Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeso a wayarka akwai abinda zanyi dasu."

Haka kuwa akayi duka hotunan safwan ya turawa bafaden,
sarki yace ka barsu a wayar ka Zan nemeka."

Suna tsaye jigun jigum a wurin suna zaman jiran fitowar likita domin suji abinda zai fad'a akan sauban fatansu daya kada ace masu ya mutu."

Suna hakan Saudat ta iso wurin tare da mahaifiyarta wad'anda sunci ado sai kyalli sukeyi tamkar wad'anda zasutafi wurin gasar nuna gwani a wurin Kwalliya ko wacce sai k'amshi take zubawa suna sanye da Alkybba wacce take nuni da jinin sarauta ne,
Kowa sai ido yake binsu dashi yana kallo cike da mamaki kamar wad'anda zasu tafi gidan biki,
musamman Saudat saikace ba mijinta bane kwance a kan gadon asibity tamkar gawa,

Wurin Hajjah da Sarki suka nufa mahaifiyar Saudat tamasu ya Mai jiki cike da nuna mulki da isa,

Ba itace a gabansu ba, Dan hakan basudamu da nuna mulkin da takeyiba Dan kuwa idan mulki take nema to a gaban,sarki take,

Bayan sun gaisa ne hajjah tayimata ya hanya,
Ta amsa tana mai daukar wayar hannunta wacce aka kirata da ita,

ta dan janye daga nesa da,wurin tana waya, bayan ta k'are wayar ne suka nemi wuri a can gefe d'aya suka zauna itada saudat da mahaifiyar tata gimbiya bilkusu taci gaba da sak'awa saudat magganu akan ciwon sauban, tana fad'in ai idan har sai ya auri shigiyar yarinyar nan gara ya mutu a hakan, KO kuma ya dawwama a cikin ciwonsa, me akeyi da kishiya wlh kishiya Annobace fitinace keni da babanki yayimun kushiya gara Allah ya k'arb'i rayuwarsa ya mutu kowa ya huta."

Saudat tayi saurin kallon mahaifiyarta tace "Kai mommy daddy kikeyiwa fatan mutuwa,
Nikam banason daddy ya mutu garadai ya k'aro auren ya maki kishiya goma da daddy na ya mutu."

"Rufemun baki gimbiya bilkisu tace a tsawace sakarai kawai wacce batasan ciwon kantaba, ni mahaifiyarki kikeyiwa fatan kishiya?
Ta mik'e tsaye tace "Zan tafi Allah yabawa mijinki lafiya,
Nasan ko badad'e ko bajima sai ya auri yarinyar da yakeso tinda inada labarin cewa tana nan da ranta bata mutuba tana cikin garin nan kingani nemanta baxai masa wahalaba, idan daddynki baiyimun kishiyaba ke mijinki zaiyimaki ya auri wacce yake so ya nuna mata soyayya sab'anin ke, dakece kike sonshi bashine yake sonki ba, duk lokacin da kika janye Addu'ar da kikayiwa mahaifinki na ya k'aromun kishiya kizo Zan taimakeki kamar yanda nasaba, kisani ke 'yatace d'aya tilo wacce nake tsananin ji da ita, amma kisani akan kishiya kowa Zan iya juyawa baya domin nakwaci 'yancina, akan kishi komai Zan iya aikatawa mutum idan yanemi yayi mun Addu'ar k'arin kishiya nabarki lafiya tayi tafiyarta tare da yiwa su hajjah da Sarki sallama wad'anda suke tsaye nesa dasu can a gefe d'aya cikin tashin hankali."

Tsaye Saudat tayi tana kallon mahaifiyarta tare da fadawanta har suka b'acewa ganinta, tana mamakin hali da rayuwa irin na mahaifiyar tata tafison kowa ya mutu akan ayi mata kishiya,
anan ta tuna lokacin tana gida kafin tayi aure wata rana mommy takira jakadiyarta tayi mata kyautar zannuwa masu kyau, sakamakon karb'o Mata wani aiki da tayi wurin bokanta kuma tayi amfani da magani taji dadinsa sosai shine tayiwa jakadiyar kyautar girma."

