Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan faffad'an kirkinsa mai cike da yalwan gashi wanda yayi kwance gwanin ban sha'awa a kirjinsa,
ringumeta yayi yana bubbugar bayanta alamar tayi shuru ta daina kuka,
Sannu a hankali ta fara samun natsuwa ta nemi hawayen dake zuba a idonta ta rasa,
Cikin wani salo ya kara bakinsa a kunneta yashiga rad'a Mata, "kiyi hakuri Saudat ba abinda kikayimun iya zamana dake bare nafad'a maki ki gyara,
A tsarin rayuwata bana da ra'ayin ajiye Mata sama da d'aya domin tara yawan mata baya d'aya daga cikin tsarina,
Nima Ina mamakin wnn auren da zanyi Wanda ni Karan kaina na. Amince dashi nake kuma jin yarinyar da Zan aura har cikin raina,
Kiyi hakuri ki 'dauki kaddara auran nan,
Kicire damuwa a ranki, insha Allahu Zan kwatantamaku adalci, ki daina cewa bana sonki, Saudat Ina sonki da bana sonki da baxan zauna dake a matsayin matar aurena ba."
Na rok'eki da ki sassautawa rayuwarki wannan zazzafan kishin dake damunki,
Yana kawai nan ya tura bakinsa a cikin bakinta yashiga aika mata da sak'onninsa Dan kawai ya sanyaya Mata rai."

Ai kuwa yayi nasara sosai wurin farantamata domin taji ranta yayi Mata sanyi sosai yau sauban ne da bakinsa yake furta Mata kalmar yana sonta,Har yake aika Mata da salonsa mai rikitarwa."
Kamar koda yaushe a yanda yasaba jinta hakan yauma yajita salam duk tasaki babu abinda yake fita a gabanta sai wani farin ruwa Mai kauri da yauk'i,
Hakan yagaji Dan kansa ya sauka akanta badan yasami kamsuwaba koyaji wani dadi a tare da ita, idan dasabo ai yasaba dajin Saudat a hakan."
Toilet yashiga yayi wanka yafito ya dauki jallabiyarsa yasaka sannan yanufi wurin dining domin ya zuba abinci yaci."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*


BY
UMMU SAFWAN
(FAREEDA BASHEER)




45



Hakan Saudat tayita lallashin zuciyarta tare da danne kishinta, babu abinda yafi d'aga Mata hankali duk takira wayar mahaifiyarta wacce take kwantar Mata da hankali ta kuma yimata Alkawarin idan har tana raye sauban baxaiyi aureba,
akashe ake cewa wayar take,
Wayar mahaifinta kawai take samu,
Idan ya dauka suka gaisa idan ta tambayeshi mahaifiyarta zaice lafiya kalau take takira wayarta mana."

Idan tace takira a kashe takejinta zaice network ne taci gaba da nema zata samu hakan zasuyi sallama ya kashe wayarsa."

Mahaifiyar saudat kuma gimbiya Bilkisu tana can itama cikin tashin hankalin fitinar kishi gobe za'a kawo mata kushiya,
Ba Saudat ce a gabantaba ita keyiwa kanta yaki wnn karon,
Tayi kuka tayi birgima tayi tashin hankali Wanda har yayi sanadiyar kwanciyar bayinta biyu a asibity akan wani mugun duka da tayi masu akan tana cikin zafin kishi, suka bata hakuri"

Macce d'aya ce zata iya kwantar Mata da hankali tare da bata shawarwari itace Hajiya laila, gashi kuma yarta zata aurawa mijin Saudat dan hakan ta dauki tsanar duniya ta Dora mata,
Tarasa dubara bare mafita taga alamar ba fashi Sarki Abdulrahaman ya kafe gobe sai an d'aura masa aure da Amaryarsa,
Ga iyayen yarinyar manyan mutane ne masu kudi da haiba bata isa tasamesu DA rashin mutumciba ko wata barazana tata,
A daren ranar ta yanke jiki ta fad'i a cewarta idan tafadi ta daina motsi ai dole a fasa daura auren a gobe wata kilama yace ya fasa ganin zata rasa ranta."

