Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafad'arsa ya kwantar da murya yace "abokina d'anka yana cikin wani hali wanda 'yata safna kad'ai zata taimakesa, amma sai naga kamar kana nuna bakasan komai a kaiba."

Murmushi Alhaji Habib ya sauke yana kallon sarki,
Snn yayi murya yace"gyara kalamanka ta yaya shegiya marar asali ta zama 'yarka?
Meyasa kakeson danganta kanka a matsayin uban shegiya wacce ka kyamata ka furta cewa gara Sauban ya mutu akan ya aureta."

Shuru sarki yayi yarasa abinda zaice,
Cikin rawar murya Sarki yace "rashin sani ne wanda hausawa sukace yafi dare duhu,
Bansan safna 'yarka bace."

Alhaji Habib ya katseshi da cewa,
Sai tana a matsayin 'yata sannan zaka taimaketa kabar d'anka ya aureta?"
sai tana matsayin 'yata sannan zakayi jink'anta kaji tausayinta ka janyota a jikinka kanuna mata k'auna kamar ko wanne d'a?"

Kasani Kai shugabane Wanda akasani da tausayi da taimako da jink'ai Wanda baya k'yamatar talakawansa a duk yanayin da yasamesu."

Amma saigashi abin mamaki a lokaci d'aya ka rik'id'e kazama mai son kansa,
Har kake kyamatar talakawanka wad'anda basada gata suke neman taimakonka, Sarki da kansa da bakinsa yake cewa d'ansa bazai auri shegiyaba marar asali, har yake Neman kashe d'ansa da kansa a kan wani dalili nasa."

Ka manta da d'a na kowa ne,
Shege da mai asali duka d'aya ne a wurin Allah,
a matsayinka na shugaba Sarki ka kyamaci marayu marasa uba,
Sauran jama'ar gari idan suka aikata hakan zaka iya hukuntasu kuwa?"

Sarki yayi shuru yarasa bakin da zai bud'e yayi magana"

Hajjah itama shuru tayi tana girgiza kai domin magaggunun Alhaji Habib sun shigeta matuk'a."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🤴 *D'AN SARKI SAUBAN*🤴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 37*





***** A cikin babbar fadar sarki,
Sarkine zaune akan kujerarsa ta mulki, a gabansa kuma shuwa gabannin 'yan jarida ne zaune a gabansa,
Bayan sun kammala gaisawa aka ga batar masu da kayan motsa baki sukaci,
Snn Sarki yayi gyaran murya ya fara da cewa "nasan zakuyi mamakin kiran da nayimaku cikin gaggawa,
Ba abin mamaki bane idan na fad'a maku halinda nake ciki Wanda a halin yanzun nake Neman taimakonku."

Ya mik'a masu hotunan safna Wanda aka cire iya fuskarta aka wanko kati guda goma,
Yace "wnn yarinyar nakeso a nemomun ita a duk inda take a,cikin garin nan,
asaka sanarwa a cikin duk wata kafa ta watsa labarai Wanda duniya zata gani cewar duk Wanda ya ganta ko yasami labarinta ya kawomun ita Zan bashi kyautar Naira miliyan biyar da gida a cikin GRA tare da motar hawa,
Cikin satin nan nakeso ta bayyana a wurina domin rashin ganinta yana dai dai da rasa rayuwar d'ana sauban da zanyi."

Jijjina kai sukayi cike da mamakin maganar da sarki yakeyi, suka shiga tunanin lallai sarki bak'aramun so yakeyiwa wannan d'an nasaba, sosai suka yiwa sarki jaje da fatan samun lafiyar d'an nasa, tare da Alk'awarin insha Allahu zasuyi iya k'ok'arinsu wurin sanarwa tare DA tallace tallace a duk cikin wata kafa tasu har Allah yasa asami Wanda zaice yasanta ko ya ganta ko yanada labarinta, sai muyi masa iso a wurinka."

"Godiya nakeyi inji Sarki tare da mik'awa ko wannensu. embulem d'in kud'i suka karb'a tare da yin godiya sukayi masa sallama suka fita."

