Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace komai ba “Karfe Tara fa ya gota madam na fara jin idanuna na rufewa Arab asuba ta gari ga makullin d'akin” Karb'a Arab yayi Adam na shiga d'akin Ruma shima Arab ya Mike ya bud'e kofa “Tashi kije ku kwanta karki manta Kuma da abinda nace” wanke hannu nayi nace Mata “Seda safe Ummuh” Murmushi nima tamin kafin tace “Allah ya tashe mu lafiya” kwashe kanunk'an abincin tayi seda ta gyara Gurin kafin ta kashe kwan wutan ta nufi D'aki ‚ da Sallama na tura kofan yana zaune bak'in katifan dake shimfid’e a kasa ya amsa min Durkusawa nayi tare da fad'in “Allah kayi Hakuri da abinda na maka in Allah ya yarda bazan Karayin rashin kunyar ba” da sauri ya kalleni Mamaki ne ya cikashi shine yau mace take durkushe a gabanshi tana bashi Hakuri abinda be tab'a faruwa dashi ba lallai a gaida Ruma dan yasan i'tace tasa Jiddah “Kaji kayi Hakuri” maganarta ne ya Kara katse shi “Naji kema kiyi Hakuri da abinda matana suka miki” A hankali nace “Na Hakura Amma dan Allah karka sake kaini Gurinsu domin zasu kasheni ne tun kafin burina ya cika” ..
“Meye burin naki” Zama nayi sosai kafin na fara mishi lissafi “burina idan na girma nayi karatu na samu aiki zan Gina katon Rijiya Kuma inyi bohol zan Gina islamiya na marayu zan ringa tallafawa gajiyayyu...” cikin gajiyawa da maganarta yace “Naji Allah ya kaimu zoki kwanta kiyi barci nik'an barci nake ji” yana fad'in Haka ya shiga cikin Gadon tare da rufe kanshi da sauri Kuma ya bud'e bargon “na manta ga maganin a saman firizan can ki balle kisha seki kwanta”
Da nasha maganin memakon inhau Gadon sena koma na zauna tare da d'ora kaina saman Gadon shuru shuru beji tazo ta kwanta ba yasa shi mikewa “Ke a Haka zaki kwanta?” d'agowa nayi cikin turo baki nace “To ai ba kyau a kwanta gado D'aya da namiji” Dariyan Shakiyanci yasa sannan yace “Amma baki da hankali an fad'a Miki wani abu zan Miki? Me zanci a jikinki? Me zan shafa naji dad'i abu sur Kashi gani da cikak'ku had'add'un mata me zanyi da jikin yarinya! inma zaki zo ki kwanta gwara ki taso” murkud'a mishi baki nayi “oh koma menene nide nace bazan hau Gadon ba” saukowa yayi “To Ni na sauka jeki kwanta” Ai da sauri nace “Wa? Bade Ni Jiddan ba gwara ma kayi kwanciyar ka‚ ni hakan yamin” be ja da tsayi ba ya koma yayi kwanciyarshi nima a Haka na kwanta kayana.


Maman Faruq
12/26/23, 8:59 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*