Sosai jakadiyar taji dad'in kyautar wacce batayi zatoba bare tsammani a wurin mommy,
Ai kuwa jakadiya ta kuma runsunawa gwaiwoyinta k'asa tashiga jerawa mommy Addu'oe duk wacce tazo bakinta furtawa mommy takeyi, mantawa tayi ta furta Allah ya tsareki da shairin kishiya, idan kuma ankawo maki ita ranki ya dade Allah yabaki ta kwarai wacce zaku had'a kanku."

Wata irin zabura mommy tayi ta tashi daga kishingid'en da take zuwa zaune tana kallon jakadiya cikin zafin rai da b'acin rai ta doka mata tsawa tace "jakadiya ni zakiyiwa fatan akawomun kishiya Wanda har zamu had'a kanmu?"
Menamaki a rayuwa daga Alheri zai zama sharri?"

Jikin jakadiya yasoma rawa, tana fad'in tuba nakeyi ranki ya dade sub'utar baki nayi."

Ai kuwa yau zakibar duniya domin banafatan na kuma ganin wnn fuskar taki,
Takira sarkin hukunci tace atafi da jakadiya a jefata d'akin azaba har sai tabar duniya."

Wnn hukuncin ya d'aurewa Saudat kai, Dan dai.a lokacin batada bakin da zatayi magana ne saboda mommy tana cikin fushi jikinta har rawa yakeyi."

Ta mere baki tace "nikam mommy banason Daddy ya mutu akan kishinki na banza,
hakan banason mijina sauban ya mutu, koda baya sona ni inason shi Allah yabashi lafiya."

Sautin k'ara bud'e k'ofar d'akin da sauban yake taji shine ya katse Mata tunanin da takeyi,

Likita sai faman share zufa yakeyi domin bak'aramar wahala yaciba Wurin ganin ya ceto rayuwar sauban daga duniyar mutuwa."
Hannu ya d'agawa Sarki akan sutafi office akwai maganar da zaiyi dashi."

Gaba d'ayansu Sarki tare da hajjah da Saudat suka nufi office din likita,
Inda suka sameshi akan kujerarsa yayi shuru yana nazari,
Dukansu suka nemi wuri suka zauna akan kujera."

Likita ya d'ago kansa ya kallesu cike da girmamawa yace "ranka ya dad'e,
Maganar d'ayace dai akan matsalar ciwon sauban kamar yanda nafad'a maka tun farko cewa zuciyarsa ta fara samun matsala tana gaf da mugawa ya rasa ransa idan ba'a bashi abinda yakeso ba,
To ko yanzun hakan ne idan har ba'ayi sauri aka nemo masa abinda yakeso ba,
Akoda yaushe a ko wanne lokaci sauban zai iya rasa rayuwarsa domin saura Kiris zuciyarsa ta buga, Wanda da Zarar ya kuma yin wani aman jinin to sai dai wani sauban d'in ba wannan ba."

Kuka Saudat ta fashe dashi,
Tasan mijinta soyayyar wata maccen ce take neman kashesa ba soyayyarta ba,
Duk da hakan tanason rayuwarsa akan mutuwarsa,
Ta durk'usa gaban sarki da hajjah tace Abba hajjah dan Allah kubawa sauban abinda yakeso kada murasashi wlh inason mijina."

Sarki ya mik'e tsaye yayiwa likita godiya ya fita hajjah ta sanya hannu ta rik'o Saudat suka fita daga ofice din likita tana lallashinta."

Waya Sarki yakeyi da shugaban yan jarida da kafafen yada labarai akan Suzo dukansu yana nemansu, yanzun nan su sameshi a gida a fadarsa."