Sosai Sarki Abdulrahaman hankalinsa ya tashi ganin faduwar da tayi,
Ya dauketa kamar matanciya yanufi d'akinta da ita ya kwantar da ita akan gadonta tare da yimata fifita,
KO alamar motsi babu a tare da ita tamkar gawa hakan ta koma,
Wanda a zahirance duk abunda yakeyi tanajinsa, wayarsa ce tayi kara ya Ciro a aljihunsa ya Kara a kunne,
Saiji tayi yana fad'in "eh karfe biyu ne daurin auren da andaura za'a tahomun da Amaryata tare da shekewa da dariya."

Zubbur tayi ta mik'e zaune tana rikeshi tana fadin kada kayi auren nan dan Allah ka rufamun asiri mutuwa zanyi,
Kallon mamaki kawai yabita dashi tare da jijjina bak'in kishi irin Nata,
Hannunta ya buge daga rukon da tamasa yana fadin aure ba fashi idan kinga bakya iya zama k'ofa a bud'e take kina iya tafiya kibarmun gidana,
Zaro ido tayi cike da mamaki tana kallonsa har yafice daga d'akin."

Washe gari tanaji tana gani aka shigo da Amarya gidan,
sai dai ta shege daki ta rufe kanta tadinga kuka tana birgima tana ihu kamar ranta zai fita takeji."
_Allah ka rabamu da wannan zafin kishin_

*********************

Kwanaki tafiya sukeyi inda yarage saura sati biyu auren sauban da safna,
Inda Hajiya laila taketa faman gyara 'yarta ciki da waje,
Safna tasha kayan mata har sunyi Mata over tunda aka sanya ranar auren Hajiya laila take tsuma yarta,
Har yakai KO fitsari zatayi sai wasu ruwan sha'awa sunbiyu daga baya,
Hakan fatarta tayi kyau tayi laushi da fari da santsi sai wani sheki takeyi,
Duk wani abu Wanda ya danganci zaman aure Hajiya laila ta karantar da safna tare da hakuri da juriya a gidan miji tare da tattalinsa da nuna masa k'auna,
Hakan ta koyamata duk wani nau'i na abinci Wanda tasan za'ayi alfahari da ita."

Kwatakwata ta hana ta dauki wayar sauban idan yakira,
Saidai Hajiya laila ce zata dauka tace masa bata nan, tana gidan k'anwarta,
Sosai sauban yashiga damuwa wacce har ya kai yaxo gidan da kansa amma aka hanashi ganinta saida aka kuma bashi hakuri cewar bata nan baxatadawo ba sai ana gobe za'a kaita gidansa."
Hakan ya hakura ya dawo gida cike da jimami da damuwa a tattare dashi."

*********************

Akwana atashi ba wuya gashi yau saura kwana uku d'aurin auren sauban da safna,
Inda tsakanin gidajen nan biyu gidan Sarki da gidansu safna ya soma cika da bak'i yan nesa sunfara karasowa."

Zaune suke a d'akin Hajiya laila su biyu safna da mamanta Hajiya laila sai nasiha take mata wacce a kullum itace a bakinta, akan zamantakewar aure musamman tsafta da biyayya,
Sannan tazamo mai tsaftar KO wanne b'angare na jikinta ciki da waje,
Daga nan tashiga nuna mata yanda zatayi amfani da turarunka da tasanya aka kawo mata daga Maiduguri, tundaga na tsugunne har zuwa na turarawa a jiki zuwa cikin d'aki."

Suna hakan Alhaji Habib ya turo k'ofa yashigo fuskarsa cike da farin ciki, yana fad'in ina safna Albishirinki."

Cike da farin ciki take kallon mahaifin nata tana fad'in goro fari Abba."

Yace "nazo maki da Albishir mai dadi yau angane babanki na k'auye ashe bai mutuba yanzun hakan yana cikin falona a zaune."

Wani irin k'arar farin ciki tasaki ta doka tsalle tanufi falon da gudu,
Turus taja ta tsaya tana kallon baba cike da farin ciki, inda shima ita yake kallo yana dariyar farinciki yana fad'in taho 'yata Allah yayi zamu gana, ashe baki mutuba,

Kuka tasaki da ta tuna da rabuwar da sukayi tanufeshi ta fad'a kan jikinsa tana fadin ban mutuba baba Ashe kaima baka mutuba"

Share mata hawaye yayi yana fad'in ban mutuba yata safna Allah ya tsiratar dani a lokacin da nafad'i ban kuma sanin inda kaina yake ba saidai na farka na ganni cikin wata bukka wata Mata bafulatana tanayimun fifita."

