Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaika zaka taka kowa son ranka! Sufa wanda kake nuna musu isa da izza kake takasu yanda kaso ba finsu kayi ba! domin suma Bani Adam ne kaman yanda kake banbanci shine kai Kanada dukiya, suma in Allah yaso lokaci ɗaya seya kwace naka ya basu nikin ba ninkin naka, Allah yasa mudace Allah ya rabamu da kwaɗayi da ruɗin DUNIYA sallama Liman yayi a hankali Asma'u ta amsa mishi miƙewa nayi naje na kwanko hannuna na dawo "Hauwa in sauran kayan mu na kusa ki duba zaki sami takarda ki ɗauko" hakan kuwa tayi karɓan takardan Mama tayi sannan ta miƙawa malam "Wannan takardan yana ɗauke da sunan Mu'azzan da numbobin wayarsa da adireshinsa mu'azzan nabin usama dubu talatin shekara guda ke nan da watanni babushi babu labarin sa ganin halin matsin da muke cikine yasa usama yanke huƙuncin biyan bashi da Hauwa kafin ya rasu sede ya faɗamin kuma jadda damin nan ta kwashe komai ta faɗa musu sunkuyar dakai kawai nayi inna hawaye "Dan Allah liman ka dubi halin da muke ciki da wanda muke shirin shiga ka samo mutumin nan Hauwa ke kuma kiyi hakuri bamu da yanda zamuyi bamuda shi bamu bawa wani ajiyan sa ba dolence tasa mahaifinki yanke huƙuncin haka" liman yace "insha Allahu zanyi i'ya kokari na gurin ganin na samoshi Allah yaji ƙan usama" da dare ina zaune saman sallaya mama na kwance saman katifan larai duk munyi shuru ga abincin da larai ta kawo mana na dare miƙewa nayi na ninke sallayan tare da cire himar ɗin dana saka "mama abinci" Buɗe idonta da sukayi ja tayi "kici Hauwa inna sane ɗazun bakici ba.. "a a mama ki faraci kafin naci" miƙewa tayi "To shi ƙenan" yanzun ma kaman ɗazun a baki na bata shinkafa da mai da yaji bataci sosai ba ta juyar da kai ruwa na bata ina shirin rufe kwanon ta buɗe nan ta shiga bani dolece tasa nakeci haka ta bani seda ta turamin abincin sosai kafin ta barni. ruwa nasha nazo na kwanta kusa da i'ta Larai na ɗakin liman a haka har barci ya ɗauki mama niƙan idona biyu domin tunda Baba ya rasu na kasa barci tunanin halin da zamu shiga nan gaba nida mahaifiyata da abinde ke cikinta nakeyi domin nasan zaman mu a gidan liman bame ɗorewa bane tun ina kuƙan zuci har ya fito fili ban saniba Hannun mama kawai naji tana share min hawaye na "Ki dena kuka Jiddan baba, Allah yana sane damu be manta damu ba , Hakuri kawai zamuyi mu rumgumi kaddararmu" a daren nan mama tamin nasiha sosai kuka nake wiwi na kasa tsayar da hawayena ashe na bankwana takemin ashe i'tama tafiya zatayi ta barni ta samin albarka tamin addu'a sosai tana shafa kaina tana magana har barci ya ɗaukeni ban sani ba kallona kawai take i'tama barci ya ɗauketa da sanyin asuba ne ya farkar dani har yanzun hannun mama na ɗaure a kaina juyowa nayi na kalli fiskanta tayi fayau se wani haske da tayi zare hannunta nayi nafita naje nayi ɗahara kafin nayi alwala na dawo ɗakin ana kiran sallan asuba naje inna tashin ta "mama lokacin Sallah yayi" a hankali nake magana amma shuru bata amsa min ba ganin haka yasa na taɓata "mama ki tashi haka lokacin sallah yayi" shima shuru kafin na sake magana sega larai "Har kun tashi" a hankali nace "na tashi mama ne take barci ina tashinta taki tashi ma" hannunta larai ta kama nan taji ya sake da sauri ta ɗaura kanta a setin zuciyarta amma ina rai ya riga da yayi halinsa domin kominta baya motsi "innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah ya miki rahama Asma'u" bansan lokacin da nayi zaman ƴan bori a kasa ba ɗif nadena jin komai....