***********************

Kwacciyar hankali tare da wadata da zaman lafiya mai had'e da hutu Mai cike da gata da Mai tattare da sakanta duk sun samu a wurin Safna,
Iyayenta sai nan nan sukeyi da ita Sam basa son ganin kuje d'aya ya rab'eta duk abinda safna tace tana so da Wanda tace bataso duk iyayenta suna k'ok'arin yimata shi,
Kwata kwata Alhaji Habib ya kasa komawa Dubai bakin aikinsa, gani yakeyi da zarar ya bar k'asar wani abin kuma samun 'yarsa zaiyi Dan hakan ya yanke shawarar zai tattaro duk kasuwancin sa ya dawo gida Nigeria idan hakan zai bashi wahala to zai tattara 'yarsa da Matarsa ya tafi dasu a can dubai d'in yana ganinsu a kusa dashi."

Safna ansami lafiya fatar jikinta ta goge tazama yar birni yar gayu rainon yan gayu sai kamshi take zubawa yo Hajiya falmata ai ba bayaba a wurin ado da kwalliya tare da kyaran jiki, duka kyan da Allah yabata ya kuma bayyana idan ka ganta tamkar wata balarabiya,
Itama hajiya falmata sannu a hankali iya Dan zaman da tayi da 'yarta duk ta fara koyamata tsafta da kwalliya tare da gyaran jiki mai had'e da tsafta ta ciki da ta waje."

Iya binciken da sukayi mata akan karatunta sun fahimci batayi wani zurfi a karatun Arabic ba, bareshi karatun boko Wanda bata tab'a zama a class ba,
Hankalin Alhaji Habib ya tashi ace kamarsa 'yarsa tilo d'aya take zaune cikin wannan jahilci,
Ya d'aga kansa sama cike da b'acin rai yashiga tunani a duniya ba wacce ta cuceshi ta zalinceshi sai hajiya Nana, da tasanya aka d'auke masa 'yarsa gudan jininsa a lokacin da take da buk'atarsu,

A ranar ba'a kwanaba sai da ya d'auko malamai na Arabic dana boko suka fara yiwa Safna lesson a gida,
A cewarsa idan ta fara ganewa kwakwalwarta ta bud'e,
Zai d'auketa yasakata a makarantar da sai d'an wane da wane yake karatu a cikinta yana burin tayi. karatu tasami ilimi mai yawa wanda za'ayi Alfahari da ita a duniya."

ai kuwa ba laifi safna yarinyace Mai.hazak'a da k'ok'ari ta fara ganewa duk karatun da akayi mata zakaji tana maimaitawa ita kad'ai ta fara iya Karatawa da rubutawa, matsalarta d'aya tunanin sauban Wanda takasa mantawa dashi a rayuwarta duk wani bugun zuciyarta da numfashinta sauban take tunani,
Tanaji a jikina yana cikin damuwa akwai abinda yake faruwa dashi,
Hakan take shige d'akinta ta rungume fillow tayi ta kuka tanajin wani matsanancin son sauban yana damunta a zuciya gashi batasan inda zata nemoshiba.'
Inama zata ganshi a halin yanzun,
Tabbas tasan idan sauban ya ganta a wannan halin da take ciki zaiyi farin ciki,
ganin iyayenta sun bayyana a gareta,
abinda yake fata da buri kenan akoda yaushe ya nemo Mata iyayenta idan hakan baisamuba zai d'auketa ya tafi da ita masarautarsu ya bata farin ciki,
Shuru tayi tana nazari tabbas yana yawan fad'a mata cewa zai d'auketa ya tafi da ita masarautarsu,
tabbas d'an sarki ne natab'ajin maigari yana fad'ar hakan,
Wato d'an sarkin garin nan ne kenan?
Tinda a birni yake da zama."

Hawaye suka ziraro mata tashiga fad'in sauban d'ina a Ina Zan ganka, ta wacce hanya zanbi nafita domin nemanka."

Sautin muryar kiran Umma taji tana kiranta tare da kusanto d'akinta,
Cikin sauri ta goge hawayen dake zuba a idonta ta share fuskarta, umma tashingo tana fad'in Suhailat zaman me kikeyi ke d'aya a d'aki bayan na fad'a maki ki daina zaman d'aki ke d'aya kina tunani."
Kuka kikayi ne?
Meyake damunki?"

