Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zanje na huta."

Duk abin Nan da akeyi baba bai San abinda akeyiba,
Shi a ganinsa rashin samun mijin aure da banyiba,
Wata k'ila Aljanu suka aure Ni, Dan kuwa duk sa'ata sunyi aure wasu har sun haihu, Ni har yanzun shuru ba miji gani kyakkyawa ajin farko."

Mutum d'aya ne ya jure korar jummai da tsangwamarta ya nace akaina cewarsa tinda Yana Sona sai ya aureni babu Wanda ya Isa ya Hana,
Sunan shi AUDU."

Audu D'an sarkin kiwo ne dake cikin k'auyen mu,
Sosai Yan matan garin suke ruguguwa a kansa domin yace Yana sonsu bai furta hakan ba sai a kaina."

Bana son Audu sam a Raina domin ni duniyar ma gaba d'aya taficemun a Rai fatana Akoda yaushe Allah yayi mun mafita, ta Alheri ya bayyanarmun da iyayena domin naji dad'in da yasa suka jefar dani a lokacin da nake da buk'atarsu." Hakan Nan nake kula Audu nasanyawa rayuwata zan aure shi Koda bana sonshi, kodan na huta da azabar Inno."

Ana hakan D'an maigari JARMAI JAN WUYA shima yafito neman aure na,
Sosai Inno tayi farin cikin fitowar Jarmai domin tasan da zarar sun Kara da Audu wurin shad'i,
ba makawa zai cinye Audu, dele a d'aura mun Aure da Jarmai,
duk yarinyar da jarmai yace Yana so a garin Nan sai ya aureta Koda Bata sonshi Dan kuwa, za'ayi zab'en fidda gwani a filin shad'i kamar yanda Al'adarmu ta fulani take duk akayi shad'i Jarmai keda nasara,
duk mutunen garin sun San da hakan,
Yanzun shekara 7 kenan duk shad'in 'akayi shine ke cinyewa, Kuma a Nan take za'a aura Masa yarinya, dare D'aya Yake farketa batare da yaji tausayintaba sai ya gama biyan buk'atar gareta har na tsawon sati daya snn yake sakota wasu yaran mutuwa sukeyi wasu Kuma sukan kamu da ciwon yoyon fitsari, wasu Kuma Allah ya taimakesu su gyaru,
yarinya bakwai Jarmai ya aura a cikin garin Nan duk hakan yake masu."

Ta share hawayen fuskarta taci gaba da cewa, "yanzun saura wata biyu ayi shad'in mu, zasu Kara tsakaninsa da Audu duk Wanda yacinye shi zan aura, nasan jarmai ke da nasara domin duk mutanen gari sun shaida hakan."

Tin daga ranar da aka saka ranar shad'inmu duk Wanda yagani, ya rabeni da sunan yana sona, ko yana mun magana indai namijine sai Jarmai yayi Masa bugun mutuwa."

Mutum biyu Yana kashewa Akan sun furta suna Sona,
Hakan ya Hana Audu yin magana Dani,
Shi kad'ai Yake magana Dani duk a cikin garin Nan, Dan hakan idan nafito kowa baya son ya ganni bare yayimun magana Domin gudun wahalar Jarmai,
Idan nafito kiwo zai dinga zagayena duk ranar da Mai rabon wahala yasa yayimun magana a ranar sai dai uwarsa ta haifi wani."

Wnn dalilin yasa nadinga fad'a maka Kayi nisa da rayuwata gudun kada ya ganmu a tare yayi maka illah sai gashi kasayeshi da kud'i a lokaci d'aya."

Ta fashe da kuka Mai sauti tace "tayaya zaka taimakeni?"
Kabarni kawai har zuwa lokacin da mutuwata zatazo ta daukeni Dan kuwa bana da gata, iyayena sun zubar Dani a lokacin da nake da buk'atarsu."

Sosai idon Sauban yacika da hawayen tausayinta,
Ashe a duniya akwai Wanda yafishi shiga cikin matsalar rayuwa?"

