Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a Masa cewar gimbiya tana buk'atar ganinsa yau da misalin k'arfe 8 na dare."

Likita bai kawo komai a ransa ba,
domin yaga yanda sarkin gida yake zirga zirga a asibityn sannan ya lura da yanda aka yarda dashi

Ganin anyarda dashi d'ari bisa d'ari yasa baiyi tinanin komaiba ya amsa Masa da to idan yatashi daga asibity idan zai koma gida Yana Nan tafe,
Yashiga tinanin wata k'ila akan maganar ciwon Sauban ne take nemansa."

Misalin k'arfe 8 sarkin gida ya tsaya a can bayan asibity inda ba Wanda zai iya ganinsa yakira likita a waya, cikin minti 5 likita yafito daga asibity dama lokacin tashinsa yayi, ya tarar da sarkin gida ya d'aukeshi a mota ya nufi wurin gimbiya Jamila dashi."

Hak'ik'a Jamila tayi farin cikin ganin likita a gabanta zaune sai murmushi take saki a fuskarta,
Ta kalli likita da kyau tace "barka da zuwa doctor."

"Yawwa hajiya barka da gida Yaya iyali?" inji likita."

Bata amsa Masa ba tace "Yaya jikin Sauban d'in ?"
ta kuma jeho Masa wata tambyar."

"Alhamdulillah sauki yanata shigosa sai dai har yanzun lakkan jikinsa Bata Fara aiki ba domin. Abinda akayi amfani dashi, Yana da k'arfi sosai domin yafi guba masifa a jikin d'an adam Wanda har yanzun mun rasa Gane ko meye."

Murmushi ta saki ta girgiza Kai, tace "likita katab'a rik'a miliyan 20 a matsayin naka na kanka?"

Wata irin zabura tare da Zaro ido sarkin gida yayi Jin Ankira miliyan 20 to Ashe shi da yace abashi miliyan 2 kad'an ya d'iba kenan tab da yasani da yace sai anbashi miliyan goma."

Girgiza Kai likita yayi yace "ranki ya dad'e a Ina zanga miliyan 20 bare har na rik'eta, kinsan aikin namu a k'ark'ashin wani mukeci, sai dai idan wata ya k'are muke k'arb'ar Albashi Wanda bazai wuce dubu 80 ba dashi muke rufawa iyalinmu asiri tare da 'yan uwanmu."

Wani shu'umin murmushi Jamila tasaki tace "kana son ka mallaki miliyan 20 naka nakanka?"

"Kwarai Kuwa likita yace tare da Kuma gyara Zama."

Jamila tace "so nakeyi a matsayinka na likita Wanda kasan sirrin jikin d'an Adam so nake kasan yanda zakayi cikin hikima da dabara irin taku ta likitoci ka kawar mun da Sauban yaron gidan Nan Wanda kake kula dashi, ya bar duniya."
Idan ka kawar dashi to kasani zaka mallaki miliyan 20 Kai har da ma k'ari domin zan K'ara yi maka wata kyautar ta ban mamaki."

Zaro Ido likita yayi gumi ya shiga wanke Masa jiki, ga k'oshi ga kwanan yunwa,
Yana son kud'i sosai Yana son ya mallaki miliyan 20 din Nan, to Amma idan asirinsa ya tonu Yaya zaiyi da sarki maimartaba Yaya zaiyi da aikinsa Wanda ya dad'e Yana nema da kyar yasameshi."



*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 12*




Taimakon Gaggawa aka shiga Bawa Sauban inda aka sakashi a cikin wata na'ura domin ceto rayuwarsa."


tayi yunkurin shiga inda yake likitoci suka dakatar da ita tare da Bata hakuri da lallashin akan bazata Sami ganinsa ba,
Sai Nan da wata d'aya domin Yana cikin wani yanayi Wanda Addu'arsu kawai ake buk'ata"

Shuru Hajjah tayi taja da baya, hankalinta a tashe Dan ganin takeyi Sauban bazai tashiba mutuwa kawai zaiyi, dibo da yanda taga wani irin kunfa Yana zuba a bakinsa,
Wuri ta nema ta zauna fadawa suka zagayeta babu abinda takeyi sai Addu'ar Allah yabawa Sauban lafiya tare da rayuwa Mai d'orewa."

