Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍




🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴




Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)





*Page 1*






*Barka da sallah da fatan kowa yayi sallah lafiya*???





****** Manyan motocine bak'ake guda biyar a jere da juna, suna tafiya a kan lafiyayyen titi wanda yaji kwalta sai jiyaniya kakeji Tana tashi " Wanda motar jami'an tsaroce Suka rako yarima sauban domin Kula da lafiyarsa."

A katafaren wani babban gida Mai girman gaske mai d'auke da kwalliyar sarauta a jikin gidan duk wanda yaga gidan yasan gidan sarauta ne dibo da yanayin gidan da kuma fadawan dake, gadin get din kofar gidan,
Idan ka diba KO wanne yana sanye da uniform dinsa blue tare da Dan sirkin ja a, jikinsu,
gidan adalin SARKI ne maiji da mulki da k'asaita."
Fadawa dake gadin get d'in k'ofar gidan zasu Kai kusan su ashirin ko wanne da abinda yake Kula dashi a wurin,
Suna jiyo jiniya da sauri ko wannensu ya mik'e tsaye jiki na rawa Suka bud'e get sai murmushin farin ciki sukeyi tare da d'agawa motocin hannu cike da farin ciki, sai da motocin Suka gama Shiga cikin gidan gaba, d'aya snn suka rufe get d'in, Suka runtuma su dukansu sukabi bayan motocin suna zubawa yarima Sauban kirari."

jiniya tare da kid'e kid'e da bushe bushe ya karad'e gidan sarautar ga baki d'aya Wanda duk, wani halitta dake rayuwa a cikin gidan yasan yarima sauban ya iso mahaifarsa."

Da gudu sarkin gida ya Isa fada ya durk'usa a gaban maimarba sarki Abdullah ya Kai gaisuwa gareshi cike da, girmamawa tare da yimasa Albishir na isowar yarima cikin k'oshin lafiya."

Murmushi sarki yakeyi Yana girgiza kai, Wanda duk Wanda ya kalli fuskar sarki kasan, yana cikin farin, ciki d'ansa Wanda yafi soyuwa a ransa ya, dawo, cikin k'oshin lafiya,

, fadawa suka shiga cewa sarkin gida, "sarki yaji dad'in wnn Albishir naka, sarkin yayi murna, sosai, tukuicin ka na musamman ne a wurin sarki Mai Adalci."

"Runsunawa sarkin gida ya Kuma Yi Yana "fad'in godiya nakeyi Allah ya k'ara Nisan kwana, da lafiya,
Snn ya tashi ya fita cikin sauri yanufi sashen fulanin sarki domin y Kai mata Albishir d'in dawowar sauban."

Cikin saurin masu Kula dashi suka fito daga motar da suke,
suka zagaye motar da yake ciki sai da aka d'auki kusan minti biyar suna zagaye da motarsa snn suka bud'e Masa ya fito, duk da dama hakan Al'adarsa take baya saurin fitowa a mota da zarar anyi parking sai ya d'auki kusan minti biyar a ciki snn yake fitowa." Saboda tsaro😎

Kyakkyawar K'afarsa yafara zurowa a waje Mai d'auke da rufafin talkaminsa masu tsananin kyau,
duk Wanda yaga yanda ya fito da k'afar sa a waje yasan mamanlakin k'afar ya Kai k'arshe wurin had'uwa da gayu,
cikin k'asaita ya Kuma ziro k'afarsa d'aya sai da a kuma d'aukar minti biyu snn,
Cikin isa da mulki yafito da gangar jikinsa daga motar,
subahanallah tsarki ya tabbata ga mamanlakin wnn halitta,
Dogone Mai matsakaicin tsawo fari ne fes, kakkaura Mai cikar halitta, fuskarsa Tana zagaye da saje Mai had'i da gashin Baki Wanda ya kwanta luf a fuskarsa ya k'ara yiwa fuskar k'awanya da adon kyau, hancinsa dogone har baka yana da manyan idanu, tare da d'an k'aramun bakinsa, fuskarsa Tana d'auke da murmushi Domin Yana cikin farin cikin ganinsa a cikin k'asarsa ta haihuwa wato Nigeria."