Maman Faruq
12/26/23, 8:58 AM - UMMI JB: *SIRRIN ƊAUKAKA..*

_Wattpad@ayshajb_


Free Book


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*





Page3 .
..........Salati kawai Larai takeyi kafin tayi kaina "Hauwa! Hauwa!!" Amma shuru da sauri tayi waje Liman da shigowarsa Kenan ya dawo daga masallaci yace "Lafiya naganki haka?" Larai tace "malam lna fa Lafiya! Asma'u ta rasu.... " Be gama jin maganarta ba ya nufi d'akin Nan ya tadda Jiddah kwance Larai na shigowa yace ta kawo masa ruwa da sauri ta d'ibo ruwan ta kawo masa shafamin yayi a fiska ajiyan zuciya na sauke ban bud'e idanuwa ba , kuka na fashe dashi shi Kenan banida uwa bani da Uba , babu dangi Na rage ni kad'ai dagani se Allah se Kuma halina wayyo haka tawa K'addarar take yanzun babu Wanda zan kalla inji Dad'i ..
"Kiyi Hakuri Hauwa.." Da sauri na katse shi "To ya zanyi inba hakurin ba! Banida kowa fa! Babu ! ni ce fa ni D'aya! Kai!!." Wani irin kuka na sake fashewa dashi Bani da Gata fa yanzun , Larai da wasu mata makotanta ne sukayiwa Mama wanka malam yaje ya siyo likkafani ina kwance inna kuka har aka gama had'a mama Akayi mata sallah koda akace inje in mata addu'a kasawa nayi rik'e mankaran nayi inna kuka harda majina na kasa furta komai ganin na jima ne yasa Larai zuwa inda nake wai zata d'agani Amma tayi tayi naki tashi karshe de maza ne suka d'agani a gaban mankaran inna ihu da shurewa haka suka d'agani fad'i kawai nake "ku barmin mamana ku wasu i'rin azzalumai ne me yasa bazaku tausayamin ba , mamanace fa zaku tafi min da i'ta so kuke rayuwata ta tagayyara? banida uwa bani da uba ya zanyi kuji tausayi na mana haba! Bayin Allah..Wayyo Allah jama'a kuna gani zasu tafi min da UWA" mutanen dake gurin seda suka kokamin na zama wata iri bani da aiki se kuka abinci bana ci magana ma banayi Sallah kad'ai shike d'agani satin mama D'aya Liman ya shiga niman mu'azzan Balarabe Numbobin wayarsa baya shiga kullun aka Kira a kashe zuwa lokaci na fara saka juriya wa zuciyata sabida kullun Liman da matarsa hard'a 'ya'yansa haka zasu tasani gaba suna tausar zuciyata da kalamai masu kwantar da hankali hakade nake daurewa ina cin abinci badon inna jin dad'insa ba, bana son gwalesu ne kawai suna kokari dani banida abinda zance musu sede Allah ya saka musu da alkhairi Wata D'aya da kwana biyar aka samu wayar Balarabe bansan abinda Liman suka tattaunaba nede yace min sunyi waya da mu'azzan hakan ya faru da kwana biyar se gashi sunzo su biyu .
Dangin mahaifina babu Wanda yazo Kuma an aika musu haka lokacin da Liman ya aika a kirasu ko da Wanda ze wakilci auren Amma babu Wanda yazo karshe shiya tsayamin wanda sukazo da mu'azzan ya zama waliyinsa A masallaci bayan sallan azahar aka d'auramin Aure da mutumin da bansan waye shi ba.