Saurin goge hawayen fuskarsa yayi Dan gudun kada tagansa,
Yasanya handkichif yashiga share Mata hawayen dake zuba Akan fuskarta ji Yakeyi kamar ya janyota ya rungumeta, shima ya fad'a Mata damuwarsa,
kukanta ya tsaya cak jin hannun D'an birni a kan fuskarta Yana share Mata hawaye,
Sai da ya goge Mata hawayen tas snn ya juyo da ita suka fuskanci juna yace "daga yau kukanki ya k'are, bana son ganin zubar hawayenki."

Safna Kin Amince Dani?"

Ta d'aga kai alamar eh."

Ya Dan saki murmushin gefen Baki, yace "yanzun a wane wuri Audu yake Zama?"

Tace "Audu baya gari yatafi binni sai ana gobe shad'i zai dawo."

Girgiza Kai yayi alamar gamsuwa zaiyi magana Kenan wayarsa ta dau ringing yacirota yayi a gaban Aljihunsa ya duba safwn yagani yaja dogon tsaki ya d'auki wayar tare da karawa a kunnensa yayi shuru batare da yayi maganaba ,
"Muryar safwan yaji Yana fad'in "aboki kana Ina ne nadubaka banganka ba."

"Meyafaru?" Sauban yace."

Tambayar me yafaru tabawa safwan haushi, yace ai Kaine zan cewa meyafaru sabida a yanda naji muryarka baka cikin natsuwarka
Kana ganin la'asar ta gabato kazo muyi Shirin tafiya, kamanta ne har zamfara zamutafi, Wai kana Ina ne hakan?"

"Bansaniba Domin baka aikeniba,
Kajira gani Nan zuwa yanzun.
idan kuma a matse kake kana iya komawa gida,
Dan nasan abinda zaka cemun kenan."

Dariya safwan yasaki, wacce yasa Sauban yayi saurin kashe wayar tare da Jan dogon tsaki,
Mik'ewa tsaye yayi Yana kallon Safna yace "ki waita Addu'a kisanya Allah a gaba domin shine Mai yin komai,
Ki daina ganin laifin mahaifanki domin bakisan dalilin da yasa suka jefar dakeba."
Ki daina yawan kuka saboda kuka yakan haifar da matsaloli a lafiyar D'an Adam."

Snn ki yawaita zagayowa wurin Nan saboda a Ko wanne lokaci zan iya zuwa nemanki a Nan."

Ya juya yayi tafiyarsa har yayi nisa ya juyo ya kalleta yaga shi take kallo tana murmushi, D'an murmusawa yayi yace "kicire tsoro Jarmai a ranki domin babu wani abu da ya Isa yaimaki Kuma insha Allah bazaki aure Shiba,
Ya juya yayi tafiyar sa."

Tafiya yakeyi tunaninta yake tare da juya magagganun da ta fad'a Masa dangane da rayuwar ta,
Tabbas tana buk'atar taimako."

A hakan har ya Isa gidan gonar ba Wanda yaga dawowarsa Kai tsaye d'akinsa yanufa ya fad'a kan gado yayi filo da hannunsa yashiga duniyar tunani,
Ba abinda yake tunani sai ta wacce hanya zaibi domin ya taimaketa,
D'an karamun bakinta yashiga hangowa yanda take juyashi tana Masa magana, tare da manyan idanunta masu zubar da Hawaye,
Tabbas Safna tana da kyau domin ko a turai baitaba wacce tayi kyantaba, wahalace da danti yasaka kyawon nata ya kusan disashewa."

Dogon tsaki yaja ya Kuma mirginawa, tare da janyo filo,
Sai mutum yaji a kan filon,.
D'aga idonsa yayi domin ganin ko waye,.safwan ya gani kwance Yana kallonsa cike da mmki."

Tsaki ya Kuma ja Yana fad'in "meye hakan safwan?"

