Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abincin ina ci, ya hakura da shi sai da yaga zan sha ruwa ya barni haka, daukar cokalin nayi bayan na sha ruwa na shiga bashi, shima yana kallona kawai sai naji a raina duk yadda aka yi. Ya rayu cikin kadaici da rashin soyayya, ya bani tausayi.
"Hammah kamar kayi rayuwar kad'aici?"

    Rike hannuna yayi tare da kallon yadda hannun suke, duba agogon wayar shi yayi sannan ya mike, mai aikin gidan ya shigo tare da tattara inda muka ci abincin. Fita muka yi bamu tsaya ba sai a wani babban shagon saloon. Kawo mishi littafin abubuwan da suke yi aka yi ya fara dubawa, sannan ya nuna musu abinda yake bukata, kafin ya koma gefe.

     Wani daki na musamman aka kai mu, anan aka fara wanke min kafana bayan an gyara min farcen, sannan aka fara wanke min kaina da mayuka masu sanyin dad'i,  haka ake wanke min kan, ana gama min wanke kafar da hannun, aka fara zana min jar lalle, kallon matar yayi sannan yace mata.
"Ki huda mata kunne domin babu hujin kunne a tare da ita,"
"Kai Hammah" na fada ina kallon shi, dage min gira yayi, wayar shi ce tayi kara, a hankali ya dauka sannan ya fita.

       Koda suka zo hujin kunnen nasan da zafi fir ba hana su, sai da ya shigo d'akin, suka mishi bayani. Yana zuwa ya kura min ido, kafin ya durkusa a gaba, yana kallon zanen da ake min, d'an mik'ewa yayi, ban san taya yayi musu magana ba, amma ya kai bakin shi kamar zai sumbaci ni naji an huda daya kunnen, ihu na saka mishi tare da damke wuyar shi da hannun lalle. Kafin na dawo daga duniyar zafi an huda daya kunnen, kuka na saka mishi. Masu aikin Saloon din sai dariya suke min.

   "Hammah dariya suke min" juyawa yayi tare da kallonsu.
"Akan me kuke mata dariya"
"Tayi hakuri" tura baki nayi ya dauko wayar shi, zai dauke ni hoto na ki, ina kallon shi.
"Hammah na b'ata maka riga da"
"Babu damuwa bari na sauya"
Ya wuce wani shashi na cikin shagon, ya sauya sannan ya fito da wanda ya cire. Haka ya zauna yana jirana har aka cire lallen ga gashina da aka gyara, yayi kyau sosai. Fuskana ma suka gyara min, sannan muka fito.

       Tunda muka fito nake lura da yadda yake zuba idanu a gurin, kafin muka shiga motar, janyo hannun yayi yana kallon shi.
"Ina son naga mace da zanen lalle kyau yake min, ki Cigaba da zuwa nan koda ban kawo ki ba, zasu miki kome da kike bukata,"

   "Toh" haka muka bar gurin ina yawan karanta irin wannan abun a cikin Novel ko films ban tab'a kawowa za a wayi gari namiji ya dauke ni domin rage min damuwa ba, wato mun yi yawo sosai bamu koma gidan ba sai dare. Sannan ya sauke ni a cikin gidan, ya taimaka min na kwashe kayan da ya sayo min,  muka shiga cikin gidan.

   Tunda na shiga Jalilah take kallona, Kafin ta dauke kanta gaida Umma nayi, sannan na zauna ina me sunkuyar da kai musamman yadda take min kallon tuhuma. "Ki shiga cikin dakin"

  A hankali na kwashi kayan na nufi d'akin.
"Jalilah kwashe kayan ki kai mata, kai kuma biyo ni d'akina." Ya mike haka ya bi bayanta, har cikin d'akinta. Zama tayi a bakin gadon ya zauna a stool.