*SAUBAN KENAN D'AN SARKI ABDULLAH*

Busa Kakeji tak'ara tashi tare da kid'e kid'e Ana zuba Masa kirari tare da yimasa sannu da zuwa a Nan take harabar gidan sarautar ta cika da kuyangi da bayi tare da fadawa ko wanne sai kawo gaisuwa yakeyi cike da girmamawa
Murmushi kawai yake sakar masu tare d'aga masu hannu Alamar ya Amsa,
Kasancewar Sauban mutum ne Wanda baya wulak'anta nak'asa dashi, snn yana daraja d'an Adam musamman bayinsa da kuyanginsa da duk Wani Wanda yasan yana k'asa dashi,
Dan hakan suma suke matuk'ar son sa suke gurmamasa tamkar sarki dake mulki,
snn suka bi bayansa sukayi masa rakiya har zuwa sashensa."

Hakince take akan kujerarta ta sarauta wacce tazo da ita tin daga gidan mahaifinta,
da gudu d'aya daga cikin bayinta tashigo ta Kai durk'ushe a gabanta tana fad'in "ranki ya dad'e Allah ya taimakeki ya k'ara maki lafiya da Nisan kwana ya uwar gijiyata nazo maki da Albishir Mai dad'i, jarumin mijinki d'a d'aya tamkar da dubu kyakkyawan mijinki Mai cikar Kamala da haiba mai kyawawan halayya irin naki, a yanzun nan ya dawo daga k'asar England ranki ya dad'e na ganesa da idona yanzun nan ya nufi b'angarensa duk wannan k'id'e kid'e da bushe bushen da kikeji duk shi akeyiwa Ana tayashi murnar dawowarsa."

Tsawa matashiyar budurwar Wanda bazata wuce shekara 25 ba, ta daka mata cikin d'aga murya tace "yimun shuru rufemun bak'in bakinki mummuna kawai marar kyawon gani tabbas yau sai kin fuskanci hukunci Mai tsanani a gareni tinda har kike iya durk'usawa a gaban idona ki dinga zanyanomun suffar mijina tare da yabonsa,
Hakan ya nuna a duk lokacin da Kika gansa sai kinbishi da ido kina k'are masa kallo kina masa kallon k'urullah, kina kallemun shi tes tin daga k'asansa har samansa."
shin ko kin Manta ban had'a yarima da kowa ba?
Shin ko kin manta da Nasha fad'a maku da zarar kunga fitowarsa ko wacce daga cikinku ta rufe idonta kada ta kuskura ko sawon k'afarsa ta kalla bare a Kai ga kayan dake sanye a jikinsa."

Ta nuna mata wani fili dake can bayan sashenta nesa da ita sosai filine Wanda ba komai a cikinsa sai itacen mangwaro da gwaiba tare da iccen bedi Wanda ya rufe wurin ruf ko wacce irin halittar k'waro mai cutarwa zaka iya samunta a wurin kasan cewar ba kowa yake zuwa wurin ba,
Ta nuna mata wurin tace "a can Zaki dinga kwana har tsawon sati d'aya batare da anbaki abinci ko ruwan Sha ba, snn kada ki kuskura nazo wurin na tarar da kwarar ganye d'aya ya fad'o k'asa batare da kin d'aukeshiba."

Runsunawa tayi tana fad'in tuba nakeyi ranki ya dad'e godiya nakeyi Allah ya k'ara girma da d'aukaka, snn ta tashi tanufi wurin da aka umurceta tana tafiya tana sharar hawaye domin tasan dolene ta aikata abinda uwargijiyarta tasakata Wanda tasan da zarar tashiga wurin mutuwa kawai zatayi domin batasan iya abinda zata tarar a wurin ba "

Yana shiga harabar b'angarensa ya d'agawa fadawa hannu alamar su dakata cak suka tsaya tare da runsunawa cike da girmamawa snn yayi masu nuni akan suyi tafiyarsu,
Cikin sauri suka juya suna fad'in kahuta lafiya yarima mai jiran gado, suna zuba masa kirari suka bar wurin, Wanda ya dad'e da shigewarsa sashensa. "

K'ofar bithdrom d'insa ya tura yashiga komai yana nan a gyaransa tsaf tamkar yana rayuwa a cikin d'akin Wanda yasan aikin Amintattun bayinsa ne masu kula da b'angarensa tare da abincin sa. "