Gimbiya bilkisu ta matso kusa da Hajjah tace "umma kiyi hakuri da izinin Allah Sauban zai tashi, zai Sami lafiya, har Abada makiya baxasu tab'a samun galaba akansa ba,
Kizo mutafi masaukina ki ki huta har zuwa gobe idan Abdullah yaxo sai a San mafita."

Hakan Hajjah ta amince tabi Gimbiya bilkisu tare da fadawan,
Ko can d'in hakan bilkisu da Anna sukayi ta kwantarwa Hajjah da hankali snn ta Fara sakin jikinta a gidan, sai dai duk wani motsi nata da t Sauban a bakinta tana jera Masa Addu'o,e."

************
Duk iya bincike anyi ba wata alama da tanuni akwai sa hannun wani daga cikin gidan sarautar wurin yunkurin kisan Sauban, domin duk abinda za'ayi Jamila tana tare da Abdullah ana binciken da ita ba abinda takeyi sai aikin kuka a cewarta tana tsananin tausayin Sauban Halin da makiya suka sakashi me ya tare masu a duniya."

Ba abinda Abdullah yakeyi sai Bata hakuri,
hakan yasa ba Wanda yataba kawo bincike a kanta
, hakan shima sarkin gida, Wanda duk abinda za'ayi a gidan shine a gaba Yana bada tashi gudun mawar, sabida Yar jajen sarki ne da Anna sunyi imani bazai tab'a cutar dasu ba, Dan hakan Koda Wasa ba'a tab'a kawo komai a kansuba."

Hakan aka kammala bincike ba wani haske da aka samu, hankalin kowa ya koma England wurin Sauban washe gari Abdullah ya shiga jirgi ya sauka k'asar England domin dibo jikin sauban."

BaYan tafiyarsa da sati biyu komai yayita faruwa daga ciki har da samun nasarar samun lafiyar sauban, domin numfashinsa ya dawo har ya Fara motsi, anyi nasarar gubar Bata iyar da gauraye jikinsaba batayi tasiri a jikinsaba "

Satin Abdullah biyu a can ya dawo gida Nigeria tare da sauran bayi hud'u aka barwa Hajjah d'aya da kuyanga d'aya tare da Anna, domin ganin lafiya ta fara samuwa ga sauban duk da dai har yanzun ba Bari akeyi ana ganinsaba Yana cikin na'ura."

Gimbiya bilkisu itake hidima dasu Hajjah wacce ba yanda Abdullah baiyiba Akan zai kamawa su Hajjah wurin zama Amma saita nuna b'acin ranta, tana fad'in wato zai nuna cewa Hajjah shi kad'ai ta haifa, Banda su kenan,
Har sarki Abdulrahaman ta bugawa waya ta fad'a Masa Wanda shima yanuna b'acin ransa sosai dajin abinda Abdullah yace, hakan dai Abdullah ya basu hakuri yabar Hajjah a Nan snn yadawo gida Nigeria a cewarsa idan Sauban ya cika wata daya kamar yanda likitoci sukace zai Kuma dawowa tare da maimartaba domin su dubashi."

A d'an Zaman da Hajjah tayi tare da gimbiya bilkisu ta Gane bilkisu macce ce Mai tsananin nuna mulki da Isa tare da izzah, sannan tana tsananin nuna soyayyarta ga tilon 'yarta wato Saudat,
Tana son Saudat sosai Wanda sabida son da take Mata Bata bawa kowa rainonta kamar yanda aka San matar sarki Bata rainon d'a da kanta, tsakanin ta da yaro sai dai idan ankawo shi yasha nono, Amma bnda gimbiya bilkisu wacce
a kullum tana tare da 'yarta hakan shima sarki Abdulrahaman da zarar ya bugo waya baya da wata magana sai ta Saudat,
Hajjah ta jinjinawa wnn soyayya da sukayiwa Yar su kwaya d'aya tilo"

BaYan wata d'aya Alhamdulillah jikin Sauban yayi kyau yasamu lafiya Wanda har magana yakeyi Kuma Yana cin abinci sosai."

A ranar sarki da Abdullah tare da sarki Abdulrahaman sukazo k'asar, tabbas sunji Dadi sosai ganin Sauban yasami lafiya Wanda yake zaune Akan kujera ana fira dashi."

