Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duniyar nan ita da abin cikin domin har ya daina hulda da ita burin shi idan ta haihu a warware wancan auran a daura dashi.   Sau dayawa yana ganin k'iyayyar shi a kwayar idanun ta, bai tab'a zaton zata girma haka ba.

    Tsawon Wata goma sha biyar ana wannan yanayin, har ranar da ta haifi abin cikin ta, wanda ko fuskar shi bata kalla ba, tayi tafiyar ta, wannan abin yayi masifar mishi ciwo, yasan muguwar al'adun sun na cire mace daga gidan mijinta a tafi da ita shi ya lalata mishi kome na shi. Tunda ta tafi ya kasa koda fahimtar kanshi da zuciyar shi,  yasan ita yake so, amma bai san yadda aka yi ya iya cutar da ita da soyayyar shi ba.

       Yayi kuka yayi danasanin, ya ji a ranshi ya zalince ta, musamman abinda ya haifa, wannan abin ya saka shi jin tsanar kanshi da kanshi, meye matsayin Yaron? Meye zai gayawa Yaron? A yanzun ina uwar Yaron take, ya cuci kanshi da duniyar shi ya kore farin cikin shi da kanshi, har yayi nadaman zuwa bikin ranar. Kafin ya gudu yakan zaga yaje bayan bukkar Aminatu ya zauna yana jin shashekar kukan Yaron, zama yake yaji duniyar tayi mishi zafi da kunci shi yasa matukar zai cigaba da ganin halin da jaririn yake ciki zai iya sanya shi zuciyar shi ta buga yasa shi tafiya ya bar Aminatu da D'an shi ba wai ya gudu dan ya tsani Yaron ba, ya gudu sabida abin kunyar da ya janyo wa yaron, ya gudu domin barwa Kanwan shi da abokin shi yaron tunda Allah bai basu ba haihuwa ba, yasa shi ya bar musu shi. Kuma yayi alƙawarin ba zai tab'a dawowa ba, ya hakura da su, har da Aminatu da jinjirin. Yayi tafiya inda shima bai san zai tsaya ba shi yasa yace karta nime shi.

***
Dawo labari....
--
A hankali ta goge kwallar da ya zubo mata, tare da cewa.
"Iya wannan kawai ya isa ya tarwatsa mishi farin cikin shi....
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx

_Tambaya suna yawa! Wasu ina iya amsa su, wasu kuma ina kallon su na wuce su basu da Amsar a lokacin.... Kuyi hakuri labarin nan dauke yake da Zanen kaddara wanda alkalamin ƙaddara ta rubutashi ba labarin soyayya bace da za a ci soyayya akwai a soyayya labari ne wanda zaka samu yana tafiya da asalin rayuwa ban ce labarin ya faru da gaske ba, sai dai labarin iya iya tafiya kamar yadda yake faruwa a wani kaulin, zaku yi hakuri dani nima kuma zanyi hakuri da ku, idan uzurina ya shigo zan jingine nayi sabgar gabana, idan kuma na sami sarari zan baku sama da yadda kuke tsammani! Banyi alƙawarin kyautatawa ba, amma nayi alƙawarin farantawa ban yi alkawarin zai yi dadi ba, amma nayiwa kai na alƙawarin zai badda yadda zai tafi, idan kuka duba taken labarin Journey of Destiny! Wato Tafiyar ƙaddara... Dan haka idan nayi kuskuren ku min Uzuri sabida nima Yar Adam ce! Idan nayi dai-dai ku tuna da kalaman ku da tunatarwa! Kuyi hakuri dan labarin Yanzun muke Littafi ba Ɗaya fatan Alkhairi 👏_

Harshen ka...
BABI NA BIYAR.

Goge kwallar tayi tare da kurawa hatsin da aka kawo mata surfe, yau kimanin shekaru goma sha daya zuwa sha biyu, babu wanda ya tab'a ganin ta tayi fada da mutane, Allah ya zuba mata baiwar hakuri da juriya, ta kuma jure halin dan rikon su. Shi yasa yaron ya tashi da mugun kaunar su.
B'ata tab'a daga hannu da sunan dukan shi dan yayi mata laifi ba, sai Addu'a, da fatan shirya shi yasa mutanen gidan da suke, wasu ke jin haushinta, ga Mamoon da mugun sakalci, bai san yayiwa kanshi wani abu ba sai an mishi. shi yasa ya tashi a sakalce, duk abinda akewa yara masu gata shi ake mishi, kai ko takalmi Mamoon baya saka me cinyayyen kasa. Kai rigar shi ce ta yage ba zai kuma sakawa ba sai wata.