_Wattpad@ayshajb_


®️🌁


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*








FREE BOOK


Page5
Barcin ma rabi da rabi nake yinsa domin tsoron ya taɓani nake ji can da barci ya fisgeni naji ya cicciɓeni ya dora saman gadon zabura nayi tare da kurma ihu jikina na ɓari dan ko gizau be yi ba, haka ya ajiye ni tsawa ya daka mata. "Ke mahaukaciyar lnace! in banda wawanci irin na ɗan kauye me zesa ki kwanta a kasa sanyi na shigarki, lna miki Gata kina kaucewa" na tsani tsawa ban sabaji ba, domin har iyayena sukabar Gidan duniya basu taɓa tsawata min ba, shiyasa na toshe bakina da hannuna kalmominsa sun ƙona min rai sosai ajiyan zuciya nake saukewa hawaye na wanke min fiska haka ya gama cimin mutumci ya kwanta abinsa takurewa nayi sosai lna ajiyan rai barci ɓarawone ya ɗauki "Bansan ki da wannan halin ba jiddah lokaci ɗaya kina kokarin fanɗarewa! raina na ɓaci in naji kina mayarwa mutumin daya amsheki batare da ya musa ba!, me akayi ko? hakuri zakiyi domin Guguwa na nan tana tunkaroki sekin tsunu ki sanyawa ranki hakuri... "amma Mama kina gani daga zuwana matanshi zasu kassarani shima zagina fa yake yi har cemin yai mahaukaciya yamin zafi! naji ciwo bazan iya ba!.." shafa kanta tayi kibar kuka kiyi hakuri da komai shi zaman duniya ɗan hakuri ne karna kuma ji kin ɗaga mishi murya.." Gyaɗa mata kai nayi cikin wani irin juriya nace "insha Allahu mama bazan sake ba" murmushi tayi tare da share min hawayen dake sauka kuka nasa sosai lna jin raina na zafi zan sake magana ta hanani lna kuka naji ya daka min tsawa ashe sosai nakeyi domin sautin muruyana na fita, "ke tunɗazu nake tashin ki kinyi banza dani kina kukan banza" miƙewa nayi jikina na rawa hawaye na zubamin ban taba tsintar kaina cikin quncin rayuwa irin na yau ba, hanyar banɗaki ya nunamin na shiga tsarki nayi da alwala lna fitowa naga ya shimfiɗamin sallaya ga himar ma , fita yayi nima na tada ikama sallanake inna kuka cikin sujadata lna kai karansu gurin Allah kaina nakasa har ya dawo ya zauna a gefen gado, ɗagowa nayi na sallame sallan ɗaga hannuna lna addu'a a bayyane "Allah kaji ƙan iyayena sanyi idaniyata abaɓen alfaharina allah yakai haske da rahama kabarinsu allah ya yafe musu zunubansu allah ya haɗasu da annabinka annabin rahama sallallahu alaihi wasallan, Allah na kawo karan wasu bayin ka, wanda sukayiwa rayuwata dirar bazata ba tare da na shiryawa haƙan ba, Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu Allah kamin katangar karfe dasu Allah duk wanda ya zalunceni kabimin haƙƙina Allah ka yafe kuskurena..."kukane yaci karfinta haka ta shafa addu'ar ta mike tare da ninke sallayar Tsungunawa nayi gabanshi "ina kwana?.." cikin masifa yace "daban kwana ba, zaki ganni? watou har karata kike kaiwa gurin Allah gani azzalumi ko?" ban kulashi ba na tashi haka ya ringa cin mutumcina ko cin kanka bance mishi ba, karshe ma fita nayi a ɗakin,
suna zaune a falo durkusawa nayi na gaida adam cikin sakin fuska ya amsa min "Ummuh lna kwana?" nace mata lna kara sunkuyar da kaina kasa "matso nan ƴata" domin a haife ta haifeta matsowa nayi na kwanta a jikinta kukan da naketa matsewa ne ya kwace min, kuka nake sosai shafa kaina tayi tare da faɗin "A duk lokacin daka tsinci kanka cikin Qunci rayuwa kace alhamdulillah base Allah ya jarrabeka da abin farin ciki zaka gode masa ba, ki zama me amsar kaddarar aduk yanda tazo miki.." gyaɗa mata kai nayi "inshaallahu nagode da tunatarwa" murmushi tayi sannan ta nuna min abinci kaɗan naci sabida raina a ɓace yake, miƙewa yayi bayan ya gama cin abinci "tafiyan kenan?" adam ya tambaye shi kallon agogon dake ɗaure Tsitsiyar hannunsa yayi tare da taɓe baki "lokaci na tafiya ki tashi" ya fad'i haka tare da tsare ni da ido rai a had'e danne kukan dake shirin kwacemin nayi tare da mikewa nayiwa ummuh sallama suna gaba lna biye dasu har gurin mota Ummuh ta rakomu tana mana fatan Alkhairi, hannun sukayiwa junansu kara rikeshi Adam yayi "Arab dan Allah ka sauko da zuciyarka kasa yarinyar nan a firgice take da kai.." "naji!" a takaice ya fad'a tare da bud'e motar ganin bana gaba yasashi tsayawa turus cikin bala'in yace "Ke fito ki dawo gaba!" lna zaune na jingina da jkin kurejar idona a rufe bamma san yana magana ba, domin nayi nisa a tunanin yaruwar data riskeni,