Anan sarki Abdulrahaman Ya kalli maimartaba tare da Abdullah da Hajjah ya Fara da cewa "ku ga farce ranka ya dad'e Ina neman wata Alfarma a wurinka Allah yasa zaka Amince da hakan, ranka ya dad'e Ina neman Alfarmar a bar Sauban k'asar Nan wurin gimbiya bilkisu domin taci gaba da kula dashi har lokacin da zai kuma samin lafiya,
Snn idan ya warke Ina neman Alfarma akan a barshi a hannunta yayi karatunsa anan har zuwa lokacin da ya mallaki hankalin kansa yasan abinda Yake Masa ciwo lokacin da zai fahimci makiyi da masoyi snn sai yakoma gida Nigeria,
diba da yanda ake farautar rayuwarsa makiyansa k'ok'ari sukeyi ta ko wacce hanya so sukeyi sai sunga bayansa."

Shuru kowa yayi yarasa amsar da zaibawa sarki Abdulrahaman domin shawarar da yanke tayiwa kowa dad'i a wurin sai murmushi ko wannesu yake saukewa."

Snn Sarkin yayi gyaran murya Fara magana kamar hakan "hak'ik'a Abdulrahaman kayi matuk'ar tunani tare da hangen nesa muna godiya da wnn karamci naka Allah yabar tare ya raya maka zuri'a."

Hakan Hajjah itama tayi Masa Addu'oe godiya tare da sanya Albarka,
Murmushin kawai Abdullah yakeyi cike da farin ciki domin yarasa abinda zaiwa Aminin nasa, iya k'auna sarkin Abdulrahaman ya nuna Masa ita da karamci, mik'ewa yayi tsaye fuskarsa tana saukar da murmushi yanufi inda Abdulrahaman yake zaune Abdullah ya rungume shi Yana Masa godiya, Yana fad'in " nagode Aminina yanda kayi mun Allah yabani abinda zanyi maka fiye da hakan hak'ik'a Kai abokine Kuma Aminine na kwarai."

Yinin ranar kowa cike yake da farin ciki,
Sai da sukayi sati d'aya a lokacin sauban ya Kuma Samun lafiya sosai har an sallamoshi daga asibity sundawo gida,
snn suka tattara kayansu har da hajjah suka dawo gida Nigeria suka bar Sauban a England wnn shine dalilin Zaman Sauban a k'asar England karatu."

_muje zuwa my friend's_⛹🏻‍♀


Bakaramin bak'in ciki da damuwa Jamila tashiga cikinsaba jin Sauban yasamu lafiya sosai k'arin Jin dad'i har da barinsa akayi a can domin yayi karatu,
Wato ana nufin bama a kasar Nan zaiyi karatuba kenan,
So akeyi yafi kowa karatu a gidan kenan?"
Tacije Baki taji wani irin tsanar Sauban tare da Hajjah ya dirar mata a zuciya domin tasan wnn duk shirrin Hajjah ne,
Domin ba Wanda Hajjah takeso takeso ganin ci gabansa kamar Sauban, ta rasa dalilin da yasa ta tsani nata yaran Sadeeq da Sageer,
wadan da ta fahimci ba Hajjah kawai ta tsanesu duk mutanen gidan basa sonsu ganin ido NE kawai da Kuma tana tsaye a kan yaranta."

ta d'auki d'amarar indai tana da Rai da lafiya ko a can Sauban bazai tab'a samun abinda yakeso ba,
Indai kud'i suna aiki sauban bazai tab'a fitowa da sakamako Mai kyauba Sauban bazai tab'a Jin dad'in rayuwarsa ko bai mutuba sai Nigeria tayi Masa wahalar Shigowa sai ta Sanya anyi tir da alawaddan karatunsa."

BaYan kwana biyu matan Abdullah suka haihuwa dukansu suka Sami 'Ya'ya Mata,
Khadija ta haihu ranar Monday Aisha ta haihu ranar Friday."
Murna a cikin masarautar abin ba'a magana,
Wanda Ina wuta Jamila tafad'a domin kwatakwata batasan ma suna d'auke da cikiba sai dai kwatsam taji haihuwarsu daga sama abinda yafi Kona Mata Rai Kenan."