In har tunanin babanki na k'auye kikeyi Wanda kulllum kike maganarsa Abbanki ya sanya ayi bincike a kansa duk inda yake za'a nemo maki shi idan kuma tabbas ya mutu zamu sami labarin hakan,
Ki daina tunani yanzun ba lokacin tunaninki bane lokacin farin cikinki ne kina tare da mahaifanki,
ki tsaya kiyi karatu domin lokaci bai k'ure makiba Abbanki yana da buri akanki musamman akan karatunki."
Taso 'yata mutafi falo muyi kallo."
Tamik'a mata hannu safna ta mik'a nata hannun ta sauko daga kan gadon umma ta rugumeta cike da k'auna suka fito daga d'akin suka nufi babban falon gidan."

umma ta zauna akan kujera tana kallon safna tace Doughter kunnamun TV can ki kamomun tashar NTA domin yanzun lokacin labarai ne musan abinda duniyar take ciki."

Safna tayi murmushi cikin ladabi tace "to umma,
Tanufi wurin Tv ta kunna ta kamo Mata tashar NTA,
Ai kuwa labaran sukeyi umma tayi murmushi ta janyo safna zuwa jikinta ta rungumeta domin jitakeyi kamar ta mayar da ita a ciki akan so, taci gaba da kullo tana murmushi a fuskarta ga dukan alama tanajin dadin wnn yanayin."

Hoton safna tagani a nuno a cikin tv tare da huton sauban d'an Sarki yana kwance a kan gadon asibity oxygen sanye a hancinsa da bakinsa tamkar Wanda ya mutu,
Mai watsa labarai yana cewa "Ana cigiyar wannan yarinyar mai suna Safna Wanda tabaro k'auyen lassa a sakamakon harin da aka kaimasu a cikin k'auyen Wanda yayi sanadin mutuwar mahaifinta itakuma ta gudu domin ta tsira da ranta bincike ya nuna ta shigo cikin garin nan na adamawa,
Sarki ya bayar da KYAUTAR mak'udan kud'i Naira miliyan biyar tare da kantamemen gida na more rayuwa dake cikin Unguwar GRA tare da makulin mota ga duk wanda yakawo masa yarinyar nan ko yaxo masa da labarin inda ya take za'a bashi kyautar wad'annan kud'aden tare da gida da mota,
Ba dan komai ba sai dan ceto rayuwar d'ansa yarima sauban daga mutuwa akan matsananincin ciwon son da ya fad'a akan yarinyar wanda a halin yanzun yana asibity yana tsakanin mutuwarsa da rayuwarsa,
Ga duk Wanda yake da labarinta ko yasamu labarin inda take yana iya tuttub'armu a wannan number kamar hakan.....

Wani irin k'ara safna tasaki mai sauti ta tamik'e tsaye tanufi hanyar fita waje da gudu tana fad'in nashiga uku umma sauban d'ina ne wlh sauban d'ina ne zai mutu,
umma Sauban ya taimakeni zai mutu a sanadin sona, umma zantafi gareshi wlh duk sauban ya mutu nima mutuwa zanyi,
da gudu tanufi k'ofa umma ta biyota cikin tashin hankali da zafin nama domin ta rik'ota ina safna har ta fita,
Karaf taci Karo da Abba yashigo da mota zata fita get tana kuka umma tabiyo bayanta tana kiran sunanta ina safna batajinta hankalinta a tashe yake,
Abba baitsaya direba ya tsayar da mota ba ya bud'e ya fito da jarida Rik'e a hannunsa mai d'auke k'aton huton safna da sauban anwatsasu a duniya ana cigiyarta, acan kan hanya yagani ya saya,
Cikin zafin nama rungumo safna ya yana fad'in dota lafiya meya faru."

Shisshikar kuka takeyi tana fad'in Abba sauban xai mutu, Abba sauban ya taimakeni,
Na Dade inaji a jikina sauban yana cikin wani hali, Wlh Abba Idan sauban ya mutu nima mutuwa zanyi, ku kaini wurinsa,
Bata rufe bakiba ta zube wurin a some."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*




*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )




*40*





Dogon nishi Alhaji Habib yaja ya burzar da iska Mai zafi a bakinsa domin ransa yana masa zafi da kuna,
Ya matsa wurin gadon sauban Wanda suke kallon duk abinda ke faruwa a d'akin,
Duk maganar da iyayen keyi tana masu yawo a kunne.'

Ya kalli sauban yakira sunansa
Yace "My son kamar yanda yake kiransa a can baya,
Sauban ya d'aga Kai ya kallesa, yace "Na'am Abba."

Yace " my son Safna ba shegiya bace,
Nine mahaifin Safna, kaddara tasa na rabu da 'yata badan inaso ba."

