Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauran bayanin, murmushi yayi sannan ya ciro wayar shi zai kira Munnah sai ya fasa, dan haka ya shiga garin ciki babu iyaka. Dan haka yake jin yanzun zai iya tura mata sakon da zai saka ta amince da shi ta wata fuskar,dan haka ya tura mata da wata wayar.

**
Da Asuba bayan na idar da sallah, ina kwance na janyo wayata na kunna, bayan na bude data. Na duba Internet, abu daya ne wato sake hotonan Hanan da Mohan, babu karya babu hassada sun dace da junar su. Kamar zanyi kuka haka na ajiye wayar, ina shafa kai na da ya fara tohowa da gashi, ina jin haushin kaina. Dan ma ina da kafar gashin ne shi yasa har ya fara tohowa.
       A hankali na koma na kwanta ina hararan wayar dan itama yanzun haushi take bani, hango sako yasani dauka na bude. Zaro idanuna nayi, cikin tashin hankali da fargaba, tare da jin cikar kwalla a idanuna. Sake wayar nayi a hankali ya fadi kasa, bayan na rike kowacce harafi da kalmomin jikin hoton da aka turo min.

*_Ina ga wannan al'amari ya gani ya juya miki baya ko? Toh ina da kuma ya kara fahimtar an shiga cikin an juye bakin mai fa_*

Daga
           Malik Dalhat.

Wani irin kuka ne ya kwace min tare da cusa kaina a tsakanin cinyoyina, ina rusa kuka, kamar raina zai bar jikina, haka nasha kuka ma more, har gari ya waye ban fita ko ina ba, ina ganin kiran Mohan naki dauka, karshe goge abin nayi tare da kashe wayar baki daya.

    Ina jin shi yana buga kofar amma naki budewa, karya kofar yayi ya dame ni zauna akan abin sallah..na takure guri guda,  takaici ya sashi takowa har inda nake yana kallona.
"Toh wannan haukar da kika min zai sa na fasa abinda nayi niyya ne? Bari na gaya miki koda aurenki nayi wallhi baki isa ki juna ni ba, wacece ke da zan kira wayar ki, ba zaki dauka ba? Dan ina sonki sai ya zama na haukace akan ki? Wacce irin daukaka kike  nima ne? Meye zan baki? Meye kike bukata na miki?"

Mikewa nayi ina kuka tare da riko hannun shi.
"Don Allah ka yarda dani! Shine kawai abinda nake bukata idan kayi min haka har abada ba zan kuma ba, ka amince ba zan maka abinda za a gaya maka ko zaka gani ba, Mohan na yarda da kai matukar zaka saka ni a jerin matanka, koda zaka iya fushi dani don Allah ka yarda dani"

      Jikin shi ne yayi mugun sanyi, yana kallon yadda nake kuka, janyo ni yayi tare da rungume ni.
"Kina boye min wani abu da ya faru dake? Me nene shi?"
"Kayi hakuri dani!" Na fada bayan na rike rigar shi.
"Insha Allah zanyi hakuri dake"
Haka yayi ta shafa bayana yana, faɗin.
"Ina tare dake, amma idan akwai wani abu ki gaya min, bana son daga baya muzo muna samun matsala"
"Babu matsalar kome Insha Allah"
"Ina jiran ki, ki shirya na ajiye ki a gurin saloon."

Murmushi nayi tare da kallon shi.
"Na aske gashin" na nuna mishi kan. Jan hancina yayi tare da cewa.
"Gaskiya ina son gashinki nan me kyau da tsantsi, dan haka muje a hada miki mayukan da zasu fito nan da wata uku insha Allah."

Fita yayi na shiga nayi wanka tare da kwalliya, sannan muka fito. Gurin karyawa muka fara tafiya. Bayan mun karya sannan ya kai ni gurin Saloon, aka had'a min mayuka masu kyau, sannan yasa aka min jan lalle, tare da gyara min fuskana.

         Bayan an gama ya kai ni gurin aiki, yana bawa Abie hakuri. Cikin harshen buzanci suke magana, sai su kalle ni sai su cigaba da magana, kafin yayi mishi godiya da sallama ya fita.