Jakadiya ta shiga dokawa Kira cikin sauri jakadiya tazo ta zube a gabanta,
Cikin d'aga murya tace "ya akayi wad'an can bayin banzan suka haihu a cikin gidan Nan?"
Dama suna dauke da ciki Baki fadamun ba?"
Ta d'aga murya cikin b'acin Rai ta Zaro Ido alamar komai tana iya aikatawa jakadiya tace fad'amun nawa suka Baki domin kib'oyemun cewa suna dauke da cikin Abdullah a cikin gidan Nan ban saniba."

Sunkuyar da Kai jakadiya tayi cike da tsoro jikinta Yana rawa cikin girmamawa tace "ranki ya dad'e har Abada kud'i bazasu tab'a tasiri a gareniba har na Kai ga cin amanarki,
Yanda Kika San Baki San komai Dan gane da cikin jikinsuba sai dai kikaji haihuwa daga sama, Nima hakan ne a gareni ban San komai ba akai kiyi hakuri ranki ya dad'e Allah ya huci zuciyarki,

Amma Kuma ranki ya dad'e meye abin daga hankali da haihuwarsu Bayan dukansu Mata suka haifa ba maxa ba,
Koda maza ne suka haifa Sadeeq da Sageer sune a gaban 'ya'yansu nesa ba kusaba nayi imani d'aya daga cikinsu shi zaiyi mulkin masarautar Adamawa."

Wani murmushi Jamila tasaki najin dad'in ance d'anta zaiyi mulki,
Ta dubi jakadiya tace "tashi kitafi naji kin wanke mun DUK wata damuwata,
Kece da shegen kwadayin tsiya nasan za'a iya sayenki da kud'i Wanda idan na fahimci hakan sanyawa zanyi a saremun kanki kinsan ba tausayi ne daniba komai zan iya aikatawa, don hakan Dole ne na zargekeki kibi a sannu domin na tsane cin Amana"

Tuba nakeyi ranki ya dad'e nafi kowa sanin halinki insha Allah hakan bazai tab'a faruwa ba,
ki huta lafiya jakadiya tamik'e ta fita a ranta tana tsinewa Jamila akan tuhumar da tayi Mata bada laifintaba"

Anyi shagalin suna a gidan sarautar Wanda Jamila ta bada tata gudunmawa sosai komai da ita akayi sosai take nuna k'auna ga matan Abdullah tare da jaririansu,
Sai dai ta ciki na ciki bak'in ciki ne fal a ranta musamman yanda taga Hajjah tana farin ciki da haihuwar Wanda Sam bataga irin wnn farin cikin a fuskarka taba a lokacin da ta haifi su Sadeeq,
Hakan shima Abdullah sai murmushi yakeyi Yana farin ciki daga ganinsa kasan Yana tare farin ciki, hakan dai akayi taron suna aka watse yara suka ci sunan fateema Bintu wato sunan mahaifiyar Sauban kenan wacce Abdullah bazai tab'a mantawa da ita ba,
d'ayan Kuma taci sunan Hajaru wato sunan Hajjah Kenan, sarki yace Kuma Sam bai yarda da a canza basu suna ba a hakan za'adin kiran sunansu."

Hakan yayiwa duk wani mutum dake cikin masarautar Dadi Amma Banda Jamila da mak'arabanta."

**************

Sauban ya Fara zuwa makaranta secondry school inda ya Fara daga jss1 kasancewar karatun can ba d'aya bane da karatun Nigeria,
Sosai Yake hazaka da k'ok'ari har malaman makarantar sun Fara Alfahari dashi Akan karatunsa,
Hakan gimbiya bilkisu tana kula da karatunsa tare da addininsa sosai da Kuma tarbiyansa."

BaYan wata uku da bikin 'ya'yan Abdullah,
Sarki ya kwanta ciwo Wanda har asibity ya kwanta yasamu lafiya ya dawo gida,
Tin daga lokacin lafiya ta Kiya Masa yau ciwo gobe lafiya,
Wata safiyar juma'a aka waye gari sarki yace ga garinku Nan."

Mutuwar sarki ta girgiza Al'ummar garinsa dama wajen garin Baki d'aya domin duk Wanda yasan sarki Abdulsalam sarkin dake mulkin masarautar Adamawa yasan sarki ne Mai Adalci da sanin ya kamata sai dai duk da hakan mutuwa Bata barin wani Dan wani."