Tambyarta nashigayi ko nan a Ina nake?
tare da fad'in sunanki Ina kiran safna Allah ya kubutar dake daga sharrin azzalumai,
Dafa kafad'ata tayi a nan take naji komai ya shafemun akai nan naci gaba da zama tare da wnn matar har na sami lafiya,
Ganin nasami lafiya ban kumayi yunkurin zuwa garinmu ba kasancewar nayi nisa da garin sosai ina cikin birnin Adamawa,
Wnn matar ita tabani wurin zama a cikin bukkanta dake gefen titi ita kebani abinci, daga k'arshe tabani jari, na fara zuwa ina sayo man fetur ina ajiyewa a gefen titi a gefen bukkata, cikin ikon Allah nasami karbuwa a wurin nashiga ciniki, har sunana ya koma Baba Mai fetur tun daga lokacin ban kuma ganin wnn matarba ban k'ara tunanin na koma gidaba,
Ana hakan ya nuna d'aya daga cikin direban Alhaji habib Wanda ya tura ya nemo shi, suna zaune gefe d'aya harda Hajiya falmata da Alhaji Habib suna saurarenshi cike da tausayi,
Ana hkn wnn yazo ya tsaya da motarsa wurina domin yasha Mai anan yake tambayata ko nasan malam Iro Wanda yake zaune a cikin k'auyen lassa andora makuddan kudi gaduk Wanda ya gansa za'a bashi dubu d'ari biyar,

A nan take gabana ya fad'i domin nasan nine iron da ake nema,
Nace yaro meyafaru ake neman malam iro, snn suwa ke nemansa?"

Wnn bawan Allah yace "mahaifin yarinyar da ya Rik'a a hannunsa Mai suna safna shine yake nemansa domin ya gode masa,
Anan na d'ora hannu akai Ina fad'in Alhmdulillah Ashe safna bata mutuba, na rik'a hannunshi ina fad'in mutafi yaro ka kaini nagano 'yata safna ashe bata mutuba, nine malam Iron da ake nema."

Hakan nabiyushi muka taho har cikin gidan nan Ina d'aukin naganki 'yata Ashe baki mutuba,
Alhmdulillah Allah Allah ya cikamun burina safna tagane mahaifanta tana cikin farin ciki Wanda akoda yaushe nake maki fatan kasancewa a cikinsa,

Safna mahaifinki ya fad'amun yau saura kwana uku d'aurin aurenki da sauban yaron kirki wanda ya sadaukar da rayuwarsa akanki,
Kai Alhmdulillah naji dad'i sosai 'yata Allah yayi maki Albarka yabaku zuri'a mai Albarka."

Gaba d'aya falon aka amsa da Ameen."

Hakan aka cikawa baba gaba da kayan ciye ciye yinin ranar safna a wurinsa ta yini suna labarin abinda ya wuce,
Da yamma tayi baba yace shi zai koma wurin sana'arsa, Alhaji Habib yace "ina ai ba inda zaitafi zasu zauna a tare yanda yasakasu cikin farin ciki na rike masu ya da yayi shima sai sunsaka mashi da farin ciki Wanda zaiyi Alfahari dasu,
Hakan aka gyarawa baba d'akin saukar bak'i aka zuba mashi duk wani abin bukata,
Cikin kwana biyu baba ya murmure yayi kyau sai sutura yake sakawa ta Alfarma,
Ranar kwana na uku ranar ake d'aurin auren safna, da sauban
Inda Alhaji Habib ya d'unka masu kaya iri d'aya da baba,
Misalin k'arfe biyu da rabi dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren safna da sauban akan sadaki naira dubu d'ari Wanda Baba shine ya d'aura auren safna abinda ya dade yana jira kenan."

Sauban da Abokinsa safwan kaya iri d'aya suka saka duk wanda yaga bakin sauban yasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa, sai hotuna kawai akeyi gwanin ban sha'awa."




_bansan da bakinda zan baku hakuriba my friends hakika kunayimun uzuri sosai, kukara hakuri dani tare da yimun Addu'a Allah yabani juriyar yimaku typing dan wlh da zarar na dauki waya da sunan Zan fara rubutu a lokacin nakejin wani bacci mai dad'i yana d'aukeni a hakan Zan ajiye wayar nayi baccin😂 wnn shine dalilin jina shuru da kukayi, amma zanyi yaki da bacci har nasamu na kammala maku wnn labari duk da dai ya kusan zuwa karshe ngd_






[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*



BY
UMMU SAFWAN
(FAREEDA BASHEER)




*46*






Bayan angama shagalin biki, Wanda daga yinin biki sai walima kad'ai akayi,
Har zuwa lokacin sauban bai sanya safna a idonsaba,
Hakan dai hakura ya danne zuciyarsa domin yasan duk b'oyon da ake Mata yau gidansa zata kwana."

