Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koya muku tarbiya ba!" Duka ta sake mishi a qirji "ka sake ni Arab..!” ta karasa kaman Zatayi kuka


d'aki na shige tare da rufo kofa inna tsaki bansan Randa zasuyi hankali ba,


Kichin na shiga na fara kokarin masa Girki domin yau d'akina yake shima zai shigo Yau zanji inma Zaina ce ta hanashi kwanan d'akina zan sani.


inna gamawa na shiga wanka karfe Tara kuwa sai gashi Saukowa nayi daga Gadon Dinnig table muka nufa abinci na zuba mishi ya fara ci can har yayi rabi yace. “Ke bara kici bane?” Wani i'rin kallo na watsa mishi “Ka damu da naci ne?” na Wurga mishi tambayar tare da tafiya da hannuna cikin Wandonshi da sauri ya mike.


“Kinga banson fitina fa.." cikin B'acin rai Nima na shiga gaya masa magana “Har na kaika? Rago kawai wadda besan yadda zai tafiyar da matarshi ta samu nutsuwa ba, to Wallahi zoka barmin d'aki domin bazai Yuwu kazo kana Cina ka fita ba, uwar me suka fini dashi, da zaka kwana Gurinsu ni bazaka Kwana gurina ba? Kaga nafa Gaji da i'rin halinka da matanka wallahi zoka fita banson sake ganinka Jelarta.." Ta fad'a a hasale (Allah sarki Uncle Arab ne jelar-Zaina)


“To kiyi hakuri.."


"Hakurin Banza Hakurin Wofi Wallahi ka fita min a d'aki kafin na rotsa kanka da kofin Nan!" Ta fad'a tana d'auko kofin silver data had'a mishi kunun Aya da sauri yace “Allah ya wuci zuciyarki Haske na” kofa ta nuna mishi da sauri ya fita.


****


Zaune tayi tare da Sunkuyar da kanta tana jin yadda yake koro mata bayanai "kina kula kuwa da kalban ?” Gyad'a masa kai tayi, Wani i'rin mahaucin dariya Boka yasa “Shegiya la'ananniya kina ina komai ya wargaje gashi tana shirin sauke ƙwanta..Hahh!..Hahhh!..hahhhh!!!”


Nuna mata ƙwariya yayi Nan jidda ta bayyana tana kwance saman gado daga i'ta sai shimi da wando iya Gwiwa bakinta na motsi cikinta ya nunawa mata “Kinyi Sakaci sosai gashi har aiki da aka masa ya kwance..." Wani i'rin ihu tasa “na shiga uku na lalace Boka ka temaka min a shafe cikin banso Naga Jinin Hauwa'u a doron kasa, banso Arab ya sake dasa ƙwansa jikin wata macen Kamar yadda na tsayar Dana sauran Dan Allah ka kwaso abinda ke jikinta Ka temake Uban Arna mugu nasanka babu d'igon imani Ka gwada Mata halinka wayyo ka temake ni ko zanyi yawo tsirara se wannan shegiyar tabar Min miji domin bai min Son da yake mata ba!" Ta fad'a tare da Kai k'anta saka a gabanshi tana mishi sujjada (wa'iyazu billahi Allah ka shiryamu ubangiji ka dad'e Kare zukatanmu).


Kuka take tana fad'in “Nawa zan biyaka ka temake ni ka toshe mahaifarta a cire cikin a tura mata cutan da zai Zama ajalinta" hannunshi yakai Yana kokarin shafo cikin jikin Jiddah wani i'rin haske ya d'auketa da sauri ya maida hannunshi baya tare da Yar farwa. "Kaihhh! Yarinyar Nada ibada Yanzun Haka ubangijinta take Kira kingan da Hannuna yayi zafi Gaskiya wannan aikin babba ne..." (Ji la'ananne wai ubangijinta take kia)


Sake zubewa tayi gabanshi “Ka tema kamin Boka ko nawa ne zan biya"


"D'auka kije ki saka mata a ruwa inhar Tasha da zaran ya kusanceta zata ringa jin zafi gabanta zai bushe shima bazai ringa samun Gamsuwa da i'ta ba, maza juye kud'i za'a aika mata da aljanin da zai hanasu zaman lafiya!" Jiki na rawa ta d'auki ƙullin maganin Kud'in jakanta ta juye mishi kafin ta shiga mishi Godiya da baya ta fita a bukkar...




