Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda zai dakatar da wani.....

_#girmamawa.... Zaku yi min hakuri da Uzuri na kwanaki biyar Insha Allah, zan kammala Aliyu Asadullah ne Insha Allah don Allah ku gafarce ni, na san zan saka ku jiran amma Insha Allah idan na kammala, zan baku dogon page ina muku fatan Alkhairi 👏 And wallahi naga comments din Wattpad da vote yayi kasa, Insha Allah idan na dawo toh wallahi zan muku irin na zanen ƙaddara ta ne Yanxun haka yana Okada 700₦ zaka saya da shi da sauran books dina na kuɗi zaku iya samun shi a Okada, so ku motsa idan ba haka ba nima next zan bada a WhatsApp, kuma idan kika biyo ni daga Wattpad wallahi saya zaki yi shi yasa nake baku a free, idan ya koma WhatsApp toh wallahi ina gama book 1 Insha ALLAH zan kai Okada 2 ma haka. So ku karanta kafin na kai inda zan jin karan kuɗi 🤣🤸😛😜🤣😂_
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx

_Alhamdulillahi books dina baki daya wanda nayi su na kuɗi suna Okada akwai masu cewa suna bukata basu da Whatsp toh ga dama ta samu ku garzaya Okada na akwai su baki daya a can da sunan RamlatArManga_

Sauyin Yanayi...

BABI NA TAKWAS.

Tsagaita dariyar yayi yana kallon Mamoon.
"Me yasa ka dariya?"
Had'iye dariyar yayi sannan yace mishi.
"Cewa kayi ka zare, shi yasa nake dariya ban kuma ga ta yadda ka zare ba shi yasa"
B'ata rai malam Ansar yayi cikin damuwa yace mishi.
"Da gaske na zare da, wallahi ka bar batun wasa, ina cikin damuwa kuma naji a raina na gaya maka ko zaka taimaka min" ajiye shiririta yayi a gefe guda, sannan ya fuskance shi.
"Ina cikin soyayya mara iyaka, kuma na kasa fahimtar kuskuren da nake shirin aikatawa, shi zaka iya fahimtar dani?"

Murmushi Mamoon yayi sannan yace mishi.
"Ina ga kayi ƙoƙarin fitar da abinda yake ranka ga ita abar kaunar taka, zai fi ka rike abu a ranka kana yawo dashi."

   "Kana ganin idan nayi haka babu laifi?" Shiru Almamoon yayi yana kallon shi, kafin yace mishi.
"Babu laifi matukar haka ba zai haifar da matsalolin a tsakanin ku ba"

   Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Almamoon, ba irin soyayyar da kake tsammanin bane, SOYAYYA ce wacce duniya zata iya kirana da mahaukaci, Almamoon ina cikin jarabawar so, idan na fitar kyamata za ayi." Ya fada kamar zai yi kuka,
"Idan kace sai duniya ta baka lambar yabo ne akan abinda kake Muradin zaka mutu baka sami abinda kake so ba, rayuwar duniya cike yake da dimauta dan haka ka rufe idanunka, ka gayawa zuciyarka muradinka zaka bi ba muradun wasu ba"

"Almamoon! Ba yadda kake tsammani bane, ina jin tsoron fitarwa ne" ya faɗa a sanyayye,
Bude mota Almamoon yayi tare da cewa.
"Toh ka kashe soyayyar bata da anfani matukar ba zata amfani wanda ake dominta ba, Malam bari na gaya maka tunda nake ban tab'a son wani abu a raina ba, idan kaga ina son abu toh tabbas abin me daraja ne, malam ko da ake surutu akan mu wallahi wai muna mummunan alaƙa, malam da ace mace ce Ni ba zan tab'a baka matsayin masoyi ba, matsayin Yaya ne kake min. Ban tab'a jin ko fadawa yanayin ina sonka ba, kayi hakuri gaskiya na gaya maka, amma ina mutumtaka sama da yadda kake tuna, kai Ubane min, shi yasa tunda naga kana kokarin tsayawa rayuwata ya sani maka kallon Babban Yayana."