Abdullah yashiga cikin tashin hankalin mutuwar mahaifinsa hakan Hajjah wacce takasayin magana sai girgiza Kai kawai takeyi,
hakan akayi Masa wanka akayi Masa sitira aka kaishi gidansa na gaskiya."
Mutune k'asa k'asa jahohi sarakuna da shuwa gabannin k'asa duk sun zo wurin ta aziyar mutuwar sarki Abdulsalam,
BaYan wata biyu da mutuwar sarki aka yanke hukuncin nad'a magajin sarki wato Abdullah."

Murna a wurin Jamila abun ba'a magana domin idan kowa Yana bakin cikin mutuwar sarki ita farin ciki takeyi sabida mijinta zai maye gurbinsa ya Zama sarki Dole a kirata da Sarauniya Kuma fulanin sarki,
Dole Hajjah taja baya tayi kallo don Dole sarautar gida ta dawo a hannunta don itace matar sarki a yanzun."

D'aya ga watan match aka nad'aga sarki Abdullah a kan kujerar mulkin Adamawa hakan itama Jamila aka d'agata a matsayin Sarauniya Kuma fulanin sarki domin ta Hana a Bawa kowa sarautar fulani, tin daga lokacin sunanta ya tashi daga gimbiya Jamila ya koma Fulani ko Kuma kuce Sarauniya.
Duk wani ragamar cikin gidan sarautar itace take gudanar da komai, batare da tayi shawara da kowa ba,
Hakan sauran matan sarki Abdullah basa da abin cewa saboda dukansu ta kaisu wurin boka an d'aure Mata bakinsu sai yanda tayi dasu a cikin gidan."

Duk abinda takeyi Hajjah tana sane da ita sai dai takawo nagani ta zuba Mata domin tasan komai lokaci ne garesa wata Rana sai labari,
Hakan zata Kira sauran matan Abdullah ta dinga yimasu nasiha tare da basu hakurin akan abinda suke gani Jamila tana aiwatarwa a gidan komai Yana da lokacin sa."

Basa nuna damuwarsu Akan ta saboda mijinsu bai wulakantasu bai bai nuna kyamata a garesu ba hasalima yafi samun natsuwa a tare dasu to meye abin daga hankali a ciki?"

Sunsani Sarai harda shima Abdullah Bata barshi a banza ba Dan hkn yke biye Mata ga duk abinda takeso amma ai komai Yana da lokacin sa Mai hakuri bazai tab'a tab'ewaba."

*****************

A kwana a tashi ba wuya har Sauban ya kammala karatun sa na secondary ya Fara zuwa jami'a mataki na farko
a lokacin yana da shekara goma Sha tara
Ya girma duk wani kyau nasa ya bayyana, dama Sauban kyakkyawa ne, snn mutum ne ba mai yawan son magana ba tin Yana k'aramunsa bare yanzun,
snn baya son a damesa da yawan magana,
Dan hakan baya da wani aboki sai safwan Wanda d'an abokin Abbansa ne da aka turosa karatu a Nan England
Sosai tasu tazo d'aya da Safwan saboda safwan Yana da son karatu sosai kusan duk ra'ayinsu yaxo d'aya, sai dai shi safwan da zarar anyi hutu yake komawa gida Nigeria sab'anin Sauban da yake Zaune a k'asar gaba d'aya,
Waje d'aya ra'ayinsu ya banbanta da sauban,
Shine safwan akwai shi da son hirar 'yan Mata abinda Sauban ya tsana kenan , snn safwan Yana da yawan surutu da barkwanci da son ya shiga abinda da bai shafesaba abinda Sauban ya tsafi tsana kenan a rayuwarsa, dan hakan wani lokacin yakeji haushin safwan idan suka hadu a makaranta."

A lokacin da Sauban Yake da shekara goma Sha Tara a lokacin Saudat take da shekara Tara a duniya,
Saudat yarinya ce Yar gata sangartaccciya wacce uwarta da ubanta suke sonta, tare da sakanta ta,
Basa son ganin kukanta bare b'acin ranta,
A duniya duk abinda Saudat take buk'ata batare da b'ata lokaci ba ake Mata shi. Wnn dalilin yasa Bata ganin girman kowa musamman bayinta masu kula da ita maza da mata duk Wanda ya Mata ba dai dai zata d'aga hannu ta wanke sa da mari ko a gaban mahaifiyarta Bata ce Mata komai sai majinjina da zata kumayi Mata na burgewa "