"Ashe za yi baikon shi?"
"Eh Abie"
"Toh Allah ya tabbatar da alkhairi!"
"Amin Ya Allah,"

Daga haka bai kuma magana ba, nima haka sai dai hankalin mu ya raja'a akan abinda yake gaban mu ne.

"Me yasa kika sare akan sha'anin ku?"
"Abie shi din dan masu kudi ne, kuma uwa uba, dan shugaban kasa ne, taya zan kai kaina gurin shi, kawai ina jin rabuwa dashi shine mafi alkhairi, sabida kamar bamu da ce da juna ba"

   "Ni kuwa sai nake ganin kun dace da juna, kuma kunsan halin juna, zaku iya zama da juna koma yayya ne, kawai ki daina saurin karaya."

Dariya nayi domin yadda yayi min maganar sai da ya bani dariya,
Toh Abie kana ganin Mahaifiyarshi zata yarda? Matar da tayi mishi matar da zai aura, kawai daga ni har shi b'ata lokacin juna muke, ka duba al'amarin mana, mahaifiyar shi tana son nasaba ni kuma ko mai kwasar shara bamu dashi ni daya ne nake karatun boko, sannan kuma."

"Kin yarda da Allah?"
"Sosai ma kuwa!" Na bashi amsa,
"Toh ki yarda da ƙaddaran ku, yace na baki hakuri gaskiya yana kaunarki,sosai kuma yana tare dake don Allah karki juya mishi baya"

   "Abie bani da wannan burin, amma idan ya cigaba da Zafaffa kishi babu bincike alaƙar mu bazata yi nisa ba." Na d'ago kai ina kallon tv dake office din ana kuma saka sanarwan baikon, da Yaren fillaci, anan kan sai da na dauke kaina.
"Masu hakuri suna tare da Allah." Ya fada tare da mik'ewa ya kashe tv.
"Na sani Abie" haka wunin ranar maganar da zai gaya min na kwantar da hankali ne, da nuna min.
Ba wai na d'aga hankali na bane, amma kuma maganar gaskiya, bana jin dadin raina,.kawai ina daurewa ne dan kar na d'aga mishi hankali,

   Domin abin saura kwana uku, kuma nayi kokarin ganin na dauke kai na akan Mohan, amma na kasa domin komen kashin laifi idan yayi min, yanzun zan tsaya nayi ta balbale shi da masifa, zuba min ido yake na gama masifar sannan na fashe da kuka, toh a nan ne zai ta bani hakuri.

      Duk da haka bana iya dogon fushi dashi, a cikin saura kwana biyu, har gidan Khausar sai da ya kai ni, ya kuma kai ni gidan yan uwan baban shi da suke yan uba, Alhamdulillahi na samu kyakkyawar fahimta a tsakanin mu dasu, kuma sun mana fatan Alkhairi, dake mutum ne mai matukar ilimin dan adam, bai yarda na tafi hannu rabba ba, domin duk inda zan shiga yana min sayayya yace musu nice na kawo, wannan abin ya kara min matukar daraja a idanun dangin baban shi har suka fara adawa da Hanan. Musamman yan matan family din su, dayawa sun ki marawa Hanan baya, karshe suka shiga rokona.
"Don Allah Addah Munari ki amince ki auri Hammah Mohan, don Allah karki ki amincewa wallahi muna sonki". Wannan abin ya kara sani samun kwarin gwiwar son kasancewa da MOHAN. Sai dai abinda basu fahimta ba, duk soyayyar su matukar mahaifiyar shi bata yina ya zama na banza, matukar bata kaunata babu amfanin  zama dashi.

   Haka ana gobe za'ayi baikon ya kai ni gidan su dan Ba'are sabida akwai wasu daga cikin Familyn su da zasu zo, koda suka zo da kan shi ya kai ni. Domin har da Kakar shi ta gurin Uwa. Koda muka shiga gidan. Ba dukkan su bane suka yi na'am da ni ba, sai dattijuwar mai suna Nahnah. Ina shiga cikin dakin da take ta zuba min ido.