Gashi dai iyayen rikon shi talakawa ne futtik, amma bai taso da yanayin talauci ba, sai gata kamar jinin gwamna. Haka ta mike tare da shiga cikin gidan ta dauko langa ta dibo ruwa ta wanke mishi tufaffen shi, wanda duk bayan wata biyu sai an dinka mishi riga da wando, kala biyu koda su basu saka ba shi zai saka. Wani irin kauna suke mishi wanda shima Yaron yasan da haka shi yasa ya taso babu ruwan shi da kowa.

Kai zunzurutun bakin hali inji mutanen gidan dan sukan ce bai gaji halin Aminatu da Malam Sanda ba, ya dauko mugun hali a wani gurin can, ko dakin mutane baya shi, yana bakin kofar shi, gashi da farin jini yara cika suke a dakin su. Idan ya kwanta ya mike kafa yace kar ayi magana babu me tari a dakin. Idan kuwa yace a fita dan Uban Yaro ko kaho ne akan Ubanka sai ka fita wannan yasa Yara dayawa suke tsoron shi. Bai da fada amma iya maganar fatan baki ya isheka bakin cikin wani guda....

<<>>
Tunda aka nuna mishi ajin shi baban shi yayi mishi fada kafin ya ciro kudin tara ya bashi.
"Bana kudin nan yayi yawa" ya faɗa yana juya kuɗin.
"Yaron arziki kenan, bai yi yawa ba. Ka rike shi kaji karka yi faɗa kaji na san ka baka da abokin fada kayi karatu kaji yaron baba."
Cogewa yayi yana kifi kifi da ido.
"Almamoon meke damunka?" Duk ya rud'e.
"Baba kazo ka ɗauke ni, a keken ka" murmushi yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah zan zo da kaina, na dauke ka yayi maka?" Ya tambaye shi gyada kai yayi, sannan ya kuma raka shi bakin aji, yayiwa malamin sallama, sannan ya ce.
"Maza shiga dan Baba." Haka ta shiga bai kalli inda malamin yake ba, ya juya yana kallon Baban shi.
"Baba idan kaje gida kaci abinci kaji"
"Insha Allah dan Baba"
Sake baki suka yi suna kallon ikon Allah, wannan irin soyayyar fa, ko makarantar Firamare da ya gama basu yi wannan dirama ba, gyara jakar shi yayi yana kallon ajin kafin ya hango wani kujera babu kowa. Ya zauna.
"Meye sunanka?" Malam min ya tambaye shi.
"Almamoon Isma'il Wodaadabe" ya faɗa a sanyayye,
"Zauna"
Ya zauna yana kallon allon, duk da makarantar kudi ne, haka bai hana shi fahimtar yadda ake koyarwa ba, kasancewar wanda ya gama ma, na kudin ne. Ana tashi tara ya ya dauki jakar shi ya fita.
Dariya yan ajin suka mishi. Murmushi yayi musu tare da kallon su. Haka ya fita yayi break da aka dawo aji aka cigaba da karatu.

Karshe daya Baban shi ya zo da keken shi ya dauke shi a gaba, a hanyar komawar su gida ne suka bi kasuwa, baban ya saya musu kayan abincin da za ayi na dare. Sannan ya dauke shi suka tafi. Har zasu tafi wani abokin aikin Malam na rana shima buzu ne yace mishi.
"Malam Umaru, idan ka dawo ina son magana da kai" dan haka ya kawo Mamoon gida ya koma, zama yayi kusa da Mutumin yace mishi.
"Malam Nasiru gani"
"Kayi hakuri idanuna idan suka ga abu bakina baya shiru, musamman kai da muke tare da kai." Shiru yayi yana kallon ƙasa kafin yace mishi.
"Idan ka tafi ka bashi wannan zoben ya saka a hannun shi duk da kana boye mishi abu akan shi. Kayi hakuri gaskiya rayuwar shi ce akwai daukaka akwai faduwa, bayan nan ban san meye Allah ya ƙaddara ba, amma gaskiya na tausaya mishi domin wata irin ƙaddara da zata sanya shi bayyana kanshi itace ƙaddarar da zata sanya shi kuka.