Kamar wanda aka watsa mishi ruwan sanyi kalau, abin tausayi jikin shi yaji mugun mugun sanyi. Duk haukar da yake ashe da gaske da sikago yake raye, murmushin karfin hali yayi sannan yace mishi.
"Balle kuma waye zai yi soyayyar jinsin ai haramun ce" yana dariya me mugun ciwo, haka ya fita daga motar suna kallon yadda dalibai suka watse, kowa ya kama gaban shi.

    "Almamoon" aka kira sunan shi. Wasu yan mata da samari ne na departmen din su.
"Wai shin kai mace ce ko namiji? Ko dai mata maza ne bamu sani ba? Ai toh ko dai dan daudu ne musu mu duba dan kamfen ka"

     Suka fada tare da kwashewa da dariya. Murmushi yayi sannan yace musu. Kallon su yayi na wani lokaci, kafin ya tab'e bakin shi, yace musu.
"Yo ku nan mata ne? Na zata kartin maza ne da sufar mata" ya fadi haka tare da barin gurin, yana. Zunzurutun maganar tayi musu zafi kallon kansu suke kawai cikin tashin hankali.

      "Ta ina muka yi kama da maza?" Suka juya suna niman wanda zai ganar musu da cewa basu kama da maza. Dariya samarin suka yi tare da cewa.
"Amma Mamoon dan iska ne, duk duniya ban tab'a ganin mutumin da maganar shi take daidai da amsar mutane kamar Almamoon ba."

        Cikin fushi wata yarinya me suna Bara'atu ta kwasa da gudu, ta nufi inda Almamoon yake tsaye zai shiga aji ta janyo rigar shi dai da ya kusan faduwar.
"Kai wai namiji ne?"

"A'a kece a tsaye" ya bata amsa zai shiga cikin aji,
"Dan daudu kawai" ta gaya mishi haka, wata shegiyar dariya yayi sannan yace mata.
"Don Allah waye mai madubi a cikin ajin nan?" Ai kuwa aka samu wata ta mika mishi ya karba a yangance yace mata.
"Ina ga kamar baki tab'a kallon kanki a madubi bane, amma babu wacce ta kai ki sufar maza duk cikin makarantar nan. Mai fuskar maza kawai"

       "Banza jaki dan luwadi kawai?" Cak ya tsaya yana kallon ta, kafin ya sake murmushi me ciwo, sannan yace mata.
"Toh nagode, jakar aji"  ya fadi haka yana me barin gurin ta, da gaske kalmar ta dake shi, ihu ta saka tana me sake kokarin shigowa ajin dalibai yan ajin suka hanata.
"Kin zage shi ya rama, kin gaya mishi magana ya rama, yanzun ma kin gaya mishi ya kuma Ramawa me kike so ki mishi? Ba zaki hakura ba kenan?"

      Wani takaici ne ya kamata,  ta shiga ihu tana faɗin.
"Dan luwadi kawai mata maza, mara amfani kai har ka mutu haka zaka kare, kai ba mace ba kai ba namiji ba, dan iska karuwan namiji kawali kawai."

     Kifa kai yayi a kan kujerar shi, yana shashekar kuka, sabida kalmomin sun mishi nauyi, karewa Malam Ansar aka kira, shi yazo ya fatattaki yarinyar,  ya shigo ajin. Dukar kujeran yayi yana kallon shi.
"Ina jiranka a Office" ya faɗa tare da juyawa ya fita, ya kai minti goma kafin ya mike a sanyayye, su kansu yan ajin yau daya sai da suka ji babu dad'i, a hankali ya nufi ofishin Malam Ansar.

Yana shiga ya nuna mishi kujera bayan ya mike tare da dauko mishi ruwa ya bashi, amsa yayi. Har lokacin kuka yaƙe. Bai hana shi ba.
"Meye dan ta faɗa maka abinda ba halin ka ba? Meye dan kawai ta fadi abinda bai zama dole a yarda ba? Kayi shiru ka daina kukan nan haka"

"Zan tafi Damagaram."
"Me yasa zaka tafi kuna tsakiyar karatu, idan itace kayi hakuri zan saka a dauki mataki akan ta kaji" mik'ewa yayi zai fita ya riko hannun shi,  juyawa Almamoon yayi tare da kwace hannun shi.
"Don Allah karka min mummunar fahimta, kayi Hakuri" da sauri ya bude kofar ya fita. Ya kasa a guje yana kuka,aji ya shiga tare da ɗaukar jakan shi ya bar makarantar, bai tsaya ba, sai a can wajen makarantar ya tsaya tare da share kwalla. Abinda bai tab'a yi ba shi yayi yau.

Tafiya yawo a cikin gari tafiya sosai bai koma gida ba dai karshe biyu na rana, ya isa gida a gajiye, wanka yayi sannan ya kulle kanshi a dakin dan tun shigowa gidan bai ga motar malam Ansar ba, ya tabbatar bai dawo ba..a sadadde ya shiga cikin gidan.

  Tare da nufar dakin shi, cikin dakakkiyar murya yace mishi.
"Ka gama yawon?" A razane jikin shi na rawa, ya juya yana me fuskarta malam Ansar, wanda ya tako har gaban shi. Sai da suka kure bango. Kauda kanshi yayi tare da cewa.
"Don Allah ka matsa a kusa dani, wallahi bana jin dadin yadda kake min, idan kana min haka zan na gani kamar ba taimako na zaka yi ba, wata Muradin ce da kai." Ya fada muryan shi tana rawa kamar zai fasa kuka,
"Ni ban fasa kuka ba sai kai?"

Makwat ya had'iye wata irin yawu da ta tsaya mishi a wuya, dakyar wanda yayi imani da Allah, yafi gayan tuwo wahalar wucewa ta wuyar shi.

"Meye kace? Kana min kallon ne kamar yadda suke min? Na zata ko zasu min kallon haka kai ba zaka min ba ashe hasashe na ne haka? Almamoon naji mamaki da abinda kake fassara Ni dashi."

       Daga haka ya matsa a gaban shi ya wuce dakin shi, abin shi yana jin kamar zuciyar shi zata buga, zama yayi tare da fashewa da kuka. Ganin kukan ba zai kare shi da kome ba ya nufi dakin shi.. rufe kofar yayi tare da nufar ban daki.

     Bayan ya fito ne, ya kwanta a kasa, yana jin kewar gida da iyayenshi.

Haka har gari ya waye, ya kuma fita ko karyawa bai yi ba, yayi tafiyar shi bai dawo ba sai can la'asar sakaliya, yana shiga ya samu Baba Mari ta fito gidan, cikin kulawa ta kalle shi.
"Angona Barka da yamma" kunya ce ta kama shi yace mata.
"Kiyi hakuri Baba ina wuni? Ya aiki da zafi"
"Alhamdulillahi! Ka dawo makarantar ne?"
"Eh wallahi" ya faɗa tare da gotawa ta gefenta, wani irin jan iska tayi da hancin ta, sannan ta bi bayan shi da ido. Haka kawai take jin wani irin abu a ranta dangane da yaron, sai kuma ta share tare da nufar inda gidanta yake, har ta zauna tana tunanin yaron.
      Haka suka ci-gaba da zama duk da babu wani kyakyawan mu'amalar da zata nuna maka ana shiri kamar baya tsakanin Ansar da Mamoon, haka bai hana shi ajiye mishi duk abinda yake bukata ba kusan har aka gama zangon karatun suka yi jarabawar da hutu, babu wata kyakyawan fahimta.

     A daren yau hada kayan shi yayi tare da tattara duk wani abu, haka kawai yake jin faduwar gaba, dan haka koda ya gama ji yaƙe kamar yayi ta kuka, dan bai san meke faruwa dashi ba.
            Haka ya gama had'a kayan shi, sai gashi an dan kira su sakamakon wasu dalilai ba zasu tafi hutu ba, sai watan gaba. Dan dole ya hakura amma a ranshi kewar gida yake, idan ya tafi makarantar dakyar yake fahimtar abinda ake duk da sati biyu ya rage ayi musu hutun, haka dai suka yi ta maida hankali da abinda ya rike su a makaranta.

   Yawan mafarkai da tashin hankali na faduwar gaba yasa shi kasa sukuni, abin da ya haifar mishi da zazzaɓin da ya kwantar dashi, Almamoon yana da makon iyaye, ya saka iyayen shi a ranshi. Har gida aka saka mishi ruwa dan yaki zuwa asibitin.

"Likita ka duba shi da kyau, yana yawan kukan ciwon ciki?" Zaro idanu yayi yana kallon likitan.
"Toh dan bamu guri"
Haka ya fita ya basu guri sun jima suna tattaunawa, kafin likitan ya saka mishi ruwa da allurai. Bayan tafiyar likitan Malam Ansar ya shigo ya mika mishi magani.
"Sannun Insha Allah zan tambaya maka damar tafiya gida ko" gyada kai yayi sannan yace mishi.
"Nagode"
Ya fada a hankali, yau kan yadda yake kwance ba lafiya muryan tafi kowa yaushe kamancecceniya da ta mata.
"Yau kam kamar mace ka fito kayi laushi! And anya kai ba mata m.."
Wani kallon banza ya watsa mishi.
"A'a mazan mata ne ba mata maza, ba dalla fita ka bani guri" ya faɗa yana b'ata rai, dan dole ya fita daga d'akin.

           ---- Washi gari bayan likitan yazo ya cire mishi ruwan tare da kara mishi allurai, sannan ya tafi. Can da yamma Ya fito diban ruwa a kicin suka yi kicibis da Baba itama ta gama abincin zata leka shi ta koma gidanta.
"Ya jikinka Mamoon?"
"Da sauki Baba mari" ya faɗa a sanyayye, sake zuba mishi ido tayi zuciyarta tana wani irin bugawa kamar zata tsage, ta rasa me zata iya fahimta.  Shiga kitchen ɗin tayi tana mishi wani irin kallo.
"Waye kai?" Ta tambaye shi,
"Ban gane ba, Baba Ni ne Almamoon fa"
"Ba sunan nakeson ji ba, kai mace ce ko Namiji?"
Gabansa ya fad'i, ya kalli kofar shiga abinka da kuruciya, sai ya rud'e tare da jin kamar an watsa mishi ruwan sanyi.
"Baba don Allah"
"Bani zaka roka ba bayanka zaka Duba, kai mata maza ne?" Kuka ne ya kwace mishi yana girgiza kai.
"Toh amma ai jini ne a bayan wandon ka" ta faɗa mishi. Da gudu ya juya zai fita suka yi kicibis da Malam Ansar, durkushewa yayi cikin matsanancin kunya da kuka.

    "Don Allah karku gayawa kowa, ban san na b'ata jikina bane" ya faɗa yana kuka, mutuwar tsaye malam Ansar yayi tare da sake kayan da yake hannun shi yana kallon shi. Cike da mamaki da mugun al'ajabi.
"Toh meye haka yake nufi? Shin kai mace ce ko namiji, ko mata maza ne?"
"A'a ni m.." ya kasa fitar da koda kalama daya ce, sai kuka da yake,.yana ganin kamar yaci amanar iyayen shi.

    "Tashi muje asibiti ya faɗa a haukace" inji malam Ansar,

Cikin wani irin kuka me matuƙar ban tausayi, yace.
"Nace bana so! Abinda kuke son sani shine ni." Ya kasa furta kome sakamakon tuno yadda Iyayen shi suka yi ta rokon shi, ta shi yayi ya shiga daki tare da rufe kofar, ya jingina da kofar yana wani irin kuka.

Da sauri ya shiga ban daki ta cire kayan shi, ya wanke wandon ya durkusa ya ci kuka kamar idanun shi zasu fita, "me yasa aka halicce ni haka?  Me yasa na kasance haka? Me yasa ba a damu da nawa nau'in ba? Haka zan gama rayuwata? Ko haka ne zai saka na."

Kuka ya sake me mugun karfi tare da zama ya kusa kanshi a tsakanin cinyoyin shi, kunzugun shi ya dauka ya gyara tare da ɗaukar wata gajeren wando ya saka tare da boye kanshi, ya ki fita ma a ban dakin balle ya koma dakin shi.

     .... Kallon juna suka yi daga Baba Mari zuwa Malam Ansar.
"Toh amma ina ganin kamar jinsi biyu ne dashi,. Kuma baya son ta faɗa"
Kamar ruwa ya cinye malam Ansar ya kalli Baba Mari, kafin tace mata.
"Baba bana tunanin haka sai dai ina ganin kamar mace ce" ya faɗa a sanyayye, sama da koda yaushe,  haka wunin ranar suka yi shi.

  Jacader

   Tun daga titin da zai kai ka cikin Unguwar zaka Fahimci unguwa ce ta masu hannun da shuni, wato attajirai masu kuɗi, yan siyasa da yan kasuwa, manyan mutane na cikin garin Maradi.

       Hukumar yan sanda ne zaka fara cin karo dasu, wanda sun kai kimanin dubu daya, a barbaje cikin unifoam, idan kayi tafiya gaba zaka taradda hukumar jami'an tsaron ko takwana wanda suke sanye da wasu kayan yaki, su kimanin dubu daya.

Gaban su kadan idan ka wuce shigen wato (checkpoint) hukumar kunce bom ne koda za a ratsa tsakanin su a kawo harin bazata, suma kimanin dari biyar da kayan aikin su. Sai gaba hukumar fasakorin shige da fice wato (custom,)  suma a nasu checkpoint, su kimanin dari bakwai, idan ka wuce su nan zaka samu get da zai kai ka first get, inda aka saka hukumar immigration, wanda sun kai dari uku a gurin, idan ka wuce get din zaka nufi get me dauke da Ash color wanda aka saka katin Stamp na Niger republic Army. Sojojin ne birji daga sojojin ƙasa, zuwa sojojin sama. Sai daura drum suke ana binciken sirri.

A gaban kadan wasu manyan mutane ne zaune duk wanda zai shiga cikin gidan bayan ya tsallake wadancan checkpoint, sai ya isa gurin su, anan za a saka abu a duba ka har cikin jikinka sai an duba ka,

  Idan mata ne akwai jami'an tsaron mata, suke kome na bangaren mata,  wani katon legendary house wanda za a iya kiran shi da Mansion, a tsakiyar katon fili, anyi ginin gidan kamar yadda akayi gina shi kamar bujr arab, wato wani hikima irinta fasihai kwararrun maganin duniya aka tara suka gina gidan, idan daga nesa ka hango zaka dauka kamar daukar gidan aka yi aka daura a saman koramar ruwa.

   Domin kuwa cikin tsari da baiwa irinta ma'abota hankali suka gina gidan a saman ruwa, kamar an dauki gidan ne aka daura a saman ruwa.  Daga nisa kana hango cikin ruwan.  Gidan da aka gina kamar gidan sama me hawa biyu, amma kuma Normal mansion ce,  sannan anyi tubalin gina zaman a jikin gidan yadda kana kallon shi zaka Fahimci wannan ginin ya kai makura a haduwa, haka roof din gidan yadda kasan kwalba aka saka a saman gidan,  gidan kewaye yake da manyan dogayen bishiyar dabino, ta gefen gidan kuwa wani kyakyawan lambu ce me dauke da manyan Swam wato agwagwan ruwa na kasar Austaraliya, lambun dankare yake da kayan ciye ciye, sannan akwai wasu kyawawan dawisu, fararre, daga can ƙasar China aka zo dasu.

     Ta gaban gidan kuwa parking lot ne, me dauke da manyan motoci guda biyar, BMW, Phantom, Mercedes Benz, sai Range, da Toyota Tacoma. Sai watan katuwar bike na kamfanin Nissan wacce aka mata ƙatuwar Stamp na sojojin. Gefe can hilux ce 40×40, army color.  A jikin kusan da motar wani katon daki ne me dauke da Police Dog,  lion dog, wadannan karanunakan ba a cika samun su a ko ina ba sai a China da Japan.

      Domin kowani guda daya ya kai girma giant Ram, wato katon rago irin me murdaddiyan kaho. Ko ina ma gidan dauke yake da Cctv. Duk inda ka gifta kuwa.
Can bayan gidan sosai, akwai BQ, inda gabaki daya ma'aikatan gidan suke.
   Cikin gidan me dauke da dakuna biyar uku a sama biyu a kasa.
    Dakuna ukun saman dakin mamallakin gidan ne,  biyu dakin kwana ne, daya kuma dakin al'amuran shi ne, gefen dakin wani study room ne, sai backyard me dauke da yar karamar gurin hutawa me kyau. An Kawata shi da wasu irin kujeru na musamman guda uku, duk yadda aka yi an tsara gidan ne daga mace daya da yaran su, sai abinda ba za a rasa ba.

      Daga step din da zai kai ka kasa an shimfid'a India capter. Red and Golden,. Sannan paint na gidan dauke yake da grey color sai minti colour. Dakin farko na sama, wanda aka zuba wasu mahaukatan furnitures daga Korea aka yi oda dinsu, kome na dakin Royal blue ne, sai furnictures din da paint dakin ya kasance cream colour. Daya dakin kuma dauke yake da simple design furnitures, whiter and Black, haka ma labulayen dakin. Fari ne me digon baki.

       Sai tiles da aka saka a kasan dakin yayi mugun yiwa dakin kyau. Haka ma wancan dakin shima tiles din shi me kyau ne.

    ... Dakin kasa kuwa daya dakin dauke yake da kome cream And Golden, yayi masifar kyau haka ma Furnictures din shi. Daya dakin kuwa dauke yake da blue and pink paint, kome na dakin Blue And pink ne, idan ka nutsu zaka ga har kayan wasa an ware.

    ....
Falon me dauke da ƙatuwar cimma tv, baya kome a kashe yake. Sai falon da yake kawace da manyan sofa, har guda ashirin da hudu,, sabida girman falon.

          Kuma ba wai a guri daya ba, a'a kowani kusurwa a jiye yake da sofar shi. Wato kujeru. A can gaba da fakon wata luxury kitchen ne, wanda idan da zaka kira shi da modern kowani suna duk daya ne.  Ma'aikata kusan shida ne. Kitchen ɗin suna aikin girki kawai, idan kaga yadda suke aiki zaka Fahimci sun gama gajiya da aikin kawai dan albashin su, sukewa wannan hidimar.

   A falon akwai wani hoton family, me dauke da hoton Wani kyakyawan Matashin Soja, dan kimanin shekaru arba'in a duniya, murmushi yake ana saka makon lambar karin matsayi. Kasar hoton an saka Firaministan Mamman Nasir Aghali.  Da Major General Mohan Mamman Nasir Aghali. Jarumin sojan kasar Nijar.
Fari kyakyawa ajin farko, dogo murdaddiyan jiki, ma'abocin manyan idanunawa da zunzurutun kwarjini.

       A watan Fabrairu waki'a ta faɗa mishi mara dadin ji, ana gab da fara bikin shi wanda ya rage sati Daya a fara, babban da ga Firaministan kasar Nijar, kuma shine kashin bayan mulkin mahaifin shi, sai dai kuma abin tausayin da ya faɗa mishi a filin yaki.

  Mamman Nasir Aghali. Shine firaministan Nijar, kuma shugaba me adalci, da son talakawan shi, mutumin da bai dauki duniya da zafi ba. Dan kimanin shekara saba'in da tara, duk da ya girma amma shugaba na gari ne, kuma adalin shugaba.