Wnn halayan nata na sangarta da rashin ganin darajar mutum tin tana karamarta,
yasaka gaba d'aya yarinyar Bata burge Sauban,
Kwata kwata Bata bashi sha'awa,
Ita kuma Saudat tana tsananin son Sauban domin ko abinci aka kammala Bata ci sai har lokacin da Sauban yadawo a duk inda ya tafi snn zataje ta d'auko takawo Masa a d'akinsa su zauna suci a tare, ba Dan ransa Yana soba sai Dan gudun kada iyayenta suga kamar Yana tsanar yarsu", Bayan sunyi Masa halacci a rayuwa
Amma shi a zuciyarsa har ga Allah ya tsane yarinyar ba Kuma yarinyar ya tsanaba sangartar ta da halayenta ya tsana,
Bayaso kwata kwata tana shigo Masa d'aki tana fad'awa a kan jikinsa,
Wanda ya lura ko a gaban idon mahaifiyarta ta fad'a a kan jikinsa Bata yimata magana illah ta dinga murmushi tana d'aukar hakan ba komai bane."

Saudat tana aji hud'u a primary,
Abinda Sauban ya lura dashi shine ko a makarantar tasu Wasa da maza ba komai bane a gareta, gaba d'aya Bata mu'amala da Mata 'Yan uwanta Abokananta sune maza."

Akwai wani lokaci da yaje d'auko ta a makaranta kasancewar shi yake Kai ta idan zaitafi makaranta Yake ajiyeta idan Kuma ya dawo yakan tsaya ya daukota su dawo a tare, lokacin da yaje daukota ya tarar da ita zaune Akan k'afar wani malaminsu bature jar fata sai shafata yakeyi tana dariya."

Cikin b'acin Rai ya fincikota daga jikinsa ya kifa Mata Mari sosai yayiwa baturen rashin mutumci snn yasakata a mota suka nufo gida."

Duk a tunaninsa zata fadawa mahaifiyarta
Domin ya shirya abinda zai fadawa gimbiya bilkisu Wanda sanadin hakan yafison ya bar gidan gaba d'aya dama Zaman gida yafice Masa a Rai sam."

Amma Sam Saudat Bata fad'a mataba,
Illah tin daga lokacin tashiga Jin tsoron Sauban duk wani abin idan tanayinsa Bata barin sauban yagani, saboda a duniya ba Wanda ya tab'a dukanta sai Sauban Dan hakan take tsananin jin tsoronsa."

Wasa Wasa Saudat sai girma take k'arawa Wanda har ta kammala primary school tashiga jss1,
A lokacin tafara sanin ko ita wacece ko ita 'yar wacece,
Tafarajin kanta Yana Mata girma, dan ta Kira bayinta ta wulakantasu ba wani abin bane gareta, domin mahaifiyarta tana nuna Mata k'askantune a wurinta ta wulakantasu yanda ranta yakeso snn tayi mulkinta yanda takeso ita kad'ai CE wurin mahaifinta Kuma sabida da ita suke zaune a k'asar England."
Wnn dalilin yasa Saudat ta tashi da girman Kai da nuna Isa da mulki Wanda a duniya ba Wanda take tsoro sai Sauban."

Lura da tana D'an Jin tsoron Sauban yasa wata Rana Mahaifiyarta takirata tashiga fad'a Mata cewa ta dainajin tsoron Sauban idan ta ganshi ta daina firgita tana fasa abinda tayi niya, tasani ba wani dangata dake tsananinsu asalima taimakonsa sukayi suka tsiratar da rayuwarsa daga mutuwa."

Shuru Saudat tayi batayiwa Mahaifiyar tata maganaba sai da d'auki Yan mintina snn ta dubi mahaifiyar tata tace "mommy Ina son Sauban shine mijina Zaki aura mun shi?" Ina sonshi a duk yanda Yake

Tas taji Mari a kuncinta gimbiya bilkisu tana Mata wani kallo, cikin daga murya tace "nawa kike mekikasani a duniya dangane da aure shekararki nawa 13 kike zan cen aure,
To bara kiji Koda kin Isa aure bazan tab'a aura maki Sauban ba saboda Baku daceba gaba d'aya baya cikin tsarin maxan da nakeso ki aura,
Kisani ke kad'ai muka haifa a duniya mahaifinki sarki ne, Dan hakan Ina da burin ki auri namiji Wanda yayi fice a duniya Wanda sunan sa yayi fice kowa yasanshi a duniya ba kamar Sauban ba, kada na Kuma jin wnn maganar a bakinki, ta janyota tana lallashinta sakamakon Marin da tayi Mata."