Kai! ranan nayi kuk'an da yafi na ko yaushe Larai tasani a gaba nayi wanka i'ta ta bani sabon kayan yarinyarta D'aya na saka Wai Ashe a ranan zamu tafi ban sani ba se da Akayi la'asar tace in had'a abinda ya dace na d'auka "Inna nifa ban gane in had'a abinda ya dace ba" Larai tace "Hauwa tafiya zakuyi.." da sauri na Mike har inna dafe Qirji "Ni dawa zamu tafi Kuma inna ne?" Murmushi Larai tayi kafin tace "Keda mijinki Kinga shi ba d'an garin nan bane..."
"Nashiga uku da Allah kimin rai mutumin da bansan wanene shiba zan bishi wayyo Allah kumin rai" kamoni tayi tare da zaunar dani "Hakuri zakiyi Aure babu inda baya Kai mutum.." nasiha ta shiga min Liman ma ya shigo ya d'ora da nashi nasihar Inna kuka suka karkatoni gurin jibgegiyar motarsa Mu'azzan dake zaune a mota shida abokinsa suna Hira cikin hiran abokinsa yace "Kai kaga yarinyar Kuwa Arab daga ganinta akwai nutsuwa kalli yanda take zuwa k'anta a kasa" mu'azzan yace "Wallahi inna tausaya mata yanda Zata shiga cikin iyayenta" Dariya Abokinsa yayi sannan yace "Gidanka Gobara ne zasu iya sata zuba mata fetur su k'yatta mata ashana" runtsa ido yayi yana tuna Gobaran dake gidanshi.
"Dan Allah kalleta fa , karaman yarinya 'yar sha uku" fitowa sukayi Abokinsa ne ya karb'i bakon kayana yasa a bayan motar Baya ya bud'e Inna kuka na shiga k'ankame jikina nayi tare da cusa kaina a gwiwa na kuka nake wiwi haka naji tashin motar Kara sautin kuka na nayi suna tafiya ba Wanda yace min ci k'anki tafiya yayi nisa min munfita Obudu har mukazo Gboko har muka bar jihar benue inna kuka daga Nan muka d'auki hanyar abuja barci barawo ne ya d'aukeni Inna sauke a jiyan zuciya Jin shuru na Dena kuka ne ya sashi lik'awa Nan yaga wiyanta ya karkace "Adam tsayar da motar na gyara yarinyar Nan" ba musu ya tsayar fita yayi tare da bud'e baya kwantar dani yayi sannan ya dawo gaba yana zama yayi shuru Adam yace "wayaga mijin mata hud'u ta hud'un ma yarinya yar Sha uku.. Allah sarki yarinya har na hango yanda za'ayi wasan qwallo dake" dukan wasa Arab ya Kai mishi "banson Shakiyanci mubar wannan maganar Wallahi fargaba na bansan yanda zamu kwashe dasu ba" tsaki Adam yaja "inna jin takaici haba se kace ba namiji ba! Ka tsawatar musu ma ya gagareka Wai ace kana da mata har uku ba kwanciyar hankali fitinar yau daban na gobe daban wallahi idan ka Kai musu wannan mareniyar suka cutar da i'ta kai da Allah domin bawai biyan bashi kad'ai aka baka ba, wallahi amanace iyayenta suka baka inka barta matanka suka nakasata Kai da Allah" Arab yace "naji Kai gwara na kaita Zaria ko na mikata Gurin Hajiya kawai , mahaifiyarshi Kenan" Adam yace " wallahi kanada aiki gwara de ka Kai musu Susan matsayinta a gurinka" Arab yace "shike Nan" a haka suna hirarsu har suka karaso abuja.
Nik'an innata ramuwar barcin da banyishi kwanakin baya ba Gidan shi nacan gaba da babangida market , Gidane babba Wanda fad'ar had'uwa da tsaruwanshi bata lokacine hon adam yayi megadi ya bud'e mishi kofa yana gama fakin suka fito hannu Adam ya Mika mishi sukayi musaba daga Nan ya Mika mishi makullin motarsa "To abokina fatan alkahairi zan d'auki motana nima naje naga tawa Matar a kula da 'yar mutane Dan Allah" Arab yace "nagode a gaida Maryama" Adam yace "insha Allahu" bud'e bayan motar yayi tare da Kiran sunana jiddah bud'e ido nayi "fito Arab na jiranki"
"Waye Arab?" Adam yace "To mijinki" take idona ya kawo ruwan hawaye haka na fito kai seda na tsorata wallahi na d'auka ba mutum bane farinshi yayi yawa kaman ka tab'a jikinshi jini a fito kasancewar d'azun ko kallonsu ma banyi ba bare nasan yanda yake babban mutumne Amma kud'inshi ya b'oye girman nashi.