_Comments Comments please in ban gani ba zan je Offline insha kar Kuma ku nime ni_






Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*


Farin Jini Writer's Association


PAGE21.


Zauna nake Amma Zuciyata na tsinkewa Haka kurun bansan Maiyasa ba, jefi, jefi nake kallon wayata tunda na Koreshi yai zuciya Bai sake waiwayata ba Yau kwana biyar Gashi banjin ƙwarin jikina sosai na kasa Gane meke damuna. Tsaki ta kuma yi a karo na ba'adadi, sannan ta mike bakinta d'auke da Sunan Allah Kichin ta nufa frizer ta bud'e tare da Kwaso Kayan marmari Kunnun Tsamiyan da tayi tun safe ta d'uma sannan ta nufo d'akin tare da Kulle kofarta.
Tana zama taji ana Kwankwasa kofar “Yah ilahi Waye?”
A ƙufule yace. “Banson iskanci Zoki bud'e min Kofa!" Bud'ewa tayi zai kamota ta kauce mishi shigowa d'akin yayi sannan ta Rufe Kofar, bata kulashi ba, ta zauna tare da D'aukar Kofin zata kai baki ya rik'e hannunta yana kallonta,


Taki yarda ta kalleshi Kanta na kasa hawaye na sauka saman fuskantar Harga Allah ta gaji da Gidan Arab maganarsa ne ya katse ta. “Kefa kika koreni..." d'agowa tayi a zafafe zata sauke mishi kwandon Bala'i sai ta ƙyale ,sanin Mahimmanci da darajar sa. Mijinta ne, be kamata ta ringa d'aga masa Murya ba, Jan hanci tayi sannan ta fara magana tare da zame Hannunta. “Kana i'ya sauke musu Haƙƙin su dake wiyanka Amma ni ka kasa, Girki na kake d'auka ka, Kai musu, ban tab'a Rik'e ka Ran nasu ba , Amma dake ni Bora ce Banida martaba da Matsayi matar Cushe ce Ni, ban i'sa ka zauna Tare da ni ba, Yaushe rabon da ka siya min sabulun wanka ko omon wanki? Kayan Abinci na ya kare, wata Uku kenan, ni nake ciyar da kai na, kana shiga kichin ko wacce da Band'akinta. ka duba abinda Bata dashi, ka zuba Mata, amma dake ni banda d'iyoyi (Yara da yawa) da kai shine ka banzatar da Lamarina Kaji tsoron Allah Yallaɓai! Ka Gyara Gidanka Ka tsaya da kafafunka , bawai ka zauna ana baka Oda ba, Banida Lafiya baka Shigomin Bare ka duba ya Nake. ban fita aiki duk da ka sani Amma baka tambayi dalili ba, da Zaina ce ko Fure Jiki na b'ari Zaka d'auki Mota..”


Jikinshi ya bala'in sanyi kalamanta ya tab'a shi Gaskiya take fad'a mishi duk anyi Haka shi akaran kanshi yasan Bai kyauta Mata ba, tana da kawaici Da d'auke kai, Hannunta ya kama jikinshi na rawa “Dan Allah kiyi hakuri” murmushin da yafi kuka ciwon tayi “Wacece ni da Mijina zai bani Hakuri naki Hakura? Hmm ya Wuce ai.." da sauri yace.


“Dan Allah" ya fad'a Yana langwab'ar da Kansa, murmushin Yak'e ta sakar masa "Bakomai" d'aukan Kofin yayi tare da kaiwa bakinta Karb'a tayi daga hannunsa Yana kallonta tana Sha, har ta kammala komai. zata kwashe kayan ya dakatar da i'ta tare da Karb'a yakai kichin , laptop d'inta ta kunna ta fara Aiki shigowa yayi tare da zama saman Gadon.


Share shi tayi duk da tana sane dashi “Kizo mu kwanta”


"Hmmm aiki..."


“Ki abinda nace!”


Kashewa tayi tare da mikewa kashe hasken d'akin tayi tare da hayewa Gadon , abinda take tsammani shi ya kokarin Yi, Bata hanashi ba, Haka tabar shi ya samu nutsuwar da yake bukata Amma da fad'a suka rabu domin ji tayi bata jin dad'in mu'amular da kyar , ya ƙyaleta Yana tsaki “Meke damunki? Ba yadda nake jinki bane Babu danshi ko kad'an a jikin ki, A bushe kike ba ‘Dand'ano.."