Safwan yace "meye hakan Sauban da ka kusan Hawa kaina."
Me Yake damunka ne Naga duk ka birgice kashiga duniyar tunani kamar Wanda ya fad'a soyayya a lokaci Daya Ina kafito?."

Jan tsaki Sauban yayi ya Kai Masa harara."

Dariya safwan yasaki tare da sauka daga Kan gadon yace "ko tsaka da tayi tsaki Allah sai da ya tsine mata,
Malam katashi tinda kadawo mu fara Shirin tafiya kasan inada iyali."

Kallonsa Sauban yayi yace "sai gobe zamu bar nan, ba yau ba."
Daga hakan ya mik'e ya bar Masa d'akin, domin Yana da buk'atar Zama yayi dogon tunani Wanda yasan indai safwan Yana a wuri surutunsa bazai barka kayi wani nazariba,



_kai Safwan a rage surutu kayi hakuri Sauban Nima hakan nake fama da nawa safwan din har ciwon Kai Yake sakani_πŸ€¦πŸ»β€β™€


Bin bayansa safwan yayi Yana fad'in "dakata malam Wai meyake damunka ne munzo lafiya k'alau lokaci d'aya duk ka wani birkice."

Kyalesa sauban yayi yaci gaba da tafiyar sa yanufi wurin lambu domin shak'ata, daga yayi tinanin da ya damesa."





_comment dinku Yanayin k'asa sosai idan Naga ba'a comment zan ajiye rubutun na Bari sai Bayan sallah wata k'ila naci gaba?_







*Mrs Ana's Bawa*✍





_Not edited_




*Mrs Ana's Bawa*✍




_comment dinku Yanayin k'asa sosai bakwa comment shiyasa banajin k'arfin gwaiwar yi maku typing kullum, gaskiya idan Baku gyaraba 'DAN SARKI SAUBAN zai koma na kud'i yasin ko a jikinaπŸ€·πŸ»β€β™€_






*Mrs Ana's Bawa*✍




_kome ke faruwa Kuma Sauban_?πŸ€”πŸ§





*Mrs Ana's Bawa*✍



*Mrs Ana's Bawa*✍


*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🀴 *D'AN SARKI SAUBAN*🀴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 19*






Kwance yake akan doguwar kujerar dake zagaye da lambun yana kallon sama, ya d'ora hannunsa Akan goshinsa ya lumshe idonsa da alama,
Tunani yakeyi,
babu abinda Yake Masa gizo a idonsa sai kyakkyawar fuskarta tare da D'an k'aramun bakinta a lokacin da take bud'eshi tare da juyashi tana fad'a Masa damuwarta."

Dogon tsaki yaja ya Kuma juya kwanciya daya tina da yanda idonta yake zubar da hawaye alamar tasaba da kukan,
Kuma Jan wani tsakin yayi ya mik'e zaune tare da dafe Kai."

Kallonsa safwan yayi dake gefensa a zaune akan d'aya kujerar dake kusa dashi Yana latsar laptop d'insa,
Ya d'an dakata da dannar laptop din yana kallon sauban tabbas akwai abinda yake damunsa a rai, shi dai iya saninsa lafiya kalau sukaxo k'auyen nan,
Murmushi yasaki yace "ya dai abokina?"
Tsakin da kakeyi akai akai nameye Allah yasa ba gamo Kayiba?"

Kuma Jan wani tsakin sauban yayi yamike tsaye tare da wurgawa Safwan harara Yace "idan kaga dama katashi mutafi muyi sallah magariba idan kuma sai ka tsaya yimun tambayoyin abinda yake damuna sai kayita zama, yayi gaba abinsa ya bar safwan yana kallonsa."

Mere Baki safwan yayi ya rufe laptop d'insa ya mik'e yabi bayansa Yana fad'in idan tayi wari ai maji."