Safna tabani labarin irin d'inbin taimakon da kayimata,
Ta fad'amun cewa ka taimaketa a lokacin da take da buk'atar taimako ka taimaki rayuwarta a lokacin da take buk'atar taimakonka,
Baka kyamaceta ba a lokacin da kowa yake kyamarta ta,
Hakan ya tabbatar mun da cewa Kai masoyin safna ne na gaskiya,
Ya dafa kansa yace "Allah ya baka lafiya my son."

Duka d'akin suka amsa da 'Ameen."

Ya juya ya kalli "hajjah yasakar mata murmushi, itama tasakar masa, ya Rik'o hannun Hajjah yace "mama ga safna nan nabarta a hannunki ta zauna tare dake har zuwa lokacin da my son yasami lafiya."

Murmushin farin ciki hajjah tasaki ta shafo kan Alhaji Habib tace Allah ya maka Albarka ya a zurtaka da zuri'a Mai yawa mai Albarka."

Ameen yace yana murmushi."

Ya nufi hanyar fita ya tsaya ta gaban sarki ya kara bakinsa a kunnensa yanda ba Wanda yasan abinda yace,
yace "ka gyara kalaman da kayi a baya ko hakan zaisa ka taimaki rayuwar d'anka idan ba hakan ba
D'anka bazai auri shegiya marar asaliba, idan kai kajanye ni banjanye ba."

Yana murmushi ya fita, Hajiya Laila tabi bayanshi jikinta duk a mace yake."

Suna gani fitarsu a sauban da safna suka kalli juna suka saki murmushi a tare,
tare da sauke a jiyar zuciya suna kallon junansu."

Sarki shima a jiyar zuciyar ya sauke tare da hamdala domin yasan komai yazo k'arshe tunda sauban yaga safna, ya juya ya kallesu ya girgiza kai yafita yanufi d'akin da aka kwantar DA saudat."

Gyaran muryar hajjah sukaji tana fad'in "sannu iyayen soyayya ai saiku saki hannun juna tunda ba aure aka d'aura makuba,

murmushi suka saki a tare suna kallon hajjah, sukak'i sakin hannun."

Hajjah ta Rik'e baki tana kallonsu tace, oh ni yaran yanzun basada kunya,
Ta nuna sauban tace kai dan buhun ubanka kasakar masu yarinya, Amana akabani."
Mataccen banza da wufi da yanzun kana lahira kuma mutuwarka bazata hana muyi abinda mukeso ba ."

cije baki sauban yayi yasaki hannun safna, suna sakarwa juna murmushi."

Turo k'ofa akayi Safwan ne yashigo tare safina matarsa, Wanda cikinta ya tsofa har yafito,
a kasalance ya shigo cikin d'akin jiki ba kwari domin yasan ido biyu zaiyi da abokin nasa a kwance cikin mawuyacin hali bawani cigaba da akasamu."

Turus yayi yaja ya tsaya yana kallon sauban yana kallon safna bakinsa a bud'e cike da farin ciki maganarma takasa fitowa a bakinsa,

cikin farin ciki da zolaya ya janyo kujera ya d'orawa safina yana fad'in zauna ranki ya dad'e maman yan biyu,
Zauna da kyau musha kallon wata sabuwar soyayya Mai cike da abin mamaki."

Hajjah na ganin shigowar safwan tasaki dariya tafita a d'akin bayan sun gaisa tanufi wurin Saudat."

Hab'a Safwan ya Rik'e yana kallon sauban Wanda sauban ganin shigowar safwan ya rufe idonsa tare da had'e fuska domin yasan iskancin Safwan na yau saiyafi na kullum."

Safwan yace "haba abokina amma gaskiya ka wahalar damu,
da tun farko kafad'a mun maganin ciwonka safna ce,
Ai da bamu kawo har asibity ba."

Tam amma a duniya ban tab'a ganin mayen soyayya kamarka ba,
Ya rik'e baki yana dariya ya kalli safna yace "sannu kinji a gaskiya kinshiga can can cikin zuciyar abokina ya matuk'ar kamuwa da soyayyarki mai tsanani Wanda ta tashi shek'ashi lahira
Kinga duk ciwon nan da yakeyi duk a kanki yakeyinsa, zai kuma yin wata maganar
da sauri sauban ya bud'e idonsa ya sanya hannu a gefen gado ya rarumo k'ofin te da yagama sha ya jefawa Safwan,
ALLAH yasa bai sameshiba."
Ya danna masa harara cikin murya irin ta marasa lafiya yace d"an iska kawai kayi tafiyarka nagode."