“Kaga Dakata! Base ka zageni ba, Zaka iya tafiya Gurin Zuma! K'orama da danshi!" ta karasa maganar tare da Nufar band'aki koda ta fito Bata sameshi ba Bata damu ba, ta Rufe Kofarta tare da tofe d'akinta da addu'a tayi kwanciyarta. Amma ta kasa barci Tana tunanin Yanayinta sharewa tayi kawai.
Washe Gari, koda tayi sallah kwanciyarta tayi sai 11:30Am ta shirya d'akin Fitowa tayi taga kaya jibge A falonta tsaki tayi tare da Nufar Babban Falon inda take jin Hayaniyar Su, tsayawa tayi tare da Rik'e K’ugunta “ Yallaɓai" Be kulata Ba, ya cigaba da Hirar da Suke “inna maka magana Kayi Banza dani!” Juyowa yayi rai a had'e “Wai ke wacce i'rin Dabba ce Me sa kike Haka ya zakizo ki tsaya tsakiyar Kan mutane kina musu ihu Jakar innace Ke!?" Cewar Fure Tana hararan Jiddah “Akwai Dabba jaka Bayan ki? Ke har kina da bakin fad'an magana ban kasa, dake ba, domin Baki i'sa nayi dake ba, Banza shashasha Da Mijina nake magana.." Murmushi Zaina tayi tana jifan Cikin jikinta da wani i'rin shu'umin Kallo, bata ce komai ba, ta Mike tare da Kama hannunshi zasu fita Jiddah Tasha gabansu “Dalla inna maka magana ka mike zagwai-zagwai zaka bita ka zama bindinta ne? Da take Gaba. Kana baya? Kaga nafa gaji, Kaman yadda kake zuba musu cikin kichin Nima kaje ka kwashe ka zuba min!" Wani i'rin duka Zaina ta Kai mata a ciki, K'asa tayi tare da saki kara Kaman ranta zai fita ta kasa motsin Kirki domin naushin Ya tab'a ta sosai ,


Jin ihu Kuma muryan Jiddah ne yasa Jumana Fitowa da sauri cikin ihu tace “Wayyo mumy zasu kashe Aunti Amariya Bata motsi" Kaman wadda aka farkar dashi daga barci ya farka Cikin tashin hankali ya Nufi inda take “Wallahi kana tab'a ta, sai de ka sake ni, Har wannan 'Yar iskan ta isa ta fad'a min magana na kyaleta? Wacece i'ta" Kasa karasawa yayi ya Koma yai tsaye Nafisa data karaso Gurin ta saki wani i'rin murmushi me d'auke da Hawaye Bak'in Ciki. “Wallahi bi'izinin lahi ta'awa wata rana zakiyi kuka Ranan nadama Mara amfani na zuwar muku, Muazzan Gaka Ga ZainaB insha Allahu zaka girbi Abinda ka shuga"


Sunkuyawa tayi tare da tab'a Saitin zuciyarta wani i'rin kuka tasa na takaicin Halin Mijinta tunda Ya Auri Zaina komai ya tab'arb'are mishi “akwai ranan da zakayi kuka kace Dana sani! da banyi abinda nayi ba, Kasan bazaka i'ya ruk'on marainiya ba, ka d'aukota? Maisa baka sauwake Mata ba! Kuna Cutar da i'ta Muazzan Kuna musguna mata tayi hakuri tayi hakuri tsawon shekaru mai yasa! Dan Allah ka fita Rayuwar 'Yar nan ko zata samu sukunin zuciya da nutsuwar Ruhi, haba! Ku ringa tuna Gobenku Mana Ke Fure baki d'auki darasi ba, har Yau kin kasa bincik'o me yayi sanadiyar Mutuwar 'Yarki, me kike Nima aDuniya ne? meyasa kike barin Zuciya tana rud'anki? Mai yasa idanunkin ya rufe da Kishin Banza! Arab ba namijin da za'ama haka bane! Ki Gyara dan Allah ki Gyara lahirarki kubar Yarinya ta Huta..