Banza dashi Sauban yayi yaci gaba da tafiyarsa,
Bayan sun kammala yin sallar magariba dukansu suka fito fadawa sai gaisuwa suke kaiwa a gaban Sauban, d'aga masu hannu kawai yakeyi alamar ya amsa, ya wuce yayi gaba."

D'ak'i yashiga ya fad'a toilet ya yyi wanka yafito ya canza Kaya izuwa jallabiya ruwan k'asa mai d'an gajeren hannu ya Sanya silifas yafito,
A tunaninsa zai ga safwan yabiyo bayansa cikin d'akin,
sai yaga ashe bai biyoshiba, yaji dad'in hakan,
sannu a hankali ya sulale ya fita ta k'ofar baya yanda ba wanda zai ganinsa,
cikin gari ya nufa Kai tsaye batare da kowa ya gansa ba.
Kasancewar duhu ya Fara mamaye garin gashi ba wutar nepa, hakan yasa yayi amfanin da fitilar wayarsa ya kunna yashiga haska gabanshi."

Wurin da suka zauna dazun yanufa, baiyi dibon dare neba, gudun kada wani abin ya cutar dashi kasancewar wurin dajine ba mutane a wurin sai yawan itatuwa."

Zagaye wurin yayitayi yakai yadawo Yana dube dube ko Allah zaisa zai yahangota, shuru ba Alamarta, sai da yaji anfara Kiran sallar Isha'i snn ya hakura ya Koma inda yafito zuciyarsa ba dad'i ya rasa dalilin b'acin ran nasa,
Kai tsaye massalaci yanufa bai ko jira safwan ba,
Sai dai safwan ya tarar dashi zaune a sahun gaba, mamaki ya cika safwan yashiga tambayar kansa meyake damun Sauban ne munzo lafiya Amma lokaci Daya duk ya birgice."

Hakan sukayi sallah suka Koma cikin gidan gonar, har a lokacin Kan sauban sama yake Yana tunanin tare da Jan dogon tsaki, zuciyarsa tana tsananin tausayin Safna jiyakeyi tamkar ya dauketa suyi tafiyarsu ya kaita cikin masarautarsu domin tasamu yanci kamar ko wanne yaro Mai gata."

Dogon tsaki yaja ya juya da karfi Cikin d'aga murya mai sauti Wanda bai San yana da itaba yake fadin natsani zubar hawayenki insha Allah Nine gatanki zanyi maki gata tamkar iyayenki."
Maganar zuci yakeyi bai San tafito fili ba."

Wata irin dariya Mai sauti safwan yasaki Yana kallon sauban Yana fad'in "haba sai yanzun na Gane wnn sauyin naka Ashe kogin soyayya kafad'a, ni ko wacce yarinyace wnn Mai sa'a a duniya,?"
sunkuyawa safwan yayi gefen sauban cike da tsokana yace "ranka ya dad'e, kogin soyayyah ne kafada ba KO tantama sonta kakeyi."

DA sauri sauban ya kallesa ya kuma Jan tsaki yana fad'in " ita wa?"
Wacece kake magana a kanta?"
ya dafe kansa yace "banga dalilin DA yasa nataho DA Kaiba wlh."

Dariya safwan yasaki yana fadin "kafini Sanin KO wacece,
Kada kadamu ko yanzun muna iya bin hanya mukoma gida idan baka iya kwana Kai kad'ai sai da macce, don kuwa nima kaina a takure Zan kwanta."

Juyawa yayi ya wurgawa Safwan harara yace "kadauka kowa irin ka ne."

Dariya safwan ya saki yace "har gwarani Ina a mayar da abinda ke raina bana barinshi a rai har yafara sanyani sabbatu maganar zuci tafito fili."

Gyaleshi Sauban yayi ya rufe Idonsa tamkar Wanda Yake bacci shi kad'ai yasan yanda yakejin a ransa akan tausayin Safna."