"Ke dan gidanku lna miki magana kin min shuru nine zan zama direvanki? "Kayi hakuri..." cikin kufula yace "fito ki dawo gaba" jiki a sanyaye na fito nan naga duk basa nan ajiyan zuciya na sauke domin na tsani cin mutumci a bainin naasi, haka na zauna na mayar da fuskana jikin glass lna kallon waje shigowa motar yayi tare da buga murfin yana jan tsaki nide ban kulashi ba, domin Allah kaɗai yasan abinda ke raina kiris nake jira na sauke nawa kwandon rashin mutumcin domin tunda ya shigo rayuwana hakurina yayi karanci,
***
Tafiya kurame shine tafiyar da mu kayi munyi tafiya sosai kafin ya tsaya a wani kauye fita yai yaje yin sallah ganin be cemin kala ba, nima na fita, ruwa na zuba a buta naje bayan gurin nayi tsarki sannan nayi alwala na rigashi dawowa cikin motar domin yaje siyan abinci koda ya dawo tekawey ya ajiye bemin magana ba nima kuma ban kulashi ba haka muka ci gaba da tafiya komai ya siya seya ajiye ni kuma banyi karanbanin tab'awa ba, ashe ranshi ya b'aci har barci ya fara fisgata ya taka wani wawan birki motar tayi gaba ta dawo baya kainane ya bugu na dafe hannunna a gurin lna cije baki domin naji zafi sosai ban zata ba , ya jawoni tare da had'a himar dina da wiyana ya shakeni sosai "Ni kika mayar asararre? in kashe kud'ina gurin siya miki abinci amma ki brshi ya lalace ga soko ko?" hawaye ne ya shiga zariya wani nabin wani da kyar nayi magana domin numfashi na ya fara barazanar barin ganagan jikina "Daka siya kace min Hauwa'u gashi? ko kace naci ne da zan d'auka ? an fad'a maka ni mayunwaciya ce , to ban bukata shi kenan! d'auki kayanka, Arab ka shafa min lafiya ka fita sab gata..." tureni yayi na bugu da glass din motar me shegen karfi abin bakin ciki kainane ya fashe amma glass din ko tsagewa beyi ba haka ya figi motar a guje ..


ajiyan zuciya kawai nake iyayi ga hawaye da yaki dena tsayawa kaina wani mugun ciwo yake min azzalumin nan ko ya juyo yaga halin da nake ciki ajiyan zuciya na sauke me karfi domin wani gargada muka shiga shi kuma yaki tafiya a sannu, seda na kara buga kaina daga nan bansan meya faru ba tsaban a zaba se farkawa nayi na ganni kaina jikin wata dattijuwa fara sol, ga kyau ga ,gayu jikinta mul-mul ajiyan zuciya ta sauke shi kuwa yana zaune fiskan ,kan da d'an dama cikin tsamin hausarta tace "jeka kira likitan" yana fita ta dawo da dubanta gareni rufe ido nayi itama bata takura min ba, ashe suma nayi koda muka iso zari'a ya tab'a ta yaji jikinta zafi rau gashi bata motsi shine y ciccib'e ta a falo yaga iyammu "cikin takaicin halin d'an nata tace koma kayi sallama domin ba d'akin kafura ka shigo ba, ai ko arnan suna konkon.."


