk da na daina na tuba amma bana jin dadin yadda rayuwar d'anka ya koma. Allah ya hada shi da mutanen kirki masu tsoron Allah. Yallabai Yaronka shine jigon mulkinka kayi wani abu akanshi ya dawo kusa da kai, Yallabai ina ga baka tab'a jin ana fadin Yan baiwa ba ko? Toh d'anka yana cikin su, domin kuwa idan yana tare da kai kowa tsoron shi yake babu wanda ya isa ya takaka, idan baya tare da kai kuwa wallahi jikin su na rawa zasu nemi bataka idan ka shirya zan duba Al'amarin shi Insha Allah za a dace"
Duk da yana jin zafin kiran sunan Mohan da Shugaban alkalan alkalai yake amma haka bai hana shi jin abin a ran shi ba
.toh waye yake niman bayan shi? MEYE! Mik'ewa yayi bayan sun idar da sallah jumma'a ya mika mishi hannun shi.
"Nagode idan ina son karin bayani zan Nime ka, alkalin alkalai" inji Primer minister,
"Nagode sosai Allah ya tsare gaban ka da bayanka"
Lumshe idanun shi yayi yana kara nazarin abinda yake faruwa, na farko tunda Mohan ya fara jinya mutane dayawa suka shiga rayuwar shi kuma suna abinda suka gadama bai isa ya hana su ba
Na biyu tunda babu Mohan aka fara mishi bore kamar zasu shi Office din shi.
Na uku kowa niman daura mishi laifi yake kome ya faru niman a cutar dashi ake? Ya rasa gane abinda yake faruwa,.ya rasa gane dalilin da yasa aka juya mishi baya, a yanzun yana da shekaru masu yawa akan mulki amma bai tab'a jin ko ya cutar da kowa ba, amma shi kullum niman hanyar cutar dashi ake, kasa fahimtar kome yayi, sai ma dage kirjin shi da yayi yana kara tausayin kanshi.
Yana kuma jin kamar akwai masu bibiyar rayuwar shi da ta iyalin shi, idan ba haka ba me yasa za a mishi wannan abun?
***
Maradi.
Addu'a ake mishi yana kara mingirawa kamar maciji, duk ya jima kamshi ciwo, sai rike kanshi yake, da sauri na mike zan kai mishi dauki domin yana cutar da kanshi, rike ni Malik yayi cikin wani irin sassayan kallo, ya rike hannuna. Fisgewa nayi na fada kan Mohan, wani irin duka ya kaiwa kirjina, sai da naji kamar raina zai fita sakamakon dukar nonuwana baki daya da yayi.
"Hyaiiiiiiii! Haaaah" na sauke wata irin numfashi tare da jin kamar an cika min iska a bakina da kirjina, tafiya nayi zan zube Malik ya tare ni, daidai shigowar Dan Ba'are, shima ya kai mun wani irin riko, suka kwantar dani a kasa, yayinda Mohan yake ta amai.
"Alhamdulillahi yau zamu bari zuwa gobe ku kula da Yaron yayi kokari wallahi"
Bai kai aya ba,Dan Ba'are ya dauke ni da gudu ya fita dani Sakamakon jinin da nake fitarwa ta hanci da baki, baya ganin gaban shi domin kamar dirka yake a step din, har asibiti ya kai ni.
A guje ya fita dani, Yaran shi da suka rako shi suna ganin shi aka bude kofar motar da sauri ya saka Ni sannan ya shiga yana me daura kaina akan cinyar shi.
"Taka motar"
Ya fada da karfi, haka suka fincike ta a guje.
Daidai fitowar Malik da Malam.
"Yanxun ya za ayi da mara lafiyan?"
"Zan kula dashi" ya faɗa kamar zai fashe da kuka, domin wani irin yanayi yake ji na takaicin yadda Dan Ba'are ya mishi shigan sauri haka kawai zai wani dauki Almamoon ai haka bai dace ba ina laifin ya kuka da Mohan shi ya kai Almamoon toh idan kuma wani abu ya faru da.....
.......... Chaiiii.....🙄 Ga masu bukatar a tallata musu Hajar su kofa a bude yake a tuntube wannan Number,08130269641
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....
_Gaisuwar wannan shafin naku ne baki dayan ku Makarantar BRRJI👏 Nagode sosai_
BABI NA SHA SHIDA.
Iskar bakin shi ya furza domin yasan dai duk abinda zai ayi almamoon namiji ne, dan haka ya juya tare da sallamar malamin, ya shiga cikin gidan. Yana me kara jin babu dad'i baki daya, ji yaƙe kamar yayi ta kurma ihu.
A yau yayi danasanin fara aikin soja, domin yana ganin kamar kasancewar shi a aikin ne ya ja mishi kaddararren wahala,haka ya taimakawa Mohan sannan ya koma bakin aikin shi dan bai ga dalilin da zai saka shi zama a jikin Mohan ba, tunda shi ya janyo haka.