Bana duba ko buga kasa, amma tabbas na hango abubuwa dayawa da yasa ba zan yaga maka ba, lokaci zai bayyana kanshi" murmushi yayi sannan yace.
"Kuyi ta mishi addu'a Ubangiji ya shiga lamarin shi. Indai har zai jarabce shi ya jarrabce shi da abin da zuciyar shi zata iya daukar shi.". Jikin Malam yayi mugun sanyi sosai.
"Karka cigaba da boye shi, domin zai fidda kan shi, wani lokacin muna son farin ciki amma sai kaga akasin ƙaddara ko tafiyar ƙaddara ta shigo mana, haka zamu yi hakuri da abinda Allah ya bamu, ba tare da mun katse wanda muke ba, idan ka duba ƙaddaran wasu sai ka zata laifi suka yiwa Allah ne yake jarabtar su.

Wani lokaci kuma kaga kamar Allah ya fison wasu shine ya basu duniya da abinda yake cikinta, Ya Allah ka jarabce mu da abinda zamu iya, karka jarabce musu da abinda na zamu iya ba. Kayi hakuri na saka ka damuwa karka yarda maganata ta sanya ka damuwa, kayi hakuri don Allah."

"Nagode sosai malam Nasiru."

Malam Nasiru irin mutnen nan ne da Allah yayi musu baiwar ilimin addinin musulunci, musamman litattafan addinin musulunci, matsalar da aka samu yana da tab'in ƙwaƙwalwa ne, domin sabida ilimin shi aka jife shi, shi yasa yake abu kamar mahaukaci, amma kuma a haka Allah yayi mishi ido, idan ya fadi abu da ya gani tabbas Allah yana tabbatar da alkhairin, sai dai idan haukar ta motsa toh kome zai fada a surdudu zai fada. Dan haka Malam yana tashi ya koma shagon malam Bukar. A kasuwar nake yana sayar da shayi, shi ya nimawa Malam Umaru gadin kasuwa, nan ya kalli Malam Umaru yace mishi.
"Naga Nasiru hoge ya kiraka, toh karka yarda da abinda zai fada dan kai ma kasan ba lafiyar kwakwala gare shi ba, dan haka ka watsar da batun da ya gaya maka shiririta ne kawai da haukar shi da ta MOTSA."

Ajiyar zuciya malam ya sauke, duk da yasha ganin idan ya fadi abu yana tabbata, haka ya saka shi watsar da batun.

***
Yana ajiye shi a kofar gida da cefene, ya juya yana faɗin.
"Maza shiga gida Dan Baba" haka ya shiga, tare da sallama kamar wani babban mutum, matan da suke tsakar gidan basu amsa mishi ba sai Innar shi ta fito tana amsawa.
"Barka da dawowa Dan Inna" wani irin murmushi yayi tare da kallonta yana faɗin.
"Yawwa Innata" ya sa kai zai shiga Dakin kai Salihu yace mishi.
"Almamoon wai da gaske ka fara zuwa boko?"
Kallon kayan jikin shi yayi, sannan yace.
"A'a ban fara ba ina jiran ranar da Iyarka zata biya min kudin ne"
" Ba dai iyata ba sai dai Iyarka"
"Eh gata nan jikin garka ta gode" ya nuna uwar Yaron da take bakin kofa zaune, ya shige da sauri dakin su. Matar me suna Murjanatu ta mike tsaye tare da cewa.
"Wallahi sai na ci Ubanka dan banza me kama da yan daudu. Me mugun hali kawai" zuba mishi ido Innar shi tayi.
"Me yasa ka cika rigima ne?"
"Kiyi hakuri" ya faɗa tare da gyara zaman rigar shi, yana kallon jerin gwanon kwanonin da aka shirya na abincin shi da na Baban shi. Zama yayi tare da fara cin abincin shi.
"Ya karatun kana Fahimta?" Gyada kai yayi ya a kwasar tuwon gero miyar kuka.
"Ina fahimta, sai dai yaran ajin mu ne zan koya musu Yaren da zasu Fahimta."
"Bana son damuwa, kayi hakuri mutane baka sauya musu halin su. Haka zaka gansu ka Barsu?"
"Innah?" Kallon shi tayi, sai kuma ya share maganar.
Lokacin islamiyyan na yi yaran gidan suka shirya baki daya, suka nufi islamiyyan.
***
Zaune yake yana kallon matar shi, bayan ya gama cikin abincin rana, ya labarta mata abinda suka yi yau a kasuwa, kallon shi tayi na wasu dakikai. Kafin ta sauke ajiyar zuciya.
"Me yasa ka tsaya kana sauraron shi ? Irin wadannan mutane basu da aiki sai na haddasa rikici a tsakanin zukatar al'umma insha Allah babu abinda zai sami Almamoon dina aniyar moɗa tabi Randa sannan ka mai da mishi zoben shi ba zai saka ba."