Bayan ya kammala yin wayarne ya shiga d'akin sauban ya kuma dubashi har yanzun yana nan yanda yake dashida gawa basuda wani bambanci, sai da ya masa Addu'a snn yafito yana Mai tauyin d'an nasa halin da ya tsinci kansa a ciki."

Sallama yama hajjah akan zaitafi gida zaigana da shugabanin yan jarida insha Allahu cikin satin nan komai zai dai daita za'akawowa sauban farin cikinsa,in har hakan zai zama silar samun lafiyarsa."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*




*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )




*38*





******* "Subahanallahi abinda Alhaji Habib yace a lokacin da yaga safna ta zube k'asa a some, cikin hanzari ya
duk'a ya d'auketa yanufi ciki da ita hankalinsa a tashe ",

Umma tabi bayansa hankalinta itama a tashe tana fad'in "wnn yaro nema yakeyi ya janyo mana bala'i, da masifa
Na rantse da Allah idan narasa 'yata akanshi sai na d'auki fansar ranta a wurin ubanshi,
Domin nafi sonta akan duk abinda na mallaka a duniya."

Akan kujera Abba ya d'orata ya d'auko ruwa masu sanyin gaske ya zuba mata a jikinta zuwa fuskarta."

Wata irin Ajiyar zuciya ta sauke tare da bud'e idonta,
Hawaye suna mata kwarara a gefen fuska, ta idan ta kalli Abba ta kalli umma d'aya bayan d'aya tace "Dan Allah Abba da umma Ku taimakeni ku kaini wurin sauban, tunkafin ya mutu ya barni."

Shuru sukayi suna kallonta ba Wanda ya bata amsar maganarta."

Alhaji Habib kuma ya fad'a duniyar tunanin maganganun da Sarki yayi ta furtawa akan safna inda yake cewa _yanzun ace kamarni ina matsayin Sarki ace d'ana Wanda nafiso a duniya Wanda nake sa ran zai gajine shine zai auri shegiya marar asali sam bazai yiwoba_

Wato ashe 'yatace shegiya?
jinina Sarki yake dangantawa da shegiya marar asali,?
Tabbas sai sarki yayi nadamar furta wannan kalmar da yayi,
Sai ya tabbatar da duk in da d'an Adam yake yana da daraja,
sai ya tabbatar da shege da mai uba duka matsayinsu d'aya ne a wurin ubngiji dukansu ba abin wulak'antawa bane da kyamata.'

Saukowa safna tayi daga kan kujera ta rik'e k'afar Abba tana fad'in Abba kA taimakeni ka kaini wurin Sauban wlh Zan mutu idan sauban ya mutu nima zan bisa."

d'agota yayi ya mik'ar da ita tsaye yace "baxaki mutu ba, dota daina kuka yanzun Zan kaiki wurinsa,
Amma ki fad'amun gaskiya."

cikin sauri ta d'aga kai tace Zan fad'a Abba."

Murmushi yayi ya kalli umma wacce bakinta ya mutu ta kasayin Magana."

Ya jasu gaba d'aya suka zauna kan kujera,
Abba ya kalli safna yace "da gaske kinsan wannan sauban d'in ya nuna Mata jaridar dake hannunsa.mai d'auke da hoton sauban d'in da nata.'

Da sauri ta d'aga kai tana fad'in wlh "Abba nasanshi shine ya taimakeni ya tallafi rayuwata a lokacin da nake k'auye,
Abba sauban ya sadaukar da lafiyarsa da gaggar jikinsa a wurin shad'i a kaina,
Na tabbata sauban yana sona yana tausayina."

Ya isa Abba yace, sannan ya kalli umma yace "maman dota kitafi ki shiryata kema ki shirya kufito mutafi asibityn gaba d'ayanmu."