Zainab 'Ya'ya mata uku gareki wadda ko Yanzun za'a aurar dasu su zauna baki tunanin hakan ya kasance dasu ya zakiji a matsayin ki, na Uwa, 'Yarki na fuskantar Matsalar kishiya ,ya zakiji idan Miji ya musguna Mata! Wannan wacce i'rin jarabankishi hauka ne? Allah ka sauko da zuciyoyinsu , Rabbi ka yafe mana, Allah mun tuba Allah kasa su Farga daga rakiyan shaid'an..." Hararanta Fure tayi “Gaki Nan babbar shaid'aniya" tace tare da Barin Gurin, wani i'rin Dariya Zaina tayi. "Da Raina! 'Ya'yana bazasu fiskanci Halin rayuwa ba, inna da Kud'in da zan juye a juyamin? Kin fahimta, namiji bai i'sa Yama 'yata Wulak'anci ko kallon banza ba,
Babu macen da zata shiga rayuwata na barta batare da na, nuna mata iyakarta ba, Nafisa na barki ne badon kinfi karfi na ba, Amma inna nan Dake zaki bar min Gida domin Gidan Muazzan dani kad'ai ya dace ba ku ba" tana kawowa Nan a zancenta taja hannunshi suka tafi,


Da taimakon Jumana suka fito da Jiddah motarta ta sakata tare da komawa ta kulle d'akinta dana Jiddah asibinta ta nufa da i'ta da kanta ta shiga duba lafiyarta Hankalinta yayi bala'in tashi Ganin i'rin Bugun da akayiwa cikin jikinta har yana kokarin zubewa ga jininta da yayi Mugun hawa , a nutse ta Gyara zaman cikin , tana maijin Farin ciki, Sai dai Jiddah kan sai yadda Hali yayi domin, Tayi dogon suma, Kwananta Biyar Ta farka bakinta d'auke da salati, Jumanace ke Zaune da i'ta sauri tace. "Sannu Aunti amariya” Murmushi ta sakar mata “Kwana na nawa kwance?" Jumana tace. “Wini shida kenan”


Tambayar data jefa mata yasa ta kallonta “Abbanku yazo?" Batace mata komai ba “Kinyi shuru"


“Hmmm" kawai Jumana tace mata tare da fita a d'akin Ofishin Nafisa taje suka tawo tare "Barka da arziki" Sunkuyar da kai tayi


“Meke damunki Yanzun?" Ya tsina fuska tayi “inna jin marana yamin nauyi” Nafisa tace “Ya Danganta da cikin Jikinki ne ki kula sosai domin an fara kawo Hari" ta fad'a tana cire Karin Ruwan da sauri jidda ta kalleta “Maman Jamil Ciki Kuma?" Nafisa tace. "insha Allahu kuwa wata hud'u kenan" wani i'rin hawayen dad'ine Ya sauko fiskanta “Alhamdulillahi Allah kai mai kub'utarwa ne Ya Arrahimu yah maliku ya ƙuddusu Yah hayyu, Yah Kayyumu, Yah Allah kaman yadda ka kub'utar dani Allah ka kub'utar da abinda ke cikina lafiya Allah ka saukaka Al'amura na ubangiji ka karamin Hakuri juriya da Dangana.." wani i'rin tausayinta ne ke sake samun matsunguni cikin zuciyar Nafisa, “Ameen” Nafisa tace sannan ta riketa a hankali take tafiya har suka shiga Bayin wanka da wanke baki tayi sannan ta d'auro Alwala A zaune ta ringa jiro sallolin dake k'anta tanayi tana Hutawa , Bai zoba har ta cika kwana Goma Nafisa ta biya komai ta kula da lafiyarta sosai bata da abinda zata biya matar domin ta sota , tamkar d'iyar cikinta haka ta d'auketa Bata rik'eta kishiya ba, randa ta cika kwana Goma Sha biyu suka dawo Gida, Jumana ce ta Gyara mata shashinta Haka ta cigaba da Mika Al'amuranta ga Allah Bata wasa da Sallah sadaka, da taimakon Gajiyayyu Har ta shafe wata Uku Gidan bai leko inda take ba, Abin na damunta Amma ta barwa ranta ta mayar da komai ba komai ba, tana masa Girki kuma Yana ci , Ganinsa ne de batayi,


Seda cikinta ya shiga wata Bakwai Ran Nan da dare inna Zaune saman kujera domin Cikin kwanakin nan inna fama da yawan fad'uwan gaba da ciwon kai Gefe d'aya da ya sarƙafeni Hannuna rik'e da Hisnul-Muslim inna duba adduo'i kaman wani munafiki Haka ya shigo kallon tsaf na masa duk ya susuce Hasken ma ya dushe D'auke kanta tayi daga kallonsa Bai lura da cikin Jikinki, dayafara turowa ba ya zauna kusa da i'ta tare da d'aura kanshi saman kafad'arta.