Dariya safwan yasaki yace "zan maka uzuri idan ka koreni a yanzun zantafi saboda har yanzun ba'a hayyacinka kakeba,
Giyar soyayya take dukanka,
Nasan gani kakeyi duk na takura maka zuwan nan nawa,
Oh Tun yanzun kenan Ina da ankai maka ita a d'akinka😊."
Ai nasan ranar saikafi Mai kura shafawa, Dan kuwa.........,
Bai k'arasa maganar ba, sauban ya wurgo masa cukali a k'afa,
Dariya Safwan yakeyi ya tashi ya nufi hanyar fita yana fad'in "Allah yabaka hakuri yariman soyayya ni natafi sai anjima idan nadawo,
Yayiwa safina alama da hannu akan sutashi sutafi."
Sallama tayiwa sauban da Safna tare da fatan samun lafiya tabi bayan mijinta suka fita."

Fitarsu ya saka sauban da safna shiga cikin wani yanayi mai cike da shauk'i,
Anan take sauban ya nemi ciwo a jikinsa ya rasa, sannu a hankali ya tashi zaune da kansa idonsa na kan safna yana kallonta ganin ta goge ta koma 'yar birni yar gayu duk wannan dattin da k'auyanci duk babu shi,
Yasaki murmushi, itama ta kallesa tasaki murmushi tare da rufe fuskarta cike dajin kunya."

Sunanta yakira cike da kulawa yace "safna hakika tausayinki tare da tausayin halinda zaki shiga a lokacin da natafi nemanki a k'auye akacemun kinb'ata shi yasakani shiga cikin wannan halin,
bani labarin rayuwar da kikayi bayan shad'inki har zuwa tafiyarki da yanda kikayi kika had'u da mahaifanki."

Sunkuyar dakai tayi tana wasa da ya tsun hannunta tashiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe."

Sosai ya tausaya mata wani b'angare kuma yayi farin cikin ganin mahaifanta da tayi."

*********************


Kuyangin saudat tare da hajjah da maimartaba tsaye a kanta tana kwance akan gadon asibity ruwa suna jone a hannunta,
Babu abinda yake fita a idonta sai hawaye, Wanda anyi bata hakuri takasa hakura,
Babu abinda take gani a idonta sai mijinta masoyinta da macce a kan jikinsa yana sakar mata murmushin da bai tab'a yimata irinsaba."

Kuka takeyi sosai tana doka kanta a jikin k'arfen gado dake saiti da kanta, tana fad'in bazai yiwoba sai a bayan raina."

Sallamar shigowar gimbiya Bilkisu sukaji tare da maimartaba mahaifin saudat Wanda labari ya samesu cewar Saudat ta yanke jiki ta fad'i itama tana asibity a kwance,
Shine suka biyo jirgi hankali a tashe suka iso yanzun nan."

Saudat tana ganin shigowar mahaifanta ta mik'e da sauri ta cire ruwan dake jone a hannunta ta nufi wurin mahaifiyarta ta rungumeta ta kuma sakin kuka mai sauti, tare da furta na shiga ukuna mommy mutuwa zanyi."
[3/30, 9:56 PM] Hayat: *DAN SARKI SAUBAN*




*Writing by*
*Ummu Safwan*
( _Fareeda Basheer_ )



*41*






"Bazaki mutuba inji gimbiya bilkisu ta janyo hannun saudat suka zauna a gefen gado ta shiga share mata hawaye,
Meyake damunki meke faruwa?
Nasan Ko baki fad'aba matsalarki d'aya ce Sauban,
Meya maki meyake faruwa?"

Kuka saudat ta kuma fashewa dashi Wanda ya janyo hankalin mahaifinta da sarki Wanda suke tsaye a gefe d'aya suna gaisawa
Lokaci d'aya Suka juyo tare suna kallonta,
Mahaifinta ya matso kusa gareta yana fad'in Saudat sannu ki daina kuka ba'ayiwa ciwo kuka Allah zai baki lafiya,
Ya juya ya kalli sarki dake tsaye a gefe d'aya yana kallonsu,
Yace " Ashe jikin nata da sauki sosai, dana san hakan Zan sameta da banzo da kainaba,
sai dai na turo mahaifiyarta ta dibata, saboda inada aiki mai tarin yawa na ajiye nazo,
lokacin da labari ya samemu cewar ta yanke jiki ta fad'i, hankalinmu a tashe ido rufe muka iso, Ashe da sauki sosai,

Ya juya ya kalli sarki yace wai meyake faruwa ne?me yake damunta?"