Gaba yayi nabi bayanshi muna doso kofan gabana ya buga ras tsayawa shima yayi kafin ya juyo ya kalleni girzgiza k'anshi yayi tare da tura kofan kwan..! Se sauk'an kofin glass a goshin sa har hulanshi ya fad'i dafe goshin yayi tare da fad'in "waiku wasu i'rin dabbobi ne! Kullun se kuci ku hau ihu kaman karnuka ! jubi Gidan Nan kullun a hargitse ni Kenan inna da mata uku bani da kwanciyar hankali haba! Haba!! Wannan wacce i'rin masiface" nide kasa nayi na d'auko hullanshi ji kawai nayi an fisge Juyowa nayi Dan inga wacece wata farar mata ce fiska a d'aure ta kalleshi sannan tace "Ibrahim Nafisa ce masifar ko Zainab dan ni Fure wallahi baka isa ka kirani da masifa ba Ga karnuka nan..." tana nuna Nafisat da Zainab "Kutuman uban Amma ke Fure'atu anyi yar..." Faf Fure ta make mata baki Nafisat ta kamo wiyan rigan Fure "ke yanzun Dan Kinga kinyi Kiban rashin zuciya shine zakice min kariya kazama dake shegiya me warin hammata..." Wallahi bansan lokacin da na k'yalky'ale da dariya ba kalli tib'a tib'a dasu Wai suna fad'a da junansu.. juyowa sukayi shi kuwa ya jani bayansa Dan yasan halinsu zasu i'ya makeni a gabanshi ba damuwarsu bane "Ke Kuma daga l'na aka rarumoki kasan de bama bukatar 'Yar aiki ko?" Arab yace "Kai! Kai!! Ya isheni haka haba!! Duk kunbi kun cikawa mutum kunni..." ZAINAB tace "Heee Tsaya nima kana cikamin kunni Bayani zaka Mana wacece wannan?" Ta karasa maganar tana jawoni "ku zauna na muku bayani to" Zama sukayi a kasa dukkansu domin kujerun ma an turasu gefe tsaban fitina da bak'in kishi i'rin nasu.
Seda ya jawo D'aya ya zauna domin be i'sa yace a kawo mishi abin Zama ba yana Zama ko sauke numfashi beyi ba Nafisat tace "munajin ka" Arab yace "yanzun ko arzikin ruwa da abinci bazan samu ba..." Fure tace "Kai kai dakata lbrahim babu baiwarka anan ka Mana bayani wannan" nunani tayi Arab yace "Matatace.." wayarshi ne yayi kara mikewa yayi tare da fad'in "Ku bata abinci da masauki inna zuwa" fita yayi da sauri yana Kara wayan a kunninsa.. a sukwane Fure ta tashi hannuna ta kama "ke fad'amin Gaskiya Wai da gaske Auro ki yaje yayi ko sadakarki aka bashi domin nasan halin mijina seya wanke hannu kafin yake zab'o mace kalle ni da kyau ki kalli sauran kin gammu da muni?" Girgiza mata Kai nayi Nafisat tace "fad'amin da gaske ke matar shi ce?" Shuru nayi Zainab ta zaburo tare da daka min tsawa "Ke ba magana ake Miki ba!" Da sauri nace "Eh Eh matar sa ce ni..." Ai ban rufe baki ba naji ta d'aukeni da mari fau.. har seda gefen bakina ya fashe da sauri Nafisat tayi kichin galan d'in karanzir ta d'auko tashiga zazzaga min a jiki Zainab ta cire min himar ihu nasa Fure taje ta d'auko a shana Tsayawa tayi tana karemin kallo "in banda maza ma da shegen jaraba uban me zeci a jikin wannan yarinyar Qirji a shafe ba cinya ba sharab'a Yau zakije lahira in aka tambayeki ya'akayi kikazo a haka kice *Matan Mu'azzan Balarabe* ne suka jefoki baki shirya ba tana shirin k'yatta