"Yallaɓai sai yau aka sako min kai kenan?” ta fad'a tana shafa Kanshi daya Tara Gashi duk da shi ba ma'abocin tarawa bane, mamaki ne ya kamata sosai.. d'agowa yayi cikin Sanyin murya yace “Dan Allah dan Annabi kiyi hakuri"


“Ni? Me kamin da kake bani Hakuri?" Ta fad'a tana sakin murmushi tare da Jan Karan hancinsa. Wani i'rin sanyi jikinsa yayi Allah ne ya bashi Jiddah Amatsayin mata i'rinta ne matan da ake musu lakabi da mar'atu-Swahliha Yana kallonta ta d'auko abinda yake aske Gashi ta joya tare da ajiye kujerar Tsunguno Zama tayi ta aske mishi Tass tare da Gyara mishi fuska kallon kansa yayi a madubi tare da kallonta Kaman yayi kuka Haka yake ji kawaicinta yayi yawa.


Komawa kujera tayi ta zauna tana sauke Numfashi tare da Rik'e Bayanta domin ya rik'e, biyota yayi tare da Zame Himar d'in da tun d'azun take sanye dashi Mutuwar Zaune yayi lokacin da idanunsa ya sauka , bisa cikinta “Hasbunallahu Yanzun kina da ciki shine ko ki sanar mu HAUWA?" Murmushi ta sakar masa “Tunda idanunka sun gane maka ai shike Nan."


Cikin wani i'rin Jin dad'i ya d'aura hannunshi saman cikinta Yana shafawa "Ubangiji ya raba lafiya Allah yasa ki Haifa min 'Yan biyu kaman yadda Halima ta Haifa" shekara d'aya kenan da haihuwar Halimatu ta haifi Aalik da Aaleen. Murmushi tayi Sannan ta kwanta cikin Kujera d'agota yayi "a a taso Yunwa nake ji wallahi..” dakyar ta Mike tana rik'e Baya a Haka cikin Daren ta d'aura Girki bata fito ba sai da ta kammala sannan ta had'a mishi saman tire a hankali take takowa har ta shigo d'akin a saman darduman carpet ta ajiye mishi Saukowa yai tare da Zama, Zuba mishi tayi zata mike yace "Zauna muci.." kawad da kanta tayi domin bata K'aunar Kallon shi bata ce mishi komai ba ta Mike ta Nufi Band'aki wanka tayi da ruwan sanyi tana zubawa jikinta tana sauke numfashi domin zafi take ji sosai tana Fitowa ta kunna Fankan dake fuskantar Gadonta ƙure gudunshi tayi sosai d'aure da zani ta kwanta tana jin yadda cikinta ke Juyawa.


Yana Kammalawa ya kwashe kayan hayewa yayi saman Gadon har Ga Allah Bata so ya tab'a jikinta daurewa kawai tayi harya nutse ga gajiyar da take fama dashi rik'e shi tayi sosai “Wai Allah bayana!" A hankali yake bi da i'ta “Banji yadda nake so Kiyi wani Abu Mana Wallahi ƙam kike Babu ruwa a Jikinki.." lumshe i'do tayi hawaye na sauka mata har yanzun Yana jikinta Amma magana yake fad'a mata tana jinshi ya gama fad'anshi "Baki da dad'i Wallahi nifa na gaji bazan iya wannan rayuwar ba, ki binciki Jikin ki" sauka yayi a jikinta tare da mirginawa Gefe, kukan zuci take, i'ta lokacin da yake da lalularsa bata tab'a fad'a mishi wani magana ba, sai ma, damuwa data daurawa kanta, Ɗan Adam kenan mai wiyar Sha'ani tana ta kokarin mikewa domin taje ta tsarkake jikinta ta kasa i'ta bata i'ya kwanciya da najasa ba. "Temaka min na mike bayana ya rik'e.." tsaki yaja tare da Juyawa Yana Gyara kwanciyarshi "Magana nake maka Yallaɓai.."