***
Muna isa asibitin da gaggawa aka amshe ni, yana rike da gadon da ake turani har bakin kofar shiga dakin da za a duba ni.
Tambayar shi nurse tayi yayi mata bayani, sannan ta shiga cikin dakin, suka mai da hankali akan duba lafiyar ta, rigar Jikinta suka nime tsagawa, likitan ya ce musu.
"Ku dakata ba sai an raba shi da kayan shi ba, idan aka duba daga wajen ma yayi."
Inji likitan yana ƙoƙarin had'a alluran da zai mata, haka suka gama abinda zasu har suka sami nasarar farfaɗowa ta, amma take likitan yayi min alluran barci.
Lokacin da aka fito dani, mikewa Dan Ba'are yayi yana kallon su. Kamar me ciwon baki yace musu.
"Ya......ya.... Ya...."
"Yallabai da sauki ya samu barci, idan ya farka zuwa jibi zamu sallame shi"
Gyada kai kai yake tare da kallon keken majiyanta, har dakin da aka kwantar da Almamoon ya shiga. Zama yayi yana kallon fuskar yaron, wanda kullum yake zagaye da saje, kusan ma dabi'ar shi, sajen har kusan kumatun shi. Yana barci kamar wani mage, ya samu auduga. Dan cuter face din shi ya kuma fitowa sosai, gwanin ban sha'awa.
A hankali ya shafa dan bakin shi nan (Ni kuwa nace bakin tsiwa ba🙄😩da bakar magana) haka yayi ta shafa bakin shi yana murmushi, bakin yayi mishi kyau dan karami kamar bana namiji ba, murmushi ya sake tare da shafa kanshi yana me kallon window dakin yana kallon mutanen da suke shige da fice daga asibitin.
Yana jin ina ma da ace Almamoon mace ce, da yau zai gabatar da kan shi sabida kar yayi sake reshe kama ganye, kuma idan ma bai yi haka ba, taya yana ganin dama zai wuce shi, murmushi yayi sannan ya zauna tare da riko hannun shi yana kara jin wani irin nutsuwa a tare da Yaron, haka kawai yake kara kallon nasibin yaron, yana kara jin yaron a cikin zuciyar shi lungu da sakon cikin zuciyar shi.
Wani irin bugun zuciya yake ji a duk lokacin da ya kalli fuskar yaron ji yaƙe kamar dan shi aka halicci Yaron,. Shafa kanshi yayi tare da jin wani sabon nutsuwa akan shi. Yaron baki daya yayi tafiyar bazata da rayuwar shi. Murmushi yayi.
---
Kallon shi tayi kafin tace mishi.
"Malam Ansar ko zaka kai Ni naga Mamoon ne zuciyata taki yarda da halin da yake ciki, ko zaka kai ni"
Yadda ta damu sosai ya kalli Baba Mari kamar zai yi kuka, yace mata.
"Baba idan muka je ba lallai su barmu mu shiga ba, amma tashi muje"
Babban mayafinta ta yafa, tare da bin bayan shi, har Jacader.
Lokacin da ta ga gidan da Almamoon yaƙe zuciyarta sai da ta girgiza, dake sun san Ansar basu hana shi, shiga gidan ba. Asalima kamar an bashi pass ne, yana shiga suka haɗu da Malik kallon juna suka yi kafin Ansar ya fito daga motar shi yana faɗin.
"Ina Almamoon na kawo kakanshi ta gan shi ne dan ta damu"
Murmushi yayi irin me ciwon nan, sannan yace mishi.
"Yana asibiti babu lafiya"
Cakume wuyar Malik yayi kamar idanun shi zasu fado.
"Me Mahaukacin ku yayi mishi? Kunga abinda nake gudu ba? Kunga dalilin da ya sani nake gudun zaman Almamoon a cikin gidan nan ko? Wallahi idan wani abu ya same shi. Sai na kashe wancan Mahaukacin"
Dukar da aka kai mishi a baya yasa shi sake Malik.
"Kyale shi Fahad, ba laifin shi bane yana da iko da Almamoon."
.wayar shi ya ciro tare da kiran dan Ba'are ya tambaye shi suna ina ga kakan Almamoon tazo ganin shi. Yana gaya mishi asibitin ya gayawa Ansar.
Shima yayi amfani da kalmar kaka ce saboda yasan idan suka ji haka zasu bar shi ganin Almamoon. Yana gaya mishi sunan asibitin ya shiga motar shi da sauri, ya bar gidan kamar zararre, dama kuma ai zararren ne (🙄🤸😁🤣)
Koda ya iso asibitin, dakyar ya sami dakin da aka kwantar da Almamoon bayan ya gama shan bakar wahala, yana shiga ya kura mishi ido, yana mai da numfashin sa, tare da goge gumin goshin sa, kafin ya kalli dan Ba'are, kasa mishi tijara yayi domin irin karfaffan mazan nan ne, da shi da Mohan fadi kawai Mohan zai nuna mishi da cikar halittar jiki irinta mazan da suke daukar karfe. Idan Mohan ya saka mata matukar ta kama shi idan zai d'aga hannun, toh rigar zata iya darewa, sabida tarin kwanjin shi.