Umma batayi musuba ta rik'a hannun safna suka nufi d'akinta domin ta shirya 'yarta kun daisan umma gwanace a wurin ado da kwalliya."

sai da yaga shigewarsu d'aki sannan ya d'aga waya yakira sarki,
Ringing biyu Sarki ya d'aga, tare da kara wayar a kunnenta yana sallama."

Alhaji Habib ya amsa tare da cewa "d'azun Ina tafiya sai kuma naga wata jarida tana yawo a gari Mai d'auke da hoton sauban da yarinyar da yakeso Ana nemanta,
Meya janyo hakan?
KO ka karaya ka gano cewa marayu ma 'ya'ya ne, ba laifin yarinyar bane laifin mahaifanta ne da suka haifeta bata hanyar sunna ba."

Sarki ya furzar da iska Mai zafi a bakinsa yace "wlh bana k'aunar yarinyar nan saboda shigowarta masarautata dai dai yake da rugujewar duka tarin asalin masarautata,
Dolece tasakani na bada cigiyarta a gari domin a nemowa sauban ita gudun kada ya rasa rayuwarsa, saboda naga alama tabbas mutuwa zaiyi ya barni abin bana wasaba bane."


wani murmushin takaici Abba yasaki,
Yacewa sarki gani nan tafe yanzun asibityn tare da yarinyar da ake nema, bai bari yaji abinda Sarki zaiceba ya kashe wayar gaba d'aya."

Zaro ido Sarki yayi ya shiga kiran number Alhaji habib domin ya tabbatar da Abinda yace " da gaske yake fad'a,KO wasa yakeyi."
Wayar a kashe take.
Hajjah ya kalla Wanda itama shi take kallo cike da tuhuma,
Yace "Hajjah kinji kuwa abinda Alhaji Habib Naira yace?"

Hajjah tace "ya za'ayi naji tunda ba Aljana nakeba,
Amma idan kayimun bayani Zan sani."
Cike take dashi tare da jin haushinsa domin gani takeyi duk shine ya janyowa sauban wnn lalurar da bai kafe akan baya auren yarinyar ba, DA duk ba'a kai da hakan ba,
Shegiyar kafiya garesa irin ta ubansa."

Murmushi Sarki ya sauke yace "Allah ya baki hakuri hajjah,
Cewa yayi gashi nan tafe tare da yarinyar da ake nema,
Alhmdulillah sauban zai sami lafiya."

Mere baki hajjah tayi tace ai da kabarshi ya mutu kaga sai Ka zuba ruwa kasa kasha ka taya mak'iya yak'in neman ganin bayan rayuwar d'anka."
*****************

Sosai Hajiya Laila ta shirya Safna cikin wata dakakkiyar shadda ruwan Zuma,
Ta d'aura Mata d'an kwalli dai dai fuskarta Wanda ya Mata kyau sosai yafito da kyakkyawar fuskar tata,
Snn ta yafa mata gyale fari talkami fari jaka fara, ta kuma feshe Mata jikinta da turare.Mai sanyin dad'I.
Hmmm duk Wanda yaga safna saiyaji tamkar ya saceta ya gudu akan kyawo"

Hakan itama Hajiya falmata ta Shek'a adonta nafitar hankali suka fito suna zuba k'amshi duk wanda ya gansu ko bai tambayaba yasan uwa da 'yarta ne."

Murmushi Abba ya sauke cike da burgewa domin sunyi matuk'ar burgeshi,
Safna tana ganin Abba yana kallonsu yana murmushi itama tasakar masa murmushi tayi gaba tarigasu fita,
Wurin umma Yanufa yana d'auke da murmushi a fuskarsa ya janyota zuwa jikinsa ya shiga sinsinar duk inda hancinsa ya kai a jikinta, yana shak'ar k'amshin jikinta mai dadi,
yana fad'in nifa a kwanakin nan nakasa ganewa,
Sai wani haske kike kumayi kina wani Shek'i kodai na kuma yin wata ajiya a cikin nan ne
Tare da shafo cikin."