"Dan allah iyanmu kiyi hakuri ki duba halin da ƴar nan take ciki.. "dakata! ince bakin halin naka ne ka gwada mata, dukanta kayi ka fasa mata kai bayan rashin tarbiyan da ƴan boko suka nuna mata (matan shi take nufi) kashe musu 'Ya kake son yi ba, kaje ni ba abinda zan muku na zare hannun na zaga iyalanka.... "dan girman Allah ki gafarce ni wallahi ba abinda kike zato bane iyanmu ba abinda na mata" share shi tayi taci gaba da karatun ta, ajiye jiddah yayi kaman ze mata kuka da kyar ya shawo kanta shima da sharaɗin ze tsaya a gidanshi ya zama namiji, ya amsa mata ne kawai amma bejin ze samu karfin gwiwar tsawatar musu domin suna haɗa mishi zafi su gwara kanshi yanda suke so ne, daga karshe seda suka danganta da asibiti tare da likita suka dawo ya cire min karin ruwan shayi ta had'a min kad'an nasha na shiga yun kurin amai iska ta ringa hura min tare da watsamin ruwan sanyi har aman ya koma "sannu fa Allah yana sane dake fatana ki zama haske a rayuwarshi Allah ya dubi lamuranki ya saukaka miki, ubangiji ya ɗaukakaki" wani kuka ne ya kwacemin bata hanani ba seda nayi me isata kafin nayi shuru lna sauke ajiyan zuciya sallama aka bamu muko koma gida kaman wani me aljanu mun isa gidan ko cikakken min ashirin bamuyi ba ya mike lokacin lna kwance a doguwan kujera iyanmu tana duba ishmawiy ya mike "Iyanmu zamu kaduna domin a gidan sawda zata zauna"


cikin gatse tace "tsawon shekara nawa?" gaba yayi tare da ɗaga kafaɗa "zuwa lokaci da allah ya takaita zamanta a gidan... "kaci gidanku" murmushi yayi tare da fita kallo na tayi tare da juyar da kai tausayin yarinyar take ji, i'ta kuma haka Allah ya kaddara mata shiga cikin iyalan lbrahimu Gidan da ake rayuwa cike da bakar kishi, "tashi ki bishi Allah ya tsare, zanso ki mayar da hankalinki kan karatu musammam ma, ta mahamadiya domin zata temaka miki qwarai wajen inganta rayuwar aurenki zanso ki fita zakka wajen ilimin islama a cikinsu domin Allah ya jefoki ne tsakiyar matan da suka jika da boko matan da basu bawa mijinsu mihimmanci kaman yanda suka maida hankulansu kan ayyukansu ba, zance ma gwara Nafisah" nide ban bawa zanceta muhimmamci ba domin na rasa inda ta dosa Allah ya temaka ma nayi wanka asibiti ..


Ga link Dan Allah idan kinsan ba karantawa zakiyi da comments ba karki shiga!


https://chat.whatsapp.com/HsMb0FG2FMMFCBLoDfHoyQ


*Maman Faruq*
12/26/23, 9:00 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*

_Wattpad@ayshajb_


®️🌁


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*




FREE BOOK



Page6
Jingine da motarshi yake yana ganin fitowarta ya shigan tare da rufe murfin a hankali nake tafiya har na karasa inna shiga yaja motar juyar da kaina nayi gefe har munyi nisa da tafiya kafin ya waigo. "i'tace mahaifiyata iyanmu mu Shida ta haifa, Sawda ce babba tana aure a kaduna malamace yarinyarta ɗaya tal, sai Musa shi kuma yana sudan da iyalanshi sai Abbas shima yana sudan Aminu yana Bauchi nine na biyar se karaman mu Zaliya wanda take ABU Mahaifin mu ya rasu shekara shida kenan" bance mishi komai ba har muka isa Kaduna Gidanta baban gidane a gefe guda akwai makaranta wanda ake koyar da matan aure har da na ƴan mata da yara megadi ne ya buɗe mana get yana de-deta tsayuwar motar muka fito yana gaba inna biye dashi a baya Da sallama muka shiga falon ba kowa zama yayi tare da nuna min kujera memakon nayi yanda yace sena zauna a kasa.
Shuru mukayi na yan mintuna kafin ya katse shurun ta hanyar fad'in, “na kawoki nan ne domin ki zauna na d'an lokaci ki mayar da hankalinki kan karatun da zakiyi domin matana ba jahilai bane , ko wacce da kika ganta da iliminta da sana'arta matsalar ki ne ki nutsu kinyi karatu domin inganta rayuwarki domin mahaifinki Yana da burin kiyi karatu banda shirme... "Hmmm kasan aiki nane shirme ai Daman nace matanka jahilai ne , daga zuwa na sun nuna min kalar tasu ilimin, da kace na mayar da hankali ko karna mayar ince hankalin nawa ne? Kuma a jikina yake, nagode insha allahu zanyi karatu zan nutsu kodan nacika burin Raina" Gyad'a Kai yayi kafin yace. “yana da kyau.." "Daman ba kyau ne?" Na fad'i Haka inna lanƙwasa hannuwana..