Ta faɗa tana jin kamar ta rufe mutumin da duka, ina ma da zata ganshi da ta zabga mishi mari, kwafa take a kai akai.
"Ayya Kabo kiyi hakuri mana."
"Assalamun Alaikum, Barka da gida" sallamar Almamoon ya katse musu, abinda suke fada.
"Waalaikumun Salam, shigo Babban mutum" inji Baban shi.
Yana shigowa ya ajiye allon shi yana tab'e baki.

"Yau na gaji, kai ka rantse da Allah nayi abin arziki" ya faɗa yana kwanciya a jikin Innar shi.
"Ai karatun ai abin arziki ne, sannun kaji tashi kasha dawwo" da sauri ya tashi ta mika mishi kofin silver, yana sha yana murmushi. Sabida yadda yaji sugar kamar zai tsinke mishi kunne.
"Innah hala baku sha ba?" Ya tambaya, mikawa Baban yayi yana faɗin.
"Nasha itama tasha kai ne muka ragewa"
"Allah ya kara muku budi, ya kuma raya ni, nayi muku abinda kuka min na zama me tausayi a gare ku iyaye na"
Kallon juna suka yi kafin suka ce.
"Amin Ya ALLAH"
"Toh ni dai zan tafi Almamoon ban da rigima ko;"
"Ubangiji ya kiyayye ya dawo da kai lafiya."

Haka suka mishi addu'o'in, sannan ya fita, bayan fitar shi ne suka shiga hira har ta fita tayi musu abincin dare, Alhamdulillahi suna ci sau uku a rana haka ba karamin arziki bane.

Kullum idan zai tafi makaranta Baban shi ke kai shi makarantar, haka ya mugun kawo renin hankalin a tsakanin yan ajin su, har ana mishi kallon abubuwan da yawa, akwai wani yaro me suna Abdul Hadi, kato ne ashe gurin zaman shi Almamoon ya zauna sunyi tafiya, ranar da ya dawo washi gari ya dawo makarantar, shine yazo ya ga Almamoon a kujeran shi, dama an kai mishi gulma.

Yana zuwa ya daki kujeran, zunzurutun karfin kai bai saka Almamoon d'ago kai ya kalle shi ba.
"Kai tashi min a gurin zama"
"Daga gidanku kazo dashi?" Ya tambaye shi,
"A'a daga gidan me kawo ka a keke"
"Gaskiya kan shi yasa na ganka haka ashe abinda ake fada akan ka gaskiya ne" ya faɗa tare da mai da hankalinsa kan Littafin gaban shi.
"Kai meye kake nufi?"
"Yo ina zan gaya maka tunda baka gane bakwai da sha bakwai, wuce kawai tukekke" ya faɗa tare da bashi guri ya zauna.
"Kai ba zaka zauna ba. Domin zaka shafa min bakin ka ne"
"Ni kuma zan zauna domin zaka da irinka arziki ne, zan gaya maka abin da ake fada a kan a cikin ajin"
Take yaron ya zaro idanu, kafin ya matsawa Almamoon, ya zauna . Yayi ta Bin shi ya gaya mishi me suke fada akan shi, fir yaki kashe idan ya dame shi da tambaya ya caka mishi bakar magana, haka yasa shi jan bakin shi yayi shiru, dan ya fahimci Almamoon ruwan sanyi ne dafa moda.

Haka suka ci-gaba da zama a tare da juna, har zuwa lokacin da suka saba da juna.


Dukda bai shiga harkan yan aji da mutanen makaranta, amma kuma, ilimin shi da kyawun dabi'ar shi ta janyo mishi soyayyar malamai, ta kai ko gasa aka saka shi yakewa makarantar su na daya, haka yasa malamai da dalibai ji dashi.

A hankali ya zamewa makarantar su, tauraro duk inda aka shiga makarantar ne ke gaba, har sai da shugaban makarantar ya bincika suwaye iyayen shi, daga karshe ganin yadda suke iya daukar nauyin shi dukda faffutikar rayuwa suke, yasa shi dauke musu nauyin biyan kudin Makarantar, haka ba karamin dad'i yayi musu ba, domin kuwa basu zata zai zame musu Alkhairi ba, lokaci guda ya sauya musu ƙaddarar su.