Murmushi umma tayi ta janyo mijinta a jikinta ta ta rungume, tana fad'ain Abban dota baka tsufa kada ka manta wurin ganin surikinka zamu tafi fa"

Janyewa yayi a jikin nata yana Sosar kai yana dariya yanufi hanyar fita umma tana biye dashi a baya suka fito,
A bakin mota suka tarar da Safna a tsaye tana jiran fitowarsu domin ta k'osa a tafi tayi ido biyu da sauban d'inta,
wurinta suka tunkara suna kallonta suna murmushi cike da burgewa, ba tun yau ba sunyi matuk'atar yabawa da hankalinta da natsuwarta tabbas Baba na k'auye yayi matuk'ar k'ok'ari wurin tarbiyantar da ita,
Dan hakan suke Addu'a Allah yasa bai mutuba, wad'anda ya tura wurin nemansa yana Addu'a Allah yasa azo masa da labarin yana raye bai mutuba yana cikin kwanciyar hankali, sunada buri akan baba nak'auye zasu sakashi farin ciki kamar yanda ya sakasu, Wurin tarbiyantar da yarsu mafi soyuwa a ransu."

Da sauri direba ya bud'e mota suka Shiga escort suna bayansu,
Sai da suka zauna a cikin motar snn direba ya rufe ya koma mazauninsa,

Da gudu escort suka nufi motocinsu suka shinshiga snn direba yaja suka fita daga gidan escort suna biye dasu a bayasuka nufi asibity."

Shigar motocinsu a asibityn ya tabbatarwa da jama'a cewar Alhaji Habib naira ne,
Ai kuwa jama'a sukayo tururuwa kansa domin neman taimako."

Ido safna ta zare domin ganin mutanen dake zagaye da motar da suke ba k'aramun firgita ta yayiba,
Tayi saurin rik'e umma jikinta yana rawa, domin duk a tunaninta wani laifin sukayi jama'a suka zagayesu za'a dakesu."

Rungume ta umma tayi tana tofa mata Addu'ar figita, DA tayi."
Alhaji Habib yana ganin hakan,
Yakira escort dinsa a waya yace "a janye masa mutanen da ke zagaye da motarsa dota firgita takeyi,
Snn a basu hakuri ba kud'i a tare dashi."

Hakan ta faru cikin minti goma escort rike da bindigoginsu suka tsawatar da jama'ar wurin,
Snn Alhaji Habib ya fito daga mota yana rik'e da hannun safna, umma tana d'aya gefen rik'e da hannunta d'aya suka sanyata a tsakiya suka nufi d'akinda aka kwantar da sauban."

Tin daga nesa Sarki ya hango abokin nasa tare da matarsa da wata kyakkyawan yarinya, wanda yasan baya rasa nasaba da 'yar abokin nasace wanda ya fad'a masa Albishir d'in ta bayyana anganeta,
Murmushi yakeyi yana kallon abokin nasa tare da lek'en bayansa da gefensa ko zai hango wata yarinyar a tare da dasu yar k'auye kamar yanda yaga hoton safna,
Baiga kowa a tare da Alhaji Habib ba sai escort nashi dake tare dashi kad'ai yagani."

K'arasowa yayi suka gaisa,
Tare da tambayar yaya mai jiki?"

Alhmdulillh yasami sauki za'ace. Dan kuwa saukinsa yana wurin Allah."

Gaisuwar da umma tamasa ta katse masa maganar da zai fad'a,
Yana murmushi ya amsa.
Hakan itama Safna ta gaidashi tana kallonsa domin sak fuskar sauban take gani a tare dashi,
Amsawa yayi yana Mai bayyana Fara'a a fuskarsa ya kalli Abba da umma yace "Masha Allah yarinya har ta girma hakan,.Kai Allah mungode maka da 'yarmu ta bayyana a garemu."
Wai ya akayi hakan ta faru?'

Dariya Abba yayi ya dafa kafad'arsa yace zakaji komai idan hankali ya kwanta mutafi naga d'ana."