ashana ya shigo a guje dan tun a waje ya fara jin hayaniyan su yana doson kofan yaji ihu na abinda yasa ya shigo a guje ke Nan ture fure yayi ta fad'i ragwajan kafin suyi wani Yunkuri ya d'aukeni kaman yar Baby da sauri ya fita Zainab da Nafisat ne sukabi bayanmu "Bud'e min Get da sauri" makuli yasa ya bud'e motan domin gudun ma be karb'esu ba Sabida Kiba Ta gurin Direva ya turani a kujeran gefe motan ya shiga yaja kofan a guje yaja de de lokacin da suke karasowa da gudu suka rufa mishi suna nishi "Zainab tace zaka dawo ka same mu wallahi" juyowa sukayi kowa na zuba masifa a bak'in kofa suka samu Fure'atu "Ina suke?" Cewar Fure Nafisat tace "Ya tafi" Fure tace "aikuwa ze dawo ya sameni" Zainab tace "i'rin ke kad'ai ce matarshi dole ya dawo ya sameki ai"




Maman Faruq
12/26/23, 8:58 AM - UMMI JB: *SIRRIN ƊAUKAKA*

_Wattpad@ayshajb_


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*





Page4 .


............Yana tuƙi yana shafa goshin shi‚ domin kofin Da aka jefo masa harya fasa mishi gurin Tausayi ya bani har bansan lokacin da na cire D'ankwalin kaina na mika mishi ba cikin masifa yayi magana "Ke dallah barni wannan kayan karanzir d'inne zansa a jikina Allah ya kiyaye duk ba ke kika jawomin wannan fitinan ba" Shuru nayi tare da mayar da d'ankwali na‚ kuka nasa inna mishi ihu harda dukan kujeran da nake kwance "Wallahi baka i'sa ka d'aukoni daga garinmu ka kawoni cikin wannan kattin banzan ba ance maka bani da gata ne! su sumin kaima ka fasamin kai da ihun ka wallahi kamayar dani inda kad'auko ni" gaangarar da motarshi yayi tare da tsayarwa "Ke! Da kike maganar kina da Gata uban waye gatan naki inba ni ba haba! wannan wacce i'rin masiface haka ! karna kuma ji kin kiramin matana da Katti inba haka ba wallahi zakiji a jikinki" wallahi bansan ina da masifa ba se yau "Allah ne gata na domin kai ba gatana bane , matanka kuma nace katti kayi duk abinda zaka min kai! nifa ba jakarsu bane da zasu fasamin baki wallahi sena rama kuma karka karacemin masifa domin ka barosu a baya kuma zaka koma ka taddasu domin na rantse da wanda raina ke hannunsa baka i'sa kamar dani wancan hargitsattsen gidan ba, Gidan jahilai wanda basu san kishi ba..." fauf ya bigemin baki "Allah ya isa kai kaci zalina matanka suci Zalina akwai Allah wallahi kuma seya saka min tunda ban muku komai ba" inna fad'ar haka naci gaba da kuka Na shikuwa shuru yayi ganin haka yasa nace “Nifa bansan amfanin tsayuwarnan da kayi ba in baka da inda zaka kaini ka bud'emin mota na fita.." Hannu ya d'agamin tare da d'aukan wayarshi dake kara tun d'azu “Adam wallahi akwai katon matsala kaina duk ya kulle bansan Ya zanyi dasu..." Nan ya kwashe komai ya fad'a mishi me Adam zeyi kuwa in banda dariya matarshi dake gefe ta rik'e baki tana kallon i'kon Allah Arab yace “Kaga malam banson hulak'anci ya zan fad'a maka abinda sukamin maimakon ka bani shawara se ka b'ige damin dariya mahaukaci ka mayar Dani?”