"Dalla malama ki ƙyale ni haba! nagaji bazan i'ya wani temaka miki ba, aikin me kikayi da bayanki yake ciwo in Zaki tashi ma ki tashi" shuru tayi tare da ƙurawa Bayanshi i'do i'ta bata son fad'a da masifa, Sunan Allah kawai take ambata domin zuciyarta zafi yake mata muddin tace Zatayi magana inna ga saiya kusan kifa mata mari, ranta ya Bala'i b'aci tsaki taja da karfi ta mike Zaune haureta yayi da kafa tare da mikewa Zaune "Ke har kin isa kimin tsaki Yar iska kawai" wani i'rin Kallo take jifanshi dashi mai cik'e da ma'anoni Da sauri ta Mike ta Nufi Band'aki jingina tayi da kofar ta fasa wani i'rin kuka mai tab'a zuciya Ya Zatayi ne? Wannan wacce i'rin jarabawa ce, wani i'rin rayuwa take fusk'anta haka.


"Allah Nagode maka Ubangiji ka karamin Hakuri da juriya!" Ta fad'a Haka tare da cire zanin jikinta a hankali take wanka tana kuka k'asa k'asa ..


Fitowa tayi ta sameshi har yayi barci sallaya ta shimfid'a ta hau nafiffilu Ranan ko barci batayi ba ta kwana saman Sallaya a lokacin da kowa ke barci i'ta Kuma tana kaima Allah kukanta Biyar da minta Goma ya farka tare da barin d'akin tana idar da sallah ta Gyara d'akinta kichin ta shiga ta fara had'a mishi abun Kari tana Kammala komai ta wanke kwanunka da yaci abinci jiya da Wanda ta b'ata Gyara gurin tayi sannan ta jera mishi abincin a falonta wanka ta shiga tana Fitowa ta fara jin Hayaniyar Fure da Zaina a falonta wadda rabon data ga d'ayansu tun lokacin da abinnan ya faru , a gurguje ta shirya tare da saka Himar ta fito ta samesu Kan abincin data dafa mishi sunyi Kaca Kaca da Falon wani i'rin dogon tsaki taja a zuciye tayi Gurin. Allah ya gani tana Hakuri dasu, Halinsu ya i'sheta.


“in ma Mijina Girki kuzo har cikin falona ku cinye sannan ku b'ata min Gurin banson damuwa fa meyasa ku, kullun in baku tada husuma ba bakwa jin dad'i haba wani i'rin ibilis ne ke kanku?.." Fure ce ta mike tare da shaketa da Himar d'in, “Dan Ubanki waye iblis shegiya ke kika sai abincin?.." tureta Jiddah tayi tana haki ranta a b'ace tace. “Bade ubana ba, Wallahi.." fincike Himar d'in jikinta Fure tayi tare da Wurgi dashi "Au ni kike zagi Aiko zaki ci Kan uwarki Yau, daman ban tab'a shiga Jikinki ba" a razane Zaina ta mike ganin cikin jikin Jiddah ya girma “Na shiga uku ni Abu ke dan Ubanki daman cikin nan Bai fita ba, durun Uwa! aiku ki Haifa in gani.." tana fad'in Haka takaima cikin duka lilis suka mata Fure na dukanta Zaina na kaima cikinta Tun tana i'ya Kare Kanta Har ta kasa ta galabaita ga jini daya tsinke mata ganin Haka yasa suka fita da gudu Karo sukaci dashi Baya yayi Yana kallon yadda suka fito a hargitsa da sauri ko wacce tayi d'akinta Yana shigowa yace “innalillahi ke Meya had'aku suka Miki Haka, wai bana ce ki daina shiga sha'aninsu bane? Allah yasa nide karsu tab'a lafiyan abinda ke ciki.."


Cije baki tayi tana kuka abinda zaice mata kenan wato i'tace ma ta jawosu ma, Yana korin tab'a ta saiga Nafisa ta shigo da Gudu domin karaman Yar Zaina sajida a Kan idonta akayi komai shiyasa taje ta sanar mata “Kai...! Karka yarda ka tab'a ta azzalimi solob’iyo Kana cikin Gida kana ji Amma dake kana tsoron Zaina ka kasa komai kalli yadda take fitar da Jini Allah Yana nan Muazzan Allah baya barci" Durkusawa tayi ta Kama hannun Jiddah "Jumanah..!" Ta kwala mata Kira da sauri tazo ta kamata suka fita.