      "Ke bafulatanar ina ce?" Ta tambaye ni,
"Libya-Nijar" na bata amsa,
"Daga wacce kabilar kike?"
"Wodaadabe Bororo"
Rike hannuna tayi tsam, tana me lumshe idanunta. Kafin ta bude idanunta.
"Ya sunanki?"
"Maimunari!" Kura min ido tayi, na wani lokaci kafin tace min.
"Allah yayi miki albarka, ya kuma had'e kanku."

   Na kalle shi, murmushi yayi min tare da lumshe idanun shi, yana gyada min kai. Kafin muka fito tare da mika musu laidar da nazo musu dashi, ita kuma Nahnah na bata katon laida mai dauke da kunshi takarda a cikin shi kilishi ne.

Koda muka fito kallon juna muka yi tare da sakarwa junan mu, murmushi.
"Gaskiya kai dan babban gida ne, kawai baiko sai kace wanda za ayi bikin shi"
Hannun shi cikin aljuhun wandon shi yace min.
"Eh ya za'a yi dan ma sauran basu zo ba, amma da kin ga family mu ba karamin yawa ne dasu na, muna dayawa ainun. Kuma duk da haka Abbu yana ƙoƙarin kula dasu baki daya, duk da haka kawai manta."

"Idan naki fa? Amma dai gaskiya Allah yana son ka da ya kawo ka babban zuri'a gashi kowa yana sonka."

   "Sabida nima ina sonsu ba dan yanzun ba, ai da ina zuwa can na zauna. Toh aikin soja ba irin na kowa bane baka da lokacin kanka sai na kasarka. Insha Allah wani sati zan koma office."

"Lallai kace mazaje za a saka unifoam!"  Na fada mishi.

     "Wai haka" ya ce min yana murmushi,
Baki daya mun kashe lokacin yau a tare da juna, kuma mun yi dogon tafiya, kafin ya kira aka kawo mana mota, tunda ya kawo ni gida nayi sallah tare da cin abincin, muke hira har kusan sha biyun dare, kafin yayi min sallama.

    Washi gari
Baiko...

Ina kwance bana jin dadin raina, kawai dai ina kwance ni, gashi Abie ya ce ba sai nazo aiki ba yau, ina jin a raina kamar na rasa Mohan baki ɗaya.

     Wayata na lalluba ka kira Hammah Mohan.
"Hello!"
"Hmmm"
"Yau ne baikonka ko?"
"Eh"
Toh Allah ya yasanya Alkhairi, ba zan sami zuwa ba, Innah bata da lafiya zan je dubata a Damagaram"

"Karya kike! Ba zaki zo bane kawai nagode, kuma wallahi na fasa"
"Hammah Mohan, ka fahimce ni"
"Ba zan tab'a fahimtar ki ba, dan haka kiyi tafiyar ki, na gode dana na jima da fahimtar ni nake hauka nake ba, maza jeki Allah ya baki sa'a"
Ya kashe wayar, ajiyar zuciya na sauke na fito daga dakina ina sanye da riga da wando. Na kayan barci. Tura baki nayi tare da cillar da wayar na zauna ina dafe kaina.
....

Hidimar da ake zaka rantse da Allah biki Mohan din za ayi zunzurutun yadda aka kawata kome, a cikin gidan shugaban kasa ake kome, dan haka Hajiya Latifah an shirya a bangaren Hanan kawayenta ƴaƴan manyan mutane sun halara,

*_Gaskiya mura ya sani a gaba! Ba zan samu typing ɗin na dare ba_*
#Mai_Dambu...
[8/8, 7:33 PM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112326619?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=b5uzlwrsmnjDJy16UxrP%2B6c%2F7MtDoc5iAfHC4HQyJIms0PfUCslcpjPlXla74C0IG9WLlc5Su6cieJVelxnZUaqj64NLFkeQVg24jiQwUO0LftfuKKKLW5VGghOyRdvm

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.

"Toh ki shirya muje mana!" Kallonta  Auta nayi a shagwaɓe,
"Auta ina jin tsoro ne, kar naje a sami matsala."

"Ba gani ba" ta faɗa cikin tsokana,
"Kai Auta me zaki iya, keda ba karfi ne dake ba, balle ni"

Harara ta tayi sannan tace min.
"Baki da mutunci kona miskala zarati, na yarda bani da karfi..dan haka maza ki shirya muje lokacin na tafi karfe biyar za ayi fa!"