Hakan suka kwana Sauban bai samu wani baccin kirkiba da zarar ya motsa safna yake gani a idonsa tana kukan nan nata,
tunani kawai yakeyi hanyoyin da zaibi domin ganin ya taimaketa."

dakyar yasamu safiya tawaye masa,Bayan sunyi sallah suka shiga Shirin barin garin zuwa masarautar zamfara,
Sosai yayiwa masu kula da gidan gonar Alheri, hakan suka tafi wurin Mai gari sukayi masa sallama shima Sauban yayi Masa Alheri Mai gari sai godiya yakeyi Yana Jin dad'i snn suka fito."

Tunani yake a Ina zai ganta gashi bai San gidan su ba,
Waigawa yayi ya Kalli safwan dake gefensa yana waya, ya wurga masa harara cike DA jin haushi tare da jan dogon tsaki, Wanda sai da safwan ya Dan juyo ya kallesa yayi masa alama DA hannu meya faru?"
Kauda idonsa gefe sauban yayi yaci gaba da kallon gefensa da bayansa yana tinanin ta Ina zata fito."

Karo sukaci DA wani d'an fillo yana kiwon shanu, sauban ya nufi wurinsa yana fadin "Assalamu Alaikum malam Dan. Allah tambaya nakeyi.

K'asa d'an fillo ya zube yana kallon yarima yana fadin ranka ya Dad'e da kanka Allah yasa nasani."

Hannu sauban ya mik'a masa alamar yatashi tsaye,
AI kowa cikin sauri d'an fillo ya mik'e tsaye."

Hannu yarima a cikin Aljihun wandonsa , yake kallon d'an fillo cikin maganarsa daki daki yace "kasan gidansu Safna?"

Safna ranka ya dad'e?" D'an fillo ya jeho masa wnn tambayar."

D'aga Kai sauban yayi alamar eh ita nake nufi."

Kallo safwan yake binshi cike DA mamaki DA Al'ahabi tare da ayar tambaya a bakinsa."

D'an fillo yace "duk garin nan safna d'ayace budurwa, wata fara marar jiki kyakkyawa, hannu sauban ya daga masa ya furta ita nake nufi Ina ne gidansu."

Cike DA mamaki d'an fillo ya shiga kwatanta masa gidan,
Girgiza Kai sauban yayi alamar ya gane, ya Ciro kudi a Cikin Aljihu ya mikawa d'an fillo, hannu na rawa ya amsa yana zuba godiya"

Sauban bai tanka masaba yajuya yanufi inda yayi masa kwatancen,
Safwan yana biye dashi cike DA mamaki ba damar yayi magana yasan halin sauban sarai DA zarar yayi magana bazai tafi dashiba, idan kuma ya dage akan sai yatafi dashi yafison yafasa ai watar da abinda yake da Niya, Wanda bazai so hakan ba yafiso yabishi a hakan har yaga yarinyar da tafara yasaka sauban sabbatu."

Sauban a gaba safwan yana biye dashi a baya, sai shanye kwana sukeyi suna bullewa wata, suna karya wata kwana kenan wanda zata sadasu da da gidansu safna kamar yanda d'an fillo yayi masu kwatance,
sai ganin mutum sukayi anjefo daga cikin gida Wanda sauban yake tunanin nan ne gidansu safna
Safna ce kwance a k'asa tana rungume da fantekar d'ibar ruwa, matar DA tajehota waje sai kunfar baki takeyi tana d'aga murya daga cikin zauren gidan tana fad'in "munafuka mai bak'in jini duk sa'arki sunyi aure sunbarki, to kisani bazakici abinci a gidan nan ba, har sai kin d'ebo mun ruwa, tinda ba ubanki yake kawo abincin ba tsinanniya wacce aka tsinta a cikin bola." Wayasani ba ko cikin shege uwarki tayi ta zubar dake a bola, Aljana Kawai."

Durkusawa sauban yayi ya rok'ota ya mikar DA ita tsaye cike da tausayi, safna tana ganin sauban ta kara fashewa da kuka, yayi saurin runtse idonsa zuciyarsa tana k'una a rayuwarsa ya tsani zubar hawayenta."