Itadai hajjah tuni tabar d'akin tun da suka gaisa da mahaifanta,
domin itama a halin yanzun jarabar kishin Saudat ya soma bata haushi,
Ba'a aure aka aureta?
Ko so takeyi yanda ubanta ya zauna da mata d'aya shima sauban ya xauna da ita kad'ai,
To uwarta tafi k'arfin ubanta shiyasa ya kasa k'ara aure,
Tunda tarigada ta magance shi shiyasa yake tsoron yai Mata kishiya,
To sauban yafi k'arfin sihirinsu domin tinda aka haifeshi na d'auki mataki a kansa sai dai a buga a barsa ba wata shegiya da zataci galaba akansa indai ba Alheri a tare da ita."

Sarki ya kalli mahaifin Saudat yasaki murmushi yace mutafi waje zamuyi magana,
Hakan suka jera suka fita suna hira cikin farin ciki, kasancewar akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu."

"Gefe d'aya sukaja suka tsaya,
Wata sabuwar gaisuwar suka soma,
Mahaifin saudat yake tambyar yaya jikin sauban da fatan andace ansami abinda yakeso."

Murmushi Sarki yayi, yace "Alhmdulillah sauki yasamu,
sakamakon nemo masa yarinyar da akayi,
Ashe ita yarinyar 'zaman 'ya take a garemu, 'yar gidan Alhaji Habib Naira ce,
Wanda ta b'ata tun tana k'arama,
Allah ya kaddara ya gane yarsa,
itace safna wacce sauban yake so."

Alhmdulillah mahaifin Saudat yace "tare da cewa komai yazo gidan sauki kenan,
Yanzun abinda za'ayi a gaggauta a d'aura masu aure shikenan hankalin kowa sai ya kwanta."

Shuru Sarki yayi baiyi maganaba,
Mahaifin Saudat ya d'aga kai ya kallesa yace yanaji kayi shuru ko akwai matsala ne?"

Sarki ya sauke ajiyar zuciya yace "akwai matsala."

"Matsala kuma daga ina?"
Wacce irin matsala kuma?"

Sarki ya kallesa yace "dalilin ganin safna da Saudat tayi a tare da sauban shine yasaka ta yanke jiki ta fad'i batare da ta saniba."
Abokina kafi kowa sanin mata suna da tsananin kishi zasu iya aikata komai a kan kishiya,
Banason Saudat ta shiga cikin wani hali akan auren safna da sauban zaiyi, Dan hakan nake tunanin akwai matsala anan gaba kodai a fasa."

"Ita d'in banza inji mahaifinta,
Akan kishinta na banza za'a hana yaro auren wacce yakeso?"
To bata isaba idan kaga sauban bai auri Safna ba to sai dai idan Allah ya rubuta ba matarsa bace, amma akan bak'in kishi na Saudat Wanda ta gada a wurin uwarta bata isa ta hanaba,
to bari kaji koni nan mahaifinta neman Aure nakeyi ban fad'awa kowa ba sai kai,
a halin yanzun Zan cen danake maka jiyan nan aka kaimun laife, so nakeyi sai an d'aura auren sannan kowa zaiji bayan ankawomun Amaryata cikin gidana, illaso duk Wanda zai fad'i ya mutu sai dai ya mutu a kan masifar kishi,
haba zama zanyi na mutu da mace d'aya to asirin da ake cewa anyimun yanzun ya karye hud'u zan aura domin inda buk'atarsu a matsayina na sarki?

Dariya Sarki yasaki ya bashi hannu suka tab'a yana fad'in "Ashe wannan karon abokina ya turza, ai duk a tunanina bakada lafiya shiyasaka ka zauna da macce d'aya."

"Mahaifin Saudat yana dariya yace " lafiya ta k'alau, zaku tabbatar da hakan idan na ajiye hud'u shekara ta zakagayo duk kuka gansu d'auke da ciki."