    "Baka da hankali ne? Yarinyar da kake so zaka dauka tun la'asar baka dawo da ita ba Da karfe goma na dare, ko an ce maka so hauka ne? Kar na kuma ji ko na gani, ai ki babu kome ka gaya min zaka fita da ita, idan da wani abu ya same ta fa? Wallahi karka kuma wannan gangancin ko kamanta kana da kane ne masu mugun rawan kai, bana so kar ka yi abinda ka san idan aka maka ba zaka ji dadi ba, kuma kaje Lateefah tana niman ka domin tazo nan ganin Yarinyar."

    "Toh insha Allah ba zan kuma ba, amma wallahil ban da rike hannunta sai da take kuka tace tana son jin dumin mahaifiyarta na rungume ta, wallahil billahi azim ban tab'a kallonta da mugun nufi ba, don Allah kiyi hakuri ban gaya miki dan na d'aga miki hankali ba, amma ita matar da nake burin ta zama uwar Yarana ce idan na b'ata duniyar mu goben mu ba zata yi kyau ba, shi yasa nake bin kome a tsarin Ubangiji gobe zata koma gida, sati biyu masu zuwa zata dawo ta fara aiki a nan." Ya fada tare da mata sallama.

   WALLAHI sai yaji duk ya bata tausayi, ya burge ta yadda ya iya fadar abinda ya aikata, Mohan ba yaro bane, amma rashin soyayyar uwa yasa shi tashi a wani irin murɗeɗɗan hali. Sai dai fara soyayyar shi yasa ya sauya fiye da  bayan idan da yana Mohan shi ne, zai iya share awa daya bai bata amsa ba, har take ganin kamar bai dace da aikin soja ba. Addu'o'in tayi musu, sannan ta mike tare da fita a d'akin. d'akina da nake ta shigo ta samu ina tattara kayan da Jalilah ta fasa min har da mayunkan da ya saya min, kallo na tayi ta ga ina share kwalla.
"Taya aka yi kayan suka watse haka?" Jan hannuna nayi domin ban iya karya ba, kuma ban san yadda zan gaya mata ba, sai nayi shiru.

"Jalilah ko?"  Gyada mata kai nayi, fita tai can sai muryan ta naji tana kuka, dan Ba'are ya shigo har dakin yana bani hakuri.
"Babu kome" na gaya mishi ina tattara kayan.
"Naga wasu sun fashe"
"Eh ba kome zan gyara su" na dauki kayan na zuba a jaka na.
"Ko zan sayo miki wasu ne" kallon kayan nayi domin kayan da Masoyina ya saya min ne, ba zan iya sauya su da wani ba.
"A'a kayan da Hammah Mohan ne ya dauka min, dan haka babu wata matsala." Na fada mishi haka, ganin bani da niyyar magana ya sa shi fita daga dakin, yana mamakin wannan yanayin, ko zubar da kayan banyi ba, dan haka yana fita ya kira Mohan bai dauka ba ya tura mishi sako  da fatan zai gani.

    ***
Cikin nutsuwa ya shiga cikin gidan, tana zaune a babban falon ta, tana kad'a kafarta. Kallon shi tayi lokacin da ya shigo da sallama.
"Waalaikumun Salam" ta amsa tana kallon shi, dama yana ganin yadda take ya fahimci kome,.taji labarin Moonah, zama yayi sannan yace mata.
"Ammyn Barka da hutawa"
"Yawwa Mohan, Ya Surukar tawa?" Kallonta yayi sannan yace mata.
"Tana lafiya"
"Dama itace kake so?" Gyada kai yayi sannan yace.
"Ammyn itace tayi jinyata kuma."
"Yar Uban waye a kasar nan?" Nan ne gaban shi ya fadi, ya rasa abinda yake mishi dad'i.
"Waye Ubanta?" Sake dukar da kai yayi.
"Ina sonta ne, ban damu da ko yar waye bane, kawai zuciyata tayi na'am da ita, bayan haka ba zan iya jure rashin ta ba, kuma ba zan iya jure tashin hankalin da zata fuskanta ba, zuciyata ta bani ita kuma na amsa hannu bibbiyu."