Adam yace “a a yi Hakuri yanzun kuzo Gidana Amma kafin nan ka siyo mata wasu kayan da Zata canza” Arab yace “Toh” duk inna jinsu kala bance mishi ba ya tada motar munyi nisa da tafiya kafin ya tsaya kusa da wani kantin kaya inna zaune a cikin mota ya fita ya siyo ya dawo tafiya kad'an mukayi se gamu a kofar wani madedecin Gida Adam d'inne ya Bud'e Mana Get yana gama faka mota ya fito Arab yace “Wai kai har yanzun bazaka sa megadi ba? Kafi so in kayi bak'i kazo ka bud'e musu get in Kuma ka fita Ruma ce zata bud'e Get yanzun Kuna jin dad'i rayuwa haka?” Adam yace “Taya zansa megadi ya ringa kalle min mata a a wallahi inna kishin matata rayuwarmu a haka yayi in nafita na dawo tazo ta bud’e min kofa ina dalili" nik'an da zaman motan ya isheni na shiga bubbuga glass da sauri Adam ya bud'e min na fito wani uwar harara na maka musu kafin naja gefe na tsaya gaba Adam yai yana dariya “Arab ka Tara mata kutt kowa da guntun nata rigiman muje ciki" Matarshi Ruma na zaune ta amsa sallamarmu da fara'arta Zama nayi a kasa tare da fasa ihu Arab yace “Kefa na lura mahaukaciya ce karki tasar musu yara suna barci...” birgima nashiga yi ina duk'an kasa “wallahi ni ba mahaukaciya bace sede matanka sune mahaukata nide dan Allah kuce ya mayar dani garina na fasa Auren zan biyashi kud'insa” Hannu ya d'aga ze mareni Adam ya rik'e shi “Haba Ya zaka huce akan karaman yarinya marainiyan Allah wannan ba yi bane Gaskiya koda wasa karka sake marmarin D'aga hannunka zuwa jikinta Su sauran matan naka kana duk'ansu ne?” zaune na tashi “Wallahi daka barshi ya dakeni tunda na Zama jakarsu kalleni fa jikanin sukayi da karanzir zasu k'onani bayan sun fasa min bak'i shima dan rashin imani ya sake bug'emin bakina Allah daka barshi inya dakeni zan rama ai ba jaka bace ni‚ in Kuma Kuna ganin banida Gata babu me tsayamin dan,ni talakace akwai Allah zan Kai mishi karar ku tunda ba zaku iya duba maraicina ba” tausayinta ne ya kamasu maganarta Kuma gaskiya ne Ruma ta Mike tare da kamo hannuna “Kiyi Hakuri Jiddah Allah ze saka miki zo muje kiyi wanka se kici abinci” Mikewa nayi nabita “Gaskiya abokina abinda kayi kaida matanka be kamata ba yarinya karama zakusa a gaba haba Mu'azzan bansan ka da duk'an mace ba” Zama Arab yayi tare da dafe kai “Ni wallahi Adam bansan mesu Nafisat sukeso dani ba, kullun burinsu suga hankalina a tashe sun mayarmin da Gida kaman filin dambe ban isa Kuma na hanasu su hanu ba ya zanyi ne wallahi nagaji kasar zan barmusu na huta da wannan fitinar‚ Mata Uku ko Gobara?” ..