********************

Da Misalin k'arfe hud'u gidan sarauta aka turo da manyan motoci tare da fadawa domin d'aukar Amarya,
Macce d'aya aka taho da itace itace Anna dattijiwar kirki,
Anna tana Shiga gidan ta gabatar masu da kanta tare da sak'on maSarauta ta mik'awa mommy kyakkyawar Alkyabba,
wacce za'a sakawa safna domin tafiya da ita gidan mijin,
wnn sak'on maimartaba ne."

Sosai aka shirya safna cikin shiga ta Alfarma aka sanya mata Alkyabbar sai k'amshi kawai take zubawa."

Hajiya Laila tashiga gyara safna ta shiryata ta d'auko wasu ruwan a cikin kofi ta bata ta shanye, snn takira 'yan uwanta tare da dangin mahaifinta suka shiga yimata nasihar zaman lafiya tare da biyayya da tsafta da duk wani abu Wanda ya k'unshi zaman takewar aure."

Bayan sun gama yimata nasihar ne suka rakota zuwa wurin mahaifinta Wanda yake zaune a falonsa tare da Baba, Alhaji Habib nasiha ya shiga y mata yana fad'amata tayi kuyi da halin mahaifiyarta domin duk iya zaman da sukayi ba'a tab'ajin kansuba,
bayan ya gama baba shima ya d'ora tashi sosai yake lurar da ita hakuri da juriya, dama yasan ita Mai hakuri ce."
Kuka safna takeyi sosai baba yana bata hakuri yana fad'in ta daina kuka hakan aka kama safna aka nufi wurin motocin da sukazo d'aukarta,

Wurin kyakkyawar motar da aka tanadar mata wacce take lullub'e da tambarin masarauta wacce akayi mata ado da balan balan,
Ita kad'ai aka saka a cikin motar snn Anna tabi bayanta ta zauna a kusa da ita,
sauran yan uwa da abokanan arziki suka shiga sauran motocin wasu duk motarsu sukayi amfani da ita, aka d'auki hanyar masarauta tare da sakin jiniya"

Kwance yake a d'akinsa yana juyi cike da farin ciki wani fanni na zuciyarsa yana mamakin kansa yau shine yake da mata biyu a gida d'aya,
Tausayin Saudat ya bijiro masa a rai,
Ya dafe kansa yana tunanin tun jiya da ta rufe kanta a d'aki bata bud'eba,
Yayi dukan k'ofar taki ta bud'e sai sautin kukanta kawai yakeji yana tashi sai faman jifa da kaya takeyi suna fashewa",
Sauke numfashi yayi yana fad'in Saudat Allah ya sassauta maki wnn zafin kishi naki, Yabani ikon yimaku Adalci a tsakaninku,
Sautin jiniyar daya karad'e gidan sarautar yabashi damar sheda cewa safna ta iso gareshi,
murmushi yasaki mai k'ayatarwa tare da lumshe ido yana mai cike da farin ciki."

Safwan abokin ango shi yake kaida komo yana gudanar da komai tunda ya lura yau Angon halinshi yakeji na miskilanci har wani shegewa d'aki yakeyi ya kwanta."

Safwan tare da yan uwan sarki sune suka tarbi bak'i,
Inda Kai tsaye wurin hajjah aka nufa da Safna,
Sosai hajjah take farin ciki da ganin wnn rana tayi masu Addu'ar zama lafiya, duka d'akin suke amsawa da Ameen, snn tabada umurni a tafi da ita d'akinta."