Ajiyar zuciya ya sauke ya kai kwance akan lafiyayyan gadonsa Wanda yaji zanen gado na Alfarma, yashiga furta Alhmdulillah tare da kai hannunsa a fuskarsa yashafi sajen dake kwance a kan kyakkyawar fuskarsa har, zuwa gemonsa ya lashe leb'onsa na k'asa tare da lumshe idonsa yashiga tunanin rayuwarsa ta, baya tare da, rayuwar da akeyi a cikin masarautar nan tare da dalilin tafiyarsa, England. "

Doguwar ajiyar zuciya ya sauke Tare da mik'ewa tsaye ya soma cire kayan jikinsa domin ya d'an watsa ruwa ya shirya ya tafi fada domin gaida maimartaba mahaifinsa
Bayan ya kammala yin wankan ne yafito d'aure da towel hannunsa yana d'auke da d'an k'aramun towel yana tsane ruwan jikinsa zuwa kansa,

Turo k'ofa akayi cikin isa da k'asaita ba tare da anyi sallama ba aka shigo,

K'amshin turarenta ya tabbatar masa da wacce tashigo, masa d'aki a dai dai wnn lokacin,
Ransa yab'aci matuk'a da rashin yin sallamarta, wato har yanzun saudat tana nan da halinta bata sauyawa ba,
shi har ga Allah ya manta da yana da wata mata a rayuwarsa." Saboda Sam ya tsani halin saudat da duk wani mai hali irin nata,
Ci gaba yayi da abinda yakeyi yayi kamar bai san tashigo d'akinba. "

Tsaye tayi wuri d'aya ta hard'e hannayenta a k'irji tana k'are masa kallo sama da k'asa cike da burgewa tare da sha'awa mai cike da so da k'aunar gwarzon mijin nata, amma isa da mulki tare da girman kai da takeji yana mata yawo ya hanata zuwa ta tunkareshi domin tayi masa sannu da zuwa tanajiran sai ya farayimata magana snn."

Jallabiyarsa ya d'auka ruwan madara yasaka tare da fesawa jikinsa turarensa mai dad'in k'amshi ya d'auki wata kyakkyawar leda wacce ya ajiye wuri d'aya da alama wani muhimmin abune ke cikinta ya zura talkaminsa ya rab'a ta gefenta zai fita. "

Gabansa ta sha tana kallonsa tana murmushi cikin k'asaita take fad'in haba sadaukina sai kace baka ganniba, bayan kasan wurinka nazo, kaddai ace har yanxun halinka yana nan baka canzaba,
Ko ka manta da cewa ni matarkace ta sunnah wacce katafi kabarni shekara d'aya KO waya baka mun bayan kasan Ina sonka Ina cike da kewarka."

Kallo d'aya ya mata ya kuma tanke fuska ba alamar wasa a tare dashi ya sanya kai yayi ficewarsa ya nufi fada wurin maimartaba. "

Sarkin gida a gaban fulani a durk'ushe yana kwasar gaisuwa, "Ranki ya dade Allah ya k'ara maki lafiya da nisan kwana, sarauniya a wurin sarki gimbiya a wurin sarki kece mai mulkin masarauta daga sarki saike wani Albishir naxo maki dashi "d'anki yarima Sauban ya sauka lafiya yanzun hakan yana cikin masarauta yana hutawa. "

Gaban fulani ya fad'i tayi saurin mik'ewa daga kishin kid'en da take zuwa zaune, a nan take ta had'e fuska,
Ta juya ta kalli sarki gida cikin k'asaita tace "bani labarin yanda ka gansa "

Sarkin gida ya saki murmushi ya kuma gyara zama yace "ranki ya dade yarima ya k'ara fari ya k'ara k'iba da cikar kamala dakin gansa kinsan yana cikin kwanciyar hankali da walwala. "

Tsawa ta daka masa tace "yimun shuru bashi na tambayeka ba,
Tanuna masa hanyar waje tace tashi kafita. "

Jiki na rawa sarkin gida yafita yana mamakin fulani KO dai akwai wani abin da yake faruwa ne da ita? . "

Cikin fushi da bak'in cikin abinda yarima ya Mata tashiga b'angarenta, ta zauna akan kujerarta ta mulki,
A nan take bayinta suka zagayeta KO wacce tashiga yimata hidima, a can mai kula da kayan marmarinta tashigo d'auke da tire na kankana tare da Apple ta durk'usa k'asa ta ajiye a gabanta ta yanko kankana tare da sunkuyawa tabata tace "ranki ya dade gata kisha idan kina da buk'ata. "

Wani irin wawan kallo ta wurga mata ai bata bari ta sauke hannunta ba ta d'auke mata fuska da Mari tare da kifa Mata tiren kankanar a jikinta, tana fad'in tashi kifita Dan ubanki na fad'amki Ina bukata ne?"