Kallonsa Sarki yayi yace amma kace mun kana tare da yarinyar da sauban yake nema kuma ni yanzun ban ganta a tare da kuba."

Murmushi Abba yayi yace mushiga daga ciki naga jikin d'ana yanxun za'a taho da yarinyar."

Sarki baiyi maganaba suka nufi d'akin da sauban yake a kwance gaba d'ayansu.'

Tura k'ofar sukayi suka shiga da sallama,
Hajjah ce zaune a kan sallaya,
Saudat tana kan kujera a kusa da gadon sauban ta k'ureshi da ido cike da tausayin mijinta tana masa fifita duk da akwai fanka a d'akin ga kuma Ac."

Gaisawa sukayi da hajjah, sannan Saudat ta gaidasu,
ido biyu Saudat tayi da safna anan take taji gabanta ya fad'i, farat d'aya taji ta tsaneta, tanaji a jikinta akwai wani abu a tare da ita, musamman yanda taga ta tsare sauban da ido tana kallonsa idonta yana fitar da hawaye." Kallon Kayan dake sanye a jikinta tayi anan take ta raina kanta domin safna ta kereta ta ko Ina musamman idon akazo a fagen kyau."

Kasa hakura safna tayi ta ruga tanufi wurin gadon sauban Wanda yake jone da na'ura ta fad'a kan jikinsa ta fashe da kuka tana fad'in sauban kada ka mutu kabarni katashi ga safna a kusa da kai."

D'an birni ka tashi, idan ka mutu nima mutuwa zanyi nima bazan iya rayuwa idan babu kaiba."

Hannunsa ta rik'e sosai tana kuka tana kan jikinsa a kwance,

Gaba d'aya d'akin yayi tsit ita ake kallo Sarki da hajjah da Saudat sukayi mutuwar tsaye a kan mamaki."

A can cikin wata duniyar Wanda sauban ya tafi acan ya tsinkayo maganar safna tana magiya akan ya tashi kada ya mutu ya barta,
Sannu a hankali hankalinsa ya fara dawowa sautin kukanta kawai yakeji, sautin Kukan da har ya mutu bazai manta dashiba,
Hannunta dake cikin nasa ya Rik'e gam, sannan k'afarsa ta fara motsi,
Numfashinsa yashiga harbawa da sauri da sauri,
Still hannunsa yana Rik'e da nata yaki sakinta
Sannu a hankali ya bud'e idonsa Wanda yake zubar da hawayen wahala karaf idonsa ya sauka akan safna dake kwance a jikinsa tana kuka."

Runtse idonsa yayi hawaye sukaci gaba da tsiyaya a idonsa."

cike da farin ciki Sarki yafita yana kiran likita."

Hajjah kuma ta gumi tayi ta Rik'e baki tana kallonsu cike da farin ciki tana fad'i "TABBAS SOYAYYA GASKIYA CE😊❤






*Mrs Anas Bawa*✍
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*




*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )







*39*






Likita ya shigo tare da Sarki dake biye dashi a baya, yana fad'in likita ya farka ya bud'e idonsa rayuwar d'ana ta dawo."

Murmushi likita yayi a dai dai lokacin da ya isa gaban gadon sauban, wanda yake sanye da oxygen a hancinsa hannunsa Rik'e dana safna,
Sai k'ok'ari yakeyi ya cire oxygen din dake june a hancinsa saboda ba k'arfi a jikinsa ya kasa cirewa."

Likita ya matsa kusa dashi, yana murmushi
ganin sauban ya bud'e idonsa har kokarin cire abun janyo numfashin dake jone a hancinsa yakeyi,
Kallonsa yayi da kyau sukayi ido biyu da likita, likita ya sakar masa murmushi yana kallonsa yana kallon safna dake kan jikinsa a kwance tana kuka tana fad'in katashi sauban kada ka mutu ka barni."

