Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kina cikin danginki sai dai ina jin babu daɗi ganin kinyi nesa dani nasan ba lallai kuma su sake bari ki zo...”
“A'a ummi karki ce haka ina nan tare dake zaki dinga gani na akai akai Ummi bazan taɓa mantawa da uwa kamarki ba, Ummi kinyi min komai wadda uwa take yiwa ƴarta shiyasa a kullum nake miki addu'a da fatan dacewa anan duniya da kuma lahira a duk lokacin da kike Son ganin Shalelen ki zata zo miki batare da kawo wani uzuri ba..” cikin burgewa Halimatu da Hanisa suke kallonsu daga ƙarshe suka saka dariya har Ummi ɗin, haka suka ci gaba da hira har dare kafin mazajensu suka zo ɗaukan su. Gida ya saura daga Ummi se yaran Halimatu tare Anwar Dan nan suke karatu suna taya Ummi hira kasancewar gidan babu kowa shiyasa suka dawo dan ɗebe mata kewa.
Hira sosai mukayi da ummi inda ta dinga min nasiha tare da bani addu'o'in, sai da akayi kwana shida ana gobe bakwai tukun muka ji labarin mutuwar Zainab wanda seda na gigice domin yadda Nafisa take faɗawa Ummi lamarin ya ɗaga hankalin mu, a ranan Ummi ta nufi Abuja gida ya saura daga ni se yara sai kuma Nabil daya tare min duk ya hanani saƙat kwana goma Ummi tayi kafin ta dawo nan ta same ni kwance ina fama da zazzaɓi “Ummi sannu da zuwa ya ƙarin haƙuri kuma? Ubangiji ya gafarta mata Allah ya mata rahama”
“Allahumma Amin Jiddah sannu ya jikin naki? Nabil yake sanar dani rashin lafiyan ki meyasa bakuje asibiti ba?” lumshe ido kawai nayi ina jin yanda cikina ke juyawa “Kinga bari na kira Nabil ɗin yazo muje asibiti..” dakatar da ita nayi ta hanyar faɗin “A'a Ummi ki bari har ki huta mana” dakatar da ita Ummi tayi tare da kiran Nabil nan suka nufi asibiti gwaje gwaje da Aune aune suka shiga mata ƙarshe de gado aka basu dan yanayin jikin nata sai a hankali sai washe gari, sakamako ya fito da wani irin murna Nabil ya rumgumeta yana faɗin “Alhamdulillah Allah na gode maka ashe ina da rabo nima Thank you for the last night Thank you Fadilah Dan nasan a gidan ki muka samu Baby...” Ai fita sukayi gabaɗaya har Ummi domin Nabil kan ya zama mara Kunya sosai sukayi farinciki ganin tana da ciki gashi yana ɗan bata wahala sai da ta kwana uku aka sallamesu bayan kwana biyu suka fara shirin tafiya saboda mutanen Chadi sun matsa sosai akan su koma badon taso ba haka ta fara shirya kayanta sauran kwana ɗaya tafiyarsu Arab ya zo tare da Aakif da wani irin murna ta rumgume ɗanta harda hawayen farinciki cikin tsananin jin daɗi shima yace “Umma na! Shine kika barni bakya zuwa gurina da Abba na!” shuru kawai tayi tana shafa kan yaron tare da kissing fuskanshi “Kayi haƙuri Aakif amma yanzun in sha Allahu komai ya wuce ina tare da kai zamu kasance tare har abada”
“To umma meyasa ba zaki zo mu zauna tare da Abba na ba?” miƙewa Nabil yayi dan basu damar ganawa da juna sosai, da kallo ta raka shi se take ga kamar maganar Aakif ɗin ne ya ɓata mishi rai Nan ta shiga mishi faɗa tare da faɗa mishi babu wani sauran zama tsaninta da baban shi hasalima tare zasu koma Chadi yaje yaga family ɗinta sannan zai zauna gurinta “Wallahi bani zuwa ko'ina batare da Abba na ba...” buge mishi baki tayi tare da faɗin “wani irin tarbiya ce wannan? Ina ilimin da ake yabon ka dashi? Ni mahaifiyarka ina faɗa kana faɗa Abokiyar wasan ka ce ni? to ka buɗe kunnuwanka da kyau gobe tare zamu