A B'angaren sauban part d'in zaman macce hud'u ne bayan sashen sauban hakan sarki ya gina masa domin yana da burin sauban ya ajiye macce hud'u,
, d'aya daga cikin part d'in dake kusa da sashen yarima Wanda yake kallon part d'in Saudat anan akayiwa safna jeren kayanta,
Wanda tsayawa tsara kyan d'akin da yawan kayan da aka zuba cikinsa b'ata lokaci ne,
Domin kusan auren 'yar gata komai yimata akeyi don nuna gatanci a gareta,

Da k'afar dama tashiga tare da neman tsari ga dukkan wata halitta mai cutarwa,
Danginta suna tare da ita suna tarairayarta,
Kai tsaye d'akinta aka nufa da ita akayi mata masauki a gefen gadonta na Alfarma,
Sannan akaci gaba da karantar da ita hakuri da juriya a gidan miji."

ana kiran sallar magariba sukayi mata sallama domin tafiya,
Kuka Safna ta fashe dashi, kuka gwanin ban tausayi tana fad'in kada kutafi kubarni ni kad'ai kubari sai gobe,
Hakuri suka bata tare da lallashinta da lurar da ita cewa a gari d'aya suke, snn tafiyarsu bashine yake nuni da sun rabu har Abada ba, tasani ita yar dangice suna tare da ita a koda yaushe,. idan aka kwana biyu zasu dawo domin duba lafiyarta,
, tayi hakuri ta sanya juriya a hakan kowa ya saba zama a gidan mijinsa."
Daga k'arshe sukayi mata sallama inda sauban ya turo masu da manyan atamfofi da shadda tare turarunka masu k'amshi yace abawa duk wacce taxo shadda kuma abawa maxa,
Hakan shima Sarki ya cikasu da Alheri mai girma itama Hajjah ba'a barta a bayaba,
Suna farin ciki suka bar gidan tare da yimasu fatan Alheri a rayuwar Aurensu."

Safna zaune ita kad'ai a d'akinta,
mik'ewa tsaye tayi tana kallon ko ina a d'akin ba k'arya Abbanta ya zuba mata dukiya,
Acan gefe d'aya ta hango wani d'akin da alama toilet ne,
Tanufi wurin tare da bud'e k'ofar ta shiga,
Aikuwa toilet d'in ne amma wnn toilet d'in yasha banban da Wanda take gani domin tsaruwar wnn abin ba'a magana,
Kai tsaye wurin famfo tanufa ta kunna saiga ruwa sunfito ta sauke ajiyar zuciya tare da sakin murmushi snn ta somayin arwala domin yin sallar magariba gashi har anfara kiran isha'i."

Bayan tagama Arwalar ne tafito ta shinfid'a sallaya wacce tagani ajiye a wuri d'aya tare carbi da Al'qur'ani Mai girma, bayan ta shinfad'a ne ta hau kai tafara gabatar da sallar magariba tare da isha'i."

A d'akin Sauban kuma bayan fito daga wanka yana shafa mai fuskarsa cike da Annuri da farin ciki,
Safwan Ne tsaye Akansa sai shakinyanci yake masa yana fad'in "Ango kasha mai KO nace zakasha mai, Angon Saudat da Safna,
Abokina kayi zari da yawafa mata biyu duk kai d'aya.
Amma kafi kowa cewa mutum jarabbe, tamu jarabar ce tafito fili,a zahirance Kai ka kafi kowa jaraba, kullum kaine cikin shan ruwan Lipton da lemun tsami Dan tsabagen jaraba Anya kuwa Kai ba hariji bane, yakai karshen maganar yana sakin dariya."

Banza dashi sauban yayi ya kuma had'e fuska yaci gaba da shirinsa,

Safwan yaci gaba da cewa "yau dai gaka ga safna, saiku cinye junanku akan soyayya, ta kwanciya a asibity ta k'are
Amma ina rok'unka daka sassautawa yarinyar mutane kada ka sauke mata jarabarka gaba d'aya Dan sabon shigace idan kuma kayi dibo da yarinyace k'arama bata sababa."

Wata irin harara sauban ya wurguwa Safwan tare da nuna masa hanyar fita yana fad'in wuce katafi saida safe."

Dariya Safwan yasaki yace "tun yanzun har kafara korata lallai da alama a buk'ace kake, baxaka bari KO sayen baki nayiba.'

Zaro ido sauban yayi yana kallonsa yace "bakinwa zaka saya?"
Safwan kafita nace katafi gidanka nagode,
Kajecan kayi jarabarka ni ba irinka bane,
Dan bansan abinda ke tattare a jikin mace ba bare har na lik'e mata yanda naga kanayi yakai karshen maganar tare da mere baki,
Ya kuma nunawa safwan hanya yace fita nace."

Safwan zai kuma magana sauban ya rarumo filo zai jefa masa da gudu Safwan yaja baya yana dariya yanufi k'ofar fita yana fad'in asha dad'i lafiya, nima da banada matar yau danasha haushi, saida safe abokina ga kazar nan akan dining domin itace gudun mawata domin raya sunnah, tareda janyo masa k'ofa ya fita yana Dariya."