Da ake matukar kaunar shi a kasar Nijar baki daya, kuma shugaban kungiyar kasashen Afrika baki daya,yana da mata biyu. Yara goma maza uku mata bakwai.

Hajiya Latifah itace matar shi na saurayi da budurwa, kuma buzuwar Agadaz ce wacce al'ummar kasar ke mata lakabi da farar mace alkyabar mata. Duk inda kake niman Jarumar mace idan kayi katarin haduwa da ita ka samu. mahaifinta shahararren dan kasuwa ne mazaunin garin Tripoli na kasar Libya.

Kasancewar ta taso daga wata kasar ta sami ilimin boko sosai me zurfi, haka ta sami na Addinin fiyye da yadda kake tuna, sai dai mace ce da take da d'agawa da son mulki, mace ce da take son Nasaba da kusancin mai kyau, shi yasa bata mu'amala da kananun masu hannu da shuni kuma uwa uba tana da nasaba da Gidaj Sarautan Agadaz tana da yara shida.
Mohan kuma babban Sojar ƙasar shine babban ɗan ta, shi yasa taci alwashin dan ta macen da zata aure shi sai ta haɗa Kyakyawan tarihi da nasaba. Sai Hadder shine yake bin Mohan, yana kasar Faransa yana koyarwa, sai Salman yana kasar Nigeriya, yana aiki a ofishin jakadancin Nijar a Nijeriya,sai Khausar Likitan mata ne na babban Asibitin Nijar da yake Niamey, sai Radiyah, tana karatun ta a jami'a, sai Karamar su Nairah tana matakin sakandiri.

Amaryan Mamman Nasir Aghali Safiya. Tana da yara huɗu duk mata, Mansura, Mahnoor, Hinduh, sai yar karamar su, Tawakaltu.

A zahiran ce zaman lafiya a gidan sai a slow, domin Hajiya Latifah mulki take da Kowa hatta shi kanshi Firaminista sai yadda tayi dashi, sam Safiya bata gabanshi, idan ka ganshi a dakin Safiya ko tazo dakin shi dauki haka a matsayin babban al'amari ne na rabo ya dauko ta, haka yayi mugun fusatatta, domin itama yar babban gida ce, amma aka maida ta kamar baiwa. Dan haka bata tab'a wani yunkurin dan kwatar kanta ba, amma kuma a hankali ta lalata gidan, a zahiran ce sai da ta watsar da Yaran Hajiya Latifah, ta hana su shiga jikin Uwar su, ta kama su duk.ta rike su, kuma bawai dan Allah bane no cutar dasu take na fitan hankali.

Mutum daya ne yafi karfin ta, Mohan Mamman Nasir Aghali, mutum ne mai matukar ilimin addini da na siyasa, duk yadda ka zo Mishi yasan take taken ka. Takai Mohan ba iya ita ba hatta mutanen da suke jikin Mahaifin shi shakkar shi suke, domin ya zamewa Mahaifin shi garkuwa, duk wanda yayi yunkurin cutar da Mahaifin shi tabbas sai dai kayi a wani gurin amma da'iran da yake karyan ka.

Sabida dalilin haka, aka tsane shi babu irin sukan da ba akayi wa mahaifin shi ba, amma zai kira shi yayi ta Mishi fada, daga baya idan suka keb'e yakance Mishi.
"Babana Ka kara himma akan na da, mutanen da suke kewaye dani basu san Allah ba, babu Allah a zuciyar su."

"Insha Allah Abbih zan yi iya kokari na, na baku kariyan da ta dace." Tun lokacin ma bai samu matsayin Firaministan ba ma ake gwagwarmaya da munafukai, lokacin da ya samu Mohan ya kai matakin babba A soja, sai aka yi ta gayawa Uban ai zai Mishi juyin mulki. Ko dar uban bai tab'a ji ba akan Dan shi dan yasan abinda ya

Please Login or Register in order to submit comment