tafi” shigowa Ummi tayi tana faɗin “Ya ya meya faru nake jin tashin muryan ki?” cike da jin haushin abinda Aakif yayi mata ta sanar da Ummi kallon Aakif Ummi tayi kafin tayi wani magana ya rigata “Ni wallahi babu inda zanje batare da Abba na ba..” Ummi tace “A kul! karka sake kuskuren ɓata mata rai kasan damuwa da ƙuncin data shiga duk saboda kai? Kasan irin wahalan data sha kafin ta saba rayuwa batare da kai ba? Haba Aakif ban sanka da wannan halin ba..” “Ummi ai bata sona inda tana sona to meyasa tayi wani Aure? taje tana jin daɗi ni kuma ta barni har wani baby aka ce zata haifa ni gaskiya bazan je ko'ina ba tayi tafiyarta kawai tunda tana da wani Mijin” Kuka Jiddah tasa tana kallon yadda yake magana yana cika yana batsewa tare da tamke fuska kaman bashi yayi maganar ba “Ummi kina ji ko? wai dan Allah meyasa rayuwa take juya min baya? tsawon shekaru ban saka shi idanuna ba, duk kewarsa da nayi da irin kalaman da zai tare ni kenan wallahi nima yayi zaman shi bani zuwa dashi ko'ina bare yaje yana rena min miji..” Ummi tace “Kaci gidanku ka duka kaba mahaifiyarka haƙuri ina ruwanka da Auren ta! laifi ne dan ta rabu da mahaifinka kai baka san ƙaddara bane? Kayi gaggawan bata haƙuri kafun na saɓa maka shashashan banza, shi uban naka yasan da haka ya sake ta”
Kuka ya saka yana jin Haushin abinda Jiddah tayi domin shi duk a tunaninsa batayi wani Aure ba. “Kiyi hakuri amma gaskiya babu inda zanje bazan iya zama inda babu mahaifina bare ayi mini Kallon agola...” “Innalillahi ummi kina jin abinda yake faɗa ko? irin abunda nayi gudu kenan tun farko gashi an ɓata min yaro babu tarbiyan arziki nasan da tun farko yana tare dani da hakan bata kasance ba Dan Allah Aakif karka ƙara min damuwa kayi hakuri Nabil ɗan'uwa nane ina Son mijina shima Abban ka ne tunda Yayana ne...” “Ni ba Abba na bane kuma na faɗa bani zuwa ko'ina kawai kiyi Haƙuri in da rabo wata rana zanzo amma banda yanzun Kina son mijinki Nima Ina son Abba na” duk yanda taso ya fahimce ta yaƙi sauraronta tayi lallashi ita da Ummi amma ina ya kafe akan babu inda zaije karshe haka zuciya ya ɗibeta seda ta kikkifa mishi mari Amma ko a jikinsa ranan tayi kuka sosai a dalilin haka ta ɗaga tafiyan tana tunanin ko zai sauko ya saurareta da safe ne suka gaisa da Arab inda take mishi ta'aziya kallonta yayi tare da murmushi yana amsawa zuciyarshi a sake domin yanzun baya jin wani rigima ko tashin hankali “Amma gaskiya Yallɓai banji daɗin tarbiyan da aka yiwa yaron nan ba, ya za'ayi ina magana yana magana sam banji daɗi ba”
“Kiyi haƙuri insha Allahu zai zo tunda yanzun yaƙi ki ƙyaleshi zan lallaɓa shi” cikin tsananin fushi Jiddah tace “Bana son a sangarta min yaro bana son goyon sangarci a bashi tarbiyan data dace bayan haka ina maka fatan alkhairi Allah kuma ya sada mu da Alkhairinsa bana jin zamu sake haɗuwa ban sani ba ko Bikin Jumana idan me gidana ya yarda to, dan Allah ina sake jaddada maka a kula a san irin tarbiyan da za'a dinga bawa yara” daga haka sukayi sallama har ta juya tana tafiya sai kuma ta juyo tana kallonshi tare da ɗan sake fuska “Na gode Jiddah ina miki fatan samun farinciki me ɗorewa a rayuwarki Allah ya sani ina Ƙaunar ki babu yadda na iya ne”
Ɗauke kanta tayi sakamakon ganin Nabil dake tsaye nesa dasu yana jiranta ba tare da tace mishi komai ba ta nufi gurin mijinta.