*******************

Tana kan sallaya a zaune tanajan jarbi,
Taji anturo k'ofa anshigo tare da sallama,
Amsa sallamar tayi tare da d'aga kai tana kallonsu,
Kuyangine su goma a jere suka zube a gabanta suna fad'in "ranki ya dad'e barka da zuwa wnn gida mai tarin Albarka ya uwargijiyarmu mune wad'anda zamu dinga yimaki hidima duk abinda kikeso muzamuyi maki,
Snn suka shiga gabatar da kansu tare da aikin da KO wacce zata dinga yimata."

Kallonsu safna takeyi cike da mamaki musamman dataji uku daga cikinsu suna fad'in mune zamudinga yimaki wanka da kwalliya wato hatta wanka yimata za'ayi tab lallai akwai aiki babba domin babu wacce zata bari tayi mata wanka da ranta da lafiyarta."

Murmushi tasakar masu tace "nagode 'yan uwana kutashi daga tsunne ku zauna dani daku duka d'aya,

Godiya yimata tare da yaba kirkinta alamu sun nuna ba halinsu d'aya da gimbiya Saudat ba wnn tafi Saudat kirki."

Sauran Fita sukayi sunayi mata godiya akabar saura mutum uku a cikin d'akin,
Kallonsu tayi tana mmkin tsayuwarsu, kafin tayi magana d'aya tawuce toilet d'inta ta had'a mata ruwan wanka masu kamshin gaske d'aya kuma tabud'e wadrup taciro mata kayan bacci masu fitinar kyau tare da wata Alkyabbar mai kyan gaske d'aya kuma tana tsaye a kusa da ita tana fad'in ranki ya dad'e komai ya kammala zamu shiryaki mutafi dake d'akin yarima,"

dukansu suka rik'ata suka d'orata akan gado tare da kaiwa k'asa a gabanta suna fadin "ya uwargijiyarmu kibamu dama zamuyi maki wanka."

"Girgiza kai tayi tace "kuyi hakuri baxan tab'a Bari. kuyimun wankaba, Zan dai shiga nayi dakaina nafito."

Shuru sukayi domin babu jayayya a tsakaninsu
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*



BY
UMMU SAFWAN
(FAREEDA BASHEER)




*47*





Mikewa tayi ta kallesu cike dajin kunya tace "zancire Kayana."

Sunkuyar dakai k'asa sukayi snn sukatashi suka fita zuwa falo domin sujirata tafito snn su shiryata."

Sunafita ta cire kayanta ta d'aura wani towel mai girma Wanda tagani ajiye a gefen gado da alama yanzun suka ajiye mata shi,
Cire kayan jikinta tayi ta dauki towel din ta d'aura ba laifi babba ne domin har ya wuce gwaiwar kafarta snn ta rufe jikinta da wani k'aramin ta nufi toilet domin tayi wanka."

Wanka takeyi da ruwa masu k'amshin gaske tana tunanin rayuwar da zatayi a cikin gidan nan, shin wai ina sauban yake rabonda da ta sanyashi a ado har ta manta,
wata kila ya manta da ita wnn dalilin yasa akeso akaita d'akinshi a maimakon shi yazo."

To waima Ina Saudat matar shi?"
Mere baki tayi taja dogon tsaki domin Saudat bata gabanta musamman idan ta tuna da fad'an da mahaifiyarta tamata, akan kada ta d'auka cewa tana da kushiya bare kishinta yayi tasiri a ranta Wanda zai janyo Mata rauni wurin kula da mijinta, snn kada ta d'auki abokiyar zamanta a matsayin kishiya ta d'auketa a matsayin abokiyar zama duka d'aya suke a wurin mijinsu."

Hakan ta kammala wankan tafito jiki ba kwari,
Tana fituwa ta tarar da ankuma gyara d'akin anlunke kayan da ta cire an adanasu,
Suna ganin fitowarta suka tarota suka nufi wurin kwalliya da ita suka zagayeta sukashiga gyarata."

Sosai suka tsantsara mata kwalliya wacce ta kuma fitar da Annurin fuskarta tare da tsantsar kyanta Mai Jan hankali na asalin bafulatana."