Takowa yayi tare da kai hannun shi zai dauki Almamoon, yaji an rike hannun. Tare da mai dashi baya, sake kai hannu yayi zai dauki Almamoon, ran Dan Ba'are ya b'aci dunkule hannun yayi zai sauke mishi naushi Nurse ta shigo.
"Nazo duba mara lafiyar ne zamu mishi allura"
Sauke hannun shi yayi yana kallon Almamoon, Nurse tana gama abinda zata yi ta fita, wani azazzaben dambe ya kaure a tsakanin su, karan buge buge ya farkar dani.
Kallon su nake kafin na tashi dakyar. Na nufe su tare da riko malam Ansar. Bakina yayi nauyi ina son nayi magana amma na kasa, dakyar na koma bayan shi na rungume shi. Tare da zaga hannuna kirjin shi.
"Ya isa Hammah ANSAR" na fada a hankali, kamar ba zan iya magana ba, cak ya tsaya kamar an zare mishi duk wata kusarin shi. Ji yaƙe kamar tunda yake ba a tab'a kiran shi da suna Yaya ba, baki daya gwiwar shi tayi sanyi sama da kullum. Yau shi Almamoon ya kira Hammah ko mafarki yake ne?
Anya ba mafarki yake ba? Indai da gaske ne shi Hammah ANSAR ne, toh tabbas Almamoon yana rungume dashi kenan. Wani bahagon naushi Dan Ba'are ya kai mishi. A fuskar shi sai da ya kufa a kasa, tare muka fadi.
"Almamoon rabu da munafuki" inji Dan Ba'are,
"Hammah Khalil! Ka daina dukar shi, bana jin dadin haka." Na shiga tsakanin su. Muna kallon juna. Tafiya nayi luuuu zan fadi suka tare ni dukkan su biyu, ɗauka ta suka yi tare da mai dani gadon, suna kallon fuskana. Lumshe idanun nake ina kuma buɗe shi.
"Ya Hammah Mohan yake?" Na tambaye su a gajiye, gyara kwanciya na suka yi sannan Dan Ba'are yace min.
"Ana ta lafiyar ka waye yake ta Mohan?"
Sam ban ji dadin abinda ya faɗa ba, dan haka na tashi zaune.
"Zanje naga halin da yake ciki"
"Baka isa ba, wallahi sai na falla maka mari, kuma mun zo da Baba Mari ne"
Komawa nayi na kwanta, haka ya fita can sai gasu tare sun shigo d'akin, suna shigowa dan Ba'are yana fita.
"Sannun kaji, Allah ya baka lafiya ashe baka da lafiya ne"
Gyada mata kai nayi ina jin kwalla na cika min idanuna, shafa kaina tayi tare da cewa.
"Zan zauna da kai kaji"
Gyada mata kai nayi, muna cikin haka Malik ya shigo tare da kallona.
Murmushi ya sakar min, na maida mishi nima.
"Ya jikin naka?"
"Da sauki"
"Allah ya baka lafiya"
"Amin Ya Allah, ina ka baro Hammah Mohan? Kasan bai da lafiya kake barin shi babu wani a kusa dashi? Kasan yadda rayuwar shi take cikin hatsari ka bar shi shi daya a gidan? Ku mai dani gidan kawai nayi jinyar a can"
"Ba zaka kuma komawa gidan ba, domin ina kaunar ka" juyawa nayi na kalli Malam Ansar.
"Ba zaka tab'a samun yadda kake so ba,dan haka babu ruwanka dani."
"Kayi hakuri dama nazo duba halin da kake ciki ne, kuma Alhamdulillahi, zan koma domin na bar Fahad a jikin shi."
Gyada mishi kai nayi, tare murmushi.
Haka ya tafi ba tare da na yarda mun kuma magana ba, sabida bana son yadda yake kallona.
Hankalin su Baba Mari da Hammah ANSAR ne ya dawo kai na.
"Baba Kinga shi taurin kan bala'i ce dashi dan haka ki saka baki mu koma gida dashi."
"Hmm" na fada ban kuma magana ba sai ga Dan Ba'are da manyan ledojin shi guda uku, ya ajiye min.
"Sannun bawan Allah Ubangiji ya saka da Alkhairi, Sannun da tallafan rayuwar shi mun gode"
Cikin wani irin murmushi yake kallon mu, irin yayi katon bajinta. Dariya ya bani irin wanda ake yin shi a cikin rai haka,
Book Chapters
Chapter 12
Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45