Duk abinda gimbiya bilkisu take fad'a a kunnen Sauban a lokacin ya tinkaro d'akin nata domin ya gaida ita, karaf a kunnensa yaji tana fad'in hakan ya girgiza Kai yafita shima a zuciyarsa Yana fad'in mezaiyi da ita Koda Mata sun Kare a duniya bazai tab'a auren Saudat ba."

Wani abin d'aure Kai dake faruwa a makarantarsu Sauban shine yanzun shekara biyu kenan duk akayi jarabawa bayaci faduwa yakeyi duk su safwan sun wucesa,
Bayan yasan duk a ciki d'aliban makarantar ba wani Wanda zai d'aga hannu ya ce yafishi k'ok'ari, indai a wurin karatune Sauban shine sahun farko, Amma abin mamaki da zarar an like suna ba wani ci gaba da Yake gani a tare dashi shekara biyu kenan Yana maimaita shekara duk wani mate nashi ya wuce shi a karatu."






*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 13*




Abin Yana damun sarki Abdullah a kan rashin ci gaban karatun sauban, kullum Yana Nan a yanda yake."

Hakan yayi tattaki yaje da kansa k'asar batare da kowa yasaniba domin yayi bincike Akan abinda Yake faruwa,
Kai tsaye makarantar ya sauka a ofishin shugaban makaranta."

Bayan sun gaisa tin kafin sarki Abdullah yayi magana ya fad'i abinda ya kawoshi shugaban makaranta ya Fara da cewa
"ranka ya dad'e dama ko da bakazoba mun yanke shawarar zamu aika maka da sak'o ta hanyar wayarka domin musanar dakai abinda Yake faruwa koda Kai zaka d'auki wani mataki a kan yaronka,sauban
Sabida munfad'awa mahaifiyarsa wacce suke tare a Nan duk abinda Yake faruwa akan karatun nasa ba wani mataki da ta d'auka har yanzun, domin mun yanke hukuncin da zarar mun fad'a maka baka kaima baka d'auki wani matakiba to tabbas kararsa zamuyi a makarantar nan"

Wato yaronka Sauban nasara dalilin da yasa yafi ko wanne d'alibi fad'uwa a makarantar Nan
Na Tara duka malamai nayi bincike akansa domin naji dalilin fad'uwar nasa,
Amsa d'aya ce baya karatu."
Dan hakan muka yanke hukuncin zamu kiraka mufada maka, idan wata makaranta zaka canxa Masa hanya a bud'e take mu munfi son hakan."

Shuru sarki Abdullah yayi snn yabude Baki yace "abinda yakawoni k'asar Nan kenan don nayi bincike saboda nima abin Yana damuna matuk'a,
Amma maganar Nan da kayimun na yanke shawarar fitar dashi daga wnn makarantar zan canza Masa wata, ya mik'e tsaye tare da mik'awa shugaban makarantar hannu yace "godiya nakeyi sai anjima yafita."

Kai tsaye gidan Aminin nasa yanufa inda Sauban Yake da Zama,
Bazata Sarauniya bilkisu taga zuwan sarki Abdullah, inda ta nuna mamakinta a fili."

Bayan sun gaisa cike da girmamawa snn tasaka bayinta aka kawo Masa abinci tare da kayan motsa baki, sai da ya kammala cin komai snn ta Kuma dawowa cike da izzah da Isa suka Kuma gaisawa."

Daga Nan Yake fadamata abinda ya kawoshi k'asar Akan karatun Sauban."
Sosai Sarauniya bilkisu taji kunya domin ansanar da ita hakan a makarantar shap mantawa tayi Bata d'auki wani mataki akai ba."

Lura da hakan da maimartaba yayi yasa ya kawar da zancen akan cewa 'ina shi Sauban din Yake Yana son ganin sa, yanaso suyi magana idan da akwai makarantar da yakeso ya fad'a, ayi komai daga you zuwa gobe,
Domin gobe yakeso ya koma."

Mik'ewa tayi jiki a

Please Login or Register in order to submit comment