Ya juya ya kalli inno dake tsaye a cikin zaure sai zarar ido takeyi ganin yarima,
Murmushi ya Dan Saki ya tako zuwa k'ofar zauren gidan ya d'an sinkuya yace ' Ina kwana Inna."

Zubewa k'asa inno tayi tana fadin ranka ya dade DA kanka a kofar gidan nan barka da zuwa bara nakira maka jauro, ta zuba cikin gida DA gudu."

Yacika DA mamaki dama jauro yana cikin gidan akeyiwa safna wnn cin mutumcin to meye amfaninsa tinda matarsa tafi karfinsa,
Dogon tsaki yaja ya juya ya kalli safna wacce take goge jikinta tana sharar hawayen fuskarta safwan yana,mik'a Mata fantekar d'ibar ruwanta."

Dogon tsaki yaja ya kuma juyar da fuskarsa kofar gidan, Wanda yayi dai dai da fitowar jauro"








*ABIN MAMAKI BAYA K'AREWA SAI DA NA TSAYAR DA RUBUTA WNN LITTAFIN AKAN RASHIN COMMENT DINKU, SNN NADINGA GANIN ANABI PRV ANA BANI HKRI WASUMA BANYI TINANIN SUNA KARANTAWA BA, TO KUBARI KUJI KO YANZUN IDAN BANGA RUWAN COMMENT BA AJIYE RUBATA SHI ZANYI SABODA INA DA ABINYI BAZAI YIWO NA B'ATA LOKACINA NAYI MAKU TYPING SABODA JIN DADINKU COMMENT YAYI MAKU WAHALAR YI, ALLAH BANDA NARIGA NAYI ALK'AWARIN BAZAN SAYAR DA WNN LABARIN BA DA TINI NA MAYAR DASHI NA KUDI KO A JIKINA*πŸ€·πŸ»β€β™€







[9/3, 6:26 AM] Hayat: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*✍



🀴 *D'AN SARKI SAUBAN*🀴



Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*Page 24*




*SHAD'I*
Kamar yanda kowa yasan yanda Al'adar fulani take musamman fulanin daji masu rok'o da Al'ada, wad'anda suka d'auki Al'ada da mahimmaci tamkar Addini."

*FAGEN SHAD'I*

Jarmai ne tsaye a tsakiyar fili rik'e da zungureriyar bulalarsa sai zarar ido yakeyi yana d'aga kwandaπŸ’ͺ🏼,
yaransa sai zuba masa kirari sukeyi suna k'Ara masa kwarin gwaiwa suna fad'in "sai kai oga mijin Safna kaine mai nasara domin nasara takace,

Gaban JARMAI a Audu ne a tsaye shima rik'e da bulalarsa fuskarsa alamun wasa a tare da shi, sai hura hanci yakeyiπŸ‘ƒπŸΌ
Dukansu ba riga a jikinsu jiran umurni kawai sukeyi sufara dukan junansu."

Gaba d'aya jama'ar gari maza da Mata sun hallara a wurin,
sun zagaye fagen wasar suna kallo suna jira a fara,
A can gefe d'aya akan kujera maigari ne zaune tare da hadimansa suna kallon yanda shad'in zai kasance."

Can d'aya gefen kuma Safna ce tsaye kusa da Baba sai kuka takeyi idanunta sunyi jajir sun kumbura Baba sai lallashinta yakeyi yana fad'in ta daina kuka Addu'a ya kamata tayiwa Audu Allah yabashi sanara ya cinye."

D'aga kai tayi alamar "to ta daina kukan,
illah taci gaba da sharar hawayen domin duk yanda takeso taga kukan ya tsaya ta kasa saboda kuka shi keyin kan sa ba ita keyin saba,
waige Waige kawai takeyi ta inda Sauban zaifito mata domin taji a jikinta zaizo gareta."