Hannu likita yasaka Cire masa abin janyo numfashin daga hancinsa tare da kallon safna yana murmushi yace hajiya ki d'an d'aga daga kanshi zanyi masa allura."

Cikin hanzari safna ta tashi daga jikin sauban sai a lokacin ta lura da ya bud'e idonsa,
Wani irin murmushin farin ciki suka sakarwa junansu a tare a lokaci d'aya, suna kallon junansu cike daso da k'auna
Gaba d'aya sun manta da akwai mutane a d'akin."

Murmushin farin ciki sarki yakeyi ya matso wurin gadon sauban yana fad'in likita kadibashi da kyau rayuwarsa ta dawo Sauban ya farka.daga suman mutuwa da yayi, murmushi likita yayi a dai dai lokacin da yake zuk'o allura a sirinji ya juya ya kalli Sarki yace "ranka ya dade ai dama ba mutuwa yayiba,
Da ransa, illah Maganin lalurarsa ne tazo garesa."

Alhmdulillah Sarki yace ya juya ya kalli Alhaji Habib yace Abokina nayi mamakin ganinka tare da safna,
Da alama kaine ka taimaki safna ka bata kyakkyawan rayuwa hakan,
Halinka na taimako yana nan abokina Allah yasaka maka da Alheri."

Had'e fuska Alhaji Habib yayi yace "Ameen tunda Addu'a kayimun amma sai dai ina maiyi maka Albishir da cewa Safna 'yatace itace Suhailat 'yata wacce kasani ta b'ata a lokacin baya Allah yyi nagane 'yata cikin amincin Allah dan hakan Safna ba shegiya bace ba 'yar tsintuwa bace ba 'yar da aka tsinta a gefen hanya bace,
safna tana da gata tana,asali nine ubanta nine gatanta sai kuma mahaifiyarta dake kusa dani ya nuna Hajiya Laila."

Dam gaban sarki ya fad'i, anan take ya gano cewa maganace a dunkule Alhaji Habib ya Sakar masa,
Murmushu yasaki ya d'an sosa gemo yace "kai Alhmdulillah amma naji dad'i sosai Abu yazo cikin sauki,
Ya juya ya kalli hajjah yace mama kinga yanda Allah yake juye Al'amarinsa ko,
Ashe Safna yatace bansaniba.'

Murmushi hajjah tayi domin cike take da farin ciki ganin sauban ya farfad'o."

A can kan gado suka tsinkayo safna tana bawa sauban ruwan te a baki yana sha yana kallonta cike da mamakin sauyawarta sai wani abun yakeji yana fisgarsa a cikin zuciya."

Gaba,an manta da Saudat tana wurin domin hankalin kowa baya kanta,
Wacce take zaune a kan kujera zuciyarta tana ta farfasa, hawaye kawai ke mata zuba anan take ta fara ganin mutane biyu biyu,
Ta d'aga kai ta kalli sauban tare da safna akan Gado tana bashi ruwan te yana sha cike DA k'auna idonsu yana cikin na juna sun kasa d'auke ido daga kallon juna ji sukeyi kamar su cinye junansu,
Wani hayakin tashin hankali mai cike da kishi taji ya taso mata tayi saurin dafe Kai ta saki k'ara mai sauti ta zube a wurin a some."

Anan take hankalin kowa ya dawo kanta,
Sai a lokacin sauban ya Lura da ashe Tana wurin, tabbas yasan kishine yake damunta domin yasan zafin kishi irin na saudat,
Cikin gaggawa nurses suka shigo suka d'auketa daga k'asa suka fita da ita d'aya d'akin suka kwantar da ita tare da juna Mata ruwa."

Hankalin Safna bak'aramun tashi yayiba ganin fad'uwar da Saudat tayi jikinta ya soma rawa hawaye suka soma zuba a idonta,
Sauba jiyakeyi kamar ya kamota ya rungumeta ya lallasheta ya fad'amata ta kwantar da hankalinta amma ina badamar yin hakan illah ya runtse idonsa yanajin wani Abu yana masa yawo a zuciya."