"Ki kiyaye harshen ki, kisan abinda zaki ringa furta min karki bata min rai"


Sunkuyar da Kai nayi kasa.


"Kayi hakuri insha allahu zan kiyaye"


"Assalamu alaikum" tace kafin ta karaso cikin shigar kamala a nutse ta zauna kusa dashi.


"Amin wa'alaikis Salam barka sawda malama Sawda ummin halimatu"


Murmushi tayi kafin ta juyo gare ni "inna yini" nace mata murmushi tayi kafin tace "lafiya lau hauwa ya gajiya da hakuri da k'anina?" Ta karasa maganar tana kallonshi bance Mata komai ba had'e fiska yayi "haba! Dan Allah ai seki sa ta renani" a hankali yayi maganar,


Girgiza Kai tayi kafin tayi waya kichin "Yahgana ki kawo abinci" kashe wayar tayi , tare da mikewa "Zo muje kiyi wanka da sallah kafin ta kammala"


Ɗakin Halima ta kaini tare da nuna min Banɗaki wanka da alwala nayi inna fitowa ta shigo da bakar leda "Yanzun arab ya aiko kiyi amfani dashi. Bance Mata komai ba ta fita Dogayen rigunane guda Shida se Himar da kananun tarkace a Raina nayi tsaki kafin na saka D'aya daga cikin kayan sallahn dake kaina duka nayi kafin na kwanta saman salayan Nan da Nan barci ya dauke ni cike da gajiya..


Yana ganin shigarsu shima ya mike masallacin dake wajen Gidan ya nufa anan yayi sallah ya dawo abincin da aka jera ya zuba ya fara ci, Ummin halima ce ta shigo "Hauwan bata fito ba?" Ba tare da ya D'ago ba ya Gyad'a mata Kai.


Dakin ta shiga Nan ta isketa kwance Girgiza kai tayi tare da dawowa "Ya naganki ke d'aya Jiddan fa" "Barci take"


Shuru ne ya biyo baya na d'an lokaci kafin ta tsake shurun ta hanyar fad'in "Muazzan naga Goshin yarinyar Nan da ciwo inna fatan ba matan ka bane suka sila?" Da sauri yace "a'a ba ko d'aya me ruwan su da i'ta da zasu tab'a ta" Qurr ta masa da ido badan ta yarda ba tace shi kenan.


"Wani shawara ka yanke game da rayuwarta?"


"Eh to in naga zan baki kudi kiyi yanda ya dace domin anan zata zauna inna tunanin inna had'ata da matana Gaskiya Bazata ji dad'in zama cikin su ba, abin da ya dace kawai tayi zaman ta Nan tunda Kinga Ga Halima naga Hanisa ma tana Nan (Yar Aminu tana karatu Gurinta). Katse shi tayi "Ban ki maganarka ba, Amma har tsawo wani lokaci Zaka tsaya a Gidanka yaushe zaka zama namiji me fad'a aji, haba! Wannan wacce irin rayuwa ce ace mutum bashi da 'Yanci shida gidanshi baka isa ka zauna na minti biyar ba tare da an tada hayaniya ba inna jin zafin wannan abun Mata uku Amma duk ba me Hankali.." Mikewa yayi cikin Gajiya da jin kalaman ta sosai suke tab'a zuciyarshi murya a dakile yace "Zan tura Miki kudi kiyi duk yanda ya dace ni na tafi"


"Dole ka tafi tunda an tab'a maka Zinari Allah ya kyauta saura Kuma ka share Yar mutane dan nasan halinka sarai... "Daman me zan Mata? bana tunanin zan zauna da yarinyar nan fa, domin bata cikin tsarin matan da nake so Gata bak'a yar K'auye ba ilimi kai bata min ba ko kad'an sallamarta tayi taje tayi rayuwarta..."