Mik'ewa tayi jiki ba kwari tashiga tsince duk kankanar da ta zube, tafita tana sharar hawaye tare da tsinewa hali irin na gimbiya saudat matar d'an sarki Sauban 'ya ga sarki Abdul'rahaman sarkin Bauchi
Amini ga sarki Abdullah mahaifin sauban sarkin da ke mulkin Adamawa. "






*labarina k'irkirana nayi mallakina ne idan kikaji yayi dai dai danaki to akasi aka samu*




*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍




🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴




Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_




*Page 3*




*Wai meyasa kukeyimun hakan ne, wasu da yawa suna Bina prv akan sunaso suyi rigester wnn littafin, bayan nariga da tun farko nafad'a maku cewa wnn book din bana sayarwa bane kyauta ne barka da sallah ne ga duk wasu masoyana masu bibiyar labaraina, pls Dan Allah ku daina Bina prv kunacemun kunaso kuyi rigester, ku kwantar da hankalinku tunda na lura da kud'in hannunku k'aik'ayi suke maku zanyi maku littafi na kud'i Amma ba wnn ba, wnn kyauta ne fatana kubani had'in Kai wurin yimun comment domin na fahimci sak'ona Yana zuwa yanda nakeso ngd*👏🏻👏🏻👏🏻






***** Runsunawa yayi cike da girmamawa da biyayya yace "nagode Ranka ya dad'e insha Allah zan kiyaye duk abinda ka umurceni dashi."

Murmushi sarki yasaki Yana kallon d'an nasa Wanda yafi soyuwa a cikin ransa, ya girgiza kai, tare da furta Allah yayiwa rayuwarka Albarka Sauban."

"Ameen Sauban yace snn yafita daga fadar ya nufi b'angaren Fulani."

A kishingid'e ya tarar da ita akan kilishinta tayi matashin Kai da titimi Mai adon gaske, tana ganin shigowar Sauban tasaki wani irin murmushi sai da ta d'auki minti biyar snn ta tashi zaune cike da yanga da k'asaita ta dubi sauban tana jiran ya Kai durk'ushe a gabanta ya kwashi gaisuwa kamar yanda ake mata,
sai ganinsa tayi yaja wuri d'aya ya zauna tare da tsureta da Ido kamar Wanda yake karantar wani abin a tare da ita.

Bak'in ciki da takaici suka rufeta, wato Yana nufin ita zata Fara yimasa magana kenan a matsayinta na sarauniya, to Yake ta gaidashi ko meye Yake nufi, ta lura da yanda Yake wani ji da kansa da nuna Isa da mulki kamar shine sarki gaba d'aya,
ta K'ara kallonsa a karo na biyu wnn karon Ido cikin Ido sukayi dashi suna kallon juna ko wannensu da irin kallon da Yake jifar d'an uwansa,
a Nan take taga y Kara yimata wani kwarjini,
Cikin ranta tace tsinanne kawai Mai halin uwarsa, saurin kawar da bintu nayi Amma bintu Bata mutuba domin tabarmun dafinta Wanda yafita fitina,
Ta Kuma kallonsa na karo na uku tace a ranta ai nasan idan zamu kwana a Nan bazaiyi mun maganaba idan bani nayi Masa ba,
Cikin dakiya da k'arfin Hali tace "barka da zuwa yarima, da fatan ka sauka lfy."