Suka kuma sakin wata dariya,
Mahaifin Saudat yaci gaba da cewa "Allah danasan ciwon kishine da ba abinda zai sanyani nazo,
Sai dai na turo mahaifiyarta tunda a wurinta taji wannan shegen kishin na tsiya."

Auren sauban kuma ba abinda za'a fasa ba barama kaji baxan bar garin nan ba sai natafi da kaina na nemo masa aure a wurin Alhaji Habib duk dai komai ya zama
Na gida, idan aka tsayar masa da rana sannan hankalina zai kwanta sai na koma gida"

Sosai sarki yaji dad'in kalaman abokin nasa koba komai yasan Alhaji Habib idan yaga idon sarki Abdulrahaman zaiji nauyi da kunyar aikata abinda yayi niya saboda akwai yarda da Amana a tsaninsu,
Dan ya tabbata idan ba atare suka tafiba akwai d'aukar fansa a cikin idon Alhaji Habib akansa."

*******************

A can d'akinsu Saudat kwance take akan jikin mahaifiyarta sai kuka takeyi mahaifiyarta tana lallashinta tare da share mata hawaye,
so takeyi hankalin 'yarta ya kwanta ta fad'a mata damuwarta."

Bayan Saudat tayi shuru tare da Jan doguwar ajiyar zuciya,
Tamik'e zaune tana kallon mahaifiyarta wacce take tambyar wai meke damunta KO sauban ne ya mutu?" Ta girgiza kai alamar A'a ciwonsa ne yayi tsanani ta girgiza kai alamar A'a to meyake faruwa ne?" Hawaye suka kuma zuba a idonta
Tabud'e baki cikin sigar kuka tace "mommy yarinyar nan bata mutuba,
Yanzun hakan suna tare a wuri d'aya akan gado d'aya a cikin asibityn nan tare da sauban."
ta fashe da kuka mai sauti tana fad'in a gaban idona suka Rik'e hannun juna cike DA k'auna da shauk'i,
Mommy a gaban idona wata macce take bawa mijina ruwan Te a baki, idonsu sarke dana juna suna kallon k'auna."

Ta dafe zuciya tace "Mommy Mutuwa zanyi idan sauban bai rabu da yarinyar nan ba."

Zaro ido mommy tayi cike firgici domin jitakeyi zuciyarta tana harbawa tamkar itace akayiwa wnn cin fuskar,
Jitakeyi kamar mijinta ne ta hango tare da wata kamar yanda saudat ta fad'a Mata."

"Karya ne wlh idan inada rai ina numfashi a doron k'asa sauban bai isa yayi wani aurenba,
cin fuska 'yata a gaban idonta, Ina raye a doron k'asa, baxai yuwoba wallahi, yanda yabar shan nonon uwarsa hakan zai bar shegiyar yarinyar nan har abadan duniya koda zai mutu"

Zabura Saudat tayi tace "A'a mommy banda mutuwa banason ya mutu."

A harzuk'e mommy ta dubeta cikin masifa da b'acin rai tace "yimun shuru shasha sha, to bari kiji da mijinki yai maki kushiya gara ya mutu, kiyi sunan ke kad'aice a wurin mijinki har ya mutu ya barki,
sakarai wacce batasan inda yake Mata ciwoba, idan Kika sanya tausayi a ranki, Kika bari ya auro maki shigiya marar asali kinshiga uku kashinki ya bushe, domin kuwa saikin zama banza a wurinsa, don ita shegiya gadon bariki tayi tun a wurin mahaifanta tunda a kan hanyar bariki aka haifeta, Dan hakan koda zata shigo gidanki, tariga da tasan komai tun a kan hanyar bariki tayi wayo,
kinaji kina gani sai dai ki Koma gefe kizama 'yar kallo, domin kina gani da rayuwarki a gaban idonki wata shegiya tsintattaciyar mage ta karb'e maki mji, dama ba sonki yakeyi kece kike sonsa."

Saudat ta d'aga ido ta kalli mahaifiyarta tace "mommy inaji ana fad'a cewa wai angane iyayenta."

Mere baki mommy tayi tace 'yar wacece a cikin garin nan suwaye mahaifanta a cikin garin Adamawa."

Saudat tace "Naji ana fad'ar wai ko 'yar wani Alhaji Habib Naira ce wacce ta b'ata tin tana jaririya."

Gaban mommy yabada dam,
Ta zaro ido waje tana tunanin kaddai a ce 'yar Hajiya Laila

Please Login or Register in order to submit comment