"Allah ya nunamin ranar da zaka zo kace in baka Hauwa Allah ya kaimu lokacin da har kasa zaka rok'e ni in baka matar ka ni kuwa a lokacin zan gwada mata bade haka kace ba? Zaka ga yanda Bak'a yar K'auye zata b'ata Lissafi da tunaninka a sauka lafiya"


D'aga kafad'a yayi alamar maganarta bai dameshi ba fita yayi yaje ya bawa motarshi wuta hotel ya kama domin washe gari ze juya,


Tun lokacin data bar d'akin na farka Band'aki nashiga tare wanko fiskata nabi bayanta Amma kafin na karasa na farajin maganar Arab da Hannun na rufe bakina domin wani i'rin kuka me ciwone naji Yana shirin qwace min duk ni d'aya yake jifa da kalaman Nan, me namishi da zafi silalewa nayi na zauna a qaka hawaye na bin fiskata bansan iya lokacin dana d'auka ba naji sallaman mutane biyu da sauri na tashi na share hawaye na falon na shiga cikin fara'a tace "harkin tashi bisimillah zoki ci abinci" Sunkuyar da Kai nayi kasa a hankali naji yaran da suka shigo d'aya wacce nakega zamuyi sa'anni tace "Ummina wacece wannan Black beauty din?" Matar Kawun ki ce wacce nake Baki labarin suna hanya" zata sake magana na kusa da ita ta make bakina "Haba Hanisa meye haka.." wacce tacewa Hanisa na kalla a qalla zata Kai sha shida , tace "Wallahi Halima kin fiya bin ƙoƙof" hararanta Halima tayi kafin tace min ."ya Sunan ki"


"Jiddah"


"Suna me dad'i zamuyi Qawance?"


Murmushi nayi kawai tare da mayar da hankalina kan abinda nake ,


Wani i'rin kallo Hanisa take bin ta dashi ba tare da kowa ya lura da hakan ba, mikewa tayi ta nufi Dakin su wayarta dake makale da Caji ya cire tare da Kiran mahaifiyarta tana d'auka tace "hello umma Kinganta kuwa yarinyace fa wacce a yanzun take 14, akwai kyau duk da bak'ace Wallahi umma tana da bala'in kyau sekin kalli hancinta da qwayar idonta dayake Nan kaman na mage zaki tabbatar da hakan"


*D'aya B'angaren*


Mikewa Bashama tayi cikin bala'in tashi hankali "Hanisa wallahi tunda na rasa Arab to Wallahi D'aya bayan d'aya dukk'an su sesun rasa shi abin takaici ya rasa wacce ma ze aura se yar cikinsa a l'na ya auro ta ma" "Wallahi umma ban sani ba Amma karki damu a hankali dan binciko Miki" Sallama sukayi tare da kashe wayar,


Rayuwata a kaduna wani i'rin rayuwana da zance Alhamdulillah domin Ummin halima tana girmama lamarina uwace na gaban kwatance Wanda ta tsaya a gidanta makarantar su Halima wacce ta nace da se munyi qwance aka sakani zamu tafi takwas Se karfe D'aya zamu dawo muna yi sallah zamuyi wanka muyi shirin islamiya Wanda yake mallakin Ummi ne tsakanin makarantar da Gidanta babu nisa sosai sannu a hankali lokaci ke tafiya har na shafe tsawon shekara biyu a gidanta na mayar da hankali sosai a kan karatuna ban cika magana sosai da mutane ba cikin Kankanin lokaci Allah ya d'aukaka al'amura na kowa son qwance yake dani Sabida kokari na, Amma basa gabana domin Wallahi Halima kad'ai da Hanisa sun isheni kokarina da qwanzo na yasa malaman makaranta ke bala'in Sona Aure kan na watsar dashi domin Daman ban d'aukeshi da wani mahimmanci ba rayuwana nake cikin qwanciyar hankali yau a matukar gajiye nake hakane yasa driver na sauke mu na shiga Gida da sauri na fad'a d'akinmu kasancewar inna fashin sallah yasa nayi wanka tare da fad'awa saman gado Hanisa da shigowarsu kenan tace "kai Jiddah yau Kuma barci ne" ya mutsa fiska nayi tare da juyawa mata baya domin bana jin yin magana tsaki tayi domin wannan halin nawa na bala'in bata haushi Sabida in na Mata i'rin Haka seta fita sabgata ni kuwa ban damuwa , l'nama nake sanin na b'ata mata rai Halima ne de dake bata da hakuri Nan zata hauni da masifa takan ce. "Gaskiya jiddo banson iskanci da shariya ya inna Miki magana zaki bawa iska ajiyata?"