"Lafiya k'alau yace a tak'aice, snn yace "Banga sadeeg da Sageer ba.
Yi tayi kamar bataji abinda yace ba, a ranta tana fad'in d'an rainin wayo ko kagansu me zakayi masu bayan ka k'ara Tula masu haushi a ransu,
Yasan taji abinda yace yasa bai Kuma yin maganaba illah yaciro wayarsa domin ya diba Miss call din da akayi Masa a lokacin da Yake fada a gaban mahaifinsa,
Ganin sunan babban Amininsa Kuma abokinsa Wanda suyi fad'a suyi dad'i wato SAFWAN, murmushi yasaki domin yasan bai fad'a Masa cewar ya dawo Nigeria ba, Kuma tinda ya kwada Kiran numbersa ta Nigeria yaga yasamu yau zai Sha mita da surutu kenan Wata k'ila har kansa sai yasaka yayi Masa ciwo."

Wayarsa ya mayar a Aljihu Yana k'ok'arin tashi tsaye sai gani yayi an zagaye shi da kayan abinci iri iri, kallo yabi abincin dashi, bai fasa yunkurin mikewa tsayenba,
Ya kalli fulani yace "gimbiya ki huta lafiya yanufi hanyar waje."

Cikin d'aga murya Mai sauti Wanda batasan tana da itaba, takira sunansa tace "Sauban baka ganin an ajiye maka abinci ne?
ai yakamata ko lemu ne ka tsaya kasha idan baka buk'atar komai."

Shuru yyi na d'an minti biyu yana nazarinta snn ya bud'a Baki yace "bana buk'atar cin komai a halin yanzun domin lokacin cin abincina baiyi ba,
Snn Koda lokaci yayi nasan Saudat ta tanadar mun duk wani abinda nake buk'ata ki huta lafiya tare da ficewarsa ya nufi b'angaren sa Yana murmushinsa na gefen baki"

Cije Baki tayi ta mik'e tsaye cike da takaicin asarar da ya janyo mata cikin d'aga murya tashiga Kiran jakadiya cikin sauri jakadiya tafito daga cikin wani d'akin takai durk'ushe a gabanta tana fad'in "gani ya uwargijyata,
Fulani tace "jakadiya ya b'arar Mana da komai ya ruguzamana duk wani shiri namu, baici abincin ba yanzun meye mafita?"

"Jakadiya tace "ranki ya dad'e ki kwantar da hankalinki, idan yasan wata ai baisan wata ba, na rantse maki da Allah ba wani Wanda zai hau kujerar sarki sai Sageer ko Sadeeq."

Fulani tasaki murmushi ta kalli jakadiya tace "Dan hakan nake sonki domin ko shaid'an Yana tsoron sharrinki tare da muguntarki,
yanzun meye mafita kinsan na kashe kud'i da yawa wurin karb'o maganin nan Amma shegen yaron Nan Mai Kama da Aljanu yasaka nayi asara."

Jakadiya tace "ranki ya dad'e kibani Nan da zuwa gobe komai zai Kai k'arshe,

Fulani ta Kuma sakin murmushi tace "tashi kitafi Nima akwai abinda nake sak'awa Nan da zuwa goben."

*******************

Wani irin mulki takeji Yana mata yawo a cikin jinin jikinta sai juya bayi da kuyangi takeyi yanda ranta yakeso,
duka k'afafunta biyu suna kan d'aya baiwarta wacce tafi tsana duk a cikin bayinta saboda bak'in da take dashi gata gajeruwa gata da k'aton Baki,
A rayuwar Saudat ta tsani tayi Ido biyu da bak'in mutum ko marar kyan mutum tafison duk abinda zatayi Ido biyu dashi ya zamana Mai kyaune, Dan hakan ta tsani wnn baiwar tata."

Baiwar sai zufa take had'awa tagaji iya gajiya sabida gaba d'aya ta sakar mata nauyin jikinta,
Sauran bayin Kuma sai hidima suke mata cike da taka tsantsan gudun kada suyi laifi."

Cike take da Jin haushin Sauban, hak'urinta ya kusa ya k'are a kan me Dan yaga tana sonshi, shine yake mata duk abinda yaga dama, itama fa jinin sarautace 'yar sarkice 'ya d'aya tilo a wurin mahaifinta,
Yanda mahaifinsa yakeji dashi itama hakan mahaifinta yake ji da ita, duk wani abinda yakeji game da sarauta tamafishi jinsa domin sarautar masarautarsu tafi sarautar masarautarsu nuna mulki da Isa,
yau kam ta shirya Masa duk abinda za'ayi sai dai ayi Amma tagaji da neman mata 'yan uwanta namiji takeso Kuma mijinta."

