You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
hujja bane."
"Insha Allah, zan gaya Mishi meye zaku yi na sunan dan na gayawa Khausar taxo ku tsayar da magana." Ya tambaye ta,
"Eh duk yadda kace"
Abu ne na kuɗi dan haka ya ware masu kudin da zasu bukata, dan haka aka shirya gagarumin walima,bayan an bawa wata gidan abincin daukar nauyin girkin walima, dan haka gefe guda haka suka yi ta zirga-zirga ita da Yar gidan Babban liman da ya bata, dake budurwa ce, gashi Radiyah bata gidan tana Nigeria, hoton yarinya aka bawa wasu masu yin aikin foste suka masu aikin dake an zuba musu kudi har da kalanda, memo, book, cup ba tangaran, stickers na mannawa a bayan waya, da abubuwa dayawa. Su kuma suka shiga hidima aka raba kaya sosai.
Lokacin da Khausar ta nunawa Hajiya Lateefah tace mata.
"Ammyn kalli wannan yarinyar ta min kyau!"
Kura mata ido tai yana kallon hoton Yarinyar da ya daki zuciyarta.
"Wacece ta haifi me kama dani"
"Ai baki sani bane, ai gobe gidan nan akwai walima dukda su yau ne suna mu gobe ne zamu yi namu matar da kika tsana ce, jinin ki Allah sai ya raba gardama gashi kowa yasan yadda Hammah Mohan yake kama dake shine Allah ya tashi sai ya sakawa Maimunari jininki me mugun kama dake."
Sake wayar tayi tare da dafe kirjinta, tace.
"Ta haifi cikin?"
"Toh dama kin kifar dashi ne? Ta haifi Maryam Sunan Nahnah, Kinga kuwa dole gidan nan ayi shagali"
Kirjinta ne yayi mata nauyi dan haka tana rike da shi, sai kallon ta take.
"Ammyn ya dai?"
"Babu kawai ina mamakin kamar da yarinyar tayi ne da mu, anya ma Yar Mohan ce?" Cikin bakin ciki da takaici tace mata.
"Ammyn Ubangiji ya dube ki da rahamar shi" ta kule dakin ta, domin tana bin na Ammyn zata fadi abinda Allah zai kama ta.
Washi gari aka yi walima kuma dake bata da kunya sai gata har a gurin tana gayawa mutane, yar Mohan ɗinta ne, gashi bata san inda yake ba, surutu irin mara hankali tayi ta sake yi shi.
Bayan an watse kayan da aka kawo na suna da mugun yawa Khausar da Ummul Aiman wacce suke kira Small Mom, suna ganin kaya, tace mata.
"Small Mom, mun hada kudi zamu mishi sayayyan namu kayan, amma ina ganin zata zo bikin Kanwar ta."
"A'a dota Abbunku yace ba zata zo ba, domin tana arba'in zata koma makaranta, kuma idan tazo zata zama abin nunawa a cikin dangi dan haka kawai tayi zamanta da yarta, idan zasu koma sai a koma mata da kayan."
**
Bayan suna da kwana ashirin, Mommy suka fara hidimar su, da shiga kasuwa sayayyar kayan Beenah da ita amaryan.
Jego ya amshe ni, idan ka ga yadda nayi kyau nida yarinya na kamar me,Bama fita Baba Mari jegon da yake min, dan haka na samu kulawa ainun.
Lokacin da muka cika kwana arba'in, Abie da Mommy da Baba Mari, da Yumnah aka bari a gida, bayan an kawo min Nanny wacce zata zauna har sai sun dawo. Yumnah suna tsakiyar karatun gama primary school ne,Ni kuma Abie ya nima min makaranta zan cigaba da aji. Duk wanda ya kalle ni ya san na samu nutsuwa kibar da nayi ta boye tsawon da nake da ita.
Ranar da na fara karatu, ranar n hadu da Malam Ansar, murna kamar zanyi yayya, har gida ya kawo ni na nuna mishi Yarinya na, haba bawan Allah haka ya dauke ta yayi ta hidima da ita. Washi gari haka ya kawo maka kaya niki niki.
A lokacin nake gaya mishi ai mun rabu da Mohan, dan haka karatu ne a gabana, kuma shima ya bani goyan baya, dan haka muka kuma dinkewa sama da baya.
... A can Nijar kuwa bayan an daura aure ne.
Anyi shagali sosai ranar budar kai wata Al'amarin ya faru.
Domin kuwa Baba Mari ta rike hannun Beenah ta mikawa Nahnah, ita kuma Nahnah ta kurawa Baba Mari ido.
"Mariya!"
"Mairamu!" Sai suka sake salati tare da fashewa da kuka.
"Mariya kina raye?"
"Mairamu kina nan da ma?" Komawa cikin gidan aka yi babban falon Abba aka zauna.
"Maza ku kira min kowa, har da Mohan da yazo, kowa karku bari har da Wancan kafiran."
Bayan minti talatin aka haɗu, kallon Mohan tayi sannan ta kalli Jama'ar falon tace musu, domin har da iyaye mazan.
"Mariya kanwata ce Yar baffana."
Share kwallar idanun ta tayi sannan tace musu.
"Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, babban zuri'a ce fa ta haɗa yammacin Afirka zuwa gabashin Afirka, domin shi din daga kasar Libya yake kuma bafulatani ne na Usul Bororo,"
(Zaku yi hakuri domin zamu leka 75yrs ne da suka wuce! Da fatan zaku bude kanyar ku, ku fahimci bayani.)
.....
75yrs ago.
Shehu Usmanu Wodaadabe ya na da tarin dukiyar dabobbin musamman shanu da raƙuma, ba a batun kananun dabobbin,
Yana da mata uku, Maimunari itace Uwargina suna kiran ta da YADIKO Munari, yana da Mai bin mata Hajara Hajjo suna kiranta Yawuro, sai ta Ukun itace Amarya suna kiran ta da Inno, sunanta Ramatu.
Dakin YADIKO Munari ita ke da Yara maza, rai shida. Kafin mata biyu.
Iro, Kalamu, Isuhu, Dahe, Kabiru, Ya'u, sai Deja da yar karamar su Laure.
Dakin Hajo tana da yara mata biyar namiji daya.
Kuluwa, Sa'ade, Sakina, sai Rabi'atu, fatsuma, da Garbati.
Dakin Amarya tana da yara biyu domin ita wabi take, Sulaimanu da Tanimu,
Dukka yaran shi nan doka sha shida, Allah ya albarkace su da tarin ilimin addinin musulunci, kuma suna bada taimako irin na laluran rashin lafiya, dan haka sai ya zama na sun yi shura a rugar baki daya. Domin daga Libya sukan tafi Mali zuwa burkina faso, suna yawo sosai.
Sannan Shehu Usmanu Wodaadabe yana da Kane maza biyu, Abdullahi da Abbas, Abbas yana burkina faso, Abdullahi yana Mali, kuma dukkan su da iyalin su.
Duk shekara suna zuwa Libya, bikin al'adar Wodaadabe, dan haka lokacin da suka zo aka tsayar da magana yar Abbas aka bawa Iro mai suna Sadiya, shi kuma Kalamu aka bashi Yar gidan Abdullahi mai suna Dayyiba. Haka aka sha bikin su,bayan sun amince da junan su.
Sai ya zamana duk shekara ana wannan haɗin,kuma ana zaman lafiya.
Bayan wasu shekaru kamar ashirin da Biyar, duk da ana zumuncin amma yayi rauni.
Zuwan da suke duk bayan shekara daya, sai ya koma bayan shekara biyu ko uku, ya zama gidajen baki daya uku auren zumuncin da aka a tsakanin su yayi baya,
Amma kuma a Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, ba a daina auren ba, a wannan dakunan.
Dakin Hajo sun yi aure yaranta a wasu gidajen..
D'ago kai tayi sannan tace musu.
" A cikin Zuri'ar iro nice nayi saura, ban sani ba ko akwai wasu dangin nawa! A Zuri'ar Isuhu dakin YADIKO Mariyah ce tayi saura ban sani ba ko a kwai Sauran! Amma a Zuri'ar gidan Ya'u Mamman ne yayi saura ban sani ba ko akwai sauran." Sunkuya da kai Abie yayi tare da cewa.
"A Zuri'ar Kalamu Ni da kanwata Amina muka yi saura dakin YADIKO"
"A Zuri'ar Sa'ade mune muka saura dakin Hajo" inji Abban Khalil dan Ba'are
Take dakin ya dauki kabbara.
( Mu Cigaba)
Bayan kamar shekaru ashirin sai iyayen mu suka fara ganin ya dace a hada yaran su aure.
Dakin YADIKO da dakin Hajo, aka ware matasa maza da mata.
Dakin Amarya aka ware yaran suma.
Dan haka aka kira Sa'ido aka ce mishi an bashi auren Hauwa'u, yar gidan Baba Isuhu. Shi kuma ɗan dan Baba Tanimu ne. Kasancewar Baba Tanimu ya rasu,
Girgiza kai yayi tare da cewa.
"Ni Ummul khairi nake so! Ita zan aura idan ba ita ba sai dai a fasa wannan haɗin"
Hauwa kuma yar gidan Baba Garbati ce dakin Hajo.
"A'a Ummul khairi an bawa Na'ibi ce."
"Hodijam! Wallahi dan anga kasata rufewa Baffana idanu za a bani abinda bana so, toh wallahi ba zan amsa ba. ko a bani Ummul khairi ko kuma na tafi da ita!"
Iyayen su tsawatar mishi amma bai ji ba, dan haka suka dauki Hauwa suka bashi, ita kuma Ummul khairi aka bawa na'ibi. Kanwar Sa'ido Aminatu aka bawa dan gidan .
Dan haka babu wanda yasan manufar shi, sai ranar da aka daura auren, Ummul khairi da Na'ibi, Sa'ido ya dauke ta ya tafi da ita.
Iyayen mu dayawa ransu ya b'aci, dan haka abin sai ya zamana ya tab'a kowani dakin. Domin dakin mu, baffan mu yayi mana fada maza da matan mu, sannan yace kar yaji kar gani.
Bawan Allah nan bai tashi dawo da Ummul khairi ba, sai da tasha bakar wahala da tsohon ciki ya dawo da ita.
Ana aka gujeta kowa ya gudu ya barta, ashe daman can akwai wani Buzu daga Nijar yana bala'in Sonta shi ya daukota ya dawo da ita Nijar bayan ta haihu ya aure ta, "Mamman kai ne!". Jikin kowa a gurin sai da yayi sanyi.
Bayan wata biyar anzo bikin kanwar Sa'idu, dakin su Ummul khairi Ya Ado ya dauke Yarinyar akan idanun Sa'idu, mai suna Deja. Ya tafi da ita, bai dawo ba sai da labarin mutuwar ta,
Wannan abin ya fara ne daga dakin Baba Tanimu, sai gashi ya shigo har dakin mu, inda Hammah Babba ya dauke yar Baba Kalamu. Maimunari mahaifiyar (Abie da Innah)
Shima Faizo kanin Maimunari ya dauke ni," kin ji ko? Allah ya nufa ba a shegu zan haife ku ba, amma abinda kuke yi dattin zina ce ta lalata min ku! Sabida ita zina masifa ce, kuma dattin ta kashe zumuncin yake kuma ya kashe min zumuntar ku tun mahaifana"
Bayan na shekara biyar Allah ya nufa na dawo gida, nima sai ba gudo Nijar gurin Ummul khairi, anan na hadu da mahaifin su Lateefah shima Buzu ne.
Sai ya zamana baki daya Zuri'ar mu ta watse, kowa ya kama gaban shi, gwara Maimunari naji labarin Hammah Babba ya aureta kafin suka rasu. Amma ban san inda take ba, ranar da naga Maimunari naji a jikina Yar Uwata ce, domin kamar yadda wancan take haka itama take. Labarin Zuri'ar mu da fadi take amma mu nan yan dakin Iro, Isuhu, da Kalamu duk mun hadu dakin Sa'ade gaka, dakin Tanimu kai ne Mamman, Sulaimanu kuma Yar shi mai sunan. Bilkusu wani Bazabarme ne ya aureta, tana da D'anta shima ban san shi.
"Wa'adin Ansar yana nan raye." Inji Abie.
Sharce kwalla Baba Mari tayi.
Sannan tace.
"Baffana yayi saurin aura min Ja'e ne, gudun kar abinda ya faru da sauran ya faru dani, tunda dan Uwana Hammah Babba ya dauke Maimunari, ashe muna namu wayon ne Allah ya shirya mana nashi hikimar, bayan na haifi yara maza da mata, na aurar da su, sai gashi Zainabu ta samu manema dayawa har da wani likita a birnin , mun saka burin son tai karatun boko, abubuwan farin ciki sun faru(babu amfanin dawo da baya muje kawai ba)
Bayan ta gama karatunta aka saka Bikinta."
Har inda abie ya kwamushe ta, (toh kunji ba kunga illar ramuko kenan wallahi dukkan su zuri'a daya ce)
"Haka muka gudu sabida abin kunyar da zamu aikata, idan yar mu ta dawo, bayan mun tafi mahaifinta ya rasu, na manta cewa Allah zai bima kowa hakkin shi, sai gashi dan Maimunari yazo ya dauki fansar uwar shi."
#mai_Dambu
[8/16, 5:52 PM] Yar Kasuwa👳🏻♀️: https://www.wattpad.com/1116237086?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=uJKhfsFaHx1OnFijgRnQ5anbrgbu69dYpl9OGkwca9A2nKghpFbmd3OLH0az9UZXH%2BXwtjoqsjLlfz094p%2BjC%2B2BV7NWPll8LKXfhlmC%2F4I7zE2IA9ygXh%2FB85HrSw%2B0
HAKKIN MALLAKATA
#Mon-Aug-2021
BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza..
BABI NA SITTTIN DA SHIDA
Ya tafi da ita bai tashi dawo da ita ba, sai da cikin shi haka yasa muka gudu, bayan rasuwar Mallam na dawo garin aka ce min suma.basu nan!"
Kukan Ammyn ne ya tsannanta, tace.
"Nahnah Yayanki ne ya dauke kakar Maimunari? Shi kuma Uban Maimunari ya dauke Zainabu, me yasa ban san tarihin mu na taya zanyi ta d'agawa."
"Baki ga kome ba, tunda gashi kin raba zumunci Allah ya haɗa kin raba, dake ke shaidaniya ce" inji Nahnah.
Addu'o'in aka yi tare da niman kariyar Ubangiji akan abinda ya faru Shekaru saba'in baya,
Sannan Mohan tace.
"Don Allah ku taimaka min ku aura musu junan su, ko bayan sallah isha ne,"
Kallon suwaye aka mishi.
"Mommy da Abien mu."
Kunyar haka yasa Mommy ta gudu, aikuwa bayan an tashi an rufe taro da addu'a,
Aka nufi masalaci, sallah magarib. Mohan ya tsaya waliyin Abie, Khalil ya tsayawa Mommy,
Haddir da Salman sune suka biya sadakin.aka daura aure cikin mutumtaka.
A ranar kowa yasan matsayin shi, musamman Primer minister, da a daren ya ajiye aiki shi. Mohan kam bai iya magana ba, domin abin yazo mishi bazata, ta ko ina Maimunari yar uwar shi ce, kai ba zai ya jiran ya ganta ba, domin yasan zai bata mugun wahala. An kai amarya d'akinta, bayan watsewar abokan Ango.
Wato ma'ana idan na leka gidan Amarya. Duk wani abinda ake na al'ada sun yi (😂🤣🙄 BENAZIR bata san tsohon tuzuru ta aura ba, amma bari mu leka dakin ko🤨😜)
Wato shi tuwon girma miyar Nama ce, domin kuwa Khalil ya gaya mata gaskiya (😎🤓 Alqur'an na rasa yadda zan rubuta kome)
Yar gidan Mommy da Marigayi ta zata auren shan minti ne, sai da aka gama tab'ayya, sannan ya zaro bayani daga karamar hukumar wandon shi, ya shiga zungure ta,....(na fecce bani da damuwa da ita)
***
Washi gari da safe, kiran Umma yayi kamar zai yi kuka.
"Umma don Allah kizo"
Haka ta nufi shashin su, daga bakin kofar kawai ta tsaya.
"Umma ki shigo mana".yana sanye da Jallabiya ruwan milk, tana shiga taga matasai a kasa, ga Beenah can a kuryan gado, ta makure, sai kuka take ta dunkule.
"Fita ka bani guri." Ta kore shi ban daki ta shiga ta hada mata ruwa me shegen zafi. Sannan ta zo ta mika mata towel tace mata.
"Tashi kinjin" ta juya mata baya,a hankali ya zuro kafarta tana kuka, sannan ya daura towel din, da kifa akan gadon. "Kin gama daurawa"
"Eh " tace a raunane, sannan ta juya tare da taimaka mata suka shiga ban daki, sai da ta gasata sosai, ta gabata cire towel din, sannan ta fito ya same shi a falon fada tayi ya mishi tare da cewa
"Zan dauke ta, tunda baka da girma sai na jikinka. Kai ko kunya baka ji ba, ka saka yarinya a gaba kamar abinci, wallahi kaji kunyar ka, ina dalilin kasaka yarinya karama a gaba kamar ka samu babbar mace, toh ya kare dan ita ba tuwo bane da zaka saka a gaba kana ciki kamar ba zai kare ba, ce maka akayi haka rayuwar auren yaƙe? Dan haka kar na kuma jin labarin ka adabi rayuwar ta haka" kunya ya yasa shi sosa kanshi. Tana fita can sai gata da magani har zuwa dakin ta kaiwa Beenah,da tea mai kauri. Haka ta sata tasha. Dan ta same ta akan abin salla ne, tana sha ta koma ta kwana, ita kuma ta fito ta same shi a falon yana zare ido, kwafa yayi mishi tare da shigewa ta barshi a gurin yana zare ido.
Tana fita shima ya shiga dakin shi yayi wanka ya shirya tsaf, sannan ya fita tare da kiran Khalil suka tafi yawon gaida Surukai, sai wani sheki yake yana wani jim kanshi kamar akan shi aka fara aure (😎🤓 irin yaci sabon d....🤨😜) Ko kallo bai ishe Mohan ba, dan wani cin magani yaƙe.
...
Tunda aka daura auren Abie da Mommy, baki daya kowannen su yaki yarda ya hadu da wani, sai ma kara boye kansu suke, musamman Mommy, da take shashin Ummul Aiman, wani kunyar mutane take ji. Shi kuwa Abbu ya sata a gaba yana zoyalarta.
"Malama idan zaki fito mu raka ki, toh dan ba zaki bar min dan uwa da kwanan kad'aici ba, ai son kai ne abin"
"Don Allah Hammah Mamman ka barni haka meye haka kake, wallahi zaka kore ni a gidanka"
"A'a Malama bana son cutar kai idan zaki fito ki fito na raka ki, ina dalilin za a bar mutum shi daya a gida, da iyalin shi."
"Assalamun Alaikum!"
Mohan da Khalil suka yi sallama,
"Waalaikumun Salam," Mommy ta amsa musu cikin kunya domin dukkan su, surukanta ne.
"Mommy ina kwana!"
"Lafiya lau, ya kuke da fatan an tashi lafiya" sosai goshi Khalil yayi sannan ya damke cinyar Mohan cikin wani irin jin dad'i.
"Alhamdulillahi" inji Haddir ya amsa mata.
"Kai dan Ubanka sake ni, dan iska sake ni mara mutunci." Mohan ya buge mishi hannu, aikuwa ya kara damke shi. Kamar yara haka suka yi ta rigima Ita kam Mommy da Small Mom sai dariya suke, domin da ga Mohan har Khalil, basu rabuwa da abin fada.
Shigowata Ammyn ta zauna tana kallonsu. Domin an maida ita saniyar ware ba.
"Maman Maimunari, baku kira min ita ba, ko baki son naji muryan Kawata ce"
"Yaushe kika fara sonta haka?"
Sunkuyar da kai kowa yayi, domin tambayar da Abbu yayi mata kenan.
"Ina ruwanka tunda na kai na tambaya ba" tashi Small Mom tayi tabasu guri dan ta fahimci suna son magana a keb'ence.
Kiran layin Zurich din tayi bayan ta dauka tace mata.
"Ki bude data zamu yi magana dake kuma ina son ganin hoton me hancin karas"
"Toh Mommy kai, Widad din ce mai hancin karas ai irin naki ne, jiya Beenah take gaya min wai an daura auren ku."
Kashe wayar tayi tare da bude data, can kuwa Haddir ya dauko Laptop din shi tare da abubuwa connecter, aka had'a tana sanye da riga da wando. English wear. Sai karamin farin gyale da ta yane kanta.
Murmushi nayi tare da cewa.
"Mommy an gama biki ni da Yumnah muka kewar ku, har da Widad. Please ku dawo" tayi wani maganar a shagwaɓe, kanshi a sunkuye yake bai san lokacin da tsigar jikin shi ya mike ba, tare da kura mata ido, yarinyar jego yayi mata kyau, kuma ta had'u iyaka, dauke kai yayi dan bata lura da shi ba.
"Ina me hancin karas?"
Dauko mata Widad nayi tana wani yatsuna fuska.
"Honey kaka tana miki magana kula ta ko zata ji dadi a ranta taga beautiful baby"
"Almamoon ya kake?" Hango Hammah Khalil nayi, na sake murmushi.
"Muna lafiya, ya kake kaima? Ya kanwata? Ya Umma da Jalilah."
"Alhamdulillahi tunda bata aure miki miji ba dole ki tambaye ta," murmushi nayi sannan na kauda zance haka muka yi ta gaisawa dasu, sannan aka had'a Ni da Ammyn hade rai nayi tare da dauke kai na nace mata.
"Ina wuni"
Daga haka na dauko abin saka yarinyar na ajiye ta na cigaba da aikina ita kuma, tana fama da jikarta suka hira wai.
"Ammyn ki kashe wayar haka baki ga yarinyar tayi barci ba, Mommy kiyi mata magana ta goyeta, tana bukatar dumin jikinta."
"Ai ba bayanka bane kuma baka saya ba balle kace ka saya ne dole a maka abinda kake so idan mutum bai fita rayuwar mu ba, wallahi zai sha wahala." Na fada ina murguda baki, na kashe kiran dan ban jira Abinda Mommy zata ce ba.
"Kayi hakuri Mohan, sai na sab'a mata Insha Allah, ai baa kanta aka fara rashin aure ba, mara kunyar banza zata ishe mutane bari ka isa Zurich din sai na mata duka.". Haka tayi ta faɗa suna bata hakuri, goggan naku sai wani murmushi yake irin matukar na kama yarinyar nan zata ji a jikinta.
Bayan kwana uku.
Suka tattara suka dawo Zurich. Baba Mari kan tace bata bin su ko ina, gurin Yar uwata zata zauna. Haka suka tafi aka bar Beenah, wacce suke soyayyar kamar zasu cinye kansu, amma duk da haka bata yarda yace zai shiga aljanna (😎🤓)
***
Bayan sun dawo ne suka fahimci Maimunari ta dan sauya, yawan waya fita babu wani kwakwaran dalili, kawai aikin Ansar ne. Kuma bata dawowa akan lokaci haka Yarinyar zata gama kuka kamar ranta zai fita, ranar taga b'acin ran iyayenta, dan kamar zasu dake ta.
Ina jin su, suna fada ban kula su ba na dauki yarinyar ina hararanta. Ina shiga cikin dakin na dangwala ta a gado, sannan na wuce nayi alola, haka tayi ta kuka kamar zata shiɗe, koda na idar da sallah, na saka mata mama yarinyar nan taki karb'a. Ruwa na bata garin.daukar waya kawai na tunkud'a mata, yar mutane ta shiɗe. Baki daya ta kafe min.
"Wayyo Allah na, Mommy mi taimake yar mutane zata mutu," na fita a haukace karbanta Mommy tayi tare da gwada mata hikima amma fir taki dawowa, ina kuka kamar zan mutu,.haka muka nufi asibitin. Dakyar suka janyo ruwan da ya shiga hancinta, ana ja yana sake wata irin Marayan kuka, nima kukan nake. Likitan ne ya fito yayi ta faɗa tare da cewa sai an hada da hukuma domin wannan cin zarafin yara ne. Dakyar suka hakura tare da sallamar mu.
Tun a mota suke fada, Ni dai ban ce kome ba, ina rungume da Yarinyana a Kirjina.
"Ance min ana ganinki da wani waye shi? Wato dan bamu nan shine bari ko fara wani rashin hankali ko?"
"Abie ba kowa bane fa, Hisham Waadi Ansar ne, kuma naga babu kome a cikin alaƙar mu, sai abo.." tass Mommy ta wanke ni da mari.
"Kar na kuma ganin ki dashi, idan ba haka ba, zan miki Yaren da zaki Fahimta, wallhi" inji Abie, da yake tuki.
"Toh duk akan me? Haka kawai ban sami farin cikin rayuwa ba, dai da na hadu da shi yanzun shima ace za a rabani dashi."
Ran Mommy ya b'aci addu'a take Allah ya kai mu gida, dan haka muka isa ta rigani fita, ta amshi yar tare da mikawa Abie.
"Kyaleta mu shiga."
Amma ina ta hau dokin zuciya, ta rufe ta da duka, sosai domin ta gaji da Iskancin Maimunari ana cewa wai dan ba a sonta, sai da ta mata mugun duka, sannan ta shige ta barta a bakin kofar, taki shiga kuma taki karbar yarta, dan haka suka kyale ta, ransu kowa ya b'aci.
Tunda Mommy ta shiga ɗakinta take kuka, sabida da ciwo a ce baka da iko akan d'anka, har kusan asuba ga yarinyar na ta kuka. Amma Maimunari tana waje, sai da Abie ya fita da belt ya bude mata ido ta dauki yar tare da shiga d'akinta ta, kwanta tana rarrashin Yarinyar.
Sam ban san me ya shiga kaina ba, nake jin haushin kowa har da Mohan, ina kwance maganar Ansar ya dawo min.
"Ke fa ba a damu dake ba, ƙawai ana damuwa dake ne sabida yar Mohan, ko yayya idan kika bari yarinyar nan wani abu ya same ta zaki ga yadda za a nuna baki da daraja, sai ita."
Lumshe idanun nayi wato da gaske ne abinda ya gaya min, sabida ita yarinyar ta hanyar aure aka same ta, shi yasa ake damuwa da ita, Ni kuma Shegiya wacce aka haifa ta zina. Haka na sha kuka na more, da safe na tashi zan tafi makarantar na ajiye yarinyar bayan na shirya ta, na rubuta Musu.
*Ba zan dawo da wuri ba sai biyar*
Na saka a kasar rigar yarinyar, ina share kwalla. Koda Mommy ta shiga daukarta bayan na tafi ta ga sakona, ko karyawa ban yi ba, haka na bar musu abin su, ranta ya kuma b'aci dan haka ta kasa hakuri ya kira Mohan, ya gaya mishi abinda yake faruwa dauke wuta yayi....
#Mai_Dambu
[8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻♀️: HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021
BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA SITTTIN DA BAKWAI.
Duk yadda Abie ya kai ga saka idanu akan Maimunari sai da ya nuna mishi gazawarshi, tare da fita harkan yarinyar tace ta yaye ta,abun yayi musu zafi dama haka take da dan banzan taurin kai yarinya yar wata uku kice kin yaye ta, sai suka shiga Bin ta da addu'a, domin kuwa abin da matukar tashin hankali, ita ba asiri ba balle ya karya zunzurutun daukar zuga.
Ranar da Mohan yazo bata gida, ya isa gidan, ya samu yar shi tana ta kuka, rungumar ta yayi yana jin wani irin kaunarta.
"Mommy saura wata nawa Mahaifiyar ta, ta gama karatu?"
"Saura wata bakwai!" Inji Mommy, gyada kai yayi sannan yace mata.
"Toh babu damuwa, ku bar ta. Karku takura mata sai tayi abinda ake bukata, ku cigaba da addu'a, idan na hadu da shi zan ci...." Yayi kwafa.
Yana jijjiga yarinyar, Maimoon bata shigo ba, sai karfe bawai a gajiye. Wata tafiya suka yi da Ansar yayi yawo da ita, har suka shiga ruwa, shine ta gaji sosai. Tana shigowa tayi tozali da Mohan, yana bawa yarinyar madara.
Wani irin tsalle zuciyata tayi amma na dauke kai kamar ban ganshi ba, kuma wallahi ina matsanancin kewar shi, kawai hakuri nake, yan fita da muke da Ansar ba karamin kama kai na nake ba, domin da zan biye mishi ban san me zancewa Ubangiji na ba, shi yasa kwana biyu da suka wuce ya rungume ni sai da na kifa mishi mari, haka yayi
Book Chapters
Chapter 41
Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45