   "Mohammed Mamman Nasir! Nace waye Ubanta?" Kallonta yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Ba yar kowa bace!"
"Ba yar kowa bace kake b'ata mata lokaci? Bayan kasan cewar nan da wasu watanin za ayi baikon ku da Hanan?"

"Ammyn ni fa bana son hanan, ni matar da bata san darajar arziki da dukiya nake nima, matar da zan bata kudi tace min me zata yi dashi nake nima, matar da zan ce mata gabas tace min toh nake nima, matar da zan ce mata zauna ta zauna ba zan yarda na auri matar da bani da iko da ita ba, ina ji ina gani haka na rasa soyayyar ku shine xan yarda ba fada hannun wata mace? WALLAHI ba zan iya aurenta ba,  iya gaskiya na gaya miki"

   Cike da mamaki take kallon shi, kafin tace mishi.
"Yarinyar da ta gudo daga gidan su, sabida namiji zaka ce kana sonta kai ma idan ya gaji da kai guduwa zata yi tabi wani, yarinyar da bata san darajar Iyayen ta ba?"
"Eh amma ai duk abinda zata yi domin gobenta yayi ba dan yau ɗinta ba, ita guduwa tayi tabar gaban iyayen ta, idan har na rasata tabbas gawata za a shigo miki da shi, dan haka ki barni da abinda zuciyata take so itace farin cikina, kuma itace hasken idaniyata, don Allah karki tab'a min abinda nake so."

  "Kai baka san girman darajar ka bane? Ko baka fahimci yadda Allah ya maka ni'imommin rayuwa bane? Ubanta yana da arziki ne?" Ta tambaye shi.

  "Ko gidan kanshi bai mallaka ba, ni dai a haka nake son abu na" ya faɗa yana kallon ta. Abin mamaki ya kuma bata. Lallai maganar Karime gaskiya ce yarinyar bata bar Mohan haka ba, yaron da mace bata ishe shi kallo ba, shine yanzun yake fada mata itace rayuwar shi. Dama tunda taji ance mata Bororoji ce tasan dole ayi haka mutane masu mugun asirin bala'i, dan haka dole ta mike domin karkato da hankalin D'anta, zata bawa Hajiya Karime damar yadda zasu karkato hankalin shi, ina wannan ai ba zata iya dauka ba.

   "Baba na, ka rabu da ita kaji ina nan ina shirya maka rayuwa me inganci, wancan yarinyar kuma ba mutuniyar kirki bace domin haka suke yiwa mutane mugun abu. Ka hakura da ita zan nima maka macen da ta dace da kai kuma ban da abinka Baga Hanan ba fara doguwa me kyau ina zaka kai wancan me duhun fatar ka hakura da ita mana.

*Nasan kuna kokari wallahi amma ku kara min yawan Vote din kunji dearies idan ba Novel din kudi ba bana hana kaina barcin safe ba, amma gashi ina idar da sallah Asuba na fara typing na gama Pagen 07:16 na cigaba da Next page kunji ku kara min sai muyi tafiyar yadda baku zata ba.... Thank You 😁💞❤️💓😍😘 Nagode*
#Mai_Dambu...
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108770833?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=XvTJ715kPu2X0PivW5mr2ueQhMuyT9VxReszdcWX9iE99sEqXcVLFhnWOGRWovfKLC7i4%2FOUqPMZZ6VWIcVOpGiYhQwcVRmRXaxx6lPfK9GN9UgTFxHmNED7gtVuw37%2F

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA TALATIN DA BIYAR.

_Ina mika sakon godiya nagode sosai Allah ya bar Zumunci musamman Team din Hajiya Innah da Hajiya Latifah 😁😛😜🤣_

Murmushi yayi sannan ya mike tare da cewa.
"Ba zan iya haihuwar Yara su tashi a wulakance ba, ba zan iya auren macen da bani da ita da ita ba, idan zaki duba alamarina ki duba amma tabbas ba zan iya daukar wannan kasadar ba, Moonah nake so. Kuma itace nake da yakinin zata zame min gata a gurin Yarana gaskiya kenan."
"Mohan ni na haife ka fa? Amma kake gaya min baka son zab'ina?"
"Ammyn ba haka bane baki daya gidan kin watsar damu, kin tab'a tuno sauran yaran ki? Haba Ammyn sauran duk matan da suke su suka aura me yasa ni ba zaki barni na zab'i abinda nake so ba? Dan tana ba yar kowa ba, ni Ita nake so wallahi"

      "Mohan ba laifinka bane dama ai Bororoji kowa yasan su da mugun tsafi shi ta maka, dan haka sai na karya da Izinin Ubangiji." Kallonta yayi tare da juyawa ya bar falon domin idan ya cigaba da biyawa Ammyn zuciyar shi zata iya dirowa a kirjin shi. Dan haka ya dauke kai kamar bai ji ba.

   Tana zaune a falon tana jiran Premie minister.
   ***
A babban falon bakin shi sun hadu baki ɗaya.
Chef of Army, Attorney general, Minister of defense, Inspector General of Police, duk sun hadu a falon.
"Yallabai ba zai yiwu Mohan ya dawo bakin aikin shi ba, sabida bamu da tabbacin me ya rike shi na tsawon shekara biyu baya nan ba, dan haka ba zamu dawo dai aikin ba gaskiya."

Kallon shi tayi cike da mamaki, shekara daya kenan yana bin su akan lallai a dawo da Mohan. Murmushi yayi sannan yace musu.
"Zai dawo bakin aikin shi! Matukar ina kan kujerata, tabbas Major Mohan zai dawo idan kun shirya toh idan baku shirya ba, Insha ALLAH nan da wata gudu dai dawo ranar bikin yancin kasa." Ya fada tare da mik'ewa ya barsu a falon. Murmushi suka yi a tare, sannan minister tsaro yace musu.
"Shi kenan tunda abinda ya zab'a kenan a barshi yayi yadda yake so"

Suka fada tare da mik'ewa suma, suna da yakinin lallai dole a dakatar da Mohan da Ubanshi domin babu adalci akan wannan maganar. Taya zasu yarda su bashi aikin da yana zuwa zai fara musu iyayi kamar wanda aka haifa  a cikin soja. Kowannen su da abinda yake tsarawa a ranshi.

   "Amma nake ga ba wani abu  bane dan Mohan ya dawo bakin aikin shi tunda dama ai ba sallamar shi aka yi ba"
"Eh haka ne amma yaron ba zamu yarda ya dawo bakin aikin shi bane domin bai da kirki sam bai dan darajar mu ba, shi yasa."

  "Toh lallai dole mu yi abu daya imma mu dakatar dashi imma mu kore shi."
"Bamu da ikon tafiyar da kome sai da Sannun Uban shi."

  Da haka suka bar gidan, ran su babu dad'i.
   **
Yana shiga  cikin gidan ranshi a b'ace tashi mishi.
"Yallabai kaji abinda Mohan yake ciki kuwa?" Wani sabon tashin hankali ya kuma shiga, tare da kallonta zuciyar shi ta gama gajiya da damuwa yace mata.
"Me ya same shi?"
"Wai soyayya yake da yar matsiyata, nayi mishi magana wai ita yake so ita kuma ya zab'a." Wani irin takaici ne ya kuma kama shi ji yaƙe kamar ya dake ta, ko zai sami sassauci.
"Ke da aka tashi miki aure ai ba a miki auren dole ba? Ko an baki ni a dole ne? Babu ruwan ki da rayuwar shi, duk abinda yaga ya dace yayi rayuwar shi ce ita wacce zaki hada ta dashi yaushe zata zauna ta kula da rayuwar shi, dan haka kamar yadda kika gurgunta min rayuwa ba zai yiwu ba ki gurgunta mishi rayuwa, kuma wallahi naji labarin kin yi wani shirme akan yarinyar da yake so zan baki mamaki"

    Ya wuce tare da barinta a tsaye bakinta bude, dakyar ta ja kafarta ta bar falon ranta yana b'aci, ita zai ciwa mutuncin akan rayuwar dan su? Wallahi sai ta tayi maganin su dukkan su. Dan haka babu wani abinda ya dame ta, haka ya shirya gobe zata kira Karime.

     **
Washi gari da safe.
Ya shigo zai gaishe ta yaji tana waya,abin ya kad'a shi dukda ya fahimci ba halinta bane, amma kuma ta bashi mamaki, dan haka ya gama sauraron ta, kafin ya juya yabar kofarta ya tafi ya shirya bai karya ba, a gidan ya nufi gidan su Dan Ba'are, yana zuwa ya nufi dakin Dan Ba'are yana barci ya dage ya maka mishi duka a cinyar shi, Allah sarki a firgice ya mike, yana sosa gurin.
"Dan iska mara mutunci akan soyayyar ka, na shiga gararin rayuwa meye nayi maka da zaka katse min mafarkin da da nake da Benazir"
"Yarinya ta na zo dauka dan Ubanka dan iska" a fusace dan Ba'are ya wurga da bargon ya mike, dariya Mohan ya saka mishi tare da nuna mishi wandon shi.
"Dan iska rago kawai, da ace kai ne lokacin da Almamoon yaƙe damkata da rungumo ni, tabbas da yanzun ka afka mata, mara mutuncin a mafarki kenan kake barin ruwa ranar da ka sami yar mutane dai an kawo mata dauki, wallhi ka zama me karfin zuciya. Ka daina daura sha'awa sama da soyayyar da kake mata, nasan kana Sonta, amma tsakanin ka da Allah meye ya ja hankalinka akan ta?"

     Cikin sanyin da damuwa yace mishi.
"Wallahi kirjinta da k'ugun ta, shine abinda ya fisge ni."

    "Kasan me yasa nake son Maimoon? Na farko Addininta! Na biyu haukatar,, na uku gaskiyar ta, kai idan zaka mata wani abu na tambaye ya wallahi zata gaya min, bata iya karya ba. Sannan bata da lokacin kananun magana, ban tab'a ganin suraanta ba, balle har ya d'aga min hankali, amma a baya idan ta rungumo ni, kwana nake ina juyi a gado, domin alamarin da ban mamaki. Dan haka karka so mace domin wani abu bata na jikinta kaso ta domin Allah. Taso min ita zamu tafi."

        Wucewa ban daki yayi tare da gyara jikin shi, sannan ya fito tare da saka jallabiya, ya nufi cikin gidan, tare da Mohan yana gaya mishi abinda ya faru jiya, ran Mohan ya b'aci sosai. Da sallama suka shigo falon Umma, suka gaishe ta, sannan suka zauna.
"Bari na taso ta, ina ga kamar sallah take." Ta fada bayan ta nufi hanyar dakin da Moonah take. Ina karatun Alkur'ani ta shigo min, sai da na kai aya sannan na kalle ta tare da amsa sallamarta.

"Ina kwana Umma?"
"Lafiya lau, da fatan kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillahi!"
"Masha Allah"
Shiru tayi sannan tace min,
"Karki kuma aikata irin wannan kuskuren, karki kuma barin gida domin saurayi, ki bar gidan ku akan namiji kuskure ne babba, dan haka ina me baki shawara karki kuma haka, idan baki hadu da me mutunci ba rabaki da martabar ki zai yi, dan haka karki sake irin haka ya kuma faru." Tayi min nasiha sosai, kafin ta fita bayan ta bani umarni na shirya na fito yana jirana a wajen,ta koma d'akinta ta haɗa min shatara na arziki,sannan  muka nufi falon. Inda na same shi yana karyawa, zama nayi ina kallon shi, sosai nake tausayin shi.
"Ki karya"
"A'a na tashi da azumi ne" da sauri ya d'ago kai, ya had'e fuska tare da mik'ewa ya ja min kujeran ya nuna min da idanun shi.
   Sunkuyar da kai nayi sannan na taso tare da nufar gurin shi, na zauna. A hankali na fara cin abincin shi da ya tura min flet din, ina ci ina kallon shi.
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillahi!" Na bashi amsa,
"Meke damunki yanzun?"
"Kirjina yake min ciwo" na fada ina diban abincin,
"Allah ya baki lafiya"
"Amin Ya Allah Nagode sosai"
"Dame fa?" Ya d'age min gira, murmushi nayi sannan nace mishi.
"Da kome"
"Toh sai kin biya"
"Toh nawa?"
"Duk yadda kika biya"
"Toh lallai kuwa zai yi araha kenan"
Na fada ina kallon shi, murmushi yayi sannan yace min.
"Maza kici babu lokaci ina son na dawo akan lokaci ne."
  Haka nayi ta cusa abincin har na dan ji na koshi, sannan na mike na gyara gurin, muka yi musu sallama, dake a mota zamu tafi. Haka yayi ta jana da hira.

    ***
Maradi.
Haka yayi ta niman Number Mamoon bai same shi so yake yaji da gaske ne mace ce ba namiji ba, toh bai samu layin ba, haka ya tattara ya nufi Damagaram. Bai samu matsala da Inna ba, sai dai kuma. Taki sake jiki dashi kamar baya, dan haka yayi ta damunta ina Almamoon yake. Kasancewar Malam na gida, yasa ta jan bakinta tayi shiru, domin tana fara magana malam zai taso ta a gaba har sai tayi shiru. Haka Malam Ansar ya bar Damagaram. Rai babu dad'i.

    Bayan tafiyar shi da awa biyar, muka shigo garin Damagaram, kallona Hammah Mohan yayi kafin yace min.
"Karki wani shirme don Allah,karki yarda ki yi abinda zai bata mata rai, don Allah ki nutsu ki zuba min ido Insha Allah zan baki mamaki zan shawo kanta cikin sauki."

  Murmushi nayi domin bana jin zai samu kan Innah a saukakkakiyar harshe, dan haka koda muka isa gidan Baba yana kofar gida. Ina sauka gurin shi naje na zauna, tare da sunkuyar da kaina.
"Maimunari kin dawo lafiya?"
"Alhamdulillahi, Baba ka yafe min" na fada da raunanniyar murya. Alamar xan iya kuka ko wani lokaci.
"Munari baki min kome ba, sharrin shaidan ne da zuciya da bata da kashi, Yaron nan yana sonki sosai,don Allah ki kula da rayuwar shi, samun mutumin da zai damu da kai arziki ne, kin ga tashi ki tafi cikin gidan." Ba dan kome na sai dan kukan da nake sosai. Jan hancina nayi sannan na shiga cikin gidan, ina sallama. Sau daya ta d'ago kanta bata kuma d'ago kai ba, ta cigaba da abinda yake yi.

     Zuwa nayi bayanta na zauna tare da kwanciya kamar yadda ta kwanta na rungume ta, ina kuka. Kuka nake sosai. Wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a yin shi ba, lumshe idanun ta tayi tare da janye jikinta.
"Da kin san ke wacece ba zaki tab'a d'aga dokar da na saka miki ba, da kin san wacece ba zaki tab'a kallon da namiji ba. Amma kin makaro ba zan tab'a yarda ki auri wanda nayi imani zaki saka shi kuka, kema kiyi kuka ba. Nayi danasanin biye muku kika tafi Jami'a nayi dana sanin barin ki mu'amala da mutane, kinsan me yasa sabida idan kika dan tushenki zai yi wuya ki amincewa kowa, duniyar tsoro zata baki."

"Amma bana kashe maganar nan ba? Ko bana ce kiyo hakuri ba? Ina cewa kika yi tafita tabar gidan yanzun ta dawo kina taso abinda ya wuce shiga Muhammad." Ya nunawa Hammah Mohan hanya, da sauri na shiga cikin dakin na, na dauko taburma yau ce karon farko da ya shigo inda talakawan Baban shi suke rayuwa, kallon yadda nake kaiwa da komowa yayi, har zuwa lokacin ban daina kuka ba.