Kwana biyu tsakani suka tafi ita da Nabil Aakif kan ya kafe babu inda zashi.
*** ** ***
Sun isa lafiya inda kowa ya shiga nuna mata soyayya tare da kulawa na musamman lokacin da suka samu labarin Juna biyun da take ɗauke dashi sunyi murna sosai haka ma Nuwairah tayi matuƙar murna tare da Addu'a Allah ya bata in tana da rabon Haihuwa Mama-sadin ma tayi murna sosai sai dai taji babu daɗi na rashin zuwan Aakif a hoto kawai ta ganshi amma duk da haka bata cire rai da zuwan nashi ba, tattali soyayya ƴan'uwa da soyayyar miji tare da Ƴar'uwa ta Abokiyar zama su suka sake kwantar min da hankali yanzun bani da wata damuwa wadda ya wuce Allah ya sauke ni lafiya kullum muna magana da Ummina ta video call su Halimatu ma haka, Hanisa yaranta Biyar yayinda halimatu take da huɗu, wata tara da kwanaki Allah ya sauke ni lafiya inda na samu Asma'ulhusnah rayuwata a Chadi cikin dagina abun farinciki ne, muna zaman mu lafiya babu me jin kanmu ban samu zuwa bikin Jumana ba amma na yiwa Nafisa aike daga ɓangaren dangin Mahaifina ma muna waya sosai kuma ina tura musu da duk abubuwan bukata ban manta da mutanen da suka tallafi rayuwata ba kamar matar me anguwa da mijinta ina musu alkhairi daidai gwargwado a baki Nuwairah nake jin labarin Aaliyah ta haihu ɗa Namiji sai dai tana cikin wani yanayi daga ita har iyayen nata sakamakon karayan arzikin da suka samu to daman dukiyan nawa ne, a wani zuwan da nayi Nigeria ne na aika mata da kuɗi tare da sutura da kayan Abinci domin ni ba mace bace me riƙo kuma ban nufi kowa da sharri ba , domin kullum ina cikin kariyar ubangiji ina addu'a sadaka domin ita maganin duk wata fitina ce, Husnah nada shekara biyu na haifi Abdallah takwaran Abba. Nuwairah kan Allah bai bata ba, domin wani hanin ga Allah baiwa ne..
END
Ƙarshe.
ALHAMDULILAH!
Anan na kawo ƙarshen wannan labarin ina roƙon Allah daya yafe mana kurakuren mu. Allah kuma ya bada ikon amfani da darasin dake cikin littafin, dani daku Allah ya bamu ladan dake cikinsa Na gode ƙwarai, Na gode sosai da jimurin jira, ina ƙaunarku dan Allah🥰❤️ kamar yadda kuke sona nima ina Sonku irin sosai ɗin nan idan nace sosai ina nufin Sosai!!! Jama'ar Wattpad Ina gaishe da kowa Son so domin ALLAH😍🤝 sai mun haɗu a sabo..


Taku ce har kullum ƴar mutan BENUE A'isha JB






*Maman Faruq*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment