Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya mike tare da tsayawa a bakin window yana kallon yadda mutane ke zirga-zirga.
*Jewel* ya ambata a hankali, yana tuno yadda tayi ta kuka da abinda yayi mata, idan ya tuno yadda take daura kanta, a kafadar shi tana kuka.
_Wai meye aka miki ne? Kawai dan na tawo dake? Meye na kuka? Toh kiyi shiru zan mai daki gida_
A lokacin dud duniya baya jin zai iya rabuwa da ita, baya jin akwai wanda ya isa raba shi da ita. Sai gashi kai tsaye mahaifinta ya karya karfin shi da yake jikin ta.

       Itace yarinyar da ya fara ta'adi da ita, yasan ya saka yan mata dayawa kuka, amma baya jin kukanta zai tab'a rayuwar shi sai da ta bar jinjirin da ta haifa mishi, sai da ta tsallake su tai tafiyar shi. Bai san me zai ce ba, amma zuwan yarinyar nan yasan ya shi jin lallai yana bukatar Ahalin shi.
"Assalamu alaikum!"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa yana kallonta, kafin ya mai da kanshi gurin Mohan.
"Kayi hankali da rayuwar ka, domin wani lokacin muna tafiya ne da ƙaddaran mu, duk wanda ka ga ya sha Allah ya dibe mishi wani wa'adi ne, ka kuma kara nisanta kanka da mutanen da suke zagaye da ƙaddaran ka, wasu Alkhairi ne ke tafe dasu, wasu kuma sharri ne, malam masoyi zaka iya daukar yarinyar ka tafi da ita, amma kazamar soyayya da ake yin nan a gaban jama'a, ayi hakuri dashi sabida kimar Uwata. Domin naga wani sako a jaridar jiya."

    A hankali na d'ago kai ina kallon shi, sai naji jikina yayi sanyi.
"Ban tab'a rungumar ta ɗan naji dad'i ba, ban tab'a rike ta naji dad'i ba, idan nayi haka ina yi ne sabida yanayin laluranta yana bukatar kulawar da tafi haka, amma a matsayin ka na babba kayi magana Insha Allah zan kiyayye hakkin Allah, gudun fadawa rudin shaidan, sannan karka manta da kashedina."

    Dariya yabawa Alkali,ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, daya yana rike da kofin fura da nono, yana kurb'a.
"Toh ai yarinyar ka, Uba ta dauke ni dan haka karka kuma damuwa da ni." takowa yayi gaban shi cikin harshen buzanci yace mish.
"Ka kula kana mata mahaukacin soyayya, itace silar kukanku. Kayi fatan Allah ya shiga al'amarin ku. Domin ina hango guguwar da ta tunkaro."
Cikin sanyin halin ya kalle shi, kafin ya riko hannunta, yana kallon shi.
"Babu wanda ya isa tsakanin mu, domin na shirya zuwan wannan yanayin, tunda na na fara bana jin akwai abinda zai raxanani sai kalmarta kawai nake jin tsoron shi."

Daga haka ya riko hannuna,muka fita kallon shi nayi ina son nayi magana, amma tsoron shi ya hanani magana, har muka isa gidan, fushi yake tayi koda zai tafi rike hannun shi nayi.
"Kayi hakuri kaji." Na fada idanuna suna cika da kwalla. Shafa fuskana yayi.
"Babu laifi dan ya mana magana akan rayuwar mu, amma kuskure ne babba ya shiga al'amarin mu kin gaya mishi wani abu ne akan rayuwar mu"
"WALLAHI ka yarda dani ban tab'a wannan gangancin ba." Na fada kwalla na cika min idanuna,
"Ya isa, ki kula da kanki"
Gyada mishi kai nayi, tare da cewa.
"Sai gobe kenan"
"Eh nazo miki hira ne? Yawwa gobe Insha Allah Rukayyah Hussain Adam, zata dawo nan da zama. Naga kina son ƙawance da ita"
"Eh" na ɗaga mishi kai.
"Toh zata dawo nan Insha Allah"
Daga haka na rako shi har waje, sannan na koma cikin gidan, na hadu da matan gidan, muka gaisa.

     ***
Baki daya Mohan ya mai da Uwar shi bita can, yana zuwa gurin Hanan amma babu abinda yake hada shi da ita, ta gama haukarta, bai kula ta sai ya gama Gajiya zai tashi ya bar gidan, sannan ya kalle ta, shima bawai dan yana da abinda zai ce mata ba.

   Bayan kwana goma sha biyu, ana saura kwana uku zayi bikin yancin kai, hankalin shi ya karkata akan wani abu na daban, bai da lokacin kowa sai kanshi.
 
  Shi da dan Ba'are dan ya zo gida, kullum suna fita tare da abubuwan kan su. Sau daya yazo a kwanakin nan baki daya ya dauke kafa, a kotu ma ina zance ina fahimta abubuwan da yake faruwa, sai dai ban cika azarbabbin shiga ba, sai Abie yayi min magana nake shiga, dan ma dai ina yawan damun shi da shiririta, da wauta nayi ta dashi dariya, idan kuma muna hira kamar wasu sa'o'in juna, abinda na fahimta a tare dashi Abie ya aikata laifuka da yawa, da suke yawan dawowa rayuwar shi, sai dai wani lokaci zai ta share kwalla, tare da kallona yana fada min wasu kalmomi masu girma da daure kai dan haka tausayin shi da damuwar shi ya kara sakani cikin wani yanayi na daban, shima Hammah Mohan, idan na kira baya dauka duk da Rukayyah Hussain Adam, tana tare da ni, amma bana jin dadin yadda nake kiranshi yana kin d'agawa. Ga wani mugun mafarki da nake yawan yi akan shi. Dan haka ranar na kira shi tare da tambayar shi,yana ina?

"Karki zo inda nake kiyi zaman ki kawai" ya kashe wayar.
Takaici ya sani bin shi, bayan na kira shi, dakyar ya gaya min. Koda naje sai naga gida ne, dan haka na shiga cikin gidan, hango shi nayi, Hanan tana bashi abu a  baki. Wani irin nauyi naji a kirjina, dan yasan na ganshi. Na kira shi waya.
"Nagode da abinda ka bukaci na gani."
D'ago kai yayi yana kallona, kafin yace zai mike, na juya tare da fita a gidan, ina jin zubar jini a hancina, duk lokacin da raina ya b'aci kai na yake sarawa, kafin nan na fara tari, idan banyi tari ba shine jini zai na zuba ta hancina, lokacin da ya fito har na tari abin hawa, ina kuka. Har na isa gida, shafa kanshi yayi sannan ya kira dan Ba'are.
" Ya kome na tafiya?"
"Eh amma ita fa tana cikin hatsari domin ana bibiyar kiranta"
"Ok gobe da dare Malik ya tafi da ita Maradi, itama Abokiyar aikin ta ta koma garin su, ka tabbatar sun bar garin nan gobe Insha Allah"

Sannan ya juya abin shi yana kashe wayar, kara wayar shi yayi sannan ya saka a kunne.
"Mohammed Mamman Nasir Aghali, ya kake? Baka saka hannun a wasan ba toh gani nan ina jiran Munnah a gidan da ka bata me kyau da tsada, zaka zo ne ko kuma zaka iya hakura domin nazo ne akan game ɗin."

   Kashe wayar yayi tare da kiran Dan Ba'are.
"Maza kazo gidan Dogo ina jiranka, ina da abu me muhimmanci a gidan Beauty"

    *
Ina komawa gida, tun a bakin get din na hango Malam Ansar, cikin kuka na kalle shi.
"Ya isa haka, dama haka rayuwa take, wanda ka damu dashi bai damu da kai ba, wanda baka damu dashi ba yana nan yana hakilo akan ka, shiga mota mu fita."

    Babu musu na shiga ina goge kwallar da nake, da hanky din da da yabani, muka fito cikin garin, han gyara garin yayi kyau da ado, wani gidan abinci ya kai mu, na kasa cin kome, ruwa kawai na sha, haka yayi ta tsokanata. Tare da jana da wasa.

   Dole na sake muka shiga hira. Inda ya min odar abincin da suka fi na farko kyau da tsada, ina ci ina bashi labarin gurin aikina.
"Hmm! Meye ya had'a ki dashi?"
"Babu kome!"
Naki gaya mishi, domin a tsakanin masoya akwai yafiya da boye sirrin juna, tun yanzun idan ban iya boye sirrin mu ba, yaushe zan koya dan haka muna cikin cin abinci, aka rike min hannuna.
"Ina zaka tafi da ita?" Cikin fushi ya sake hannuna ya zabga mishi naushi dai dai shigowar Alkali. Sai da bakin shi ya fashe.
"Mohan!!!" Na kira suna shi da karfi....🤣
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110255281?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DdYNxkS6yN8uhfrR37h62zbfOjOm1OLDDCckdNme%2BKjEwnbGDu4mL6048YMV1h%2B07%2FeXZoIeF7Jb4dl3nS6A6LUJkIqi7ROIE9bf%2BgkMcMKV8M17P9CSRPPYeYAU9QZF

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARBA'IN.

Tsayawa nayi a gaban shi, cikin takaici ina kallon shi, zuba min ido yayi, kafin yace min.
"Ba zan miki dole ba, amma kuma yana da kyau ki fahimci suwaye a tare dake, su waye suke son amfani dake, tashi muje gida."

  Ya fada min, kasa mishi musu nayi ma mike, ashe haka ya b'atawa Malam Ansar rai yace min.
"Nagode"  juyawa nake son shi yi, amma abun mamaki Mohan ya hanani, muna fitowa ya saka ni a motar shi. Muka bar  gidan cin abincin kamar zanyi kuka haka nake bin shi.

    Baya tafiyar shi, Malam Ansar ta juya zai ya hadu da Alkali, cike da mamaki ya kalle shi. Sannan ya kasa magana, har ya fita yana kara juyawa yana duba alkali.

   *Taya mutumin nan yake kuma da Munnah?  Kamar ta B'aci sosai* shi daya yake zancen zuci, har ya shiga motar shi, wayar shi ya saka a kunne, yana me cewa.
"Yaki amsa sabida ya san zai fadi, dan haka duk rintsi ka dauko min ita idan ka sami damar haka, idan ka sake kuma na dauke ta, tabbas zan tafi da ita ne duk inda yayi min."

     Wani murmushi yayi tare da cewa.
"Kwantar da hankalinka, yanzun zaka ji ruwa mai yawa, zan baka abinda baka zata ba, yanzun zan koma diffa, idan na dawo zan kira ka."

    Kashe wayar yayi tare da sake wani murmushin gefen baki yana faɗin.
"Hmm! Ta kare maka Mohan" ya faɗa yana murmushin mugunta, a hankali ya tadda motar,tare da barin Niamey.

   Abincin ya saya tare da biyan kudin, sannan ya nufi gurin da su Mohan suka tsaya, ganin wayar Maimunari yasa shi dauka, hotonta ne a kai lokacin tana Almamoon, kura mata ido yayi zuciyar shi tana bugawa, da sauri ya kashe wayar baki daya. Abincin da bai ci ba kenan, haka kawai zuciyar shi take raya mishi wani abu akan Yarinyar,duk da ya lura bata da kwaranniya irinta sauran matan, gaskiya da ban mamaki yanayin su da yake gani a tare, abu daya da yake kara fisgan shi a kanta, kafewarta akan abu. Bayan haka baya jin akwai wani abin da ya ke yanayi daya da nashi, sai fuskar shi da kuma yana yin fatar su, sai dai tafi shi washewa kaɗan, kasancewar shi mai duhun fata sosai. Lumshe idanun shi yayi.

A da baya tunanin haka sai da wani abokin shi alkali daga tahua yazo da ya ga Maimunari ne yayi ta mamaki.
"Wodaadabe wannan yarinyar yar ka ce?" Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Eh toh kasan ban da iyali dai? Aiki ya kawo ta nan bayan nan kuma gaskiya babu wani abinda ya had'a mu sai dai ina jin ta kamar wacce ta fito jikina" ya faɗa yana murmushin jin dadi. Yau an had'a shi da d'a shi da yayi kuskuren tafiya ya bar baya da kura.

  Bayan abokin shi ya tafi ya tuna sakon da ya barwa yar uwan shi.
_Ban sani ba ko meye muka haifa! Ba zan iya duba shi ba, don Allah ku rike shi da amana, idan namiji ne ku bashi ilimin addinin musulunci, idan mace ce don Allah ki tayani boye sirrinta, dan kar hakkin mutane ya tambaye ni akanta na had'a ku da Allah."

         Lumshe idanun shi yayi kafin ya bude sunyi jajjur har da ruwa sun cika.
"Ina namiji ta haifa, kuma tarihin shi zai rufe,mace kuwa tabbas soyayya zai bude tarihin ta, kuma de ƙaddara zata ratsa tsakanin. Allah kasa namiji ne. Allah kasa kar ya gado mugun halina, ya Allah kasa kar ya dauki halin da na jefa wasu iyayen."

Ya fada yana jin saukar kwalla akan fuskar shi, tabbas yayi kuskure sosai, kuma yayi danasanin rayuwa,domin ya cutar da yaran bayin Allah da yayi ka,abun na mishi ciwo.  Gashi girma ta cimma shi babu iyali shin Zainabu tana raye ne?  Takawa yayi babban falon shi yana kallon yadda rayuwa ta mike mishi, a cikin shekara ashirin yayi faffutikar niman ilimi, yayi karatun boko dan yana da ilimin addini, bayan faffutikar da yayi na yawon karatu kasa kasa, ya halarci yaki da jahilci da yake garin Kano, idan ya damu shekara biyar yana karatu, bayan ya gama ya koma Nijar yayi karamar diploma kan harshen French na shekara uku. Sannan ya nime gurbin karatu ta hanyar wani mutumin da ya tab'a yiwa taimakon sakamakon asirin da aka mishi, akan shi da yaran shi. Mutumin shi ya dauki nauyin shi tafi kasar Faransa yayi karatun lawyer, inda ya shekara takwas yana karatun, yana gamawa ya kuma komawa makarantar horon alkalai anan Faransan, idan ya samu shekara goma sha biyar yana karatun shi bai da lokacin kanshi baki daya ya kuma tafiya jami'ar Madina inda ya karanci Shari'a musulunci a can suka  haɗu da Primer minister, inda ya karya mishi asirin jikin shi, sannan ya gaya mishi wasu abubuwan. Akan Yaron shi da suka haɗu dashi wato Mohan.

     Yana kammala karatun shi, a Saudiya suka dauke shi aiki Nan babban Kotun musulunci, albashin da tabarkallah, haka yayi ta rayuwa ga yan mata da suke bibiyar shi, amma bai tab'a kawo su rayuwar shi, asalima mace daya yake so har kwanan gobe.

       Lumshe idanun shi yayi idan ya tuna yadda yayi ta yawon niman abokin shi da Kanwar shi kamar ai yi hauka, yayi ta niman Zainab da danginta, kamar Mahaukaci. Haka yayi ta jin kamar ya tsani kowa a duniya, bayan ya dawo Nijar domin Primer minister ba karamin addabar rayuwar shi yayi ba akan lallai ya dawo kasar shi yayi musu hidima, yana dawowa aka bashi alkalin Alkalai na kasar nijar, tare da albashin mai kyau amma bai kai wanda Saudiya take biyar shi ba, idan yanzun zai ga Zainab ko dukkan dukiyar shi ya zab'a ya bata zai sallama mata indai zata zauna dashi. Numfashi yaja tare da d'aga kan shi sama, yana jin babu dadi. Ya rayu a kad'aici gashi Yanzun ma kadaicin ce ta kuma takura shi.

    Buga mishi kofar gida da aka yi ya sashi bude kofar shiga gidan, manyan mutane ne baki dayan su. Shigowa suka yi bayan sun nime izinin haka. Tashi yayi tare da dauko musu ruwa, ya ajiye musu.

   Ya zauna yana kallon su, bayan ya daura daya akan daya.
"Ina jin ku meke tafe da ku?"

"Muna niman goyan bayanka, kan aikin da zamu yi, kuma Alhamdulillahi mun samu nasarar wasu manyan sai dai wasu daga cikin mu sun yi kokarin kin bamu hadin kai."

      Murmushi yayi yana kallon su.
"Kusha ruwa" daukar goran ruwan suka yi tare da kaiwa baki, shima ya dauki nashi yana kallon suka bude tare da kaiwa bakin su. Suka sha, rike musu ruwan yayi, a wuyar su bayan ya damke goran hannun shi.

"Kun zo kuyi min tayin na shiga kifar da gwamnati Mamman Mohammed Nasir, bayan baku san tarihina ba, tun ba yau ba nasan zaku zo. Kuma idan kuka tafi zaku iya juyowa gare ni, wannan abin da kuka yi hukuncin kisa zan yanke muku domin wallahi ba zaka yi nasara ba, koda zaku yi faduwa ce zata biyo baya, sake goran yayi suka shekar da ruwan suna tari.

"Kafin ka tunkari mutum ka fara dubar waye shi, jarumta ba a jiki yake ba a zuciya yake, idan kuma aka yi katarin haduwa da karfin jiki Magana ya kare maza ku tashi ku bar min gida idan na fito muku a asalina, mutuwa zaku yi domin da bakin ku zaku fadi abinda kuka aikata."

    Mikewa suka yi tare da barin gidan a guje, domin basu tab'a tsammanin tantiri bane shi sai yau.
Murmushi yayi sannan ya fara niman wani layi, bayan sun jima suna magana sannan ya kashe, yana jin wata irin nutsuwa a ranshi.
    
  ***
Wullani yayi cikin motar ran shi na kara b'aci..
"Dalla malam karka karya musu yar mutane, ka manta kai ka daukota a gidan su? Kishin banza kishin wofi ko ce maka aka yi yar ka ce ita? Baka isa ka hanata kula samari ba, tunda ba aurenta kayi ba. Haba Mohan! Meye tayi maka da zafi haka? Meye ta tsare maka haka? Idan wani abu ta maka zai ka gaya mata. Amma ba kayi ta nuna mata abinda bai dace ba, ta baro gaban iyayenta a wahale, tazo nan kana wahalar da ita"

"Kyale shi Hammah Khalil, ban san b'ata min lokaci yake ba, sai da nagan shi da yar uwan shi, ya hanani nayi rayuwa da wani, sannan shi ya kasa fahimtar dani wacece ni? Bayan tashin hankalin da na gani nazo zan shiga gida Ansar yazo, da naso wulakanta ka da a gaban shi zan ki kula ka, na bishi amma kai a rayuwata gaskiya ne baka tab'a min gori ba, nasan kana kishina amma haka  baya nufin cewa zaka wulakanta duk wanda yake tare dani ne, Hammah meye nayi maka da zafi? Dama can yar uwarka zaka aura"

"Eh ita zan aura"
"Mohan ka gaya mata gaskiya mana, meye amfanin boye mata abinda kake?" Inji Dan Ba'are,
"Ba zan gaya mata ba, idan ta gadama gobe tana dawowa aiki ta shirya zata koma Damagaram" cikin takaici na kalle shi, ban iya mishi magana ba, na dauke kaina haka muka isa gida, har na fito daga cikin motar na shiga compound na gidan. Ya biyo ni da sassarfa.
"Ki hada kayan ki nace gobe" dauke kai nayi.
"Maimunari ina magana dake" banza na bawa ajiyar shi. Hannun shi ya d'ago zai rike ni, na buge hannun.
"Karka kuma gigin tab'ani, idan ba haka ba, zan mare ka" na fada mishi ina wuce shi. Kasa motsi yayi tare da cizon lip din shi na kasa, furza da iska yayi. Wayar shi ce tayi kara ya dauka.
"Malam da alamu kome dai yana tafiya dai-dai, ko ta watsar da kai ne tayi tafiyar ta, ok kasa hannun muyi wasar mana ko kana tsoron zaka fadi ne!"

"Kai!!!! Kana ina ne?"
"Ina kofar gidan ka mana, kazo domin da shaiduna nake."

   Kashe wayar yayi, sannan ya fita da mugun gudu ya shiga motar.
"Taka muje."
"Ina dan Ubanka sai kace aljanu ne suka shafe ka"
Bai kula shi ba kallon agogon hannun shi yake.
"Gidana mana" da gudu suka bar apartment din, suka isa gidan, ko tsayawa basu yi ba, ya bude motar tare da sauka, yana wani irin ciccira kamar wani lantarki yana spark,  takawa yayi zuwa gaban su. Ya daki motar su,
"A'a Mohan! Karka lalata min mota na mana." Ya fito yana kurb'an wine.

     Takardan ya ajiye mishi. "Ka duba mana, meye a cikin shi ban da yarjejeniyar da aka kula idan bai maka ba, sai ka rubuta wanda kake so"

Ya fada tare da kallon abokanshi biyu  da suke cikin motar. Yana faɗin.
"Yan iska zaku fito ku tayani saka hannu ko ya?" Dariya suka yi tare da fitowa suna kallon Mohan.
     Gira ya d'aga mishi yana nuna mishi takardan daidai fitowar dan Ba'are, tare da ciro bindiga a k'ugun shi.
"A'a. A yarjejeniyar mu babu harbi babu fada. Duba mana"

    Daukar takardan dan Ba'are yayi yana kallon shi.
"Ba zai shiga ba"  ya riko hannun Mohan.
"Hhhh! Kunji dan mace toh tunda ba zaka shiga ba, inji abokin ka nima dai zan maka Yaren da zaka gane"
"Zan shiga"

"Mohan"
"Zan shiga! Bani. Amma idan nayi nasara zan Barka a raye domin ganin mu shi zai kara maka fahimtar kome na Allah ne"

     Cika gurin yayi, sannan ya juya zai bar gurin.
"Mohan ina maka fatan nasara"

Cak ya tsaya, sannan yayi gaba abin shi. Bai kuma kula kowa a cikin su ba, har suka shiga motar bai iya magana ba.
"Mohan"
"Please"
Yace mishi, tare da juyar da kanshi.
"Idan baka yi nasara ba zai iya daukar ta da?"
"Nasara ta Allah ce, ka yarda da faduwa. Don Allah ka barni" Ya fada mishi haka.

Murmushi yayi bayan sun bar gurin.
"Me yasa ka dage ne? Naga dai baya so kamar tilasta mishi kayi."
"A'a yana so mana, da baya so ba zai shiga ba, nasan abinda nake shima kuma ya sani, idan da bai da ilimi ba zai shiga ba, saka ido ka gani."

   ***
Tunda na shiga dakin nake kuka, ban san me yasa kome yake zuwa min haka ba, amma tun haduwa na da Mohan nake kuka,  mik'ewa nayi tare da hada kayana ina gayawa Rukayyah Hussain Adam,
"Auta tashi ki hada kayan ki, zamu bar garin nan sai bayan bikin yancin kai zamu dawo."

"Toh lafiya?"
"WALLAHI ban sani ba, Hammah Mohan ya sani haka." Na shiga had'a kayana. Ina ƙoƙarin b'oye damuwa na. Tunda na gama muka kwanta.
*1:am
Kokarin rike jan numfashi na nake, amma baki daya ya shake ni, ya hanani sakat ban san meye manufar shi ba, sai dai hango shi da nayi ya fad'i kasa warwar ya sani farkawa da sauri ina ajiyar zuciya, ban daki na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallah nafilla.
Har asuba idanuna yaki barci a duk lokacin da na rufe idanuna abinda ya faru a mafarki yake dawo min, har aka yi sallah asuba,nayi sallah sannan na zauna na cigaba da azkar. A hankali barci ya dauke ni.