Binsu Yayi da motar shi tsaban ta galabaita ko idanunta Bata iya bud'ewa ‘Dakin taimakon Gaggawa akayi da i'ta Kasa komai Nafisa tayi domin ta tsorata da lamarin sosai likitoci ne suka rufu a kanta Fitowa tayi tare da zama a kujeran Reception d'in Tafukan hannayenta tasa a fusk'anta tana kuka Yana tsaye Yana kallonta Hankalinshi a tashe wayarta ta d'auka tare da Kiran iyanmu ta sanar mata, kasa Kiran Ummi tayi sai sako data tura mata da Gmail d'inta Halimatu ta kira, ta sanar mata kashe wayarta tayi tana Zaune d'aya daga cikin likitocin ya fito, Mikewa tayi cikin rawan murya tace. “Dr Aliyu lafiya ya take..?" Dr Aliyu yace “Kai Dr Nafisa Gaskiya ana zalunci Yanzun su waye kuka daki cikinta haka..?" Nafisa tace. "Sanin wannan lamarin sai Allah ni dai ya Lafiyar ta dana cikin?" Dr Aliyu yace "Za'a mata C's domin alamu sun nuna tun jiya take nakuda" tafiya yayi da sauri ya d'ibi kayan aiki Suna Tsaye gurin aka fito da i'ta tare da Nufar wani D'aki kimanin awa d'aya da rabi wata Nurse tazo ta kirata tana shiga d'akinta ta sameta kwance kaman Gawa kafin tayi magana wayarta yayi Kara.


"Kuna wani asibiti?" Cewar ummi da i'sowarta Kenan daga Kaduna Nafisa tace "Muna asibiti na Harkun karaso kenan" kashe wayar Ummi tayi sannan ta fad'awa iyanmu wadda kusan lokaci d'aya suka i'so "Barka da arziki An samu maza biyu mace d'aya sai dai biyu ba lafiya macen ta samu karaya sosai a jikinta namijin dai hannun d'aya ne ya karye sai na ukun Sabida mace ce farko ga yaran can" ya nuna mata inda aka sanyasu a kwalba, kallon gurin tayi taga su ƙananu Jiddah ta kalla tare da kallon shi tana jiran Karin bayani "Kwankwasonta ya Goce dole in d'inkin ya warke
za'a kifata a mata aiki"


Fita tayi a d'akin.


Saida ta kwashe sati Uku a kwance kafin ta farka da dare, Sai dai Bata i'ya komai tana kwance Ummi na Gurinta da iyanmu ga Nafisa ma dake tsaye kanta , sai washe gari ta ganshi da sassafe ya shigo Ko kallon inda yake batayi ba, “Sannu Allah ya Kara lafiya" sanin ummi da Mahaifiyarshi na gurin ne yasa ta amsa domin bata so su fahimci halin da take ciki dashi , Bata samu Ganin yaran ba domin suna kwalba Dole sai sun cika adadin kwanakin ,


Alhamdulillah Bayan kwana Goma aka d'aurata Kan magani komai na tafiya dai-dai da taimakon Allah Dana Nafisa sai Ummi domin Iyanmu ta koma sai an kwana biyu zata dawo A hankali lafiya yake samuwa Har ta fara mikewa sai dai Bata mikewa duka Zuwa lokacin an Ciro mata yaran wadda tana ganinsu Allah ya d'ora mata masifar K'aunarsu tayi kuka sosai Ganin yadda saura suke ba lafiya, Macen taci Suna Sanah Mazan Kuma Aakif da Aaki Bayan kwana Biyar Macen da da Aaki suka koma Ranan kaman zata mutu Dan kuka domin yaran sunki Kama nono Aakif ne kawai ke Sha seda aka kara Mata ruwa domin zazzab'i ya rufeta Ummi ke rarrashinta da nasihohi Tana samun karfin jiki suka dawo Gida Zaina da Fure ba wadda ya lek'o ta, makota nata shigowa Suna mata Barka, Zaina bakin ciki kaman ta mutu Ganin Jiddah na raye har da D'a , lallai da sauran Aiki gabanta , Ummi ce ke lura da lafiyarta dana Aakif duk da ba wankan jego take ba Amma tana Amfani da ruwan zafi sosai tsakaninta da Arab sai dai kallo domin ko zai shekara Mata magana Bata

Please Login or Register in order to submit comment