     Buga kofar mu akayi, ita ta tafi a hankali ta bude kofar.
"Kina niman waye?"
"MG Mohan ya aiko ni nayiwa. Maimunari kwalliyar"
"Toh shigo mana" ta bude kofar ta shigo. Juyawa nayi na kalle ta.
"Laa! Aunty Uwani shigo mana"
"Ya haka karfe hudu saura amma baki shirya ba, gashi can ya addabi rayuwata da kira. Uwani ki tabbatar kin fitar min da ita, Uwani ki gyara min fuskarta."

     Murmushi nayi domin indai Mohan ne zai rina.
"Aunty bari na watsa ruwa."
"Ok! Amma tsaya ga wannan"
Ta mika min wata jaka.
"Ki duba zaki ga yadda ake anfani da shi."

    "Toh nagode"
Tunda na shiga ban daki na shafa wannan, na goga wannan. Kai har su gashin hammata duk dai da na fitar, sannan na yi wanka da wani sabulu na musamman, na fito, zan goge jikina sai ga auta da wasu mai.
"Malama zauna na shafe ki!"
"Wallahi baki isa ganin jikina ba."
"Toh ko nakira Hammah Mohan ne dan nasan shi zai iya gani har can birnin lintsin" ta fada tana min dariya.
Bayana na yarda ta shafa min, sauran na shafa da kaina, bayan na gama na saka doguwar riga naje na zauna. Aka fara kwalliyar. Tun karfe hudu aka fara bamu gama ba, sai biyar saura minti biyar, sannan na mike na saka doguwar gown din da ya bani ranar, sai yanzun nake yabawa da shi,  dauko min wani set na bracelet diamond ja mai mugun kyau da tsada, dan kunnen shi da abin hannun shi, da wata zobe mai mugun kyau duk nashi. Sai yar siririn agogo duk nashi. Kallon shi nayi da kyau.

   Ina jin kwalla na cika a idanuna, jan hancina nayi sannan nace mata.
"Ban san iy adadin soyayyar da Mohan yake min ba, amma kyautar tayi min girma"
"Ke dai Allah ya tabbatar da alkhairi" inji Auta. Wani hula me kyau ta saka min bayan an shirya ni, sannan aka shiga daukar hoton, tare da tura mishi.

Sannan ta gyara auta itama tayi kyau sosai, buga mana kofa aka yi. Auta ta bude,
"Barka da zuwa Khalil"
"Yawwa Auta, kun shirya?"
"Eh! Uwani ai ba dan Surukata karta ga nayi azarbabbi ba da na je na dauko Beenah amma babu kom.."
Daukar wayar yayi yana faɗin.
"Banza kawai idan kayi hakuri zan kawo ta, kafin a saka maka. Shege mayyen mata"

"Zan ci Ubanka!"
"Na yarda, ku tashi kafin Mohan ya tawo dan ba kunya ce ta ishe shi ba."

Takalmin da aka ciro min na gani kamar zanyi kuka nace musu.
"WALLAHI tunda Uwata ta haife ni dau daya na saka irin wannan takalmin don Allah ku barshi, zan fad'i" jan kafana Aunty Uwani tayi sai da ta daka min ta daure min belt din, sannan ta mika min yar pose din, sannan ta shiga fesa min turare, sannan ta saka auta ta riko hannuna. Muka fito.

    Motar da ina da yakinin bai tab'a shigar ta ba, domin naga alamar sabuwa ce, bude min baya Khalil yayi sannan na shiga auta ta zauna kusa dani, muka fara ajiye Aunty Uwani a shagonta. Mika min wata jacket yayi tare da cewa.
"Mutumin ki yace ki saka."
Amsa nayi, tare da rikewa har muka shiga kofar farko na fadar shugaban kasa.