    Karfe tara na bude idanuna, ganin shi nayi zaune, ajiye min kofin shayi yayi tare da mika min brush. A hankali na tashi babu yabo babu fallasa, na nufi ban daki ina fitowa na dauki shayin da magani na sha, sannan na koma nayi wanka ban same shi a dakin ba na shirya sosai, sannan na fito, ina kallon shi suna hira da Rukayyah.
"Insha Allah karfe biyu zaku bar garin nan ki gaida iyayen ki," ya mika mata wata jaka, sannan ya kalle ni.
"Muje"
"Yan mata bari na fita"
"Toh sai kin dawo" ta ce min, haka muka fita, gabaki dayan mu jikin mu a mace yake, kamar wanda wani abu zai zame mu, gurin cin abincin ne. na zamani.
Kujera ya ja min na zauna. Sannan ya zauna yana kallona, kawo mana kayan abinci aka fara yi. Ina kallon shi.

    Kasa cin kome nayi ina kallon shi.
"Ci mana"
"Na koshi" bai ci ba, ya rike hannuna.
"Ban sani ba ko zan kai labari, sai dai ina rokonki Abu daya. Don Allah koda na mutu karki auri Ansar ki, Don Allah ki auri Khalil ko Haddir, sune kadai zasu rike ki kamar yadda nake rike dake. Sune kawai zasu soki kamar yadda nasoki.  Kasar da Mahaifina nake son bawa kaina don Allah ki taimaka min kinji karki Auri Ansar"

   Ya fada yana dauke kan shi tare da saka bakar madubi a idanun shi, domin kwalla ce take son zuba mishi.

"Me yasa zaka gaya min haka"
"Sabida bani da zab'i, rayuwar mahaifina"
"Mohan kasan yadda nake ji akanka? Me yasa zaka gaya min haka?"
"Sha ruwa" ya mika min.
Buge hannun shi nayi, tare da mik'ewa dan kula shi ma, bata lokaci ne. Haka na barshi ya zo ya same ni a gurin.

    Haka muka fita yayi ta yawo dani, kusan amanar kaina yake bani kar na auri Ansar.

*🤔🙄 Toh ya zamu yi daku domin mutanen da suka biya kishi a tsakanin zubda jini sun fara niman shi fa😌😠 🙄 wai suna jiran dan haka zan fara shi ku kuma zan mai da ku posting sai dare sau daya shima sabida nayi alƙawarin shine ɗan haka kuyi hakuri,  toh ya na iya an fara tambayana 👏 kuyi hakuri ba laifina bane na mutanen da suka biya kudin su..... Nagode*

#Mai_Dambu....
[8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110533172?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=aSbcpjgn9asSsm9lZXK1GTYd1hkBoALGTEin2VPj2rrHh0qsHukAEkcdgVB%2Bbd47RHlGBNNnsyrNYAxk4FDLM8zZE%2BhDR1NGlY7Kh7sDrXNrEAQA9XmoAHfTO2Lcqj9H

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARAB'IN DA BIYU.

Gurzawa yake cikin wani irin shauki me mugun dad'i, har yaji shi ya shige cikin jikinta kamar mahaukaci a zauce da ita, ya gigice domin bai tab'a kawowa zata kai mishi ba, dan haka lokaci guda yaji an shake mishi wuyar shi.

Ban san yadda zan kwatantata muku yadda nake ji ba, ban san wani irin yanayi nake ciki ba, sai dai duhun da na fahimta yana rufe min idanuna, karar da naji wanda ya tafi da jina da gani na baki daya, daga nan ban kuma sanin me ya faru ba, na ga dai ana tafiya dani da gudu, ina wuce wani irin haske. Sai muryan da ban san ta waye bana yana kirana can da nisa.
"Munnah!!!"

    Cikin wani irin faduwar gaba ta fito bayan ta gama sauya kayan ta, tana kallon abokan. Aikin da da suke mata magana, jin su take amma ba zata ce tana sane da abin da suke fada ba.
"Dr Zainab kina lafiya?"
Wani irin bugun zuciya taji lokacin da aka shigo da wata mara lafiya, mai da kallonta tayi kan yarinya domin a hannun wani mutum take yana niman agaji.
"Ku taimaka min don Allah," da sassarfa

Please Login or Register in order to submit comment