Ganin firgicin da safna tayi yasa Hajiya Laila ta nufo wurinta ta mik'a mata hannu tazo Gareta,
Cikin sauri safna ta sauko daga kan gadon tazo wurin mahaifiyarta jikinta yana rawa,
Hajiya laila ta rungumeta tana shafar bayanta tare da lallashi, cike da kulawa irinta mahaifa, tajuya tayiwa Alhaji Habib magana akan cewa sutafi gida kawai hankalin dota a tashe yake."

Alhaji habib ya juya yayiwa Sarki sallama tareda hajjah tare da yimasa fatan samun lafiyar sauban."

Suka nufi hanyar fita,
Idon sauban a kan safna hakan itama safna idonta a kan sauban sun tsorawa juna ido cike da k'auna da rashin son rabuwa da juna,
hawaye Kawai suke zuba a idon safna,
Sam batason tayi nisa da sauban, musamman a yanda ta ganshi cikin mawuyacin hali Wanda yake neman taimakonta."

Da saurin sauban ya dafe saitin zuciyarsa ya mayar da ido ya rufe, yana sauke numfashi sama sama alamar ciwonsa zaidawo,
Cikin tashin hankali da zafin nama safna ta fisge hannunta daga rik'on da umma ta mata nufi wurin sauban ta dafa goshinsa tana fad'in "meyafaru sauban bud'e idonka gani kusa dakai
Ta matso da hannunta zuwa saiti zuciyarsa ta dafa zuciyar da hannunsa anan taji yanda take bugawa da sauri da sauri,
Zaro ido tayi hawaye suka wanke mata fuska tana fad'in nashiga uku sauban kada kamutu gani kusa gareka bazan barka ba."

Bud'e idonsa yayi sannu a hankali ya d'orasu a kanta, ya kamo hannunta ya saka cikin nashi ya Rik'e gam, ya cije baki tare da kuma lumshe ido shikad'ai yasan zugin da yakeji a zuciyarsa,
cikin muryarsa ta marasa lafiya yace "Safna kinaso na mutu?

Tayi saurin girgiza kai alamar A'a tare da share hawayen fuskarta."

Yace "muddun kikayi yi nisa dani Zan mutu,
Zuciyata da gaggan jikina suna son zama dake bansan daliliba, inaji a jikina kece farin cikina lokaci d'aya na tsinci kaina a cikin wnn halin, dan Allah Safna kada kitafi kibarni."

Cak mutanen dake cikin d'akin sukayi,
Anan take suka k'ame wuri d'aya suna kallonsu,
Iya tausayi sun basu tausayi musamman sauban Wanda Sarki da hajjah sukeda yak'inin da zarar safna ta tafi ciwonsa zai dawo, sunga alamar hakan tun kafin tabar d'akin."

hakan Alhaji Habib sunyi matukar burgeshi dabashi tausayi musamman sauban Wanda ya fahimci yana matukar son tilon 'yarsa, amma kalaman sarki mahaifinsa har yanzun suna k'ona masa zuciya Wanda yakeji bazai iya kyaleshiba har sai ya gane kuskurensa."

Dogon numfashi yaja ya kalli inda safna take a kusa da sauban hannunsu Rik'e Dana juna cikin k'arfin hali yace "dota ke muke jira, zamu tafi kitaso mutafi gida."

Cikin sauri sarki ya kallesa cike da mamakin abokin nasa,
Kamar baiji furucin sauban a kan yarsa da yayi a yanzunba na cewar baya iya rayuwa idan ba da itaba, to meyake nufi da ta taso sutafi, yana nufin baya tausayin d'an nasa ne, ko Kuwa?"

Sarki ya matso kusa da Alhaji Habib ya dafa

Please Login or Register in order to submit comment