   Rike hannuna Auta tayi, tare da cewa.
"Sabida ke yau zan shiga fadar shugaban kasa, anya sunanki ba Noor ba!" Murmushi nayi tare da rike hannun ta. Muna shiga yayi parking, sannan ya kira shi.
"Gamu nan"
"Ok ka shigo da ita"
"Toh amma tare suke da kawarta."
"Ka hada ta da Radiyah"
"Ku fito" haka muka fita, sai da ya kira Radiyah ya hadata da Auta, sannan yayi min jagora, har shashinsa ta baya, muka shiga ya gama shiryawa yana saka links, na shiga da sallama. Duk falon da abokan shi, na wuce su, Hammah Khalil ya nuna min dakin na shiga, tare da sallama a karo na biyu.  Kaina a sunkuye, "ki karaso" yace min, a hankali na karasa inda yake.
"Me yasa kike wasa da hankalina?"
.hararan shi nayi sannan nace mishi.
"Ni banyi wasa da hankalin ka ba"
"Ok dan ina sonki sai ki ta wulakantani?" Shiru nayi, domin ya fara bani haushi.  Wayar shi ya tab'a sannan yace.
"Zoka tafi da ita"  duk wannan jarabar da yake wallhi ya juya min baya, yana shiryawa. A hankali na juya sakamakon kwankwasa kofar da aka yi. Mamaki na bashi da bance yayi hakuri ba, har na juya zan fita naji ya ce min.
"Baki iya bada hakuri bane?"
"Kayi hakuri"
Na fada, tare da barin d'akin, bin bayan ta yayi da ido, tare da tab'e baki, Munarih akwai ji da kai, hakurin ma a kasaice aka bada shi.  Dafe kirjin shi yayi yana faɗin.
"Wannan yarinya duk ranar da ta ga girma na.. na shiga uku"
"Baka shiga uku ba dan iska. K'ugun kawai na gaya maka a shirye suke ka auna min Ash'aria, ina kuma da macen da take gaban ka. Yarinyar sai kac.
"
"WALLAHI ka fadi surar matana sai naci mutuncin ka, billahi azim." Ya fada kokarin cire kayan zai daku da dan Ba'are.
"Kwantar da hankalinka, wallahi ba da manufa ba, akan me zan fadi wani abu, ai ko lokacin tana mata maza ma banga girman kirjin ba sai yau da aka saka."

Cire takalmin shi yayi tare da jifar shi da shi, yana faɗin.
"Ka tsaya mana dan Ubanka, na nuna maka rashin arziki. Mayyen mata kawai, kai kan ranar da ka kwana akan mace toh Billahi azim sai mun kaika turu."

Daga waje yace mishi.
"Eh na yarda ba laifina bane laifin kayan da suke bawa amaren ne, kai kuma ina da yakinin duk ranar da ka tabo dukiyar fulaninta, sai ka kwana goma kana hauka."

"Dan Ba'are!!!"
"Aghali!!"
"Zamu hadu dai na gaya maka rashin mutunci zan nuna maka bani da daraja!"

    Haka ya shiryo tare da fitowa, yana hararan su, kusan dukkan su abokai ne na family.
Wato suna ganin, shi suka kwashe da dariya, tare da cewa.
"Hammah Mohan!" Suka kira sunan kamar yadda Maimunari take kiran shi. Cikin nutsuwa da wata irin sanyi, ya yi gaba. Tare da nufar inda ake taron.

    .
Lokacin da  muka fito, ya kai ni inda aka tanadar domin mutane su zauna, bayan tafiyar shi dai ga Jalilah. Tana zuwa kawai ta watsa min ruwan a jikina. Allah yasa akan jacket din ta zuba, dai da na bari zata wuce kawai na saka mata kafa, faduwa tai sosai kamar yarinya karama, mik'ewa tayi yana kallona tare da nufo ni, nima na mike, mermaid   trappist gown  saka, take na taka Jelar gown ɗin tare da kallonta.

"Idan kika sake kika yi wani shirme zan ja takalmi na, kuma zai yaga kayan jikinki, ba zuwan ku nayi ba, dan haka wuce babu ruwana dake"

           A hankali na d'aga kafana kan Jelar gown din, babu musu ta wuce, jikinta yana mugun sanyi,. Sannan na koma na zauna, a hankali gurin ya shiga cika, manyan mutane da ga gwamnatin kasar suna shigowa.