**
Lokacin da suka shiga aji uku, a lokacin ne suka tashi a gidan da suke, sakamakon sayar da gidan duk suka watse, suma suka koma wata unguwa kusa da makarantar su. A lokacin Almamoon yana da shekara goma sha biyar.

Ya zama matashin saurayi, me tashe da kanshi. A lokacin kan shi yana masifar ja ga kuma Yan mata da suke mugun rigima akan shi idan yazo har hidima suke mishi, wasa wasa yaran masu kudi suka shiga mishi barin kudi, hidima suke mishi. Idan aka yi break haka zasu mishi sayayya kayan abinci har fada ake akan shi, bai tab'a d'ago kai ya kalle su ba.

A lokacin daga Aminatu da Sanda, hankalin su yana kan shi kome yake suna kallon shi, ga Addu'a, da ake bashi na rubutu da na kariya saboda kambun baka da kambun ido, sai da ta kai baki daya basu da nutsuwa domin duk wata saiwa da itacce haka ake sassaka mishi ana bashi yana sha.

Ba sai ga Almamoon ya fara gane gane ba, ranar da ta fara ganin abu, kwana suka yi akan shi. Domin kuwa hana su runtsawa yayi. Haka suka kwana akan shi, sai goshin asuba ya samu barci.

A ranar bai je makaranta ba, sai da aka kwana biyu, sannan ya koma makaranta, sai da takai zoben da yake gurin Malam Umaru shi ya saka mishi a hannu, shine ya sami saukin abinda yake gani, sai suka kai ta kokarin rufe mishi ido, tunda garin niman gira an rasa ido baki daya.

Karshe dai da yaga suna damuwa da halin da yake ciki sai ya daina gaya musu, amma yana tsorata sosai, dan ma yana da taurin zuciya ne.

Haka suka yi jarabawar su ba gama aji uku. Suka shiga aji huɗu. Abu daya yake damun shi yadda abokan shi suke mishi tsaya da me muryan mata. Haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba, yazo gida yana gayawa Iyayen shi. Rarrashin sa suka yi tare da gaya mishi kar ya sake ya biye musu, dan ba abokan kwarai bane. Ya fita hanyar su.

Sai ya ji maganar ya fita hanyar su, har ya fara maida hankali a abinda yake gaban shi, aka dawo da wata Daliba makarantar, me suna Salimah Dawood, kamar da wasa yarinyar ya makale mishi. Kullum sai anyi dambe da ita da wata tsuhuwar budurwan shi,(😛🙄 Maryam Mimi ayi a hankali dan baki yayi kasuwa dambe ake akan shi)

Haka zai zauna yana murmushi cikin jin dadi, ana dambe akan shi idan kaga yadda ake abin zaka fahimci yarinta ke damun su baki daya. Idan shugaban makaranta ya kira shi shaida murmushi yake sannan yace mishi.
"Yallabai ban me yasa suke dambe a kaina ba, sai dai kawai naji ana kiran suna na, Ni uwayena karatu suka turo ni ba soyayya ba, dan haka duk wacce take ganin zata iya tayi abinta, dama ta samu "

Abin yayi matukar bawa kowa mamaki, domin tunda ake dashi bai tab'a magana kan ana dambe akan shi ba, sai yau. Haka suka fito bayan anyiwa yaran fada. Tare shi Salimah Dawood tayi tana kallon shi.
"Ka kyauta abinda kayi?"
"Meye ya faru!" Ya tambaye ta,
"Toh kenan baka san meye kayi ba?"
"Ina zan sani, tunda ba ofishin yan kai kara bane ni" ya faɗa zai wuce.
"Wai meye ka taka ne?"
Murmushi yayi tare da ce mata.
"Abinda kike bi, abinda kika gaza gani a kan sauran mazan makarantar." Ya taka gabanta tare da kallon cikin idanunta,
"Suna kike bi, abin da nake ji dashi kike bi, shi yasa baku gaba na karatu nazo yi"

"Dan matsiyata kawai dan an damu da kai"
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Sabida kudin Ubanki kika gaza mai da hankali akan karatun ki, kina bin malamai Office suna kara miki maki, shi yasa aka cire ki a can aka kawo ki nan, toh ki duba nan baki daya sansani na ne, kika sake na kuma kamaki kina dambe da Daya daga cikin yan matan makarantar nan sai na zane ki a gaban jama'a mata, Ni matsiya ci ne, amma kuma me tsaye akan kafarshi me bin maganar iyayen shi, bake da baki jin batun iyayen ki ba."