     Abun ya dame shi sosai, dan haka yake ta bina da ido, ina kawo mishi ruwa cikin kulawa yace min.
"Beauty zauna na gode, ya isa haka kukan nan idan ba so kike na fara kukan ba, ya isa haka."

      Kallon shi nayi domin ya bani tausayi musamman yadda yake magana a dame kamar zai fasa kuka.

      Gyada zama nayi ina kallon kasa, Baba yayi min nasiha ba iya Ni ba har Mohan din, sannan ya mike zai tafi ma raka shi, ina kallon shi ya shiga sauko min da kayana, tare da kawo min cikin gida da kanshi ni kuma ina jikin motar shi yace na tsaya.

    Koda ya shigo zuwa yayi ta zube a gaban Innah, ya gurfanar kamar me niman gafara.
"Don Allah kiyi hakuri karki Zafaffa mata, kiyi hakuri karki juya mata baya, tunda ta bar gidan har yau kece a ranta, Innah idan wani yayi mata gori kece zaki fara jin ciwon abin amma ke da kika mata gorin har yau kuka take, Innah da xan iya rabuwa da Maimunari wallahi da na rabu da ita. WALLAHI ba kome nake nima a gurin ta ba, kaunarta da Allah ya daura min ya wadatar dani. Innah kiyi hakuri nasan baki son alaƙar mu amma ni, ina sonta sosai ina sonta kamar na cire zuciyata na bata, Innah wallahi da ki rabani da ita gwara ki zuba min yawan kuɗin da zan biya sadakinta ina son Maimunari ina kaunar Maimunari, ina bala'in kaunarta ina son ta."

Kasa magana tayi tana kallon shi yadda yake magana kamar mahaukaci, abin yayi mugun b'ata mata rai dan haka tace.
"Ba zan baka ita ba, kaje kayi rayuwarta itama tayi nata. Kuna da banbancin rayuwa dan haka kai dan masu kudi ne ita kuma kaga inda muke dan Allah ka fita a rayuwar ta, indai ba wani abu kake bukata ba."

   "Kiyi hakuri zan cigaba da baki hakuri amma ba zan tab'a sarewa ba, domin ina son Maimoon ce" yana gama fadar haka ya mike tare da nufar hanyar waje. Ina kallon shi ya fito, yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya rike kaina tare da sumbatar goshina..
"Kina raina koda yaushe" daga haka ya koma ya shiga motar shi sauke gilashin motar yayi sannan yace min.
"Kiyi hakuri idan sati biyu ya cika zan zo daukar ki."

    Gyada kai nayi ina share kwalla da yake kwaranya a fuskana, daga haka na dauki sauran kayan na nufi cikin gidan, na samu ana rigima tsakanin Innah da Baba, banyi magana ba sai dai tunda na shiga dakin naki kula su,
     ***
Kallon mijinta tayi cikin kuka, wannan shine karo na sha takwas, zuwan shi rugar Alu. Babu iyayenta babu Sumail Wodaadabe da Kanwar shi.
"Mommy kiyi hakuri mana, sai kuka kike idan shi wancan baki ganshi ba, Baga mu ba. Kiyi hakuri mana kullum muka zo sai jininki ya hawa. 

"Benazir baki da hankali ne? Kin san yadda take ji? Sai na sab'a miki mara jin magana" inji Dr Khalid wanda yanzun yake matsayin ministan lafiya.
"Dad gaskiya ba fada mata ai idan da tana son shi ba zata tafi ta barshi ba, dad ban san meye ba but wallhi ba zan tab'a barin Yarona a wani gurin ba ko ku da kuka haife ni ba zan bar muku Baby na ba, haka sai kace babu zuciya a kirjin ki."

  "Keep quiet!

Please Login or Register in order to submit comment