   A hankali idanuna ya kai kan Abie, lokacin da yake gaisawa da manyan mutane, sannan na ciro wayata na tura mishi sakon.
"Abie kayi kyau cikin suite"

Duba wayar yayi tare da juyawa yana nima na, d'ago mishi hannu nayi ina murmushin jin dadi,  takowa yayi har inda nake ya zauna.
"Kinyi kyau"
"Nagode sosai"
Na fada ina risinawa, "taso muje na gabatar dake a gurin mutane."
"Toh " nace mishi, daidai isowar Mahaifiyar Hanan, tare da Hanan tana rike da hannun Mahaifiyarta. Sanye da wani masifaffen gown Royal blue, sanye da whiter gold kan nan babu mayafi balle dan kwali, ganin kishi zai sani na kauce hanya, nayi maza na dauke kai na. Tare da barin gurin baki daya.

  Na nufi wani gurin na zauna ina jin kwalla na zuba min, ina jin ka fara fadin ga Mohan nan, lokacin da suka saka kidan sojojin kasar tare da taken sojojin kasar, kafin aka fara gabatar da manyan mutanen da suka halarci taron, bayan babban Chef Imam ya gabatar addu'o'in, sannan ya sakawa baikon albarka.

Kafin MC din ya bayyana wasu abubuwan da suka danganci Mohan, a katon majigi. Tare da cewa.
"Muna bukatar  Khalil Ibrahim Dan Ba'are yazo ya gabatar mana da wannan bayanin akan MG Mohan"

   A hankali ya fito bayan ya gaida iyayen da yan uwa, sannan yace.
"Mohammed Mamman Nasir Mohammed Aghali, wanda muka fi sani da Mohan!."
Yadda yake bayanin abubuwan Cigaba da ya karu sosai da Mohan, da abubuwan. Sannan ya maida abin maganar.

    Nan a ka saka kidar taushi, wato (Cool music) kafin aka kira Mohan da Hanan iyaye suka saka musu albarka, tare da bayanin yanzun za ayi baikon tare da musayan zobba. Ina ganin haka na cire jacket din na ajiye musu a gurin, sannan na juya.
"Kafin ayi musayar zobe don Allah a bani minti biyar kacal!"
Ya fada yana kallon Dan Ba'are.
"Khalil tawo min da ita"
Nima na ya shiga yi,  kafin ya hango ina ƙoƙarin barin gurin, cikin sauri ya tawo tare da riko hannuna, cikin karfin hali da danne kukar da ya taso min na juya.
"Yana kiranki"
A hankali na juya tare bin bayan shi, muna isa kuwa hasken wutar da aka saka a gurin da na Cameras ya cika fuskana. Tun kafin na isa gaban Hanan ya gama faduwa.

"Ammyn ina me baki hakuri da abinda zanyi amma, iyakar gaskiya ce daga zuciyata.  Maimunari itace zab'ina amma duk da haka zan amshi Hanan a matsayin zabinki"

A hankali ya tako cikin wani irin izza da mulki, uwa uba kwarjini da isar shi tana kara bayyana akan fuskar shi, yana zuwa ya zuba gwiwar shi daya a kasa daya.
"Zaki Aure Ni.......
*_Wallahi mura ya dame Ni dakyar nayi wannan fa! Hahhhh Hajiya Lateefah! Hajiya Karime! Hanan! Jalilah! Zata fashe fa! Wai ina An Niger ne? Yasin ku fafata ko na tafi jinyar mura🤷🏽‍♀️🤷🏼‍♀️🏃🚶🤸_*
#Mai_Dambu......
[8/9, 10:29 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1112737045?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Zioa4Y%2F3Hu%2BHlUSk66YueQO%2BpbPAhg0irEJcowTIrXaYPT9Z1eBnkRuAOXMIzo1imod4QTdXoGp%2FGjSekGkrqI9y9tm6Kgi%2FKpQsmzrrREW8q3mkPoldIzQqc5mqaVfv

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARBA'IN DA TARA.

