Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan, amma me yasa" murmushi nayi sannan na cigaba da wasa da hannuna.

      Riko hannun yayi yana faɗin.
"Moonah kin min adalci?" Sunkuyar da kai nayi ina gyara zaman mayafina.
"Ba haka bane, naso nayi maka bayani amma baka saurare ni ba, ka mai da batuna shirme."

"Moonah!"
"Na'am Hammah na."
"Me kike ji a kaina?"
Kallon shi nayi kafin na mai da hankali na, kan yatsuna.
"Alkalamin ƙaddara ta zana kaddarar mu tare, sai Yau da nake tare da kai sai nake ga kamar nayi shishigi da son kaina dayawa, na zake dayawa. Sam na manta da akwai irin wannan lokacin, gani nake kamar  ni din Yar kaina ce, sai yanzun da gari ya waye na Fahimci wacece ni."

          Na kai hannu zan bude kofar motar, rike ni yayi yana kallona.
"Me yasa kike son kawo wani damuwa kuma?"
Juyawa nayi na kalli hannun shi da yake rike da hannuna. Wani irin kallo na mishi wanda yasa shi saurin sake mayafin. Murmushi nayi domin ya burge ni yadda yayi saurin fahimtar yanzun ba da bane.
"Ni da kai muna da banbanci fa, Kai dan Shugabanan kasa ne, ni kuma ko dagaci Ubana bai rike ba, dan haka yana da kai ka fahimci wani abu, kawai alaƙar mu a iya abota ne bayan haka bana jin akwai wani abu da za...."

       "Bana son jin haka!" Ya fada da karfi,
"Kin san yadda maganarnki yake kona min rai?"
A hankali na bude motar na fito, ina kallon waje, shima fitowa yayi tare da zuba hannun shi cikin aljuhun wando shi. Sai yanzun na kare mishi kallo ya hadu sama da kullum. Dauke kai anyi ina wasa da hannuna.
"Me yasa?"
"Ban sani ba, amma koma meye ai suna da hujjar bani abinda ya dace, koma meye suna da ikon  sauya min ra'ayina."

"Amma basu da ikon sauya miki ƙaddaran ki, basu da ikon sauya miki goben ki, ki tsaya a matsayin mace kamar arziki ne" murmushi nayi sannan nace mishi .

"Gobe na? Ƙaddara ta? Yau nake dashi gobe bani da kome sai abinda Allah ya bani." Rike hannuna yayi sabida ya lura tafiya zan yi, juyawa nayi tare da zame hannuna cikin nashi.
"Ka gane yanzun da baya akwai banbancin, idan da shaidan bai samu galaba akan mu ba, a yanzun da muka san kan mu zai iya samun damar shiga rayuwar mu."

"Har ila yau ba ki faɗa min me kike ji a kaina ba" murmushi nayi sannan na juya ina faɗin.
"Bana jin kome a raina akanka, asalima sai yanzun na fahimci kai Mutum ne mai matukar gundura da hawa kai"

    Cafko ni yayi tare da sake dariya, yana mai d'aga ni sama, dariya nake kamar zan zauce.
"Tun ba yau ba na gaya miki yadda nake jin ki a rayuwata Me yasa ba zaki gaya min yadda kike jina ba?"  Sauke ni yayi yana kallon yadda nake wani jijjiga, tare da mai da kaina kamar mazari na nakasa rayuwa guri daya.
"Idan na gaya maka yadda nake jin ka me zaka bani?" Na hada index fingers dina ina buga su.

"Kawai zan tafi gidan tv na basu labarin kaunar da nake miki ne"
" A wannan shekarun naka?" Na tambaye shi ina wani hararan shi.
"Ayya kuma ta nan kika ɓullo min? Me kika fito yi toh" Ya tambaye ni,
Tab'e baki nayi ina kallon shi, kafin na yatsina fuska ina faɗin.
" Kuka na fito yi, amma da na ganka sai na ji na hakura. Ban cika damuwa da kome bane kaje idan na san me nake ji zan kira ka na gaya maka."

     Shiru muka yi tare da kallon juna, kafin ya juya tare da shiga motar yana faɗin.
"Ubangiji yasa karki gaya min, aikin banza aikin wofi" ya buga motar. Dariya ya bani, san haka ina kallon suka bar unguwar gyara zaman mayafina nayi tare da saka hula, na nufi gida.

   Lokacin da na shiga cikin gidan, Innah tana kallona ganin na shigo da walwala yasa tace min.
"Me ka samu?"
"Babu" na wuce dakin.
"Mamoon!" Da sauri na fito,
"Meke damunka?"
"Babu"
"Zo ka gaya min?"

Cikin tsoro da abinda zan tambaye ta, yasa Ni zare ido. Kirjina yana mugun bugawa kamar zai b'alle,
"Me yasa ka damuwa?"

   Shiru nayi ina kallon ta, kafin ba ce mata.
"Innah me yasa?" Shiru nayi,
"Me yasa me? Ina jinka ?"
"Innah ai ni ba namiji bane? Me yasa na."

"Mutumin nan shi yazo da motar sojoji ko?" Ta tambaye ni tana murmushi. Girgiza mata kai nayi jikina yana rawa,
"Kin Fara soyayya ko Maimunari? Maimunari gaya min soyayya ko? Da nace ki rabu dashi baki rabu dashi ba? Toh bari na gaya miki ba sonki yake ba jikinki yake bukata, idan ta gama dake ba zai kuma kula ki ba, Yaran masu kudi haka suke."

"A'a Innah Mohan ba haka yake ba?" Dukar bakina tayi tare da cewa.
"Baki isa ba wallahi"
Cikin fushi na mike tare da cewa.
"Na isa na gaji..... Wayyo Allah na Nepa suna wahalar da mu fa😭😭 wallahil babu wuta.
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1107772645?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=It8W%2FoFtRBNmtv626Ht7hoebrG%2FLVlSJZLNfj7SZVFb70I%2BU8R57oeYt0nQfprrru5On2xw2q9Wa9DKvsVlrhYzw3HNW938T6zol7nYvstpRTnu2EztkBZZewXp3wWvE

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA TALATIN DA D'AYA.

Dafe goshin sa yayi tare da lumshe manyan idanun shi, ya bude tar akan likitan.
"Karka bari iyayena su sani"

Ya fada yana me gyara kwanciyar shi a jikina matashin, yana jin kamar ta cire zuciyar shi ya huta. Ya gaji da damuwar Almamoon, allura likita yayi mishi wanda zai sanya shi barci. kuma anyi nasarar haka, domin yayi barci cike da mafarkin Mamoon tana sanye da wasu shegun kaya. Ga kai yake tare da mika mata hannu.

    Amma sai wani ja mishi rai take tana wani yauki.

   **
Kallon juna suka yi tare da Amincewa da bukatar su, kafin suka ce.
"Idan muka bar shi zai cigaba da kare Ubanshi, idan muka tab'a shi zai iya daukar kasadar tab'a mu, amma idan muka saka Ubanshi ya kashe shi wannan alfarma ne kuma samu.

   Ranar da kasar mu ta samu yancin kai ranar zamu basu kyauta da ya dace dasu, daga dan har Uban zamu bashi kyautar da zasu iya daukar shi."

    Sannan ya cigaba da tsara musu kome, cikin nutsuwa da sanin ya kamata, kafin ya mike kamar mutumin kirki, ya bar dakin da suke taron sirrin.

   **
Yau kwana biyu.
"Wallahi Yaron nan mace ce ba namiji ba" inji Mohan.
"Kamar Ya?" Ya tambaye shi a rud'e.
"Mace ce kamar yadda ka sani, taya hankalina ba zai tashi ba yaron ya gama cutar dani." Kasa magana yayi yana kallon Mohan,

"Ban san yadda zan yi ba, amma ina cikin tashin hankali" ya faɗa a sanyayye,
"Tashin hankalin Uban me? Malam kana son Yarinyar nan tun tana namiji, dan haka yanzun ya dace ka fidda abinda yake ranka, idan kuma ka b'oye toh wallahi damar da wasu suke nima kenan, ka tafi ka tambaye ta meye yasa ta boye kanta na tsawon lokaci haka? Yaron bai iya karya ba, sai dai idan bai dagamar fada ba, sannan ban ga abinda zaka daurawa kanka yawan jini ba, kana son ta sosai duk wanda yake tare da kai yasan kana son Yarinyar."

   "A'a ba soyayya bane, kawai shakuwa ce. Na shaku da yaron kuma ina matukar tausayin shi. Ashe mara mutunci bai damu da yadda na damu dashi ba."

   "Komo meye malam me taurin kai mun san kome, tunda har ka iya hana mu mishi magana yana namiji shine yanzun zaka kawo min gulma me ciwon soyayya kawai."  Gyara kwanciyar shi yayi tare da Lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi yanawa Almamoon wani irin mugun SO ne kuma shi kanshi bai san da me yake son Yaron ba, idan yace da zuciyar shi ce toh ba mamaki karya ne amma idan yace da ranshi ne wannan gaskiya ne. Dan haka ya cigaba da sauraron shawarar da Dan Ba'are yake bashi.

        Murmushi yayi sannan ya mike da karfin shi, ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya fito k'ugun shi daure da towel, hannun shi rike da wata karamar towel yana goge kanshi, murmushi ya sake irin gashi ga Mamoon suna cikin farin ciki.

    Shiryawa yayi cikin jamfa da wando kaftani, sai wata hular dara wacce ya murza akan shi, yau yake jin shi kamar zai tafi zance. Dan haka ya shirya kai yadda yake shiryawa kamar ba shi ba, domin kuwa shi kan shi yasan yayi kyau. Privet jet zai bi domin idan ba shi ba zai isa Damagaram a kan lokaci ba. Kiran Dan Ba'are yayi ya gaya mishi. shi kuma ya kira sojojin da suke Damagaram akan ga Mohan nan zuwa.

Yana kashe wayar shi Ammyn na kiran shi.
"Ina ka shiga ne yau kwana biyu ina niman ka, toh duk da dai babu damuwa, kaje Hanan tazo kuyi magana da ita."

"Toh"
Ya fada tare da duba layinta ya ajiye ya a blacklist, koda zata kira shi ba zata sake shi ba.

      Bai bi takan wata hanan ba, yayi fitar shi, anan Khalil ya bashi sakon da ya samu.
"Dama meye shirin ka?"
"Kyale su, haka nake bukata ka kula da kanka."
"Abbu da?" Khalil ya tambaye shi,
"Karka damu zan mishi bayani."
"Batun Hanan fa?"
Kallon shi yayi na wasu lokuta kafin ya mai da kallon shi bisa titin.
"Yarinyar ta cika tsani, sannan siririya ce tana da kyau amma ba Matsalata bane kyanta, ka duba yanayin su da yanayin Almamoon. Koda ban sonta matukar zata zauna dani nasan zan sami yara masu tarbiyya, ban sami soyayyar Uwa ba, sai gashi na samu soyayyar Mace da tausayina, dan haka ba zan iya auren Hanan ba domin daga uwarta har uwar da ta haife ni halin su daya, itama zata iya tashi da mugun halin su, Yarana su tashi a wahale, gwara wanda zan ajiye guri daya duk inda zanje zan dawo na ganta cikin Yayana, zata zame musu gata da jin kai. Ita kuma gata yayi mata yawa ba zata san hakkina da yake kanta ba."

Ya fada tare da lumshe idanun shi.
"Nima shekara daya da wani abu ne hadu da wata yarinya a Maradi, sai dai har yau ban kuma haduwa da ita ba, gashi Nanna ta matsa min na fidda matar da zan aura, wallahil ina cikin damuwa da soyayyar Yarinyar."

     Dafa hannun shi yayi tare da cewa.
"Insha Allah zaka ganta, zaka same ta." Da wannan ya ajiye Mohan a airport, shi kuma ya koma gida ya cigaba da aikin su.

    Yana isa jirgin yana tashi da shi sai Damagaram.
.
Kawai a raina nake son kuka dan haka ina tashi ban tsaya ba, nayi ficewa ta, domin Innah tana barci tun ranar da Hammah ya daki Shago na samu hutu a cikin Unguwar mu, kowa mutuntani yake.

       A hankali nake tafiya so nake na bar cikin unguwar baki daya, motar sojoji ne ya tsaya  a gefen Hanyar.
"Dan saurayi? Don Allah kasan gidan su Almamoon" kallon shi nayi yana cikin Hilux, a hankali na sunkuyar da kai tare da jan hancina.
Hular kaina na cire bayan na gyara tsayuwa ta, na warware mayafin da yake jikin hular tare da baza gashina har ƙafadana.
"Eh nasan dai gidan su Maimunari Isma'il Wodaadabe" na fada tare da rike k'uguna.

        "Toh ya shigo zance ko ta shigo"
"Anya yanzun duniya babu yarda da fatan ba harbe ni za ayi ba."  Saukowa yayi  tare da takowa gaba na.

        Sai na ganni yar cakwai, a gaban shi. Bude min kofar yayi na shiga, sannan ya shiga shima. Kallona yake kawai ina gyara mayafin kaina.
"Dama nasan da wannan, amma me yasa" murmushi nayi sannan na cigaba da wasa da hannuna.

      Riko hannun yayi yana faɗin.
"Moonah kin min adalci?" Sunkuyar da kai nayi ina gyara zaman mayafina.
"Ba haka bane, naso nayi maka bayani amma baka saurare ni ba, ka mai da batuna shirme."

"Moonah!"
"Na'am Hammah na."
"Me kike ji a kaina?"
Kallon shi nayi kafin na mai da hankali na, kan yatsuna.
"Alkalamin ƙaddara ta zana kaddarar mu tare, sai Yau da nake tare da kai sai nake ga kamar nayi shishigi da son kaina dayawa, na zake dayawa. Sam na manta da akwai irin wannan lokacin, gani nake kamar  ni din Yar kaina ce, sai yanzun da gari ya waye na Fahimci wacece ni."

          Na kai hannu zan bude kofar motar, rike ni yayi yana kallona.
"Me yasa kike son kawo wani damuwa kuma?"
Juyawa nayi na kalli hannun shi da yake rike da hannuna. Wani irin kallo na mishi wanda yasa shi saurin sake mayafin. Murmushi nayi domin ya burge ni yadda yayi saurin fahimtar yanzun ba da bane.
"Ni da kai muna da banbanci fa, Kai dan Shugabanan kasa ne, ni kuma ko dagaci Ubana bai rike ba, dan haka yana da kai ka fahimci wani abu, kawai alaƙar mu a iya abota ne bayan haka bana jin akwai wani abu da za...."

       "Bana son jin haka!" Ya fada da karfi,
"Kin san yadda maganarnki yake kona min rai?"
A hankali na bude motar na fito, ina kallon waje, shima fitowa yayi tare da zuba hannun shi cikin aljuhun wando shi. Sai yanzun na kare mishi kallo ya hadu sama da kullum. Dauke kai anyi ina wasa da hannuna.
"Me yasa?"
"Ban sani ba, amma koma meye ai suna da hujjar bani abinda ya dace, koma meye suna da ikon  sauya min ra'ayina."

"Amma basu da ikon sauya miki ƙaddaran ki, basu da ikon sauya miki goben ki, ki tsaya a matsayin mace kamar arziki ne" murmushi nayi sannan nace mishi .

"Gobe na? Ƙaddara ta? Yau nake dashi gobe bani da kome sai abinda Allah ya bani." Rike hannuna yayi sabida ya lura tafiya zan yi, juyawa nayi tare da zame hannuna cikin nashi.
"Ka gane yanzun da baya akwai banbancin, idan da shaidan bai samu galaba akan mu ba, a yanzun da muka san kan mu zai iya samun damar shiga rayuwar mu."

"Har ila yau ba ki faɗa min me kike ji a kaina ba" murmushi nayi sannan na juya ina faɗin.
"Bana jin kome a raina akanka, asalima sai yanzun na fahimci kai Mutum ne mai matukar gundura da hawa kai"

    Cafko ni yayi tare da sake dariya, yana mai d'aga ni sama, dariya nake kamar zan zauce.
"Tun ba yau ba na gaya miki yadda nake jin ki a rayuwata Me yasa ba zaki gaya min yadda kike jina ba?"  Sauke ni yayi yana kallon yadda nake wani jijjiga, tare da mai da kaina kamar mazari na nakasa rayuwa guri daya.
"Idan na gaya maka yadda nake jin ka me zaka bani?" Na hada index fingers dina ina buga su.

"Kawai zan tafi gidan tv na basu labarin kaunar da nake miki ne"
" A wannan shekarun naka?" Na tambaye shi ina wani hararan shi.
"Ayya kuma ta nan kika ɓullo min? Me kika fito yi toh" Ya tambaye ni,
Tab'e baki nayi ina kallon shi, kafin na yatsina fuska ina faɗin.
" Kuka na fito yi, amma da na ganka sai na ji na hakura. Ban cika damuwa da kome bane kaje idan na san me nake ji zan kira ka na gaya maka."

     Shiru muka yi tare da kallon juna, kafin ya juya tare da shiga motar yana faɗin.
"Ubangiji yasa karki gaya min, aikin banza aikin wofi" ya buga motar. Dariya ya bani, san haka ina kallon suka bar unguwar gyara zaman mayafina nayi tare da saka hula, na nufi gida.

   Lokacin da na shiga cikin gidan, Innah tana kallona ganin na shigo da walwala yasa tace min.
"Me ka samu?"
"Babu" na wuce dakin.
"Mamoon!" Da sauri na fito,
"Meke damunka?"
"Babu"
"Zo ka gaya min?"

Cikin tsoro da abinda zan tambaye ta, yasa Ni zare ido. Kirjina yana mugun bugawa kamar zai b'alle,
"Me yasa ka damuwa?"

   Shiru nayi ina kallon ta, kafin ba ce mata.
"Innah me yasa?" Shiru nayi,
"Me yasa me? Ina jinka ?"
"Innah ai ni ba namiji bane? Me yasa na."

"Mutumin nan shi yazo da motar sojoji ko?" Ta tambaye ni tana murmushi. Girgiza mata kai nayi jikina yana rawa,
"Kin Fara soyayya ko Maimunari? Maimunari gaya min soyayya ko? Da nace ki rabu dashi baki rabu dashi ba? Toh bari na gaya miki ba sonki yake ba jikinki yake bukata, idan ta gama dake ba zai kuma kula ki ba, Yaran masu kudi haka suke."

"A'a Innah Mohan ba haka yake ba?" Dukar bakina tayi tare da cewa.
"Baki isa ba wallahi"
Cikin fushi na mike tare da cewa.
"Na isa na gaji..... Wayyo Allah na Nepa suna wahalar da mu fa😭😭 wallahil babu wuta.
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1107772644?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=bf4OKGFXFm%2BbTBcRYFtIWwkeTpAjYWx%2Ft%2B8piwgYnGj%2BHz02%2BCq8Olw61eWGNCGWLrWoWOYkU9DLRDRLwKRvQ2vFDZM4QGfJKL8gnNicMhI2rfKBsb98bQg%2Fv%2BXS7kmh
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA TALATIN DA BIYU.

"Na gaji wallahi na gaji, ina son na rayu da abokin tarayya, babu amfanin boye ni da kike yi. Don Allah ki barni na rayu kamar sauran Yan matan  don Allah kinji na had'aki da Allah dan girman Manzon Allah karki hanani rayuwar da ta dace dani" na fada cikin kuka, ina me rokon ta ina kuka ina. Bata hakuri amma bai saka Innah tausaya min ba,  duk da tana dukana amma ban fasa rokonta ba,, sai yau zancen Baba nasiru ya dawo mata. Lokacin da Malam ya ke gaya mata zancen sai yanzun ta kuma kara fahimtar dalilin da yasa Munari take sake kin zama wajen ta,ashe soyayya ya faɗa.
_Duk abinda zai sanya shi bayyana kanshi tabbas shi zai sanya shi kuka! rayuwar shi zagaye take da zanen ƙaddara dan haka babu wanda ya isa sauya ƙaddaran wani_

Kura min ido tayi sannan tace min.
"Ba zan baki damar ki salwarta da rayuwar wasu sabida naki ba. Soyayyar da zata zame miki masifa? Ko ba soyayyar da zata zame miki Bala'i ba, Munari ina miki kallon mutuniyar kirki ashe idanun ki sun bude har kina yarda namiji ya dauke ki ko ya rungume ki, Munari tunda kika iya haurawa katanga ya sani fahimtar soyayyar da ta saka ki kika iya haurawa katanga, soyayyar da tasaki kika tambaye ni zaki rayu akan jinsin ki ba karamar abu bace ko ya kwanta dake ne? Kike tsoron kar  ya gudu ya barki"
Dariya nayi domin yanzun kam na fara hango tsagwaron zalinci da son zuciya na fara fahimtar abinda Innah take nufi dani?.
"Innah zargina kike dan  ina son shi! Abinda na sani na haukace akan shi. Innah ina son Muhammad ina mishi mahaukaciyar so ne. Amma duk da haka ban tab'a kusantar zina ba, Innah wallahil billahi azim ban tab'a zina ba, amma kike tambaya na ko ya kwanta dani? Innah tun ina yar miciciya nake kare kaina, Innah na shiga jami'a na kwana a dakin da maza suke ban yi zina ba sai yau rana tsaka ai wallahi ko wani ne ya gaya miki zan iya bazaki yarda ba, balle balle kuma ke da kika da na dauke ki kamar Uwar da ta haife ni"

Da mamaki take kallona, kafin taja wani itacce ta rufe ni da duka. Tana kuka tana dukana, ban yi mamakin dukar ba, amma yadda nake jin zuciyata ko zata kashe ba zan fasa ba.

  "Ki dake ni, ki zage ni matukar zaki barni a raye toh wallahil ba zan fasa ba, kuma ba zan bar kaina a matsayin namiji ba, Ina son rayuwa dan haka duk abinda Kiyi min matukar zaki bar ni da shi ba zan tab'a zama a  ?matsayin namiji ba da bakinki kike kirana karuwa bayan ban tab'a ba, ko ciki nayi na kawo miki bazaki kirani da karuwa ba sai dai ki min Uzuri. Innah kawai rayuwa nace zanyi mike min haka ina kuma da nace zan gudu sai kin kashe ni duk abinda zaki yi kiyi

   "Ni zaki tozarta kamar yadda Iyayen ki suka tozarni, ni zaki wulakanta kamar yadda iyayenki suka wulakantani, bakar ƙaddara, ai tunda iyayenki suka gudu suka barki babu wanda zai iya zama dake, Shegiya yar iska, ni zaki watsawa kasa a idanu?"

   "Nasan da iyayena suna raye ba za su bar ni haka ba, kuma da suna nan ba zasu wulantani haka ba, zasu bani abinda nake so ki dake ni idan har dukar zai cire miki bakin cikina Innah ki dake ni, na gaji ina son Yancin."

   Shigowar Baba yaga yadda take dukana kuma ban fasa fadar abinda yake raina ba, yasa shi amsar itaccen.
"Baki da hankali ne? Kan me zaki tirsassa mata? Dole ne?" Ya fada da karfi, tare da tasowa ya d'aga ni.
"Baba don Allah ka barni na rayu kamar kowacce mace, wallahil zan kama kaina, don Allah ka Amince min na rayu."

  "WALLAHI ba a cikin gidan nan ba, sai dai a wani gurin ba zaki zauna min a gida ba, sai dai ki zab'a mu ko shi wanda kike son?"

  "Innah korata kike?" Na tambaye ta hawaye na zuba min, shiru tayi, ba ita ba hatta Baba sake baki yayi yana kallon ta.

"Ina kika ce na fita na bar miki gidan dan kawai nace ina son Mohan? Innah ba zan tab'a tafiya ba, ba zan zama butulu ba. Amma zan baki lokaci idan kika huta zan dawo." Na saka kai na shiga d'akina na hada kayana, har bana ganin gaba na.

   
             Wayata na dauka na shiga niman Number Mohan, amma da na tuna kar wata rana yayi min gori yasani kiran Ansar, na tambaye shi yana ina?

      "Ina diffa!"
"Ok gani nan a hanya" kawai so nake na nisanci Innah ne, dan haka na fito da kayana, hijab ne da katin bankina da Mohan ya bani. Ina fita na sami Innah ta kafe idan ban hakura da Mohan ba na bar mata gidan ta, sake kiran shi nayi, tare da tambayar shi a ina Baba Mari take, ya gaya min tana gidan shi na Maradi, dan haka na duba jaka na, na dauki key din gidan da Mohan ya saya min, na nufi Maradi dan na gaji bana son na cigaba da zama da Innah dan zan gaya mata magana..

      ***
Niamey.

  Karan cikala a yadda ake gudanar da cin abincin ban da Mohan, domin juya cokalin yake. Har suka gama,

    Kallon shi tayi kafin tace mishi.
"Mohan meye yake damunka?"
Murmushi yayi sannan ya mike tare da cewa.
"Babu"
Ya bar gurin su, tare da kara sauri.
"Meye alaƙar ka da Yaron nan? Naji an ce mace ce ko mata maza ce" cak ya tsaya ya kasa motsi, a hankali ya juya tare da kallon ta.
"Hmm hmm, kawai karya mutane ne" ya faɗa tare a barin gurin da sauri,

         "Yallabai Mohan yaki zuwa gurin Hanan, ita yarinyar tana son shi amma shi yaki zuwa ban san me yake nufi ba!" Ta fada a dame.
"Babu abinda yake nufi sama da ki bar shi ya zab'i macen da yake so Mohan ba yaro bane, kuma tunda yaki zuwa yana bukatar matar da yake so ne" ya bata amsa yana kallon tv,

    "Amma ai zab'in shi bai zama dole ba, tunda yarinyar da zai kawo bai zama dole ta cika abinda ake bukata, ina ga kawai a fara shirya kome kafin zuwan ranar da kasa zatayi murnan zagayowar samun yanci" kallon ta yayi tare da cewa.
"Toh! Amma ke me yasa baki son ya zabi wacce yake SO?"

"A'a kasan bai zama dole ya kawo yar masu kudi ba, ko wata yar manyan nafi zargin yaran talakawa yake niman kawo mana"
"Meye banbancin mai kudi da talaka? Gani nayi dukkan mu bayin Allah ne amma sai ki ta nunawa kamar baki yarda da Allah ba."

     "A'a nifa ba haka nake nufi ba, kawai dai bana son ya dauko mana yar karamar gida ce, kawai kome ayi shi a cikin harkan arziki."
"Latifah kenan,gani nayi ba a haifi kowa da dukiya ba a duniya ya samu me yasa kike nuna son kan ki dayawa, me yasa baki tuna gobenki?"
Dariya da tayi sosai, kafin ta mike tana faɗin.
"Wallahi ina da buri akan Mohan, matar da Mohan zai aura ba karamar mace bace, matar da Mohan zai aura zata kasance mai nasaba wacce duk inda zan shiga da ita ce kyawawan tsaro zan hada shi da ita, wacce duk inda muka shiga za a gane yar babban gida ce kamar Hanan"

      Abinda ya fahimta matar shi tayi nisa a don duniya, matar shi tana da mugun son kai, dan haka ta mike bai kulata ba ya barta tsaye tana bayanin abinda take son akan Mohan.

    ....
"Munmohan" ya kira sunanta a sanyayye,
"Na'am Hammah na" ta amsa a hankali, tare da jan hancinta alamar tana kuka, ko kukan yana son zuwa mata. A rud'e ya shiga tambayar ta.
"Babu kome,

Please Login or Register in order to submit comment