A can ta hangoshi tafe ya tunkaro wurin cike da k'asaita da isa mai cike da tsantsar mulki, fuskan nan tashi sai Annuri take fitarwa,
safwan yana gefensa, fadawa guda biyu suna bayansa sun take masa baya,
wani irin murmushi tasaki Wanda batasan tanayin irinsa ba,
yunkurin zuwa wurinsa tayi cike da farin ciki Baba yayi saurin tareta yana mata gargad'in kada ta karya Al'ada."

Ido yadawo kansa kowa cike da mamakin zuwan nasa yakeyi,
Murmushi maigari yasaki yana kallonsa domin ganinsa a dai dai wnn lokacin ba k'aramun mamaki yabashi ba."

Maigari yabada umurnin akawowa yarima abin zama,
Cikin minti uku aka d'ora kujeru sauban da safwan suka zauna fadawa suka zagayesu a baya."

Gaisuwa maigari ya kai wurin yarima,
yarima yana fara'a suka gaisa."
Tare da tambayarsa yaya maimartaba?"

Lafiya k'alau sauban yace,
maigari yana murmushi yacewa sauban "yau Allah ya kawoka a dai dai lokacin da muke gudanar da Al'adarmu ta shad'i Allah yasa zata k'ayatar dakai, duk da dai kaima bafulatanine amma na birni."
Murmushi sauban yasaki tare da jinjina Kai."
snn suka maida hankalinsu wurin shad'in a dai dai lokacin da ake neman maigari yayi magana a fagen wasa domin yayi gargad'i tare sanarwa tare da yin tini akan abinda ya gabata akan shad'i kodan ganin yarima ya halarci wurin ."

A can ya hangota tsaye kusa da baba tana kallonsa tana murmushin farin ciki hawaye suna zuba a idonta."

Shima murmushi ya Sakar mata,
Yayi mata alamar ta share wayenta ta daina kuka."
Ai kuwa cikin sauri ta share hawayenta tana sakar masa murmushi."

Ido Safwan yake binsu yana kallo cike da mamaki k'iri k'iri ga gaskiya ta bayya sauban son Safna yakeyi Safna son sauban takeyi amma saboda taurin kai irin na Sauban baitab'a yarda da Sonta yakeba har b'acin rai yake nunawa idan akace sonta yake, sai yace shi tausayinta yakeyi a daina cewa yana sonta saboda shi baya da lokacin wata soyayya can ta shirme bai masan abinda an soba kuma baya fatan yasani saboda baya da lokacin shi son."
Safwan ya Rik'e baki yana mamaki to yanzun kuma meya kawosu nan?"

Maigari yasoma bayani kamar hakan "kamar yanda kuka sani a duk bayan shekara d'aya mukan gudanar da Al'adarmu ta fulani wato shad'in fidda gwani,
Wanda Al'adace wacce muka taso muka tarar iyayemun da kakanninmu sunayi kuma suka d'oramu akai,
Indai Kai bafulata nine Wanda kake rayuwa a cikin wnn k'auyen dama wajen nan in har zaka mallaki macce, komai kudinka KO Mai mulkinka saikayi shad'i tare da abokan kashewar ka,
Anan zaka nuna bajintarka da k'arfinka snn k'arfinka ya baka macce."

Dokokin shad'i sune bamason hayaniya tayi yawa,
Snn duk Wanda aka daka har zafin duka yasakashi ya fad'i k'asa, kamar yanda kuka sani yafad'i a fagen shad'i,
Wanda kuma bai fad'i ba shine mijin Safna banason fad'a ko wani tashin hankali a nan."

Snn yaba da umurnin a Fara wasa."

Anan take jarmai da Audu suka shiga dukan junansu da bulala ba girma ba arziki,
Ko wanne k'ok'ari yakeyi yakai d'an uwansa k'asa."