_Fatan Alkhairi ga shafin ku nan gaisuwar shi taku ce Yan Uwa Yan Nijar 😘🤝💓💞 sai kun gadama ku bawa wani domin wata miyar sai a makota 🤷🏼‍♀️🏃_


A hankali ya mika min hannun shi, tare da yar karamar kwatin da Haddir ya mika mishi.
"Je t'aime tellement! Je t'aime, je te protégerai de tout mon souffle, j'arrêterai de pleurer de toutes mes forces, je te protégerai de toute ma vie. Maimoon, je te critiquerai plus que quiconque, je t'aimerai plus que quiconque, j'arrêterai de pleurer. Je rirai de ton rire, je pleurerai et pleurerai ! crois moi je t'aime même dans mon sang ! Je t'aime de tout mon cœur, Maimunari je t'aime je te supplie de m'épouser !"  
      (Ina son ki sosai! Ina kaunarki ki, zan so ki da dukkan numfashina, ba zan taba barin ki kiyi kuka ba da dukkan karfina, zan kare ki da dukkan rayuwata. Maimoon, zan ba ririta Al'amarin ki fiye da kowa,   Zan yi dariya da dariyar ki, zan yi kuka da kukan ki! ni ina son ki da dukkan  rayuwata! Ina son ki da dukkan zuciyata, Maimunari ina son ki ina rokon ki da ki aure ni!). Fasali yaja tare da kallon mahaifiyar shi, sannan ya taka har gaban ta, yace Mata.

"Ammyn idan ina tare dake Mantawa nake da ita, idan ina tare da ita tunawa nake dake, sabida babu mace da ta cancanci na d'aga darajarta sama dake," sannan na cigaba da cewa cikin Faransa. Tare da komawa gaban Maimunari.
"J'élèverai votre dignité et votre valeur devant tout le monde, j'élèverai votre cause devant tout le monde ! je vous respecterai je respecte votre famille aussi longtemps que vous restez avec moi!"
(Zan d'aga darajar ki da kimar ki a gaban kowaye, zan ririta Al'amarin ki a gaban kowaye! zan girmama ki na girmama danginki matuƙar zaki zauna dani!)

         A hankali ya mika min hannu, tare da kallona. Baki daya jama'ar gurin tafi suke mishi, sabida yadda yake amayar da soyayyar shi, kamar wanda aka sakawa wani abu.

    Idan ka cire Hajiya Lateefah da jikinta yake rawa, bata kaunar ta b'ata kome, Amma tabbas idan ranta ya kai dubu ya b'aci sosai, domin har duhu duhu take gani.
"Maimunari! Gani a gaban ki, ga jama'a a zagaye damu. Maimunari ina kaunar ganinki cikin farin ciki da! Bani hannunki na saka miki."

     Wani irin kuka nake mara sauti,ina kallon shi. Tare da mika mishi hannu nawa, a hankali ya rike tare da saka min zuben danyen zinari wanda aka saka mishi dutse mai daraja akan shi na lu'ulu'u, tafi gurin ya dauka ina kuka tare da kallon shi, mika min karamin akwati Dan Ba'are yayi na cire zoben azurfa har da agogon shi an daura mishi madubin dutse mai daraja, haka na cire zoben na saka mishi, kwalla na zuba min, sanan na cire agogon na saka mishi,  tare da kifa kaina ka gefen hannun shi ina kuka,  a hankali ya taka har gaban Hanan ya dauki zoben da aka tanadar domin ya saka mata ya riko hannunta, ya saka mata, karfin hali take kawai amma ta gama firgita bata cikin hayacinta, kallon zoben take. Jikinta har rawa yake,. Duk abinda ya bukata ba ita ya bawa ba. Wa wancan kaskantarciyar ya bawa!

    Hatta kayan da ta saka ita ce ta zab'i na jikinta amma daga baya ta tura mishi kalar jan yaki kulata, ita da kanta ta zab'i jan bracelet diamond, amma ai gashi ta gani a jikin Maimunari. Kallon uwarta tayi hawaye na tsinkewa daga idanunta, da kyar ta samu tabbar gurin ba ita daya ba. Hatta Hajiya Lateefah da take jin kamar ya cire zucuyarta ta huta, kallon mu tayi, tana kara jin tsana da bakin cikin kamar ta shiga filin tayi ta dukar Mohan da Maimunari.

           A hankali aka saka kida mara sauti dan haka. Ya cigaba da cewa.
"A lokacin da duniya ta manta da Alkhairi na, da aikin

Please Login or Register in order to submit comment