Wata rigar bacci suka bata ta sanya wacce sai da taji kunyar kanta a lokacin da tasaka rigar ta kalli madubi domin komai najikinta a bayyane yake a cikin rigar,
Har zata cire rigar ta tuna da hud'ubar mahaifiyarta ta mata, akan mahimmanci saka kayan bacci musamman idan zaka kwanta gado d'aya da miji, rufe fuskarta tayi cike dajin kunya, tabar rigar a jikinta,
Tayi saurin d'auko Alkyabba ta d'ora akai tin kafin kuyangi sushigo susameta a hakan,
Bayan ta kammala saka kayanne suka shigo,
Suka fesheta da turare snn suka zube a gabanta suna zuba mata kirari,
Murmushi kawai takeyi cike da jin kunya,
Sukace ya uwar gijiyarmu yanzun zamu rakaki d'akin yarima a can zaki kwana."

Shuru tayi kamar tace bata zuwa shi meyasa baxaizo ya sameta a d'akintaba ko duk sarautar ce,
mere baki tayi ta mik'e tsaye suka dafa mata suna zuba mata kirari suka nufi b'an garen yarima Sauban da ita."

Da Sallama suka shiga d'akin sannu a hankali suke kutsa kai cikin d'akin wani k'amshi mai cike da Sanyin dad'i sai dukan hancinsu yakeyi,
har suka isa bidrom nashi ba wani motsinshi bare alamarshi,
Alama ta nuna yanzun yafita domin k'amshin turarensa ya nuna hakan."

A gefen gadonsa suka zaunar da safna wacce ta sunkuyar da kai ta rufe fuskarta da Alkyabba, tashiga tunanin zuci to wai Ina Sauban ya shigane?
Wnn alamun kad'ai ya isa yanuna mata baya sonta tausayinta yakeji kamar yanda yake fad'a."

sautin muryar kuyanginta suka katse mata tunanin da takeyi a lokacin da suka kai durkushe a gefen k'afarta suna fad'in "ranki ya dad'e a gafarce yarima yana zuwa yanzun."
Suka fara bata labari domin ya d'ebe mata kewa kafin yarima yashigo."

Sauban kuma bayan ya kammala shirinsa cikin dakakkiyar shadda ruwan madara domin tarbon Amaryarsa sai k'amshi yake zubawa zuciyarsa fes cike da farin ciki,
wani b'angare d'aya na zuciyarsa yana mai tsananin tausayin Saudat kwana biyu kenan bai sanyata a idoba, tana d'aki ta rufe kanta baci basha,
ya salam ya furta tare da dafe kansa, ya fuszar da iska Mai zafi a bakinsa yana fad'in wnn yarinya kada ta kashe kanta,

Cikin sauri ya mik'e tsaye ya d'auko extra key d'in d'akinta yafita da sauri yanufi d'akin Saudat,
Key din ya zura a kofar ya murd'a anan take k'ofar ta bud'e yasanya kafa ya shiga,
Gabansa ya yanke ya fad'i a lokacin da yayi Karo da b'arnar da tayi gaba d'aya d'akin kacaca ko ina anzubar da kaya,
Duk ta farfasa tv tare da kwalaben turare,
dube dube yashigayi ta Ina zai ganta,
A can k'asa ya hangota zaune a gefen gado kanta ba d'ankwali da turje gashin kanta tamkar mahaukaci duk ta rame tayi bak'i,
Cike da tausayi ya nufeta, tana ganinsa ta taso da gudu ta fad'a kan jikinsa tafashe da kuka Mai sauti,
Tana fad'in kaji tausayina sadauki inasonka kada ka had'ani da wata kai nawa ne nikad'ai, ta kuma fashewa da Kuka, rungumeta yayi a jikinsa ya zauna tare da ita a kan gado yana share mata hawayen fuskarta cike da tausayinta yake fad'in "waye ya fad'a maki ni banaki bane, Saudat ni mijinki ne ke Matata ce inasonki kidaina tunanin komai a ranki, ki d'auki kaddarar da tafad'a kanmu domin auren danayi baya nufin na wulak'anta,
ki sassautawa rayuwarki wnn zafin kishin diba kigani yanda kika koma."

Kinci abinci kuwa?
Ta girgiza Kai alamar A'a."
Meyasa kika rufe kanki yau kwana biyu kenan duk kinsanya hankalina ya tashi,
Murmushi tasaki domin ko bakomai sauban ya fara sonta,
Cikin muryar

Please Login or Register in order to submit comment