Haka ya yab'a mata bakar magana sannan ya barta a tsaye a gurin, tana kuka.

"Ai dama bata san waye shi bane, shi Sarkin mu ne, gashi talaka da babban zuciya, shi ba irin sakarkarun makarantar nan bane." Suka tafi suna mata dariyar renin hankali, tuni ta fara kuka me ƙarfi.

Almamoon ba yawa ba dad'i, idan yayi yawa ma sai kayi kuka da kanka
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx

_Real integrity is doing the right thing, knowing that nobody’s going to know whether you did it or not._

Tafiyar ƙaddara..
BABI NA SHIDA
Rayuwar da aka gina shi domin Allah tafiya yake cike da Yardan Allah, duk wata nasara tana tafe da wanda Allah ya baka, wannan shine adadin farin cikin da Almamoon wanda yayi saukar Alqur'ani wanda yayi daidai da kammala makaranta shi na Sakandiri, kuma Allah cikin ikon shi ya samu tallafin karatun jami'ar Maryam Abatcha dake garin Maradi...

Duk wani ƙaddara ta fara ne daga wannan yankin, duk wani tafiya daga nan ta fara, sai gashi cikin Ikon Allah tafiyar ta kuma canzawa izuwa Maradin.

Bayan kwashe watanni suna jiran sakamakon, yana fitowa shi da iyayen shi suka kuma dawowa Maradi domin su abinda zasu iya mishi, Allah cikin ikon shi ya kuma basu tallafin wasu mutane, suka taimaka musu har aka kammala cuku-cukun makarantar, sannan suka dawo dashi gida, aka shiga fadi tashi yadda zasu sami damar nima mishi dakin makaranta domin nauyin karatun shi aka dauka su kuma zasu biya kudin daki da na littafai, abin tausayi wannan karon ma akwatin asusun ta kuma fasawa aka samu kudi me yawa, sannan ta bawa Malam suka dawo Maradi da Almamoon aka kuma biyan kudin makaranta. Sannan suka koma.

Cikin kewar shi suke kallon shi.
"Kasan waye kai? Ka kuma san dalilin ka na zama a gurin nan, akwai al'amarin da zamu gaya maka amma a yanzun shekarunka basu kai nauyin ɗaukar abinda zamu gaya maka ba.

Jami'a ba kamar Sakandiri bane, a can gidan Yanci ne. Ba gidan da zaka zauna kayi laifi wani ya fito yayi maka fada bane, guri ne na kowa kanshi ya sani, dan Allah ka dubi girman Allah karka samu kuka, kamar yadda kace zaka sanya mu, farin ciki ka cika mana burin mu, mun san ba iyawar mu bane yasa kake kare kanka Allah ne yake kare ka, zaka shiga inda babu kunya ko tsoron Allah, don Allah karka watsa mana kasa a idanu, ka taimaka kayi abinda muka turaka Allah ya tsare maka imanin ka."

Kallon su yayi yaga yadda suke share kwalla, sai yaji a ranshi akwai abubuwan da ya dace ya tambaye su. Amma kuma,
"Babana me yasa kuke son na rayu a haka? Bayan akwai matsala idan wata rana."

Rufe baki Innar shi tayi tana kuka tace.
"Ban da karatun nan bamu muna biya ba, wallahi da ka fasa, tsoron goben ka muke ji, shi yasa muka lullube farin cikin ka, kayi hakuri kayi wannan tafiyar shima kamar tafiyar ƙaddara ce, babu wanda yasan me zaka taras a gaba, don Allah karka yarda wani ya yaudare ka, kaga kai ɗaya muka mallaka, don Allah ka rufa min asiri."

Kallonsu yayi yana son tambayar su, amma a yadda yake hango firgici da tsoro ya saka shi had'iye tambayar, ya haɗa kayan shi da wanda yake daya sakamakon dan kudin da iyayen shi suke bashi dukda ba wani samu suke ba, dan Tun lokacin da yace musu yana son fara aiki a kasuwa suka daina barin shi yana niman abubuwan bukata, wani lokacin har kuka yake me yasa ba zai tafi kasuwa ba. Haka suke kokarin faranta mishi amma sabida sun hana shi sake yasa shi hakura.

Yadda ake kaf-kaf dashi wallahi ko mace sai haka, akwai ranar da ya faɗa ai yana da yan mata, a makarantar boko, ranar sai da Innar shi tayi zazzaɓi, idan ta

Please Login or Register in order to submit comment