“Wallahi ka i'sa ka Hana Kuma su hanu inhar kaci gaba da nuna musu kana tsoronsu abinda zasuyi maka Nan gaba seya fi haka‚ Ga abinci kaci kaima se kayi wanka” Band’aki ta kaini Tsayawa nayi inna bin gurin da kallo kwab'a baki nayi zanyi kuka tace “Ya salaam! Meye Kuma?” Seda na gama cire kayana kafin nace “toya zanyi nayi wankan?” bata ja da tsayi ba tamin wanka tsefe kitson da yafi wata uku tayi tare da wanke min kai mun dad'e a bayin domin Gaskiya ta wankeni sosai Kuma na wanku sede hasken fatata ta fito tana wankeni tace “Masha Allahu Tubar khallah Ibrahim ta zab'o mana kala me kyau wankan tarwad'a” babban tawul ta bani da sufe jikina yayinda take goge kaina da karami seda ta busar min da gashin da wani abu ko menen oho gurin Jane na ringa mafa ihu domin da zafi Nan da Nan gashina na sake ya kwanto har wiyana‚ ga shi baki sid’ik Mayuka masu khamshi ta shafani dasu “Jirani inna zuwa” Falo taje Amma babu kowa ledan dake gurin ta bud'e Nan taga kayane doguwan riga me ruwan zuma ta d'auko da d'ankwalinsa Duk ta duba kayan babu kanfe dole cikin kayan yaranta ta samo karamin wando nasa Himar ta bani nasa Nan nashiga yin sallolin da banyi ba inna idarwa ana Kiran isha‚ sallan isha'in nayi naso inyi shafa'i da hutiri sena tuna inna tashin dare Dalilin da yasa banyi ba Kenan Zama nayi inna lazumi se takwas da rabi‚ nabar saman Sallayan duk abinda nake Ruma tana kallona ji kawai tayi na birgeta barinma yanda nake abubuwana cikin nutsuwa “Zo muje kichi abinci” Bin ta nayi har falon d'azun zama nayi a kasa ta zubomin tuwon shinkafa da miyan taushe se farfesun kayan ciki.
inna cikin cin abinci Ruma ta fara min fad'a “Jiddah karki Kara d'agawa Arab murya in yana fad’arshi in bazaki iya ce masa yi Hakuri ba karki kuskura ki tanka masa Sannan ki Dena ce mishi kin barshi da Allah Kinga babu kyau yima babba rashin kunya matsayin miji yake a gareki tunda wa'yancan banzaye sun kasa rik'eshi inna so ke ki rik'eshi ki jawoshi a jikinki sosai ki zama me share mishi hawaye a duk lokacin da yake kuka da halayyarsu ki zama maganin damuwarshi karki Kara d'aga mishi murya domin babu kyau mace ta ringa d'agawa mijinta Murya sannan innaso in yazo kice ki tsuguna har kasa ki bashi Hakuri matan shi Kuma babu runki dasu ki Dena ce musu katti Kinga sun girme Miki tsakaninki dasu mutumtawa da girmamawa Kinji” tunda ta fara min nasihar Nan nayi shuru ji nake kaman mamana ne take min magana cikin sanyi murya nace Mata “To nagode Mama Amma dan Allah kice ya Dena dukana iyayena har suka rasu babu Wanda ya tab'a dukana Kuma kice mishi ya Dena cemin mahaukaciya bana so kalman yamin zafi” sharemin Hawaye Ruma tayi kafin tace “insha Allahu bazai Kara ce Miki mahaukaciya ba matukar kikayi abinda nace miki Kinga anan zaku kwana Kuma d'aki d'aya inna so idan kunje kwanciya kice mishi ya yafe miki bazaki sake ba, Kuma Gobe ze kaiki Zaria ki gaida mahaifiyarshi daga Nan ze kaiki Kaduna Gidan Yayarshi i'ta zata rik'eki zata zame Miki uwa da uba domin malamace zata koyar dake abubuwa kala kala Dan Allah banda rashin kunya ki Mata biyayya kinji” Gyad’a Mata Kai nayi kafi nace “Amma kince d’aki D'aya zamu kwana Kuma babu kyau fa...” katseni tayi “Ai mijinki ne da kaman ba mijinki bane shine za'ace babu kyau” ..
Kafin na Kuma cewa wani abu se gasu sun shigo kasa kasa na kalleshi Nan naga ya canza kaya da alama shima yayi wanka tab'ashi Adam yayi tare da yin magana kasa kasa “Kai Arab kaga Amariyarka kuwa Gaskiya ka samu mata Ashe haka take da kyau” Had'e Gira Arab yayi ba tare da yace komai ba sema satar kallonta da yakeyi batare da anlura dashi ba ‚ Zama sukayi Arab yace “Sannu da kokari Ummuh Rumana” murmushi kawai tayi ba tare da

Please Login or Register in order to submit comment