Kuyangarta tashigo da gudu ta durk'usa a gabanta tace "ranki ya dad'e ankawo sabbin bayi 'yan mata ne wad'anda komai yaji a tare dasu nasan zakiji dad'in ma'a mala dasu sosai."

Mari ta kwad'a mata a fuska har sau biyu tare da sanya k'afa tayi shuri da ita, sai da kanta ya daki wani tebur Wanda kayan fruit suke a jiye a kansa, cikin d'aga murya Mai cike da Jin haushi tace "bana buk'ata tashi kifita,
Ta sauke k'afarta daga kan jikin baiwar tata, ta mik'e tsaye a fusace tanufi b'angaren Sauban."

Zaune yake akan lafiyayyen gadonsa da waya a kunnensa Yana magana da Safwan yana fad'in "inajinka kasan fa banason surutu kafa kiyaye,
Safwan yace "eh zakace hakan tinda kana kusa da gimbiya Saudat ni wlh Sauban kabani mamaki ace kadawo ko waya bazaka iya yimun ba ka shaidamun kadawo da Ban kirakaba da shikenan,
Allah wnn halin naka ya kamata ka canza shi,
Murmushi Sauban yayi tare da dafe Kai domin kansa ya Fara Sara Masa akan surutun Safwan yace "kaga yanzun dare ne inada buk'atar hutu gobe kazo zamuyi magana."

Safwan yace "kace hakan jarababbe asha soyayya lafiya,
Mere Baki Sauban yayi yace "Kai kasan abinda ake nufi da hakan, ni bansan hakan ba,
Safwan yasaki dariya yace zaka sani ne ai,
Da sauri Sauban ya kashe wayarsa domin kada ya Kuma damunsa a surutu."

Wnn karon da sallama ta shigo d'akin,
Wanda Sauban da yake zaune a kan gado sauke wayarsa kenan akan kunnensa ya d'aga Kai ya dubeta tare da amsa mata sallamarta."

Ido ya zuba mata Yana kallonta, itama shi d'in take kallo anan take taji duk wata tsewa da rashin mutumci da tazo dashi ta nemesa ta rasa, domin ba k'aramun gwarjini ya mata ba."
Kusa dashi ta nufa ta zauna a gefen gado a inda yake zaune k'afafunsu suna gogar na juna tace "Sadaukina lokacin cin abincinka fa yayi,
Ya kamata a gabatar maka da komai."

Shuru yayi bai amsa mata ba,
Yin Shurunsa hakan Yana nufin Yana buk'ata kenan,
ta mik'e cikin tafiyarta Mai cike da k'asaita da yanga tafita,
da kanta ta had'o Masa duk wani abinda tasan yana buk'ata domin Bata barin bayi ko kuyangi su tab'a abincin mijinta domin tana tsananin kishin mijinta Bata son kowa ya rab'eshi sai ita kad'ai
Gabansa ta dire Masa komai tare da zuba Masa farfesun kifi da fresh milk Mai sanyin gaske, sai da ya d'auki minti uku snn ya mik'a hannunsa da niyar zai d'auki kofin ya Kai bakinsa, tayi saurin sanya hannunta ta d'auka ta mik'a masa kallo Ido cikin Ido sukayiwa juna Sauban yayi saurin kauda idonsa daga kallonta snn ya amshi kofin ya Kai bakinsa Yana kurb'ar milk d'in,
Sai da ta tabbatar da yaci komai ya k'oshi snn ta had'a kayan da kanta, tafita dasu waje,
Ido yabita dashi Yana kallonta har zuwa lokacin da tafita daga d'akin ,
Yashiga tunani a ransa, indai kyaune Saudat kyakkyawace ajin farko domin babu inda Allah ya rageta, sai wuri d'aya zuwa biyu." Na farko shine Sam Bata da hallaya na gari akwaita da wulak'anta d'an Adam, d'ayan Kuma sirrinsa ne shi kad'ai yasan komeye,
shi dai har yanzun yakasa jin wani abin Dan gane da ita yasan tana sonshi tana kishinsa Amma

Please Login or Register in order to submit comment