"Kiyi hakuri" iya abinda nake ce Mata kenan, duk da haka be Mata se tayi kananun surutai i'ta bata son wannan halin nawa na fiya miskilanci wani lokaci se Ummi ta daka mata tsawa take hakura da mitan,


A hankali nake kirga kwanakina har na shiga kirga mako har na koma wata ayau nake lissafin shekarata Hud'u a Gidan ya kasance inna da sha takwas kenan mun kammala sakandiri lafiya sakamako yayi kyau Dan murna har azumi nayi domin duk nafisu Makin me kyau, a so biyu Arab ya tab'a zuwa tsakanina dashi gaisuwa dan nama manta da matsayinsa gurina. Zaman wata uku mukayi kafin Ummi ta samo Mana wani makaranta ban tab'a tsintar kaina cikin damuwa da bak'in cikiba seda ta shilar shigata jami'a domin seda na gwammace da banyi karatu ba a rayuwata nayi kuka Kuma har gobe inna kuka domin abinda nayi ban tab'a tunani ze shafi ahalina ba, tunda na had'u da Arab nake kuka Kuma har yanzun kuka nake.


Cikin doki da murna muka fara zuwa makaranta a gida kuwa Ummi ta dage sosai gurin koya Mana girke girke yau da huri muka muka fito inna zaune nida Halima Hanisa muke jira Halima ce ta mike tare da fad'in "Kinga bari na duba abu a library inna zuwa" hankalina na kan karatun da nake nace Mata "toh" batare da na d'ago ba, wata Yarinyar dake nesa dasu tana ganin tabar gurin ta karaso muga desk din tayi "Hi Jidda Usama" d'agowa nayi domin sarai nasan muryanta tun shigowata take bibiyata ta nace min yanda kuka San cingon, murmushi tamin Tami nima na mayar Mata roban yogurt biyu ta ajiye tare da tura d'ayan gabana "bisimillah" Girgiza Mata Kai nayi domin kawa kawai naji zuciyata ta kasa nutsuwa da i'ta marerece min tayi ni kuwa naki karshe mikewa nayi tare da kashe littafaina nace "Aliya nagode azumi nake" juyawa nayi na bar gurin tab'a Bluetooth din dake makale da kunninta tayi "kunde ji Wallahi taki Sha dan Allah zan gwada in tasan wata bata San wata ba"


Cikin tsananin b'acin rai ta ture Yogurt din tare da barin gurin daman ba tafiya nayi ba duk abinda ta fad'a inna jinta d'aura hannu nayi akai tare da sallati Nan da nan hawaye ya cika idona wake bibiyar rayuwata ne? Banida me bani wannan amsar cikin tashin hankali na fara kokarin tafiya ji nayi an dafa kafad'a na da sauri na juya Hanisa tace "Jiddah lafiya na ganki ke d'aya me kike anan? Halima fa" cikin rawan murya nace "Taje duba abu ke muke jira tun d'azu" Hanisa tace "Amma meke damunki naji muryanki haka?" Girgiza Mata Kai nayi, "bakomai"


Karasowan Halima yasa muka tafi Gida tun daga wannan lokacin na rasa walwalata Hanisa

Please Login or Register in order to submit comment