Sosai Audu ya daku ya jigata jikinsa da fuskarsa suka fara fitar da jini, amma yaki ya fad'i sai buga in buga sukeyi da jarmai Wanda jikinsa kawai ne yayi kwancen bulala, jini bai fitaba,
Kuka safna ta fashe dashi a lokacin da taga jarmai yana neman cin galaba akan Audu domin jini har ya fara wankewa Audu fuska amma har yanzun bai fad'i k'asaba, Wanda da zarar ya fad'i shikenan jarmai ya ci galaba a kansa."
hakan Audu yake dukan jarmai
jarmai yake dukan Audu, a can jarmai yasami sa'ar Audu ya doka masa bulala a tsakiyar kai, anan take Audu yasaki wata irin k'ara ya fad'i k'asa a some."

Da gudu Safna tanufi wurinsa tana kuka tana jijjagashi tana fad'in katashi Audu katashi meyasa kabari Azzalumi yaci galaba akanka?" kana gani za'a auramun azzalumi,
ta d'aga murya cikin sauti sai da gaba d'aya wurin ya amsa tace Audu katashi ."

Dariya Jarmai yasaki cike da jin dad'in samun nasara,
Hakan masu goyon bayansa suna murna tare da ihu suka d'aukeshi suka d'agashi sama suna juyashi,
Yashiga yiwa kansa kirari kamar hakan "saini jarmai angon Safna mainasara, sai ni Jarmai d'an maigari ba Wanda ya isa ya tab'ani ya zauna lafiya."

Snn ya sauka daga d'aukar da aka suka masa,
Yanufi wurin safna dake durk'ushe a gefen Audu tana jijjigashi tana kuka tana fad'in tashi Audu karka mutu,
hannu jarmai yasaka ya ruk'o hannunta ya mik'ar da ita tsaye ya Janyeta a wurin,
tana tirjewa tana dukan hannunsa a kan yasaketa yak'i yasaketa sai da yafito da ita tsakiyar fili ya d'aga hannunta sama yana fad'in saini jarmai na Safna,
Safna ta wace idan akwai wani Wanda yakeji da kansa yafito mukara idan uwarsa bata haifi wani ba."

Safna tana kuka idonta akan sauban, Wanda ya runtse ido jikinsa sai rawa yakeyi alamar ransa a b'ace yake."

Cikin zafin nama sauban yamik'e tsaye tare da cire rigar jikinsa sai ciccira yana neman yashiga filin shad'in,
Safwan ya rik'eshi hakan fadawa sukayo kansa suka rik'eshi suna fad'in ranka ya dad'e meye had'inka da shiga filin shad'i?"
bazaka iyaba, ka rufamana asiri bamaso mujewa maimartaba da mummunan labari."

Hannu biyu yasaka ya turesu gefe d'aya dukansu sai da suka fad'i k'asa har safwan,

jikinsa sai rawa yakeyi yanufi wurin jarmai ya fisge hannun safna daga hannunshi ya turata gefe d'aya snn ya duk'a ya d'auki bulalar da Audu ya jifar k'asa
Yanuna Jarmai yana fad'in,
Kana fad'in sunanka Mai nasara amma yau kasanyawa ranka daga yanzun sunanka marar nasara,
domin bakomai akeyin nasara akansaba,
har yanzun Safna bataka bace Safna ta mai raboce tsakanin ni da kai."

Da gudu safna ta nufo wurin yarima tana kuka takai durkushe a gabansa tana fad'in banaso na rasaka, domin bazaka iya da wnn Azzaluminba kayi tafiyarka kawai."

janyeta yayi a gabansa domin ya tsani ganin kukan nan nata a idanunta, ransa ya kuma b'aci jijiyoyin kansa duk suka firfito jikinsa sai rawa yakeyi yana kallon jarmai."

Dariya Jarmai yasaki yana kallon yarima yace "d'an birni zaka iya karawa dani?"

Bai iyar da rufe bakinsaba cikin zafin rai Sauban ya sakar masa bulala a tsakiyar gadon bayansa,

Please Login or Register in order to submit comment